Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamanta ba.
Yadda aka tarbe mu kawai ya isa mu gane Mansur sananne ne a wurin.
Shi ya zaɓi abin da za a kawo ma A'ishah yayin da ya nemi mu zaɓa da kanmu,amma sai A'ishar ta nuna masa ko wurin aiki cikin plate ɗaya muke cin abinci don haka nan ɗin ma ba za a ware mu ba.
Shiru yayi ya na ɗan tunani,bisanin ya bai wa serveur ɗin umarni kan yayi yadda ta ce.Lafiyayen abinci ne,haka muka fara ci hankali kwance ba tare da wani tunani ba shi kuwa Mansur duk ya zama wani iri.
Tamkar wacce aka sa ƙugiya ana ƙoƙarin zaƙulo hanjin cikinta haka na fara ji cikina na min ciwo,da sauri na fidda hannuna na ce na ƙoshi.
Na tashi tare da tambayar masu kula da wurin ina ne toilet,aka nuna min na shiga.Amai na ta kwarara wa kamar raina zai fita,tsabar azaba har wata zufa ke tsatsafo min ina buɗe ƙofar toilet na yi kiciɓis da saurayin A'ishah....
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI💫✍🏻```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________



Page 5


Na yi tunanin ko banɗakin zai shiga hakan yasa na ɗan yi saurin ja baya na basa wuri.Amma da mamakina sai na ga yayi tsaye ƙiƙam hakan yasa na ɗago na dube shi.
Kamar mai son tantance wani abu haka yake kallona bisanin ya ce min “fatan dai lafiya?”
“Alhamdullah!” na amsa masa a takaice “okay!” ya faɗa tare da koma wa baya yayi tafiyar shi.Na bi shi da kallon mamaki bisanin na take masa baya,ina zuwa sai na tarar ya zauna kujerata wacce na tashi kawai sai na yi tsaye.
“Ki zauna mana” ya faɗa cike da kulawa,ban sani ba ko bai lura ba ne ya zauna a nan ɗin oho amma dai haka kawai na ji ban ra'ayin zama inda ya tashi .

“Ke ma ki zauna mana ga kujera nan,ki yi tsaye kamar wata soja?”cewar A'ishah,ganin haka yasa na zagaya zan zauna kan kujerarsa ba don na so ba don haka kawai nake jin akwai makircin da ya shirya,cikin ikon Allah wayata ta ɗau ringing,ina duba wa sai na ga sunan Momah .
Ina ɗaga wa ta ce “a ina kika tsaya har yanzu ba ki zo gida ba?”
“Momah gani nan zuwa yanzun nan” na faɗa cikin rawar murya.
“Ki na ina na ce?”
“Tare da su A'isha Momah ” na faɗa tare da mayar da wayar a hand free ta yadda za su ji abin da Momar za ta ce sai kuma na yi masu alama da su yi magana,sai dai kafin su kai ga yi Momah ta ce “ki dai yi sauri ki dawo gida sam jikina na bani babu hairan a ind....” ban bari ta kai Aya ba na kashe kiran ina muzurai “zan tafi sai gobe in mun haɗe”shi ne abin da na iya furta wa bisanin na yi tafiyata ba tare da na jira cewar su ba.




Bayan na fito daga restaurant ɗin sai na yi tsaye turus,don rasa ta ina zan bi na yi.Tamkar an sauya hanyar, lokacin da muna cikin mota lafiyayyar kwalta ce saɓanin yanzu da na tsinci kaina cikin jeji.

Wurin babu gida ko ɗaya sai ciyayi,da na waiga ma hatta restaurant ɗin babu ta ɓace ma ganina.A nan take na fara jin tsoro duk da ni ɗin ba ma'abuciyarsa ba ce,tafiya na fara ba tare da na san inda nake jefa ƙafata ba har na isa wurin da hanya ta tsage ta rabu biyu.Wata irin ƙishirwa nake ji a cikin mintin da bai gaza goma ba,maƙoshina ya bushe ƙamas.
Idona suka fara ɗaukar caji,na lumshe su a hankali kuma bakina ya fara fitar da sautin wani Yare.Ban buɗe idona ba sai da na ji ƙarar motoci da zantukan mutane.
A bakin titi na tsinci kaina, Allah ya taimake ni na hangi wani gu ana sayar da ruwan leda na tsallaka na sayi leda huɗu a nan tsaye na shanye su.Na ja ajiyar zuciya kamar wacce aka dawo ma da ruhi haka na ji,daga nan na tari taxi sai gida.





A can restaurant kuwa sosai hankalin Mansur ya tashi,muryar Momah tamkar busar sarewa haka ta ratsa dodon kunnen shi.Ya so ya tsayar da Ayodele saboda hatsarin da ke da wurin,amma da ya tuna zuciyarsa ba ta aminta da lamarinta ba sai ya ƙyaleta tare da yaƙinin sai dai a yi labarin wata amma ba dai ita ba.
Bayan sun gama cin abinci ya ɗauki su a mota,sai da ya fara ajiye Fatimah sannan ya kai A'ishah.
“Wai wace ce ita? Wato abinci mai magani ba zai taɓa zama a cikinta ba shi yasa ta amayar da shi.Na tsane ki! Ita kuma uwarta ta wace ce? Ya aka yi har ta san na shirya plan akan ɗiyarta?” ya jero ma kansa tambayoyin ya na mai bugun sitiyarin mota a haka har ya isa tankaɗeɗen gidansa wanda ya ji komai na more rayuwa.Sai da yayi wanka ya sha madara mai sanyi sannan ya kira A'isha suka yi ta hirar soyayya a ƙarshe ya tambaye ta “ya labarin ƙawar ki?”
“Wace daga ciki?”
“Wannan mai siffar Inyamurai” ya bata amsa,ta yi dariya ta ce “don dai ta na da jar fata ne sosai amma ai ba ta kama da Inyamure ”
“Fatan ta je gida lafiya?”
“Wallahi ba mu yi waya ba”
“To ki kira ta mana,sam ban yi kirki ba da ban bata ko da kuɗin taxi ba ne”
“Jira na kirata to” cewar A'isha ta na mai kashe kiran,Mansur ya lumshe ido ya na jin zuciyarsa na ɗan dokawa burinsa guda A'isha ta kira ta ce masa ta mutu.




AYODELE

Ina isa gida Momah ta wani jawo ni a jikinta ta rungume bisanin ta fara duduba ni kamar wacce ke neman ko na samu wata illa ne.
“Daga yau kar na sake jin kin tafi yawo kin ji ko? ”
“To Momah ” na amsa.
“Ayodele ke ɗin ta daban ce,dole ki dinga taka tsantsan duk da ina da yaƙinin ababen bauta ba su taɓa bari a cutar da ke ba,domin su na tare da ke a ko ina amma ki dinga kulawa ba ko ina ba ne ake zuwa” Momah ta sake faɗa ta na mai kallona cikin ido.Kai kawai na jinjina mata bisanin na wuce ɗaki,kaya na cire na yi ɗaurin ƙirji na je na yi wanka .
Ina tsaka da cin dambun shinkafa da Moma ta girka kiran A'ishah ya shigo,gabana sai da ya faɗi a take duk abin da ya faru da ni ya dawo kaina,hakan yasa har kiran ya katse ban ɗauka ba . Lokacin da na biyu ya shigo kuma a daidai nan maƙociyarmu Asabe ta shigo ta na rangaɗa sallama.

Na amsa mu na gaisa wa,Momah ma ta fito .Godiya ta zo ta na ta faɗa mana yadda lamarin ya kasance da Zeinab nan muka yi ta hira kan Mayu da illolinsu.Sai bayan ta fita ne na duba wayata ,har zan maida kira kuma sai na fasa na tsunduma zancen zuci ‘tabbas da walakin goro cikin miya! In babu rame mi ya kawo zancen shi? Mine ne na biyana har toilet? Babu shakka akwai abin da ya saka a abincinmu,to shi kuma restaurant ɗin da ya zama kamar ɓatan wata? Hummm! Zan nutsu,na ankare komai sai na gano gaskiyar lamarin’
Abincin ma sai ya fita raina,tashi na yi na fiddo fararen rigunan da nake saka wa na likitanci na wanke su tasss bisanin na kwanta ina yin bacci don jiya mun sha aiki sosai.

Tamkar a mafarki na ga wasu mutane masu fararen kaya sun zagaye ni,idona sun min nauyin da ba zan iya ware su duka ba amma tabbas ina iya ganin abin da ke gabana.Kaina na ji an fara shafa wa yayin da sauran kuma ke yin hira cikin wani Yare wanda in ba zan manta ba shi ne na taɓa ji Momah ta yi.Cikin wannan yanayi na lula duniyar mafarki,yau ma kamar kullum sanye yake cikin kayan ƴaƴan sarakuna ya saka kayan yaƙi,daidai ƙugunsa kubai ne mai ɗauke da takobinsa.Gefensa kuma masu tsaron lafiyarsa ne a tsaye cikin shirin yaƙi akan duk wanda ya kawo masu farmaki.Murmushi yake sakar min ya na kallona daga nesa, cikin izzar da ban san yaushe na same ta ba na fara takawa izuwa inda yake muna facing juna.Da sauri na lumshe ido sa'ilin da ya tsaka ɗan yatsansa manuni ya dangwala min jininsa a goshi a nan take wani sanyi ya luluɓe ni yayin da kuma nake jin shigar wasu lamurran da ba zan iya fassara su ba su na ratsa ɓargo da tsokar jikina.

“Ayodele? Ayo....” a kasalance na buɗe idona na zube su kan Momah wacce ke faman jijigata da kiran sunana.
Ta sakiya wata nauyayyar ajiyar zuciya bisanin ta ce “daga yau kar na sake ganin kin yi bacci a daidai lokacin da tartatsin rana ke tsakiya ban so”
Dakyar na iya buɗa baki na ce “don me?”
“Lokacin babu wata albarka a cikinsa ,bacci ya haramta ga al'ummar Victoria Falls ”

Da mugun sauri na ce “su waye kuma al'ummar Victoria Falls ? A wacce ƙasa ce? Mine ne haɗi na da su?”
Da mamakina sai na ga Momah ta rikice,abin da na lura ma kamar suɓutar baki ce ta yi.“Ki na ji Ayodele mu bar wannan maganar,ke dai kawai ki kiyaye abin da na ce.Am...na ce ... Ki taso na koyar da ke saƙar hannu” duk a rikice take,ni kuwa na zuba mata ido.Lokacin baya babu yadda ban yi da ita kan takoya min saƙar hannu ba ta ƙiya,amma yau sai gashi yau take son koyar da ni.


Fuskata na wanke,na gyara zama ta fara nuna min yadda ake fara aza zaren farko na Foundation ɗin sannan a fara zarga wa gabanin ta miƙo min ƙarafan saƙar.
Abu guda ya ban mamaki yadda na iya tafiya da takun saƙar kamar wacce tun can farko na taɓa koyon ta ,Momah na daga gefe ta ƙure ni da ido .Ko shakka babu ta zurfa sosai cikin tunani duba da yadda na yi mata magana sam ba ta ji ba.Ganin haka yasa na je na fara cika bokiti da ruwa,“oh! Har kin gaji?” na tsinkayo muryarta, murmushi kawai na sakar mata bisanin na ɗauki bokitin ruwan.
Ina kai soso fuskata na ji wani irin uban raɗaɗi tamkar na zuba barkono ,da sauri na wanke na fito direct ɗaki na shiga na ɗauki madubi.Ɗigon ja na gani a goshina mai ɗauke da wani ƙaramin tauraro.Shiru na yi ina daɗa kallonsa,“Momah???” na ƙwala kiranta ,ta na shigo wa na ce,
“Dubi wannan abun mine ne? Zafi yake min”
Cike da kula wa ta ce min “ki jira har ranar da kika cika shekaru ashirin da biyu duk zan yi miki bayani”
Na turo baki gaba na ce “ni dai ki faɗa min yanzu”
“Ke ban fa son sakarci ,wai haihuwata ma kika yi da za ki tsare ni da tambayoyi ? To ban sani ba” ta na gama faɗa ta shige ƙurya ɗaki.

Yadda na matsa wa kaina sanin mine ne har Allah yasa na tuna da mafarkin da na yi,wato na masoyin ɓoye.Har ban san lokacin da na saki murmushi ba,cike da nishaɗi na shirya cikin riga da wando na fita ƙofar gida.



FATIMAH

Tun lokacin da ta ci abincin da Mansur ya saya masu a restaurant take jin wani mugun sauyi a jikinta.Tamkar wacce ba da lafiya haka ta samu wuri ta kwanta,wani irin tsoro da shakkar saurayin ƙawarta take ji ba tare da ta san dalili ba.Ummarta har tambayarta ta yi abin da ke damunta amma ta ce babu komai.Ta rufe kanta cikin ɗaki kawai ,domin wani irin son kaɗaici ne ya zo mata.Wayarta ta ɗauka ta tura ma Nasir saurayin ta text ,duk da ba ta son shi haka ta ji ra'ayin kula shi.Da wannan ta ɗan rage faɗuwar gaban da take ji,har ta samu ta ɗan saki jiki.

A can ɓangaren A'ishah kuwa haka ta kira Mansur ta shaida masa ta yi ta kiran Ayodele amma ba ta ɗauka ba.Har ƙasan ransa ya ji mugun daɗi don dama ya na tabbacin fatalen da ke kan hanya kawai sun isa su kasheta da tsoro.


Washegari
A asibiti duk muka haɗu,ko kaɗan ban yi ma A'ishah maganar kiranta da ban ɗauka ba hasali ma ban so wata doguwar hira ta haɗa mu.
Ina ƙoƙarin saka wa wata mata tiyon fitsari A'ishah ta matso kusa da ni,ta ce “jiya Mansur na tambayar ki” sai na yi shiru kamar ban ji ta ba,ta sake maimaita min sai na ce “ki jira har mu fita mana,ki duba sauran patients ko akwai wanda ba a yi masa aiki ba ” na yi tunanin na rabu da ita kenan amma mu na fito wa ta sake tara ta da zancen “jiya sai da ya tambaye ni ,sam bai ji daɗi da bai baki kuɗin taxi ba”
Na ce “ba komai ana tare,ki tuna min don Allah zan baki kuɗin anko sai ki sayo min”
“Ok to babu matsala,amma Mansur ya ce min abokansa sun shirya party kin ga ya zama dole a sake fitar da wata ankon ”
“ A'ishah yanzu fa babu kuɗi ba lallai kowa ya iya sayen har anko biyu ba”
“Zan yi masa magana to,ƙila su abokan su saya maku”
“Hum!” kawai na yi,bisanin na ce “wai ita Fatimah ba za ta zo ta kama aiki ba ne?”
“Kanta ke ciwo ta na can baya wurin ƙofar emergency ”

Da sauri na kewaya ta bayan na sameta a kwance kamar ba likita ba.“Fatimah?” na kira sunanta,ta buɗe ido dakyar ta dube ni ai ban san lokacin da na yi zaune ba na ɗauko kanta na ɗora a cinyata.
“Mine ne taƙamaimai abin da ke damun ki?”
Murya na ɗan sarƙe wa ta ce “ A'ishah ce sai hirar mijin da za ta aura take yi min,ni kuma wallahi mugun tsoronsa nake ji.Ban so ko kaɗan ana kiran sunansa” shiru na yi na ɗan wani lokaci bisanin na ce “yaushe kika fara jin tsoron nasa?”
“Jiya”
“Bayan kun dawo daga restaurant ko kuma kafin mu je?”
“Bayan mun dawo” ta ban amsa ta na wani irin tari,na lumshe ido ‘ tabbas zargina ya zama gaskiya.Saurayin A'ishah ba mutumen kirki ba ne,to amma wace iri ce ɓoyayyar fuskarsa? Ban sani ba!’ na faɗa a zuci tare kuma da tunanin mafita.


Can dubara ta faɗo min na ce “Fatimah a Addinin ku ba a sanar da ku yadda ake karye asiri ba?”
“Mi ya kawo zancen Addini kuma?” cewar Fatimah don na santa sarai,ba tun yau take guje duk hirar da za ta kawo banbancin Addinai ba.
“Ke dai ki ban amsa” na sake faɗa,ta ce “eh an sanar da mu mana,gaba ɗaya Alkur'ani waraka ce akan dukkan ko wace matsala”
Ta na gama faɗa min na ce “ok jira ni” sai na sauke kanta kamar yadda na tarar da shi tun farko bisanin na koma can ciki.Direct office ɗin Dr Haleema na nufa,mace ce mai matsayi babba sannan ma'abociyar Addini ga ta kuma da sauƙin kai ba ta hantarar na ƙasa da ita.
A zaune na tarar da ita ta na duba wasu takardu ,da murmushi ta dube ni ta na mai cewa “Ayodele dama ke ce ke buga ƙofa? To zauna”
Na zauna tare da gaisheta bayan ta amsa na ce “Dr don Allah a Musulunce wane abu ne ina nufin addu'a ko kuma magani wanda yake saurin kare asirin da mutum ya ci”
Cike da kulawa ta ce “sanamaki! Ganye ne mai matuƙar amfani wurin kare tasirin asirin da mutum ya ci ,in an tafasa shi sai a yi addu'a cikinsa a sha”
“A ina zan same shi don Allah?”
“Wurin masu sayar da ganye ko kuma Islamique center,mike damun ki Ayodele?”
“Babu komai Dr na gode,jira ina dawo wa”

Ina fito wa daga office ɗinta na je na shiga ɗakinmu inda na aje jakkata,kuɗi na ɗauko sannan na fita bakin hanya.Na samu mai taxi na yi masa bayanin inda zai kai ni,wata cibiyar sayar da maganin musulunci ya kai ni.A can na sayo sanamiki mai kantin ya haɗo min da zuma,sannan na dawo asibiti.
Tun daga nesa nake hangen Dr Jaleel ya na masifa,ina zuwa ya ce “daga ina kike? Wa ya baki izinin fita?”
“Ka yi haƙuri matsala ce ta ujila ” na furta ina mai sunne kai domin yin ladabi.
“Su majinyatan da kika bari fa? In wata matsala ta faru ki sani a bakin aikin ki” nan ya shiga yin min masifa kamar wata ƴarsa kafin yayi gaba.
Office ɗin Dr Haleema na sake komawa na nuna mata ,“Ayodele ki faɗa min abin da ke faruwa mana sannan ba ko wane lokaci ba fa ake shansa”
“Dr Fatimah ce babu lafiya,kuma na tabbata sihiri ne ke ɗawainiya da ita ki taimaka min ki yi min addu'o'in ciki na bata ta sha don ta galabaita sosai” shiru ta yi,bisanin kuma ta ɗauko moɗar ƙarfe wacce take dafa Lipton a ciki, da ita ta yi amfani wurin tafasa Sanamakin bayan nan ta zuba zuma ta shiga yin karatu ciki.Na yi mata godiya na karɓa,inda na bar Fatimah nan na same ta.Dakyar ta iya tashi zaune ta yi Bismillah ta sha,a nan take zufa ta karye mata.Sai ta fara sauke ajiyar zuciya bisanin ta ce “Ayodele cikina na murɗawa toilet zan shiga ” da sauri ta miƙe,na take mata baya har muka isa banɗakin da aka tanada don likitoci.


A wannan wunin tun ina ƙirga adadin da Fatimah ta kewaya har lissafi ya ɓace min, zawayi kawai take mai ɗan uban wari don ko ni da ke tsaye bakin toilet ɗin ina jin warinsa.A ƙarshe dai har ni sai da na shiga toilet ɗin don ta galabaita sosai,idonta tuni sun faɗa ta yi zuru.Ganin an ɗauki sama da minti ashirin ba ta samu wata murɗawar cikin ba,na taimaka mata ta yi wanka sannan mu ka fito.A ɗakinmu ta kwanta,sai a lokacin A'ishah ta san da ciwon yayi tsanani.Ƙarin ruwa na saka mata,bayan ta sha lemu exotic baiwar Allah sai bacci.

A'isha ta tsaya tare da ita ni kuma na fita na hau aiki don kusan ban yi komai ba.Sai ƙarfe tara na dare na nufi ɗakinmu,duk bacci suke.Na taɓa wuyan Fatimah na ji babu zazzaɓi ,na je na haye gado sai bacci.

“Yaanhun! Uhun ! Uhun!” shashekar kuka ta tashe ni daga bacci,na lalubo wayata na duba.Ƙarfe biyu ta gota,na ja tsuki tare da fita na nufi MUTUWARE don tuni ruhina ya lamunta da lamarin da ke faruwa da ni.
Ɓangaren mata na shiga inda ake aje gawa,kwaɗon kawai na taɓa ya buɗe kansa na ja ƙofar na shiga sanyi AC ya ratsa ni sosai bisanin na yi tozali da wata sabuwar gawa don ko wanka ba yi mata ba.Mu na haɗa ido da ita ta bar kukan,a gajiye nake hakan yasa nake jin haushin tashe ni daga baccin da ta yi.
“Sai ki tashi ki faɗa min abin da yasa kika jawo ni izuwa nan” na faɗa ina waige-waige don neman wurin da zan zauna,sai dai ban farga ba na ji wani hannu ya jawo ni da mugun ƙarfi na yi baya tare da faɗa wa cikin akwatin mutuwa.....




My book is only 500 duk mai son biyan kuɗin karatunta za ta iya tuntuɓata kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 sai na bata account ɗin da za ta saka kuɗin.
[31/10 à 11:05] MRS SADAUKI 💫: *MUTUWARE ...*🧟‍♀️
GIDAN GAWA🧞‍♀️🌬️

Love
and
Horror story

```MRS SADAUKI💫✍🏻```

Dedicted to Ameera Adam


FCWA ☀️

_________________________


*Promo:* mai ra'ayi zai iya biyan 400 kafin na gama free page a maimakon 500,wacce ta shirya biyan kuɗin karatunta za ta iya min magana kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 sai na bata account ɗin da za ta tura na gode!


Page 6


Kiciniyar fita daga cikin akwatin gawar na fara sai dai ga mamakina wata gawar na gani a tsaye kan ƙafafunta ta na ƙoƙarin danna ni ciki.Da dukkan alamu akwatinta ne,cikin wata irin murya ta maso duniya take cewa “ki zauna madadina don Allah na ga ke lamarin duniya bai sha maki kai ba,ban shirya zuwa can mazaunar fatale da ruhika ba”
Idona na ware sosai kan matar, datijuwa ce a ƙalla ta kai shekara hamsin da ɗoriya fara ce tasss sai tsagen fuskarta na kurmawanci da ya fito raɗo-raɗo.
Tabon goshina ne na fara jin ya na motsi,kamar almara sai gani na fito daga cikin akwatin na tsaya kan ƙafafuna.
Gawa ta fashe da kuka,cikin tsawa na ce “je ki koma makwancin ki,wato lokacin da malamai ke yi muku wa'azi kar ku biye ma ruɗin duniya ku na yawon dare amma kuka yi kunnen uwar shegu da su kuke fita cikin dare farautar bayin Allah.Yanzu kuma da zanzaro ya tonon gidan Rina gari ya kwaɓe miki za ki neman ki dawo duniyarmu?”
Idonta na zubar da hawaye ta shiga akwati ta kwanta wani haske ya fita daga goshina ya daketa tsit kake ji har esprit ɗin nata ya bar motsi,na maido dubana ga ɗayar wacce ke shashekar kuka na zuba mata Mayun idona masu masifar kaifi na ce “ ke kuma ina jin ki”
Cikin kuka ta fara yi min bayani “wannan da kike gani mahaifiyata ce,ta ja ni izuwa wani ƙauye ne don yin shagali ita da ƙawayenta a can suka nemi da ta bada jinina su sha da ta ƙiya ne hanyarmu ta dawowa mu ka yi hatsari.Kin ga ban mutu ba sun ɗaure ni da azargagi ne,shirinsu shi ne in an kai ni maƙabarta su je su haƙo ni su tsotsen jini”
A ɗan takaitaccen bayaninta na fahimci mahaifiyarta ta na cikin wata ƙungiyar Mayu ce masu shan jini,sannan duk shekara su na gudanar da bikin ƙara danƙon zumunci inda a dole wata za ta bayar da kyautar jini daga cikin ahalinta,kamar ɗa,jika ko ƙane.

Kallon tsaf na yi mata,sai yanzu na lura da goshinta da gefen bakinta duk a fashe suke alamun buguwa.Tunani na fara ta inda zan taimakonta,sai dai na kasa samun mafita don ban san fuskokin masu son kaita ƙasa ba.
“Ki taimaka min kar ki bari a kai ni maƙabarta da raina ban mutu ba sun juyar da hankulan mutane ne kawai ake min kallon gawa ” muryarta ta katse min tunani.
Na ja dogon numfashi bisanin na ce “ki na ji na,a halin yanzu banda mafita amma na yi miki alƙawari zan cece ki ko bayan an haƙa miki kabari ne an saka ki ci to zan zo gare ki”

Fararen idonta ta zuba min uwanda sam ba su da ɗigon baƙin ciki,na jinjina mata kai alamar tabbatar wa kan ƙudirina.Ban sani ba ko ta yarda da ni ɗari bisa ɗari,amma a sannu na ga ruhinta da ke dabaibaye da wasu Kambu ya ɗan samu salama.
Sai da na shafi fuskarta bisanin na fito,direct ɗakinmu na wuce sai na tarar da Fatimah a zaune.

“Kin tashi? Ya jikin naki?” na tambayeta.
“Da sauƙi alhamdullah! Na gode sosai Ayodele,haƙiƙa ke ƴar baiwa ce.Da ace musulma ce ke da tabbas ba ƙaramin gudumuwa za ki bayar ba”
Na sakar mata murmushi na ce “duk Ubangiji muke bauta ! Banbanci kaɗan ne,sannan shi ke tsara komai iyakacinmu mu yi aiki da baiwar da ya bamu amma komai daga Ubangiji yake”
“Zance na hikima! Anya kuwa ruhinki ba na Musulunci ba ne gangar jikin kaɗai ke ta Yahudawa?” Fatimah ta faɗa,dariya na yi na canza zancen “ai yanzu dai kin bar jin tsoron komai ko?”
Ta ja tsuki tare da cewa “shi ɗin banza Allah na tsane shi ,amma yanzu ban ji shakkar shi .Wai daga ina kike ko an kawo sabbin patients ?”

Na ja ajiyar zuciya domin tambayarta sai ta tuna min da danbarwar da na baro a can MUTUWARE.“Ki koma ki kwanta don kin galabaita sosai ,ni ma baccin nake ji akwai aikin da nake son yi cikin bacci” na faɗa tare da kwanta wa kan gado,Fatimah ta waro ido bisanin ta ce “kin san kuwa a jiya ne ko yaushe da kika yi bacci gidansu A'ishah wallahi sai da kika bani tsoro don ba zan ɓoye miki ba shi ne dalilin da yasa na sulala zuwa gida”
Na lumshe ido ba tare da na bai wa abin da take faɗa muhimmanci

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment