Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,nan take bacci ya ɗauke.Duk a mafarki aka nuna min maƙabartar da za a rufe wannan baiwar Allah,da kuma duk abin da zai faru da yadda zan kuɓutar da ita.

Washegari muka hau aikin safe bisanin mu sauka,tuni Fatimah ta yi tafiyarta A'ishah kuwa a gabana ta kira Mansur kan ya zo ya ɗauke ta.Na taɓe baki don na lura har wani rawar kai take wanda yawancin amare ko kuma wanda za su auri mai kuɗi suke yi.
Kafin ya zo ne na samu tsure A'isha da ido na ce “bayan Mansur ya dawo daga Lagos halan kasuwanci ya fara?” shiru ta yi bisanin ta ce “wallahi ban sani ba,kin san in mutum ya je neman kuɗi da zarar ya dawo to fa hutu ne kawai yake,ina ga shi ma bai komi”
“To in kuɗin suka ƙare fa? Ke dai ki tambaye shi ƙila ya na kasuwanci ya ɓoye miki ne” na faɗa cikin son jawo ra'ayinta,don zuciyata ta fara aminta kan na rusar maganar auren nan .


“Wallahi ba zan iya ba,ƙwarjini yake yi min ba zan iya tambayarsa ba.Kin san kuwa yadda nake jin mugun tsoron Mansur? Wallahi yau da ya zo ɗaukata kasa kallon ƙwayar idonsa na yi”
“Hum! Wai dama ki na sonsa ko kuwa yanzu ne da ya zama mai kuɗi kike ra'ayin shi?”
“Sosai kuwa! Dama rashin kuɗi yasa ba a bari muka yi aure ba.Abbana ya ce sai na ida karatu duk don kar ran Mama ya ɓace kin ɗan Yayarta ne”
Kai kawai na jinjina ina tunanin wani babban al'amari,bisanin na ce mata “okay ni zan tafi in ya zo ki gaishe shi”
“Ki jira mana sai ya sauke ki gida”
“A'a na gode!” A'ishah ta riƙe ni ta na cewa “ wallahi babu inda za ki je dole mu aje ki gida”
Muna cikin wannan yanayi motar Mansur ta tsaya,fito wa yayi.Sanye yake da baƙaƙen suit idonsa manne da baƙin gilashi,cike da ƙasaita ya iso kusa da mu.

A inda yake tsaye zan iya hango tsantsar mamaki kan fuskarsa,wanda tuni na fahimci na gani na a raye ne.“sannu angonmu” na faɗa cikin raha,sai ya ɗan daburce ya na mai cewa “oh! Na shagala da kallon amaryata ne shi yasa,fatan ki na lafiya?”
“Garas nake!” na basa amsa ina mai kallon tsakiyar idonsa don tuni ya cire gilashin,ya kawar da kai ɓangaren A'ishah ya na mai cewa “amarya ba kya laifi! Mu je ko? ” ga mamakina kamar raƙumi da akala haka A'ishar ta bi bayansa ko kallona ba ta yi ballantana zancen yi min sallama ko kuwa ta yi maganar sauke ni a gida da ta ce.

Na rumtse ido tsabar takaici,ganin Mansur ya ci taya ƙura ta tashi duk ta baɗe ni.A hankali na buɗe su tare da bin motar da idon har ta ɓace ma ganina,jiki a matuƙar sanyayye na je na tsaya bakin hanya.Tsabar yadda ruhina yayi baƙi har ban san lokacin da na tsayar da wata farar mota ba madadin taxi,sai da na ji muryarsa ya na cewa “hanya zan rage miki?”
Cike da masifa na buɗa baki na ce “aka ce ma banda kuɗi ko na yi ma kama da irin ƴan iskan ƴan matan nan?”
Ya waro ido ya ce “keee! To ce miki aka yi motata taxi ce?”
Sai a lokacin na farga da mota ce,na yi baya ina cewa “ka yi haƙuri ”
“Na ƙi ɗin dole ki shigo na kai gida”
Zan kuma ƙara yaɓa masa magana sai na ga yayi min ƙwarjini don babban mutum ne mai cike da kamala zai kai shekara arba'in da biyar.Na haɗe yawu na ce “na gode” amma fafur ya ƙi tafiya ya nace a ƙarshe dai na yarda na shiga.
Mu na tafe ya mayar da volume ɗinsa,ƙira'a ce ke tashi ana karatun Alkur'ani.Ban san mi ya shige ni ba,amma sauraren sautin ya saka na fara jin sanyi a raina .“Wace unguwa za mu je”
“Unguwar ƴan tsofi” na basa amsa don haka ake kiran unguwarmu.Ya ci gaba da driving,ni kuwa sai sauke ajiyar zuciya nake ina jin nutsuwa na daɗa ratsa ni har mu ka isa layinmu.A ƙofar gida ya sauke ni,na masa godiya ina mai ficewa.




A'ISHA

Yanayin kallon da Mansur yayi mata ya saka duk wata gaɓa ta jikinta ta yi sanyi.Tamkar za ta shiɗe haka ta ji,ga wani tsoronsa da shakkarsa da ta ji sun ƙara dirar mata.Allah na gani sam ta manta da Ayodele na kusa da ita,hakan yasa ta bi bayan Mansur da take jin ko yanka kanta ya ce ta yi to babu shakka za ta yi tsabar biyayya.
Su na shiga mota ya kamo tafin hannunta,cikin salon yaudara yake mata magana “na tsani arniyar can mi ma sunanta?”
“Ayodele” ta furzo lafazin dakyar.Ya ci gaba da cewa “yawwa! Daga yau ina so ki nisanta kan ki da ita,kar na sake ganin ku na ƙawancen na yanke shi kowa yayi harakar gabansa ki na ji na ko?”
A'isha ta jinjina kai ta ce “in sha Allah ko magana ban sake yi mata”
“Yawwa my Ayush! Kar ki sake ce mata ko kanzil! Ki goge lambarta daga wayar ki kafin nan ki tabbatar kin yi blocking nata”
“Yanzun nan kuwa Oga!” A'isha ta faɗa tare da fiddo waya ta aiwatar da duk abin da ya ce.Ya saki hannunta,ya na canza akalar motarsa zuwa restaurant ɗin jiya.
A'isha na zaune Mansur ke cewa “gishiri bai kama kaza ba yadda nake so,ka san a jiya wasu sun ci da rabonta shi yasa na kawota yau ta yadda komai zai tafi daidai”
Wanda zai kawo abincin ya ce “an gama ranka shi daɗe!” can ya tafi ya kawo,tsabar mugunta ta Mansur shi ya dinga bata abincin da Allah kawai ya san adadin tsafin da aka yi masa,ita kuwa sai ci take.Bayan ta gama ya kaita gida zuciyarsa fal farin ciki,“na tsane ki Ayodele! Daga yau dai na yi ma takalme tubkar hanci” ya faɗa a bayyane ya na wata irin dariya.


FATIMAH

Tunanin kar Mansur ya tarar da ita ya saka ta yi tafiyarta tun da wuri.Addu'a neman tsari take kar Allah ya sake haɗa ta da shi,duk da ta na jin cutar da ya bata ta ci duk ta zawayeta amma hakan bai hanata jin normal tsoro a kansa ba tun da shi ɗin mugu ne.Ta na zuwa gida ta samu tuni ƙanenta ya karɓo mata babur ɗinta daga wurin gyara,sosai ta ji daɗin haka don ta na tunanin ta kaucewa shiga motar mugun saurayin A'ishah.


AYODELE

Ina shiga gida na tarar da Momah zaune kan tabarma ga wani akwati a gabanta ,ta na gani na da sauri ta rufe shi ta shige ɗaki,na bi bayanta sai na ga ta tura shi ƙarƙashin gado.
Ban damu ba don ko magana ban yi mata ba,kayan jikina kawai na canza na fito.Jikina na bani kan na je maƙabarta hakan yasa na fito na samu wata taxi na masa kwantace da inda zai kai ni.Kamar dai yadda na gani cikin mafarki tun daga hanyar da aka bi da ni har izuwa maƙabartar.
Daga nesa na yi tsaye,mutane sai bisa suke ido kawai nake bazawa ko Allah yasa na ga kabarin wannan baiwar Allah.
Wani ihu ya ja hankalina,da sauri na juya ɓangaren haguna,sai na ga ashe akwai wasu kaburbura ma ta nan.Idona ya sauka kan gawarta,mugayen tsofin nan kuwa jira suke a rufeta su far mata.Ban buɗe bakina na yi magana ba,amma tabbas na kira su izuwa gare ni.Duk da alamun tsoro a fuskarsu yayin da kuma suke ƴar kallon-kallon,ban basu isasshen lokaci ba na dirar masu ko kuma na ce esprit ɗina ya shiga yin faɗa da su har na ci nasara a kansu duk suka gudu.
Daidai nan na dawo cikin hayyacina,wasu daga cikin mutanen da ke ƙoƙarin turbuɗeta suka ja baya su na kiran “wallahi da ranta” ina jin haka na yo baya na yi tafiyata.


Lokacin da na iso gida na Momah na banɗaki ta na wanka,hakan yasa na yi saurin shiga ɗaki na jawo akwatin ina buɗe wa na yi arba da wani hoto da yasa kaina yayi bala'in sarawa ya na daɗa juyawa......




Iya page 10 zan yi a free,ki yi amfani da wannan damar ki biya 400 kafin na gama free page in kin shirya ki min magana +22795045822
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI💫✍🏻```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________

*Masu maganar gari babu kuɗi na hauda farashin littafi daga 300 zuwa 500, na faɗa maku wannan ba gajere ne ba.Amma tun da kun ce 300 ɗin za ku biya mu je a haka amma ni ba zan yi dogon labari ba sai na mayar da shi gajere*🤷🏻‍♀️

Wacce ta shirya yin payment za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta WhatsApp +22795045822

Page 7


A cikin hoton zan iya gane Momah duk da ƙarancin shekarunta a lokacin,hannunta riƙe da baby girl an yi wa gashinta wani tozo daga gaba,gefenta kuma wani gawurtacen namiji ne dattijo amma ka na ganinsa ka ga jarumi.
Duk cikin hoton yanayin shigarsu ce ta fi ɗaukar min hankali,ba kaya ba ne irin wannan da muke saka wa ba.A'a nasu kamar fata ce aka sarrafa aka mayar da su kayan,su ma ɗin iya cinya ne a saman riga kuma wata rabaja ce kamar zaren kwakwa.
Kaina banda sarawa babu abin da yake,daga bayana na ji taku da sauri na mayar da hoton cikin akwati ina ƙoƙarin mayar wa.
“Ayodele mi kike a nan?”
Da sauri na miƙe na ce “babu komai Momah ” kallon tuhuma ta fara yi min amma na share tare da fito wa tsakar gida,zuciyata fal fargaba ‘wannan shi ne mahaifina? Wace ƙasa ce wannan ke shiga kamar ta arna? Sai yaushe Momah za ta kai ni gare shi? Ina son mahaifina’ duk a zuci na yi maganar kafin na zauna na kishingiɗa ga katanga.Wasu hawaye masu mugun ɗumi ne suka shiga sintiri a kumatuna, “na fita zuwa kasuwa sai na dawo” na ji muryar Momah ,na buɗe ido ina kallonta sarai ta ga ina hawaye amma ba ta tambaye ni ba ta fice.

Ko mi ta tuna oho,sai ga ta kuma ta dawo “tashi mu tafi tare ” na miƙe na ɗauko kallabina na saka takalmi,sai da na wanke fuska sannan na fito.Momah ta rufe ɗaki da gida mu ka wuce kasuwa,tun da mu ka shiga nake jin tsikar jikina na tashi.


Ina nan tsaye na ga wata yarinya na jaye da wani tsoho irin masu Bara a kasuwa,sai cewa take “a bamu sadaka saboda Allah da Annabi ” kafe su na yi da ido sun tsaya gaban wata mace mai sayar da busasar zogale.
Cike da azama na yi tako ɗaya zuwa biyu na damƙe hannunsa,cike da mamaki yake kallona idonsa da suke a rufe ƙarya ce ba makahon gaskiya ba ne.
“Mine ne za ka yi? Kan mi za ka saka hannunka cikin kwagirinta na kuɗi?” na tambaye shi,duk sai ya rikice ya ce “ki yi min rai ƴata,doli ce ta saka nake wannan ɗabi'ar ”
“Kake damfarar mutane ba! A yadda kake duk wanda ya ganka zai ji tausayin ka amma ka yi amfani da maganin rufa ido ka na cutar bayin Allah ”
Hawaye na ga su na zuba a idonsa ya ce “saboda na ciyar da iyalina ne amma ba da son raina nake hakan ba,amma na yi miki alƙawari daga yau ban sake wa”
Na sakar masa hannu,abu guda da na fahimta kaf uwanda ke kusanmu babu wanda ya gani ko ya ji tattaunawar mu.Dube-dube na fara can na hango Momah da ɗan saurina na ƙarasa gun ta.

Mun yi gaba kaɗan wani yaro ya faɗi gabana,cike da tausayi na miƙar da shi ina mai tambayarsa “mi kake ma kuka?” da hannu ya yi min nuni ya na magana amma ba ta fita saboda yadda kukan ya ci ƙarfinsa,hannunsa na ja mu ka shiga tafiya direction ɗin da yake nuna wa har mu ka isa wurin wani mutum.
Na buɗe baki zan ƙara tambayarsa kawai idona ya sauka kan ƴar ƙaramar baro mai ɗauke da doya.
Cikin dake wa na dubi mai sayar da doyar na ce “mi ka yi masa yake kuka?”banza yayi da ni hakan ya ban haushi na yi kururuwa duk mutane hankalinsu ya dawo kanmu wasu tuni sun zo su na tambayar lafiya.
“Faɗa masu abin da ya faru” na cewa yaron,cikin ikon Allah yayi bayani yadda kowa ya ji “mu na tafiya ne ni da twin ɗina sai wannan mutumen ya kira mu ya ce mu zo mu karɓi chocolat sai ni na ƙi zuwa Amra ta je ta karɓa shine ta zama doya”

“Laaaaha'ilah! ” duk kusan mutanen suka faɗa,amma mai doya ƙiri-ƙiri ya ƙaryata yaron ya ce “ka ji zai ƙulla min sharrin duniya,tun yaushe nake sana'ar sayar da doya a nan an taɓa kama ni ne? To nuna min ƴar uwar taka wacce na mayar”
Cike da yarinta yaron ya je ya nuna ɗaya da ke can ƙasa,shi kuma mai doyar ya ɗauki wuƙa ya yanka.

Da hannu na shiga taɓi na ce “a gaishe ka sarkin macuta na duniya,wato masanya ka yi to yanka wannan mu gani” na faɗa tare da nuna doyar da idona ƴar ƙaramar yarinya ce ƴar shekara huɗu.Muƙut ya haɗiye wasu yawu,cikin tsawa na ce “ka yanka aka ce ko kuma na kira ma ƴan sanda”
Ya ƙanƙance ido zai yi magana amma mutane ba su basa dama ba saboda hantarar shi da suka fara kan ya yanka ko kuma su kashe shi.Hannunsa na rawa yasa wuƙa zai yanka na ce “ba nan ba” sai dai tuni ya yi wulish ya yanka nan jini ya fara tsirta.Kawai sai ya fashe da kuka,wani ya kira ƴan sanda a nan cikin kasuwa ya mayar da ita mutum wurin da ya yanka kuma kusan idonta ne.
Ɗan kwalina na keta na ɗaure mata gun,ƴan sanda suka cabke shi kafin ƴan sanda su tafi da su suma don doli sai an kira iyayensu.

Neman duniya na yi wa Momah amma ban ganta ba ,a doli na dawo gida.
Bakin ƙofa na zauna ina zaman jiranta,kamar wacce aka mitsika na je na buɗe ramen da na saka Kambun Kunkuru.Har yanzu da ransa,sai dai ya ɗan gaji ya kuma ƙara girma.Na kuma mayar da shi a karo na biyu na rufe,ina nan zaune taxi ta tsaya .Momah ta fito,har muka sa kaya cikin gida ba ta ce min uffan wato fushi take da ni.
“Mom...”
“Yi min shiru! Wato ke ba za ki taɓa ganin abu ki yi shiru ba ko? Kaf kasuwa zancen ki ake ,ko kin yi tunanin ban san abin da kika yi ba? Na san yanzu zancen ya zo har nan unguwar shikenan sai a dinga kasa mu a faifai ana tallarmu duk irin gargaɗin da na yi miki amma kika yi fatali da shi kin kyauta!” ta na gama ta shige ɗaki.


Duk jikina ne yayi sanyi,a fili na furta “in sha Allah daga yau ba zan sake shiga sabgar kowa ba,ko da kuwa ace ni ce za su cutar zan yi shiru su kashe ni ”


Kamar yadda Momah ta yi hasashe kuwa hakan ce ta faru,zancen Ayodele ya cika unguwar tuni ma wasu sun fara zarginta da mayya.Dama ba su gama tantama akan al'amarin ceton Zeinab da ta yi ba.Yau kuma ta ceto yarinyar da aka mayar doya,tambayarsu ita ce inda a ce ba ta da ido uku ta ya aka yi har take fahimtar abubuwan da ke ɓoye wanda normal mutum bai gani? Wannan al'amari ya ƙara tunzura sauran Mayun da ke unguwar,tare da ɗaukar alwashin sai sun tozarta ta a bainar nasi.



★Washegari

Yau juma'a ce,da baƙin cikin abin da A'isha ta min jiya na kwana duk tun a jiyar na yi ƙoƙarin kiranta na wanke ta tasss amma ban same ta ba.
Ina isa asibiti na tarar da ita bakin ƙofa a tsaye jikin mota sai uban murmushi take zuba wa,da alamu sallamar Mansur ce za ta yi wanda shi kuma yake a zaune ya fiddo ƙafarsa ɗaya waje.
Na danne zuciyata na ce masu “sannun ku da hira” in dai ganye bedi na magana to su ma sun tanka ni,tunani na yi ba su ji ba sai na yi tsaye na ce “duk soyayyar ce haka?” Mansur kawai ya dube ni shi ma bai yi magana ba ,ita kuwa A'isha ko waiwaye .
Ganin irin cin kashin da suka yi min ya saka na shige cikin asibiti,na ja ƙyaci ina mai cewa “ai za ki zo ki tarar da ni ”

“Ayodele lafiya kike magana ke ɗaya” cewar Fatimah,na ce “ A'ishah ce wai don ta na gaban saurayi ta yi banza da ni ”
“Kai haba? Ni kuwa sai da mu ka gaisa har da shi Mansur ɗin”
“Hum!” kawai na iya yi bisanin na je na aje jaka na saka farar rigar likitoci.
Sai da mu ka yi nisa cikin aiki sannan A'ishah ta shigo,ina jin lokacin da Dr Jaleel ke yi mata faɗa kan ta zo lati sai haƙuri take basa.
Cikin sigar wasa na zo daf da ita ina mai cewa “na zata har shi Dr Jaleel ɗin banza za ki yi da shi,ko da yake yanzu masoyin naki bai nan” wani kallo ta yi min ba tare da ta ce komai ba.
Ni ma na kama gabana,ko lokacin cin abinci haka A'isha ta ware kanta duk yadda Fatimah ta so ta ja ra'ayinta amma ta ƙiya.


Tun daga wannan rana mu ka fara takon saƙa da ita,tun mutane ba su gane ba har suka fahimta.Dr Haleema har zaunar da mu ta yi ta yi mana nasiha amma a banza ,haka zan yi ma A'ishah magana ita kuma ta basar.In muna zaune cikin jama'a sai ta bai wa kowa hannu in ta zo gare ni sai ta tsallake,tun ina yi mata uzuri har ni ma na aro rigar rashin mutumci na yaɓa ma kaina don dama can ni masifaffiya ce ta ajin farko.

Yau saura kwana uku bikin ta,ina ji ta na bai wa Fatimah labari “Oga dai ya matsu a yi aurenmu,kin san a baya ya sha wuya sosai wurin soyayyata yanzu lokaci yayi da zai cika burinsa”
Fatimah ta ce “ai ke ma ga shi sai zumuɗi kike,na matsu mu miƙa ki gidan Mansur ko hankalinmu ya kwanta”
“Ai fa dai na matsu wallahi ”
“Ayodele kin ji yaran zamani ko?” Fatimah ta sako sunana,ina jin lokacin da A'ishah ta ja tsuki.
Ina cika takardu na ajiye na kalle ta na ce “da wa kike?” shiru ta yi ba ta ban amsa,na miƙe a hassale Fatimah ta sha gabana ta na cewa “don Allah ki yi haƙuri! Kin ga dai ba ta ce da ke take ba”
“To da uban wa take?”
“Ba ta dai ce ke ba, A'ishah don Allah tashi ki yi tafiyar ki tun da lokacin tashi yayi” cewar Fatimah,kamar jira take ta ɗauki jakarta ta fice.
Sosai Fatimah ta yi ta danna zuciyata tare da roƙona kan na je bikinta na nuna mata ba komai ba ce duniya,bisanin ita ma ta tafi.
Sai da na gama cika takardu sannan na fito. “Ƴan mata?”
Da mamaki nake kallon shi na ce “kai ne?”
“Eh wallahi na zo wurin abokina,ashe wannan asibitin kike aiki ?”
“Eh! Wurin wa ka zo?”
“Dr Jaleel mana,kin san abokina ne yanzu haka shi nake jira za mu wuce gidana”
“Ok yayi”
“Ba ki faɗa min sunan ki ba,tun ranar nan dai da na rage miki hanya na ji kin burge ni” karon farko da na taɓa jin haka daga namiji,sai abun ya ban dariya ban kai ga magana ba Dr Jaleel ya fito hakan yasa na yi tafiyata.



Tun daga nesa nake tsinkayen yadda mutane suka yi dandazo a ƙofar gidanmu.Gabana tuni ya fara dakan uku-uku,ina iso wa wasu suka fara faɗin “Ga ta nan!” can kusan ƙyauren gidanmu na ga Momah a rakuɓe idonta sun yi ja jawur,kallon mutane kuwa tuni ya dawo kaina......
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI💫✍🏻```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________



*Har yanzu ƙofa a buɗe take,za ki iya biyan 400 domin shiga vip group wacce ta shirya biyan kuɗin karatunta za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta WhatsApp* +22795045822


Page 9


A lokacin da na juyo na fuskance shi,a sa'ilin ne kuma na tantance fuskarsa duk da ƙarancin haske da ke wurin.Fuskarsa baƙa ƙirin ce mai ɗauke da ƙwalayen idanuwa babu komai sai gurbinsu da ya bai wa jini damar gangaro wa kan lamutsatsun kumatunsa.
Zuciyata ta fara rawa,hankalina ya tashi farashin tsorona ya ninku ainun ina ta ƙoƙarin cira ƙafata sai dai bai bani damar ba domin kuwa tamkar an dasa ni haka nake a tsaye ƙiƙam.

“Mi bil'adama yake a duniyarmu?” ita ce tambayarsa.
Gabana ya ƙara bada wani sautin rasss,tsabar firgici ban san lokacin da na furta “Ayodele yau kin ɗebo ruwan dafa kan ki”
“Ayodele? Ayodele?” ya maimaita sunan har sau biyu cike da mamaki,bisanin ya ci gaba da cewa “ƴar sarki Lassey?” A daidai wannan gaɓa samaniya ta ɗauki wani irin rugugi da kuma wata irin walƙiya.
Da sauri na lumshe ido jin saukar ruwan sama,wanda suka zame min tamkar wankewar tsoron da ya aure ni.Ji na nake kamar ina kan gajiyar izzata wacce nake juya gawa tare da yin magana da su ba tare da na ji tsoro ba.
Na ji saukar hannunsa akan kafaɗa a karo na biyu,“barka da zuwa duniyar ababen bauta,haƙiƙa ƙarfin ruhinki da nacinsa ya jawo ki izuwa nan.Zo ki yi ziyara gun dangin kakannin ki”
Na ware idona,a yanzu kam ban san mi ya shige ni ba sam ba na jin tsoronsa haka fuskarsa ma ba na ganin muninta.

Tamkar raƙumi da akala ya yi min jagora izuwa tsakiyar maƙabartar wacce take maƙil da kaburbura.
Wasu sanaye ya shiga ambato dukkanninsu babu ɗaya na musulmi,kamar almara sai na fara ganinsu su na fito wa daga cikin kabarinsu su na yin zaune.
Gabatar min da su ya fara ɗai baya ɗayan har aka kawo kan wani tsoho ya nuna min shi da hannu ya ce “kin ga wannan shi ne kakan ki Sarki Octbar,shi ya haifi mahaifin ki Sarki Lassey,waccan kuma da kike gani Yayar baban ki ce sunanta Déborah bayan ta sauka daga mulki mahaifin ki ya hau.Je ki gare su na san za su baki saƙo ,bayan nan sai na kai ki gun ababen bauta”
Gun wanda ya kira da Kakana na je na yi tsayi,hannuna ya kama bai yi magana ba sai jimƙe shi kawai da yayi.Tamkar yadda ake turan abu a xender haka na fara jin sabbin abubuwa na ratsa jijiyoyin hannuna su na shiga magudanar jinina wanda don dole na lumshe ido.
Ya na sake min hannu ya shige ƙarƙashin ƙasa,“ungo wannan zoben ki saka shi,na san komai daren daɗewa za ki je Victoria Falls duk da mahaifiyar ki ba ta so.In kin je ki gaishe min da ƙanena ” Déborah ta faɗa ta na saka min wani tsobe a yatsana manuniya na hagun.


“Mu je” na ji muryarsa, “André kar ka kaita ko ina ka mayar da ita duniya,a halin yanzu akwai tazara mai ƙarfi ita da karagar mulkinta.In lokaci yayi ababen bauta su za su neme ta da kansu,amma mi zai hana ka nuna mata ababen tarihin shahararrun matsafa da kuma yadda suke wanzar da tsafin?”

Sai da ya dube ni da kyau bisanin ya jinjina kansa , Déborah ta ɓace ma ganina a kuma daidai wannan lokaci na tsinci kaina cikin wani hatsabibin daji.Na fara waige-waige,wani irin “wuhummm! Zummm!” nake jin ma'adanar sautina na zuƙo min ai kuwa na toshe kunne,ashe hakan shi ake kiran ainahin ga wofi wai harare cikin duhu don hakan da na yi bai canza zane ba.
“Haƙuri za ki yi da sannu za ki saba”cewar André ,bisanin ya shiga nuna min wasu itatuwa wanda suka fi ɗaukar hankalina su ne wanda suke jere su uku an yi masu ado na penti masu nuni da kalolin tsafi da asiri (mai son ƙarin bayani ya nemi littafina na ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI)


Mun yi yawo sosai sai bayanin abubuwa yake min,cikin haka ne na shagala sai ji na yi na yi baya.“Kar ki bi ta nan...”

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment