Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi har da wanda
nayi yi dalilin taruwarmu anan yau na roki Allah ya
baiwa uwata haihuwar da namiji da wasu mazan
masu yawa bayanshi in ya bata da namijin to ni
kuma ya bani rai da lafiyar da zan yi tarbiyar shi
ta yanda zai zamo makarancin Alkur'ani wannan
shi ne dalilin da ya sa da na ji tana da ciki sai na
roketa da ta haihu mijinta ya nemi ta koma
dakinta ba zai viwu in hanata ba sai nasa hannu na
karbe jaririn duk da kankantarshi don nayi

131

alkawari akanshi, to gashi nan a yau kun shaida
alkawarin ya cika, sannan ita uwata bayan shi ta
haifi wasu mazan har guda b1yar ina ganin ma har
yanzu bata da ya mace, ya dan juya da sauri yana
sauraron abin da yaya Junaidu yake gaya mishi
sannan ya juya cikin murmushi yana cewa au to,
ashe kun ji wai daga bayan nan ta haifi Maryam
cikin zuciyata na ce tafdijan wato ma Baba
mancewa da ita yake yi, yanzu dai ga Junaidu nan
zai gaya muku yanda tafiyar tamu ta kasance.
Yaya Junaidu yana mikewa sai ya soma
godiya ga Ubangiji ya yabe shi kan alhairorinsh
ya gabatar da salati ga Manzon Rahma (S.A.W
ya yi wa Alkur'ani kirari, ya fadi darajojinshi da
daraicjin makarantunshi a ranar alkiyama da
sakamakon wadanda suka tarbiyantar da yayansu
akan karanta shı, da ya gama wannan sai ya shiga
bayar da labarin gwagwarmayar da Abdulhakam
ya yi a kokarinshi na yin haddar Alkur'ani mai
girma da yand. suka tsaida shawarar shigar da shi
cikin gasar karatun Alkur'ani don a kara zaburar
dashi da ya zo karshe sai ya ce to tun a shekara
bara mai alfarma sarkin Borno ya nada mishi
rawanin zama goni a lokacin da ya lashe
musabukar da ya shiga ta izifi sittin inda ya samu
damar wakiltar kasa a musabukar duniya da za'ayi

132
a birnin riyard ta kasar Su'udiya, to gamu a yau
mun dawo ina kuma farin cikin shaida muku
cewar shi ne yazo na uku, gaba daya dakin ya
dauki kabbara mai karfi da aka natsa sai ya ce to
kamar yanda aka saba a dukkan gasar da muke
zuwa akan tuho da kyaututtuka to a wannan ma
haka ne, an bashi dama ta yin karatu a jami'ar
Madina an bashi kudi da littatafai to 1littatafai
dama kullum shi ke amfani dasu kudi kuwa akan
raba su ne a tsakanın malamanshi to wannan ma
hakan za'ayi don haka a yanzu sai mu kara
natsuwa don mu saurari karatun Alkur'ani mai
girma daga bakin goni Abdulhakam Mustapha.
Abdulhakam ya mike cikin natsuwa dama
kuma mai natsuwa ne bai da hayaniya gashi kama
da kamun kai sai dai kuma fuskarshi bata rabuwa
da fara'a cikin murya mai cike da natsuwa ga amo
yana kuma karanto ayoyin kusa da karshe na cikin
surarui Ma'ida, da ya gama sai ya koma ya zauna
ya bar jama'a suna ta share hawaye, yaya Almu ya
kalle ni a hankali ya ce min Allah ya yi mishi
baiwa da murya ta karatun Alkur'ani, a hankali
nima na ce mishi haka ne yaya, ya sake kallona
cikin natsuwa ya ce min gashi dai namu ne ni
dake mu muka haife shi, to amma kin san ba
renon mu ba ne bamu muka tarbiyantar dashi bai
133


ba mu muka karantar da shi ba, Baba da matansh
guda uku ne suka yiwannan aikin mu namu
ya'yan mun kwashe su duka mun kaisu karatun
boko, na kalle shi cikin mumushi na ce mishi a
bamu makara ba yaya ya yi maza ya ce to taimake
ni rabina mu sake samun wani gonin kamarshi na
ce mishi to.
Da muka shirya ni da yaya Almu zamu tafi sai
na kamo hannun Maryam dina falon baba muka
shiga shi da Abdulhakam muka samu suna cin
tuwo da hannu a kwano daya tsayar mishi da
yarinyar nayi a gabanshi ni kuma na durkusa a
gefe na ce mishi baba gata nan na kawo maka ka
ganta da kyau, Umma Amarya ce don nan gaba
kar ka sake mancewa da ita baba ya zuba mata ido
yana kallonta cikin murmushi zuwa can sai ya ce
min na ganta da kyau uwata ba zan sake mancewa
da ita ba duk inda na ganta kuma zan shaideta
tunda ma gashi ta yi sa'a irin idanuwan
Abdulhakam dina ne a tare da ita, ni da yayaa
Almu muka yi murmushi na fito naje na yi wa
Umma amarya da Umma karama sallama sannan
na nufi wurn Ummana da zamu yi bankwana da
ita sai na ce mata Umma yi mun nasiha, ta kalle ni
cikin natsuwa ta ce min banı da wata nasiha da
zanyi miki illa ta bin mijin ki rike shi gam da

134
[6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: yayi yawa ya ce amma Umma.....tayı maza ta
katse shi ta ce ba wurinka ya aiko ni ba ka bari sai
ya ce yana so ya ji naka bayanin sai kayi wa
wanda ya aiko maka tana fadin hakan kuma sai ta
mike tayi tafiyarta.
Da yamma na isa legos saboda Baba ya kira
mu gidan a cike yake su yaya Zubairu su Yaya
Kabiru dukan su suna nan sun zo gaba dayansu
kowa fada yake yi min kan abin da nayi.
A falon Baba kowa yana nan har da Ummana
da Umma karama da Umma Amarya gasu yaya
Zubairu duk an hallara, Baba ya ce kai Kabiru na
kira ku ne anan dukanku don ku zo ku shaida abin
da ke faruwa ko ya faru tsakanin Lamido da
uwata cikin ku dukanku babu wanda ban yiwa
shari'a tsakaninshi da iyalinshi ba, hakan bai
damen ba saboda zo mu zauna zo mu saba, amma
bayanin da Maryam tazo min dashi dazu ya
banbanta da naku don haka na ce kuzo ku taya ni
ji ke uwata kiji tsoron yin karya don ba za ta
amfana miki komai ba, ki fadi gaskiya na ce mishi

59

to yanda na rattabawa Umma Amarya komai haka
nan nayi bayan1 sai ma da na ga Umma karama a
zaune na shaidawa Baba cewar duk sati biyu take
zuwa gidan tunda Lailatu tazo bata kuma taba
shiga dakina ta zauna ba wani lokaci ma fitanta
kawai nake gani nan da nan jikin Umma ya dauki
rawa ta kama kame-kame tana fadin wai ai ita
Rabi'atu take zuwa gani, Baba bai kula ta ba
wurin Yaya Almu ya juya ya tambaye shi anyi
wadannan abubuwa ko ba ayi su ba? Yaya Almu
ya sunkuyar da kai ya ce anyi su Baba, amma
akwai dalilai, Baba ya yi maza ya ce to ko zaka
gaya min dalilin dasa kasa uwata tayi wata takwas
tana girki ita ka dai bayan ga abokiyar zamanta?
Ya soma kame-kamen bayani ya sake tambayarshi
da ta mare ta a gabanka ka hanta ramawa wane
hukunci ka yi mata? Baba ya sake juyowa wurina
ya ce min ke uwata don me ba ki taba gaya wa
Zuwairah abubuwan dake faruwa ba? Na
sunkuyar da kaina na ce mishi naje zan gaya mata
ta ce min kar in koyi kai karar mijina in zama
matar rufin asiri, Baba ya yi shiru dakin ma ya yi
shiru, zuwa can sai ya ce daga yau na sanya
Maryam da Junaidu su zama wakilai akan
al'amarinki duk abin da ya dame ki ki gaya musu,
na ce mishi to Baba.

60

Baba ya sake kallon su yaya Kabiru ya ce
musu a yau na taraku ne anan don in shaida muku
cewar randa duk aka wayi gari bana duniya to
dukanku na bar wa amanar uwata ba wani mutum
daya ba saboda ni da Baba ya yi gamsuwar da ya
bar min amanaar Zuwaira ni kadai bayanshi
rayuwa tasa na barta ta wahala balle Lamido da ya
iya wahalar da uwata akan idona da na uwarshi,
lokaci mai tsawo Baba ya dauka yana yin magana
kafin ya ce, ke uwata laifin da kika yi na zartar wa
kanki da hukunci da kike yi shi ne yasa ba zan yi
komai kan duk wani abin da akayi miki ba, ina
kuma so in kara jaddada miki cewar ko bayan
raina ban yarda kisa kafa ki fita daga gidan
Lamido ba don haka ki koma dakinki ki zauna na
ce mishi to, ke kuma karama ba zan ce miki
komai ba kije kiyi duk abin da kika ga yayi miki
daidai.
Mun fito zamu tafi yaya Junaidu ya kira ni
nayi maza naje wurinshi sai ya kalle ni cikin
natsuwa ya ce min kar ki rudu da abin da Baba ya
yiwa Mustapha a cikin mutane ki dauki hakan
tamfar wata dama a wurinki da za ki rinka yi,
mishi abin da ki ka ga dama ina fatan dai kina
sane da cewar hakkukuwanshi da suke kanki basu
sauya ba, sannan duk da bayanan da ki ka yi nina
61

yarda da cewar babu wani abin da Mustapha zai yi
da nufin ya cuce ki don haka kiyi hankali da kanki
ya wuce ya tafi ya bar ni a tsaye cikin tunani.
Kalaman Yaya Junaidu sun kashe min jiki sai
dai kuma inda mas'alar take shine a yanzu ba na
son ganin Yaya Almu a kusa dani ko maganarshi
naji sai in rinka jin gabana yana faduwa, babu
lokacin da na kan samu natsuwa irin lokacin da na
san ba ya gari bisa wannan dalili sai nafi sha'awar
da a bar ni in koma wurina in yi zamana ni kadai
in yaso su bar auren ace yana nan bai mutu ba don
kuwa ni kaina ban taba sha'awar mutuwar auren
namu ba don bana yiwa kaina sha'awar zawara.
A wannan dawowar da muka yi babu abin da
bai yi ba don mu daidiata mu zauna lafiya naki
yarda bana shiga komai na hidimar gidan sabuwar
'yar aikin da suka kawo ba na sa ta ba na hana ta
tsakanina da ita ina kwana ne kawai ina gajiya?
Kayan da nayi amfani da su nawa nan take nake
gyara su in adana na ma daina shiga kicin din da
yake na hadakan a wanda yake cikin falona nake
aiki na ba na kuma yin girkin tare da kowa, ina
zaune cikin falona, Ice-Cream din da nayi nake
sha, yaya Almu ya shigo ya zauna yana yi mun
magana, Rabi'atu ta rarrafo ta shigo cikin falon
tazo ta dafa jikina ta mike ta tsaya tana kallona da
62

sauraron inyi mata wasannin da muka saba, don
kawai in bata mishi rai na kwalawa Baba Talatu
kira ta shigo na ce mata dauke min wannan
yarinyar ki bai wa wancan matar ita ta mika ta
dakinsu, Baba Talatu tayi maz ata fice daga dakin
tayi tafiyarta ba tare da tayi abin da na ce din ba,
shima yayan ficewa yayi ya bar min dakin saboda
yazo iya wuya da abin da nayin, sai bayan fitarshi
ne nasa hannu na sureta muka shige can ciki, ko
zuwa wurina yayi ranar girkina zai min wata
magana sai in gaya mishi in raba ka da mai
haihuwa zai mun wata magana sai in gaya mishi
in raba ka da mai haihuwa don ka zauna tare dani
da bana haihuwa to ai kai kuma sai kawai ka fita
hanyata me zaka yi dani? Duk wani abin da na
rinka yi mishi a wannan lokacin shanyewa ya
rinka yi tanfar dai ba shi ne yaya Almun da na
sani ba, illa iyaka dai gaba daya shima ya kame
kanshi ya fita harkata.
Ina kwance a dakina ranar Talata da safe
bayan na gama wanke kurarrajin bakina da garin
ararrabi da aka bani shawarar anfani dashi, ji nake
tanfar in kurma ihu saboda tsananin zugin da
bakina ke yi, Baba Talatu ta shigo ta same ni,
yaya dai uwardakina? Na kalle ta cikin nutsuwa
na ce mata bakina ya dame ni Baba ga kada
63

gwarzo yau ma ya sake fito min ko ruwa bata iya
sha, ta kalle ni cikin kulawa da tausayawa sannu
uwardakina ai kece kina fama da ciwo amma kin
ki yarda ki gayawa maigidan an taba yin haka ace
kana zaman mutum amma ba za ka gaya mishi
damuwarka ba.
Ina kwance anan wurin ina fama da kaina
saboda matsanancin zazzabin da ya kama ni ina
cikin tunanin abin yi sai ga Yaya Almu ya shigo
cikin kwalliya sosai nan da nan kunshin turarenshi
ya gauraye ko'ina ina shirin mu gama gaisawa in
nemi izininshi don zuwa ganin Likita kan
mas'alolin da suke damuna sai kawai naji ya ce
min zan yi tafiya zuwa London da Lailatu zan
akai ta ayi mata wankin ciki saboda yawan barin
da take yi a dan tsakanin nan ina daga kwancen
nace mishi to sai kun dawo, Allah ya kiyaye
hanya, ya juya bayan ya ce amin, itama Lailatu ta
shigo ta sha kwalliya ita da Rabi'atu sunyi
matukar yin kyau suma kamshin suke yi mai dadi
na mike muka y1 sallama nayi musu rakiya har
zuwa jikin mota sai da suka tafi sannan na shigo
gida, ina hawa kan gadona na soma kuka na fara
gajiya da al'amuran yaya Almu, komai kankantar
abin da yayi min a yanzu sai in ji kirjina yana ta

64

ciwo in ji kamar zan sa hannu in dauko zuciyata
sbaoda tsananin zafin da take yi min, Lailatu da ta
haihu watanni takwas da suka wuce ita ce wai an
tafi da ita London don yi mata wankin ciki saboda
tana yawan yin baci alhalin ni tun zuwan Lailatu
gidan ya hanani zuwa ko'ina, hatta bikin da aka yi
a Katagun bai bar ni naje ba duk da a gidanmu ne
sai kawai ya tasa Lailatu a gaba suka yi tafiyarsu
ya ce wai ta riga ni tambayarshi zuwa bikin kuma
zata kai musu Rabi'atu su ganta, na ce haka ne ni
kuma bani da abin kaiwa a gani sai kun dawo.
Jikina yayi tsananin zafi saboda tsananin bacin
rai ga kukan da nayi tayi don haka sai na kwana
cikin matsanancin halin da sai da Baba Talatu ta
taya ni kwana, gari na wayewa ta yiwa Baba wayya
ta shaida mishi halin da nake ciki, ba a dauki wani
lokaci mai tsawo da yawa ba sai ga Yaya Junaidu
ya iso yana ganin halin da nake ciki ya tasa ni a
gaba sai Legos kai tsaye gid aya kai ni gaban
Baba, ya zuba min ido yana kallôna wane irin
lalacewa kika yi haka uwata? Gaba daya kin
tsangwami kanki kin hana kanki sakat kin ki ki
saki ranki kiyi kyan gani, maganganun da Baba ya
Soma yi min yasa na kama kuka ina rokon shi ya
barni in zauna a gida na gaji da zama da yaya
Almu yana nema ya haddasa min ciwon zuciya,
65

tsawon lokaci yana rarrashina kafin na hakura na
daina kukan da nake yi.
Washe ga rin zuwana Legos Ummana ta iso
saboda kiran da Baba ya yi mata a dakinta ta same
ni a kwance nayi kuka har idanuwana sun
kumbura, Umma ta zuba min ido tana kallona
cikin natsuwa da tausayawa me ke damunki haka
Adawiyyah? na ce mata ban sani ba Umma illa
iyaka dai kirjina yana min ciwo zuciyata ji nake yi
tanfar in dauko ta saboda tsananinz afin da take yi
min ga kada gwarzon dake damuna ta ce to tashi
muje in kai ki asibiti ga Junaidu yazo zamu tafi
tare nace mata to.
Ina zaunc gaban Likita ina amsa tambayoyin
da Likita ke yi min, sai Umma ta ka rbe tambayar
ta hanyar cewa tana da mas'ala ne Dakta, gwaje-
gwajen da aka yi mata a baya sun nuna tana da
mas'alar kankantar mahaifa da yawa wanda suka
ce ba zai bari ta haihu ba, Likita ya sake kallona
kafin ya ce to amma a sakamakon wannan gwajin
ai ya nuna ciki ne da ita, j1 na nayi tanfar ina yawo
kan gajimare saboda rudewa, Umma kuwa cewa
tayi a kira mata yaron da suka zo tare yana nan a
waje, nan da nan yaya Junaidu ya shigo
hankalinshi a tashe saboda yayi zaton wani abu ne
mai tsanani ya faru.

66

Zauna ka taya ni jin wata magana Junaidu, ya
yi maz aya zauna yana kallonta cikin sanyin jiki
ya tambaye ta me ya faru Umma? Umma ta kalli
Likita ta ce mishi Dakta me ka ce yana damun
Adawiyyah? Likita yayi murmushi ya ce shekara
nawa ne da auren nata ne Hajiya? Har ki ke so ki
debe tsammani ta ce mishi bakwai har da wasu
watanni, yaya Junaidu ya gyara zama ya ce mishi
menene Dakta? Likita ya kara kallon takardun da
aka kawo gabanshi ya ce, wannan normal abu ne
yake gare ta, yaya Junaidu yayi wani motsi mai
karfi kafin ya ce yi mata scarning Dakta don mu
kara tabbatarwa yayi maza ya ce to shi kenan.
Ina kwance kan gadon, Likita gaba daya
hankalin Umma da yaya Junaidu har da nima yake
kan allon computer da Likita ke dubawa, bayan ya
shafa min wani ruwa mai dan sanyi yana kuma
bin marata da dan wani mulmulallen abu yana
goyawa nan da nan allon ya shiga baiyanar da
abin da ake son gani gashi nan ai har ya zama
mutum maganar Likita kenan yaya Junaidu ya ce
tsarki ya tabbata ga Ubangiji, ya shiga yin tasbihr
yayin da Umma ke ta faman kuka, ni kam a
kwance nake zuciyata sai faman bugawa take yi jl
nake tanfar a mafarki nake wai ciki ne dani abin
da na riga na debe tsammani kowa ma ya hakura

67
cikin zuciyata na ce Allah na gode maka, Ubangiji
kasa abin da nake ganin na motsin mutum a cikin
cikina ya tabbata gaskiya ne ba mafarki nake ba,
ciki ne gashi watanni kusan biyar ba ya motsi ne
mai karfi a dalilin Rarancin kuzarin da ke gare shi
bata cin abinci bata kula da kanta ta rasa abubuwa
masu yawa, don haka shima ya rasa Rarfi ijikin
Umma yana rawa ta ce yanzu meye abin yi Dr.?
Ya ce zamu dan sa mata drip don ya rage mata
yunwa kafin mu dauki matakin da ya dace.
Ina kwance kan gadon Likita ana yi min karin
ruwa a sabon dakin da aka kaini bayan tafiyar
yaya Junaidu gida har lokacin Umma dake zaune
a gefe na bata iya cewa komai ba in ban da kukan
da take yi tsawon lokaci muna nan a haka har
bacci mai karti ya dauke ni, farkawa kawai nayi
daga baccin na samu Baba a tsaye a kaina tare da
Likitan da ya duba nin, 1tama Umma tana tsaye a
gefenshi, kin tashi uwata? Na ce eh Baba na
yunkura don in tashi in gaishe shi yayı maza ya
maida ni da hannunshi koma ki kwanta ki huta ki
samu natsuwa, in Allah ya yarda Allah zai kawo
mana karshen damuwarmu, ban yi magana ba
saboda sai na ji ina jin nauyin amsawa, ya sake
kallon Likitan ya ce mishi tunda ta farka a sake
yin scarning din nan da nan Likita ya bi umarnin
68

da aka ba shi. Dr ya ce gashi nan yallabai,
mutunne ka ganshi in kana son sanin mace ne ko
namiji ma zamu iya dubawa, baba yayi maza ya
ce a'a ba abin da nazo gani kenan ba mun gode
Allah shine mafificin mai baiwa shine wanda ba a
debe tsammani daga samun alherinshi, Umma ta
yi ajiyar zuciya mai karfi ta ce haka ne, ya kara
Juyawa wurinta ya ce iko sai Allah, wa yaga mun
Zuwairah rike da dan da uwata ta haifar mata?
Umma tayi murmushi a karo na farko tun bayan
kukan da tayi, ta yi ta ce a'a menene da ban sauran
ya'yan da nayi ta dauka fa? Yayi murmushi ya ce
uh'uh dai Zuwairah, ya sake maida hankali wurin
Likita ya ce mishi sallame ta su koma gida za a
kula da ita kai kuma in ka tashi sai ka biyo ka ka
r6i goron albishirinka, ya ce to ya yi ta godiya tun
katin yasan me za'a ba shi.
Mun dawo gida Likitan da ya ganni a asibiti
kuma shi ne wanda ya ci gaba da zuwa gida yana
duba ni saboda irin alherin da Baba yayi mishi,
magunguna ya rnka bayar wa tare da shawarwari
kan irin abincin da ya dace in rinka ci saboda
kurarrajin dake damuna, nan da nan na samu karfi
a jikina saboda na fara rabuwa da yunwa da nayi
kan kace meye wannan kuma sai ga cikina ya
kama motsi akai-akai, ba zan iya kwatanta farin

69
cikin Umma ba a wannan lokacin ba zan iya cewwa
ga halin da take ciki ba.
Duk da Umma karama tana gidan bata san me
ke faruwa ba abin da ta sani dai kawai shine bani
da lafiya, gashi kuma Umma tayi sa'a baba ya ce
kowa ya kama bakinshi yayi shiru ba ya so ayi ta
yawo da maganar sai dai kashedin da Baban yayi
bai hana Umman yin waya ta shaidawa Umma
Amarya abin da ake ciki ba.
Sati biyu cif da tafiyar su Yaya Almu sai gasu
sun dawo a gida suka sauka don isowar dare suka
yi daga shi har Lailatu da Rabi'atun sun yi shar
gwanin sha'awa da su kai ka ce ba asibiti suka je
ba, daga butun amarci suka dawo, sai dai ganina
da yaya Almu ya yi a gida. yayi matukar 6ata
mishi rai, kasa boye bacin ranshi yayi don kuwa
ko tafiya masaukinsu da aka basu shi da
Lailatunshi bai je ba, ya zauna gaban Umma yana
tambayarta abin da yasa ake keta mishi haddin
gidanshi.
Umma ta kalle shi cikin natsuwa ta ce mishi,
to Babangida sai kayi hakuri nima kirana kawai
Al haji yayi ya ce min in zo in kai Adawiyyah
asibiti bata da lafiya.
Cikin daren rannan muka hallara a gaban Baba
saboda yaya Almu ya tubure ya ce bai yarda da

70

gatan da ake yi min bá wanda yake bani damar
wulakantashi, don me' shi ba zan gaya mishi bani
da lafiya ba sai bayan ya bar gida zan sa a fadaa a
gida? In ba raini da wulakanci ba me zai sa in yi
haka in ban da nasan ina da wadanda suka tsaya
min? Yaya Junaidu shima ya shigo saboda kiran
da aka yi mishi don yaya Almun ya ce yana da
magana dashi.
A fusace ya kalle shi ya ce mishi kái kake
daurewa Rabi gindi kan duk wani abin da take yi
min, kana shiga cikin harkokin iyalina da yawa, a
wurinka ta samu kudaden da ta sai gida har ta
samu tashi ta bar dakinta ta koma can da
taimakonka tayi hakan tayi min rashin kunyar da
yasa na hanata zuwa biki katagun sai da ka nuna
min rashin jin dadinka kan hakan ka ce ban yi
mata adalci ba, na hanata zuwa cikin dangi yanzu
kuma ka shiga gidana ba izini kaje ka fito da ita
ba tare da ka nemi 1zinina ba kuma baka samu
lokacin da kayi waya ka gaya min abin da ake ciki
ba to ya ishe ni haka nasan duk kokarinka bai
wuce wai kai ka nuna min kai kawunta ba
ne............ kan ya karasa maganar da zai fada yaya
Junaidu ya katse maganar tashi ta hanyar ce mishi
gyara maganar da kayi ta ce min wai kawu fusatar
yaya Almu tayi yawa tanfar dai ya mance a gaban

71

Baba suke sai ya sake ce mishi an ce maka wai
kawu, ni ina yi maka abin da kake yi min ne ko
kai ba ka da mas'ala ne a gidanka? Yaya Junaidu
ya ce mishi ina da ita, ya daga ido ya kalli Baba
cikin natsuwa da girmamawa ya ce mishi Baba
Mustapha ya yi min rashin kunya na ce min wai
kawu da yayi baba ya ce rashin kunya mai girma
kuwa don ya kamata ya fi kowa sanin cewa kai
din ba wai ba ne tunda ya san uwarta ce tasha
nono ta bar maka, don haka tunda ka nemi ya
janye maganarshi ya ki to ni nasan kai ba wai ba
ne a wurin uwata, shi yasa ma nake shugabantar
da kai akan dukkan al'amuranta, nima kuma ba
zan yarda ya maida kai wai ba, don ka wuce wai
din, yaya Almu ya yi maza ya ce to kayi hakuri
baba na janye maganar tawa raina ne ya baci da
irin abin da Junaidu yake yi min, Baba ya ce eh ai
nasan ranka ne ya baci shi yasa kayi mishi ràshin
kunya a gabana ya kuma nemi ka janye rashin
kunyar taka ka ki, saboda haka zan koya makaa
yanda zaka rinka yin magana dashi nan gaba ko
ranka ya baci saboda Junaidu surukinka ne, kai
Junaidu yaya Junaidu ya yi maz aya ce na'am
Baba, Baba ya ce mishi ka dauki uwata ka tafi da
ita gidanka, kuje can ku sasanta randa Lamido ya

72
gane kai din kawunta ne da gaske ba kawun wai
ba ne sai ka mayar mishi da ita gidanshi.
Umma ta yi maza ta ce a'a Alhaji kar kayi irin
wannan hukuncin a tsakaninsu shi Lamido ya ba
Junaidu hakuri kawai ya dauki matanshi gobe su
tafi gida.
Baba ya ce ba zata bishi ba, ai har da laifinki a
cikin rashin kunyar da ya yi wa Junaidu, a gabana
ya kira shi wai? Junaidu wai ne? A haka Umma
tana kuka Baba ya zartar da hukuncin in bi yaya
Junaidu gidanshi, ni kam nayi matukar yin murna
da hakan saboda na riga na gaji da yaya Almu da
matarshi ko da dai a yanzu na daina jinz afin da
nake ji a zuciyata, game da su, to amma kuma ina
bukatar nima in 6oye musu cikin da nake dashi
kamar yanda shima baba ya ce bai son a baza
labarin cikin ya fi so kawai a bar shi ya fito da
kanshi a gani.
Ina zaune gidan Yaya Junaidu daga shi har
Anti Rahma ji suke kamar zasu kashe ni saboda
tarairaya ta da suke yi, ga kuma ya'yansu da suke
matukar debe nmin kewa wadanda nayi matukar
shakuwa dasu nake kuma son su kamar me, na yi
matukar sakewa a gidan yaya Junaidu sau goma
shima in ya shigo gidan sau goman kuma zai
tambayi Anti Rahma ina Adawiyyah take? ta ci

73
abinci kuwa? tasha maganin ta? Nanj da nan na
dawo cikin hayyacina na samu lafiya da
kwanciyar hankali a dalilin na rabu da bacin rai
gashi nan babu mai kuntata min.
Yaya Almu kuwa yazo gidan nan ya kai sau
goma don suyi maganata da Yaya Junaidu shi
kuwa yaya Junaidun ya ki yarda suyi maganar sai
suyi hirarsu su gama in ya kawo mishi zance na
sai ya ce mishi mu bar wannan maganar tukuna
sai ka gane ni din ba wai ba ne, yaya Almu ya ce
haba Junaidu na ce kayi hakuri kan abin da ya
faru ba zan sake ce maka kawun wai ba ka
taimake

Please Login or Register in order to submit comment