Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi a lokacin gani
yake tanfar cikin wata bakwai ne dani.
Kwana biyar bayan danben namu na tashi da
daddare cikin matsanancin rashin lafiya mai
tsanani ciwon baya da ciki mai gigitarwa na kira
Baba Talatu dake taya ni kwana tayi maza ta farka
tana tambayata yaya dai uwardakina ruwa zan
baki ko me? Don tasan ina da dabi'ar yawan shan
ruwa na ce Baba yau kam ina jin haihuwa zan yi
don wannan ciwo ya tsananta nan take ta kama
salati tana kuka wai zai haihu loka ci bai kai ba na
ce mata kiyi fatan mu rabu lafiya kawai, tsawon
daren idonmu biyu bamu runtsa ba tayi juyin
duniya wai zata je ta taso yaya Almu ta ce mata
ban yarda ba Baba mutumin da baya magana da
kowa kyale shi kawai zata fara yi min fa da nayi

111

maza na kama yi mata kuka dama kuma wahala ta
ishe ni gashi babu Ummana a kusa babu kuma
umma amarya nan da nan ta shiga bani hakuri sai
ni ce nake ce mata shafa min baya Baba shafa min
nan shafa man can cikin zuciyata nace kai Umma
amarya dai ta iya tarairayar mai nakuda.
A haka muka yi ta fama har sai wajen asuba
sannan na haifi wani dan kankanin yaro bai ko
kusa da girman Abdulhakam ba, Baba Talatu ta
dauke shi cikin murna da godiyar Ubangiji tana
fadin ikon Allah bakwaini ne amma kuma
lafiyaiye na ce mata ba bakwaini ba ne Baba ke
dai kawai karami ne nayi mishi addu'o'i na kuma
diga mishi ruwan dabino, a baki, kamar yanda
naga Umma Amarya ta yi wa dan uwanshi, ina
zaune ina jiran biyowan mahaifa addu'o'i iri-iri
nake ta karantowa ina kuma neman sauki wurin
Ubangiji yayin da Baba Talatu keto son in barta ta
j1iga ni wai mahaifa ta fado ni kuwa naki saboda
tsanin da jikinnawa yayı zuwa can sai kawai na
sake jin wani yunkurin kankace meye wannan sai
ga wani yaron ya fito har kuma da mahaifar gaba
daya shima yana fitowa hakan ya kama kamar
yanda dan'uwanshi yayi da gudu Baba Talatu ta yi
waje har tana sulewa kofar yaya Almu taje tana

112

duka tana fadin fito Babangida fito yau kaga
alherin da ya sauka a gidanmu.
Ina jin shigowarsu na shige cikin toilet nasa
key na kulle nayi wanka na zuba ruwan zafi da
detol na shiga ciki na zauna nayi ta matse cikina
lokaci mai tsawo kafin na kintsa kaina na fito na
zauna ina shafa mai na amsa gaisuwar Lailatu na
kuma ce mata hada min tea ki bani ta ce to ta
hado min, na karba na sha na gyara kwanciyata
lokacin ne yaya Almu ya shigo bayan ya gama da
yaranshi sannu Rabi na ce mishi yauwa, babu dai
mas'ala ko? Na ce mishi eh, Baba dasu Umma
suna gaishe ki na ce to ina amsawa ya zauna anan
yana yi mun magana kan haihuwar da nayi a gida
na.ce ai ba komai gida da asibiti duk Allah ke
rabawa.
Washe gari da sassafe sai ga Umma karama ita
Baba ya turo tazo tayi min zaman biki nayiwva
Baban tudu waya na ce mishi a turo mun wata
daga katagun, nan da nan ya turo min Baba Marka
suka hadu da Baba Talatu su suka tsare min
komai suka tafiyar dashi yanda ya kamata, Umma
karama kuwa tan far ba zaman jego tazo mun ba
bini-bini tana wurin Lailatu ko me suke kulluwa
oho, ni dai cikin zuciyata cewa nake yi kuje kuyi
tayi yanda Ummana tafi karfinki haka nan nasan

113

nafi karfin Lailatu cikin yardar Allah don haka ba
kwa ga bana ban iya cewa ga irin cincirindon
jama'ar da suka rinka zuwa da irin hidimar yaya
Almu da suka rinka cikin yaya Almu bai
kwatantuwa kan wannan haihuwar yini yake yi
yana kaiwa abokanshi masu zuwa yi mishi murna
yara suna gani su kuma sai su rinka cewa a'a
Adawiyyah kuma haihuwa ta samu ni wancan
babban ya ma shekara kuwa? Shi kuma yana
dariya yana fidin a'a haba ya shekara mana
wannan watan ne ya cika shekara guda sai kumna
su kwashe da dariya suna fadin to ga biyu kuma
hidima sosai yaya Almu yayi don a wannan
haihuwar ne baba ya sakan mishi lamarin gidanshi
sauran duk abubuwan da ake yi a baya baba ne
mai bada kudin yin komai ko kuma yayiwa yaya
Junaidu umarnin ya bayar.
Yanda Baba ya tura sunan Abdulhakam
katagun ya bar wa Baban tudu zabin sunan da za'a
sanyawa jariri haka shima yaya Almu ya tura
radin sunan katagun sai dai sh
Da hannunki bibiyu kiyi mishi riko irin Wanda kikaga nayiwa mahaifina shi ita kuwa kuwa kishiya ba ruwanki da lamarinta a Kullun dai ki tabbatar kin Mata adalci,in baki mancema nama ai gaisawa suna da Karin maganar da suke cewa wai kowane tsuntsu kukan gidansu yakeyi,nace hakane imma nayi Mata sallama na like nake nayi sallama Dasu imma amarya da umma karama natafi naje na samu Yaya almu Dake ta faman jirana muka Kama January komawa kaduna badon hidimar ta Kareba saidon damamu kiranmu akayi muka lailatul da anti rahamane suke tsaye akan dukkan alamarin,
Akan hanyarmu ta komawa gida Ina kwance jikin mijina abayan mota yayinda direba ke janye damu,Yaya almu ya ratsa hannayenshi ya Kara rungumo kafadata yace na gode Miki Rani da Kika zamo uwargida ta kirki a gareni,na gode Miki da Kika TSAYA wajen ganin na samu Zaman lafiya a tsakanin iyalina da gode Miki da Kika tashi shigowa gida baki shigo hannu haka ba sai Kika riko gishirin miyar umma kika tahomin tare dashi,na daga Kai ahankali na kalleshi cikin fara'a da murmushi nace mishi banyi nasarar yin hakan ba Yaya sai danayi nasarar yin dace da arziki da rufin asirin da Ubangiji yayi min wajen hadani da miji na kwarai bawa daga cikin bayinsa salihai,na godewa daya Sanya ka zamo Miki gareni Kuma uban yayanmu,Dadi ya kamashi ya Kara kankameni ajikinshi,taimakeni Rani taimakeni mu sake samun wasu mahaddatan acikin yayanmu,nace da iko Allah Yaya saidai aikin ba nawa bane ni kadai Dani da Kai da lailatune zamuyi hakan,Yaya almu ya kelkele da safiya jindadin kalamin da nayi mishi.
Sai anjima mu sake haduwar cikin wani laittafin nawa da yerdar Allah Mai suna ayi dai mugani.
Fatan Alheri gareku dukkan KU na gode.
Hafsat chindo sodangi.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment