Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taja maka, komai , kayi gsky bakayi k'arya ba"

Akram da mamaki lulub'e a fuskar shi yace kana, nufin kace min kai d'an uwanane. Kuma kaima wannan mazinaciyar ce...."


Daka ma 'akram tsawa Dr Samir yayi,

"Kai ,kana da hankali kuwa 'kasan me kake fad'i duk lalacewa dai 'ita ce mahaifiyar ka , karna sake jin haka".

Akram na hawaye yace.

"Mahaifiyar k'adaddara ba, wannan matar tacuceni arayuwa, wlh bazata, shiga 'Aljana ba, Allah ya isa tsakanina dake ".

Tari Dr Samir ya soma yi don furucin akram sun fara tab'a masa zuciya baze iya jure jin suba.

Duk yanda 'akayi bugun da yayi akan shi sun tab'a masa brin d'in shi , tari yake sosai har yana shid'ewa duk tarin daze fitar sai jini ya zuba ta hancin sa, Salma da Khadee ne sukayi saurin taimaka masa ,sukabar d'akin dashi, Ummi ma bayan su tabi.

ITako Hajar ta kasa koda motsa d'an yatsan k'afar tane bare ta, tafi tana daskare agurin.

"Hajjo na zalun ceki Allah ma ya sani pls ki yafe min ko zan samu ,sassauci arayuwa ta, nayi nadaman rayuwa ta , don Allah ki ,kawo min yata na ganta ko sau d'ayane arayuwa ta kafun ,nabar duniya."

Sai alokacin wani k'arfi ya zowo Hajar ta juyo ta kaleshi daga shi ,har mahaifiyar sa,

Wata dariyan takaici ta saki tace

"Yanzu kai bakaji kunyar cewa kana son ganin yar kaba, waya baka ita? Ita ina ka samo ta? Ta hanyar zina ? Kasan duk zakaje ka 'amsa wainan tambayoyin kow?.

Tow kasani wlh !wlh!!wlh!!! Har abada,bazaka tab'a sanin taba kuma bayar ka bace,

Maganar hakuri kuma, baka cencenci nayafe maka ba kuma baka isa na yafe maka ba, kuma baka ,kai matsayin da zan yafe maka ba, zan yafe makane kawai saboda nayi koyi da fiyayyan halitta 'Anabi muhamadu, dayace damu ,muzama ,masu hak'uri a inda mukasan muna da k'arfin ramawa , mu zama. Masu tawakali ,kaji dalilin dayasa zan yafe maka.

Ko yanzu Alhamdulilah Allah ya bimun hakina, ko yanzu addu'a ta ,ta k'arbu , ko yanzu Burina ya ciki.

Dama bani da Burin daya wuce naga ka wulak'anta 'aduniya ka tozarta 'aduniya bama kai ,kad'ai ba da ,duk wanda 'aka had'a baki dasu, ko a haka 'Allah ya barka wlh ya rama, min kuma kad'au darasi bama kai d'aya ba harma da masu Hali 'irin ,naka.

Sai kuma kajira hukunci da Ubangiji zaiyi maka tsakanin ka da y'ar ka".

*(Rayuwa ba komai bace face makaranta , kuma litattafi ce wace idan ka bud'e wannan babin ka ,karance shi tow gobe bashi zaka bud'e ba wani daban zaka ,gani, yan uwa musani cewa duniya ba wajen zama bane aro aka bamu kuma yanda mukazo haka zamu koma.*

*Ku sani cewa mutuwa bata salama, zuwa takeyi aduk sanda lokacin zuwan ta yayi, mezai hana mu watsar da, duk wani rayuwan duniya mu rungumi abunda 'allah ya turo muyi.*

*Da yawan mutane sukan manta, cewa 'akwai mutuwa ,akwai ciwo akwai k'adaddara, suyi ta shuka tsiyar su a duniya, suna tunanin ,nan gaba zasu gyara*.

*Basu ,san cewa lokaci k'urewa yakeyi ba rayuwa k'arewa takeyi ba, sai sunga 'abu ya jagule musu kuma sai ,su fara neman Ubangijin su, bayan lokaci ya riga daya k'ure musu, damar su tariga data kufce musu*

*Da wannan ,nake tunatar da yan uwana musulmai da mufarka daga baccin da mukeyi , duniya ba wajen zaman ,mu bane*

*Ubangiji kasa mudace, kasa mufi k'arfin zuciyar mu*)

Tana kaiwa nan ta kama hanyar fita jin anrik'ota yasa, ta ,tsayawa.

Maida hankalin ta, tayi kan wanda ya rik'e mata k'afa ganin Maman Akram yasa ta jin wani bugun zuciya.

"Hajjo kad'in daban ce, cikin mutane, ba kowani mutun bane ze iya ,abunda kikayi a yanzun , mun gode Allah ya ,yimiki Albarka.

Tababbas Akram beyi k'arya ba, nice sular gurb'acewar tarbiyayyar sa, nice silar shigarshi duk wata ,matsala, nid'in karan kaina ,nasan ba 'uwa ta gari bace, na kasance mace meson abun duniya, na zalunci abokiyar zamana tare da mujin mu , na kasance mace meson kanta da yawa, arayuwa zan iya komai akan ,kud'i.

Yau jibi yanda 'Allah yayi dani, abubuwan dana shuka ,su nake girba, kaico na kaico da masu hali 'irin ,nawa , bansan makomata ba ,wlh ban san matsayina 'agurin ubangiji naba.

Saboda ni, nasan ,nayi abubuwa dadama na zunubi arayuwa ta, Hajjo nima dole na ,nemi yafiyar ki saboda nice anadin komai nice sula , don Allah kiyafe min".

Hajar nason tayi kuka 'amman ta danne zuciyar ta, wani dariyan takaici ta kuma sakewa tace.

"Karki damu ,Mama nikam ,nayafe miki duniya da lahira, fatan da nike miki dai shi Ubangiji ya, sau-sauta miki, ya kuma yaye miki zunuban ki ,na barku lafiya".

Tana kaiwa nan ta fice daga ,d'akin ,komawa Maman Akram tayi gareshi, ta dinga bashi ,hak'uri da neman yafiya 'akan irin tarbiyayyar data bashi dak'er ya 'amence ya ,yafe mata, yan sanda ,suna jiranta bakin k'ofa ,sun barta , zuwa gobe zasu tafi da ita.

**

"Talatu kamar akwai abunda kike shiryawa , kwana biyu sai naga kina ta murmushi ke d'aya".


Wani shu'umin ,murmushi Talatu, ta saki tace.

"Susu , akwai dalilin wannan murmushin ,nawa 'Amman ki bari zuwa jibi zaki gane manufar ,murmushina, zan shayar daku madaran mamaki, ke bama ku ,kad'ai ba har dangin mu gaba d'a ,wlh sai na yi abunda zasuji kunya muje zuwa"


Murmushi Susu tayi tace.

"Kidai bi ahankali Talatu nasan halin ki, kuma kinsan baki shike ,karya wuya, ki dena fad'in haka ,kad wani abu ya faru 'a dangi ace kace".

"Tow sai me Susu afad'a idan anfad'a tsiro zemin ? Koka mutuwa zanyi? Koka shize hanani cigaba da walwala ?".

Girgiza kai Susu tayi tace.

"A'a ko d'aya 'amman ,nidai nace miki ,kibi duniya 'asani ,kinfa girma Talatu kefa ba yarinya bace ,yakama 'ace kinwa kanki ,karatun tanutsu, Alhaji Hadi ya jima yana k'aunar ki ,kin tsaya shirmen banza da hofi, Umma tayi maganar har tagaji, ta zura miki na mujiya 'Abba ma kafun ya rasu ,yayi yayi ,ya gaji, muma ,munyi munyi mun gaji haba Tali kiyawa kanki fad'a tunkan lokaci ya k'ure miki".

Talatu idon ta cike da bala'i da masifa tace.

"Eyee lalle Susu wuyanki, yayi kwari ya isa yanka, yanzu ni kike fad'i ma haka?, tow dan gidan ku bazanyin ba ko ,ina da ,damar da zaki min, ne? ,shasha kawai".

Tana kaiwa nan tabar d'akin tana jan tsaki.

*
"Sanu Dr Allah ya baka lfy ni zan wuce gida, dare yayi ,insha 'Allah jibi zamuyi masa'Aiki Captian idan akwai wata matsala zaka iya kirana ".

Khadee na gama fad'ar haka ta kwashe komo tsanta, tayi gaba.

Shiko Dr Samir a halin da'ake ciki ma baya iya magana, sai da kawai ya d'agawa mutane hanu ,

Wurin k'arfe tara na dare lokacin Dr Samir yana bacci Maman Akram tazo ,ta dubashi sanan ,suka zauna sukayi doguwar magana da Ummi , sosai Maman akram ta nuna mata, nadamarta 'afili sananna ta nemi gafaran ta, daga nan kuma ta, tambayi abunda ke damun Dr Samir babu abinda Ummi ta b'oye mata ,ta gaya mata koma.

Jin, jina kai ,kawai tayi ,tana me ganin k'okari da juriya irin ,na Dr Samir.

Koda ta koma d'akin Akram bata b'oye masa komai game da'abunda ke damun Akram ba
.

Jin ,jina kai yayi lokaci guda ya fara hawaye ,yana duban Maman tashi da ido yace.

"Mama daga safiya zuwa yanzu ,nayi kuka babu adadi, nayi nadama babu adadi, Mama jibi yanda rayuwata, ta koma.

Ina son tashi na kasa ina son juyi na kasa, ina son inji 'ina motsa kafafuna da hanayena 'Amman babu dama.

Yau mun wayi gari bani da k'afa ,d'aya bani da hanu d'aya , bazan kuma tashi ba, wannan yana ,nufin haka zan dawama har k'arshen rayuwa ta,

Wannan yana, nufin bazan kuma ,moruwa ba, ina son ,naje naga d'an uwana 'amman babu dama ina son ,naga d'iyata koda sau d'ayane a rayuwa ta, Amman hakan bame yuwa bane.

Duniya kenan ,duniya makaranta , rayuwa 'abin tsoro, wato shi rayuw kamar pencil yake ahankali yake cinyewa har yazo k'arshe, Mama da ina da hali dana gyara kuskure na, pls mama kimin ,magana da 'wannan abokin d'an uwan ,nawa da kuma ,mahaifiyar shi 'ina son magana dasu kafun ,na cika."

Yanda ' Akram d'in ya buk'ata hakan tayi Amman Captian dak'er ya, yarda yaje Saida Ummi tasa baki tukun.

*

Idon shi na rufe ya kama hanun Captian yace.

"Naji irin sadaukarwan da kayiwa d'an uwana , kuma hakan yasa naji dad'i, mungode mungode Allah yabar zumunci.

Amman ina, neman wata 'alfarma guda ,d'aya 'agurin ka ".

Yana kaiwa nan yayi shiru.

"Ina jinka ".

Captian dayaji shirun yayi, yawa ,yace haka.

Saida 'Akram ya busar da iska daga bakin shi, ya sauke wani ajiyar zuciya, sannan ya sauke idanun shi kan Captian yace.

"Ka barni ,na bawa Samir k'odata, pls ina son , nima naga nayi masa wani abu 'arayuwa ta koda sau d'aya ne kafun ,nabar duniya"......







*By Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 45

"Ina son ,naga nima na faran ta masa pls Junaid kayi hak'uri ka barni".

Hawayen da ya zubo cikin idon Captian ya goge, yana jin tsanar Akram har cikin naman jikin sa, yayi k'arfin halin cewa.

"Babu damuwa 'Akram d'an uwan kane, kuma kana da, damar da zaka iya bashi koma ,miye, Ubangiji ya baku lfy".

Yana kaiwa nan ya tashi ya mik'e ya fice daga cikin d'akin.

Ummi na kuka ta kama hanun Akram tace.

"Allah ya baka lfy Akram Allah ya saka maka da mafificin Alkairi akan wannan, irin sadaukarwa da kayi ma d'an uwan ka, Ubangiji ya baka ladan ,niya.

Allah ya ,yafe maka ,kura kuren ka, wannan jarabobi da kake gani k'addara ce Allah ya sasauta maka".

Akram idanun shi arufe yana wani'irin ,nishi yace .

"Ameen Ummi bana son cigaba da rayuwa 'anan duniya bana so , a yanzu nafi buk'atar mutuwa 'akan kome na rayuwan duniya, kuyi min addu'an cikawa da imani kawai shi nafi buk'ata 'ayanzun".

Ummi na kuka, tare da tausayin Akram ,jinshi take tamkar itace ,ta haife shi,

Hak'ika be samu 'uwa tagariba 'a rayuwan shi, da Mahaifiyar shi batabi son zuciya ba, da, duk hakan be faru ba.

Kama hanun shi tayi, tace.

"Tabbas Akram ,mutuwa itace zata ,zame maka hutu, a irin wannan halin da kashiga 'ayanzun,

Amman ,mud'in munfi son ganinka, a hakan da rashin ka, ba mutuwar ake tsoro ba'abunda mutuwar ze haifar ake tsoro bayan babu kai".

Murmushi Akram ya saki ,kawai ba tare da yace komai ba, hakan yasa Ummi ta, tashi ta fita, takoma d'akin Dr Samir.

Tana shiga ta samu Salma harta dawo daga, gida ta gyara musu inda zasu kwanta. Ta kuma taho musu da'abinci.

Dak'er Ummi ta iya shan, shayi shima saida Salma ta matsa mata sannan tasha badon tana jin dad'in shiba.

**

"Khadee ya jikin Dr Samir d'in hope da sauk'i ,kow?"

"Tow zan iya cewa da sauk'i Amman gsky yana jin ,jiki sosai, saidai fatan sauk'i kawai, nace Captian idan akwai matsala ya sanar dani koma yaushe ne".

"Tow Allah ya bashi sauk'i.

Wlh Khadee nifa har yanzu fad'uwar gaba ,nakeji sai nake tunanin kodai , akwai abunda ze kuma faruwa dani".

Dafa kafad'ar ta khadee tayi tace.

"Babu komai fa insha 'Allah kawai ganin Akram ,ne ya girgiza ki ,ki, kwantar da hankalin ki dan Allah,

Karfa ki manta jibi ne d'aurin auren ki".

Sai alokacin Hajar ta, tuna da ,d'aurin auren wani fargaba da tashin hankali ne taji sun kuma ziyartan zuciyar ta, lokaci guda taji k'irjin ta na dukan tara tara.

Jawahir dake ,kwance kusa da ita, ta kuma ,matsewa 'ajikin ta kamar wacce ake shirin kwace ta, lokaci guda ta fara tunani yanda 'Captian ze k'arb'i Jawahir da kuma, matsain daze sata.


Haka ta dinga sak'e sak'e har bacci b'arawo ya sace ta.

*
KARFE UKU DA MINTI D'AYA NA DARE

"Hajjo tashi ".

Kamar a mafarki taji k'iran Khadee , ba tare data bud'e idanun taba ta juya taci gaba da baccin ta, tana.

"Pls ki barni Khadee wlh dak'er na samu bacci ya kwashe ni".

Khadee na kanta, ta kuma cewa .

"Hajjo ki tashi muje Hospital Dr Samir ciwan shi ya tashi sosai, yanzu Captian ya kira ya sanar dani wai sumar sa 'uku, kuma sai wani'irin ,nishi yakeyi kamar ,me neman, mutuwa".

Babu shiri Hajar ta wangale idon ta, kamar ba ita bace wanan me gigin baccin,

Ko ,kallon Khadee batayi ba, tadiro daga kan bed tazari hijabi da key d'in mota, tace.

"Mutafi".....

Sauka ,k'asa ,sukayi suka ,wuce ko su ,Ummi basu ,sanar wa ba, suna zuwa me gadi ya wangale musu geta, suka fice.

Taka motar, take da mugun k'arfi cikin ,mintuna kad'an suka, k'arasa 'cikin asibitin.

Suna zuwa ,sukayi sa'a Dr Dived yana ,kusa be tafi ba, suka ,kira shi , suka had'a kayan aiki suka shigar da, Dr Samir wani d'aki , wasu na'urori suka fara jona masa, wanda saida ya d'auke su awa biyu suna yinshi, kafun suka gama , sannan suka saka masa ruwa da roban abinci , suka fito.

Ummi na ganin fitowan su ta nufo su ,tana kuka tace.

"Lfy likita ya 'ake ciki ya jikin ,nasa kozan iya ganin shi?".

Murmushin k'arfin Hali Hajar tayi tace.

"Kwantar da hankalin ki Ummi , jikin da sauk'i , insha 'Allah ze warke.

Yanzu bazaki 'iya ganin shiba harsai munyi masa'aiki zuwa gobe da 'azahar insha 'Allah zaki ganshi.

Yanzu mune kawai zamu iya shiga don, duba lfyn shi".

Ummi na kuka tace

"Tow mungode Allah ya biya ku, ubangiji ya bashi lfy "

"Ameen Ameen".

Cewar Khadee.

"Hajjo ".

Hajar taji Captian, na kiran ta yayin da zata wuce office d'inta , tsayawa tayi tare da fad'in .

"Na'am".

Saida ya matso daf, da ita sanan yace.

"Ya jikin Samir d'in?".

Kanta 'ak'asa tace .

"Jiki da sauk'i".

"Tow Allah ya k'ara masa lfy barin je masalaci na dawo zanzo ,office dinki muyi magana".

Ji tayi gaban ta na wani ,irin fad'uwa ,bakin ta na rawa tace.

"Tow sai ka dawo".

Ta wuce shima ya wuce




*By Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 46

Bayan ,ya idar da Sallar Asuba ya shigo ya samu Hajar ta kifa, kanta ,kan tabel.

Takawa yayi, ya k'arasa ya zauna sanan yace.

"Hajjo".

Sai alokacin ta d'ago, ta sauke manya manyan idanun ta kanshi ,tace.

"Na'am harka dawo ne?".

Da fara'a ,d'auke a fuskar shi yace .

"Eh har mun idar".

Kanta, ta sunkuyar tace.

"Yayi kyau".

Shirune ya biyo baya, saida ya gama nazari da tunane, tunanen sa ,sanan ya tsuke baki yace

"Hajjo dama, nazo da wata magana ce akan Aikin da za'ayi wa Dr Samir na dashin k'oda.

Tow da ,dai gsky kamar yanda nayi alk'awari nine zan bashi , k'oda ta, so yanzu kuma bani,bane".

Be k'arasa ba yayi shiru.

Shirun da taji yayi, ne yasa ta d'ago ta kalle shi tace.

"Ina jinka Captian ya kuma kayi shiru?".

Saida ya d'anyi jim kad'an sanan yace.

"Akram..."


Jin sunan Akram daya fad'a yasa taji wani fad'uwar gaba, lokaci guda taji yawun bakin ta ya k'afe , kafafun ta sun sage, k'irjin ta ,na wani ,irin bugawa da sauri da sauri, zuciyar ta na yi mata wani, irin k'una.

"Akram yace ze bashi, ya nemi Alfarman hakan daga wajena, ni kuma bazan iya ce masa 'A'a ba saboda ,d'an uwan shine".

Hajar b'oye damuwar ta, tayi tace.

"Hakan ma yayi kyau, Allah ya nuna mana ranar, ni zan koma gida, kuma daga yau balale, na sake fitowa ba, har sai bayan d'aurin aure.

So Khadee zasu cigaba da kula da, Dr Samir Allah ya bashi lfy".

Murmushi yayi ,yace.

"Ameen ,my wife Allah ya nuna mana, darai da lfy, anjima zan, zo".

"Tow Allah ya kaimu, tow shi auren Dr Samir d'in fa ya 'ake ciki za'ayi gobe,ne koko sai ya warke?".

"Da munce a d'aga kawai, Ummi kuma tace kawai a d'aura".

"Gara 'a d'aura d'in Ummi tayi gsky matar shi, ta cigaba da jinyar shi, har Allah ya bashi lfy ".



**

"Captian ya shirye shirye, da zirga ,zirgan asibiti".

Hajar ta, tambaya.

"Gashi muna ta fama dai, yanzu daga nabar nan gidan ku asibitin zan koma, idan ,naga ko mai na tafiya dai-dai sai na je na karb'o d'inki da zan saka gobe".


"Ae dama ka wuce gurin d'inkin, ka ,kawai don Khadee tace, min komai na tafiya dai-dai, kuma kasan bama samun ganin shi zakayi ba".

"Haka, ne sai na wuce d'in kawai,kinji wai zariya za'a tafi d'aurin auren ko?".

"Eh ,Haka Dady ,yace kasan wani kawun mune ze d'aura so baze iya zuwa nan kano ba, shiyasa Dad yace aje cen d'in kawai".

"Eh duk Abba ya fad'a min,ni wlh ,haka nan yau tun safe bana jin dad'in jikina, kuma sam duk abunda naci sai naji babu test, narasa dalili".

Murmushi Hajar tayi tace

"Nima dai haka, ni duk satinan ,ma haka nike jina wata iri wlh, sai nake jin akwai abun daze faru".

"Tow miye dalili hakan? Ubangiji kasa'alkairi ne ".

"Ameen dai ".

Captian saida yad'anyi shiru sanan yace.

"Tow kinga yanzu aure zamuyi Hajjo zamu shiga wata sabuwan rayuwa nidake, duk zunuban mu Allah ze wanke mana shi, hakan yasa nake rok'on ki da kiyafe min duk wani abu danayi miki arayuwa ,saboda ina so gobe ,na fara wata, rayuwan daban".

Murmushi Hajar tayi tace.

"Nikam bakamin komai ba, nayefe maka nima ka yafe min pls".

"Baki tab'amin komai ba Hajjo na yafe miki, ina Jawahir kwana biyu ban ganta ba?".

"Tana ciki".

Hajar ta bashi amsa.

"Pls d'auko min ita ,ina son ganinta kuma, mu gaisa."

Yanda yace tayi hakan tayi.


WASHE GARI

yaune Jumu'a za'a d'aura, auren Hajar da Captian da kuma Dr Samir da Salma bayan Salar jumu'a 'a Babban masalacin dake yankin zariya.

K'arfe goma da kusan rabi Salma ta koma gida, don d'auko wa Dr Samir kaya, don yau ne za'ayi masa ,dashin koda, k'arfe biyu dai-dai zasu shiga dashi dak'in tiyata, kamar yanda suka fad'a.

Tana shiga ,gidan sashen ,shi ta shiga Darec d'akin shi ta danna kai.

D'akin kaca kaca ,duk ya baza kaya'akan gado, zama tayi gefen gadon ta fara duba masa kaya cikin wanda suke zube agurin.

Tana d'aga wani ,wando ta hango diyari d'in shi ta d'auka.

Ju-juyashi ta farayi a hanun ta, wata zuciyar tana ,kibud'e ki ,karan ta wata zuciyar kuma tana kad, ki bud'e , cikin jakar hanun ta, tajefa shi ciki, tayi sauri ta zab'a masa kaya ta fice.


**

Sanye ,yake cikin wata dakakiyar shedda ruwan toka, yashi aikin hanu, Babban riga ce, sai ya sanya wata Zana buk'ar wacce zata shiga da kayan sosai, ya d'auki takalman shi mekyau da tsada sau ciki ya saka, ya fashe jikin shi da turaruka masu tsada ,da k'amshi.

Kanshi ya kalla jikin madubi.kayan sun balain masa kyau sajen fuskar shi sun kwanta luf, luf saman fuskar shi, ya wani k'ara kyau da haske ,sai dai kuma ya d'an fad'a , wayan shi daya fara, ruri ya d'aga yaga d'aya daga cikin abokan shine, d'auka yayi da Salama yace.

"Abdul ya 'akayi".

"Kaji ango tun ba'aje ko ina ba har ka fara cenza min ,murya".

Dariya Captian yayi yace.

"Kaga malam bana son wanan zolayar taka ya'akayi ne?".

"Babu komai dama,nakira nace maka, mund'au hanya ne tunda kace kai ,d'aya zaka taho, mukam, munyi gaba".

"Yawwa 'Allah yasa kuriga su Abba isa don suma sun d'auki hanya, mu kawai ake jira don ,iyayen Hajjo sun jima da isa, nima yanzu, zan fito insha 'Allah".

"Tow kade hanzarta 'ango sai mun had'u".

Ya tsinke wayar.

Fita, yayi daga ,d'akin shi yaje sashen Hajiya cike yake, da yan uwa da'abokan arziki, sai tsiya suke masa, beda kula suba har ya samu ya shige d'akin Hajiyar sa.

Zaune ya sameta, ana mata k'itso tsugunawa yayi har k'asa cikin girmamawa yace.

"Sanu Hajiya zan tafi".

Hajiya na zaune gaban me kitso ta juyo tace.

"Harka fito Junaidu, Allah ya kiyaye, kayi sauri kasan tun d'azu su Alhaji suka fita, kuma kasan baya son jira, ina ce ,cen d'in zakayi, yanzu".


Cikin girmamawa Captian yace.

"A'a zan biya gurin Dr Samir".

"A'a menakon ,ko bari sai kun dawo Junaidu?".


Girgiza mata kai Captian yayi ,yace.

"A'a hajiya kibarni kawai naje, k'arfe biyu za'a masa dashen k'oda ,kuma gsky bazan iya tafiya ban yi masa, salama ba ,nidai addu'ar ki nake buk'ata".

"Tow D'an lelena, Ubangiji ya tsare min kai yasa kuje a sa'a ku dawo a sa'a yayi maka 'Albarka, sai ka dawo kuma 'akula da tuk'i banda tuk'in gan,nanci".

Mik'ewa yayi, yace.

"Ameen Hajiya nagode kuma insha 'Allah ahankali zan tafi".

*

Captian yaje ya samu su Khadee sai had'a kayan aiki suke, kafun lokaci yayi, gurin ta yaje ya nemi Alfarman yana son yaga Dr Samir dak'er ta 'amince masa don, dokar asibiti ce babu me shiga wanan d'akin sai ,iya likitoci.

*

Kwance ya sameshi 'idanun shi biyu , yana kallon sama.

Kallo d'aya Captian yayi masa ya kauda kai, don baze iya kuma kallon shiba.

Duk ya rame yayi bak'i ya fita hayacin sa, kamar wani me ciwan H.I.V haka ya koma.

Jin k'amshin turaren Captian ya sashi kallon k'ofa , tsaye ,ya ganshi yana hawaye.

Cikin k'arfin Hali a hankali yace.

"Junaid lfy kake, kuka yau ranar farin cikin ,ka?".

Maganar tashi ma dak'er take fita.

Saida Captian ya matsa kusa da, Dr samir ya tsuguna jikin gadon shi yace.

"Samir bana jin farin ciki, kamar yanda zakayi tsamanin zanji, naci Burin wannan auren kamar ba gobe.

Amman rashin ka gurin d'aurin auren yasa naji komai baya min yanda ,nakeso .

Tun jiya nake jin fad'uwar gaba Samir bana son katafi ka barni, inaji ajikina kamar akwai abunda ze faru Samir, inajin ajiki ,kamar akwai wani babban abuda ze faru da kai ko dani.

Da ina da hali Da nace bazanje gun d'aurin auren ba, kodon naga lokacin da za'a shiga dakai da kuma lokacin da za'a fito dakai, Amman hakan baze yuwu ba".

Samir ayanzu kwata kwata baya iya Kuka baya iya hawaye saidai, ya d'inga jin zugi cikin zuciyar shi.

Wani abu yaji ya tsaya masa'a mak'oshin sa, lokaci guda yaji komai ya tsaya masa cak.

Dafa Captian yayi ,yace.

"Ka, kwantar da hankalin ka 'Abokina ka d'auka cewa komai dake faruwa muk'adaddari ne, da kuma wanda ze faru.

Ina so kayi 'imani da Allah kuma ya, yarda, da k'adaddara, ka d'auka cewa komai ba komai bane face jarabawa, idan Allah yayi zan fito dole ka dawo ka gani, idan Allah yayi zan tafi dole ka dawo ka samu babu ni.

Ko ,kana kusa dani ko baka, kusa dani dole indan lokacinane dole natafi.

Kuma ina so ka sani cewa cuta bata kisa, sai 'idan kwana ya k'are, zakaga me lfy ya tafi yabar mara lfy kaga wanan yana, nuni da cewa bafa sai baka da lfy zaka tafi ba.

Da wanan ,nake rok'on ka da katashi, ka tafi gurin d'aurin Auren ka, kad lokaci ya k'ure, Allah ya baku zaman lfy".

Jiki a sukwane Captian ya tashi ya fice batare da yace wa Samir komai ba.

A k'ofar d'akin ya iske Salma fuskar ta ya kunbura tsabar kuka, so take ta ,tsayar dashi tayi masa ,magana 'Amman ta kasa tsaida shi ,harya b'ace ma.

Zama tayi ta cigaba da rera kuka, abunda ta gani yau ,ya balain d'aga mata hankali, ji tayi dama tun cen tasan da hakan da, duk Dr Samir be shiga halin dayake ciki ya'yanzun ba.

"Ya 'Allah ".

Shine abunda ta iya furtawa, yayin data lalubo wayan ta don kiran Captian, ta sanar dashi komai tun kan lokaci ya kure musu.......





*By Dija_Waziri*
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 47

Hajar tun jiya da, dare take ,kuka ita kanta ,takasa gane ainahin meke damun ta.

Su Mami sunyi rarashin harsun gaji sun barta,

Tunda ta kulle kanta cikin d'aki bata fitoba har safiya kuma duk takashe wayoyin ta.

Haka, kurum taji shi'awar ta keb'e ita kad'ai don bata son hayaniya.

*

Zariya
K'arfe biyu daidai aka gama d'aurin aure ,yan uwa da 'abokan Captian sai sanya Alkairi sukeyi masa tare da fatan Allah ya basu zaman lfy.

Shiko Captian binsu kawai yake da murmushin yak'e shikad'ai yasan abunda yakeji cikin zuciyar shi, ji yayi gabaki d'aya komai ya cenza masa lokaci guda.

Salama yayi da 'abokan shi akan shi ze fara gaba, soboda baya jin dad'i kanshi na ciwo , Abdul babu yanda beyi dashi ba'akan ya bari sutafi tare Amman yace suje kawai shi ze tuk'a ,kansa haka babu yanda ya, iya dole suka barshi ya tafi.

*

Mami na gama waya da ,Dady ta nufi d'akin Hajar babu walwala 'atare da ita .

Tana shiga ta sameta zaune kan gado tana danna wayar ta, tayi wanka fes da ita, tasa wani shedda ruwan ganye yasha duwatsu da fulawu, Amman batayi kwaliya ba sai k'amshi takeyi.

Kusa da ita Mami ta nema ta zauna , fuskar ta da 'alamun tausayawa tace.

"Hajjo And'aura , Auren ki yanzu Dad ya kira ya sanar dani.

Sanan yace gashi a hanyar dawowa gida yanzu, yana son ya ganki, yana son kuyi wata muhimiyar magana.

Abunda ,nake so dake shine ki ,kwantar da hankalin ki, insha 'Allah komai yayi ,yanda zuciyar ki, da gangar jikin, ki, keso".

Tunda Ummi tace And'aura ,Auren ta, taji gabaki d'aya jikinta ya mutu, wani

Please Login or Register in order to submit comment