Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Arman Malamina ya gaya min cewa akwai wacce ya fad'a tarkon k'aunarta, kuma da alama akwai wani rabo mai zafi a tare da ita, Mlm ya ce dole mu bari ya aureta shine kawai zamu bari burinmu ya cika yadda muke so, dole saita shigo gidan nan tukun, zamu iya cin galaba akansa harma ita, a lokacin zamu sa masa tsananin k'aunarki zamu sa Mlm yasa masa kasalar Ibada ta yadda zamu ci galaba akansa da wuri, ke kuma zamu sa ki rink'a shige masa ta yadda zaki rink'a had'a husuma tsakaninsa da matarsa, komai a shirye muke, ita kad'ai muke jiran zuwanta cikin gidan nan"

Tashi tsaye Salma tayi sab'anin da, da take zaune kusa da Haj Shuwa

Ta ce "tabbas kuwa kun iya dabara, ni kuma sauran aikin ku barsa a hannu na Umma".




*SURURE, LOGAS NIGERIA*


"Wai mi kake cewa ne, Aliyu, na kasa fahimtarka Husainar ce aka nema ta aka rasa" Mimi ta k'are maganar had'e da tashi tsaye manne da waya a kunnanta

daga cikin wayar Aliyu muryarsa hankali a tashe ya ce "wallahi Mimi sai da na ce mata tahau jirgi idan zata tafi katsina tayi min gaddama. Mimi is privileged and pregnant, my mind is awake"

"Wai abunda ban gane ba, kai kana ina harka bari hakan ta faru, kasanfa katsina hanyar bata cika kyau ba, the kidnappers have attacked the town a lot"

"Mimi knows that, he talked to her since I told her to go and see home, ni kuma nabar mata komai na baro Abuja ina kwatano ni yanzu haka, munzo wani taro ne ashe ita kuma tasa direban gida ya kaita.I took my plane, she got on

"Insha Allah zata dawo lafiya, ka nemi wayarta ne?"
"Mimi tun d'azo nake neman layinta baya shiga. And they didn't get enough from morning to night, Mimi hankali ya kasa kwanciya kamar matata na cikin matsala hankali a mugun tashe yake wallahi"

Sauk'e lumfashi Mimi tayi tana k'ara kwantar mai da hankali, daga k'arshe ta ce "ina so karka sanar da danginta tukun muga mi Allah zaiyi, karmu tada masu hankali kasan Mahaifiyarta bata cika lafiya ba"
"Insha Allah Mimi, amma idan lokacin sanar dasu yayi dole su sani"

"Na sani Aliyu amma kabi komai a hankali tunda bamu tabbatar an sace tan ba, ni nafi ba ko dai motarce ta lalace masu kan hanya"

"Hakane Mimi"


Sallama suke Mimi ta dawo dubanta wajan Lalaah dake tsaye a kusa da ita, tana ta dumunta da cewa mi yake faruwa hankali a tashe itama.

Fitowarta kenan, da murnarta na ta fad'ama Mimin Doctor Arman ya turo mata kud'in zanenta kusan Million goma, ita da bata d'auka yawan kud'in zai kai haka ba, ta d'auka bai wuce a bata dubu d'ari ba. Sosai ta rud'e har sai da Arman d'in da kansa ya kirata, tayi mamakin kiran sa. Inda take ce mai kud'in sunyi yawa, ina zata kai su?, sai dai yayi mata murmushi ya ce ta bada sadaka idan ba abunda zatai dasu, daga nan yayita janta da fira, har lokaci yaja. Tayi mamakinsa matuk'a yadda lokaci guda ya sake da ita, har ya tsaya yana zuba mata surutu haka, wadda ji take kwata-kwata kamar ba doctor Arman data sani take jin labarinsa ba, take gani a gidajan Tv da redio, wai shine a cikin waya yake mata sauk'in kai haka, ta kasa gaskata abun. Ta sakko ne da murna domin ta sanarma Mimi ta iske wannan tashin hankali da Mimi take ciki, na Y'ay'ansu Aliyu da matarsa, wadda auransu bai wuce shekara biyu da yinsa ba, matar y'ar asalin garin Katsina ce, acan suka gamu wajan wani taron kasuwancin Abbie d'aya wakilta zuwa suka had'u da Husaina.

"Bari Lalaah muna cikin tashin hankali, why da Husaina baza ta hau jirgi ba?, tasan hatsarin hanyar dake garin su"

"Dan Allah Mimi ku kwantar da hankalin ku insha Allah Aunty Husaina tana nan cikin k'oshin lafiya, kawai isane basu yi da wuri ba"


Lilaah ce ta shigo parlon itama duk hankalinta ba'a kwance yake ba. Amma ita damuwarta daban take da taso, domin ita dama kullum damuwarta bai wuce ta Arman ba. Ganin su haka yasa ta d'an tsaya kamar abun arzik'i ta ce "Mimi mi yake faruwa ne haka, na ganku haka"

"Hmm Aunty Husaina ce ta d'auki hanyar katsina daga Abuja gidanta, shine har yanzu bata isa ba, kuma wayarta ita da drivern bata shiga har yanzu kuma tun safe suka d'auki hanya, amma Kinga yanzu har tara na dare shuru basu isa ba. Can gidan nasu ma hankalinsu ya fara tashi soma, danma Y Aliyu na b'oye masu wani abun"

D'an jim Lilaah tayi kamar wacce zata ce abun arzik'i sai kuma ta ce "ai kaji matsalar d'an k'auye wallahi, ai shine yaji ya gani, Allah ya bayyana ta"

Ta na idasa fad'ar haka tayi sama abunta.

Mimi cike da takaici zata mata magana Lalaah ta girgiza mata kai, alamar tayi hakuri.

Lilaah kuwa gani take ai ita wannan ba damuwarta bane. Shi Aliyun shita shafa, gashi dama haushinsa take ji yaje ya auro masu y'ar k'auye taso ya auri Bilkees k'awarta.........
*K'ADDARAR SO*
(Destiny Of Love)




*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝
Share Fisbilillahi





*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*



Chapter 7


*FUNTUWA LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA*


Tsaye take tana dakan surfen wake. Da gudu Inna Saude ta fito daga d'aki, d'an dakatawa tayi tana duban Maryam dake surfe.

"Kan uban nan kayyasa, ke ina kud'i na dana aje a cikin d'aki jiya?, na duba ban gansu ba, kuma ke ce kad'ai kika ga inda na aje su, na rantse da sarkin da ke butsan lumfashi idan baki fiddo min da kud'i na ba, sai nayi miki bugun mutuwa wallahi, inga ubanda zai zo ya kwace ki"

Jikin Maryam ne ya kama rawa, had'e da tashin hankali, wani irin bak'in ciki ne ya cika mata zuciya, wani abu mai d'aci taji ya tokare mata mak'oshinta. Sharrin sata, abunda bata tab'a yi ba, ka aje abunka ta d'auka, koda kwana dubu zaiyi zaka zo ka same shi inda ka gansa, bata tab'a shi ba, bare har ta canza mai waje, ita kanta Inna Sauden ta sani, yau dai rashin mutumcin nata akanta zai k'are kenan?.

Kamin ta dawo cikin tunani taji an tsinka mata mari, fauuuuu. Da mugun sauri ta dafe kuncinta wasu zazzafan hawaye suka b'alle mata.

"Ke kin mai da ni y'ar iska ina magana kinyi banza dani, wato ga banza na magana nayi na gama kin d'auka kenan ba?, nayi abunda zanyi"

"A'a a'a Umma na rantse ban d'aukar miki abu ba, kin sani ban tab'a miki sata ba"

"Dalla rufe min baki munafuka, na sani ko kin canza hali ne, d'an Adam da ba wuyar canza hali yake ba. Wallahi sai kin fiddo min da kud'i na, ko kuma nayi miki dukan da zaki kasa tashi"

Izuwa yanzu kam, Maryam kukan nata har shashshaka take, duk'ewa tayi k'asa tana sake cewa "na rantse ban d'aukar miki kud'i ba, ki sake dubawa dai"

Wani hanb'ari ta kai mata, da k'afa Maryam ta tafi ta bige goshinta. Goshin nata bai sauka ako ina ba sai akan wani dutsen da ake had'a murho, buguwar data yi yasa goshin fitar da jini dandanan ya kunbura. Wani ihu marar sauti Maryam ta fasa, wata irin azaba ce taji ta shigeta.

"Ahh ahh mi zan gani ni Lami?, ke Saude kiji tsoron Allah wallahi, yadda kike azabtar da wagga baiwar Allah"

Juyowa Inna Saude tayi a zafafe tana nuna d'an Lami da shigowarsa gidan kenan ya tarar da abunda Inna Sauden kema Maryam shikam bai iya gani ya kyale

Ta ce "Lami kake ko d'an Lami?, koma dai minene ka fita a harka ta, ka daina shigar min hanci d'an Lamiiiii"
Taja sunan da k'arfi tana nunasa da d'an yatsa.

Wata shawa D'an Lami ya saki yana tab'a hannu had'e da rik'e k'ugu ya ce "ai idan baki daina yima Maryam mugunta ba a cikin gidan nan to wallahi ni kuma bazan daina tanka miki ba a'ato eheee kiji da kyau"

"Maryam d'in K'anwar uwarka ce kota ubanka?, D'an Lami zan karta ma rashin M wallahi"

Zai sake magana sai ga Mafida ta shigo d'auke take da kaya a saman kanta, a roba ce k'atuwa kayan mata ne shak'e da rabor data koma saidawa kwanan nan, gida gida take bi gari-gari take talla gidanjan aure na mata.

Sauke kayan tayi tana duban Inna Saude ta ce "ke Inna kin cika fitana mike faruwa ne?"

"Ubanki ne ke faruwa shegiya y'ar iska, miye ruwanki a ciki?"


"Kinga Inna Saude ki ban amsa, k'ila ma ina da sa hannu a ciki kawai ki gaya min minene"

D'an Lami zaiyi magana, karaf Inna Saude ta dube sa da sauri ta ce "to d'an san a sani, fad'i ba'a tabbaye ka ba, kaga d'an Lami ka daina min haka zan fyato ka kana shigar min hanci fa"

D'an Lami zaiyi magana Mafida ta kyafta mai ido. Shuru yayi domin ya d'au haske.

"Kinga kud'i ne na aje masu yawa, kud'in aikina da aka biya ni na wata, na nema na rasa kuma y'ar iskar yarinyar nan kin ganta ita kad'ai taga inda nake sak'a kud'i na"

"Hmm Inna Saude kenan, ai kin san dai Maryam ba abunda zatai da kud'i ko?, ni ce to na d'auke su na k'ara jari na kayan matan da nake saidawa in..... Kamin ta Idasa maganar ma, kawai sai dai taga Inna Saude a gabanta taci kwalar rigarta ta shak'e mata wuya. Zare ido Inna Saude tayi tana cewa "ai ko uban kuturo yayi kad'an bare na makaho, yau duk gidan ubanda zaki samo kud'i na sai kin bani, idan ba haka ba uhmm wallahi Mafida sai na barki kwance"

D'an fincike cikinta Mafida tayi daga na uwar, kamin ta ce "a'a dakata Inna Saude ai dad'in uban na zuba jari kuma na maida kud'i na, dan haka kinga kud'inki"

Zaro y'ar jakarta Mafida tayi tana k'irga kud'i, ta k'irgo dubu goma ta dank'ama Inna Saude.

Zaro ido Inna Saude tayi tana washe baki ganin iyayen kud'in da Mafidar ke k'irgawa.

Ta ce "kai y'ar albarka ki ce sana'ar da kika fara akwai riba haka sosai, ai ko nima zan zuba jari a ciki. Yanzu dai a bani riba ta tunda da kud'i na akayi sana'ar kuma an samu"


Wani duba Mafida tabi uwar dashi. Sai kuma ta kalli d'an Lami dake kallon Inna Saude cike da mamaki suka had'a baki wajan cewa "to yau Inna Saude mune y'an albarkar, wai yau za'ayi ruwa harda k'ank'ara kuwa"

Sai kuma taga sun had'a hannu sun tab'a a tare, suna sake sakin wata shewar.

Rik'e baki kawai Inna Saude tayi, lallai duk yadda take d'aukar Mafidar tata, ta wuce Nan......





*SUKUNTUNI, K'ARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES NIGERIA*


Fulani ba k'aramin tashin hankali tayi ba, ganin yadda garin nasu ya koma. Kota ina kururuwar mutane kake ji, ga k'arar Bindigogi dake tashi a gidajan mutane, kallon ko ina take ganin yadda y'an Bindigar suka zagaye duka ilahirin garin.

Y'an Bindigar tare suke da motoci manya-manya, had'e da Mashina sunfi guda d'ari. Gaba d'aya dukiyoyin mutane sun kwashe sun tasa wasu gaba cikin dokar daji sunyi gaba dasu.

Y'an matan da suka kwasa kuwa zasu kai su goma irin su Fulani.

A k'asa aka tasa k'eyar su Fulani suna tafiya cikin dokar daji ga dare ya tsala. Wasu na kuka da kururuwar rasa iyayensu da sukai. Ita ko Fulani kukan ma izuwa yanzu hawayen sun k'afe babu sai zuciyarta dake mata zugi da rad'ad'i. Abu biyu ne ke mata kai kawo a zuciyarta had'e da tsainin damuwa, na rasa su Inna Wuro data yi, ji take inama da ita suka had'a suka halbe, da itama ta huta da wannan duniyar mai cike da d'unbin abun tsoro da azzalumai da suka zagaye duniyar. Sai kuma na cewa wai su Innar ba sune suka haifeta ba, kai wannan abu na mata ciwo sosai har yanzu ta kasa gasgata abunda ke faruwa da ita.

Halbin bindiga taji, ba shiri sauran y'an matan suka fasa ihu, ganin yadda aka halbe wata, data d'auke wai ita bazata iya tafiya ba ta gaji, ganin zata b'ata masu lokaci suka halbe ta nan take.

Take zuciyar Fulani ta kama wani zullo yanzu mutanan nan kwata-kwata su kashe rai ba'a bakin komai suka d'auke shi ba, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, wani sabon tashin hankali ne taji ya rufe ta.


Tafiya yankin azaba, domin kuwa tafiya suke wacce babu tsayawa ko a hutawa, idan ka ce zaka tsaya kuwa, zaka yi a bakin ranka ne. Ga dare gashi Fulani ko arzik'in takalmi bata saba, kai ba ita kad'ai ba bata jin ma gaba d'ayansu sun sa wani takalmi, ai sai da kwanciyar hankali ake iya tuna komai.


Wata irin k'arar azaba Fulani ta saki, jin wani irin rad'ad'in azaba data ji shi daga k'asan k'afarta, har izuwa kwanyarta, Tabbas tasan k'aya ce ta taka, amma tasan ko k'aran hauka ya cijeta bazata tsaya ba. Wata mai suna Fyushind'o dake kusa da ita, ta zaro ido, fuskarta shab'e-shab'e da hawaye ta ce "Fulani ba dai k'aya kika taka ba?, wallahi karki tsaya kashe ki zasuyi kinga kusan mutum biyu suka kashe saboda irin tsayawar nan"

Wani kalar miyau Fulani had'e mai d'aci, ta ci gaba da d'angyashe k'afar tata, bata ce komai ba. Suna tafiya tana runtse idonta saboda ita kad'ai tasan yadda take jin rad'ad'i da k'afar tata ke mata.

Sun shafe daren gaba d'aya suna tafiya, masu raunin cikinsu tuni suke zubewa a kasa, su ko y'an Bindigar basu tsayawa wani b'ata lokaci suke halbe mutum, izuwa yanzu sun kashe mutum ya kai biyar. Har sanyin Asuba ya fara kunnu kai, babu alamar zasu tsaya. Fulani kuwa izuwa yanzu ta galabaita ainun ga tafiya da d'angyashi ga k'ayar dake har yanzu a jikin k'afarta, tana kallon yadda k'afar ke zubar da jini harta d'an yi fushi ta kunbura.

Safiya ce tayi masu, amma ga mamakin Fulani bafa wata alamar zasu tsaya wa'innan mutane, wani kalar dokar daji su Fulani suka tsinci kansu a ciki wadda basu tab'a ganin irinsa ba, ga duhu gashi ko tarin mutum baga ji, babu gida baya babu gida gaba, tsabar dokar dajin ce kawai. Fulani tasan sunyi tafiya mai tsayin gaske wacce ma bazata iya cewa ga adadi nisanta ba, tana da tabbacin sun baro nahiyarsu gaba d'aya sun shigo wata nahiyar kuma, baza suce dai ga inda suke ba, domin ko ina daji ne wadda baza'a iya kiran sa da gari ba.


Wata irin rana mai zafin gaske ake kwanyarawa, ga azabar yunwa data fara nuk'urk'usar wasu daga cikin su, dauriya kawaii suke ga bala'in tsoron su tsaya suyi k'orafi a kashesu, tafiyar kawai suke mai cike da tsananin azaba.


Wani irin sansani, su Fulani suka ga sun iso, mai d'auke da y'an Ta'adda, zagaye da wajan, an kafa wata runfa guda uku, gashi nan harda murhu a wajan, kota ina sune zagaye da wajan wasu a tsaye rik'e da bindigogi, wasu a zaune suna zuk'ar sugari wasu kuma shayi suke sha irin na buzaye, kai da ka kalli idanuwansu zaka shaida lallai babu imani a tare da su.




*SURURE LAGOS NIGERIA*


"Wallahi Mimi sune suka d'auke ta"

Cewar Aliyu da isowarsa kenan, a garin Logas.

Cike da tsananin tashin hankali ta ce "ka daina fad'ar haka in.... "Mimi ya za'ai bazan fad'i sace ta akai ba?, Mimi kina gani fa Abbie yasa an baza jami'an tsaro a can hanyar katsinar kawai abun tashin hankalinma an tsinci motar da suka tafi da ita tare da gawar drivern, Mimi wallahi sune, Mimi kuma sunk'i koda kiran waya ne su fad'i ko nawa suke so a basu, wallahi Mimi ko dukiyata zata k'are zan basu su sakar min mata".
Ya idasa maganar tare da fashewa da kuka, kamar mace. Mimi zuwa yanzu ma kukan take itama, dole tasa kawai ta tashi ta haye sama tana hawaye, domin idan ta ce zata cigaba da zama inda Aliyu yake itama kukan zasu had'u suyita yi. Lalaah dake rik'e da Aliyu itama ta d'an kwanta akan k'irjinsa tana sakin wani sassanyan kuka itama. Sai can ta tashi ta ce "Y Aliyu ba kuka ya kamata mu zauna muna yi mata ba, kamata yayi mu tashi muje muyi alwalla muyi sallah, Allah kar ya basu ikon cutar da ita, musa a sauke al'qur'ani mai girma Allah ya bayyana ta"
Share hawayen yayi wasu kuma na sake zubowa, cikin muryar kuka ya ce "Lalaah akan Husaina ni mai rauni ne wallahi, ina matuk'ar tausaya mata ita da abunda ke cikinta, kina gani fa d'auke take da ciki a jikinta, wa'innan mutanan basu da imani fa ko kad'an ina gudun kar suyi mata wani abu, ita da abunda take d'auke dashi". Wasu hawaye Lalaah ta sake share mai duk da itama hawayen ne ke zuba a cikin idon nata.

Da kyar ta lallab'a shi yayo alwalla, sai da taje tayi sallar tata harta dawo ta iske shi bai ma sallame ba, yana sallar yana kuka, yana kai kukansa wajan Ubangijin sammai da k'assai.



A wajan Mimi ma tana shiga d'akinta, dama bata rabo da alwalla, ita kullum zaka same ta da alwalarta. Kawai ta kabbara salla itama tana hawaye.

Bayan ta gama taji wayarta na tsuwwa. Da sauri ta duba sai taga ashe Abbie ne, da azama ta d'auka kamin ma ta ce wani abu ya ce "na kusa dawowa dole na aje komai na dawo k'asar domin aji da wannan abun, dole a baza jami'an tsaro kota ina dake cikin garin katsinar da wajenta"

"Amma Abbie baka ganin kar ayi hakan, saboda kasan su y'an Ta'addar nan, basa su ana sa masu jami'an tsaro a cikin abun su, ya kamata dai mu bari muga ko zasu kira waya"

"Hmm Mimi kenan tunaninku kenan na Mata amma dole asa Jami'an tsaro a ciki, ai an riga dama ansa sun, domin sune suka binciko inda motar da suka fita take, tare da gawar driver, kinga kuwa duk motsinmu zasu sani, kuma yanzu haka suna kan bincike ne ma"

Girgiza kanta kawaii Mimi tayi, har yanzu Abbie bai san suwaye y'an Bindiga ba, su da suke kamar aljanu idan aka ce yanzu haka sun san da Jami'an tsaron da akasa cikin lamarin ba'a gaddama, yanzu haka sun d'an dakata ne suga iya gudun ruwansu.


Sallama sukai kawaii inda take shaida mai ya tsaya ya idasa abubuwan dake gabansa, zata sa a ci gaba da addu'oi had'e da sauk'e al'qur'ani mai girma, su had'u kuma suyita mata addu'ar Allah ya k'are ta daga duk wani sharrinsu.

Bai wani yadda ba, shi dai yasan dole ne cikin satin ya duro Nigeria.........
*K'ADDARAR SO*
(Destiny Of Love)




*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝
Share Fisbilillahi





*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*


Chapter 8


*ARMAN HARUN'S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA*


Yau ta kama weekend ne, kowa yana gida. Safiya ce mai cike da nishad'i domin garin hadari ne ya had'u sosai ya saki wata irin ni'ima, garin yayi luf-luf dashi gwanin ban sha'awa.

Babban parlon gidan ko ta ina ma'aikata ne ke aikinsu, masu shirya darning table nayi, sunfi ba darning table d'in mahimmanci wajan jera abincin safen da masu gidan ke gaf sakkowa domin su ci. Kamin a shafe y'an mintoci, sun shirya kan darning table d'in, had'e da gyara parlon ya d'au wani k'amshi na daban.

A hankali a hankali mutanan nan gidan suka rink'a sakkowa suna zama kan darning table d'in. Ga wata ma'aikaciya tsaye kana zama ita ce mai tabbayar ka miye kake son ci, zata zubama abunda kake ra'ayi da son ci, wannan shine aikinta kawai.

Kowa ya sakkowa harda su Daddy amma banda Arman a wajan. Salma ce ta d'an duk'a dai-dai inda Haj Shuwa ke zaune suna kusa da juna ta ce "Umma ya banga Arman d'in ya fito ba, kowa kuma yana ya hallara?"

"Hmm rabu da miskilin banza, yanzu haka yana can ya tsaya yangarsa, shifa ba wani abinci yake ci sosai ba, bari kiga koda ya zo ba wani zama yake ya dad'e a cikinmu ba"

Tab'e baki Salma tayi tana d'aga k'afad'arta irin ko a jikinta d'in nan.


Haj Zulaihat ce nufo darning table d'in, itama fitowarta kenan Bilkees dake danna waya ko kallon su Salma batai ba, bare ta san miye suke ciki. Humaira ce ma dai da Sa'adha dake kusa da juna, suke duban Salma yadda ta wani hakimce kamar wata sarauniyar gidan, Sa'adha bata dad'e da dawowa gidan ba, tana k'asar India tana karatu tazo hutu ne, Humaira kuwa d'iyar k'anwar Momma ce, dama ita gidan take zaune tun asali tare suke da Sa'adha, Humaira tafi son karatun k'asarta ta haihuwa, ita ko Sa'adha tana da ra'ayin fita. Hakan yasa iyayen Humaira dake zaune k'asar India suka bata goyan baya, take zaune a gidansu ita kuma d'iyarsu Humaira dama can ba zama k'asar take ba, tunda wayonta ta baro India ta komo gidan Momma, baka tab'a gane cewa ba Momma ce ta haife ta ba, haka itama Sa'adha idan tana can India baka tab'a cewa ba Iyayen Humaira ne suka haife ta ba, haka suke rayuwarsu cike da tsananin son juna.

Salma kuwa da biyu tayi dama, duk tana sane dasu. Tana cikin tunani Arman k'amshinsa kawai ya fara masu maraba da cewa gashi nan isowa. Su Sa'adha murmushi suka saki a tare, suna waigawa, suna duban Yayan nasu. Kai ita kanta Salma sai da ta had'e abincin dake bakinta ba shiri. Wani mayen kallo take binsa dashi, yaushe rabon data sashi a idonta, gani tayi yayi mata wani mahaukacin kyau, ita kanta bata san sadda ta saki wani murmushin munafurci ba, a zuciyarta take cewa. Tabbas Arman ka cika Zakin Maza dole y'an mata zasu rink'a harinka kota ina, na samu na shiga gidanka dai, amma ni nayi daban da y'an matan dake hauka kanka, ni dukiyar taka muke da buk'ata, ko kwanciya kayi dani wannan ma kad'ai ya wadatar dani. Ta k'are maganar tana k'ara fad'ad'a murmushinta.

Kowa ya gaisar dashi, amsawa yayi a takaice, shi kuwa kai tsaye sai da ya fara zuwa kusa da Daddy da Abba, ya kwashi gaisuwa suna ta samai albarka. Kamin yaje kusa da Momma ya rungumeta yana mik'a gaisuwarsa, cike da k'auna take samai albarka. Wajan zamansa ya zauna, da kanta Momma ta tashi ta zuba mai abunda tasan yana yana so.

Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees tana d'agowa ta banka mata harara, k'asa-k'asa ta ce "wato ke dai baza ki daina halinki ba ko?, wato ke ta danna waya ma kike, bana ce idan ya fito ki rink'a zuwa kina amsar Momma ki rink'a zuba mai abincin da kanki ba?, da haka zai saba dake har ki d'an samu matsagunni a zuciyarsa sakarai dake komai sai ance kiyi"

Turo baki Bilkees tayi bata ce komai, itafa gaskiya abunda Momy ke son ta had'a tasan ba mai yiwuwa bane.


Haj Shuwa k'asa k'asa itama yadda Haj Zulaihat zata jita ta ce "hmmm ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta"

Wani kallo mai cike da takaici Haj Zulaihat ke aikama Haj Shuwa tana kama leb'enta na k'asa ta d'an ciza, kwafa tayi tana kallon Salma, wato kenan Haj Shuwa ta canza shawara itama, so take wannan d'iyar y'ar uwar tata itama ta samu shiga wajan Arman kenan?, kan uban nan kayyasa ai ko da sake wallahi, ita Haj Shuwa zatai ma haka?, dan taga tana so itama tata yarinyar ta samu shiga. Wani dogon tsaki Haj Zulaihat ta saki, wadda yaja hankalin gaba d'aya mutanan wajan, kallo ne ya dawo kanta, basarwa tayi tana tashi gaba d'aya daga kan darning table d'in, tana ma Bilkees inkiya da ido akan ta biyo ta d'aki yanzun nan. Domin idonta ne yayi mata tozali da yadda Salma ke bin Arman da mayen kallo, kuma tuni ta harbo jirginsu ita da Haj Shuwa.




Bilkees na shigowa part d'in nasu, Haj Zulaihat ta kalleta ta ce "wai ke sai yaushe zaki gane abunda nake hango miki dangane da auran Arman ne?, har yanzu baki da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment