Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[18/04 17:55] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦




💦Hajarat M Bash💦




Assalam Alaikum godiya da dukkan yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bani ikon fara wannan littafi kuma cikin ikon sa da isan sa ina rokan sa da ya bani daman kammalawa lafiya, Amin....


Bismillahir Rahmanir Rahim....



💦1-5💦


Kwance yake kan dogon kujeran kayataccen palon yayi matashi da hannayen sa dukka biyu,

Idanun sa lumshe kai kace bacci yake a zahiri amma idon sa biyu yana sauraran duk wani motsi dake cikin gidan ga tunanin da yayi masa kane kane ya hana sa rawan gaban hantsi, a kullum ya kwanta ko idan yana gida ran weekend da yake ya kasance mutum mara yawo da son hayaniya to bashi da aiki da ya wuce tunanin halin da gidan sa ke ciki, Tunani ne guda daya tak da ya harde masa rayuwa sannan ya rasa ta yanda zaiyi ya gyara, ba wani tunani bane face halin matar sa UMMU RUMANA!


Kana ganin sa tun daga fatar jikin sa zuwa ga kalar fatan jikin sa wanda ba fari ba haka kuma ba baki ba, ga wani suma da ya kwanta luf a kansa yana yalki, kai da ka gani kasan hutu ya ratsa ko ina a rayuwar sa, kyakkyawa ne ajin farko, miskili ne sosai wanda har mutane ke ganin yana da girman kai sannan shi mutum ne wanda bakagane hakikanin inda yasa gaba, fukarsa bata tantance ko yana farinciki ko kishiyarsa.....

kwasss! Kwasss! Kwasss! Yake jiyo takun takalman ta tana saukowa daga stairs, wani dan gajeren tsaki ya ja cikin ransa yace

"Na tsani wannan dabi'a ta yahudawa da RUMANA keyi ina ma laifin ta sanya sofa mara kara tunda ya zama kamar dole sai tayi yawo da takalmi a cikin gida...

Saukowa take a hankali tana taunar chewing gum yana fidda karan kas kas, da ka ganta kasan mace ce mai aji irin first class din nan, fara ce irin mai daukan idanu, kayan dake jikin ta kawai ya isa ka gane cewa yar gayu ce da kuma tsadan su, tayi kwalliya iya kwalliya tamkar mai zuwa gasar kwalliya.

Kamshin turaren ta shi ya daki hancin sa wanda ya tabbatar ta karaso kusa dashi, bai gama tunanin ba yaji ta zauna a kan kujeran da yake kwance kusa da kafafun sa duk da haka bai motsa ba hasali ma bai nuna mutum ya zauna kusa dashi ba...

Sarai ta san idon sa biyu dan tasan halin gogan nata, a haka dai ta danne zuciyan ta domin ita tazo nema don haka ya zama dole ta jure walaqancin sa a cewarta da kuma duk wani ji da kanta.

Tabe bakin ta tayi ta kalle shi gabadaya sannan ta yamutsa fuska tare da yin kwafa wanda ya tsaya iyakacin leben ta tare da yin farr da idanu tana tunanin ta inda zata fara...

abinda bata sani ba shine tun zuwan ta da zamanta duk yana kallanta ta kasan idonsa, murmushi yayi cikin ransa yace bari yaji yau kuma da wacce tazo dan yasan tabbas wani abu take nema da babu abinda zai kawota kusa dashi a wannan lokaci da tafi bawa chatting da kwayenta muhimmanci.

"Daddyn twins" ta fada cikin murya mai jan hankalin mai sauraro sai dai kash wanda akeyi domin sa ko gezau, "daddyn twins" ta sake maimaitawa tare da jan babban yatsan kafar sa cikin wani salon jan hankali
"Please ka tashi muyi wata shawara nasan kana jina shariyace kurum kaji? Ta karashe cikin muryan shagwaba

"Uhmm" kawai ya iya cewa dan takaici

" Habibi Ka tashi mana dan Allah"

Takaici ne ya kama shi wai RUMANA bata san tattala miji ba, bata san damuwar sa ba, bata in and out din sa ba sai tana neman wani abu sannan zaiji sunan masoya iri iri...

"Idan baza ki fadi maganan ba please you kindly work out "

Ganin zai lalata mata zuciya kuma ga ba biyan bukata tayi saurin gyara murya tana wasa da yatsun kafar sa ta fara magana cikin sanyin murya kamar ta Allah

"Dama nace batun zuwana Dubai saro kayan ne, wlh idan nayi order bana ganin abinda nayi tsammani sai nake ganin kamar yafi naje da kaina ko?

Bai kulata kuma bata damu ba tunda tasan yana jinta ta cigaba

"Yanzu ma wasu sabbin kaya ne suka fito shine nace gwara naje da kaina saboda na zabo qualitative ones ko?

Daga nan ta dakata tana jiran taji mai zai ce tana addu'an Allah yasa ya yadda

"Habibi kayi shiru baka ce komai ba please"

Idanun sa masu rikitarwa da sanya mara jin magana nutsuwa ya bude ya zuba su akanta, baza ta iya jure wannan kallon ba tayi azaman dauke nata idon zuciyarta na bugawa.

Tamkar baya son magana ya fara "wato RUMANA kin raina ni ko, wallahil azim har yanzu baki san true color na ba amma if you really wanna know who is JUNAID B ARAB ki sake kawo min makamanciyan wannan magana, yana gama maganan ya mike cikin tafiyar sa ta kasaita da ko kaki Allah sai ya birge ka ya nufi dakin sa.....

Da wani mugun harara tabi bayan sa tare da jan dan karamin tsaki amma ita kadai ta jiyo kayan ta saboda duk iskancin ta tana shakkar sa, a fili tace

"Namiji har namiji, mutum har mutum, class iya class, kana ganin sa zakayi tunanin wayeyye ne amma ba fuss, kai Allah wadaran zuciyata da tayi tunanin JUNAID shine Mr right dina har take jin rayuwa babu shi is useless, wani gajeran ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta jikin kujeran da take kai tana tunanin mafita da kuma wannan miji nata mai ra'ayin rikau.....




08038231353 for comment and please share to other groups
[18/04 17:55] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦





💦HAJARAT M BASH💦



💦6-10💦



💦Allah ya sada mu da dukkan alkhairan da suke a kowace rana..... 💦



Yau asabar an wayi gari sai shirye shirye ake babu kama hannun yaro a gidan Alhaji YUSUF JAJERE wanda akeyi dan tarban tilon dan su daya namiji ALIYU YUSUF JAJERE, shi kadai ne da namiji sai kannen sa mata hudu, duk irin gatan da suke nuna masa bai sanya yayi watsi da tarbiyan sa ba....

Aliyu matashi ne mai kimanin shekaru ashirin da takwas a duniya, dan gaye ne sosai mai ji da kansa saboda akwai naira, gata sannan uwa uba kyau wanda ya samo asali daga wajen uwa da uba wanda suke fulanin usul......

ALIYU ya kasance mutum mai son raha, zolaya da barkwanci, shi kowa ma abokin wasan sa ne sai dai akwai zuciya bashi da dadi idan ka tabo sa, halin sa da yafi birge kowa shine baya kula mata duk da irin hadaddun matan da suke kawo kansu wajen sa amma ko tayawa baya yi hasali ma shi bai taba soayayya ba a ganin sa duk bata lokaci be.....


****************************

Aiki nake a kitchen cikin nutsuwa da sanyi tunani fal cikin raina
"Yau dai zanga wannan yaya aliyun da kowa ke rubibin ganin sa kuma ake dokin ganin sa, kowa ka taba a gidan nan to labarin dawowan yaya Aliyu yake wanda ya debe shekaru bakwai bai leko kasar sa ta haihuwa ba inda ya tafi karatun likitaci ta bangaren mata wato gynecologist. Kowa ka taba a gidan hiran dawowan yaya Aliyu zaiyi maka, duk da lokaci zuwa lokaci suna yawan waya ko video call amma koda wasa bamu taba gaisawa ba haka su aysha zasuyi ta nacin mu gaisa amma naki domin ni a ganina shishigi ne sannan kuma ina gudun walaqanci duk da ma na shaidi yaran mami ba haka suke ba, a photo kam na gansa kuma lallai na yadda dasu Aysha da suka kaf gidan yafi kowa kyau sannan kuma diban yanayi da UNCLE JUNAID.....

Ajiyar zuciya na sauke ina cigaba da dauraye warmers Baba kuma na wankewa

Ban gama tunanin ba na juyo muryan mami tana kwalo min kira

"DEENA! DEENA!
Da sauri na ajiye warmer dake hannuna na nufi hanyar fita a kitchen inda muka ci karo da mamin zata shigo kitchen din, murmushi ta sake tare da dafa kafaduna da yake mami wato HAJIYA ZAINAB mace mai son mutane, babu ruwanta da kyamar talaka ga faram faram da kyauta mahaifiyar Aliyu kenan tace

"Yauwa sannu DEENA kiyi maza kije ki shirya karfe biyar jirgin su zai sauka kinga su Aysha ma sun shirya wato kannen ALIYUN, maza yi sauri muna jiran ki" ta juya zuwa palo

Ba yadda na iya ne amma da bazan bisu dauko sa ba saboda na tsani shiga waje da mutane, haka jiki a sanyaye na fita daga cikin gidan na nufi boys quarters inda anan muke zaune a gidan nida mahaifa na,
Da sallama na shiga palon na tadda babu kowa sai na nufi dakina nayi wanka da sauri ina fitowa mai kurum na shafa na bude wardrobe na ciro doguwar bakar riga da dan kwalinsa na zura na sanya flat shoe baki a kafafuna sannan dauko turare na fesa dama ni ba ma'abociyar son kwalliya bace....

Na fito palo na tadda Ammina ta fito daga dakin ta ta kalle ni cike da kulawa "ina zuwa haka ko tare zaku je filin jirgin?

Ban kai ga bata amsa ba na jiyo odar mota daga waje alaman dai dani akeyi, da sauri na nufi kofar fita nace Ammina sai mun dawo sannan na fice da sauri gudun kar na bata musu lokacin.

A farfajiyar gidan naga motoci uku na rasa wanne zan shiga ma kafin na karasa aka bude kofar motan tsakiya, mami ce ta leko tace
"DEENA shigo nan"

Zan bude baya tace na shiga gaba na zauna, haka dai ba yadda na iya na bude na shiga na zauna tare da rufe marufin motan....

Wanin daddadan kamshin turare mai sanyin dadi ne ya ziyarci hanci tare da bugun zuciya ganin ko waye ke jan motan domin duk a tunani na daya daga cikin drivers din gidan ne ashe Uncle JUNAID ne wanda yake kani ne a wajen mami...

Cikin hardewan murya da rawarn baki na furta
"Ina wuni uncle J" yanda yaran mamin ke kiran sa

Bai ko kalle ni ba yace "lafiya" a takaice

Nima na ja bakina nayi shiru tare da dauke kaina zuwa ga window..

hira suka dingayi shida mami wanda kusan rabin hiran mami ce keyi har muka isa airport, ai da hanzari na bude motan na fice na isa wajen su aysha, islam, mufida da yar karamar su nana wacce bata wuce shekara tara ba, islam ce ta rungumo tana cewa

"Shine kika shige motan Uncle J ko ai kuwa kin bar hira saboda uncle OMAR(shima kani wajen mami) ne ya kawo mu ana hira da dariya"
Aysha ce tace "ai mun tausaya miki da muka ga motan da kika shiga" ta karashe mgn tana dariya irin ta muguntan nan

Ban kula su ba sai murmushi da nake yi, matafiya sun fara saukowa, kowa sai wulla ido yake yaga fitowar yaya Aliyu....

Saukowa yake a hankali jikin sa sanye da kananan kaya fuskar sa toshe da sun glass, gashin kan nan sai yalki yakeyi, da ka gansa kasan hutu ya samu waje, kai kace hutawa ya tafi ba karatu ba.....

Islam ce tayi dan kara mai hade da dariya tace

"Yeee ga shi can ga yaya Alinmu"

Ai kuwa kowa ya hango shi sai faman dariya suke suna ji kamar suyi tsuntsu su kamo shi
Ni kuwa tsam na tsaya ina kare masa kallo sannan baka iya tantance halin da nake ciki farinciki ko akasin sa...

Aysha ce ta dan zungure ni da kafadanta tace

"How do you see our handsome brother "

Murmushi nayi na furta "masha Allah " dan ko hasidin bai isa ya kushe shi ba....
A haka ya karaso ya rungume mami irin missing hug din nan sannan ya rugume sisters din sa a dai dai lokacin da idanunsa suka sauka cikin nawa, nayi maza na janye nawa idanun ina mai jin wata faduwar gaba da ban san ta macece ba

A haka yaje ya rungume uncles dinsa amma still idanun sa na kaina

Kayan sa aka sanya cikin buth sannan aka debi hanyar komawa....

Mota daya muka shiga dashi amma wannan karon ina baya kusa da mami shi kuma yana gaba shida Uncle J suna hira amma dukkan hankalin sa da kallon sa yana kaina

Duka nabi na takura na rasa inda zan tsoma raina domin na tsira daga wannan mayataccen kallon da yake min ta madubin gaban motan, wata shawara zuciyata ta bani na kuwa yi amfani dashi inda na janyo mayafina na rufe fuskata tare sa kwantar da kaina baya jikin kujera....

Shi kuwa bangaren Yaya Aliyu ji yayi kamar ya janye mayafin fuskar tawa domin ji yake koda kwana zaiyi bazai gaji da kallona ba...

A zuciyansa yake tambayan "a ina mama ta soma wannan good innocent looking din? Tunda yake bai taba kallon mace sau uku balle ace har ya zuba mata na tsawon wasu mintina ba har kuma yaji baya son ya daina kallon nata ba sai wannan baiwar Allahn"

Mami ce ta juyo ta kalleni tace

"DEENA sarkin bacci, a motan ma baccin zakiyi ko?

Yamutsa fuska nayi kadan nace "mami kaina ke min ciwo ne"

"Ayya sannu mamana, ai kun sha aiki ne yau, bari muna zuwa gida kisha magani sai ki kwanta ki huta ko"

Toh na furta a hankali......





08038231353 for comment and please share to other groups
[18/04 17:55] W Hajara MB: 💦KWARYA TA GARI💦





💦HAJARAT M BASH💦




💦11-15💦




Muna shiga gidan akayi parking kowa ya fara fitowa cikin farinciki, main palon aka shiga baki daya aka zauna kowa na fadin albarkacin bakin sa kan yaya Aliyu shi kuwa sai dariya yake idanun sa sai yawo suke akaina, duk na rasa samun nutsuwa da sukuni wallahi

Sisters din sa duk suna makale a gefen sa suna zuba masa surutu shi kuma sai biye musu yake yi kasancewar sa mutum mai son wasa da dariya ne...

Ni kuma sai binsu nake da kallo ina taya su murmushi suna mai birge ni...

Aysha ce ta kalle ni tace
" DEENA ba na gaya miki yaya Aliyun mu yafi kowa kyau a gidan nan ba? to ya kika gansa" ta karashe maganan tana dariya

Rankwashi yaya Aliyun ya sake mata a kai yace "sarkin surutu har yanzu baki canja ba?

Turo baki tayi gaba tace
"Dan ka samu na yabe ka ma, toh na fasa Uncle J yafi kowa kyau duk family"

Dariya kowa yayi banda uncle J da ya galla mata harara tare da mikewa ya dubi mami yace

"Anty ni zan wuce gida"

"Har tafiya JUNAID? Ka bari kaci abinci mana ba yan aiki bane sukayi fa yan mata na ne sukayi"

Guntun tsaki ya ja yace

"Toh ba gwara Yan aikin ba da jagwalgwalon wadan nan ba" ya fada yana kallon su daya bayan daya

Babu wanda ya samu daman magana sabida baya wasa dasu amma da uncle Omar ne da sun fara magana son ransu

Dariya mami tayi tace
"A a wlh duk sun iya girki ba laifi"

Maida kallon sa yayi kan Aliyu yace "kai kuma sai kaje gida mu gaisa da kyau ko? Ya karashe maganan tare da nufan kofan fita

Uncle Omar ne yace jira ni mana mu fita gabadaya akwai inda zan wuce

Kowa yabi su da Allah ya kiyaye hanya Aliyu kuma yabi bayan su da dan yi masu rakiya

Wajen mami na nufa nace mata zanje nasha magani na kwanta daga nan na juya na nufi boys quarter, ina tafe ina tunanin hali irin uncle J sam sam mutum bashi da fuska kullum kamar an aiko masa da sakon mutuwa, yau ranan farincikin ma kamar baya farinciki, shi kam halin sa sai shi, ni kam tsoron shi ma nake ji....

A haka har na iso bangaren mu inda mukayi kichibus da Ammina zata shiga wajen mami

"Har kun dawo?
" mun dawo Ammi"

"Nima yanzu zan shiga naga Aliyun mami

Dariya nayi nace yana nan kam nima yau dai na gan sa" na fada tare da karasawa cikin gidan ammi kuma ta nufi side din su mami....

Bangaren Aliyu kuwa yana dawo daga rakiyan su Uncle J ya dawo palo ya kalli Mami yace

"Mamina bari nayi wanka na huta sai zuwa anjima kafin nan ma Abba ya dawo"

"Toh shikenan a huta gajiya ko, sai ka fito"

Har zai wuce sai ya faki idon kowa ya kamo hannun Aysha ya ja ta zuwa can side din sa

Ita dai sai kallon ikon Allah take ta kasa magana shima Aliyun bai ce mata komai har suka karasa side dinsa suka shiga palo sannan ya cika mata hannu ya tura kofan yana karewa dakin nasa da yasha gyara sai tashin kamshi yake, a hankali ya karasa kan sofan dake palon ya zauna tare da sauke sassanyan ajiyar zuciya

Sai a sannan Aysha itama ta sauke ajiyan zuciya tare da karasawa kusa da Yaya Aliyu tace

"Yaya Aliyu lafiya kuwa? Ka tsorata ni fa"

Murmushi yayi ya gyara zaman shi da kyau yace

"Sis tambayen ki zanyi pls"

Harde hannayen ta tayi a kirjin ta tace

"Oh yaya Aliyu yanzu tambaya ce shine har sai ka janyo ni nan"

"Ai sirri ne bani son yan gulman can suji, yana nufin su mufida da islam.. zauna dai muyi magana kinji tawan"
Ya fada tare da janyo hannun ta ya zaunar da ita kan kujeran dake gefen sa yana murmushi

Itama murmushin tayi tace
"Alright i'm all ears"

Sassauta murya yayi tare da yin fuskan tausayi yana kallon yar uwar tashi kuma abokiyar shawaran shi ya furta

"Sister i fell in love, LOVE AT FIRST SIGHT! tell me what to do please "

Da mamaki Aysha ta kalle shi tace
"Love? With who?

Kwantar da kansa yayi jikin kujeran yana lumshe ido a hankali ya

"DEENA!

wani ihu Aysha tayi har sai da ya tsorata yana kallonta sai yaga sai dariya take fuskanta na bayyana tsantsan farincikin da take, shima sai ya tsincin kansa cikin farincikin

"Kai yaya Aliyu amma naji dadi sosai, kayi iya zabe wallahi kuma akayi dace dama DEENA bata kula kowa, ga hankali da tarbiya ga uwa uba kyau ai kai kam yaya Aliyu ka iya zabe, bari ma naje na gaya mata" ta fada tana shirin mikewa zata fita

Da sauri yaya Aliyu ya kirata yace

"Ke uwar azarbabi ba yanzu ba ki bari so nake na shigar da kaina da kaina, ko so kike ta raina ni na kasa zuwa sai da nayi aike? Ki bari a hankali zan nuna mata ina sonta"

"Uhm uhm fa yaya Aliyu a bari ya huce shi ke kawo da rabon wani fa, kar tsaya kallon ruwa kwado yayi maka kafa

"Kar ki damu In sha Allahu DEENA tawace ni kadai"

"Allah yasa, nasan kowa zaiyi farinciki da wannan abun barin ma mami, kasan yanda take son DEENA kuwa?

"Hohoho sarkin surutu zaki fara ko?


Cinno baki tayi gaba a dole tayi fushi yace mata mai surutu

"Na shiga uku yi hakuri tawan kin san nida ke 5&6 ne ko? Yanzu bari nayi wanka na huta anjima zaki bani duk labarin gimbiyar tawa ko?

"Toh yaya Aliyu a huta gajiya tace tare da mikewa zata ta fita sai kuma ta juyo tace

"Yaya Aliyu banga tsaraban mu ba fa" ta karashe magana kamar mai shirin kuka....

"Hohoho sisi dadina dake rashin hakuri, to tsarabar ki ma dabance"

Wani tsalle tayi tana dariya sannan ta fice

Shi kuma furzar da iska yayi da karfi ya kwanta kansa jikin kujeran ya furta DEENA a hankali cikin wani salo da bai san ya iya ba, sai hasko fuskanta yake lokacin da suke airport har lokacin da suke cikin mota har izuwa lokacin da suke zaune a palo

Wani smile ya sake yana shafa sumar kansa, a ransa yace "LOVE AT FIRST SIGHT......



08038231353 for comment and pls share to other groups

💦KWARYA TA GARI💦




💦HAJARAT M BASH💦




💦16-20💦



Tsaye yake gaban tangamenen dressing mirror dake cikin kayataccen bedroom din sa yana feshe jikin sa da wani tsadadden body spray mai kamshin gaske wanda kamshin sa kawai zai tabbatar maka da tsadan sa....

JUNAID B ARAB ya kasance mutum mai son kamshi da tsafta sai dai kash baiyi dacen samun mata ma'abociyar tsafta ba, idan kaga RUMANA na kyalkyale jiki to fita zatayi ko kuma ana son wani abu gurin miji, ita dai RUMANA masu aiki ne ke yi mata komai, mace ce mai halin i don't care miji baya gabanta baya ga neman kudi babu abinda ta sanya a gaba balle kuma ta kula da yaranta da suke tsananin bukatan kulawar uwa, idan akace yau harka ce ta neman kudi to kuwa sam sam bata wasa dashi anan za tafi maida hankali.

JUNAID kuwa ma'abocin son rayuwa ne yana son yaga yana gudanar da rayuwan aure kamar wasu LAILA DA MAJNUN amma kaddara ta riga fata wadda ta hada shi da UMMU RUMANA.....

A hankali ya gama feshe jikin sa da spray din yana karewa kiran halittan da Allah yayi masa, wani guntun tsaki ya ja gami da ajiye spray din ya nufi wardrobe din sa ya ciro wani three quarter wando da armless riga duka farare kasancewar lahadi ne

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment