Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan Yaya
Almu na farko kenan, da sauri yaya Almun ya fito
yana yi mishi sannu da zuwa bai tanka mishi ba,
ya kalle ni ya ce min nan nace miki ki zauna
umarnin da na baki kenan, ya juya ya fita ya tafi.
Yaya A lmu ya shigo yana min sannu da zuwa
tare da tambayata inda na tafi? Ban tanka mishi ba
na dai gane kawai hankula sun tashi saboda daga
shi har Lailatun sun shiga cikin hankalinsu, banga

57

su Tanbai ba ban kuma tambayi inda suke ba sai
wata sabuwar mai aikin.
Dare na yi yaya Almu ya shigo don dama yana
ta nuna zumudi da farin cikinshi kan dawowana,
na ce mishi ba na dawo zama ba ne balle ayi
rabon kwana dani, nazo sauraron hukuncin da
Baba zai zartar ne a tsakaninmu. Fafur na ki
sauraron komai daga Yaya Almu balle kuma wata
Lailatu na ma daina ganin Rabi'atu in sa hannu in
dauke ta balle ayi min wulakanci girki kuwa in
nayi ni da Baba Talatu nake zubawa in bar saura
anan mai so ya diba.
Sati guda cif da dawowana sai ga Umma
Amarya tazo da sassafe ina zaune a kasa a
gabanta bayan na gama shirya mata abin karyawa
shima yaya Almu yazo ya gaishe ta ya kuma ki
fita don ya san Baba ne ya turo ta, sai ta ce min
Alhaji ne ya turo ni in zo kiyi min bayani kan abin
da ke faruwa, bayani na dalla-dalla na yiwa
Umma tun daga farkon zuwan Lailatu gidan har
kawo ranar da na bar gidan ban rage komai ba tun
daga girkin wata takwas da ya sani nayi babu
sannu babu madalla har kawo marina da tayi a
gabanshi da hukuncin da yayi na sanya Lailatu ta
rama dukan da nayi mata kawo kan cewar da ya yi
na yi asirin da na raba shi da ita don kar ta sake
58

haihuwa, babu abin da ban gaya mata ba har da
maganganunshi na cewar bakin ciki zai kashe ni.
Shiru tayi tamfar wacce ruwa ya cinyeta bata
ce komai ba sai shi Yaya Almu ne da yaga shirun
yayi yawa ya ce amma Umma.....tayı maza ta
katse shi ta ce ba wurinka ya aiko ni ba ka bari sai
ya ce yana so ya ji naka bayanin sai kayi wa
wanda ya aiko maka tana fa
[6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: Yanda Baba ya tura sunan Abdulhakam
katagun ya bar wa Baban tudu zabin sunan da za'a
sanyawa jariri haka shima yaya Almu ya tura
radin sunan katagun sai dai shi yaya Junaidu ya
bar wa zabin sunan da za'a sanyawa jariran don
haka ranar suna da sassafe bayan anyi kiran suna a
can sai yayi waya ya fadi sunan yaran Jabir da
Jibrin, muka yi sunan ma a Kaduna suma su
Umma suka yi nasu sunan a gida anyi suna da

114

kwana biyar Umma karama tafi tana barin gidan
kuwa na tsukewa yaya Almu fuska ya tasani a
gaba yana son sanin dalili na ce mishi to dama
muna magana da juna ne yaya Almu? Ai gaba
kake yi dani ba sai muci gaba ba kawai ya ce
amma bai wuce ba? Na ce da aka yi me ya wuce?
Ina halin rashin lafiya baka ji tausayina ba kana
fushi dani sai na samu lafiyar ka ce ya wuce? Ai
muyi tayi kawai, ya kalle ni ya ce baki da hankali
Rabi nayi maza na ce mishi da sannu ai zanyi.
Muna cikin wannan zaman ni dashi sai kuma
Lailatu ta fito da wata ka'ida wai bata yarda da
shigowan da yake yi wurina ba tunda sbanci da
girki zaman jego nake yi ya ce mata haka ake yi
Lailatu ke da kika yi naki jegon haka tayi miki
rikicin yayi tsanani a tsakaninsu har takai karar
shi gidansu aka musu shari'a ban san me aka ce
mishi ba ni dai naga ya shigo dakina yazo ya
zauna ya ce min Rabi taimake ni ki karbi girkinki
yau ban ce mishi don me ba? Ban kuma ce mishi
ba zanyi ba don ba zai yiwu ace ta ko ina ba zai ji
yanda yake so ba don haka sai kawai na ce mishi
to, yayi matukar jin dadin hakan da nayi yayi min
addu'a ya kuma tashi ya fita ya shiga wurin
Lailatu.

115

Duk da sati uku ne kawai da haihuwata Baba
Talatu tana gama abincin gidan dana sata tayi sai
na fito ina sanye da kayan sanyi na suturta jikina
na shiga kicin na shirya mishi abincin shi da
lokacin kwanciya yayi kuwa shigowa yayi ya
sallami Marka da Baba Talatu dake taya ni kwana
da yaran ya ce musu su tafi wurinsu sai da safe shi
zai taya ni duba yara suna cikin gadajensu muma
muna namu, na kalli yaya Almu na ce mishi kai
yaya Almu jego fa nake yi, ya ce nafi kowa sani
tunda ga yantagwaye biyu can ina kallo wadanda
Ubangiji ya azurtani dasu amma hakan ba zai
hana ni in yi abin da naga zan iya ba, jego mai
dadi nayi ran girkina ina manne jikin mijina a
haka muke kwana in yara sun motsa kan in tashi
ya riga ni zai yi musu komai sai dai ya miko min
su ina daga kwance in ba su nono in sunsha sun
koshi ya maida su wurin kwanciyar su, sannan ya
dawo mu kwanta maimakon in takura sai kuma
naga ni gata ma tayi min in bani ce da girki ba
kuwa bana jiran sai yazo ganinsu ana gama musu
wanka da gyara in na basu nono suka koshi sai in
ce akai mishi su nima in kintsa in yi kwanciyata in
yi ta baccina maid a di, kafin in yi wata guda daga
ni har su munyi gwanin sha'awa.

116

Rannan na karbi girki, rannan kuwa kwanan
mu talatin da bakwai ne, kwalliya sosai nayi wa
mijina da zamu kwanta kuma na sanya wata
shu'umar rigar barci da ban taba amfani da ita ba,
ni ina ki ka samu irin rigunan baccinnan ne Rabi?
Na dan kalle shi kadan kafin na maida hankalina
kan yaron da nake baiwa nono don yaya Almu ya
matsa in sa su suyi bacci na ce mishi tun rannan fa
na gaya maka na ce maka set din akwati biyu
Umma tayi min na rigunan bacci kawai, ya mika
hannu yana wasa da igiyoyin rigar tare da fadin
Tiga ce mai kyau Rabi na ce mishi eh.
Kwalliya nayi don in burge yaya Almu in
kuma faranta mishi rai amma ba don wani abu ba
sai kuma ya ki yarda da tsayawa kan wasannin da
muka saba yi, ya ce fafur shi yayi kokari kwanaki
talatin da bakwai din da akayi ai tun ban fi sati
biyu ba yake ganina ina sallah, to ina laifinshi? Da
dai lura kin yarda na zai kawo bacin rai mai yawa
sai kawai na sallama iyaka dai nayi tunanin
matakin da zan dauka wanda zan taimaki kaina
dashi.
Randa muka yi arba'in ranar na tafi Legos ni
dasu da Rabi'atu tare da baba Marka da Baba
Talatu muka je na kaiwa Baba su ya gansu Baba
yayi murna, murna kuwa mai1 tsanani ya kalleni

117

ya ce ikon Allah yau ga uwata da haihuwa har da
ta yantagwaye, ni kam murmushi kawai nayi
Umma karama co a wurinshi itama ina aka saka
damu tayi, nayi kwana daya anan daya kuwa a
gidan yaya junaidu zamanshi da matanshi gwanin
sha'awa komai zasu yi tare suke yi shi kuma yana
tsakaninsu, anti Rahma kuma ta yaba mun da
adalcin yaya Junaidu, daga Legos gida muka
wuce in da muka samu Ummana da Umma
amarya muka fara bakunta mai dadi kwananmu
uku da zwa sai ga Yaya Almu yazo wai zuwa
yayi mu tafi ni kuwa na tubure na ce ai ba haka
muka yi da shi ba, Umma cewa nayi zanyi kwana
biyu a Legos in zo nan in yi bakwai in tafi
katagun in yi biyar sai kuma kawai ko bakwai
dinfarko ba ayi ba ya biyo mu ya ce bakuntar ta
isa haka? Umma ta ce haka kuka yi Babangida?
ya ce ch amma ai ta kwashe mutanen gidan ta tafi
dasu don haka na fara bakuntar ta ishe ni haka
tazo kawai mu tafi gida, Umma ta ce a'a ba zai
yiwu ba sai taje katagun ta kaiwa su Alhajin tudu
yara sun gansu don haka washegari muka nufi
katagun har da yaya Aimu muka je mukayi kwana
biyu muka wucc gida.
Watana shida da haihuwa su sabir sunata
zamansu har suna nema suy1 rarrafe sunyi

118

matukar yin girma gasu da lafiya gasu kullum
kamanninsu sai karuwa yake yi yaya Almu sai ji
dasu yake yi in suna wurinshi barin komai yake yi
yayi hidimarsu, na shiga dakinshi na same shi tare
dasu na ce mishi yaya ko zan je asibitin ne? Ya
kalle ni cikin natsuwa ya ce me kuma ya faru? Na
ce mishi yauma al'ada nake yi kuma ba ka ga
yanda take zuba ba kamar ba kwana bakwai ba ne
kawai da daukewar wancan ya ce min to har na
kama hannun Rabi'atu zamu tafi sai naji ya ce min
tsaya Rabi, bari in zo mu tafi tare na gaji da
wannan al'adar taki tunda muka fito daga asibitin
yaya Almu bai ce min komai ba ga dukkan alamu
dai ranshi a bace yake ban san mne Likitan ya gaya
mishi ba don ya kira shi sun kebe can cikin
Zuciyata cewa nake yi Allah dai yasa ba wani abu
ya gaya mishi ba.
Muna shiga gida naji ya kira Marka da Baba
Talatu ya basu yara ya ce su kula dasu, shi kuwa
ya biyo ni daki ya nemi wuri ya zauna ya daga ido
ya kalle ni ya'ce min Rabi ai kin dade kina barin
yin nesa dani ko? Ban iya amsa mishi tambayar
ba saboda mamakin da ta bani kan in yi tunanin
amsar da zan bashi sai naji ya ce za ki iya yin
hakan a yanzu dama kina da gidan da kika sai wa
kanki don hakan to ki koma ciki ki zauna ba zan

119

zo inda kike ba, na kalle shi na ce me ya faru? Ya
ce babu komai ganinki ne kawai bana so na kuma
baki minti talatin ne ki fita ki bani wuri, na ce ba
ma sai an kai haka ba na mike na dauki jakata na
fita na tsaya ina kiran Baba Talatu ta kawo min
yara ya biyo ni da sauri ya ce bar su a inda ki ka
same su.
Tsananin mamaki da kaduwa ne ya same ni
don haka ban je inda ya ce din ba gida na wuce
kai tsaye don nasan Umma tana can na gama
mayar mata da bayanin yanda aka yi duka
mamaki ya kamata ta ce me kika yi mishi haka?
Na ce nima ban sani ba sai tà ce to bari yazo muj
tunda na kira shi, sai dare yaya Almu ya iso na
kuma yi sa'a yazo da yaran har da Rabi'atu, yana
shigowa ya ganni ya ce me ya kawo ki gaban
Umma Rabi? Me yasa in wulakancin ki ya motsa
ba kya barin abin ya tsaya tsakanina dake sai
kinzo gabanta don kiyi sana din 6acin ranta? Ba
gidanki na ce ki tafi ba?
Umma ta ce haba nifa nasan haka kawai ba za
ka yi irin wannan hukuncin ba, ina kuka yaya
Almu ya kalle ni cikin takaicin ya ce ban san me
zance miki ba Umma iyaka dai kin san mas'alar
data samu Rabi ta yawan al'ada har tana ta zirga-
zirgar asibiti Umma ta yi maza ta ce mishi eh, ya

120

ce to allurar da take yi ta hutun haihuwa da tsarin
iyali ne ta jawo mata abinda Likita ya gaya min
kenan.
Umma tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta yana
ganin haka ya mike zai fita wai zai je gaida
Umma amarya Umma ta ce mishi debi su Jabir ka
kai mata, ya ce to yana barin dakin Umma ta
Soma zagıina wani irin zagin da bata taba yi min
ba har tana kirana butulu, haihuwar da muka nema
kamar yaya? Muka hadiyi bakin cikin da bai
misaltuwa akanta ita ce a yau kika je neman tsari
da ita saboda ke butulu ce maimakon ki zauna
kiyi tayi wa Ubangiji godiya kan ni'imar da yayi
mana, to ni ba su ishen ba jeki ki haifo su a jaka
Adawiyyah ki kawo mun su, ba Lamido kike so
kiyiwa tsiya ba, ni da dan 'uwana kike so kiyiwa
don mune bamu da wata hanya ta yaduwar
zuriyarmu sai ta dalilinki, Lamido ai in ya kara
aure zai samu ya'ya a tare da matar, yanzu ma
kuma kina tare da wata na kuma ji karama tana
cewa ciki ne da ita, har yaya Almu ya dawo
Umma bata hakura ta bar fadan da take yi min ba
cikin sanyin jiki ya nemi wuri ya zauna ya shiga
bata hakuri har yana ce mata wai ba butulci ne
yasa nayi hakan ba wahalar kurarrajin bakin dake

121

hana min sukuni ne dalili amma nan gaba 71
dauki matakin da ya kamata.
Da aka natsa yaya Almu ya ce in tashi mu tafi
gida sai na ce mishi a'a ya barni kawai ya yi
tafiyarshi ai tunda ya ce in fita in bar mishi gida
ba zan sake komawa wannan gidan ba, ya soma yi
min magana kiyi hakuri Rabi raina ne ya 6aci
kema kin san.....Umma tayi maza ta katse shi ta
ce kar ka baiwa Adawiyyah hakuri Babangida,
kyaleta tayi abin da taga ya yi mata daidai ba dai
burinta ta bata min rai ta sanya ni bakin ciki ba?
To ta yi ta ji dadi ni kuma na yafe mata, na yafe
miki Adawiyya na yafe miki kiyi min duk abin da
kike so ba zan ji zafin ki ba, zanyi ta yafe miki
tana maganar tana kuka, hankalin yaya Almu yayi
matukar tashi ya shiga bata hakuri yana fadin
laifinane Umma da na zartar da irin wannan
hukuncin na dauka zata bi umarnin da na bata
nata koma wurinta ban san zata kawo maganar
gabanku ba amma kuyi hakuri, ke Rabi jeki ki
dauko su Jibrin sai kizo mu tafi, Umma tayi maza
ta ce a'a abar wa Maryam su bata da kowa a
dakinta zasu yi mata dadi.
Zubewa nayi a kasa ina kuka a gaban Umma
bata kula ba, yaya Almu ya soma bata hakuri
cikin sanyin jiki don shima bai son rabuwa da

122

yaran ta ce mishi kul ka ce zaka yi min wata
magana ai na bar muku su sune ina jiran ku samu
wani kar ayi ta barinku cikin kewa tunda kuwa
basu dame ta ba to taje.
Haka muka fito daga gidan daga ni sai yaya
Almu itama Rabin Umma ta ce a barta a gidan ni
kam nayi kuka har na gaji a gida kuwa ga kewar
Rabi'a da yara ga ciwon nono gashi yaya Almu ya
tasa ni a gaba duk wanda ya tambayi yana sai ya
gaya mishi abin da nayi wanda yasa Umma ta
kwace su duka wai har da yaya Junaidu ya gaywa
shi kuma tunda ya gaya mishi ya daina maganna
dani ko gaishe shi nake yi a dake yake amsawa
wai bai taba ganin mai rashin hankali irina ba
gaba daya na tsargu babu abin da nake so irin in
sake jin Rurarrajin baki sun sake feso min shiru
babu su babu dalilin su, hankalina yakai matuka
wajen tashi kar dai na daina haihuwar kenan?
Kullum tambayar da nake yiwa kaina kenan a duk
lokacin da na tuna abin da nayin da irin wahalolin
da muka sha a baya da bakin ciki da gorin
haihuwar da akayi tayi sai inga to in ban da
butulcin da Umma ta ce ina dashi me zai sa in je
ieman hutun haihuwa? Ina yin irin wannan
tunanin sai in yi maza inyi ta istigifari ina neman
gafarar Ubangiji, yaya Almu kuwa kusan kullum

123

sai ya gaya min cewar shi fa ya riga ya saba da
mu'amalla da yara tunda ni da Lailatu mun sake
zama juyoyi to shi gaskiya zai nemi auren
badurwa mai sha biyar ko sha shida wacce kafin
ta gaji da haihuwar zata haifar mishi ko guda
goma, in ce yana kyau haka din gara ka himmatu,
ana cikin wannan halin rannan ina kwance kan
gadona da rana na ji wani motsi da yayi min kamaa
da motsin da a cikina zumbur nayi na mike zaune
na kasa kunne ko zan sake jin wani motsin ban j1
ba, shiru ban sake jin komai ba na yi ta duba
bakina ko zanga wurin da kurji ke shirin fitowa
babu wata alama, har na hakura. Washegari dai da
sassafe na nemi 1Zinin yaya Almü na zuwa asibiti
ba tare da ya nemi sanin abin da zani inyi ba ya
bar ni na tafi ina zaune a gaban Likita yana yi min
dariyar yanda aka yi wai na haihu har da 'yan
tagwayc amma na zauna da ciki yayi watanni ban
gane ba, cikin zuciyata na ce Albamdulillahi na
karbo magungunana na kama hanya na dawo gida
ko Umma ban gaya wa abin da nake ciki ba, jan
bakina nayi na yi shinu, gashi kuma nayi sa'a
wannan cikin yasha banban da saura, cin abincina
nake yi bani da wata mas'ala sai nayi kyau nayi
kiba nayi mulmul gwanin sha'awa cikin kuma ya
6ace a jikina kamar babu shi, an dauki lokaci mai

124

tsa wo yaya Almu bai gane ba shima don anyi
dace ne yayi motsina shi.kan ya ankara kuwa sai
kawai yaga na haihu sai dai wannan karon ma da
namiji aka samu sai aka sanya mishi Muhammad
Bello wato sunan Baba kenan tun daga wannan
lokacin ban sake wani tunani na neman hutun
haihuwa ba tuni ma na daina sha'awarshi na kuma
koma ganin wautar mata masu yi saboda irin
illolin da ya haifarwa.
Abdulhakam bai gama cika sheka ru takwas ba
a duniya sai da na haifar mishi kanne biyar gaba
dayansu kuma maza don haka a yanzu yaya Almu
ya'ya bakwai ne cif dashi mace daya Rabi'atu sai
maza shida dan karaminsu kuwa shi ne takwaran
yaya Junaidu.
A wannan lokacin tausayin Lailatu nake ji tun
daga haihuwar Rabi'atu ko bari bata sake ba, tayi
karyar cikin har ta gaji ta zubawa sarautar Allah
ido ga Maryam mai auren kwanannan wai har ta
haifi 'ya'ya uku a gidan yaya Junaidu. Anti Rahma
shida amma ita shiru, duk da mun yi kwanaki sun
kai hudu ni da ita ba wani kula juna muke yi ba
saboda in suna 'yartsama da yaya Almu sai ta
hada har dani da na ji tana yi mishi maganar zuwa
asibiti bai kula ba wai shi ya gaji da biyan kudin
wankin cikin da babu am fani, shiga daki nayi na

125

dauko kudi nazo na bata na ce mata jeki Asibitin,
ta ce a'a tana dasu na ce karbi dai nawan ai ba ke
ya kamata ki biya kudin asibiti ba, ta je ta dawo
kuma na tambaye ta abin da suka ce, bata boye
min ba don haka da kaina naje na samu Baba na
gaya mishi mas'alar da Lailatu ke ciki, bayanin da
nayi mishin yasa ya sanya yaya Junaidu ya
shiryawa Lailatu tafiya kasar Cairo don ganin
Likita.
Bayan dawowan Lailatu Umma karama tazo
gidan ban san me ta ce mata ba na dai ji ta kawai
tana cewa a'a Umma ni na riga na gaji da wannan
fitinannen zaman, a yanzu nafi bukatar zaman
lafiya akan komai, musamman ma da yake duk
mugun abin su da ake gaya min nima dai ita mun
yiwa juna rashin kirki, tunda ita kam sha yanzu ne
magani yanzu, to uwarta kam in na ce ta taba yi
min wani abu ba alheri ba na yi mata karya, don
haka a yanzu zan koma amfani da zahirin abin da
idona ya gani maimakon jita-jita da tsofaffin
labarai na abin da aka yi shekara da shekaru, ina
jin umma karama ta kama salati nayi maza nayi
wucewa ta, cikin zuciyata dai murna nayi da
Lailatu ta gane fitintunun dasu Umma karama ke
sanyata ba komai zasu haddasa mata ba illa rashin
zaman lafiya da kwanciyar hankali.

126

Tun daga wannan lokacin na dauki matakai
masu yawa don ganin mun zauna lafiya da
Lailatu, don haka in zan sai wa kaina abu sai
itama in saya mata, in kuwa naji tana neman wani
abu wurin yaya Almu bai yi mata ba sai in yi mata
da kuma na lura tana kokarin gyara mu'amallarta
da yara maimakon da da bata shiga harkarssu
yanzu har tana sauraron maganarsu sai nima na
rinka dorata kan al'amuransu, ko wani abu nasu
ne ya taso sai in ce yaya Almu ya sata tayi, shima
kuwa yayi matukar jin dadin hakan, nan da nan
sai zaman mu ya dawo gwanin sha'awa rannan na
shirya zan tafi makarantar islamiya ta asabar da
Lahadi da nake zuwa sai na ce mata Lailatu ko
zan karbo miki form ne mu rinka zuwa makaranta
tare muna jin wa'azi? Kinga ba wani wahala ne da
ita ba sau biyu ne kawai a sati? Yaya Almu yayi
maza ya ce min a'a Lailatu ai tun tana 'yar karama
taji wa'azinta wuce su nayi na tafi don nasan
zolayarta yake so yayi da zan dawo sai nazo mata
da form din ta cike muka soma zuwa tare. Nan daa
nan ni da ita muka zama tanfar 'yan uwa komai
zamu yi tare muke yi, in wani abin gida ne ya taso
sai in shawarce ta mati yawanCin lokaci kuma na
kan yi amfani da ra'ayinta ne in bar nawa a
wannan lokacinne na fahimcI Lailatu mutunivar
127


kirki ce, mafi yawancin abubuwan da tayi ta yi a
baya sata aka rinka yi ba halinta ba ne ita da kanta
Lailatu taji dadin halinta da ta canza saboda yanda
matsayinta ya karu wurin yaya Almu ni da kaina
ban san yana yi mata irin son da yake yi mata ba
sai a wannan lokacin da ta yarda da zaman lafiya,
nasha jin shi yana cewa yana girmamata da ganin
darajarta tare da jin tausayinta saboda ita ce uwar
Rabi'atu 'yar da yake so kamar me? Sannan gashi
bayan ita bata sake ba don haka a yanzu shagwaba
take yi mishi irin yanda yanda taso nima kuma
bana sanya ido kan abin da ya shafe ta da mijinta,
tunda tana bani girmana ta kuma sa hannu biyu ta
rungumi al'amarin yara.

**
Shekaru goma bayan wannan lokacin na 1sa
gida da yamma ni kadai amsa kiran da Umma tayi
min nayi.
Gidan cike yake da jama'a babu masaka tsinke,
duk kuma wani wanda yake cikin gidan in ma dai
da ne da baba ya rike ko kuma jika don haka taro
ne na yan uwa, ma'ana babu wani bare a ciki.
Sashin Umma Amarya na fara zuwa, Jibrin na
fara gani ya fito da sauri zai karbi jakar dake
hannuna, na kalle shi nayi murmushi na ce mishi

128

ga dukkan alamu aiki kuke yi saboda irin gumin
da nake gani a tare da kai don haka jcka kayi
aikinka ni zan iya kai jakata cikin daki tunda ai
kaga makale take a hannuna ya taya ni
murmushin da nake yi ya wuce ya tafi, na samu
Umma a zaune a nemi wuri na zauna na gaishe ta
na ce mata yaya jiki ta ce da sauki ai na ji sauki
sosai na ce babu inda yake miki ciwo kenan? Ta
kalle ni cikin natsuwa ta ce anya ana yin haka?
Kayi irin wadannan shekarun da muka yi sannan
ace an zauna babu abin da yake yin ciwo? An dai
gode Allah tunda komai kana iyawa, na ce haka
ne umma sai da muka danyi hira kafin na mike na
nufi wurin Umma karama na gaishe ta sannan
naje wurin Ummana, tana ganina ta daure fuska
ke in banda na kira ki in ce ko da ba za ki zo ba
ne? Na yi shiru ban ce mata komai ba ta kama yi
min fada, Lailatu dake wurin ta kalle ta cikin
murmushi ta ce mata da kuma tahowa don kanta
tayi Umma da kinyi mata fada kince tayi rashin
kunya gaba daya aka kwashe da dariya Umma ta
yi murmushi ta ce to shi kenan na bar fadan tunda
yar uwarki ta tare miki to amma ai wannan
sha'ani ba biki bane hidima ce ta addini ai kya zo
ayi ta dake, ni dai ban ce mata komai ba. Anti
Rahma ta shigo wacce ita da Lailatu' ne a tsaye

129
kan hidimar tunda aka fara ta sunyi kusan sati
guda a gida suna shirye-shiryen zuwan ranar sun
sauka Umma yanzu an tafi dauko su nan ba da
dadewa ba za su iso Umma ta kama murmushi
tana share hawayen dake zuba a idonta tare da
fadin babu Abdulhakam da uwa sai ni da Alhaji
mune muke gunan musu, nan da nan aka shiga yi
musu addu'a ita kuma ana bata hakuri.
Wajcn karfe takwas da Rabi na dare suka iso
kai tsaye babban falon karbar biki aka zarce an
riga an shirya komai don haka ba'a dauki wani
lokaci mai tsawo ba aka soma gabatar da al'amura
bayan an gabatar da nau'o'in abinci iri-iri ga
jama'a.
A hankali na shigo wurin daga can baya na
tsaya ina kallon duk abin da ake yi Abdulhakam
wanda ake yin abin dominshi yana zaune tsakanin
baba da yaya Junaidu tanfar wani babba alhalin
shekaru goma sha bakwai ne kacal da shi, kullum
kamanninshi da baba kara bayyana suke yi abin
da kc sa wa mutane da yawa suke zaton wai ko
karamin danshi ne kamar kullum yauma anko
suka yi dai dai yau ankon nasu ya dan banbanta a
dalilin shi Abdulhakam yana sanye da alkyabba
da kuma rawanin da aka nada mishi

130

Baba na samu yana magana kamar bayar da
labari yana kuma maganar ne cikin murmushi
alamar dai a Cikin farin ciki yake.
Ita kuwa ai hakurinta ba mai yawa ba ne
uwarta ta fita hakuri, a zuciyata na ce a'a yau
kuma me na yiwa baba yake kirana mara hakuri
bayan na saba jin shi yane yabona akan hakurin?
Da na kasa kunne da kyau sai na ji shi yana cewa,
lokacin da ta rasa haihuwar nan ai nema tayi ta
bijirewa Lamido na ce mata uwata aure daban
haihuwa kuma daban ko babu haihuwa ana zaman
aure ta ce a'a ita in bar ta kawai ta yi nesa da shi
ya gara zama ya ce to a wancan lokacin nayi ta
min addu'o'i da alkawura masu yawa saboda ina
son auren nasu, na kuma san rashin-haihuwar ita
ce babbar barazanar da auren yake fuskanta a
cikin addu'o'i da alkawuran da na

Please Login or Register in order to submit comment