Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta
miko min, ina bashi ya kama ya shiga tsotso yana
ajiyar zuciya tanfar da ba'ayi ta fama dashi ya
kama ya ki ba, Umma tana zaune tana sauraron
abin da baba zai ce mata sai ya kalle ta ya ce dazu
Junaidu ya yi min waya ya shaida min cewar
Abdulhakam Alhajin tudu ya kira mish, ba Umma
93


ba hatta ni da ban san shi ba gabana faduwa yayi
don ban yi zaton hakan ba sunan mahaifina
mutumin da ban z0 duniya na sane shi ba sai dai
tun daga ranar da aka bani labarinshi shi da mata
rshi ban taba fashin yi musu addu'a ba.
Umma ta daga ido ta kalli Baba ta ce ikon
Allah, Abdul hakam ne? Sai kuma hawaye suka
biyo bayan maganar tata suka yi ta gudu a
fuskarta shar, shar,shar suka ki tsayuwa, Baba
kuwa sai ya kawar da kanshi ya fita ya bar mu, ina
gama bashi nono Umma ta ka rbe shi tasa a
bayanta ta goya ta shiga hidimominta nima na
gyara na kwanta wunin rannan kuwa babu abin da
zuciyata ke yi in ban da tunanin mahaifana
Abdulhakam da uwa kamar yanda su Umma suke
kiranta.
Satinmu biyu da haihuwa yaya Almu ya fara
tasa Umma a gaba da maganar komawana dakina,
ta ce ya dan kara hakuri muyi koda wata guda ne
ya ce mata to, muna cika watan ya dawo ya ce
mata Umma nazo ne kan alkawarinmu na
komawar Rabi gida, Umma tayi murmushi ta ce ai
kuma alkawari abin cikawa ne tayi maza ta mike
ta nufi dakin Baba zuwa can sai gata ta dawo
Tuskarta a daure, ta nemi wuri ta zauna ta kalli
Yaya Almu ta ce mishi Alhaji ya ce bai hana ka
93

tafiya da matarka ba duk lokacin da ka shirya yin
hakan, amma ya ce in gaya maka ita kadai zala
dauka ban da Abdulhakam, gaba dayanmu daga
ni bar yaya Almu tsura mata ido muka yi muna
kallonta.
Umma ta ci gaba da magana nayi kokarin ya
yarda ku tafi in yayi wayo sai a dawo mishi dashi
bai yarda ba, shiru yaya Almu yayi kamar ruwa ya
cinye shi don haka maganar tafiyar dai ranar bata
yiwu ba.
Randa'muka cika wata biyu cif ranar ne kuma
yaya Almu ya gama azumi sittin din da ya jera
ranar kuwa a Legos yayi buda baki, ni na shirya
mishi abin shan ruwa na kai mishi dakin da yake
sauka bayan na tsala mishi kwalliyar da ko a ranar
sunan ban yi irinta ba, sai da ya gama addu'o'in
shi muka shafa kafin ya jefa dabinon da ya yi
buda bakin dashi bakinshi duk abin da ya ci a
lokacin dangin fruit ne sai da yaje yayi sallar
Isha'i, ya dawo sannan ne ya soma cin abincin da
na shirya mishi yana cin abincin ya daga ido yana
kallona yanzu yaya zamu yi da maganar Baba
Rabi? na ce kamar yaya? Ya ce to za ki yi ta zama
a gida ne don renon yaro? Ai gara dai musan abin
yi ko? Ni yanzu nazo mana da wata dabara zan
rinka zuwa kawai ina yin kwana biyu anan in-je

94
gida in yi kwana biyu zan koma rabon kwana
tsakaninki da Lailatu kin san ba zai yiwu inyi ta
zaman zuba miki ido ba Rabi ba sai na tsaya yi
miki dogon bayani ba tunda a yanzu babu
maganar jan rai da wahalarwa a tsakaninmu.
Na ce eh yaya Almu amma dai gaskiya irin
wannan sarin ai zai yi wahala yau kana nan gobe
kana can kuma a gabansu Umma da Baba suna
kallonmu ma bai yi tsari ba, ka dai yi hakuri
kawai ka dauka ni na zo wankan gida ne a gida
kuma kana da matarka in ka samu lokaci kawai
sai ka rinka zuwa duba mu.
Ya sake kallona kafin ya ce min zan so mu
fahimci juna ta yanda zamu taimaki kanmu mu
duka ni da ke da yaron in kin yarda da hakan zan
iya barinki har wata hudu nan gaba don ya samu
yasha nono na tsawon watanni shida kafin in
dauke ki mu tafi mu bar musu shi in kuwa baki
yarda ba sai mu tafi yanzu mu barshi ai ba nono
ke raya mutun ba, nayi maza na ce hu'un ba zan
ya ba ya ce to shi kenan amma za ki kwana anan
yau ko? Na ce ba zan iya ba hira kawai zan yi in
tafi ya ce to jeki kawai ki bar hirar bana so na ce
to na tashi nayi tafiyarta.
Washe gari da safe na fito daga wanka kenan
na gama shafa mai ina cikin sanya kayana sai

95

kawai Umma ta ce mun wai baba ya ce a tambaye
ni in akwai abin da nake so ayi mun in fada don
asahn nan zan koma dakina, na kalli Umma cikin
natsuwa ace mata Umma da yaron? Ta yi mazata
tsuke fuska ta ce mun babu yaro anan gidan za ki
bar mishi shi tunda Lamido ya ce a bashi ke ku
tafi naga kuma kema tun randa uwarki ta haife ki
ta bar mishi ke shi ya rene ki ba nono ba, na yi
maza na ce mata kiyi hakuri Umma saboda na
gane ranta ya baci da maganar da nayi tana jin na
bata hakurin kuma ta juya ta fita.
Umma ce taja shirin komawar tawa har aka kai
sati biyu saboda ta gane ina da damuwa game da
barin yaron, duk da dai na 6oye don ba zai yiwuu
Baba ko Umma su zartar da hukuncin da ba zan
iya hakuri dashi ba ko da kuwa wane iri ne.
Ana gobe zan koma Anti Rahma ta dawo daga
Kaduna saboda ita ta jagoranci aikin gyaran
wurina da aka yi ina jin ta tana baiwa Umman
labarin irin yanda aka tsara wurin da yanda aka
tsarawa yaro dakinshi Umma tayi murmushi ta ce
shi Junaidun bai san ban da yaron ba ne a
komawan har yake kashewa dakinshi kudi? Anti
Rahma ta zaro ido tana kallon Umma sai dai ta
kasa ce mata komai.

96
A haka na kona gida washe gari Umma
karama ta maidani don da yaya Almu yazo
daukarmu sai Ummana ta ce mishi ya tafi da Baba
Talatu da Rabi'atu ni kuwa Umma karama ce zata
dawo dani hakan kuwa aka yi tayi waya ta ce
mata tazo ta maida ni dakina.
Na koma gida na samu Lailatu cikin wani irin
hali bata yi zaton dawowana ba watakila ta yiwa
yaya Almu maganar raba mana gidane don ta
fahimtar dashi cewar bata son zama dani, Lailatu
bata dauki maganar dawowa na da sauki ba
watakila tafi gwanmace wa da wata sabuwar
kishiyar aka kawo mata kwana biyun farko da
nayi a gidan nayi sune cikin halin zazzabi mai
tsanani a dalilin ciwon nonon da ya rufan mun shi
da kanshi yaya Almun duk zumudin shi na son in
dawo da zalamar da ya nuna a sarari ya hakura ya
saurara min saboda ganin halin da nake ciki ammna
hakan bai sa Lailatu ta shigo dakina ta tambaye ni
yaya jiki ba, gaba daya hidimar gidan kuma ta
tsame hannunta wai ba girkinta ba ne, duk da
hakan da tayi ban canza ba daga niyyar da na
dawo da ita don kuwa Umma ta gaya min cewar
ya zama dole in samarwa yaya Almu kwanciyar
hankalin da yake bukata a cikin gidanshi na ce
mata to ai wancan karon ma ba akan son raina aka

97

yi wancan zaman ba ta ce eh amma ai ke macece
gidan ki kuma tazo kin san yanda zaki yi kdyi
gyaran da ya dace, gaba daya laifin abin da ya
farun a kaina Umma ta dora shi shima yaya Almu
ta ce abin da ya yi duka ba wani laifi ba ne hakan
da tayi ya sanya ni na yi ta yi mata kuka.
kwana uku nayi ina fama da zazzabi na samu
sauki don haka washe garin rana ta hudu ranar da
zai sake dawowa dakina kenan sai na wastsake na
fito nayi shirin karbar mijina a yau tun safe nake
ta shirya irin nau'o'in abincin da zan shirya mishi
gaba daya littatafan girkina na dauko ina ta
dubawa don in ga abin da ya dace in shirya mishi.
Ina zaune a tsakar gida ina jira a gama min
gyaran kicin din mai aikin da Lailatu ta kawo ce
mai yi min aikin Azumi don na riga na yanke
shawarar yin mu'amalla da kowa, sai ga Rabi'atu
ta nufo ni da gudu zata zo wurina cikin murna da
dariyarta kan ta iso sai kawai naga Lailatu ta biyo
ta da sauri ta cafe ta tana cewa ja'ira mara zuciya
ni duk tsiyar mutum ba zai lashe min ke ina
kallonshi ban ce mata komai ba, sai da na gama
komai bayan cin abincin dare nayi kwalliya sosai
wurin yaya Almu zan tafi sai na shiga dakin
Lailatu nasa hannu na dauki Rabi'atu dake bacci
na sabata a kafadata zan fita da ita ta kalle ni ta ce

98

ina kuma za ki kaita? Na ce zan je in lashe ta tawa
ce ai tunda agabanki akan idonki Babanta ya bani
ita daga yau na karbe ta na wuce naje na kwantar
da ita a dakin da aka shirya don yaro wanda ba'a
dawo dashi ba.
Babu fitinar da Lailatu bata yi akan karbar
yarinyar da nayi ba har yaji ta yi ta ce wai ba za ta
dawo ba sai an mayar mata da 'yarta Ummana ma
ta ce in mayar mata da 'yarta tunda ta dage kan
hakan na ce mata sai dai in ba za ta dawo ba tayi
ta zama da kuwa naga zata tilasta ni mayarwa
Lailatu da ita nayi maza na gayawa Baba, shi
kuwa ya ce ai ba kwace mata ita nayi ba shi bai
taba ganin in da aka kwacewa uwa danta ba
musamman ma da yake ba barin gidan akayi da ita
ba don haka ta ishe mu dukanmu suka gaji da rike
ta suka dawo da ita, aka zauna a haka, ni kuwa na
dauki matakin duk in da zani da Rabi'a nake
tafiya har Ummarar da muka tafi da Anti Rahma
da ita na tafi ban barta a gida ba.
Gaba daya al'amuran gidana na karbe su babu
wani abin da nake sanyawa Lailatu ido akanshi in
tana sha'aninta da mijin ta babu ruwana in kuma
hidimar gidana ta ce ba zata yi ba sai kawai in sa
ta yi ba tare da na saurareta ba, da kuwa na ji
mijihta ya ce min ciki ne da ita sai kawai nasa aka

99


nemo mana mai girki na danka mata hidimar
abincin gidan amma ban da na yaya Almu wannan
ni da kaina nake yi mishi ban kuma damu da
cewar ga girkina ba ga nata ana cikin haka nima
na samu kaina cikin matsanancin halin zazzabi ga
wasu kurarrajin bakin da nake fama da su nayi
kamar 1n gayawa yaya Almu sai kuma kawai na
ce bari dai in hakura tunda yana zumudin cikin da
Lailatu ke dashi wacce har a tsakar gida take
gayawa masu aiki cewar wannan karon namiji
itama zata haifa ban tanka ba kallon su kawai
nake yi musamman ma da yake ba ni take wa
zancen ba.
Rannan ina zaune a gida ina tare da yaya Almu
abin karyawa nake shirya mishi sai ga yaya
Junaidu yana sallama yayi maza ya mike ya karbe
shi suka shigo tare nayi mishi sannu da zuwa na
kuma zuba mishi nashi abin karyawar shima yana
cikin karyawan ne ya kalle ni ya ce min Mustapha
ya gaya miki cewar zan yi aure ko Adawiyyah?
Da hannu biyu na dafe kirjina saboda tsananin
kaduwar da nayi na ce aure yaya Junaidu? Me
Anti Rahma tayi? Nagga kuma tana iyakacin
kokarinta, ya y1 maza ya daure fuska ya ce kina
nufin sai mace ta gajiya ne ake kara aure? Da aka
ce mu auri mata bibiyu ko uku-uku ko hurhudu

100

kina nufin in matan sun gajiya ne zamu yi hakan?
Ba haka ba ne in mun gamsu da adalcinmu ne aka
bamu ikon yin hakan in kuma muka ga ba zamu
iya ba sai aka ce to mu zauna da guda daya, nayi
ajiyar zuciya mai karfi na ce haka ne to Allah ya.
sanya alheri amma Anti Rahma fa? Ya ce na bari
Umma zata je gidan tayi magana da ita ni kam
zaman Jimami na koma na rasa me zanyi? Murna
zanyi kawuna zai yi aure ko kuwa bakin ciki
zanyi za'ayiwa Anti Rahma kishiya.
Shi da kanshi yaya Junaidu ya gane jikina yayi
sanyi da zancen auren nashi ya kalle ni ya yi
murmushi ya ce Adawiyya kenan wato ku dai
mata zumuncinku karfi ne dashi in ba haka ba ni
da Rahma wanene ya fi kusa da ke? nayi
murmushi na sunkuyar da kaina kasa ina yi mishi
bayanin ba wai bana murna ba ne tashin hankali
ne ba shi da dadi ya ce haka ne to ki kwantar da
hankalinki babu wata wacce zata zo ta dagawa
Rahma hankalinta in dai ba ita ce ta nemi ta daga
wa wani ba, zan yi iyakar kokarina don in ga sun
zauna lafiya, na ji dadin kalaman nashi na ce to
Allah ya sanya alheri ya ce amin, na sake wani
murmushin na ee lalle za muyi biki kenan ga
bukin gidan ma ya zo yau bai fi saura kwana
goma ba ga kuma wannan yaushe za ayı? Ya sake
101
kallona ya ce ai a gidan za'a bani auren baba ne
zai kara min nayi maza na ce kawu a gida kuma?
Ya ce eh mana Adawiyya ga kyawawan yanmata
a gida yaushe zanje ina neman a waje? Na yi
murmushi na ce ai fa anyi kyawawan yanmata a
gidan ga kwalliya sai dai akwai wata da ta fisu
kyau kawu iyaka dai bata isa auren bane kawai ya
ce wacece? Na ce mishi takwarar Umma Amarya
ya sake kallona ya ce yanzu nan Maryam bata isa
aure ba? Na ce bata isa ba kawu sha shida ne
shekarunta ya çe haka ne.
Washe gari muka nufi Legos ni da yaya Almu
wurin Anti Rahma naje don in dan tausata anyi
sa'a bata dauki auren da wani tsanani ba tunda ya
gaya mata cewar baba ne ya ce zai ba shi ba shi ne
ya ce yana so ba, sabanin yanda ni kuma ya ce
min shi ya ce yana so lokacin ne na tuna lokacin
auren Lailatu nima cewa aka yi min ba yaya
Almun ne yake so ba ba şhi kawai akayi.
Daukar auren yaya Junaidu da sauki da Anti
Rahma tayi sai yasa al'amura suka yi matukar yin
dadi ta kowane 6angare mu'amalla mai dadi ake
yi.
Shirin biki sosai akayi gaba dayan mu rufe
gidanmu muka yi a Kaduna muka nufi gida cikin
shirin buki sosai.

102


Baba zai sake bukin wasu 'ya'yan buki na uku
kenan tun bayan aurar damu da yayi sai dai tun
daga wancan loka cin bai sake bukin yara masu
yawa ba, kamar na wannan karon a yanzu zai yi
auren 'yanmata bakwai ne samari kuma biyar in
aka hada da yaya Junaidu mai yin kari shida zai
ba da daya kuma a waje.
Mun isa gida duk da ba wannan ne zuwan
Lailatu gidan na farko ba nayi matukar kokarina
wajen ganin na maida ita 'yar gida a gidan komai
zanyi zan neme ta muyi tare ko da yake ita bata
yarda ta zauna a inda nake wai ita 'yar dakin
Umma karama ce don haka can take zuwa tana na
mikawa, da daddare na dauki Rabi'atu naje falon
Baba don in kai mishi ita sai na kira Lailatu muka
tafi tare muka samu Umma amarya yaya Junaidu
da kuma yaya Almu a ciki baba yana zaune a kasa
yayin da Abdulhakam yake kan cinyarshi yayi
matukar yin girma sai rigima yake yi mishi yana
ta kokarin cire mishi madubin idonshi muka
gaishe shi ni da Lailatu na kuma matsa kusa da shi
na tura Rabi'atu na ce mata je ki ki gaida Baba ya
mika mata hannu ya dauke ta yana cewa ke mai
gashin doki wannan gashin dai ba naki ba ne kari
uwarki tayi miki don kiyi barazana na ce a'a Baba
nata ne ai gashi ne da ita don ma ina yankewa,

103


ban san Ummana ta shigo ba sai ji nayi tana cewa
uh ka ji ashana sau daya nefa ta yanke matà
gashin amma ka ji ta ce wai tana yankewa gaba
daya aka kwashe da dariya.
Umma ta dauki Abdulhakam ta gama ba shi
kunnunshi ta ajiye a kasa ya ci gaba da
wasanninshi yayin da baba yake tattanbayan
Lailatu wasu abubuwa don dai ya nuna mata
itama yarshi ce ni kuwa ina kusa da Umma
amarya wata magana nake yi mata sai dai ba a ji
muna cikın zancen sai naji baba yana cewa uwata
ce dai ban san dalili ba kullum ka ganta a rame
dubi yanda ta koma dakin gwanin kyau amma yau
dube ta, wai maimakon Ummanta fadi wata
magana ko kuma taja bakin ta tayi shiru sai kawai
naji ta ce mishi Adawiyyah ai kishi ne da ita mai
tsanani kishi kuwa hana mutum kyan gani yake yi
sai kullum ayi ta rama in ba haka ba me ke
damunta ba ga 'yar uwarta nan ba gwanin sha'awa
da ita tayi mul-mul.
Jawabin na Umma ya firgita ni a gaban kowa
zata ce wai kishi ne yake hana ni yin kiba ban san
lokacin da na sona yi mata kuka ba ina cewa babu
bata kishi ba nc baba, yayi maza ya ce yi shiru
uwata ba kishi ba ne amma menene damuwarki?
Na ce mishi kurarrajin baki sun dame ni bana iya

104


cin abinci da yunwa nake wuni da na gaji da
hakan nema na ce gara kawai in rinka yin niyya
ina yin azumi har kafin su warke.
Umma Amarya ta ce to an taba yin haka
kullum ana azumi? Ba za a dauki matakin daya
dace ba'? Yaya Almu ya ce ai Rabi taurin kai ne da
ita umma gata da musu nayi mata magana tun
farkon abin ta ce ba haka ba ne kurarraji ne kawa
kuma Sun warke, ta ce amma ai kai lalurar da ta
kawo kurarrajin aka yi ba ganewan da na yi
tonawa kaina asiri kawai na yi a gaban kowa da
kowa maimakon in kare kaina daga zargin kishi
da Ummana ta yi min sai kawai na sulale na fita
daga wurin na bar Baba yana yiwa yaya Almu
fada har yana yi mishi barazanar sake rike ni har
sai na haihu na yaye kafin ya bar ni in koma
dakina tunda dai shi ba zai iya taimakona kan
lalurata ba.
Ni kam dakin Umma Amarya naje nayi
kwanciyata saboda nasan wurin Ummana a cike
yake da jama'a, Umma Amarya ta shigo ta same
ni yanzu yau da kike yi Azumin da me kika yi
buda baki? Na gaya mata ta kama yi min fada ke
yarinya ce karama ba za ki taimaki kanki ba tunda
kin san ga yanda kike in dai kowanc ciki sai anyi
wadannan kurarrajin ai ya zama dole ke da

105


mijinki ku dauki matakin da ya dace, shiru nayi
ban ce mata komai ba.
Muna nan dakin muna hirarmu ni da Umma
Amarya sai ga yaya Almu ya shigo, na daga ido
na kalli agogo sha daya da rabi ne na dare, ya
nemi wuri ya zauna cikin natsuwa ya kalli Umime
ya ce mata in ranki ba zai baci ba Umma zan
hakura da zama da Lailatu in yaso na natsa sai sai
in kara wani auren don bana sha'awar zama da
mace guda daya.
A hankali Umman ta tambaye shi me tayi
maka? Ya ce mata yanzun nan a daki, Junaidu ne
ya banbare hannunta daga jikina yana bata hakuri,
Umma ta ce a'a me yayi zafi haka? ya ce ta ce wai
muna munafurtarta n1 da Rabi bamu gaya mata
Rabin tana ciki ba sai anan a cikin mutane akaci
mata fuska, na ce mata nima yanzu ne na tabbatar
don a gida da na tambaye ta musu tayi min, amma
bata yarda ba ta tada rigima wai sai na sake ta da
na tashi zan fita kuma ta rike ni in ban da anan
gidan nanne Umma ba zan yarda da hakan ba ta
ce mishi to kayi hakuri amma ai babu wani abin
bacin rai itama ba tuntuni ake cewa tana da nata
Cikin ba wa yayi tashin hankali? Duk da kiran da
Umma Amarya ta yiwa Lailatu tayi mata
maganganu na kwantar da hankali ta kuma yiwa

106

yaya Almu fada a gabanta bai hanata barin gidan
ba da sassafe ta tafi gidansu, don haka bata nan
aka yi sakun lalle aka shiga hidimar bikin, ni kam
ko wurin Ummana bana zuwa balle in ji ko ta san
abin da ake ciki a sashin Umma Amarya nake
zaune wacce duk da hidimar Jama'ar da take fama
dasu bai hanata tarairayata ba sai wani ji dani take
yi tana kuma nuna min cewar in yi iyakacin
kokarina wajen ganin mijina ya zauna lafiya a
gidanshi, gashi Allah ya baku haihuwar nan da
aka dade ana nema.
Ranar Asabar wajen karfe goma sha biyun
rana aka soma hidimar daurin aure abin mamaki
wai har da mai sunan Umma Amarya a cikin
yanmatan da aka daura wa auren kuma wai ita
aka baiwa yaya Junaidu.
A wurin liyafar cin abincin dare da baba ya
saba shiryawa 'yan uwa da abokan arziki a duk
lokacin da yayi irin wannan hidimar ina zaune
tare da yaya Almu yayin da Rabi'atu ke kan
cinyata na waiwaya na kalli yaya Almun bayan na
gama kallon yaya Junaidu da yar yarinyar da ya
aura sai da nayi tsaki kafin na ce mishi gaskiya
ban san yaya Junaidu budurwar zuciya ce dashi ba
sai yau, don Allah dubi yar yarinyar da ya ce
yana so kuma wai Baba ya bashi ita, ita kuma da

107
yake sokuwa ce dubi yanda take ta faman
murmushi ko me yake gaya mata? Oho. Ita bata
san tsobho ta aura ba.
Yaya Almu yayi murmushi ya ce ba za ki gane
abin da yayin ba komai ba ne sai nima na ce Baba
ya bani wacce naga tana tasowa yanzu, nayi maza
na galla mishi harara na ce ai sai kuyi tayi ku
rinka auren sa'o'in 'ya'yan cikinku yayi daniya ya
ce ba komai ba ne Rabi an riga an yardar mana
yin hakan sai dai kuma kin san ko yar sila zan
aura son da nake yi miki dabanne da wanda zan
yiwa kowacce da haka na danji sanyi cikin
zuciyata,
To an tashi biki gaba daya amare da angwaye
sun nufi gidajensu, don haka baki ma watsewa
suke tayi, ina zaune tare da Baba a falonshi hira
muke yi ni dashi da yaya Almu Abdulhakam yana
bacci a gefenshi, hakan ya kara tabbatar min da
maganar da Ummana ta gaya min cewar duk inda
yake bai rabuwa dashi duk matar da take tare
dashi kuma ita ce mai kula mishi dashi ko da
kuwa wacece.
Na kalli Baba cikin ladabi na ce mishi Baba
ashe dama zaka iya ba da kari? Yayi murmushi ya
ce zan bayar mana uwata ba hudu aka ce ayi ba?
Na ce haka ne, yaya Almu ya kwashe abin da na

108
fada akan yaya junaidu da amaryarshi ya fada
mishi baba yayi murmushi ya ce bai mata tsufa bba
uwata, Junaidu ai yaro ne, yaya Almu ya ce ai1
nima nan gaba gida zan zo a kara min Baba cikin
yankananan masu tasowa, nayi maza na ce a'a
baba shi yaya Almu ai dama mata biyu ya ce min
zai yi to ga riga kuma ya yi sai dai kawai ayi
mana addu'ar zaman lafiya baba da yaya Almuu
suka kyalkyale da dariya, baba ya kalli yaya
Almu ya ce to ka ji Lamido uwata ta ce ya isheka
haka.
Mun koma gida bayan an kammala biki iyayen
Lailatu kuma sun dawo da ita saboda ganewan da
suka yi Yaya Amu dai bai shirya binta ba, sai dai
ta dawo dinne kawai amma bata shirya a zauna
lafiya da ita ba, tunda ta gane ciki ne dani ta tsire
neman fitina mai tsanani bata zauna lafiya da
mijinta ba balle kuma dani hatta su Baba Talatu
da Azumi da ita da kanta ta kawo ta ta ce wai
itama munafuka ce ta koma wurina.
Kullum burinta tayi danbe dani ne ban san me
take nufi ba watakila gani take tunda ina da lalura
zata iya dukana, rannan na fito daga dakina zan
shiga kicin ita kuma daga kicin din take zata nufi
nata wurin, ban yi aune ba sai kawai naji ta
bangaje ni, ni kuma sai nayi wuf na sharara mata

109

mari mai tsananin karti nan take ta juyo ta rarumame
ni da karfi, abin da ya zama danbe mai tsanani a
tsakaninmu daga Baba Talatu har Azumi baba
abin da ba su yi ba don su raba mu Lailatu bata
yarda ba kokarin ta kawai shi ne nata samu damar
da ta buge ni a ciki ko kuma ta kai ni kasa, shi ne
kuma abin da bata samu ikon yi ba saboda
shigowan mutumin da ke kulawa yaya Almu da
tsabtar gida abin da ya shafi share-share da gyaran
furanni.
Washe garin faruwar abin su Umma suka iso
saboda kiran da Yaya Almu ya yi musu, Umma na
ce tazo ita da Hajiya Hauwa sai Abdulhakam da
tazo dashi.
Gaba dayansu ni suka dorawa laifi a cewar
wai da Lailatu ta bangaje ni sai in rabu da ita in
yaso in yaya Almu ya dawo in gaya mishi tunda
nasan bani kadai ba ce, Yaya Almu ya nuna musuu
bacin rai mai yawa kan abin da nayin suma kumna
suka taya shi jin haushina, Umma kuma ta sani na
bashi hakuri, kafin ta kalle shi ta ce mishi to ko
Adawiyyah zata je gida ne a'a Umma ba zai yiwu
ace duk lokacin da take da ciki sai taje gida ba ta
Zuana Hajiya Hauwa ta ce gaskiya ne Lamido to
Allah ya raba su lafiya ya ce mata amin.

110

Bayan tafiyarsu na yi fama da rashin lafiya
mai tsanani ga ciwon jiki ga kumburin da
kafafuwana suka yi tayi amma ban gaya wa yaya
Almu ba saboda duk da ba wani dadi muke yi ni
dashi ba a dalilin fushin da yake yi dani dana lura
da kyau kuma sai na gane rashin dadin da suke yi
da Lailatu ya fi haka yawa don ya dage kan cewar
kisan kai take so tayi mishi a gida in ban da haka
me zai sa tayi danbe da mace mai ciki wata
bakwai? Ko so kike itama tayi barinshi kamar
yanda kika ce kinyi naki? don

Please Login or Register in order to submit comment