Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ishe ta tun dazu take ce mata juya ai taga arzikin haihuwa amma sai dai aita ci da ita tana kashi kiransa tayi be wani dau lokaci ba ya ɗaga kuka tasa ta fyece majine tace

"Sule yau gani ina cin arzikin ka sule Allah ya bawa samha ka ganni nan sai cin kaji nake sule wallahi na tausaya maka da akai maka baƙin ciki baka zo ka ci ba ina ci kai nake tunawa ko ka tada komaɗa,


Girgiza kai yayi wato me hali baya fasawa yace


"To inna Allah ya basu zaman lafiya,


Cinya ta ɗauka ta ci tace


"Amin sule sai anjima,

Kashe wayar tayi kafin safiya inna ta shiga toilet yafi sau biyar duk ta fita hayyacin ta yo pepper chicken taci ga taco🌮 ya ci kayan lambu

cikin ta ya ɓaci ga uban Attahiru cewa take anya ba dangin mayu suka kawo samha ba ai sunsan baki ne yaushe zasu sa Attahiru a girkin su dariya aka kwashe da ita ganin sun mai da ita yawa mahaukaciya sa ta yi shiru da bakin ta badan ta soba


*RANA BATA ƘARYA*


Cikin wata ɗanyar shadda White colour ya shirya anmai aiki da golding colour hular da yasa me tangaran wacce zata dace da shigar da ga agogo dan gidan rado takalmin da golding colour wani irin kyau yayi na ban mamaki yau ya yarda yan jaridu su ɗauke shi tun daga filin jirgi ake mai video har zuwa masallacin juma'a Na Sheikh isaya rabi'u daurin auran ya samu halattar manya manyan mutane har da farar fata sun zo inda duniya ta sheda ɗaurin auran bilkisu sulaiman (samha) da na ma'aruf jafar jabir

wata iriyar kabbara aka saki nan maroka suka shiga wasa shi dun guma akai har kan karofi kamal aeman suna tare da shi hutuna sukai da su kahu isah har kahu Ismail ba abarsa a baya ba abin mamaki baya ƙarewa kahu bilyaminu na gani yana washe baki sai bin abba yake duk inda yasa kafa ƙaguwa yayi yana so ya ga samha

amma ba dama mutane sai hutu na suke da shi ba shi ya sami kansa ba sai bayan la'asar lokaci kuma ya kure ana ƙoƙarin kai ta gidan tane tun safe take kuka ga wani irin ciwon kai da take duk ta rame cikin tane ya murɗa jin ana tayi sauri ta shirya jirgi baya jira da sauri ta tashi tana xare ido ta shiga toilet dariya nuratu ta saki tace


"Samha amarya da ga jin kaiki har da gudawa,


Dariya yan ɗakin suka saki fitowa tayi tayi wani irin fari kai kace wanko fatar ta akai atamfa ce Ingila a jikin ta blue Black ɗinkin riga da zani tayi mata cib yawa an gwada ta aunty salma CE ta shigo tace


"Yauwa zo ,

Jitayi kafarta tayi nauyi da ƙƴar take ɗagata wanka tasa tayi da ruwan turarurruka sannan ta bata lace onion colour anmai adon flower light pink and blue wata hadaddiyar lufaya tasa bule colour tayi kyau ga sarkar gold a huyan ta sai kamshi take ba aimata wani make'up ba zama tayi hawaye na bin fuskarta anty salma tace

"Oni salma samha yau she zaki bar kukan nan ,


Ƙasa tayi da kanta tana wasa da fingers ɗin ta ya ci lalle ja da baki ya ƙara haskaka fatar ta daman abin ka da fari

torowa akai zasu tafi gun abba aka kaita yayi mata fada sannan ƙanwar kakar ta tayi kukan rabuwa da su a hankali jerun motocin da zasu raka ta suka fara tafiya har suka isa airport shiga jirgi sukai da yake duk wanda zashi na kusan tane an siyamai ticket to bayan sun sauka kai tsaye bangaran

hajiya Sa'a aka kai ta aka danka amanar ta cikin mutunci da karramawa ta amshe su tashi sukai a ka kaita ɗakin ta da kafar dama ta shiga a luxury bed ɗinta ta zauna su nuratu kowa sai hotuna suke barin hamziyyah yar tiktok direct wasu bayan sun gama ganin gida aka dauke su a mota za amai da su kano

su nuratu kuwa sai gobe yaye lullubinta tayi ganin gidan yayi tsit ba kowa kallon ko ina take futsari take ji tashi tayi ta shiga toilet ɗin dake manne adakin ta

Ta shiga shagala tayi da kallo yawa mutum zai kwanta fitowa tayi ta ɗauro alwala domin tasan yanzu dai anyi isha salla tayi bayan ta idar tayi addi'o in samin zaman lafiya a rayuwar auran ta duk kan wata fitina Allah ya kade musu ninke prayermat tayi ta bi lafiyar gado ta kwanta duk irin tsiyar da suke mata bata kula su ba

washe gari da safe jirgin su ya ɗaga samha ruƙo aunty salma tayi tana kuka da kƴar aka kwace ta zama tayi tana kuka bakowa ko breakfast ba su tsaya sun ci ba tun safe ammi ta aiko suhaila da rakiba suka kawo

Akan royal sofa ta zauna ta zuba ta gumi wani irin tsoron gidan take baka jin komai sai kukan tsuntsaye ashe mutum ma rahama ne bataji sallamar da yayi ba sai ji tayi an taɓata zubbur ta tashi gumi na yanko mata dariya yayi yace


"Sarkin tsoro tunanin me kike har na shigo nayi sallama baki jiba?,


Ƙasa tayi da kanta ta durkusa ta dauko mayafin ta da tsoro ya sata ta wadar da shi tace


"Ina kwana,


Dagota yayi ya zauna da ita akan cinyarsa ƙoƙarin sauka take amma be bata dama ba yace


"Ni bana son irin wannan gaisuwar nan nake so ba,



Kunya ce ta kamata ta kautar da kai ganin yana ƙoƙarin kamo bakin ta ganin taƙi ya sauke ta ya ruƙo hannunta yace


"Zo muje muyi breakfast ,

Binsa tayi dining chair ya ja ya zaunar da ita ya ja ta kusa da ita ya zauna abaki ya dinga bata tun tana nuƙewa har ta saki sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya tashi ya goge mata baki shima ya goge hannunta ya ruƙe yace


"Muje mu gaishe da ammi,


Bata ƙiba haka ta bishi yana gaba tana baya shammatar ta yayi ya ruƙo hannuta ko da suka zo dai dai kofar ɗakin ammi taso ta kwace amma yaki sallama sukai nazifa da rakiba da suhaila sai ammi duk suna zaune amsa musu sukai har ƙasa ta durkuwa ta gaishe su domin dukka sungir meta hannuta ammi ta kamo tace


"Zonan ya'ta,

Matsawa tayi kusa da ita zuciyar su rakiba ce take suya ashe shi isa yaƙi yarda ya aure su balarabiya zai auro ko ya ko ina tai musu fintin kau ga kana nan shekaru yarinya sharaf da ita tashi yayi yace


"Ni zan fita tun da anmin wariyar launin fata,


Dariya ammi tayi tace


"Kowa na son sabo sai ka dawo yau gani da ƴa'ta Allah ya ,


Murmushi yayi yace


"Amin,


To hira suka fara da suhaila tun bata biye mata har ta fara biye mata bashi ya dawo ba sai bayan magarib be shigo gida ba sai da akai sallar isha tarar da su yayi suna kallo gai shesa suka amsa musu yayi kamar ko da yaushe zama yayi yace


"Ammi barka da dare,


Misfruit da take sha ta dakata tace


"Yauwa ka dawo lafiya?,


afakai ce yake duban inda samha take ta wani rakube yace


Lafiya qalau ya tashi yace sai da safe


Ammi tace


''ba zaka tsaya kayi dinner a nan ba ,


Ƙeya ya sosa yace


"Ammi inna yi wanka naci ko fruit salad ,


Duban inda samha take tace


"To samha tashi kije ki haɗa mai,


Badan ta so ba ta tashi ta bishi tashi raƙiba tayi ta shiga ɗaki ta saki kuka yau zasu kwana tare sai wani kishi ya danni zuciyar ta dole ta bar gidan in kuwa taƙi za adau gawar ta

*BAYAN SHEKARA UKU*

Bayan shekara uku samha ce ɗauke da wata kyakkyawar yarinya yar kimanin wata hudu gifen ta ma'aruf ne ruƙe da yara maza masu kama daya fara re tas da su wato arif da irfan arif yaci sunan abba irfan ya ci sunan abbie macan kuma sunan inna tace ana ce mata afnan cikin sallama suka shiga wani tamkeken gida abba nagani da baba hajara sosai sukai murnan zuwansu bayan sun gaisa sun dan taɓa hira suka tashi za su gidan suhaila da kamal fitowa sukai nana ta gani da katon ciki ta zama abar tausayi tace


"Samha,


Samha tace


"Nana,


Kuka tasa tace


"Dan Allah ki yafe min kinga irin yarda rayuwa ta zamar dani ko,


Cikin nuna jimami tace


'allah sarki wallahi na dade da yafe miki,

Usman ne ya fito ya zama babban mutum gaisawa sukai kyauta tayi wa yarsa ta bawa nana itama ba samha ta zama babbar mace dan a yanxu dgree ɗin ta na hudu take yi amfanin economics tana aican shiga mota sukai ganin irin cin maganin da yake tace


"Habibty yau fushi ake da ni,

Kara hada rai yayi yace


"Bana so in ga kuna magana da wani namiji balle wanda kuka taba soyayya,

Dariya tayi ta kwantar da murya tace


"Haba sweetheart gaisawa mukai muka ai a gaban ka ne ko tunda baka so na daina,


Dariya yayi yace


"Yauwa my lovely wife,

Sosai suhaila tayi murna da ganin ta bayan su gaisa suka je gidan nuratu to shima ba su da deba suka fito inda suka hau jirgi domin komawa gida



Alhmdllh alhmdllh alhmdllh Allah na gode maka da kani iƙon gama littafin nan lafiya


Ranar talata 21-5-2024

Ƙarfe 4:27

Na mallakawa king 👑 and queen 👑 writing chamber




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment