Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maku shi b'ata baki ne. Gaba d'aya ginin gidan irin na K'asar India ne, irin na masu kud'in cikin K'asar, wadda girmansa da fad'insa, sai wani d'an k'aramin K'auye su zauna a cikinsa, har yayi masu yawa. Kai hatta darning table d'in girmansa ya isa, kalar ruwan zinari ne, gaba d'aya parlon hatta kujeru kuwa, su kansu kujerun sun k'eru iya k'eruwa, kamar na gidan sarauta, haka kalar su take, da tsarinsu, ga wasu mahaukatan labulaye iya ganinka, kai tunda nake ban tab'a ganin irin saffarinsu ba, iya kyale-kyale an zubasa a wanga parlo ga wasu mahaukatan Ac ta k'asa data sama, da suke bada wani mugun k'amshi ko ta ina busowa suke, komai yaji sai wadda ya gani, kai ko fadar shugaban k'asa iya abunda za'a iya zubawa kenan.

Ba wadda bai d'ago ba ya kyalleta sai mutum biyu, My love, da Arman dake zaune a kujera dake kallon juna. Tana kallonsu, sai zuba mata tab'ara yake, amma ba wadda yake fuskantar hakan, sai su biyu ne kad'ai. Ita kuwa Haj Shuwa tunda ta sakko idonta na akansu, wani kalar bak'in ciki ne da hassada ya turnuk'eta. Idonta ne ya kai kan Haj Zulaihat data ciki ta batse, saura kad'an tayi bindiga, Saboda yadda taga Alhaji na bin Haj Shuwa da kallo. Itama tabbas tayi gayun iya gayu, amma sai take ganin na Haj Shuwa yafi nata nesa ba kusa ba, hatta kayan kai da ka kallesu zaka shaida tsadar kayan ba d'aya ba ce da nata, shaid'an ne ya fara zugata, a zuci take cawa "wato Alhaji dama kud'i yake ba Haj Shuwa ita da y'ay'anta, ita kuma yake ware ta da nata Y'ay'an, idan ba shi ba waye zai bata kud'i harta sayi irin wannan kaya haka, gwala-gwale.

Wani farin ciki ne kuma ya kama Haj Shuwa ganin kishiyar tata ta shak'a iya shak'a kuwa, dama haka take so tark'onta ya kama.

Gaba d'aya ahalin gidan suna zaune ne akan darning table d'in, sai wasu y'an tsiraru ne da babu, wadda Y'ay'an y'an uwa ne. Arman ne farkon tashi yana ma Mahaifiyarsa kiss gushi, yayi mata sallama tare da iyayensa Maza, yayi Maza ya fice domin ya makara yau wajan aiki.

Yana tashi Haj Zulaihat ta zunguri Bilkees dake kusa da ita, murya k'asa-k'asa ta ce "shashasha, ki tashi ki bisa ku tafi tare mana. Duk ba waje d'aya kuke aiki ba, na ce ki rink'a d'an shige mai yasan da soyayyarki amma kullum ina tufka kina warware wa ko?"

"Haba Momy, kullum fa saina mai-maita miki cewa Bestie na Lilaah ke son Arman, ni kuma zan iya sadaukar mata da komai kin sani"

"Bestien ta ce bura ubata, kinji?. Kiji min shashashar yarinya, wacce bata san inda ke mata ciwo ba, ai da alama Lilar ta fiki hankali, wacce mace ce zata bari irinsu Arman su sub'oce masu. To bari kiji tun wuri ma gara ki fito ki fad'a mata kece keda Arman, ba ita ba, domin ina doran duniya dai ba wacce zan bari ta auri Arman bake ba, dan sai inda k'arfi ne ya k'are"

"Haba Momy kiyi magana a hankali mana sosai, nidai gaskiya bazan iya iyama Lilaah haka ba, dan baki san yadda take sonsa bane in.... Buge mata baki tayi, ba wadda ya lura da su. Sai dai Haj Shuwa tana ankare da duk abunda suke, saboda fad'in darning table d'in kuma nesa suke da kowa, shi yasa ba wadda yake lura da rad'ar da suke yi.

Haj Zulaihat ta sake cewa "zaki tashi ki bisa ko kuwa, sai ranki yayi mummunan b'aci?"
Turo baki Bilkees tayi tana tashi a hankali yadda ba wadda zaiji sai Momyn tata, ta ce "nifa Momy bazan tab'a iya abunda kike fad'a ba, kuma indai Arman ne kin san zuwa yanzu ya tafi, tunda kinfi kowa sanin halinsa, ba jirana zaiyi ba, kuma koda na ce ya tsaya mu tafi tare ba yi zaiyi ba, kin san yadda ya tsani mace wacce take zubar da darajarta ta mace kuwa a wajansa?, to ko Lilaah kullum cikin damuwa take da fama dashi, har yanzu ba wani kulata yake yi ba, nikam bazan iya wannan abun..... Maganar Bilkees ce ta mak'ale ganin wani kallo na takaici da Haj Zulaihat ke binta dashi, ba shiri ta rataya jakarta da d'aukar farar rigarta ta doctor's ta sagalata a hannunta, tana ciro key d'in motarta ta k'ara gaba. Tana mitar mutum da motarsa amma ace yaje yana k'aramar murya. Ta idasa fad'ar hakan a ranta, dai-dai ta k'araso inda ake ajiye motoci, ta shiga tata, tayi mata key, aka bud'e mata kafcecan k'aton get d'in, wadda masu tsoron wajan zasu kai su biyar, baccin masu tsoron gidan dake shawagi a harabar gidan, kota ina. Harta fice suna d'aga mata hannu masu aiki a harabar gidan, masu ba fulawowi ruwa, tare da masu wankin motocin gidan...........
*K'ADDARAR SO*
(Destiny Of Love)


*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝
Share Fisbilillahi




*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*


Chapter 5


*FUNTUWA, LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA*

Tunkwal tunkwal tunkwal. Sautin dakan da D'an Lami keyi a tsakar gidan, yake bada wannan sautin. Dakan yake abunsa, yana yi yana chab'e tab'aryar, yana wak'ar umar m sharif, yana tab'awa had'e da rik'e k'ugu.

Yanzu ma d'an dakatawa yayi da dakan gana duban Maryam dake wanki a duk'e a k'asa, fari yayi da ido, yana cewa "ke y'ar uwa ke kuma a haka zaki k'are da zaman gida, da bautawa wasu, ya kamata dai ki san abunyi kinji k'awalli?"

Dubanta ya sake yi jin babu abunda ta ce, kai bama ta d'ago ba bare har yasa ran zata tanka masa. Tsaki yaja yana cewa "miskila kawai" yana murgud'a baki.

"Ahayee nanaye". Ya saki wata shewa ganin Mafida an fito za'a tafi yawon data saba.

Matsawa yayi suka tab'a da Mafida, suna sakin shewa kamar wasu abokai.

"Kai kin ganki kuwa ta waje na, kyau iya kyau, dan uban namiji dole ya sara miki, dole k'anwar nak'i kici kud'in k'ato, ahh ahhh haaayeee", ya idasa maganar tare da sakin wata shewar

Fari tayi da ido, tana cewa"kai Lami shi yasa fa, duk gidan nan, nafi shiri dake, ke d'in k'awar arzik'i ce. Ni ko ya maganar mu ta zuwa wajan Malamin nan, ka amso mana ganin nan, kasan wannan harkar dole ake had'awa da Malaman tsubbu"

Wata shegiyar dariya ya saki yana tab'a hannu, ya ce "ai kin san Lami bata wasa da Malaman tsubbu kwaro-kwaro lingu-lingu, ba inda bata san inda Malamai suke ba, ai ko nan da birnin sin ne, indai nasan Malamin tsubbu yake to sai na je can, domin duniyar nan ba'a zama haka"

Dariya suka sake saki had'e da shewa. Maryam dake jin mi suke cewa, yasa ta saki ajiyar zuciya, tana binsu da kallon takaici, bare ma Mafidar wai y'ar uwarta ce haka, ita kam baccin ance dangin Mahaifiyarta ba'a san inda suke ba, kawai dama K'anin Kawu Jafaru ya had'u da ita, ya taimaka mata ya aureta, amma harta koma ga Allah basu san danginta ba. Wasu hawaye ne taji suna shirin zuraro mata, ba shiri ta kai hannu ta share su, tana addu'ar duk inda dangin Mamarta suke, watan wata rana, Allah ya sadata dasu.




*SUKUNTUNI K'ARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES NIGERIA*


"Zauna Fulani ina so na sanar dake wata magana wacce ya kamata ace kin sani a yanzu, domin ina ji a jikina kamar lokacin sanar dake ne yayi"

Da mugun sauri Fulani ke duban Inna Wuro dake maganar, ganin ta d'akko wani k'unshin zani had'e da wata sark'a. Usman ne ya jawota a jikinsa ya zaunar da ita. Audu kuwa bai so Inna ta sanar da Fulani abunda ya dad'e da shud'ewa ba.

Inna ta ci gaba da cewa "hak'ik'anin gaskiya, Fulani, nida Baffa Mlm ba mune muka haife ki ba..... Wata irin hajijiya Fulani, ta fara gani, duk da a zaune take, amma gani take kamar juyata ake, maganar ce ta dake ta tunda take a duniya bata tab'a jin magana makamanciyar wannan ba.

"Inna, amma dai wasa kike min ba?"

"Fulani mun tab'a wasa irin wannan dake ne?, ki natsu kiji abunda nake son sanar dake"

Kwata-kwata Fulani ji take kamar ba'a duniya take ba, wasu zazzafan hawaye taji suna zub'o mata, kai ina hakan bazai yuwu ba, tunda taso ita su Baffa ne ta sani a iyayenta, koda wasa basu tab'a nuna mata wata alama da zata fahimci cewa ita ba y'arsu bace, amma rana d'aya azo ace mata wai ba sune iyayenta ba, ina hankalinta bazai tab'a d'auka ba.

Tashi tayi a zabure tana girgiza kai, tana cewa "wallahi Inna bana son sanin gaskiyar, ni dai ki barni a hakan, dan Allah Inna ki ce min wasa kike"

Wata tsawa Audu ya daka ma Fulani, wacce tasa ta koma ta zauna ba shiri, jikinta ya kama kyarma hawaye na zuba kamar an bud'e fanfo.

Inna Wuro ta kalli Audu tana watsa masa harara, k'asa yayi da kansa yana batsarwa.

"Fulani ba wasa nake yi ba, tabbas ba mune muka haife ki ba, ki bani aron hankalinki kiji ya aikai kika kasance tare damu"


*Shekarun baya da suka wuce*


Tsaye Baffa Mlm yake, ya gama yo itacensa yana niyar d'auka domin ya nufi gida, Usman dake can yana k'ora masu shanaye da basu wace guda goma ba. Kamar ance Baffa ya juya ya hangi, wata mata yashe a k'asa duk taji ma kanta ciwo kamar bacci take kamar a sume take, ga k'aton ciki da take d'auke dashi.

Da zafin nama, Baffa Mlm ya kwad'a ma Usman kira, ba shiri Usman ya zo da saurinsa harda had'awa da gudu, ya iso wajan. Ganin abunda Baffa ya gani ne yasa ma Usman d'an tsorata, d'an ja baya yana cewa "Baffa, ko dai aljana ce karka tab'a ta Baffa"

"Haba Usmanu, ya zaka ce karna tab'a ta, kama min ita muje gida da ita domin mu bata taimako, baka ganin tana bukatar hakan, kuma ba aljana ba ce mutum ce, kuma koda aljanar ce ai mu da niyar taimako muka zo". Ba yadda Usman ya iya haka ya taimaka Baffa wajan kama matar, domin yasan Baffah bazai fasa taimaka mata ba, shi haka yake da tsananin tausayi da kuma taimakon jama'a.


Shigowarsu cikin gidan, Inna Wuro dake madafa tana d'umamen tuwo, taji Baffa na kwala mata kira. Da sauri ta fito daga madafar, abunda ta tarar ne yasa itama waro ido waje, gabanta na fad'uwa ta ce "Baffa ina kuka samo wannan kuma?".

"Yanzu dai kije ki samo min ruwan zafi, zan had'a mata magani, sana ki taimaka mata kiyi mata wanka, ki gyara mata jikinta, kayan dake jikinta ki tabbatar kin adana su saboda da nan gaba"

Da to kawai Inna Wuro ta amsa, tana tashi domin cika umarnin mijin nata.

Duk abunda ya kamata sai da Inna Wuro tayi, kayan kuma ta idana su, hatta wata sark'a dake wuyan matar Inna Wuro ta b'oye su kamar yadda Mlm ya buk'ata.

Kwana biyu matar nan bata farka ba, anata mata maganin hausa, da yake Baffa Mlm yana bada taimakon magani matane da yawa a garin shi ke basu magani.

Yau kusan sati kenan matar nan dai bata farka ba. Zaune suke a tsakar gida, Inna Wuro ta kalli Baffa ta ce "ni ko Mlm, anya matar nan zata farka kuwa, abu shuru kamar wacce ke baccin mutuwa?"

"Zata farka insha Allah, ai inda zaki lura, tana lumfashi a yadda take, motsawa ne kawai bata yi, bugun zuciyata na tafiya ina ganin kamar dogowar suma tayi, kuma kamar akwai sihiri tare da ita"

"Haka Mlm nima na lura da hakan"

Suna cikin tattaunawa akan zancan ta suka ji ihu daga cikin bukar da matar take kwance. Ai ko da gudu suka nufi bukar, Mlm na cewa Alhmdllhi.

Koda suka shiga, a zaune suka iske ta, sai bin d'akin take da kallo, babu um babu umm umm tana ganinsu ta sake tsorata, da kyar da kyar suka samu ta d'an saki jiki dasu, a tak'ace dai sai dai suyi mata magana ta d'aga masu kai, amma baki babu shi.

A haka ta shafe wata d'aya a tare da su, harta yi sabo da su, a hankali a hankali kuma bakin nata shima ya bud'e sosai sukai sabo da Inna Wuro.

Watan haihuwarta yana kamawa, da Baffa da Inna kai harma da su Usman ko ta ina ganin gata take, inda ko sunanta ta manta shi, sai inna dake kiranta da Fulani kawai.

Wata rana ta tashi da nak'uda sosai hankalin Inna ya tashi dan har Baffa yaso a kaita asibiti, amma ganin haihuwar ta taho gadan-gadan, data zo kuma saita tsaya hak'ik'a tasha wahala sosai, kamin Allah ya sauk'eta lafiya, ta haifo y'an biyu duka mata. Karku so ganin irin farin cikin dasu Baffa suka tsinci kansu a ciki, Baffa kuwa kamar shine akai ma haihuwar.

Kulawa iya kulawa, Inna Wuro nayi ma Fulani sosai suke bata duk wata kulawa data dace. Ranar suna aka sama yara sunansu na asali wato Hassana da Husaina, Baffa ne ya yanka masu rago har biyu da shano.

Wata rana da su Baffa baza tab'a mantawa da ita ba, ranar da suka tashi da safiya babu Fulani babu labarinta sama da k'asa suka nemeta suka rasa, ita da babynta guda d'aya, sai dai ta tafi ta bar mana ke Fulani. Wadda ni ce nasa miki sunan Fulani na maida miki yadda muke kiran Mahaifiyarki dashi, domin Allah yayi muku kyau kamar Fulanin asali, hakan yasa nake kiranki da hakan keda ita. Wadda Baffa yayi kukan rashinta , ke hatta muma da kyar gidan nan ya dawo yadda yake, domin kamar kurciya akayi mata ne, take yawo gari-gari, kuma tana tashi tayi gaba da y'ar uwarki, amma tabar miki kayan jikinta data zo dasu, da sark'ar dake a wuyanta ranar da su Baffa suka kawo ta gidan nan".

Inna ta idasa maganar hawaye sun wanke mata fuska, kuka kawai Fulani keyi, ta rungume kayan Mahaifiyarta, tare da kallon sark'ar, gaba d'aya kayan ta had'a ta rungume tana rusar kuka. Usman dake kusa da ita ya rungumeta yana d'an bubbuga bayanta alamar lallashi, idonsa shima yayi jawur tuno da Mahaifiyar Fulanin mace mai kirki da sanin ya kamata.


Da kyar suka lallashi Fulani da daina kuka, amma duk ta zama suku-suku ko magana yanzu wahalar yi mata take, sai dai tabi mutum da ido, gashi wannan fad'uwar gaban har yanzu sake jinta take, sosai.

DARE 11:00Am na dare

Garin sukuntuni ya d'auki shuru, kowa yana makwancinsa yasa hak'ik'arinsa domin ya huta. A dai-dai wannan lokacin kuma Fulani ta tashi domin shan ruwa, wata irin k'ishir ruwa ce ta tayar da ita. A sanan kuma mafarin K'ADDARAR ta zai soma, domin yanzu bata ga komai ba, harta kai ga matakin nasara a rayuwarta. Haska fila tayi, tana kallon Inna dake bacci, fita tayi gabanta na tsananta fad'uwa, bakin randar ta tsaya. Ta kai hannunta domin d'ibar ruwan kenan, taji wata irin k'arar Bindiga, had'e da kururuwar mutane, kamin kota ina k'arar Bindigogi su k'arad'e gaba d'aya ilahirin garin nasu, ihun mutane had'e da kururuwa, tashin k'arar Bindigogi kawai kunnuwanta ke jiyo mata. Sakin k'ofin Fulani tayi ruwan da bata Sha ba kenan, jikinta ya kama kyarma kamar wacce aka jonama wutar neper. Da gudu su Inna Wuro suka fito daga d'aki, tsayawa sukai tsakar gidan hankali a mugun tashe.

Inna ta ce "mun shiga uku, Audu ba dai y'an Bindiga bane yau a garin nan, Innallihi wa'inna alaihir raju'on"

Da sauri taje ta kama Fulani tana cewa "wayyo Allah Usman ku ceci y'ar uwarku kurku bari a kasheta bata sadu da y'an uwanta ba"

Inna na idasa maganar suka ji an banko k'ofar gidan, an shigo, wata wawar bugar zuciya ce ta riskesu su duka. Zubewa su kai gaba d'ayansu a k'asa, gani y'an Bindigar sun shigo gidan, sun zagaye su, ga Bindigogi nan rik'e a hannunsu masu hatsarin gaske.

"Dan darajar Allah kuyi hakuri karku yi mana komai in..... Wata uwar tsawa wani daga cikin y'an Ta'addar ya bugama Inna dake maganar, ya ce "kai jirin miye kuke dasu, ku kashe kowa amma banda wannan y'ar shilar, da ita zamu tafi sana ku koro shanayensu gaba d'aya"

Kamin ya rufe baki ma, wani ya sakarma Usman harsashi a tsakiyar kansa, nan take ya zube babu rai a tare dashi. "wayyo Allah na shiga uku na lalace sun kashe mana Y Usman wayyo Allah Inna kin gani"
Cewar Fulani da gaba d'aya ta fice daga yaccinta. Wata gigitacciyar tsawa suka bugama Fulani wacce tasa tayi suman wucin gadi ba shiri ta had'e maganar dake bakinta. Kamin ta dawo duniyar mutane taji k'arar sukar harsashi guda biyu. Wata irin k'ara ta fasa, ganin Inna Wuro ce da Audu aka harba gashu nan yashe a k'asa babu lumfashi.

A lokacin itama da za'a d'au rayuwarta itama da zata so haka. Tashi kawai tayi tana matsawa kan gawar Inna Wuro, sai da ta tab'a fuskarta ta k'ara tab'awa, ganin fa babu rai a tare da ita, yasa kawaii Fulani fad'awa kanta ta fashe da wani irin kuka, mai matuk'ar ban tausayi. Kuka take tana surutai wadda basu da kan gado. Tashi ta sake yi ta matsa kan gawar Usman shima, maganar take tunawa inda yake cewa "ki daina kuka haka nan kinji, baga mu ba tare da ke, kuma zamu ci gaba da kasancewa a tare da ke"
"Wayyo Allah na Y Usman ina al'k'awarin da kayi min na kasancewarku tare dani har abada, ya zakuyi min haka?, ya zaku tafi ku barni cikin wannan duniyar mai d'auke da azzalumai, dan Allah nima ku kashe ni". Ta Idasa maganar tana duban wani daga cikin y'an Ta'addar dake tsare da ita sauran sunje koro shanayensu.

Wani abu Fulani ta tuna da sauri tayi cikin d'aki, d'an Ta'addar harya saita bakin Bindigarsa zai sakar mata ita, kawai yaji wani ya ce "kyale ta dole dai sai ta bimu tunda Oga ya ce banda y'an mata irinta, su a taho dasu kawaii yake so".

Fulani kayan Mahaifiyarta ta d'akko ta k'udundune su a mararta sark'ar kuwa, a cikin gashin kanta ta sata ta d'aureta, sosai yadda ba wadda zai ganta, kuma bazata tab'a fad'u ba.


Wani ne yaje har d'akin ya janyota ya tasa keyarta a gaba yana dungurinta da bindiga yana zaginta, suka fito waje, a yanzu kam Fulani zuciyarta ta bushe sai kallon gidan take had'e da kallon gawar su Inna, a cikin zuciyarta wani irin rad'ad'i mai azabar zafi take ji, a yanzu kam sai had'iyer zuciya take, idonta sunyi jawur.........
*K'ADDARAR SO*
(Destiny Of Love)




*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝
Share Fisbilillahi





*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*



Chapter 6


*ARMAN HARUN'S HOSPITAL LOGAS NIGERIA*


Turo k'ofar Office d'in, tayi cike da yanga da takunta mai jan hankali. Sai dai d'an k'aramin tsaki taja, ganin wadda take danshi ko arzik'in ya d'ago ya kalleta ma baiyi ba.
"My Arman"
"Uhum"
Shine kawai abunda ya amsa mata
"Haba Arman ya kamata ace zuwa yanzu kasan irin d'unbin k'aunarka da nake you should give me a chance, I don't want to love you for myself, you should stop like that to me. Bubi fa yanzu ko kallo ban isheka ba, wallahi kaine kad'ai kake iya min wannan dizgin". Ta idasa maganar cike da takaicin kanta

Cike da izzarsa ya d'ago dararan idonsa yana cire d'an gilashin dake manne a idonsa yana d'an dubanta kad'an. And ko kad'an Lilaah bata birgesa, duk da yasan ba k'aramin so take mai ba. But shi baya sonta ko kad'an. But the one he loves is different, and he knows that there is definitely a dust every day that he says to the one he loves.
Katse mai tunani tayi da cewa "My Arman, please give me a chance and you will be happy with me"
Murmushin gefen baki Arman yayi wadda yasa ma Lilaah fad'uwar gaba, saboda wani bala'in kyau data ga ya k'ara mata, ga wani sonsa dake fisgarta. Kai wallahi idan bata samu Arman ba akwai matsala, tana jin babu abunda bazata iyayi ba akansa. Ta shagala da kallonsa, har bata san ya tashi daga inda yake ba, sai da taji saukar muryarsa, yasa tad'an saki ajiyar zuciya.

""Lilaah, you should be patient now. Nasha gaya miki ni bana son mace wacce zata iya furta tana son namiji. If you were yourself, you would have kept your love for me in your heart and maybe you would have valued yourself. And ni yanzu naga wacce nake so Nan........ ""What are you saying Doctor Arman" ta fad'a a zabure

D'an taku ya d'anyi ya matso gabanta ido cikin ido ba shakka fuskarsa babu wasa ya ce "what you heard me say is, I won't reveal who I want soon"

""It will never be possible, surely whoever I can kill by God against you, I am jealous of you. Arman ina bazai tab'a yuwu ba wallahi"

"You are saying that it will never be possible, and knowing yourself must be possible, where life and life are my choice"

Maganganun da yake gaya mata, daya san yadda take jin saukar su a cikin ranta da gangar jikinta da ko kad'an bazai d'akko maganar wata yana danganta kansa da shi ba. She felt a kind of heartache, including a very jealous feeling, lokaci d'aya taji ta tsani wacce yake ikirarin zai aura, lokaci d'aya taji duk duniya ba wacce ta tsada sai wannan halittar da zatai mata shamaki da samun cikar burinta. Dole ne cikin biyu ayi d'aya, kodai Arman ya aureta a zauna lafiya, ko kuma yaje yayi aure ta hanasa zaman lafiya, daga shi har wacce ya zab'a ma kansa.




*ARMAN HARUN'S FAMILY HAUSE LOGAS NIGERIA*


K'as k'as k'as sautin taunar chingum ke tashi a tsakiyar parlon. Humaira dake sakkowa daga kan bene tana nufar kitchen, ta d'an tsaya tana duban, Salma dake tsaye da akwati, sanye take da wasu y'an iskan k'ananan k'aya, ance matsu ga wani kafcecan gilas data manna a idonta, tana bin parlon da kallo. Ganin Humaira yasa ta k'ara wani kame kanta yatsine baki tayi, bata da niyar tanka mata, tana niyar barin wajan, ta nufi hanyar da zata sada ta da part d'in Haj Shuwa, taji Humaira na cewa "Ohh su Salma ne a gidan namu"

D'an juyawa tayi, a hankali tasa hannunta kamar bata so ta cire gilas d'in dake manne a idonta, tayi mata wani kallo kamin ta ce "hmm kware mune a gidan naku, kuma da alama munzo kenan"

"Allah sarki, ai kin san mu dama masu taimakon mutane ne, kowa yazo zai iya zama gidanmu domin yaci arzik'i yabar arzik'i inda yake"

Da sauri ta dube Humaira data yi maganar kamar wacce ba ita ce tayi ta ba, maganar ta shigeta kamin ta ce "uhum koda yake mufa munfi k'arfin muzo muci arzik'i domin muma ansan ba matsiyata bane, da abun duniyarmu a hannunmu, kuma da alama mun kusa zama masu gidan gaba d'aya, sai dai azo aci namu arzik'in"

Humaira zata sake magana kenan, Momma ta fito tana duban Salma, duk taji mi suke cewa, d'an murmushi tayi irin na manya, duk abunda matan gidan suke akan d'an nata tana sane, kuma duk wani takunsu nason had'a y'ay'ansu da yaronta d'aya tilo tamkar da dubu ta sani.
"Humaira abunda yasa kika sakko kenan?, son magana, bana hane ki da sa baki a maganar da bata shafe ki bane?"

K'asa tayi da kanta ta ce "sorry My love" tana Idasa fad'ar haka ta Idasa shigewa k'aton kitchen d'in nasu.

Salma kuwa, ko kallon inda Momma take bata yi ba tayi shigewarta part d'in Haj Shuwa.
Girgiza kai kawaii Momma tayi, tana tunanin a haka zata amince d'anta ya auri wannan yarinyar marar tarbiyya, ina ai bazai tab'a yuwu ba kam.

Da gudu taje ta rungume Haj Shuwa dake tsaye tana waya.

"Ahh ahh, harkin iso, mutanan Abuja da alama jirgin safe kika biyo yanzu muke waya da Mamarki Binta ai take sanar dani ai kin taho"

"Uhum, Umma ai dama kin san nafi son tahowar safe"

"Hakane y'ar albarka fatan kin iso lafiya?"

"K'alau Umma na iso"

"To madallah, ai kin san abunda muke ciki ba sai na sake miki baya ni ba. Karki sakan kance ki fad'a sonsa da gaske domin kuwa nan gaba kad'an zamu aika sa inda ba'a dawowa"

Wata dariya Salma ta saki tana duban Umma ta ce "ai Umma a shirye nake kawai umarninku nake jira"

"Tabbas dama nasan zaki iya, to amma fa akwai y'ar matsala guda d'aya"

"Wacce irin matsala kuma Umma?"

"Hmm

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment