Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nata yana bata shawara rinka yiwa Rabi
dabara kina tambayarta wasu abubuwa zata koya
miki ita ba mai ganin kyashi ba ce, bata bi shawarar
tashi ba nima kuma ban yi karambani na tsoma
kaina cikin lamarin ba, duk abin da ta girka dai ina
kokarin in ci don kar ace aba ci mas'alar tsakaninta
da shi ne don bai yarda ya ci abin da bai kwanta
mishi ba, na maida ranar girkina lokacin shiryawa
yaya Almu nau'o'in abinci iri-iri, kuma kala-kala in
kuma tsala mishi kwalliya ta burgewa gani kuma da
daukar kwalliyar gashi kuma dama ba wasu shekaru
masu yawa na baiwa Lailatu ba ni ina tsakanin
ashirin da hudu ne zuwa da biyar yayin da ita kuma
take da ashirin da uku tazarar tamu ba mai yawa ba
ne in ta dauro ma sai ayi ganin girmanta don ni
jikina ba mai budewa ba ne da sauri ita kuwa daga
zuwanta har ta fara habakewa in ina tare da Yaya
Almu mancewa da komai yake yi ya tasa ni a gaba
ya raba dare wajen jiyar da kanshi al'amuran da zai
iya abin da yay1 matukar damun Lailatu don nasha
jin ta tana yi mishi kunkuni a duk lokacin da ta zo

21

tana yi mishi magana ta ganshi yana gyangyadi a
kishingide sai ka ji tana cewa eh ni kam ai in ina
tare da kai ba ka da wani aiki sai na ramakon oacci
tunda in kana can kwana kake yi idonka biyu, ko shi
bai ce mata komai to balle ni kuma da dama
maganar bata shafen ba.
Tun daga wannan lokaci sai wani, irin rashin
lafiya ya same ta na kullum in ni ce da girki sai
cikin dare kamar goma zuwa da rabi ya gama kallon
labaran kasa zai yi wanka ya yi shirin kwanciya sai
ka ji ta kurma wani irin ihu mai tsanani daga cikin
dakinta in anje ganin abin da ya faru sai a sameta
amimmike babu numfashi. Yaya Almu ya yi ta
faman fifita yana tofa addu'a iri-iris sai kuma ta
kama buge-buge tana furje-furje tana wani irin
gurnani, Lailatu, Lailatu yana kiran sunanta sai ka ji
an ce kai kul shiga hankalinka ba Lailatu ba ce
wannan, da sauři ya ce to waye? Sai a fadi wani
suna na daban, na ce to ko zamu kaita asibiti ne? Sai
kawai aka daka mun tsawa da wata irin murya mai
ban tsoro matsa can munafuka ke munafuka ce ba
ma son ganinki a kusa damu, da sauri Yaya Almu
ya sake cewa ke Lailatu menene haka? Aka ce kai
kul ka sake kiran wannan sunan an gaya maka
wannan ba Lailatu ba ce Zubaida ce mun zo ne mu
tayata murnar aure da kuma bakin cikin shanye
mata miji da aka yi ta auri sammatacce an maka
22

sammu an sihirce ka baka, da katabus sai abin da
aka shirya maka baka gani saboda an rufe maka
baki da ido, tsawon lokaci ana amfani da bakin
Lailatu wajen aibanta Umma na duk wani tsohon
abin da aka yis ai da aka fade shi na gaskiya da na
sharri duka wai mutanenta ne masu maganar ba ita
ba ce ina kallonta ina kuma kallòn Yaya Almu dake
faman to fa mata addu'o'i, a haka muka kwana sai
kusan Asuba ta dawo hankalinta bayan ta yi
atishawa mai karfi guda biyu, tana bude ido ta
ganmu kuma sai ta fa she da kuka Yaya Almu ya yi
ta rarrashi nima: nayi mata sannu na ce mishi bari in
je in dan mike tunda ta dawo cikin natsuwarta ya ce
min to Rabi sannu kin ji? Bari in dan kara zama
kadan don ba zai yiwu mu tafi mu barta ita kadai
ba, don kar wani abu ya sake faruwa na ce mishi to
na tafi na bar su.
Tun dapga wannan lokaci wannan ciwo na Lailatu
ya zama mishi ka'ida kullum ranar girkina sai ya
tashi ya yi dalilin da ya raba nr da mijina sai ya
koma-dakinta sai a kwana lafiya ban taba cewa yaya
Almu komai ba, tunda nasan shi kam da zuciya
daya yake yin komai, Lailatun ce dai rannan tazo
zata wuce ni ina zaune a tsakar gida yayin da Baba
Talatu ke tsefe man kaina sai na ce mata zo nan
Amarya, ta matso ta zauna kan kujerar dake kallon
tawa, na kalle ta nayi murmushi na ce mata, Amarya

23
kenan, ba zan daina ce miki amarya ba saboda
iyayenki ba su gaya min sunanki ba da suka kawo ki
dakina, cewa suka yi ga amarya sun kawo sai dai1
tazo ne zata zauna ba ta leko ne zata koma ba, ko ba
haka suka fada ba? Zuba min ido ta yi tana kallona
don bata taba jin nayi mata irin wannan maganar ba,
na ce to kema kenan balle ni don haka na kira ki ne
in baki shawara ki gayawa mutanenki dake zuwa
cewar in sun zo su rinka tsayawa kan abin da ya
kawo su kawai su daina zagan min uwa suna
aibantata, in ba ki sani ba kuma in gaya miki ni da
kike kallona babu abin da ban iya ba, duk abin da
naso yi kuma ina kwatantawa, don a shekaruna na
kuruciya yaya Aimu ya kai ni maka rantar kwana
don haka suma irin wannan da kike yi ina ganin
kamar zan iya yin wanda ya fishi tunda ai ke an ce
jeka ka dawo ma kika yi ko? Jikinta yayi matukar
yin sanyi da maganganun da nayi mata har na tashi
najc na kama aikina bata motsa ba rannan kuma sai
muka kwana lafiya ni da mijina mutanen Lailatu ba
Su 70 sun shiga tsakaninmu ba, sai girki biyu bayan
nan sai kuma aka sake, don haka nima ranar girkinta
sai nayi mata irin nawa suman da na iya wanda ya
banbata kwarai da wanda take yi. Yaya Almu ya
kwana yana dibi-dibi a kaina ita cikin matsanancin
tashin hankali har yana kwalla yana gayawa Baba

24

Talatu cewar tunda yake bai taba sanina da wata
matsala ba sai yau.
Wajen karfe hudun asuba na farfado na tashi na
zauna cikin natsuwa ina magana da kyar-da kyar na
ce mishi jeka ka dan huta Yaya, ya ce to Rabi gobe
sai muje asibiti, na ce mishi to, ya tashi ya nufi1
dakin Lailatu don ya dan huta kafin ya nufi
masallaci kamaar yanda ya ke yi a wurina in ta
kwana da irin wannan ciwon sai kawai yake ya
samu ta garkame kofa bude min mana Lailatu yaya
za ki rufe min kofa? Tana daga ciki tace mishi ka
koma can ka karasa kwana tueda kaje can ka
kwana, ya ce a'a haba Lailatu lalurar rashin lafiya
kuma wa ya fiki ciwo a gidan nan? Ta ce ai nata
ciwon na karya ne, karya take yi lafiyarta kalau
ciwon kare ne yayi juyin duniya ta nude mishi kofa
taki har ya gaji ya tafi nashi dakin ya kwanta.
Gari na wayewa Lailatu tayi yaj1 ta tafi gidansu
da yamma aka dawo da ita na shiga na gaida iyayen
nata da suka rakota na fito naje na gayawa yaya
Almu zuwansu shima yaje ya gaishe su inajin shi
yana yi musu bayanin abin da ya faru yana kuma
gaya musu ita Lailatun tafi kowa yawan lalura, suka
ce eh ai ita dama haka take wani lokaci sukan tashi
mata sai dai da tayi aurc yanzu ne suka fi tashi
saboda tana yawan samun bacin rai an gama
maganganun sun tafi dare yay1 yaya Almu ya nufi

25
dakin amarta ashe wai zance bai kare baa fusace na
ii shi yana cewa, ke Lailatu kama bakinki ban saba
irin wannan rashin mutuncin ba, ni mijinki ne
ba'ayi miki tarbiyar girmama miji ba ne? Ban san
me take fada ba sai ya shiga cewar ya ishe ki haka
lallene kisan ya ishe ki Umma ba uwar Rabi ba ce
tawa ce kama bakinki kiyi shiru watakila bata ji
wannan kashedin da yayi mata ba ne cikin fusata
mai tsanani don kuwa nan take naji ya rufe ta da
duka mai tsanani yana dukan kuma tana zaginshi
tana hadawa da Umman tana kwashe musu albarka
abin da ya kara tsananta al'amarin. Da gudu Baba
Talatu taje tana dukan kofar dakin dake rufe cikin
kuka tana rokonshi ya bude bai fasa abin da yake yi
ba sai da ta ce mishi zata kira Umma a waya ta gaya
mata sannan ya bude ya fito ya nufi wurin shi
Lailatu tana ta faman gurnanin kuka tana fadin an
zage ta din an gaya mata magana munafukar
tsohuwa kawai, menene nata ban sani ba tayi nuku
asiri a gishirin miyar gidanku ta shammace ku sai ta
rinka nuna wai ita mai kirki ce saboda ta iya
munafurci mugu....bata kara sa ba ya sake fadawa
cikin ba zato don haka tayi kus, takardar saki ya
danka mata jeki gida na hakura da auren bana yi
tunda dai shine ya baki damar da kike zagin
iyayena, to na bar shi duk da abin da ke tsakanina
da Lailatu na kiski da kin zuwanta gidan da nayi ga

26
kuma tasa mun uwa a gaba da tayi da wulakanc1
ban ji dadin sakin da Yaya Almu yayi mata ba,
jikina yana rawa naje na same shi don in ba shi
hakuri ya ce kar in yi mishi magana na dawo dakina
cikin rashin jin da di ban taba sanin haka sakin aure
yake ba. Yaya Almu ya sake lekawa dakin Lailatu
fita a kaiki gida ga mota can nayi waya na gaya wa
Umma abin da ya faru.
Da yamma kuwa sai ga Umma ta iso kai tsaye
falon Yaya Almu ta shiga na same ta a can fada
sOsai take yi mishi ina amfanin wannan abin da kayi
don ta zagi iyayenka sai me? Aure ai ya wuce haka,
sai ka shirya kaje donni daga gidan nasu nake yanzu
sun ce ba zata dawo ba sai kaje kai da kanka.
Yaya AImu yayi maza ya ce a'a Umma tunda dai
ki kaje ba su ga girmanki sun dawo da ita ba to babu
abin da zai kai ni su barta tayi ta zama, ta ce mishi
kar kayi haka, yayı maza ya ce a'a Umma wannan ai
wulakanci ne zuwana har yali naki muhimmanci?
Ba za ni ba, akan dole yaya Almu ya amsa wa
Umma za shi tà kuma tilasta shi tafiyan tun tana
nan, da daddare ranar Lailatu ta dawo, sai dai
dawowan da tayin da wani damaran ta sake zuwa,,
Wuni take yi tana habaici ina kallonta donni ban
saba irin wannan abin ba, ban ga kuma kamar zan
ya shiga cikinshi ba, ilai rannan ta sake yi mun irin
wannan abin ran girkina ban yarda na bita bashi ba

27
tana karbar girki nima nayi mata abin da ya yi
matukar kona mata rai, gari na wayewa kuma na
tsala kwalliya ina kaiwa da kawowana, da hantsi
wajen karfe goma sai ga su Umma sun zo ita da
Umma Amarya saboda wayar da Yaya Almu yayi
musu tun cikin dare ya shaida musu cewar bani da
lafiya wata irin lalura ta same ni.
Ina zaune gaban Umma Amarya da ta shigo
dakina bayan fitowarsu daga dakin Lailatu yayin
da ita Umma ta shiga wurin Yaya Almu, Umma
Amarya ta kalle ni cikin natsuwa ta ce mun me ya
same ki Adawiyya? Mijinki ya ce lalura ta same
ki kwanannan sau biyu abin yana tashi, me ya
same ki? Na daga ido na kalle ta ba zan iya yi
mata karya ba, na ce mata lafiyata kalau Umma
na soma bata labari hawaye suna gudu a idona
saboda ni kaina ba akan son raina nake yin abin
da nake yin ba, na fi so da Lailatu ta yarda mun
zauna lafiya tunda zama ya hada mu.
Umma ta zuba min ido sai da na gama bai wa
Umma bayanin komar sannan sai ta ce min to don
me za ki kirkiranwa kanki rashin lafiya?
Yaya Almu ya biyo bayan Umma Amarya doon
ya gaishe ta ya same i ina kuka a gaban Umma,
yayi zaton ko kararshi na kai mata, don haka ya
zauna Cikin sanyin jiki a sanyayc ya gaishe ta,

28
Umma ta shigo bayan ta baro dakin Baba Latatu
aka hadu a falon.
Umma tana kallona ta ce min, ke Adawiyyah
ban sanki da wata lalura ba menene dalilin
wannan abin da yake faruwa? Nayi shiru ban ce
mata komai ba, kul na sake jin wani abu
makamancin haka ya faru, yaya Almu yayi galala
yana kallon Umma cikin mamaki, Umma ai ciwo
ne ciwon ciki ne yake murde ta tayi ta fama da shi
yayi ta bayani bata ce mishi komai ba, sai bayan
da ya fita ta sake kallona ta ce min na ce miki kul
kema za ki wahalar da shi ne? In ki ka yi hakan
ribar me ki ka ce? Na ce to amma Umma shi bai
san ita din abin da take yi karya ne ba yake biye
mata? Ta ce bai sani ba tunda kema da ki ka girma
a gabanshi bai gane wanda ki ka yi ba balle ita da
ya ganta da girmanta.
Umma Amarya ta yi tsaki ta ce, zama dai irin
wannan yana da wahala sai dai addu'a kawai.
Bayan tafiyar su Umma dole na zuba wa
Lailatu ido tana shakiyancin ta, tunda ta ce ni kar
in sake yin haka sai dai daga baya da na ga abin
nata ya 1she ni ni nayi shawara kan abin da zanyi
tunda ba zai yiwu in zuba mata ido ta raba ni da
mijina ba. Rannan na karbi girki tun rana yaya
Almu yake so in bashi lokacina ni kuwa naki

29

yarda na bata loka cin a kicin ina shirya mishi
abin da zai ci da daddare mun shiga wurin shi
kenan sai kawai muka jiwo ihun Lailatu gada
daya muka fito muka same ta a mimmike tana ta
faman furzar da yawu, yaya Almu yayi mata
addu'o'in da zai iya tana kwance da ya dan natsa
yana hutawa sai na kalle shi cikin natsuwa na ce
mishi Yaya Almu ko zamu je daki ne tunda ko
mun zauna ba yanzu zata farfado ba, ni kuma yau
ban ga kamar zan iya hakura da kai ba, tun kafin
in karasa fadin abin da nayi niyya yayi maza ya
ce muje, muje Rabi kira Baba Talatu tazo ta zauna
da ita na ce to.
Cikin dare Lailatu ta faki idon Baba Talatu ta
fita ta nufi gidansu ita kuwa Baba Talatu ta yi ta
binta ckin sanda har sai da suka isa kofar gidan da
zata shiga ciki sai ta ce mata, to ni zan juya daga
nan ta dawo gida ta karasa kwana da gari ya waye
ta yiwa Yaya Almu bayanin yanda suka yi duka
bai bi bayan Lailatu ba kwana da kwanaki har dai
1yayenta suka gaji suka zo da kansu. Ina jin shi
yana gayawa wanta da aka turo wurinshi cewar
shi lokacin da za'a bashi ita ba'a gaya mishi cewar
tana da wata lalura ba don haka tunda sun ce ba su
yarda a kaita asibiti ba, to shima ya gaji da kwana
ido biyu da yakc yi yana gadinta don haka a barta

30
a gida kawai ta zauna a neman mata magani in ta
warke shi kenan ta dawo dakinta, amma in bata
warke ba to a barta a gidan kawai ya hakura, 'yan
kwanaki kadan bayan nanne suka aiko wai sun
karbo mata magani don haka zata dawo dakinta,
ya ce to shi kenan amma in ciwo ya sake tashi to
zai turo ta gida daga wannan lokacin ne Lailatu ta
warke ciwonta don ganin zai iya yi mata sanadin
aurenta.
Tun daga wannan lokaci kuma sai Lailatu ta
tasa Baba Talatu a gaba da rashin kunya da
wulakanci ga sa aiki na rainin hankali abu ko a
kusa da ita yake ba zata sa hannu ta dauka ba sai
ta ce wai sai Baba Talatu tazo ta mika mata
rannan dai da abin nata ya ishe ni sa na ce mata
ke Lailatu Baba Talatu ba mai aiki ba ce a gidan
nan uwata ce in kin lura da kyau za ki ga ba
umarni nake bata rokonta nake yi ta taimake ni
tayi min abin da nake so tayi min don haka daina
yi mata tsawa kina maida ita kamar wata wacce
take zamanki. Sai kawai Lailatu ta kalle ni ta ce
mun tunda kuwa zan tuka in bata ta ci ai dole in
sata aiki tayi nace to daga yau kar ki sake yin
girki da ita kar kuma ki yarda in sake jin kin ce
tayi miki wani aiki na hana, kan wannan takai
Karana wurin Yaya Almu ya kira ni ya tambaye ni

31


dalilin da yasa na hana Baba Talatu ta rika
taimakonta na ce mishi in tana son mai aiki a
dauko mata amma Baba Talatu uwata ce zamana
kuma take yi, ya ce haka ne to a bari in gaya wa
Umma ta kawo muku mai taimako na ce mishi to
na tashi na tafi na bar su Lailatu fuska a daure ba
haka taso yayi ba, ba a cika kwana bakwai ba
kuma sai ga masu aiki har guda biyu Tanbai da
Larai. Lailatu ta ce sai kowa ya dauki mutum
daya shi kuwa Yaya Almu ya ce a'a su din zasu yi
zaman gida ne gaba daya.
A wannan lokacin Lailatu ta rasa inda zata
tsoma ranta ta ji dadi ta rasa inda zata yi ta shiga
tsakanina da Yaya Almu kullum na kar6i girki
kan in fita girkin sai tayi kuka idonta yayi luhu-
luhu, ko kuma ta yi ta fushi in na gama girki na
kai mana wurin Yaya Almu na ce tazo muci sai ta
ce ita ta koshi, in kaga tana walwala to girkinta
ne, ni kam ina kallonta tun dai nasan bata da
yanda zata yi dani. Muna cikin wannan zama ne
aka wayi gari Lailatu babu lafiya, ni da Yaya
Almu muka kaita asibiti bayan yan gwaje-gwaje
da yan tambayoyi yan kadan Likita ya tabbatar
da cewa ciki ne da ita na tsawon makonni shida,
ban taba ganin fuskar Yaya Almu cikin yanayin
da na ganta a wannan lokacin ba, don haka in na
32

tsaya cewa yayi farin ciki to 6ata bakina kawa
nake yi. Likita ya sallame mu da magunguna
muka fito daga ni har Yaya Binta da sannu-sannu
muke yi tana ganin wata kujera taje ta zauna akai
wai ba za ta iya tafiya ba saboda jiri gashi kuma
jikinta ciwo yake yi, makullin mota Yaya Almu
ya miko min ya ce muje ki tuka mu na ce to shi
kuwa yasa hannu biyu ya suri Lailatu ya rungume
a kirjinshi nayi maza na yi gaba naje na bude
musu kofar motar ta wurin zaman mai mota suka
shiga yana kankame da ita ni kuwa na koma
wurin direba na tashi motar muna tafiya yana yi
mata wasu maganganu masu kama da sambatun
daki yayin da ni kuma zuciyata ta tafi wajen
tunanin wata shida kacal da auren Yaya Almu da
Lailatu zata zama uwar iyalınshi shi kenan abin
nema ya samu tun daga ranar da Likita ya bayar
da tabbacin Lailatu na da ciki to tun daga ranar
kuma komai ya sauya gaba daya gidan ya zama
Lailatu ce mai juya shi ko ni ke da girki to abin da
ta ce nake girkawa, saboda ita mai juna biyu ce
yaya Almu kuma a yanzu komai take so shi ma
abin da yake so kenan ko da kuwa ba dai dai ba ne
na yi kamar in kai karar yaya Almu kan sabuwar
dabi'ar tashi sai kuma naga zan tada hankalin
Umma sauran jama'a kuma suce don naga Lailatu
33

na da ciki ne yasa nake bakin ciki da ita don haka
dole naja bakina nayi shiru.
A wannan lokacin kusan kullum ni ce mai yın
girki saboda kowane lokaci Lailatu tana kwance
wai bata jin dadi bata da lafiya don haka ya ce in
kar6i abincin gidan gaba daya, na ce mishi to
gashi kuma a hakan ma babu mutunci a gaban shi
ma sai ta mulmula bakar magana ta gaya min sai
ya ce wai in yi hakuri mata masu juna biyu a
fusace suke don haka hakuri ake yi dasu na sake
cewa to don haka ina zaune Lailatu take gaya min
abin da taga dama ina kallonta, wani loka ci Baba
Talatu ta yi ta kuka tana bani hakuri in ce mata
babu komai Baba kowa da irin kaddararshi don
haka ya zama mun dole nima in yarda da nawa.
Gaskiyar magana ita ce a wannan lokacin ne
nasan lalle yaya Almu yayi aure don duk abin da
ya taba faruwa a baya sai da ya zama wasan yara
kan sabbin abubuwan da suke faruwa a yanzu,
Umma karama ma duk sati take zuwa wai tana
zuwa gaida mai laulayi haka nan yan uwanta
gidan ya zame musu wurin wuni wai suna jinyar
mai laulayi shi kuma Yaya Almu sau goma zasu
shigo sau goma zai yi musu hidima ya kuma sa a
maida su gidanjensu, bayan ya yi musu godiya
mai yawa akan idona dana Yaya Almu 'yan uwan

34
Lailatu suke hirar karshen mulkin matan da basa
haihuwa sai kuma a kwashe da dariya cikin shewa
da tafa hannu. A wannan lokacin in na ce ban
shiga wanı hali ba to ban yiwa kaina adalci ba, to
amma bani da yanda zanyi yaya Almu da ciki
kawai yake ji zai samu abin da yake nenmå za'a
haifan mishi da wannan shine abin da yake
gabanshi, gashi Ummama da ta zo duba Lailatu ta
jaddada mun muhimmancin inyi hakuri don haka
sai na dukufa wajen addu'ar neman karin hakuri
da juriya, sai dai kuma hakurin nawa bai hana
zuciyata ciwo ba.
A wannan lokacin Yaya Almu babu ce kawai
bai dauko ya kawo wa Lailatu ba, wuni yake yi
yana jido kaya yana kawo mata da sunan sayayyar
kayan haihuwa. Baba 1lalatu tazo ta same ni tana
tambayata anya uwardakina ba za ki sa ayiwa
Babangida magana kan irin dukiyar da yake
kwasa yana bai wa mutanen nan ba? Nayi
murmushi na ce Baba kenan to Lailatu ko ya bata
dukiyarshi ko kar ya bata ai ta zama tata da fa zata
haifan mishi bar su kawai suyi duk abin da suka
ga yayi musu daidai, ta ce to shi kenan, kema ai
ba mu fitar da rai ba, in yi murmushi kawai in
kawo wani zancen don ni kam na riga na hakura
na fidda raina kan zancen haihuwa.

35
Ni da Yaya Almu sai da ta kai ma bai iya
tantance girkina da wanda yake na Lailatu saboda
tsaban kowanc lokaci yana dakinta, gashi kuma a
yanzu kusan kullum sai mutanenta sun tashi cikin
dare wai suna zuwa tayata murnar juna biyun da
ta samu.
Saboda tsananin samun wuri kuwa rannan
magana kawai ta yi na amsa mata saboda na gane
shirun da nake y1 mata yayi yawa sai kawai ta
warwarc hannu ta share ni da mari a fuska a gaban
Yaya Almu, cikin tsananin fushi na yunkura zan
yi maganinta sai kawai yayi caraf ya rike ni ai ba
za ki kula ta ba Rabi, ai hakuri kawai za ki yi ta ci
darajar abin da yake cikin cikin nan nata, na tsaya
ina kallonshi yana rike da hannun da na kawo
mata marin dashi, sai ya ce min haba Rabi yanzu
ke in aka ce miki ki bugi Lailatu sai ki buge ta?
Mai ciki ce fa? Ko so ki ke ta haifi dan da shatan
duka a jikinshi? Ya juya wajen Lailatu ya ce mata
ke kuma ki daina saurin hannu kinji na gaya miki
abin da kawai ya fada kenan ta fashe mishi da
kuka wai ya goyi bayana ya yi rarrashi har ya gaji
ban san yanda suka karc ba, don kuwa tashi nayi
na fita na basu wuri na dawo dakina wunin rannan
Cikin tsananin bacin rai na yi shi haka nan ban
samu damar yin baccin dare ba, don kuwa marin

36
da Lailatu ta yi min yayi matukar kona min
zuciya.
Da gari ya waye shiryawa nayi na tafi gida
nufina in je wurin Ummana in dan yi hira ko zan
ji dadin zuciyata, ina zaune a gabanta cikin
kwalliya sosai don dai taga kamar bani da wata
damuwa, muna zaune muna hirarmu idanuwan
Umma akaina suke ta zuba min su ko kiftawa bata
yi ni kuma ina ta kokarin yawaita murmushi da
fara'a a fuskata don dai ta dan ji dadi zuwa can sai
naji ta ce min a dan tsakanin nan bana iya bacci
Adawiyyah saboda nasan kina cikin wani hali,
sannan a yanzu ramar da na gani a tare dake tafi
komai tada hankali sai dai kuma hakan ba zai
hana ni cewa ki kara hakuri akan wanda nasan
kina yi ba, duk wanda ki ka ganshi ya yi hakuri
bai ci nasara ba Adawiyya to bai yi hakurin mai
yawa ba ne, na ce mata to Umma.
Ina zaune a gida bani da wani aiki sai na
abincin gida da kuma sallolina dana sanya a
gabana, saboda shi kanshi Yaya Almu in aka
tambaye shi yaushe ne girkina? Ba zai iya fada
ba, kullum dai nice a kicin nice mai abinci yayın
da shi kuma yake wuni a dakin Lailatu, ya kuma
raba dare yana tare da ita in kuma ya dan saci jiki
ya shigo wurina to naan da nan mutanenta zasu

37

tashi su yi ta furje-furje suna fadin maganganu na
aibanta ni tare da Umma da fadin wai irin asire-
asiren da muke yi mata suna zuwa suna tonewa
kuma wai duk akan cikin da take dashi ne muke
son barar mata, ni kam a yanzu ko mutanen nata
sun tashi bana zuwa tunda na riga na san
shakiyanci ne sai in bar shi shi kadai yayi ta
Zirga-zirganshi.
Ni da shi muka zama wani iri tamfar bamu ne
muka yi wancan zaman na lokacin dadin mu ba in
ka ji ya kira ni to wani aiki zai sani ko kuma zai
min fada kan wani laifi da aka ce mishi nayi
rannan dai na gaji na ce mishi to wai ni wake baka
labarin abubuwan da nake yi tunda kace bana
yinsu akan idonka? Ya ce to masu fadan zasu yi
miki karya ne? Nayi maza na ce mishi a'a ai sa
masu gaskiya ne, ko zama a inda Yaya Almu yake
bana yi saboda kallo daya zai yi min yaja wani
mummunan tsaki ya ce dubi duk yanda ki ka
maida kanki kin wani rame kin kanjame saboda
bakin ciki ni ba ruwana tunda dai babu abin da
nake yi miki ke ki ka tsangwami

Please Login or Register in order to submit comment