Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ka barni in tafi da matata Junaidu.
Yaya Almu yayi shiru yana sauraron yaya
Junaidu ya ce mishi to zan bishi mu tafi, sai kawai
ya ji ya ce mishi to kaje sai na duba tukuna, abin
yayi matukar bata mishi rai ya ce amma dai kasan
babu gaskiya da adalci a cikin lamarin nan naka
Junaidu, me nayi da zafi haka da zaka goyi bayan
wannan abin da ake yi min? Me nayi wa Rabi
wanda ba a taba yiwa wata ba? Ka fini adalcin
aure ne? Yaya Junaidu ya ce to ka dai kama
bakinka, yana fadin haka yaya Almu ya mike ya
bar gidan.

74
Kwana biyar bayan nan sai ga aike daga gidan
Baba wai maza-maza muje ana neman yaya
Junaidu dani a lokacin nan kuwa kwanana arba'in
ne cif a gidan Yaya Junaidu na yi mulmul, nayi
gwanin sha'awa nayi kyau har ba a magana na
maida jikina na murje nayi fes dani gashi nayi yar
kiba mai ban sha'awa.
Mun isa gida muka samu Baban tudu ashe shi
ne yazo, yayi aiken muna shiga falo ya ganmu ya
fara yin magana an ce maka kawun wai Junaidu,
ni kuma na ce maka ka wun bahza kawun wofi, in
ba kawun banza ba wa ke shiga gidan aure ya fito
da 'yarshı? Wannan yarinyar ce mara lafiya? Ja'ira
mara kunya mara jin magana, kina wani zazzare
ido kamar an shake k, kin samu ana daure miki
gindi kina yiwa Babangida rashin mutunci, a
kanshi aka fara yin mata biyu? me yake yi miki?
Har ya kara aure? Wannan dai shi ne laifin nashi
in ban da shi kuma ban ga abin da yayi muku ba
kai Junaidu ka fita daga idona ka fita daga goyon
bayan Adawiyyah da kake yi tana yi wa mijinta
rashin mutunci, wannan ai abin kunya ma kake yi
don me za ka rike mishi matarshi? Maza-maza ka
maida Adawiyyah dakinta, Yaya Junaidu ya amsa
mishi ya kuma bashi hakuri, nima aka sallame ni
na koma dakin Ummana akan zan shirya in bi

75
Yaya Almu mu tafi tare, saboda har yanzu
Umman tana nan don Baba ya ce ba za ta koma
gida ba zata zauna nan ta kula da lafiyata, sai na
koma dakina tukuna, itama zata soma canje-canje
da su amma a yanzu canjin yana tsakanin Umma
Amarya ne da Umma karama, ina cikin zaman
sauraron yaya Almun ban san yanda aka yi ba sai
kawai naji an ce ya tafi ba tare da ya yi sallama da
kowa ba.
Tun daga nan ban sake komawa gidan yaya
Junaidu ba ina zaune a gida daga Baba har Umma
ji dani suke yi kamar zasu lashe ni, gashi kuma
wannan karon Umma Amarya ma tazo tana nan
kullum da sassafe take aiko min da abin karyawa
wanda take shirya min da kanta, sai dai a yanzu
duk da halin da nake ciki na kwanciyar hankali
tunanina ya koma kan mijina na gaji da ganin abin
da ake yi mishi kullum yazo gida sai ranshi ya
6aci so yake in koma dakina Baba ya hana nima a
yanzu na fi son dakin nawa, yaya Almu mijina ne
da muke .matukar son juna ni dashi, mafi
yawancin abin da ya rinka shiga tsakanina dashi a
baya daga mas'alar rashin haihuwa ne a yanzu
bana tare da wannan mas'alar ciki ne dani har na
tsawon watanni takwas har da wasu kwanaki, ba
na jin haushin kowa ji nake tanfar ba zan sake
76

bacin rai ba a duniya, tunda babbar mas'alata an
riga an yaye min ita, a yanzu babu abin da nake
sha'awa irin ace na zauna kusa da yaya Almu na
yaye mishi cikin dake tare dani wanda nake ta
faman boyewa cikin manyan riguna ya gani, in ga
irin nashi farin cikin da zai yi to babu hali, Baba
ya ce bai yarda a gayawa kowa sai dai duk da
haka yau kam nayi kewar yaya Almu, ji nake
tanfar in ganni a gabanshi na tsunduma cikin
tunanin hidimominshi da alhairorinshi iri-iri a
gare ni tun daga kuruciyata can baya lokacin da
nake ganin tanfar ni dashi din uba daya muke har
kawo zamana dashi a matsayin miji da mata,
zuwan Lailatu da kuma haihuwar Rabi'atu da tayi
da abin da ya yi ta faruwa a tsakaninmu a wannan
na tabbatarwa kaina da cewar yayi komai don
yayi adalci abin da ya faru na kuskure kuwa
wannan ajizanci ne irin na dan adam, don haka ba
ma shi da yake mijina kuma dan uwana ba, hatta
Lailatu dake kishiya wacce mafi yawancin
sabaninmu dashi ya auku ne saboda ita na yafe
mata duk wani abin da tayi in na ganshi kuma zan
roke shi gafara kan irin 'yan rashin kunyar da na
rinka yi mishi a dalilin kishi, ko da yake dai ni
dama ba mai dabi'ar maidawa miji magana ba ne
matukar dai ba wacce zai ji dadinta ba ne, balle

77
aje ana jero mishi fiye da abin da yake fada
saboda Ummana ta riga ta tarbiyantar dani da
cewar shi miji girmamashi kawai ake yi a kuma yi
mishi biyaiya, na mika hannu na dauki wayata na
soma danna lambobinshi da nufin kiranshi karo na
farko da nayi hakan tun bayan dawowana gida,
har ta fara alamar zata shiga sai nayi maza na
katse ta saboda tunanin wata kila yana tare da
matarshi musamman ganin lokacin farkon dare ne,
sai dai ina katsetan kiranshi ya shigo tayi kara har
ta katse ina kallon wayar ban dauka ba ya sake
har sau uku ban motsa ba da dai naga ba zai daina
kiran ba sai kawai na kashe wayar tawa gaba
daya.
Tsawon daren nan ban wani runtsa ba tunanin
yaya Almu ya dawo cikin raina ban san dalili ba
kishi ne yake damuna, na ni ina gida a zaune yaya
Almu yana gidanshi tare da matarshi wajen wata
hudu na bar mata shi ita kadai, Umma dake
kwance can gefe da itama ta hakura da nata mijin
ta bar wa Umma Amarya, saboda wai ba za ta
rinka barina ina kwana ni kadai a daki da tsohon
ciki ba saboda ba ta san abin da zai faru cikin dare
ba, ta bude ido ta kalle ni ta ce min lafiya yau ki
ka kasa bacci ko wani abu yana yi miki ciwo ne?
Cikin natsuwa na ce mata lafiyata kalau Ummna,

78
yaya Almu ne kawai.....shiru nayi ban karasa ba
saboda ganin yanda ta lumshe idonta a hankali ta
kuma juya min baya alamar bata son jin maganar.
Washe gari da sassafe sai ga Yaya Almu ya iso
har cikin daki ya shigo ya same ni, don da nayi
sallah komawa nayi na kwanta, yayi kwalliya
sosai yayi matukar yin kyau sai wani annuri ke
fitowa daga fuskarshi ga kanshinshi na kowane
lokaci a tare dashi, a bakin gadon ya zauna ya
zuba min ido yana kallona me ya faru Rabi? Jiya
kinyi nufin kirana ki ka fasa na kira ki kuma ki ka
ki dauka daga baya ma ki ka kashe wayar me ki
ke son gaya min? Na ce ban kira ka ba, ya yi
murmushi ya ce ban san ki da karya ba Rabina
gaya min kawai in kinji kewata ne...na daure
fuska na oe in yi kewarka saboda me tunda kai ba
tawa kewar kake ji ba, ya ce uhun Rabi kenan,
dama kin zo kin zauna a gida ne don kina tunanin
zan rinka kewarki? Don ki samu ki yi ta azabtar
dani ta haka, duk abin da ki ka rinka yi min muna
tare bai ishe ki ba sai kin baro gidan kin dawo nan
kin zauna saboda in yi ta azabtuwa da kewarki?
Saboda in kuntata in kasa jin dadi, don kina ganin
in ba kya nan a gidan ba zan samu natsuwar da
nake bukatar samu ba, saboda ki nuna min ni din
ba komai ba ne a wurinki, saboda ki nuna min

79

cewar za ki iya rayuwa mai dadi ko da kuwa babu
ni a kusa da ke har ma kina ganin in kinyi nesa
dani za ki fi samun kwanciyar hankali don haka
ma ki ka tanadarwa kanki wurin zama, to in ke
mace za ki iya nuna irin wannan jaruntakar to ni
namiji fa? Ko fa ni kadai ne mijinki iyakar kuma
gatan da su Umma da Baba zasu yi miki bai wuce
dai wanda suke yi mikin yanzu ba, su yi ta
tattalinki suna tarairayarki kina kiba irin ta rashin
zuciya, ni kuwa fa? Ya zuba min ido yana kallona
ban san dalili ba sai kawai naga na kama yi mishi
kuka bai fasa ba ya ci gaba da maganarshi zaman
gidan nan da kike yi dai kema kin san ba bis
ayardana kike yi ba. Fin karfina aka yi aka rike
min ke, don haka ke kin fi kowa sanin irin zaman
da kike yi, naje na kai kara gun Baban tudu shima
ban san me Baba ya ce mishi ba, ya ce wai in dan
kara hakuri kadan, to zanyi tayin hakuri Rabi ba
kadan ba ma zanyi mai yawa, to amma ki sanı
daga yau ban yarda ki sake fita daga cikin gidan
nan ba ko da kuwa gidan Junaidu ne balle in ji
labarin kinje wani wuri ko da kuwa yiwa su
Umma rakiya ne zuwa tafiyarsu, ki gaya musu na
ce ban yarda da fitarki zuwa ko'ina ba kiyi ta
zama a gida tunda gidan yana yi miki dadi.

80
Kukan da nake yi ya tsananta saboda na kasa
hana kaina yin kukan a dalilin kalaman da yake ta
jerowa wadanda ba masu dadin ji ba ne a wurina,
don kuwa alama ne na yana cikin fushi mai yawa
game da zaman nawa sai ya kara matsowa kusa
dani yana cewa gaya wa Baba yau za ki koma
dakinki Rabi sai muyi tafiyarmu ki koma dakinki
kiyi zamanki ke kin san ina sonki fiye da komai a
duniya, kin sani sarai kece mafi darajar abin da
nake dashi a rayuwata, in kinyi abin da kika yin
ne don ki horar dani ki nuna min matsayinki to na
horu Rabi, na kuma kara jinjina al'amarinki tunda
gashi ba barinki gidan nima na kasa zama a
cikinshi, rabon da inyi kwana bakwai ina zaune a
gid ahar na manta Rabi, yau ina nanne gobe ina
can, kiyi hakuri ki yafe min abin da nayi miki
wanda yasa kika yanke wa kanki hukuncin yin
nesa dani ba tare da kinyi tunanin abin da hakan
zai iya jawo min ba, ganin da nayi Yaya Almu
yana shiin durkusawa da guiwowinshi biyu a
kasa don ya roke ni yasa nayi zunbur na mike
daga kwanciyar tawa, na zauna a tsakiyar gadon
ina rokonshi kar kayi min haka yaya Almu ba sai
ka durkusa min ba zan dawo dakina, da sauri ya
ce min yaushe? Kan in ba shi amsa sai ya sake
zuba min ido cikin natsuwa yana yi min wani irin

81
matsanancin kallon da ya yi dalilin da nayi maza
na jawo abin ruhuwana na rufe kirjina da ya
zubawa ido, ciki ne dake Rabi? Nayi maza.na ce
mishi wane irin ciki? Cikin lafiya? Ni mai
haihuwa ce? Ya ce to kirjinki da ya cika haka fa?
Ban taba ganin nonuwanki sunyi irin cikan da
suka yi ba yau mu gani? Na bata ido na ce kaga
me? Nayi maza na mike na shige bandaki nayi
wanka har na fito yana zaune a wurin zaman jiran
fitowana yake yi, me ya canzaki ki ka zama haka
Rabi? na ce zaman gaban iyaye na samu
kwanciyar hankali da natsuwar da nake bukata,
ban yarda ke ba Rabi dole akwai wani abin da ke
tafiya wanda yasa Baban Tudu ya hakura ya huce
fushin da ya zo da shi ya bar ki kike zaman gidan
nan.
Na ce to ko mna dai menene ai kuma ba ciki
bane tunda yaushe? Yaushe rabon ma da ace an
wani abinnan? Kaima yanzu ai ba za ka so ace
maka ni ina da wani abu ba in dai ba nema kake
wata babbar magana ta taso ba, wuce shi nayi
cikin hanzari na nufi dakin Umma Amarya, a can
na karya na kuma yi zamana tare da ita, rannan a
gidan yaya Almu ya wuni. sai dai ni kam ban
yarda mun sake zama dashi a wuri daya ba.

82
Kwana biyu bayan nan ya sake dawowa gaban
Umma yana magana da ita can komawa gidanshi
ya ce Umma in zama da Lailatu ne bata so sai in
canza wa Lailatun wani gida in kai ta wani wuri
don itama dama tana yi min magana akan in Rabi
zata dawo to in kai ta wani wuri ita in bar ta anan
gidan na ce mata a'a wannan gidan ai don Rabi
aka gina shi sai dai in ma raba sun zanyi ita in kai
ta wani gidan.
Umma ta ce kul ka ce zaka raba su su zauna
tare ai ya ishe su suyi hakuri da juna kawai, kai
kuma kayi kokarin yin adalci a tsakaninsu, shi
kenan.Yayi maza ya ce to Umma, to yaushe zata
koma? Ta ce to bari in ga Alhaji anjima zan yi
magana da shi ko zuwa gobe sai ka dawo ka ji
yanda muka yi, ya ce a'a Umma ai wannan karon
na riga na yankewa kaina hukuncin in yi ta zama a
gidan nan in jira har zuwa lokacin da zaku yanke
abin da ke tsakanina da Rabi, ku bani ita mu tafi
ko kuma ku gaya min dalilin rike ta da kuka yi, ni
ban taba ganin kun yiwa wani irin abin da kuka yi
min ba Umma, ban kuma san dalilin da yasa ki ka
yarda aka yi min hakan ba in wani laifi nayi miki
ki yafe min, ya durkusa da guiwowinsa duka
biyu a gabanta in har zaki juya min baya Umma to
ai kenan na zama bani da kowa duniya ki yafe

83

min Umma, nan da nan Umma ta soma share
hawaye a idonta tana fadin ba ka yi min komai ba
Lamido baka yi laifin komai ba Babangida to me
zaka yi min? Me zai faru da har zaka yi tunanin
wani abu zai shiga tsakanina dakai Babangida? Ya
sake dago ido a hankali ya kalle ta cikin natsuwa
ya ce mata, to me yasa aka raba ni da matata kina
kallo Umma? Ai kin fi kowa sanin ina sonta
sabanin dake shiga tsakaninmu ai ba kiyayya ba
ce yau da gobe ne kema kuma kin sha gaya min
cewar zaman aure hakuri ne duk yanda aka kai da
Son juna in ba ayi hakuri ba zaman ba zai yiwu
ba, kiji tausayina mana Umma ba fa na iya zama a
gida sosai, ba na jin dadi ji nake tanfar nayi laifi
1yayena sun kwace matar da suka bani saboda ban
iya rike ta ba.
Kafin Umman tasan abin da zata ce mishi sai
ga Yaya Junaidu ya shigo da saurinshi kamar an
aiko shi zo mana Mustapha dama Kaduna zan tafi
don in ganka sai naji ance kana nan kazo, yaya
Almu ya mike suka fita, suna barin dakin na kalli
Umma cikin sanyin jiki na ce mata Umma yau
kuma fitsari a zaune nake yi nayi-nay1 kuma in
tsaida fitsarin na kasa, da sauri ta ce min fitsa
Adawiyya ko dai haihuwa ce tazo? tashi mu gani,
na yi kokarin nmotsawa in yunkura in tashi na kasa

84
janye kafata da na mike na sake kallonta cikin
natsuwa na ce mata Umma masokiya ta rike min
kafafuwana duka biyu ba zan iya tashi ba.
Nan da nan jikin Umma ya kama bari tana
fadin watakila dai haihuwa ce tazo miki
Adawiyya, Allah dai ya raba ku lafiya tana fadin
hakan ta kama kuka, kuka sosai Umma ta kama yi
ta kuma kasa hassala komai kukan da take yi din
ya bani tausayi don nasan abin da take tunawa
wanda kuma shi take tsoro, na kalle ta cikin
natsuwa na ce mata kiyi hakuri Umma.
Umma Amarya ta shigo daidai lokacin da
cikina yayi wani irin murdawa mai tsanan a
firgice na kama salati ina ambaton sunayen
Ubangiji da sauri Umma Amarya ta rike ni ta
kaini wani daki dake kusa da na Ummana ta
kwantar da ni kan wani gado wanda dama akanshi
Nos din dake zuwa dubani take yi min awo, kiyi
hakuri Adawiyyah kiyi hakuri yanzu Likita zai zo
duba ki, don na ce a kira shi, tana maganar tana
shafa ni bayana take shafawa tana kuma gaya min
kalamai masu kwantar da hankali, zuwa can wani
irin ciwo ya sake taso min mai tsananin rudarwa
nayi matukar kidimcwa ina fadin waiyo Allah na
waiyo Allah, ita kuwa Umma tanfar bata jin
tausayin halin da nake ciki taki tabar ni in huta sai
85

fadi take yi, yi nishi Adawiyyah yi nishi mai karfi
ga kan yaro nan ya iso yi nishi mai karfi sosai
nayi matukar dagewa da iyakacin karfin nawa
nayi nishin da take cewa in yi cikin yardar
Ubangiji sai gashi a hannunta, yana ta faman
kyara kuka ita kuwa bata kula ba sai tofa mishi
addu'o'i take yi ta ko'ina, nan da nan kuma ta
tauna dabino a bakinta ta diga mishi ruwan a
nashi baki, sannan ta matso kaina tana nuna min
shi kin ganshi Adawiyyah da namiji ne bari in
mikawa Hajiya shi ta ganshi tana kai shi ta dawo
kaina bata bar Nos ta taba ni ba sannu Adawiyyah
sannu da kokari ke kam jarumar yarinya ce gaki
kuma da hakuri har Umma ta gama abubuwan da
zata yi min kalamai masu dadi na fatan alheri da
addu'o'i iri-iri take yi min don haka har ta gama
ban gundura da komai ba da kanta tayi min wanka
ta riko ni ta dawo dani dakin Umma ta bani mai
na shafa ta miko min doguwar riga mai laushi
sabuwa na sanya bayan na sanya sabbin under
wears ta bani tea nasha sannan ta ce wa Nos din to
zo ki yi mata allura ta juya ta fita lokacin bata iya
yin komai saboda tsananin tsorata da tayi.
Umma Amarya tana fita sai ga Baba ya shigo
da saurinshi iko sai Allah uwata ikon Allah yau
uwata ta haifar min kani sannu uwata sannu da

86
kokari, kin ji wani abu yana yi miki ciwo ne? Na
yi maza na ce mishi a'a Baba lafiyata kalau, ya
mika wa Nos yaron ya ce mata gama kintsa shi
sannan ya koma jikin Ummana ya zauna ya ce
mata dubi nan ya nuna mata ni da dan yatsanshi
ya ce mata uwata ta haihu lafiya ita da danta
lafiyarsu kalau babu dalilin wannan kukan da kike
yi ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same
ta wannan mafarki da kika yi ba komai ba ne
dama na ce miki babu abin da zai same ta ita da
cikinta sai alheri tsawon lokaci Baba yana
rarrashinta na dago ido na kalle ta na ce mata
Umma kiyi hakuri ki bar kuka ni lafiyata kalau
taimake ni ki bani abin da zan ci don ji nake
tanfar an sace min kayan cikina, da sauri Umma ta
mike bari in sake hada miki tea, na yi maza na
bata rai na ce tea kuma Umma tea me zai yi min?
Ni tuwo za ki bani ko sakwara, ana cikin haka sai
ga Yaya Almu ya shigo da saurinshi sallama yazo
yi zai tafi gida, Umma tayi maza ta ce mishi to
dan dakata min kadan Lamido ina zuwa, tayi
maza ta dauki yaron ta danka mishi ta ce ungo
wannan duba min shi tukuna kafin ka tafi, yana
zubawa yaron ido ya nemi wuri ya zauna cikin
sanyin jiki da natsuwa a hankali ya bude baki ya
ce mata to da dai Rabi ta yarda da cewar da nayi

87
tana da ciki sannan haihuwa wani abu ne mai
sauko to da sai in ce Rabi ce ta haifar min shi
Umma, don kuwa kama dani da Baba ya yi kinga
kuwa kama da gidan nan yake yi inda so kuwa shi
ne namu ai da nine na dace da haihuwar dan da
zai yi kama da mahaifina Umma ba wani ne zai
haifa ba.
Cikin natsuwa Umma ta ce mishi naka ne
Lamido, Adawiyyarka ce ta haifar maka shi,
tsawon lokaci yana zaune kanshi a sunkuye
idanuwanshi akan yaroa ko kifta su ba ya yi yana
kuma sauraron abin da Umma ke gaya mishi na
cewar ba a kwance maka matarka ba Babangida,
an dai rike maka ita ce don ta samu kwanciyar
hankalihar ta haifar maka danka lafiya
musamman da yake cikin nata mai lalura ne ko
shi Yayan tudun da yazo kan maganarku rokon da
Albaji yayi mishi kenan na abar mishi ita ta haihu
a gabanshi.
Shigowar da Umma Amarya tayi rike da
foodflask mai wuri biyu a hannunta na dama ga
kuma platc-plate a daya hannun nata yasa
hankalina ya tashi daga sauraron zancen Umma da
danta ya koma kan Umma Amarya da abincn da
ta kawo min tuwon dawa ne miyar kukan da aka
yi da naman kaji ga man shanu da yajin daddawa
88

ya ii, Umma hada min miyar da tuwon kawai a
wuri daya, ta yi murmushi saboda tasan ba
dabi'ata ba ce yin hakan, na gama cinye tuwon da
ta zuba min din na kalle ta na ce mata na koshi
bari in shiga toilet in wanke hannuna bana son
wankewa a nan a zaune ta ce to bari in rike ki don
ba karfi ne dake ba, yaya AImu yana jin haka yayi
maza ya ce bari in kaita Umma, ta debi
kwanukanta ta fita shi kuma ya rike ni ya kai ni na
gama abin da zan yi ya dawo dani sai da ya gyara
min kwanciyar da nayi sannan ya kalle ni cikin
natsuwa ya ce tausayinki ya kama ni Rabi, kin yi
ta wahala ke kadai ban ma sani ba sannan a yau
din nan da kike fama da nakuda na sanyaki a gaba
ina gaya miki bakaken maganganu ki yafe min
duk wani abin da nayi miki na kan gaya miki
magana ne don in dan ji sanyin bacin raina sbaoda
gani nake tanfar kin ki zama da ni ne ki ka gudu
kika barni amma na rantse miki Rabi ranar da ki
ka bar gidan nan aka neme ki aka rasa a zaune na
kwana akan kujera zuwa yau kuma da safe ban
samu jin dadin da na saba ji ba a tare dani, amma
a yanzu da naga wannan mutumin na gane duk
abubuwan da ake yi min din suna da dalili har
kuma ga kyautar da Ubangiji yayi mana, Rabi sai
naji bani da sauran matsala a tare dani na godewa

89
da ya rufa min asiri ya yaye mana mas'alar
Allah da ya bani haihuwa tare dake na gode mishi
rayuwarmu na kuma gode mishi da ya azurta ni da
dan da Ummana tayi ta zubar da hawaye don
rashin samunshi, ya dago idanuwanshi a hankali
ya kalle ni kafin ya ce min wannan dan na Umma
ne Rabi nan gaba dai za ki haifar mana namu
amma wannan nata ne ita da Baba da ma su suka
yi renon cikin shi, nayi maza na ce mishi da
Umma Amarya ma ya ce a'a Rabi Umma Amarya
ai bata shiga lamarinmu tana jin kunya nayi
murmushi na soma ba shi labarin abubuwa har dai
daga karshe na ba shi labarin karbar haihuwar da
tayi na kuma ce mishi to ko wannan kayan dake
jikinmu ni dashi ai ita tazo dasu randa taje Umra,
ya yi murmushin jin dadi ya ce to naji amma dai
ba zan yarda kice su dukansu ukun ba sai dai
kawai in kika kara haifo wani nan gaba sai ita
Umma Amarya ta dauka, na ce mishi to shi kenan.
Haihuwar da na yi lafiya ta saukar da wani irin
farin ciki da annashuwa mai yawa cikin zukatan
yan uwa da abokan arziki, tun ma kuma ba
iyayenmu ba ko da yake dai Umma ta boye komai
ba za ka ganta kaga wani canji a yanayinta ba, ta
dauki haihuwar kamar kowacce da aka saba yi, to
amma kuma kowa yasan ta boye abin da ke ranta

90

ne don kuwa dama ita mai barwa ranta al'amarinta
ne na farin ciki ko bakin ciki ba ka safai takan
baiyanar har kowa ya gane abin da take ciki ba.
Yaya Almu kuwa tun washe garin ranar da aka
yi haihuwar ya fara azumi saboda wai ya taba
viwa Ubangiji alkawarin duk sanda ya bani ciki to
zai yi mishi azumi talatin don godiya sannan ya
sake yin wasu talatin din in na haihu lafiya.
Sanin halin Ummana da nayi na kin dabi'ar
'yan zamani na nuna rashin kunya da rashin kara
kan yayan da suke haifa na fari ya sa nayi
matukar kamewa don dai in kara mata farin
cikinta, tun washe ga rin haihuwar da yaya Almu
yaje gida da zai dawo ya taho min da Baba Talatu
da Rabi'atu, don haka Baba Talatu ke kula da
al'amarin yaron yayin da Rabi'a kuwa take manne
dani don bata manta ni ba, Lailatu kuwa da 'yan
uwanta ba za a ce musu komai ba don ko barka ba
su zo ba, itama Lailatun sai da taga abin zai zame
mata bacin rai sannan ta biyo shi suka zo tare
saboda sun ce wai dan ba na asali ba ne dashenshi
akayi min don dai an matsu a ga na haihu.
Gaba daya Baba ya hana shagalin suna mai
yawa ya ce maimakon a maida hankali ga yin
Shagalin suna gara ayi ta addu'a Ubangij1 ya rayaa
abin da aka samun ya kuma sa ya zamo mai

91
albarka don haka gaba daya'sunan sai ya ce a tafi
katagun ayi wannan dalilin yasa tun ana saura
kwana biyu sunan yaya Junaidu da iyalinshi suka
nufi katagun ya hada har da Rabi'atu wai ba za'ayi
sunan Baba ita ba itama Umma amarya shiryawa
ta yi ta yi tafiyarta wai zata kóma gida saboda
masu zuwa gidan don Umma karama ma tana
katagun din sai aka barni daga ni sai Ummana sai
ko Baba don Baba Talato ti tafi.
Ranat sunan da safe Baba ya shigo daidai
Umma tana fama da yaron wanda ya tashi daa
rikici sosai yasa hannu ya karbe shi daga gare ta
yana kallon kukan da yake yi tare. da yi mishi
magana tanfar dai yana jin abin da yake gaya
mishi haba Mallam me yà same ka? Menene
damuwarka? Kai kuwa ai bha kuri ya kámata kayi
don kuwa wanda ka gaji sunanshi mai hakuri ne,
Umma ta daga ido cikin natsuwa ta kalle ni ta ce
sun fadí sunanne? Baba ya ika mata shi ya ce
bata shi ta bashi nono tayi maža ta karbe shi

Please Login or Register in order to submit comment