Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanki in ce mishi
haka ne in yi tafiyata.
Rannan ina dakina da daddare addu'a nake yi
bayan na idar da sallah hakuri da dangana nake
rokon a kara min, sai na jiwo salatin Lailatu cikin

38

gurnanin kuka, da sauri na shafa fatihar na yiwo
waje zan shiga dakin nata don naga kofar a bude
sai kawai naji Y aya Almu yana rarrashinta wai ta
bar shi yaje ya taso ni don bai kamata su tafi
asibiti bai gaya min ba ina jin haka nayi sanaf-
sanaf na koma dakina na hau gadona na kwanta
tunda dai bata son in sani. Zuwa can ban san
yanda aka yi ba sai gashi ya shigo dakina yana
fadin ke Rabi tashi muje mu kai Lailatu asibiti ina
ganin nakuda ce ta tashi mata kamar in ce mishi
ba zani ba tunda bata da bukatar zuwan nawa sai
kuma naga to don me zan yi hakan'? Na sanya
hijabina na biyo bayanshi nasa hannu na kinkimi
manyan akwatuna guda biyu da aka shake da kaya
tanfar dai in anyi haihuwar can za'a zauna, shi
kuma yaya Almu ya ciccibota ita da cikin nata
zuwa cikin mota a haka muka isa asibiti, sai
faman gurnani take y1 ina ta nanata sannun da
nake yi mata, amma ban samu ta amsa guda daya
ba.
Gwajin farko da aka yi mata Nos din ta ce
Hajiya da kin rike wannan nishin naki da kike
faman yi sai bukatar nishin ya taso tukuna don in
haihuwa tazo miki da sauri to sai kiyi ta nan da
awa shida, na kalli agogo na ce zuwa takwas din
safe kenan, yaya Almu ya bar mu a asibiti ya tafi

39

gida kan cewar zai je yayi sallah ya yi wanka ya
dawo na ce mishi to, ina nan a wurin sai ga
mutanen gidansu sun is0 in ban da na gaishe su da
babu wanda ya ce min in ci kaina, muka zauna a
haka suna sha'aninsu nima ina lazimina sai in sun
jiwo mun hada ido su kwashe mun da dariya ina
kallonsu.
Wajen karfe bakwai yaya Almu ya dawo, na
ce mishi to bari nima inje gida in dawo ya ce, a'a
bana so ta haihu ba kya nan a wurin nan na ce
mishi to na hakura, haihuwa bata zo ba sai wajen
karfe daya da kwata muna wurin a tsaye, Nos ta
fito tana tambayar ina wadanda suka kawo Lailatuu
Mustapha muka yi maza muka mike ni dashi
muka ce gamu suka ce to ta haihu an samu ya
mace ni da Yaya muka kama murna yayin da
fuskokin yan uwan Lailatu suka sauya alamar daa
ba haka suka so ba.
Muna shiga dakin na nufi Lailatu na rungume
ta don murna turus din da ta yi mun ya dawo dan
Cikin haiyacina na juya wurin yaya Almu dake
rungume da yarinyar cikin matsanancin farın ciki
yana ganin na kalle shi ya miko min ita, ungo ta.
Rabi 'yarki ce ki rike ta taki ce ki rike ta da zuciya
daya kiyi mata reno da gata irin wanda Umma
tayi min ki kuma yarda da cewar haka kaddara ta

40

shiryo mana don kuwa kin san in da ina da iko
akan al'amura to da ba haka ba, da na baki
haihuwa kinyi ta-Rabi, kin yi ta har sai ta ishe ki
kafin in baiwa sauran mutan da suke nema to bani
da ikon komai don haka kiyi hakuri, na ce mishi
babu komai Yayaa Ubangiji ya raya mana ita da
imani yace mun amin.
Juyawan da zamu yi sai kawai muka ga Lailatu
tana ta faman kuka da sauri Yaya Almu ya
tambaye ta ko menene? Sai ta ce mishi wai tun
bata wastsake daga azabar nakudar da ta sha ba
har yayi mata kyauta da yarta kuma a gabanta
yana cewa dashi ke ba da haihuwa to da ba ita zai
baiwa ba ni zai baiwa t ai abin na Allah ne in ma
shi ba ya sonta Ubangijin da ya yi ta yana sonta ni
da Yaya muka yi ta rarrashi muna yi mata bayani
don fahimta r da ita abin da ake nufi.
Bayan fitar Yaya Almu 'yan uwan Lailatu suka
shigo suka karbi yarinya ina jinsu suna cewa
wannan yarinya irin kamar da ta yi da Ubanta ina
jin da namiji aka yi niyyar yi, surkullen da aka yi
tayi ne yasa tazo a mace, surkullen da aka yi
kuwa cikin da ya fiddo mace ai shine watarana zai
fiddo namiji, naje yi dai ko in ce a juri zuwa rafi
da tulu gaba daya suka kwashe da dariya.

41
Ni kam jin su kawai nake yi ina kuma
sabgogina tanfar dai ban san dani suke yi ba.
Tunda 'yan uwan Lailatu suka wastsake daga
kaduwar ya macen da aka samu maimakon
namijin da ake sa ran gani sai kuma suka koma
hirar da suka saba na fadin darajar mace mai
haihuwa yanda nan da nan take zama ta gaje gida
ta zama ita ce uwar iyali ita da miji kuma sun
zama daya sun zama ita yashi shi ya ita ta zama
shi da dukiyarshi duka nata yanzu fa daga wannan
haihuwar da Lailatu tayi komai na Lamido na
tane, dayar ta ce na tane mana tunda ko mutuwa
yayi 'yarta ce mai gadonshi, gabana ya yanke ya
fadi saboda jin ana anbatowa Yaya Almu mutuwa
don kawai an haifi 'ya guda daya tare dashi.
A wannan lokacin na samu kaina cikin
tsananin son Ummana da jin tausayinta saboda naa
kara fahimtar ba karamin hakuri tayi ba a zaman
da tayi gidan Baba ni dama nake zaune da Yaya
Almu cikin gatan da babu wanda ya isa ya fito fili
ya nuna min wata kiyaiya ko wulakanci saboda
1don Umma ya tsare al'amura masu yawan gaske
kenan nake ganin haka akan rashin haihuwata to
ita fa yaya taji da nata a lokacin da babu mai tsare
mata? Ni kam a yau na sami ko Umma karama
dake ta faman kai-kawo cikin al'amarin a boye

42
take yi sai dai ta cinma ayi amma bata fito fili ita
da kanta tayi ba shi yasa ma ban taba buda baki
na gayawa ita Umman ko baba irin zirga-zirgan
da take yi a wurin Lailatu ba.
Hakika na yarda na sakankance cewar matar
dake da mas'alar rashin haihuwa suna ganin abin
da suke gani na bakin ciki da kunan rai,
musamman idan suka yi dace da irin mutanen nan
da aiki da hadisin Manzon Rahama mai cewa
Imanin dayanku ba zai cika ba har sai yaso wa
dan uwanshi abin da yake so wa kanshi.' bai dame
su ba.
A wapnan lokacin ji nake yi tamfar ba don
kaina nake son haihuwar ba ba kuma don Yaya
Almu ba tunda shi kam ai ya riga ya samu son
haihuwa nake yi don Umma na ta dai sa hannu ta
dauki dan da na haifa dan da na san shi kadai ne
zai zo duniya ya debe mata kishirwar haihuwa da
bakin cikin rashinta da ta rayu a ciki, sannan ni
ban damu ba ace mace ko namiji na samu in dai
mutum ne mai amsa sunan bil'adam ai bani da
zabi sai ko godiya, in na tuna halin da nake ciki
da yanda Umma ta rasa kuzari da lafiya tun daga
auren Yaya Almu zuwa yau duk da dai ta hadiye
komai a cikinta babu mai sanin tana da wata
damuwa.

43
Muna dawowa gida nay1 shiri na dauki yarinya
na lullube ta na hau Jirgi na nufi Legos da ita na
kaiwa Baba ya ganta, tana hannun Baba bayan ya
gama yi mata addu'a yana kallona cikin tsananin
farin ciki ya ce a'a uwata kun samu ya a gidanku,
na yi murmushi na ce mishi wannan tawa ce Baba
ni kadai in ta sake haifo wasu to suma sai su
samu, Baba yayi dariya ya ce kiny1 gaskiya uwata.
Kwana uku ca dawowarmu Baba ya aiko min
da wata motar sabuwa dal wai tukuicin kai mishi
yarinya da nayi, Lailatu da 'yan uwanta kuwa abin
yayi matukar kona musu rai har suna fadin wai ai
wannan shi ne wani da tusa wani da karbe riga,
wannan in dai ba Jirgun sama Zai sai wa maijegon
ba ai baa kulla gaskiya ba.
Kwana hudu da haihuwar Ummana tazo ganin
yarinya kai tsaye dakin Lailatu ta fara shiga ta
dubata suka kuma gaisa da yan uwanta sannan
tasa hannu ta dauki yarinya ta fito da ita ta shiga
falon yaya Almu na same su a ciki tana kokarin
hudawa yarinyar kunne wanda in ban da Yaya
Almu yayi kashedin kar a huda da tuni iyayen
Lailatu sunyi hakan na ce Umma shi ne sai yau ki
ka zo buda mata kunnen bayan tasha iska ta gane
zafin jikinta, Umma tayi dariya ta ce ita dai
raguwa ce kawai mika ta a bata nono na ce to na

44
karbe ta na kai musu na dawo na zauna muka
gaisa sai ta miko min wani dan akwatin da ta
fiddo daga cikin Jakarta nasa hannu biyu na karba
ina kallonta sai ta ce min kayan kwalliyar yarki
ne a ciki na ce to Umma ai kuwa dai mun gode.
Anyi shagalin suna irin wanda ba zai yiwu a
tsaya bada labari ba, abu guda daya da zan fadi
dai shine, 'yan uwa na birni da na kauye abokai na
cikin kasa da waje sun halarci sunan, gaba daya
cewa ake yi Lamido ya samu haihuwa, don haka
ya zama dole a zo mishi suna Rabi'atu sunan da
yaya ya sanya mata kenan, kyaututtuka kuwa inin
wadanda Lailatu ta samu abin sai wanda ya ganı,
amma bata gamsu ba saboda gaba daya kayan da
ya fito daga gidanmu raba daidai akayi mana
banbancin kawai shine kayan yara haka nan
abokan yaya Almu suma kyautar raba daidai suka
yi mana wannan dalili sai yasa ta kawar da kai
daga kan abin da ta samu ta zubawa nawa ido tà
mance cewar ita ce ta haifi 'yar, ta mance da
cewar ni zan iya bayar da komai nawa don in
samu 'yar kawai kar a hada mun ita da komai.
Bayan yan suna sun watse muka dunguma
cikin wai sabon zaman kuma zaman da nake
matukar son ganin nayi mu'amalla mai kyau da
yarinyar da muka samu yayin da ita kuma uwar

45
yar take iyakacin kokarinta wajen ganin ta shiga
tsakanina da ita, nayi matukar kokarina wajen
ganin al'amura sun daidaitu tsakanina da Lailatu
musamman ma da yake ita ce wacce zata zama
uwar 'ya'yan yaya Almu to me zai sa muyi ta
fitina da ita? Na so ace Lailatu ta yarda mun
zauna lafiya tayi ta haihuwar 'ya'yanta ni kuma ina
renonsu to taki duk wani tayi na zaman lafiya da
na kawo bata karba ba ta kabar dashi maimakon
ta fahimci dalilin sassaucin da nake yi ta dan
karyo don mu zauna lafiya, amma ina? Sai ta
maida abin tsoro a bisa wannan dalili sai ya zama
mun dole in kare kaina daga mummunan
wulakancin da take fito min dashi babu abin da
Lailatu ke yi min da yake matukar kona min rai
irin sau goma in zan sa hannu in dauki Rabi'atu to
sau goma kuma zata biyo ni tazo ta kwace ta ta
tafi tana cewa zo muje kar a lashe miki kurwa
kamar yanda aka lashewa ubanki.
Rannan tayi hakan akan idon Yaya Almu ya ce
haba Lailatu me yasa kike yin irin wanan abin ne
Ta ce a'a a'a ta haifi nata, yi kokari ta haifi nata
kawai amma kar asa min ido akan nawa bana son
1ya yi da neman wurin shiga irin nasu na gado.
A fusace yasa hannu ya karbe yarinyar ya
miko nmin ita ni kuwa sai nasa hannu na karbe ta

46
na rungume ina rarrashi saboda kukan da take yi a
dalilin tsorata da tayi ita kuwa Lailatu sai cewa
tayi tir da halin rashin zuciya irin taku ke kam ina
jin sanda ake rabon zuciya ba kwanan a wurin ta
juya ta nufi dakinta tana ganin Yaya Almu ya
shiga wurinshi tayi maz ata fito tazo ta sure
yarinyar ta shige daki ta kullo kofa ta barta tana ta
ihu.
A wannan lokacin dan Rankanin abu ne zai
tashi Lailatu tayi mun gorin haihuwa ta ce mun n
da da sai dai inga shirwa ta dauko dan tsako, ko
kuma ta ce haihuwa ai ba abar banza ba ce
gadonta ake yi in na zauna zanyi kukan bakin ciki
sai Baba Talatu ta rufe ni da fada ta ce kukan
butulci nake so in yi in ba haka ba menene ba ayi
min ba na ni'imomin rayuwa? In ban da halinki na
rashin zuciya me zai sa ba za ki fita hanyar yarta
ba ba akanta take wulakanta ki ba? Na ce ba 'yarta
ba ce Baba 'yar Yaya Almu ce don haka tawa ce,
taja tsaki ta ce ai sai kiyi.
Kalaman da Baba Talatu ke yi mun sun sanya
Di na zamo mai yawan godiya a duk lokacin da
damuwar rashin haihuwa ta bijiro min na kanyi
maza in shiga kirgo ni'imomin da aka ni'imtani da
su misali ni din marainiya ce bani da uwa bani da
uba ban ma sansu ba, to amma sai na girma cikin
47

gatan da ya hana ni sanin ni din marainiya ce
saboda samun Umma da Baba da nayi wadanda
suka yi min gata suka maida ni yar lelensu har
vau din nan kuma ban taba neman wani abu na
rasa ba matukär abu ne wanda zasu iya yi min shi ba.
Rannan ina cikin kicin ina aikin abincina don
ni ke da girki ina shirya abincin rana duk da nasan
Yaya Almu ba ci zai yi ba saboda yakan kwana
ashirin bai ci abincina ba wai ban iya ba, abincin
nawa babu dadi (taste) wato dandano, don haka in
daina yi dashi na ce mishi to.
Aikina nake yi ina rero baitocin Celine dion
cikin wakarta mai taken Becouse u luv me.
For all the standu stood for me,
For all the truth dat u made me see
For all the joy u brouth to my life,
For all the wrong that u being right.
Aikina nake yi ban kula zirga-zirgar da Lailatu
ke yi tana fadin za'ayi kwaba ba har na iso inda
take cewa. I was blessed b/cos was loved by y,
sai kawai na ji Lailatu ta kwashe da dariya tana
fadin da kenan amma yanzu ba ta taki ake ba kina
dai zaman rashin zuciya ne kawai.
Ajiye bayan Lailatu nasa hannu na cafke ta na
bayan Lailatu nasa hannu na cafke ta na wanketa

48


da marI sau biyu, ta miko hannu zata rama na
cafke shi na murde da karfi, ta kwallara ihu, Baba
Talatu ta fito, kar kiyi fada da ita ga goyo a
bayanta uwardakina, na cc mata to, na saki
Lailatu na juya zan shiga kicin in ci gaba da
aikina, sai kawai ta kama zagi tana ashar tana
fadin wasu mugayen maganganu akan Ummana
har tana tambayata wai menene bata sani ba
namu? Ai komai an bata labarinshi da dai na ji
rashin mutuncin nata ya ishen, sai kawai na fito na
same ta nasa hannu na 6alla tawul din da tayi
goyon dashi na kama yarinyar na ajiye ta a kasa,
Tambai tayi maza ta dauke ta tana rarrashinta
saboda kukan da take yi, Lailatu ta shiga fadin bar
ta ta kashe ta dama duk abin da take mata
munafurci ne taga anyi anci niba to anan babu
wata ribar da zaki ci, na ce mata waye yayi ya ci
riba? Tayi maza ta ce uwarki mana saboda itama a
yanzu ta shiryawa danben musamman da yake
taga ta ajiye teba, nayi maza na buge ta ga guiwar
hannuna a baki abin da ya yi matukar kidimata
duka na yiwa Lailatu ranar irin wanda bata taba
zaton zan iya yi mata ba, sannan daga Baba Talatu
zuwa su Larai da Tambai babu wanda ya yi
kokarin rabawa sai cewa suke yi kuyi hakuri su
dukansu suna daga nesa, ni da kaina ne na kyale


49
Lailatu saboda ganin da nayi duk wani kokarin
ramawa da take yi ta daina nace mata gobe ma in
wata magana ta tashi ki sake zagin uwata ki gani
mara mutunci wacce 1yayenta ba su yi mata
tarbiya ba na wuce na shiga wurina na bar ta tana
fadin a zaga din sai dai bata sake ambaton
Umma ba.
Yaya Almu ya dawo ko leka inda yake banyi
ba don kuwa dama ni dashi ganin nanne kawai ita
ce dai tayi ta zirga-zirga zuwa can sai naji yana
kwala min kira ban amsa ba na dai tashi kawai na
tafi na ce mishi gani, a fusace yake magana me ya
faru tsakaninki da Lailatu yau a gidan nan? Na ce
babu komai ya kara fusata babu komai kamar
yaya? Wannan ciwon da ki ka jijji mata fa kamar
wata maiya? Me tayi miki ki ka buge ta? Kina
nufin don takamar kina da karfi sai ki buge ta
'yarki ce? ke wake dukanki, to ba zan yarda ba
don haka zaki yi mamakin matakin da zan dauka
kan wannan abin da ki ka yi zaunar da ke zanyi ta
rama dukan da ki ka yi mata a gabana, na daga
ido na kalle shi nayi murmushi nace wannan shine
tatsuniya, na tashi zan fita daidai ita kuma ta shigo
saboda kiran da yayi mata naga bata da shirin
kauce min a hanya nayi maza na hankada ta ta
fadi a kasa don bata yi zaton zanyi mata hakan ba
50

a gabanshi na wuce na shiga falona, ya biyo ni
yana fadin in baki yi hankali dani ba za ki raina
kanki, da sauri Baba Talatu ta shigo ta shiga
tsakanina dashi tana bashi hakuri, cikin kuka na
ce mata bar shi ya buge ni Baba kar ki hana shi
dukana bar shi ya ramawa Lailatu dukan da nayi
mata ai uwar 'yarshi ce ni kuwa fa? Ina fadin haka
Baba Talatu ta durkusa da guiwowinta biyu a
Rasa tana kuka na wuce naje na shige bandaki na
zauna nayi kuka sai da na gaji sannan nayi wanka
tare da alwala na fito.
Da daddare bayan yaya Almu ya tafi kai
Lailatu da Rabi'atu asibiti saboda wai itama har da
ita na daka naje na kira Baba Talatu a dakinsu ta
biyo ni muka dawo wurina, na shaida mata abin
da na shirya zan yi, cikin sanyin jiki ta kalle ni ta
ce min amma da kararshi gida kika kai aka
tsawatar mishi ina ganin da yafi, na ce ba zan iya
ba ba zan je ina bata shi a gaban iyayenshi ba.
Tunda akayi haka na kama kaina sosai girki
gida dai gaba daya na daina yi sai dai in sa masu
aiki suyi, kullum kuma bana wani cewa ga wata
rana ta girkin Lailatu yaya Almu kuma ko kallon
inda yake bana yi balle inje ina yi mishi wata
magana in dai na ce mishi ina kwana ina gajiya to

51

shi kenan sai kuma gobe. Cikin raina dai nasan
abin da nake shiryawa.
Rannan bayan fitar Yaya Almu da rana sai
nayi mishi waya na. ce mishi lalura ta same ni
yanzu zan fita, ban jira naji amsar shi ba don
nasan cewa zai yi bai yarda ba, nayi maza kuma
na kashe wayar nayi ficewata daga gidan naje na
gama abin da zan yi na dawo sai na same shi a
tsakar gida a tsaye cikin huci ina kika je? Nayi
maza na bude jakata na debo mishi magunguna na
nuna mishi na ce kada gwarzo da kurarrajin baki
sun dame ni, ya kawar da kai daga magungunan
yana fadin tun-tun-tuni da kika fita kina wurin
sayen maganin kada gwarzo da kurjin baki? Na ce
eh na shige dakina ban sake sauraronshi ba.
Wata guda bayan wannan loka cin ina kwance
a dakina da daddare misalin sha biyu da rabi sai
kawai naga yaya Almu ya shigo dakina alhalin
girkin na Lailatu ne, na zuba mishi ido ina
kallonshi cikin, mamaki gashi kuma babu alamar
walwala a fuskarshi, na zuba ido ina kallonshi
cikin sauraro sai kawai naji ya ce min wai me kike
nufi ne da wannan abin da kike yi min? Wai ni
haihuwar nan wani ne yake ba da ita Rabi da zaki
je kina yi min surkullen da ban san dalilinshi ba?
Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi, me nayi

52

maka? Ya ce kar ki ce min ba ki san komai ba don
na riga an tabbatar da cewar ke kika yi kece kika
yi abin da ki ka shiga tsakanina da Lailatu duk
sanda zan kusance ta in rasa karfi saboda kina
tsoron kar ta sake samun wani cikin, to akwai
bakin ciki ne a tsakanina da ke?
Na zuba wa Yaya Almu ido ina kallonshi cikin
kaduwa da kyar na iya buda bakina na ce mishi
darajar aure dake tsakaninmu da kuma na iyayen
da suka haife mu na yafe maka duk abin da kake
yi mn na juya na gyara kwanciyata tare da cewar
amma daga yau ka gama.
Washe gari da safe yana wurin Lailatu ina jinta
tana kuka shi kuma yana ta bata hakuri tare da yi
mata alkawarin daukar mataka kan abin da ke
faruwa, nasa makulli na kulle wurinaa na kira
Tanbai na bata kudi na ce su raba na kuma kira
Baba Talatu muka fice daga gidan.
Ina zamu uwardakina? Na ce mata ke dai zuba
ido kawai ki gani Baba ta ce to.
Titin Sultan na kaimu na yi tafiya ta cikin
layin dake tsakanin bishiyoyi banyi wata tafiya
mai yawa ba na saki babban titin na koma kan
wanda ya nemi yamma gaban wata katuwar
katanga naje na tsaya nayi bon maigadi yazo ya
bude min kofa na shige ciki, sai da ya rufe kofar
53

ya biyo bayana muka gaisa sannan ya koma
wurinshi nima na nufi cikin gidan sosai sai da
naje muka gaisa da matar gidan dake zaune a bovvs
kwatas wacce ta maigidan ce sannan na dawo
nasa makulli na bude asalin gidan muka shiga ciki
ni da Baba Talatu ajiye jakata kawai nayi na shige
wani daki mai bandaki nayi alwala nayi sallah
raka'a biyu nayi addu'o'ina na shafa sannan na fito
na samu Baba Talatu ita kadai a falo, tana zaune
sai kalle-kalle take yi.
Na kalle ta nayi murmushi na ce gidan da na
saya ne wannan Baba hannu biyu ta saka ta dafe
kirjinta alamar kaduwa da mamaki na ce mata
kishiya ce ta koro ki Baba sai ki ka zo kika yi
renona a yau ke uwata ce duk inda zani tare dake
zan tafi, tunda nima kishiyar ta koro ni yanzu sai
kije ki debo mana 'yan jikokinki guda biyu ki
kawo mana su taya mu zaman gidan nan.
Baba Talatu ta zuba min ido cikin mamaki
tana kallona, ke ki ka sayi gidan nan kika gyara
shi haka uwardakina? Na ce mata eh Baba ko ba
ki yarda ba ne? Ta yi maza ta ce a'a uwardakina ai
ba ki da irin wannan wasan na dai kara jinjinawa
al'amarinki ne nace mata tashi ma muje kiga
wurin sosai na zaga da ita wurin na nuna mata

54

ko'ina ta yaba cikin murna da addu'o'i masu dadin
1i sai kuma naga ta fashe da kuka.
Nayi maza na tambaye ta dalili sai ta ce min to
Babangida fa? Na kalle ta cikin sanyin jik na ce
mata to yaya zanyi dashi Baba? Ba zan iya
wannan zaman ba ai gara kawai muyi nesa da juna
sai wajen yamma nayi wa Umma text a dalilin na
kasa boye mata kaina don nasan zata shiga
tsananin damuwa ina tura mata text dn kuma nayi
maza na sake rufe wayata.
Ni da Baba Talatu muna zaune abinmu
zamanmu gwanın dadi hankalinmu a kwance
babu wata fitina girkinmu kawai muke yi muci1 sai
muyi kallo in dare yayi mu kwanta da wuri
saboda biyu da tabi nayi zamu farka ba kuma
zamu sake kwanciya ba sai garı ya waye, bayan
sallar asuba. Tun muna da kwana hudu a gidan
Baba l'alatu ta sanya ni a gaba wai sai lalle na
bude wayata da tata da na rufe don a san inda
muke ai ko ba komai a yanzu tasan Yaya Almu ya
gane kurenshi kan abubuwan da yake tayi min,
nayi murmushi na ce Yaya Almu ai yanzu Lailatu
da yarta ce damuwarshi ta ce wanc shi don dai
kawai yana ganinki ne.
Baba Talatu tayi matukar kaduwa da ganin
gidan da na mallaka na kuma gyara sannan na

55

kawatashi da kayan alatu muna zaune da ita a
bayan gidan cikin harabar dake baya shan iska
muke yi ta kalle ni ta ce min, ni kuwa uwardakina
yaya akayi ki ka samu ki ka mallaki wannan wuri
haka? Nayi murmushi na ce komai nawa na sayar
Baba har da sabuwar motar da Baba ya bani da
duk kayan kwalliyata ko wannan sarkar dake
jikina abin da yasa na barta don Umma ta ce min
ta mahaifiyata ce na kuma hada da ajiyata ta
tuntuni, Baba tayi murmushi addu'a kawai take yi
ita kam ta gamsu ta yarda cewar wai ni din ja
ruma ce don rago baya iya yiwa kanshi maganin
abin takaicin da ya dame shi.
Satinmu biyu cif a gidan rannan ina kwance a
daki bayan na idar da sallar walaha sai kawai na
mika hannu na dauko wayata dake ajiye kan
mirrow nasa hannu na bude wayar nan da nan sai
ga sakonni suna ta shigowa da sauri har wajen
guda biyar, sakon da naga numbar Baba akai na
fara budewa ga abin da na gani:
Anya uwata kin kyauta min wannan abin da
kika yi?
Kafin in kai karshen sakon sai kawai ga wayar
Yaya Junaidu ta shigo kasa bijire mata nayi don
haka na daukc ta da sauri ya tambaye ni kina ina

56

ne Adawiyyah? Na gaya mishi na maida wayar na
ajiye.
Awowi biyu bayan sai kawai naji wayar yaya
Junaidu yana shaida min 1sowarshi kofar gida,
nayi maza na ce wa maigadi ya bude mishi, banyi
zaton ganınshi tare da wani ba don haka nace ya
shigo falon sai kawai na ganshi tare da Baba. A
kidime na durkusa a kasa ina. yi mishi sannu da
zuwa, bai amsa ba sai ya ce min wuce mu tafi ban
yi magana ba nayi maza na bi bayanshi zuwa
cikin motar da suka zo a ciki, shima yaya Junaidu
ya gama kalle gidan ya taso Baba Talatu a gaba
suka zo suka shiga ya fara tuki, har muka isa
gidan Yaya Almu babu wanda ya ce komai in ban
da ni da nake ta faman kuka saboda na gane
maidani zai yi.
Kai tsaye Baba ya tasa ni a gaba har cikin
falona shi da Yaya Junaidu zuwan shi

Please Login or Register in order to submit comment