Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: WACECE NI?

4

Na
Haj. Hafsat C. Sodangi
(Mrs. Yunus Abdullahi Dabai)






GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take Madaukakin
Sarki, gwani mai hikima cikin dukkan ayukanshi.
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
Shugabanmu Annabin karshe, Muhammad (S.A.W)
da Alayenshi da Sahabbanshi da wadanda suka bi
tafarki na gaskiya har zuwa ranar Alkiyama, amin.
Godiya mai dinbin yawa gare ku Makaranta
littafin nan na kusa da na nesa na gode da irin
kulawarku, Allah kuma ya kara zumuncin dake
tsakaninmu ya kuma saka muku da mafificin
sakamako amin summa amin.

TUKUICIN LITTAFIN NAKI NE
Yar uwa rabin jiki, Hajiya Khadija C. Sodangi
(Mrs Nasir Kiru)

SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin taku ne makaranta
littattafaina, na nesa da na kusa na gode da irin
kulawar da kuke nunawa rubutuna, na gode.

JINJINA
Jinjinar taku ce.
Rabi'atu Abdul One Muhammad (Adawiyya)
Rabi'atu Barau Potiskum (Amarya)
Rahi'atu Ibrahim Gusau (Rabi)
3

Rabi'atu Bashir Sambo
Rabi'atu Maikudi lafiya
Rabi'atu Muhammad Aliyu

GORO
Goron littafin naki ne yar uwa, aminiya, Hajiya
Lami Nasiru Goshi, na gode da kulawarki.

JINJINAR LITTAFIN NAKA NE MIJINA
Alhaji Yunusa Abdullahi Dabai, babansu Maryam,
Aisha, Yunus da Abdulmajed, Ubangiji Allah ya
saka maka da alhairinsa, amin.

Hakkin Mallaka
Hakkin mallakar littafin na Marubuciyar shi ne;
HAJ. HAFSAT CHINDO SODANGI (Mrs Yunus
Abdullahi Dabai)

GORON NAKI NE
Zuhuriyya Ibrahim Usman Zaria

KINA RAINA
Diyata Hafsat Abubakar Mamadawa

GAISUWAR SADA ZUMUNCI GARE KI
Halima Salihu Kwayakusur Maiduguri, Borno
State.

4

YABO
Yabon naki ne Aisha B. Dahiru
(Mrs Shehu Tijjani)




5

Littattafan SODANGI:

NAGA TA KAINA

ABU NAKA

HATTARA

GARIN BANZA

DAGA KIN GASKIYA

DUK DAYA

DA KAMAR WUYA

YIWA WANI

RABON KWAD0

WACECE NI?

KIFI NA GANINKA...

MAI UWA A GINDIN MURHU...

6

WACECE NI? 4
D uk da ban wani samu isasshen bacci a
cikin daren ba, ga gajiyar wahalar biki ga
rashin bacci da suka hadu suka haddasa min ciwon
jiki mai nukurkusar kashi. Da gari ya waye na yi
kokari na fito bayan na idar da sallah na shiga kicin
na fara shirya abin karyawa saboda Ango da
Amarya da kuma sauran Jama'ar dake gidan. Tunani
sosai nayi don in shirya abin da zan gamsar da
mutane, sai da na dama kunun gyada na shinkafa
nayi alala sannan na shirya potato da corned Beef ga
abubuwan da nayi amfani da su:
(1) Dankalin Turawa manya takwas
(2) Butter cokali takwas
(3) Albasa guda biyu manya
(4) Naman jajjagagge daidai kima.
(5) Kayan kamshi dan madaidaici
(6) Dessert Apple guda biyu manya

Da yake abincin nawa bai wuce na mutum hudu
ba, to ga yanda nayi na sarrafa komai, wanke
dankalin nan nayi sosai ya wanku da kyau ba tare da
na fere shi ba, na ajiye shi wuri mai tsabta sai da ya
bushe sannan na goga mishi butter na dora shi kan
bakin sheet na saka sh1 a oven ya gasu na kusan awa
daya cikin madaidaiciyar wuta sai da naga ya gasu
7

Sannan na ciro su na kwakule cikinshi sai dai na
kiyaye ban lagabar dashi ba ban kuma huda wani
bari ba, na kawo jajjagagren naman nan na hada da
wannan garin dankalin da na kwakwale na hada da
maggi yankakken apple din nan da kayan kamshi na
cakuda shi da albasar da na soya cikin butter tayi
laushi sannan nayi ta cusawa cikin dankalin nan sai
da na gama maida shi ciki gaba daya na sake
sanyawa a oven ya yi ta gasuwa kafin na sake ciro
shi na sanya shi cikin kwanon da na tanada mai
tsabta.
Ina cikin kokarin dora ruwan zafin da na tafasa
cikin flask sai ga Baba Talatu ta shigo sannu da aiki
uwar dakina, na cc yauwa Baba kin shigo? Ta ce
mun ch, ta kuma kara marsowa kusa dani alamnar
wata magana zata gaya min, don haka na kara bata
hankalina. "Kinga idon wannan yarinyar kuwa?
ani mirsisi da ita ni nace anya ma ihun nan da
take tayi jiya na kama hannunne kuwa da gaske?
Banga alamar ta kai budurcin nan ba." Na ce "Baba"
Ta ce "Na'am." Na ce "Mu bar wannan magana." Ta
ce "To." Ta shiga taya ni kintsa wurin zuwa can sai
na sake jin ta ce min "in banga maigidan yayi
wankin kayan shimfida ba irin na wancan karnon,
anya budurcin nan..Nayi maza na katse ta na ce
"Baba Talatu daina yi min wannan maganar, tana
fadar min da gaba, don bana son jin ta wannan abin

8

da ya shafe su ne ita dashi bai shafe ni ba." Daga
bayana na ji muryar Yaya Almu yana cewa,
"menene bai shafe ki ba? Baba Talatu tayi maza ta
fita ni kuwa na soma gaishe shi bai wan1 amsa ba ya
kara matsowa gab da jikina, me zan samu Rabi? Na
sunkuyar da kaina don bana son kallon fuskarshi, na
ce duk abin da kake so akwai, ya ce 'to in dai haka
dan fara bani bakinki in ji kwananshi, in ji
laushin la6 6anki, nan da nan wani abu ya tokare ni
a zuci har ban san lokacin 'da na bude baki na ce
mishi, uh'uh in baka ji wadannan ba ai ka ji
wasu..bai bari na karasa ba ya ce mun kul, kar ki
rinka irin wannan maganar in ina tare dake ina tare
dake in bana tare dake kar ki yarda zuciyarki ta raya
miki komai ki dai yarda kawai a duk inda nake ina
kewarki ina kuma son ganinki a gefena, na ce haka
ne.
Na kammala shirya komai kan tire na dauko na
barwa Yaya Almu wanda zai taimake ni dashi
juyowan da zanyi sai kawai naga Lailatu tana
lekowa ta matsin kofarta tana kallon abin da ke
faruwa tsakanina da Yaya Almu. Na yi kamar ban
ga abin da take yi ba, na wuce naje na shirya komai
a falon shi na sake dawowa na shiga dakin nata
nace mata Amarya ina kwana? Ta ce min lafiya,
amma dai sunana Lailatu, na yi kamar ban ji ta ba

9
na ce mata ki zo falo maigidan yana jiranmu, na
juya na fita na barta.
Mun zauna muna karyawa dukanmu muna kuma
hira dukanmu saboda kokarin da Yayan ya yi wajen
ganin ya tsoma kowa cikin maganar tashi, da aka
natsu sai ya kalle ni ya ce mun Rabi ga Lailatu nan
na sani kishiyarki ce, to amma zan so ki maida ita
yar uwa ki yarda cewar taki ce zaki yi mu'amalla da
ita bisa adalci ba don kowa ba sai don ni, tunda kin
san ni na kawo ta na kuma san za kı 1ya y1 min
adalcin maida duk wani abu nawa ya zama naki ko
da kuwa ba akan son ranki yazo ba, saboda kin san
duk wani abin da ya shigo gidan nan arzikinki yazo
ci in kuma mallakarshi nayi to na ki ne."
Cikin natsuwa ba tare da zuciyata ta raya komai
ba, na ce mishi haka ne, sai kuma ya juya wajen
Lailatu ya ce mata, ke Lailatu ga Rabi nan matata ce
ko babu aure tsakanina da ita kuma 'yar uwata ce na
kuma san duk yanda kishi yakai da zafi cikin
zuciyar ta a ifin halinta da na sani da kuma irin
tarbiyar da aka yi mata zata yi iya kokarinta wajen
ganin tayi miki adalci, to ki bata hadin kai ki bata
girman da ya dace da ita don ina bukatar ganin kun
zauna lafiya kun samu fahimtar juna a tsakaninku.
Wannan shi ne sha'awata da burina game da mata
biyu, ke Rabi kinji abin da na ce? Na ce mishi ch,

10

naji Allah ya taya ka riko, ya yi maza ya ce min
"amin, Lailatu dai bata ce komai ba har na fita.
Zuwa can wajen karfee sha biyu da rabi bayan
fitar Yaya Almu, ina falona ni da Baba Talatu ina
kuma hango duk abin da tsakar gida ke ciki, yayin
da Lailatu ke falonta tana kallo sai ga Umma
Karama da Hajiya Hairan sun shigo gida da sauri na
fito ina yi musu sannu da zuwa na kuma jagorance
su don in kaisu dakina duk da dai nasan Umma
Karama bata taba takowa tazo gidan saboda ni ba,
to amma sanin da nayi cewar duk bakon da yazo
gidanmu matukar ya fara ganin Umma to ko ba
wajenta yazo ba to wurinta zata fara sauke shi ta
bashi ruwa da abinci kafin tasa a kai shi wurin
wanda yazo, to balle Umma Karama duk yanda
takai da kina dolenta ni 'yarta ce, kan idonta aka
haife ni ko babu wata alaka tsakanina da Baba ta
dalilin Umma kawai ita uwata ce, balle kuma inta
juya ta wurin Baba ni jikarta ce har yanzu kumna
surukarta matar dan mijinta, amma bata şhiga dakin
nawa ba sai ta ce min na rako Hairan ne tazo taga
dakin Amarya, bari mu fito tukuna. Cikin murmushı
na ce mata to, na shiga kicin na shirya abinci na
bisu dashi zuwa dakin Lailatu na shiga na same ta
tana cewa, in ana zancen aure ai babu maganar
Zumunci a ciki dukanku daya ne dukanku daidai
kuke in ta dauro ma kwanan nan sai ki kwace shi

11

tunda ke kam ai matar haihuwa ce kadan ya rage
banyi 6ari ba, nayi maza na shanye bugun da
zuciyata tayi nayi sallama suka amsa na shiga na kai
musu abin da na shiryo musu na kuma gaishe su har
na tsaya ina tambayar Umma, Umma daga Legos ku
ke ne? Ta ce a'a a satin nan ne dai zan tafi na ce ai,
na tashi na tafi nawa wurin da suka gama abin da
zasu yi kuwa daga tsakar gida ta yi mun sallama
wata kilama da ban ga fitowarsu ba da tafiyarsu
kawai suka yi ba tare da sunyi min sallamar ba,
Baba Talatu ta kalle ni ta ce tafdijam, wannan mata
da rashin mutunci take in ban da Hajiya ta samu da
ba a san irin tsiyar da ta yiwa mutane ba, na yi
dariya kawai na tashi na nufi kicin don shirya
abincin rana. Ina shiga kicin din sai ga Yaya AlImu
ya dawo cikin kicin din ya biyo ni, na kalle shi cikin
murmushi na yi mishi sannu da zuwa, ya kalle ni
cikin wani murmushin mai gamsarwa ya ce min ran
uwargida ya dade, na daga ido na kalle shi kamar in
yi mishi wata magana in gaya mishi bana son sunan
sai kuma na fasa na sunkuyar da kaina kawai da
nufin in kama aikina, sai na ji ya matso kusa dani
sosai yana fadin ke uwargida ce Rabi duk da
mas'alar da muke da ita kuma zuciyata tana raya
min cewar kcce uwar 1yalina, musamman ma da
yake a yan kwanakin nan ina mafarkin kin haifar
mun ya mace, na yi murmushi saboda jin dadin
12

kalaman nashi, na jawo kayayyakin da na hada zan
soma aiki na sai ya ce mun me za ki shirya mana ne
yanzu kuma? Na ce mishi stuffed chiken (2) in ba
ka manta ba ka taba cin 1), din ya ce ch ban manta
ba Rabi duk da dai na cishi ne tun ina saurayi, to
gaya min me dame ki ka tanada? Na ce mishi gasu
nan a gabanmu kana kalio sai dai hakan ba zai hana
in gaya maka sunayensu ba (1) kaza, butter,
shinkafa, kayan lambu, nama, curry, sai kuma
maggi. Juyowan da nayi na hango Lailatu tana leko
mu ta matsin kofarta yasa na ce wa yaya Almu jeka
wurin amarya yaya in na gama zan zo in same ku
bai yi musu ba ya juya ya tafi.
Na kama aikin abincin san zuciyata a kun tace
saboda ba wastsakewa nayi daga zafin kishin dakc
cina ba, gashi kuma na ganc ita Lailatu bata shigo
gidan da niyyar yarda da tayin zaman lafiyar da ni
da Yaya Almu muke gabatar mata ba idonta da
hankalinta gaba daya to kan mu a mallata da mijina
take duk da cewar shekaran jiya ne kawai ta shigo
gidan wannan in ta yi kwanaki yaya za'a kwashe da
ita? Wannan ita ce tambayar da tazo cikin zuciyata,
gani kawai nayi na gama girkin amma ban san
yanda aka yi na hada komai ba, saboda tsananin
tunanin da na samu kaina a ciki har na kammala na
shirya komai kan tire na dauko na nufi falon Yaya
Almu ban san da wani a ciki ba don haka ban wani

13

tsaya yin doguwar sallama ba na tura kaina cikin
falon jikinshi na same ta tana yi mishi wasu
abubuwan da nayi maza na kawar da kaina daga
gare su, naje na ajiye musu abincin duk da ba
yunwa nake ji ba na zauna muka ci tare don kar in
basu damar da zasu gane na samu wata damuwa, sai
da aka gama na tashi na tafi wurina.
Da daddare ma na sake shirya tuwon Semovita
miyar kuka da kuma farfesun bindin saniya, ina idar
da sallar Isha'i nayi wanka na hau gado na na
kwanta da nufin in yi wadataccen baccin da zan ji
dadi in samu naatsuwa a jikina sai dai kuma kash!
hakan bai yiwu ba ina rufe idona da nufin yin bacci
sai inga Lailatu a jinshi tana tuhumarshi irin dai
yanda na same ta tana yi mishi sai kuma in ji
Zuciyata tana raya mun cewar yanzu haka ma abin
da ke faruwa a tsakaninsu kenan, na yi kuka rannan
har na gaji saboda ganin abin da ban taba ba kan na
farko ken an da naga wata mace tana taba Yaya
Almu a tsawon rayuwata tare dashi.
Nayi matukar kokarina na shanye komai na
hadiye duk wani abin da ya dame ni na yiwa Yaya
Almu da Amaryarshi duk wani abin da ya dace in yi
musu na kyautatawa a tsawon kwanaki bakwai din
da yayi a dakin nata, duk da kasancewar kwanakin
masu tsanani ne kwarai a gare ni.

14

A haka rannan ya dawo dakina bai jira naje
nashi dalkin ba wurina yazo ya same ni sai dai duk
Rokarin da nayi na in nuna mishi bani da wata
mas'ala na kasa sakin jikina dashi sosai, ya zuba
min ido yana kallona saboda ya gane abin da nake
nufi a hankali cikin natsuwa da murya kuma irin ta
rarrashi ya ce min auren da na yi fa bai canza komai
ba tsakanina dake sai ma kara wa da ya yi saboda a
yanzu babu abin da nake tausayi kamar ki ina ji ya
ambaci tausayi sai na ji zuciyata tana raya min
cewar saboda yasan ya cuce ni, nan take na kama yi
mishi kuka, na yi kuka irin wanda ban taba yi ba, na
yi kukan da tun yana rarrashina cikin tausayi har ya
gaji ya ture ni ya fita daga dakin ba zan iya wannan
zaman ba ba zan iya ba, abin da zuciyata take gaya
mun kenan, na mika hannu na kira Umma da nufin
in gaya mata cewar ta yafe mun tayi hakuri ta bar ni
in yi abin da naga zai fiye min sai na ji muryar Yaya
Junaidu yana cewa, Hello Adawiyya yi magana
magana, menëne? Ashe lambobinshi na danna ban
sani ba nayi maza na kashe wayar na maida ita na
ajiye sai dai kuma kama ruri tayi shi ne ya sake
bugowa cikin natsuwa nace mishi kayi hakuri
Umma nayi nufin kira ya ce da wannan tsohon
daren za ki katse mata baccinta? Na ce ar na fasa ya
ce min to sai da safe, na ce to mu kwana lafiya na
maida ita na ajIye sai dai kuma gari yana wayewa

15

da yaya Junaidu muka karya a gidan da sunan wai
yazo ganin Amarya yayi wa yaya Almu fatan alheri
ya kuma yiwa amarya kyauta sannan ya nemi 1zinin
Yaya Almu ya biyo ni har cikin falona, nasiha mai
yawa yayi min ya kuma nuna min muhimmancin in
yi kokari ina boyewa Umma damuwata saboda ita
din ta riga ta fara girma na ce mishi to ya sake
kallona cikin natsuwa ya ce min in kina da damuwa
rinka gaya min zan taimake ki da shawarwarin da
zasu taimake ki, na sake ce mishi to ya sake kallona
ya sake tambayata yanzu menene damuwarki? Na
ce mishi ina so in yi nesa da Yaya Almu ina so in
daina ganinshi a kusa dani, ya sake zuba min ido
cikin natsuwa ya ce min amma kin san mijinki ne
wannan aure da yayi kuma ba laifi yayi ba halal
dinshi ne, na ce eh, ya ce to kar ki yawaita tsananta
al 'amarin a wajenki ki dauki komai da sauki zan
kuma shirya miki tafiya Umra don ki je kiyi ziyara a
Madina na ce mishi to.
Sati guda bayan nan komai ya kammala na
shirye-shiryen tafiyata saura tashi kawai, amma sai
Yaya Almu ya ke kasa kasa ya ce babu in da zan1
saboda ba a nemi izininshi ta hanyar da ta dace ba,
hanyar da aka bi wajen sheda mishin ya fi yi mishi
kama da sanarwa maimakon neman izini.
Ina zaune a dakina cikin bakin ciki da takaicin
abin da ya yi na neman ya kuntata min tunda sau

16

nawa Yaya Junaidu yana shirya min irin wannan
tafiyar bai tába cewa bai yarda ba sai a wannan
lokacin, wannan neman kuntatawa ne kawai abin da
zuciyata ta raya min kenan. Ya shigo dakina ya
same ni don ranar ma girkina ne, na daga ido na
kalle shi cikin natsuwa na ce mishi me ka ke nufi da
hana ni tafiyar da kayi? Ya cc abin da nakc nufi
kenan ki gane zan iya nukurkusa ki in saki bakin
ciki matukar ba ki janye daga matakan da kike
dauka ba, na zuba mishi ido ina kallonshi, sai ya ce
min kalle ni da kyau rabi don ki kara gane ko n
wane iri ne na iya yin rarrashi in yi alheri in kuma
saka mai kyau da mai kyau kamar yanda zan ya
kuntatawa in saka munmuna da munmuna in halin
hakan ya kama, ina yi miki wannan bayanin ne don
in fahimtar dake ki gane cewar babu abin da zai fi
zaman lafiya da bai wa juna hakki dadi a tsakanina
dake, na rasa abin da zan ce mishi sai kawai na
kama yi mishi kuka ina tambayarshi me nayi maka
Yaya Almu? Me nayi maka ka tsane ni ka ke nema
sai ka gana mun azaba? Me nayi maka da zaka tsare
ni a cikin gidanka ka hana ni zuwa in da zan ji sanyi
bayan ba sona kake yi ba, na gama kukana na mike
na wuce shi zan shiga cikin dakina in kwanta yayi
maza ya mika hannu ya kamo ni na fada jikinshi zo
ki gaya min abin da nayi miki wanda yasa kika ce
bana sonki ina kuntata miki? In ina sonki me kike

17

so in yi miki bayan wulakancin da kike yi mun
yaushe rabonki da ki gyara mun shimfida?
Rannan dai dole na na yarda muka shirya da
Yaya Almu saboda yayi rantsuwar ba zai yarda da
danne mishi hakkinshi da nake yi ba, ganin mun
shirya yasa na sake rokonshi ya bar ni in je in yi
Ummara ya ce ba yanzu ba zai shirya mun hakan a
lokacin da yaga ya dace, amma yanzu ga Lailatu
bakuwa bai kamata in fita daga gidana in bar mata
shi ba da irin wadannan kalaman nashi ya kwantar
min da hankali.
Lailatu ba ta yi kama da amarya budurwa mai
gane al'amuran gidan aure a hankali ba komai ake yi
idonta yana kan duk da haka dai ina iyakacin
kokarina wajen ganin na kawar don kaina, don in
samu in cika umarnin da Umma ta bani na yi mata
girgi tsawon watanni biyu wai taci amarci.
Rannan da safe naje zan shiga dakin Yaya Almu
sai na ji ta a ciki tana ce mishi ni fa na gaji da karbe
mun kudin cefane da ake yi da sunan wai ana taya
ni girki, daga yau a rinka bani kudina a hannuna ina
yin lissafin cefanen in an kawo sai ta girka in har
abin kirkin take son yi maka da gaske ba iya yi ba,
ba na son kina fadin irin wadannan kalmomin akan
Rabi Lailatun rannan na gaya miki bana so maganar
kudin cefane kuwa ni ban saba bayarwa ba mafi
yawancin lokaci ma ni bana sanin loka cin da ake

18
kawo abubuwan da ake amfani dasu a gidan nan, na
koma da baya na koma wurina na basu wuri su
gama maganganunsu sai da ya gama abin da zai yi
ya fito yazo wurina zai yi min sallama ya miko min
kudi ya ce ku raba ke da Lailatu wannan kuma ki
bai wa Baba Talatu, nasa hannu biyu na karba nayi
mishi godiya naje na bai wa Baba Talatu dubu
goman da ya bata tayi ta godiya tana sa mishi
albarka ita kuma Lailatu naje na ce mata amarya
gashi in ji maigida dubu hamsin ne amma ko a
jikinta na fito abina na dawo na same shi na ce
mishi dukansu sunyi godiya muka gama maganar da
za muyi da zai fita sai na ce mishi zan bai wa
Amarya girkinta yau tunda kaga tayi wajen kwana
arba'in a gidan nan gara muci irin nata girkin kuma
muji irin dandanonshi bai yi wata magana ba
alamar bai so in yi hakan, ni kuwa yana fita sai na
kwala mata kira amarya, ta fito tazo ta ce mun gani,
sai dai ni fa sunana ba amarya ba ne, ta yi maganar
tana cune da baki na ce ni kuma sunan da nayi
niyyar kiranki dashi kenan, Amarya ki shiga kicin
yau ki yiwa mijinki abinci ya ci, na wuce ta naje
dakina na yi wanka na tsala kwalliya na fito na
zauna a inuwa a tsakar gid aina kallon mu'amallar ta
da kicin din nata na kalli Baba Talatu dake gefena
na ce mata ina jin anjima zan bukaci shan kunun

19

gyada ko za ki iya dama min? Ta ce yanzu kuwa
uwar dakina ai ba ma sai anjima ba.
Da daddare ranar ina dakina naji muryar yaya
Almu yana kwala min kira nayi maza na amsa na
tafi kwanukan abinci na samu a gaban shi ita kuma
tana zaune a gefenshi tasha kwalliya ga baki yasha
jan baki ita da kwanukan abincin nata sai sheki suke
yi, ina ce mishi gani ya fara fada meye sunan
wannan abincin da ki ka kwaba yau? Ban ce mishi
komai ba sai ta yi maza ta ce mishi ai ni na yi bai yi
dadi ba ne? To bari in sake shirya maka wani ta yi
maza ta suri kwanukan ta fita dasu ta koma kicin
nima na juya zan koma dakina sai ya yi maza ya
kira ni me yasa kika bata girki ba da izinina ba? Na
ce saboda na gaji na wuce na fita na koma dakina
ban tsaya a falo ba don ganin ya biyo ni dame kika
gaji? Da abincin da za ki girka min in ci? Me yasa
kike nema ki koyi rashin kirki da can shekara nawa
ki ka yi kina yin girkin ke kadai? Nayi shiru yayi ta
maganganunshi sai da naga bai gane zurun da nayi
mishi ba sai na ce mishi ai nayi kokari in ma kai
baka gani ba ni na gani kwana arba'in ina yi muku
girki sanda aka kawo maka ni ai shekaruna basu kai
nata ba ni sha tara ce a lokacin ita kuwa an kawo
maka ita da ashirin da uku, ni a wancan lokacın
waya rinka yi mun girki, tunda ta iya gyara maka
shimfida ai sai ta iya baka abincin da zaka rinka ci,
20

zuba mun ido yayi cikin takaici sannan yaya Wani
mummunan tsaki ya fita.
Tun daga wannan lokacin kullum ran girkin
Lailatu ta rinka dibi-dibi kenan a kicin babu abin da
zata girka ya gamsar gashi ita kuma fadin rai ya
hanata ta rinka neman taimakona kamar yanda naji
mijin

Please Login or Register in order to submit comment