Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi saurin faɗa sai dai tuni na ɗora ƙafata ɗaya wacce nake jin kamar a garwashin wuta take.Tsabar azaba ban san lokacin da na fasa ihu ba,kaina ya juya daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba.



“Ayodele keee ?” muryar Momah ta daki kunnena,na ja ajiyar zuciya tare da buɗe idona dakyar da suka min nauyi.
“Lafiya kika kwana a titi? Wato ƙofar gida shi ya fiye miki kan ki kwanta a ciki?” Momah ce ke faɗa rai ɓace.
Kallon wurin da nake na yi,eh a dai ƙofar gidan ne nake zafin rana na haske ni.Dakyar na yunƙura na tashi tsaye,ƙafata ta dama ce na ji ta riƙe “washhh! Wayyooo Momah ” na faɗa hawaye na min shatata.
Abun ka ga uwa tuni ta haɗiye ɓacin ran ta fara taimaka min,dakyar na shiga gida kuka wiwi nake rera wa ita kuma ta na tambayata abubuwan da na yi jiya.Sam ban iya tuna wa ba,to ina ma na ga nutsuwar da zan tuna ɗin.
Jiƙe-jiƙen magani ta yi ta bani na yi wanka,babu laifi na ɗan ji dama musamman da ta saka min maganin massage abokini ta min tausa.Wunin ranar dai na dawo ƴar lelen Momah kamar can farko,duk fushin da take da ni ta janye.


“Allah sa dai ba jan magana ki ka je ki ka sake yi ba! Na sha faɗa miki ba komai ne mutum yake magana ba,haka ba kullum ya zama dole sai ka yi taimako ba.Amma ba ki ji,kunnen ƙashi ne da ke ! Duba ta dalilin ki inda mu ka dawo,da ace kin zauna ɗam da duk hakan ba ta faru ba”
Sama-sama nake jin furucinta don tuni na lula duniyar tunani,wanda ba na komai ba ne sai na mutumen nan mai suna André duk abubuwan da suka faru kuma suka dawo min daram a kwanya sai dai ban san ya aka yi na tsinci kaina ƙofar gida ba.
Na ja a jiyar zuciya ‘ta yi yu kuma mafarki ne na yi’ na faɗa a zuci bisanin na lalubo wayata,na kunnata saƙonnin Fatimah da kiranta ne barkatai na yi ta cin karo da su.


Kiranta na yi,har sai da ta yi ajiyar zuciya wacce nake kyautata zato ta murna ce.
“Wallahi duk kin tashi hankalina,kin kashe waya na je gidan ku kuma kun tashi har wasu sun shiga” cewar Fatimah.
“Yi haƙuri ƙawata tashin ne ya zo cikin wani yanayi,ya aiki kuma ku na ta zuwa?”
“Ina ta dai zuwa! A'isha yau wajen kwana nawa rabonta da aiki,kin san kuwa Dr Jaleel ya karɓi lambar ki wurina”
“Hum! Wasa dai kike,kuma sai kika basa?”
“To ya zan yi?” ta faɗa cikin tausayi,tuni na fahimceta don na daɗe da sanin Fatimah na mugun son Dr Jaleel.
“Oh! Na gane yanzu haka abokinsa ya tambaye shi,ban faɗa miki ba wani ya rage min hanya kwanaki har ya ce na burge shi wai”
Fatimah ta saki ranta,ta ce “wai ne ma? Don Allah Ayodele ki yarda ki fara soyayya a yi mutum kamar jikar almutsutsai”
Shiru na yi ,tunanina ya koma duniyar da na je jiya sai na ce mata kawai “Fatimah zan sake kiran ki” ƙittt! Na kashe kiran.

So nake na tantance shin wai mafarki na yi ko kuwa gaske ne,ina ta tunanin hanyar da zan bi na gaskata cikin ɗaga murya na ce “Lassey!”
Ji kake kwacaaaa Momah ta saki kwandon kwanoni da ta gama wanke wa,dama da gangan na yi don na ga réaction ɗinta.
Da sauri kuma ta shiga kwashe su jikinta har rawa yake,na kuma furta “Lassey fa?” sai na yi tamkar waya nake,ina ankare da Momah a wannan karon ma sai da ta zabura.Na saki murmushi na ce “to Allah kyauta sai an jima”

Duk motsin Momah a wannan ranar kan idona,ta yi wani irin sanyi liƙis abinci ma dai ban ga lokacin da ta ci shi ba.Sai na ji ta ban tausayi,kusa da ita na ƙarasa ina ɗingishi.Na kwanta tare da ɗora kaina kan cinyarta na ce “Momah gobe zan koma aiki”
“Allah kai mu” shi ne abin da ta faɗa ta na cire hullar kaina,“sabon kitso za a yi min?”
“Eh na gwara na rufa ma kan naki asiri je ɗauko mai da tsinke da kuma mashaci”
Hakan kuwa aka yi, Momah na min kitso ina ji lokaci zuwa lokaci ta na ajiyar zuciya haɗi da “hum” can ta kasa haƙuri ta ce “Ayodele ɗazu ke da wa kuke wa?”
“Fatimah ce”
“Na yi tunanin musulma ce fa,sai kuma na ji ki na ambaton sunan mahaifinta irin na Kirista”
Na gane sarai da Momah wayo take son yi min don ta ji gaskiyar lamarin,amma da yake ni ma hatsabibiyar kaina ce sai ce mata na yi “wane suna kuma?”
“Wai ina A'isha ? Har an yi bikin?” Momah ta canza zance,na lumshe ido na ce “bacci nake ji” na yi hakan ne don ɓoye mata abin da ya faru tsakanina da A'isha don za mu iya shirya wa ko da yaushe ,amma in na sanar da Momah ta yi yu ta riƙe abun a rai.





★MANSUR


Ya na fita daga gida ya wuce can gidan ogansu,bayan ya gaishe shi ne ya gayyace shi can tamtsetsen falonsa mai ɗauke da hatsabiben aljannu.Ka na ganin wurin za ka gane babu rahama,saboda komai na ciki baƙi ne wuluk hatta da capet da labulaye da kujeru.
Bayan sun zauna sun nutsu ogan ya fara bayani “Mansur ƙarshen watan April za ka kawo sacrifice ɗinka,budurcin mata huɗu,sai zuciyar jinjirin yaro sabuwar haihuwa”
Hankali tashe Mansur ya ce “oga a ina zan samu jinjiri? Su ƴan matan ba matsala ba ne saboda ina da gumbar susa,ga shi kuma watan Valentin Day ne ba za su wuya ba amma oga saboda Allah....”

“Noooo! Bar kira min sunan shi cikin falo! Wa ya faɗa maka muna buƙatar rahama a nan da za ka kira abun bauta ?”
Mansur ya kalli ogan nasu da kyau,ƙaton Arne ne mai yaƙi da Musulunci abin da ya fahimta bai son jin sunan Allah tsabar taɓe wa.
“Sorry oga! Amma please a duba min a ina zan samu jinjiri?”
“Wannan ba matsalata ba ce,sannan abu na gaba ba za ka yi wanka ba sai ka tara janaba sau talatin da tara” ogan ya faɗa cikin bagwariyar Hausar shi.
Mansur ya waro ido,dama yau ɗin ya ƙi yin wanka da Sallah ne a bisa sharaɗin ogansu.
“A dai duba oga! Yanzu haka ji na nake duk a takure da ban yi wanka ba”
“To maganar kake so sai kuma ka je ka yi wankan ka ga abin da zai faru da kai! Tashi ka bani wuri”
Da mugun sauri Mansur ya fito,a kan hanya sai tunani yake kan mafita cikin haka kiran Momynsa ya shigo “Allo Momy?”
“Na ce sai yaushe za ka zo ka ɗauke ni ne tun jiya na haɗa kayana” ta faɗa daga can ɓangaren.
“Gani nan zuwa Momy ” sai ya kashe kiran ya je can gidan mahaifansa.


Bayan sun gaisa ta basa fura ya sha sannan ya ɗauki tulin kayanta ya saka bayan mota,wasu ma a gidan baya ya zuba su.Ta shiga gaba suka wuce gida,ya na parker mota A'ishah ta fito da ɗan gudunta irin na sabbin amaren nan amma sai ta tsaya cak ganin Mansur ya zagaya baya na fiddo kaya ,Momy kuwa hannunta riƙe da uwar jaka sai ka ce mai biki.
Wani zungureren bido ta fiddo ta shiga yayafa ruwan da ke ciki a tsakar gida ta na yi ta na yin wasu surkullenta.

Babu shiri A'isha ta koma ɗaki jikinta na rawa,babu sallama duk suka shigo.Rasa mi za ta ce ta yi kawai ta yi tsaye su na ƴar kallon-kallon,“laaa! A'isha ko ba ki gane ni ba ? Ni ce Mairo Yayar Tani uwarki kin wani yi tsaye kin tare hanya ko ba ki so na zo ba ni da gidan ɗana ”


“Momy ai zuwan ne na ga kamar ba na lafiya ba har da kayan jiki sai ka ce wacce za ta dawo nan da zama?” ba ta rufe baki ba Mansur ya zube mata yatsunsa biyar tare da ɗora mata kwandon masifa.
Momy ta yi murmushi ta ce “yaro man kaza! Wato A'isha duk wulaƙanci da ku ka yi mana ke da uban ki duk kin manta? Bai da kuɗin aure ƴata karatu za ta yi ba zan sayar da Akuya ba ta dawo gida ta na ci min darni ba” Momy ta kwaikwayi muryar Abban A'isha .
Mansur ya ɗora da nasa furicin “daga rana irin ta yau doli ki yi duk abin da Momah ta saka ki saɓanin haka ki saka a ran ki kin ƙulla aure da ƙunci” ya na gama faɗa ya nufi ɓangaren da dama tun can na Momy ne,ita kuma ta take masa baya. A'isha ta faɗi gwaram ta yi zaman ƴan bori ta na jin wani matsanancin tashin hankali....
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI💫✍🏻```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________


Ba kusan a mayar da labari gajere amma kuma ba kusan biya daidai hum!
MUTUWARE book ɗin kuɗi ne 300 normal group,vip kuma 500 ba zan rage ko tamma ba ki zaɓi wanda kike so wacce ta san ba ta shirya ba don Allah kar ta min magana.Ki tuntuɓe Ni kai tsaye ta WhatsApp domin biyan kuɗin karatunki +22795045822




Page 8


Da sauri na nufi Momah ina mai tambayar ta “mi ya faru? Lafiya kike kuka?” ba ta kai ga bani amsa ba na ji an wani jawo ni ta baya ,dakyar na iya miƙe wa kan ƙafafuna na juyo ina fuskantar shi.Namiji ne dattijo wanda ya ba shekara saba'in baya ,shi ne ya jawo ni yayin da sauran tsofin da suka haɗa maza da mata suka yo gaba.
“Yau dai asirin ki ya tonu,shegiyar yarinya ashe mayya ce ke shi ne kika fake da sunan ceto kike.Wancan Kambun maitar da kika rufe shi muke so ki tono kafin Sarkin Mayu ya ƙara so ” ya faɗa ya na mai yin nuni da inda na rufe Kambun Kunkuru.

Banda haske babu abin da wurin yake ,wanda a bayyane yake kowa na ganinsa har da normal mutane.A daidai wannan lokaci ba zan iya yin wani dogon tunani ba ballantana na samo mafita ,duk ma ba wannan ba halin da Momah ke ciki shi ya fi ɗagan hankali.

Tsofin unguwarmu sai zagi ne suke a gaban jama'a, miyagun kalamai wanda duk mai zuciya ba zai iya jura ba.Sosai na yi mamakin dalilin da yasa ban ji sarawar kai ba ,saɓanin sauran lokuta da nake harzuƙa na ɗauki ɓoyayyar fuskata.
A na haka har Sarkin Mayu ya iso,sosai na yi mamaki ganin mutumen nan da muka taɓa haɗuwa cikin taxi.Bayani suka fara yi masa,shi kuma yayi kamar bai taɓa gani na ba tare da umarta ta “je ki haƙo abin da kika ɓoye”
Sai a lokacin na juya na dubi Momah,jiki a sanyayye na duƙa na buɗe ramen tare da ciron Kambun Kunkuru.Haskensa ya ƙara yawaita kan lokacin da yake cikin ƙasa,Sarkin Mayu ya karɓe shi ya na cewa “kin ji kunya ƴar ƙanƙanuwar yarinya da ke amma kin zama muguwa mayya kawai” da mugun sauri na rumtse ido ina jin hawaye na min zuba.

Mutane ne suka fara suratai akan sai mun tashi mun bar masu unguwa,zagi kam ya fi cika buhu babu kalar baƙar maganar da ba a faɗa wa Momah.Ita kuka ni kuka,Sarkin Mayu ya ƙara ɗaukar magana inda yake cewa “na baku nan da awa ɗaya kacal ku tashi ku bar nan ko kuma na sa a ƙone ku da ranku”

Jama'a suka ɗau ihu,da mugun sauri Momah ta shiga gida na take mata baya.A ɗaki na tarar da ita ta na gangamar kaya,rasa abin da zan ce mata na yi kawai sai na faɗa jikinta ina kuka.
“Kukan mi kike? Ina ce ke kika saya mana wulaƙancin da kuɗin ki,tun ranar da kika zo da abin nan sai da na ce ki mayar mai shi abinsa amma kika yi kunnen uwar shegu da ni” ta ida faɗa ta na mai ture ni na yi baya.
Daga inda nake ina jiyo hargowar mutane sai juya suke mana cikin gida tare da zaginmu.Cikin ƙanƙanen lokaci Momah ta haɗa kayanmu,dakyar da siɗin goshi muka samu mu ka isa bakin hanya.Ɗaiɗaikun mutane ne kawai ke tausaya mana,ciki kuwa har da Asabe don a gidanta ma Momah ta kai ajiyar sauran kaya.



A wannan wunin mu ka bazama neman haya sai dai kamar abun tsiya ba mu samu ba,sai a wata unguwa mai ƙarancin mutane kamar za a fita gari shi ma ɗaki ne ciki guda.A haka dai mu ka share mu ka zauna bayan Momah ta kwaso sauran kayanmu.






Komai na ta tafiya cikin tsari, musamman bikin da ya kasance tuwona maina ne.Amayar da angon duk ƴan uwa ne,sosai abun ya tafi cikin tsari. A'ishah sai rawar kai take,abokanta kuwa duk sun haɗu wurin kanmu . Fatimah kuwa sai ƙoƙarin kiran Ayodele take a waya saboda rabonta da ita wajen kwana biyu wayarta ma ba ta shiga,cikin wannan zullumi dai ta yi shagalin bikin.
Ranar ɗaurin aure tamkar babu gobe haka aka yi abun hauka musamman ɓangaren Mansur da yake taƙama da Nera.Motocin ɗaukar amarya kaf ɗinsu babu tsohuwa sun jeru rasss sai wacce ranka ya yi ma za ka shiga.A haka aka miƙa A'isha tamfatsetsen gidan mai kama da aljannar duniya,duk yadda ta so Fatimah ta tsaya fafur ta ƙi don dama kan babur ɗinta ta je ko kaɗan ba ta saki jiki da abokan Mansur ba don ƴan magana kan ce sai hali ya zo ɗaya ake abota.


Bayan kowa ya watse Mansur ya shigo tare da abokansa.Kallo ɗaya za ka yi wa gizner jikinsu ka ga Nera ce ke magana,suratansu suka fara ita dai A'ishah ta na rakuɓe sai da suka matsa mata ne ta ɗan ɗage mayafinta.Amanar abokinsu suka bata bisanin yayi masu rakiya ya dawo shi ɗaya.

“Ki sauko mu ci abinci mana” ya faɗa ya na mai jawo hannunta,cike da mamaki A'isha ta bisa har suka baje kan capet.Ta sha ji daga abokaina abu na farko da ake yi in an kai amarya sallah ce domin nuna godiya ga Ubangiji,amma sai ta yi masa uzuri da tunanin ko yunwa yake ji shi yasa.Ba ta kai ƙarshen mamakinta ba sai bayan da suka cika tumbinansu Mansur ya fara aika mata saƙonnin soyayya har ya kai da ya kusanceta,ko Bismillah ba ta ji yayi ba ballantana wai addu'a.

Washegari
Tsabar gajiya da ta yi ya saka ta rasa sallar asubah,hasken rana ne ya daki fuskarta ya sa ta yunƙura ta tashi zaune ta na kallon window.Gefenta kuwa Mansur ne ke ta sharar baccinsa,ta kai hannu ta na jijiga shi “Ogana ka tashi ka kai ni toilet ka min wanka please ba zan iya tashi ba” a shagwaɓe take fitar da harufan har ta ci nasarar tayar da shi.
Ya buɗe idonsa ya zuba mata su ,iya kallon da watsa mata kaɗai sai da gabanta ya faɗi.
“Mine ne?”
“Wanka za min ”
“Can a gidanku wa ke yi miki?”
Ras gaban A'isha ya faɗi jin furucinsa sun yi hannun riga da wanda ya sha faɗa mata satin aurensu.
Dakyar ta ƙoƙarta ta je ta yi wanka ta zo ta gabatar da sallah.Ta na nan zauna har Mansur ya tashi daga bacci,direct wurin drower ya wuce ya fitar da kaya masu kyau ya saka.
“Ka manta ba ka yi wanka ba fa ” ta faɗa ganin bilhaƙi yake shirin,“uban waye ya faɗa miki manta wa na yi?” Mansur ya faɗa a zafafe ya na kallonta.
“Ka yi haƙuri ”shi ne kawai abin da ta iya furta wa.
“Ki tashi ki ɗora min breakfast!” ya faɗa ya na mai fesa turare.
“To” ta amsa tare da tashi.Tsabar takaici sai da ta zubar da hawaye ,amma a haka ta haɗa masa frite da gasashen kifi don ta ga kusan akwai komai.

Kan table ɗin cin abinci ta ajiye bisanin ta wuce bedroom,waya ta tarar da shi ya na yi sai magana yake cikin ladabi.Da ace mahaifinsa na da rai da to babu shakka za ta ce da shi ne yake waya.
Bayan ya gama ne ya zo ya rungume ta tare da cewa “har kin gama?” kai ta jinjina masa,“ok mu je”
Falo suka koma a tare suka ci abincin, Mansur na yi mata hirar soyayya hakan ya kuma ƙulle mata kai.


“Zan tafi wurin aiki,tun ɗazu shugaba ke jirana” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye.
“Aiki kuma? A cikin satin aurenmu?”
“To sai aka yi mi? Kin ga ban so sakarci sai na dawo” ya na gama faɗa ya fice. A'isha ta zube kan salon ta na jin wata irin damuwa na dabaibaye ta,tun kafin aje ko ina auren Mansur ya fice mata a rai.“Babu wankan janaba ballantana a yi maganar sallah anya kuwa na auru? Mine ne ma ya hana shi ko fuska da baki ya wanke?” ta furta hawayen takaici na zubo mata bisanin ta ɓingire bacci.


Hayaniyar ƙawayenta ce ta tashe ta,sosai ta yi murnar zuwan su.Sauran kazar jiya ta ɗauko masu kafin a hau hira da girke-girke cike da nishaɗin ƙawarsu ta auri mai kuɗi kowacce ta sasaɓe zane ta ci abubuwa na kayan daɗi ta ƙoshi da za a tafi gida kuwa har da yin tsaraba.




AYODELE


Tun da muka dawo sabon gida Momah ke fushi da ni mai tsanani ,duk uban haƙuri da magiyar da na ta yi mata kanzil ba ta ce min ba.Hakan ya jefa raunatacen ruhina a cakwakiyar matsala,na bar cin abinci kan ƙa'ida,na kashe wayata aiki ma sam na bar zuwa.Amma hakan bai sa Momah ta tausaya min ba.
Kamar kullum wuraren ƙarfe takwas na dare na fito ƙofar gida na yi zaune,unguwar tsit take ko tsuntsu babu.
Wani mutum na ga ya bi ya wuce ta gaban ya nufi wani ɗan gangare,na bi bayansa da kallo kawai ina mamakinsa don yau kusan sau uku kenan da ina ganinsa.
Zuciyata ce ta raya min na bi bayansa,kamar aikaka haka na miƙe har da haɗa wa da gudu na take masa baya.Mun yi tafiya mai ƴar nisa bisanin na tsaya,domin ya kai wurin da ke da tsananin duhu ba zan iya shiga ba.
Idona ne ya sauka ga allon sanarwa mai ɗauke da sunan MAƘABARTA,gabana ya bada ras! ‘Ko shakka babu irin mutanen nan ne masu haƙo kabari don yi aikin asiri ko tsafi’ na faɗa a zuci ina mai ƙara ɗan yin gaba ina ɗigirgire ko Allah ya sa na hango wani abu.Daga bayana na ji an dafa kafaɗa,da mugun sauri na juyo muka haɗa ido a take hanjin cikina suka hautsana......





Ban jin daɗin jikina ina barar addu'ar ku🙏🏻
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI💫✍🏻```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________


To alhamdullah wannan ce page ɗin ƙarshe ta kyauta,don haka duk mai son ci gaba da karatu zai biya kuɗinsa na karatu 500 ta wannan account 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank kafin na saka shi group sai a turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822



Last free page 10



A'isha na nan zaune cikin halin ƙaƙanikayi Momy ta fito Mansur na bayanta.Kan salon ta hakimce ta sune ta tare da cewa “ A'isha ruwan gidan ma ba za a bani ba sai na roƙa ko kuwa ban isa ba ne?”
“Haba Momy ya za ki ce haka? Ai ko ban auren Mansur ke ɗin uwa ce gare ni domin ciki guda kuka fito ke da Mamana ” cewar A'isha ta na mai tashi da sauri har jikinta ke yin rawa ta nufi kitchen.
Drinks da abinci ta haɗo mata,ta dire su a gaban Momy sai bayan ta zuba mata komai ne ta tashi ta shige bedroom.Matsanacin kuka ya kubce mata,ta faɗa kan gado ta rusa shi cincin ƙarfinta.
Mansur ya shigo,“ A'isha?” ya faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ne ya ga ma yi mata tsawa ba.
Ba ta daina kukan ba ballantana ta kula shi,ya isa gare ta ya na mai jawo ta jikinsa ya shiga aikin rarrashi amma ta ƙi yin shiru .Sai da Mansur ya kai ruwa rana sannan ya shawo kanta,ashe shi ma da walakin wai goro a miya.Buƙatarsa ce ta kawo shi,kuma ko da ya samu abin da yake so ya bar ta nan.
Cike da baƙin ciki A'ishah ta isa toilet,abu ya tare mata goma da gomiya tara.
Kamar wata zararriya ta shiga dukan ruwa ta na cewa “da me zan ji? Wace rayuwa na tsoma kaina ni A'isha? Wayyo Allahna!” sai ta ƙanƙame dukkan jikinta jin tamkar ana kallonta .
Ƙoƙarin fita daga bawon wankan ta fara,sai dai tamkar wacce aka jone fatar jikinta da bawon haka ta ji ta liƙe gam.Cincin ƙarfinta ta buga wani uban ihu wanda ya karaɗe duka gidan,sai dai ko motsin wucewar ɓera ba ta ji ba ballantana Mansur ko Momy su kawo mata agaji.
Dakyar ta ci nasarar fiddo ƙafafunta waje,sai ta ga su yin wani ja ƙau jawur babu kyawun gani kamar jan nama.Hankalin A'isha bai ida tashi ba sai lokacin da Allah ya bata iko ta tashi kan ƙafafuwanta.Kaf shap ɗinta ya zube kamar an zuba sukari a ruwa,jikinta ne ya ɗauki wani irin rawa ganin ƙugunta kamar muciya saɓanin da can farko da take turbakallah.
Towel ta saka ta fito da mugun sauri,bayan Momy ta gani ta na mai fita daga ɗakinta ba tare da ta san mi ya kawo ta ba.
Bakin ƙaton madubi ta tsaya ta na kallon kanta,sai kuma ta ganta normal ba ta san lokacin da ta saki ajiyar zuciya ba.“Ashe gizau ne ban canza ba” ta furta cikin murna bisanin ta shafa mai da turare,ta saka kaya sai kuma ta fito falo.
Turus ta yi ta na kallon Momy na yayafa ruwa a duk wata kusurwa ɗaki,ba abin da ya fi bata mamaki irin sunanta da na Mansur da ta ji ta na ambato.
“In kin gama gulmar sai ki je ki yi abin da za ki yi” cewar Mamy ba tare da ta juyo ba.

‘Ko ya aka yi ta san na fito?’ A'isha ta tambayi kanta bisanin ta wuce kitchen.Girki ta ɗora ,bisanin ta dawo falo ta ɗauki wayarta.Fatimah ta kira,cikin sa'a ta same ta tamkar rariya haka A'isha ta buɗe baki ta na ba Fatimah labarin abin da ya faru da wanda ma ke kan faruwa ba tare da ta san babban kuskure ta aikata ba.


Da dare Mansur na dawo wa ya shiga ɗakin Momy,bayan ya gaisheta ne take ce masa “ɗazu matarka ta kira wata mai suna Fatimah ban san ya suke ba,amma kaf sirrin gidanka ta sanar da ita na mu'amalar ka da ita .Hum! Ni kuwa cewa ta yi jarababiyar tsohuwa ko amarci ba ku gama ci ba na zo na tare muku a gida”
Ran Mansur ne yayi bala'in ɓaci ,ya tashi da sauri ya fita.Ya na shiga ɗakin ya tarar da A'isha ta zanzare ta ci uban ado,tuni ya manta abin da ma ya kawo shi ya je ya rungumeta.
Gabanta ne ya faɗi lokacin da Mansur ke ƙoƙarin yi mata kiss saboda wani uban wari da bakinsa ke yi,warin hammatarsa kuwa ko bunsuru albarka .Amma a haka ta daure suka raya sunnah,cike da kula wa ya dube ta ya ce “daga yau kar na sake jin kin fitar da sirrina ,ko Momy ba ta faɗa min ba zan gane wa”
A'ishah dai ba ta ce komai ba ,zai lokacin da zai mayar da kaya ta ce masa “don Allah ka je ka yi wanka”
“Ba zan yi ba” ya bata amsa a takaice.
“Ko brush ka yi”
Mansur yayi saurin juyo wa ya na ƙare mata kallo cikin ido,‘ko dai maganin da na bata har ya karye ne da har ta ke iya faɗa min magana kai tsaye babu ɗigon tsoro?’ ya yi wa kansa tambayar a zuci.
“Ka yi haƙuri don Allah ” ta faɗa a ɗan daburce bisanin ta shiga toilet ta yi wanka.


Ɓangaren Momy kuwa shiru har yanzu ba ta ji ihun A'ishah ba ,ta yi zaton shegen duka Mansur zai lakaɗa mata.Ganin haƙar ta ba ta cimma ruwa ba yasa ta tashi ta rufe ƙofa da key,kayan jikinta ta cire

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment