Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Oga?"
Ma'aikaciyar ta fad'a dake sanye da kayan aiki, sai Lalaah taga tana mata kallon kamar mamaki kamar irin baza ta iya ba.
Tsuke bakinta ta d'an yi ta ce "Yeah I say"

"Okay Follow me"

Shine abunda kawaii ta ce. Bin bayanta Lalaah tayi, tana kallon irin tsaruwar company nan, hak'ik'anin gaskiya company nin yayi wani mahaukacin kyau na fitar hankali, har idan kana ciki baza ka tab'a gane cewa wai akwai rana a waje ba, bare kayi tunanin a Nigeria kake ma.
Tunaninta ne ya k'ara kwancewa ganin sun shigo wani Office mai kama da aljannar duniya, kware haka zata kira sa, saboda had'uwar Office d'in bata san sadda ta had'e wani miyau daya tsaya mata a mak'oshi ba. Kallon Office d'in take cike da d'unbin mamakin had'uwarsa, baza ka tab'a cewa mutum ne ya tsarashi ba, ga girma ga fad'i gashi an zuba kayan more rayuwa a ciki. Wani k'aton table ne mai d'auke da gilas a jikinsa, mai fad'in gaske sai d'aukar kyalli yake, sai kuma wata kujera dake a gabansa dake jujjuyawa, ba kowa samanta da alama nanne shugaban Office d'in yake zama. Sai kuma wasu kujerun guda biyu kamin ka k'arasa da jikin table d'in sai wani d'an k'aramin table dake a tsakiyar su, alama na tarbar bak'i ne idan sunzo, daga can b'angaran dama kuwa, da hagu ko ina AC ce ke busuwa tare da wani mugun k'amshi mai kwantar da hankalin mai shak'arsa. Hannunka na dama kuwa idan ka shigo Office d'in an aje kayan zane, dama ansan da zuwan mai zanen babu abunda ba'a aje ba, ga wani tantausan kafet da aka malala a wajan, daga gefen wajan kuma ga wata firiza nan, sai kujera mai d'an tsawo da aka aje wajan allon zanen.

Tunanin Lalaah ne ya katse da barin kallon Office d'in da take yi da kallo na k'urulla, jin matar data kawota take cewa "it's a lot of your artwork and everything, it's Oga's office here. He didn't reach the end, he stopped at his hospital and reduced his work a little, he would like you to finish the drawing, I will pass".
Cewar ma'aikaciyar tana dubana, gyad'a mata kai kawai Lalaah tayi.

Tana juya kenan tana gaf ficewa daga Office d'in, ita kuma Lalaah ta k'arasa inda zatai aikin daya kawota, taji matar ta sake juyowa ta ce "if you need someone, here's the phone, call me and I'll come"

"Okay" kawai Lalaah ta amsa mata dashi, ita kuma ta k'ara juyawa ta fice.

Tana fita Lalaah ta sauk'e ajiyar zuciya, ta fara zanenta a tsanake cikin kwanciyar hankali. Ta d'au awa uku tana abu d'aya kamin ta kammala zanan gaba d'aya, ita kanta data gama zanen gaba d'aya, sai da ta kalla ta sake kallo, wayarta ta zaro tana d'aukar zanen, domin yayi mata kyau sosai, ta baje basira a zanen. Dai-dai ta gama d'aukar zanan hoto, taji an turo k'ofar Office d'in, har gabanta ya d'an fad'i, sai kuma taga ma'aikaciyar nan ce ta farko wacce tayi mata jagora zuwa office d'in, d'auke take da wani faranti mai shegen kyau wadda yake shak'e da abinci lafiyayye. Tana k'arasowa wajan ta aje kan table dake wajan, ta matsa jikin firiza ta d'akko lemo ta aje, tana cewa "hello, Oga is about to arrive, am... Maganarta ce ta mak'ale ganin zanen da Lalaah tayi idonta yayi mata tozali dashi. Waro ido waje tayi cike da tsananin mamaki al'ajabi, ta rik'e baki tana cewa "Omo, You are now saying that you have done this design so well?"

D'aga kanta kawaii Lalaah tayi tana murmushi, domin ta saba jin haka wajan mutane mabanbanta, idan tayi zane, wasu ma k'aryatata suke har sai tayi a gabansu sun sheda.
Matar sosai ta rud'e itama ta d'akko waya tana d'aukar zanan hoto,

Ta dad'e tana santin zanan, har tana cewa"lallai Oga zai yaba sosai da wannan zane gaskiya na jinjina miki"

D'an kallonta Lalaah tayi jin yanzu tayi mata Hausa, domin tunda suke magana ta d'auka bama tajin hausar ai, ashe tana ji girgiza kai kawai tayi tana murmushi, ta d'an zauna. Ita kuma ta fice ta zan can zanen da Lalaah tayi.

Ta kusa rufe awa d'aya a wajan, da gamawa tana zaune kawai ita bata ci abincin da aka aje mata domin ba jin kuma zata iya cin wani abinci a waje ba gida ba, domin bata saba hakan ba. Zamanne ya fara gundurarta, har ta d'an fara sakin tsaki a ranta, a ranta take mitar sofa masu kud'in nan dama haka suke, su wani ajiye ka kana faman jiransu, sai ka ce maula ta zo, ta sake sakin tsaki a fili yanzu.

Tana cikin wannan tunani taji an turo k'ofa, a d'an gajiye ta mik'e bata kalli wadda ya shigo ba bare ta shaida waye domin ta juya baya ne, tana cewa "Ohhh, my sister, I'm tired, I think I'm going to go, when your Ogan comes back and asks for my address... Ta fad'a dai-dai tana juyowa had'e da d'an turo k'ara min bakinta, fuskarta ta nuna alamar shagwab'a. ARMAN HARUN, daya shagala da kallonta tun maganar farko data yi, yake dubanta, kallon sani yake mata yana mamakin ina ya tab'a ganinta, sai da ta juyo gaba d'aya ya shaida ashe fa a shopping suka tab'a had'uwa harya rage mata hanya.

Sai da PA d'insa yayi gyaran murya tukun, Arman ya lura da irin kallon da yake binta dashi. Sai a lokacin itama taji wani azababben k'amshi ya k'ara bud'e Office d'in, yasa gabanta yayi wata irin bugawa, har k'irjinta na d'agawa. Tama kasa koda motsa d'an yatsanta ne. Har sai da suka iso wajan, Arman kai tsaye inda take tsaye ya nufa, yana takunsa na k'asaita da birgewa, PA d'insa kuwa kai tsaye inda zanan yake ya nufa, yana waro ido tare da zuba santin zanen sosai. Duk abunda PA yake fad'a basa jinsa, domin kuwa wani arnan kallo Arman yake bin Lalaah dashi, har sai da jikinta ya fara d'an rawa, had'e da k'ara turo baki, ciki-ciki ta ce "nifa na tsani kallo"

"And I'm the one I'm opinionated about"

Taji saukar muryarsa akanta

D'agowar da zatai a mamakince domin bata tab'a tunanin yana ma kusa da ita har haka ba, bare yaji miye take cewa, tayi maganar ne iya mak'oshinta, sai dai d'agowar data yi ta gansa gaf da ita, har sai da ta d'an matsa baya kad'an, tana d'an kallonsa ta k'asan ido. Kwarjininsa duk ya cika wajan, sai taji duk tayi muguwar takura, duk da PA d'insa dake wajan, bata so yake ba yana can yana ta zan can zane.

Binsa take da kallo, harga Allah Arman, kyakykyawa ne, ba irin shima kallo d'aya zaka kirasa da mai kyau ba, ba fari bane kuma ba bak'i bane, gashi nan dai tsaka tsakiya yake, amma fa dogo ne tubarkallah, dan daya tsaya gabanta saita hango kanta a k'arama. Jikinsa da dantsan hannunsa a murd'e suke, alamar yana kula da jikin nasa, k'irar k'arfi garesa had'e data sadaukai, girarsa had'e take da y'ar uwarta, wadda gashin idonsa zara-zara kamar macen da aka k'arama gashin ido irin na idon mace, sai dai shi nashi ne na asali, bakinsa dake d'auke da jan leb'e, bakin nasa madai daici ne, sai idonsa masu girma amma kai tsaye idan kamai kallon tsaf baza tab'a wace idonsa masu girma bane, domin kullum a shanye suke kamar mai jin bacci, sai idan yana cikin b'acin rai ko wani abu, ya ware su zaka san idonsa masu girma ne da haske kamar farin wata, ciki kamar an zuba masu madara.

Muryarsa taji kamar ana busa mata iska mai dad'i ko na ce sarewa, saboda taushinta da kaurinta, yana cewa "look, don't eat me"

Wata muguwar kunya ce taji ta kamata, ashe haka ta jima tana kallonsa, dan har ya kai kujerar table d'in ya zauna, ita tana a tsaye harya gifta ta ya wuce bata ankara ba, sai da taji saukar muryarsa.

PA d'insa ya d'akko zanen yana nunama Ogan nasa. Shi kansa daya yayi tozali da zanen sai da d'ago da sauri yana binta da kallon mamaki, jinjina kansa yayi yana nazarinta, lallai nan gaba ba k'ana nan kud'i wannan yarinyar zata samu ba kuwa. Tattare kayanta ta fara yi tana idasawa, ya dubeta a tsana ke, ya lura ko abincin da aka kawo mata bata tab'a ba, sai yaji ta k'ara birgesa, alama bata cin abinci a ko ina, haka kawai ta sake shiga ransa. Amma idan ya kalleta tana mai kama da ciwon kansa wato Lilaah kenan, amma shi sai ya d'auka ko kawai shike ganin kamar, kodan kullum tana damunsa da soyayyar shirmanta a kullum, wadda ta gama felank'enta baya ko kulata ko yanzu da ciwon kanta data sashi ya baro hospital d'in. Katse tunanin Lilaah yayi, yana kallon Lalaah alama yayi PA d'insa, PA na ganin haka yasan miye.


PA ya juyo inda Lalaah take ya ce "Oga ya ce zaki iya bada katin ki da account number zaki ga sak'o"
"Okay" kawai ta ce tana sa hannunta a jakarta ta d'akko wani firin kati mai d'auke da komai da suke buk'ata, ta mik'a ma PA d'in, tana mik'a masa tayi godiya ta fice, PA d'inma na gode mata.

Ogan naku kuwa wasu ayyukan ya kama, amma hankalinsa rabi na gareta, harta fice, a sadda ta idasa ficewa ya samu kansa da sauk'e wata irin ajiyar zuciya, daya rasa ta miye...


*FUNTUWA, LOCAL GOVERNMENT KATSINA STATES NIGERIA*


K'as k'as k'as, sautin taunar chingum d'in da Mafida ke tauna a bakinta, ya karad'e tsakar gidan, harta idasa shigowa tsakar gidan, d'auke take da tallar mangwaro da Kawu Jafaru ya k'irk'ira samata, kuma ya d'aure mata gindi na zuwa tallar kwaro-kwaro gari-gari. Wadda har Inna Saude tana ganin ana ciniki tasa hannun jarinta. Sai dai kuma duk sadda kud'inta suka b'ace ko y'ar biyar ce ranar Mafida mugun duka take ci, ko kuma suyi bigi in bugu ita da uwar.

Yauma tana shigowa, ta aje kayan tallar, tana yamitse biki, Maryam dake zaune tana tsintar waken Umma, daya zame mata dole a yanzu, a kullum kuma, duk da Inna Saude bata so kullum cikin yada ma Umma magana take, amma fa sai idan bata a cikin gidan.

Da sauri Inna Saude ta yaye labulan d'akinta tana fituwa gaba d'aya, tana bin Mafida da wani kallo, sai can ta ce "to yar iska daga ina?, yau kwananki biyu baki gida gidan ubanwa kika je shegiya, kuma ina kud'in mangwaro na bani bani maza tunkan na sab'a miki kamanni wallahi"

Sautin k'as ne ya k'ara fitowa daga bakin Mafida tana duban uwar tata a wulakanci ta ce "ke ni Inna Saude ba sai ki bari na d'an huta ba tukun ko miye sai ayi". Haka suke kiran uwar dashi babu ruwansu yadda kowa yake kiranta dashi haka soma.
Wani kallon baki isa ba wallahi Inna Saude ta bita dashi.

Matsowa Inna Saude tayi, tana sa hannunta ta warce wata y'ar jaka dake k'ugun Mafida. Sauke numfashi tayi ta koma gefe ta k'irga kud'in dake ciki yafi a k'irga ganin basu kai ko kwatar kud'inta ba, yasa ta warga ma Mafida wani kallon zaki ci uban ki yau kuwa.

Mafida ko a jikinta ta ce "Inna Saude ki daina min haka, dakin bari a tsanake na baki kasonki tunda kinga bake kad'ai keda shi ba". Ta idasa maganar cike da rashin kunya tsantsarta.

Wani kukan kura Inna Saude tayi ta jawo Mafida ta tuma da k'asa ta taushe ruwan cikinta ta fara kai nata naushi kamar ta samu abokin danbe, Mafidar itama batai wasa ba wajan kai mata cizo da yakushi, amma ko a jikin Inna Saude, dama ga Inna Saude jikinta a murd'e yake, saboda aikin wahalar da take yi ita ce buga can buga nan, ga k'arfi kamar na doki, kwata-kwata suffar Inna Saude kamar bata mata ba, kamar wani basamudan k'ato. Yanzun kar kaso jin k'arar naushin da take kaima Mafida, sai ihu take, Inna Saude na kwashe mata albarka tana cewa "ai wallahi gara na jifgi kud'i na, gobe ma ki sake kashe min kud'i, kina can d'akin k'ato kin kwana kin kashe mai kud'i mai makon ke ki samu kud'in amma da yake ke y'ar iska ce wacce ubanta ya gama lalatawa ya d'oraki kan hanyar da bazata b'ille ba gara...... Maganar Inna Saude ce ta mak'ale jin an rik'e mata hannu, juyowa tayi tana duban, D'an Lami, D'an daudu ne daya lak'aba ma kansa dole Lami sunansa, shima haya yake a cikin gidan.

Fisge hannunta Inna Saude tayi, tana bin D'an Lami da kallo, da yake tab'a hannu yana y'arfar dashi, yana lauye hannu tare da rik'e k'ugu yana cewa "Ohhh ni Lami miye zan gani haka?, haba Inna Saude ya zaki turmushi K'awata haka, kina jifga kamar kina dukan k'ato, kin san fa mu mata ba'a mana irin wannan dukan...... Katse sa tayi a zafafe tana cewa "kai dalla rufe min baki, d'an daudu kawai dake, kana garjejen k'ato dake kike kiran kanka da mace, Allah wadaranka wallahi"

"A'a Saude bari kiji na gaya miki ni Lami ba'a min haka yawwa, yada magana zaki rink'a maida ni namiji k'ato fisbilillahi, ya Hakan"
D'an Lami ya idasa maganar yana tab'a hannu tare da yin fari da ido.

Wani takaici ne ya kama Inna Saude wani dogon tsaki taja tana sake cewa "kaga d'an Lami.... "Ahh ahh dakata Saude ya haka wai, kike kira na da D'an Lami, Lamin ce baza ki iya cewa ba ko mi?, ya kike maida ni namiji ne wai"

D'an Lami ya katseta yana daka tsalle kamar wata mace.

Maryam dake gefe tana jin abunda ke faruwa, wani ya sata murmushi wani takaici. Tana tunanin lallai Nanah tayi sa'a da aka d'auketa aikatau a can Abuja, gidan da Inna Saude ke masu aikin abinci nan ne d'iyar gidan tayi aure a Abuja, ta haihu, shine suka nemi mai tayata aiki mai mata rauno, Inna Saude bata b'ata lokaci ba, wajan bada Nanah, yanzu kusan shekara d'aya Nanah bata gidan, Maryam tana tunani lallai dama ita ce tabar gidan, da ace Nanar na nan, da itama yanzu tabi layin Mafida wajan yawon banza da rashin kan gado.........
*K'ADDARAR SO*
(Destiny Of Love)





*©ZAHRA ROYAL STAR*🌝 Share Fisbilillahi



*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*


Chapter 4


*SUKUNTUNI, K'ARAMAR HUKUMAR KANKIA KATSINA STATES*


Da gudu ta shigo y'ar k'aramar bukar su, zan birki tayi jin yadda Inna Wuro ke kuka kamar ranta zai fita. Zubewa tayi k'asa tana zare ido k'irjinta na bugawa kamar zai rab'e gida biyu.

Idonta har yanzu Baffanta yake gani kwance cikin jini a tsakar d'akin da alama kukan da Inna Wuro ke yi kamar na mutuwa ne, wata wawar faduwar gaba ce ta rinki Fulani dake zare ido har yanzu tama k'asa magana. Inna Wuro tayi saurin juyowa jin motsi a bayanta, kuka ta sake saki tana cewa "Fulani sun kashe mana Baffanki, ki duba tunda abun nan ya faru suka sassare shi bai k'ara lafiya ba, mi yasa baza su gane mu ba y'an ta'adda bane?, muma kanku masu satar mutanan idan suka samu sace mu suke, mutum nawa aka d'auka a rugar nan, amma mutane sunk'i su barmu mu huta, ki duba fa Baffa bai san hawa ba bai san sauka ba, kawai cikin dare suka shigo suka kamasa da duka, wai ai shine ya sace masu D'an uwa, wayyo Allah ya suke su muyi da rayuwarmu ne?"

A yadda Inna Wuro ke rusa kuka tana dawo da abunda ya wuce na baya zaka san cewa ta fara fita daga yaccinta ne, domin sai surutu take zubawa hawaye na mata kwaranya a idonta. Rushewa da kuka Fulani tayi iya k'arfin kamar ranta zai fita, jikinta har wani jijjiga yake. Tsoro ne ya kama Inna Wuro ganin yadda Fulani ke yi, kamin tayi wani yunk'uri Fulani ta zube a sume. Wata gigitacciyar k'ara had'e da salati Inna Wuro ta ramka, wadda ya zawo hankalin mutane wajansu.


Fitowa Inna Wuro tayi rik'e da Fulani tana kwalama sauran yaranta kira ba k'ak'k'autawa, da gudu samari guda biyu suka shigo cikin gidan. Sai yanzu ne na k'are ma gidan kallo, ashe ginin k'asa ne, sai ka shigo daga cikin gidan zaka iske buka guda biyu, sai d'akuna biyu sai inda suke sanwa dake gefe. Usman ne yayi saurin amsar Fulani gabansa na fad'uwa yana cewa "Inna, ba munce karki bari Fulani taga gawar Baffa ba?, mi yasa kika bari ta gani". Ya idasa maganar cike da ciwon abunda akaima Mahaifinsu.

"Usmanu, ya za'ai bazata sani ba wadda ko gawar ba'a shirya ba ta shigo da gudu, dama daji taje wai samo masa maganin ciwon k'afarsa da aka bugeta sosai ita duk d'aukarta zata iya samo masa gani, bata san ashe Baffa tafiya zaiyi ya barmu ba". Inna Wuro ta k'are maganar kuka na sark'eta. Audu dake gefe bai tanka ba, daka kallesa zaka san a zuciye yake, idonsa yayi jawur ba alamar hawaye sai bala'in dake cikinsu na d'aukar fansa tsantsarta.

Juyawa yayi kawai zai fuce waje, Inna Wuro tayi azamar tsayar dashi ta ce "ko kusa ko alama ban lamunce maka d'aukar wani mataki ba, indai akan abunda ya samu Baffanku ne, ku barsu suda Allah, ko suwa ye sukayi hakan"

"Amma Inna, saboda mi?, da kin kyale ni munje nida abokai na mun tada fitina a cikin garin nan, dole a fiddo mana wadda suke wannan aikin"

"Kaima baka ji mi kake cewa bane Audu?, babu dad'in ji, wai fitina miye affanin tada ita to, tunda bamu san su waye sukai mai hakan ba, sanin kanka ne ka sani cikin talatainin dare suka shigo gidan nan, sukai mai wannan ta'asar ku kyale komai ya wuce. Yanzu abunda nake so duka kai Usman shiga da Fulani cikin bukka, kar a watsa mata ruwa har sai ankai Baffah Mlm makwancinsa na gaskiya, idan yaso sai a watsa mata ruwa ta farka, domin suma tayi, bana so ta sake tashi taga gawarsa wani abun ya sake samunta itama"

Inna Wuro ta k'are maganar, har yanzu hawaye ke zuba a idonta, dauriya ce kawai take, domin ji take kamar zata had'iye zuciya ta mutu itama.

Ba yadda Audu yayi iya, haka aka kira mutane aka sallaci Baffa aka mik'asa makwancinsa na gaskiya, sai lokacin Audu ya shige d'aki yana durzar kuka kamar ba gobe. Shi ko Usman sai da Fulani ta farka, tana kuka mai ban tausayi ne ya rungumeta shima ya fashe da kuka.

Inna Wuro dake dubansu ta ce "ya kamata ku daina kukan nan haka nan, addu'a kawaii yake buk'ata"

Fulani ta d'an janye daga jikin Usman ta ce "shikenan yanzu Baffa na, ya tafi bazan sake ganinsa ba kenan?". Wasu hawaye hawaye Usman ya sake share mata ya ce "ki daina kuka haka nan kinji, baga muba tare da ke kuma zamu ci gaba da kasancewa a tare da ke".
Wata irin fad'uwar gaba ce haka nan Fulani taji ta sameta lokacin da Usman ke yin maganar, wani irin kallo take binsa dashi, har sai da ya hura mata iska yana mata murmushin yak'e yana sake cewa "ya da wannan kallo haka kamar na baza ki sake gani na bane, muna tare fa". Da sauri ta lumfashe idonunta gabanta na tsananta fad'uwa, kyakykyawar fuskarta duk tayi ja saboda da kukan data sha, har yanzu wasu hawaye ke sake wanke mata fuska, domin harga Allah fad'uwar gaban da take ji tayi yawa, ga girarta da hagu da take ji tana mata motsi sosai, ga wani irin k'uncin zuciya dake taso mata, duk maganar mutane da su Inna Wuro ke mata na ta kwantar da hankalinta haka nan, amma ina tayi nisan kiwo, ita kad'ai tasan miye take ji a cikin jikinta.





*HARUN'S FAMILY HAUSE, LOGAS NIGERIA*


"Ai Binta nake gaya miki shegen yaron nan ya dawo, ya kama aikinsa kamar yadda ya saba, inaga fa asirin nan da boka ya bamu bai kamasa ba kwata-kwata nake gaya miki, abun ya fara bani tsoro, yaro sai ka ce aljani komai akai mai baya kamasa dandanan, koya kaman bai wuce na y'an kwanaki abun ya b'aci".
Haj Shuwa ta fad'a ranta a b'ace, rik'e take da waya a manne a kunnanta. Daga cikin wayar Aminiyarta ta ce "ai ko dole a sake sabon shiri, domin a tarwatsa rayuwarsa, shi d'in mi Aunty Shuwa har da zaki tsaya kina b'ata ranki a banza, kika ma b'atar da wasu kuma suka b'ace duniya bata sake jin d'uriyarsu bare Arman shi a wa, dole ya fad'a tarkonmu karki wani damu idan yasan wata ai bai san wata ba".
Wata shewa suka saki, sai kuma Haj Shuwa ta sake cewa "amma fa ina ganin kamar y'ar iskar abokiyar zaman can tawa itama fa tana shirin wani abo, domin duk ina ganin take-takenta so take Bilkees ta auri Arman, ita kuma Bilkees bata sonsa, bai cikin wadda take so, so take tayima wata k'awarta kamunsa wai wata mai suna Lilaah, duk ina sane da duk abunda suke k'ullawa".

"Lallai Bilkees bata da wayo, mutum kamar Arman ka ce wai baka sonsa. Amma Aunty, kina ganin baza mu sake shiri ba, nasa Salma ta dawo gidanku da zama, ko Allah zai sa muma mu had'ata da Arman aure, muci dukiyar, idan yaso daga baya musa ta kashesa, amma ya kike gani"

Wani shuru ya d'an gifta sai can Haj Shuwa ta ce "tabbas kin kawo shawara mai kyau y'ar uwa, ai da duk ni ban kawo hakan ba, kinga ni dama kinga Bobo baida wani aiki saici gashi nan yayi wata shegiyar k'iba, ina so ya zama wani abu amma ya za'ai ya zama yana a haka?"

"Karki damu Aunty, Bobo shine zai gaji dukiyar Alhaji"

"Nasan da wannan amma, ni dukiyar Alhaji Harun nake so, bawai dukiyar Mijina ba, domin Alhaji baida dukiyar Alhaji Harun ko kama k'afarsa baiyi ba, wajan dukiya, kina fa gani duk arzik'insa muke shida yaronsa tilo Arman, da uwarsa Haj Badiyya, ko kishiya fa bata da ita, daga ita sai yaranta su biyu, Arman da Sa'adha. Sai mune y'an cin arzik'i nida kishiyata, wacce aka laluk'a min ita, shi Alhaji Harun baiyi auran ba sai K'aninsa da aka zugasa yayi, shida maida wani abun duniya, ai wallahi duk wadda ya zuga Alhaji ya auro wancan guzumar ban yafe masa ba".

Haj Shuwa ta k'are maganar idonta jawur.

Binta dake cikin wayar ta ce "ya kamata duk ki manta da wannan abun wadda ya wuce, ki tuna fa, kinyiwa k'awar Haj Badiyya kurciya tabar gidan nan da cikin, mijinki, wadda shekara kusan goma sha takwas kenan babu amo babu labarinta, sai bayan b'acewarta ne aka sa ya auro Haj Zulaihat, harta zo ta haifi Bilkees, itama Haj Zulaihat d'in dakin bada dama da tuni an kawar miki da ita"

"Na tuna da wannan, ni nama shafe babinta ai tuni, ta mutu ita da cikin insha Allahu, sana kuma Haj Zulaihat ita ina da wani babban shiri kuma k'udurin da nake son cikawa da ita. Ita na barta ne a bisa dalili nawa, zaki jisa nan gaba kad'an"

Motsin bud'e k'ofa, Haj Shuwa taji, hakan yasa sukai sallama da Binta, suka tsayar da maganar Salma zata dawo gidan.

Inna Kande ce mai aiki ta turo k'ofar d'akin. A wulakanci Haj Shuwa kuma a tsawace ta ce "Kee kee ya haka, zaki rink'a shigo min d'aki bako sanarwa, bana hanaki shigo min d'aki haka kawai bane?"

Ta k'are maganar a tsawa ce

"Haj kiyi hakuri dama Haj Babba ce ta ce na kira ki abinci za'a fara ci ya kammala a darning table"

Wani dogon tsaki taja, tana cewa "naji gani nan fitowa"
Da sauri Inna Kande ta juya tana rufo k'ofar a hankali kamar wacce ke jin tsoro karda k'ofar ta b'alle.

Sai da ta sha iska, da mula dan kanta tukun ta fito, a yanzu asha wani wanka na fitar hankali ansha ado sai walwali take. Domin Haj Shuwa irin matan nanne wadda kota ina basu so suga an wuce su kota ina, sunfi son suga sune gaba, game da komai.

Kwasss kwasss kwasss. Takun tafiyar Haj Shuwa dake sakkowa daga matakalar bene dake shashinta, ta nufo parlo. K'atoton parlo ne, wadda tsayawa ma fasalta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment