Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ɗan gaba da fatihan nan in muka ƙara masa ? Ita kuma Nuratu macece tana auranta zataje wani gida ta cigaba da haihuwanta mu taimakesu mana mu duba gazawansu mu karba Kila sanadiyyar hakan Allah ya dubemu ya bamu namu!"

"Tab Allah ya kiyasheni abun kunya in riƙe ɗan mai aikina ,me mutanen gari ma zasuce mun ,wai in yara kake so mai yasa bazamuje gidan marayu mu darzo kyakyawa ba ma , why hers?uhum me yasa sai nata ???"





#Vote
#Bamalli's care
09065990265

Mutanen ƙwarai sunyi nisa da biyan kudinsu , Inshaalh zamu gama freepg a page 10 sai ki hanzarin biyan naki don wasan ma ba'a fara ba

Hanyar biya ta Asusun bankin nan
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb
Shaidar biya ko katin mtn ta
09065990265
Ƴan Niger katin Artel ta wannan Number kuma
[11/29, 12:33] أم افنان✍️💞: *🫧SUGAR MUMMIES🫧*

Na
Hassana Bamalli
Oum Aphnan
9️⃣

_Critical bastard as well_

Ahmed kansa ya dauki caji da ƙyar ya shawo kan Fauza ,sannan suka dawo falon ,duk suna nan inda suka barsu basu motsa ba.

"Mr. Man" ya kira mai gadin da wannan sunan

Ɗagowa yayi ya kalli Ahmed "Oga"

"Kana da wani plan ne akan yanda zakayi da cikin jikin Nuratu?"

"Oga banda wani dubara...oga saidai in mutuwa kukeso Inyi"

"Me yayi zafi ? Magana akeyi akan jariri ba wanda zai mutu anan" karaf Fauza ta karɓe maganar

"Tabbas wani zai mutu kuwa , eventually 😑ta yaya zai iya daukan nauyin yaransa da ƴaƴan shegu?"

"Fauza _Calm down_ now, Nuratu kinada wani plan akan _Un born child_ ɗinki?"

Hade giran sama da kasa tayi ba tareda tayi magana ba ta girgiza masa kai alamar ‘A'ah’

"Okay. Dalilin da yasa nayi magana na kawo mafita ne da zai taimaki duk kan ku....Ammmm mai gadi ya kake gani idan na tura maka dubu ɗari biyar a asusun bankin ka zai isheka kaja jari?"

Zubewa akan gwuiwarsa yayi da sauri yina murna yina kwararo masa godiya da Addu'oin nasara a gabaɗaya rayuwarsa.

"Ya'isa ,koma ka zauna ...sai ke Nuratu zamu nema duk hanyar da zamu saki kiyi walwala har zuwa ki haihu daga nan kuma yaronki zai zama namu Ni da matata Fauza" duddulo ido waje Nuratu tayi tana shafa cikinta kamar maijin wani abu .
Sosai ya lura da facial expressions dinta alama ne da yake nuna bata gamsu ba sosai ko bata fahimta ba .

"Yes I and my wife we're intended to adopt your child ,hakan yayi maki?"

Miƙewa tsaye tayi tana girgiza kai alamar za tayi masifa kenan

"Ya Ahmed gaskiya..."Taran numfashinta yayi da sauri kafin yaji me zatace "Eh zan ware maki miliyan ɗaya da rabi"

Girgiza kai tayi alamar ba ta yarda ba fa ,ta coge a gaban su tana karkaɗa ƙafa

Murmushin yake yayi wanda yafi kuka ciwo "To shikenan Miliyon biyu fa"

"Ya Ahmed wai ban gane ba cinikin me ake ba,kawai bazan iya ba period!!"

Gyada kai yayi ya watsa hannuwarsa akan gwuiwoyinsa yina shafawa " _Perhaps_ miliyon uku fa?"

Katse shi Fauza tayi "Wohoho wai menene haka Ahmed Are You drunk? Miliyon daya biyu uku ban gane bane ...ke Nuratu sa idonki cikin nawa ,Ko dai ki bada ɗan ne ko ki fita a gidan nan shawara ya rage ma mai shirin shiga rijiya"

Mai gadi waigawa yayi ya kalli Nuratu "Haba ke ko don dai ɗan shege za'a rabaki da abun kunya ki yarda mana!"

"Karka sake ce ma ɗana shege na fada maka don yina da ubansa !"

Miƙewa Fauza tayi ta kama ƙugu " Fitsara!!!? Nuratu nace ma cikin ki cikin shege nima ,Ko ki yarda da ƙudurin mu ko ki barmun gidana bazamu raini cikin shege ba"

"Haba ke babba ne ki sassauta mata mana kinsan masu ciki suna da saurin fushi ki mata uzuri....Nuratu yaya zaki taimaka ki bamu ɗanki mu baki miliyan ukun?"

"Sai nayi tunani!" Amsar da ta bashi kenan ya juya ta fice a ɗakin.


‘Tabbas Lokaci yayi da Nuratu zaki koma gida ki kai masu kyautar lamban yabon da bariki ta baki (Cikin jikinta)’
Abunda Nuratu ta faɗa a sarari kenan kafin ta soma haɗa kayanta.

•°•°•°•°•°•°°•°°•°°•°•°•°•

Washenkari

Tsaf Nuratu ta gama haɗa kayanta tana jiran su fita aikine taje ta yanki tikitin jirgi V.I.P da kuɗin da take tarawa ta koma ƙasar ta na gado (Nigeria)

Ahmed kam gabaɗaya ya susuce ga damuwa gashi ya koma aikin gida sai ya gama sannan ya wuce aiki ,yauma haka ta kasance dashi ,da sassafe ya haɗa break ɗin Fauza a matsakaicin tray ya biya dashi har ɗakin barcinta

Tana kwance ko tashi barci batayi ba ya shigo
"Weki...weki wake up. Hi durling" yaje daidai saitin goshinta yayi kissing dinta da tray din break din a Hannunsa

Juyi tayi a hankali fuskarta take ya washe ta saki murmushi tayu zumbur ta mike zaune "Good morning my gorgeous,shine har ka shirya kayi mana girki baka tasheni ba? Awnnnnn😍” ta amshi abin hannunsa ta daura akan cinyarta

"Ai nasan kin gajine shiyasa daran jiya ansha aiki😃" hararan wasa ta sakin masa "Me nayi da zan gaji ? Kaiko " ta sa hannu taja kunnuwarsa duk biyun,dariya ya fashe dashi "Ya'isa yanzu ki karya ,ki huta ki barci ba sai kin fita ko'ina ba "

"To shikenan mijina...(dafe kai tayi da sauri) oh no no no! Ina da client da zan gani a asibiti yau,bari ma kaga hujja ta "Nan take ta daburce tana kokarin dakko masa wayarta ta nuna masa wani abun da zai zama madogaranta na fita.

Ransa ne yaji ya sosu ,shidai yinaso ya zama man with authority a cikin gidansa, yana son matarsa ta zama cikakkiyar matar gida wacce zai fita aiki ya dawo yana da tabbacin zai tarar da ita a gida. amma ina bazai yuwu masa da Fauza ba,she too like money!

"Aaaah shikenan shikenan na yarda, duk saboda kudine ko Allah ya tsare _I've to be on my way_ Ni na tafi"

Tuntsirewa da dariya tayi " _Try to provocate me this morning_ "

"I'll 😃" ya Bata amsa yina dariya yayi hanyar ƙofa

"Kayi kyau sosai yau mijina"
Juyowa yayi ya buɗe mata hannuwarsa "Ke kikasa hakan ,jiya da daddare kin bani kulan da ya dace "

"😄😄😄 I do"

Ficewa yayi ya barta tana mika .ta janye tray din abincin ta ajiye a gefe zata fito a cikin bargo sai gashi ya turo ƙofa ya sake dawowa

Marvelously ta tambayesa "Forgot something ? Ehem ka yi mantuwa ne?"

Waskewa yayi ya fara sosa ƙeya "eh ,Aah dama...dama ina tunani ne ,Madam Plz me zai hana mu rage ma Nuratu aikin gidan da takeyi, in yaso sai a samo wata me aikin?"

Caɓe baki tayi "Love wai ka manta Nuratu me aiki ce ? To in batayi aikin nan ba wa zaiyi ? "

"Aah wallahi na sani kawai dai ina duba halin da take ciki ne kinga tanada ciki,banason tana stressing kanta da aikin gida saboda inason ɗanmu yafito lafiyayyen kyakyawa"

"Hello durling,ban taba jin inda akace mai ciki bazatayi aiki ba saboda hakan zai taba girma da wellness din ɗan cikinta ba .
so, _Nuratu must do all her domestic chores_ Kaje aikinka kaji mijina bye ,have a nice day"

Ba yanda ransa ya so ba yaje ya bata feck a saman leɓɓanta💋 ya fice gwuiwa a sanyaye jiki ba laka!.


Nuratu kusan duk abunda suke tattaunawa a kunnenta yake itadai abinda takeso ta samu su fice ta gudu ,don haka tana maƙale ta window har Ahmed ya fice a gidan.

Tana ganin ya fita itama ta sulale ta sunkuci kayanta ta fice a gidan

Zuwanta airport ba daɗewa aka samar mata jirgin da zai tashi da safen nan ,saboda kudin da ta ninnika yasa batayi jiran kwanaki ba kafin visa dinta ya fita ba , tunda nata yayi expire tuntuni
Dukda jirgin ba direct zai wuce Nigeria ba sai ya biya China ya kwashi kaya ya wuce Thailand ya ajiye passenger sannnan zai wuto Africa sai ya sauke tsirarun pasinjojin Nigeria a Lagos ciki kuwa harda Nuratun hakan ya mata daɗi ,ko banza indai taje Lagos ta fara jiyo ƙamshin Kano gida daɗi!.

•°•°°•°•°°•°•°°•°
Ba wanda yasan Nuratu ta bar gidan har sai da suka dawo daga wajen aiki ,nan fa Fauza ta soma ƙorafi an bar mata gida gaja gaja ita bazata juri ƙazanta ba ,waye waye
Ɗakin Nuratun ta shiga nan takaga ko'ina a bubbude sannan ba akwatinta a sama ,ƙwalla mata kira tayi ta nufi toilet tana taban ƙofan ya buɗe ba kowa a ciki ,da sauri ta fito tana kwarara ma Ahmed ɗin kira

A furgice ya nufo dakin nuratu "menene Fauza ? Atimes You scared me"

"Noor ta gudu!"

Ɗif ya ɗauke wuta na ƴan sekonni kafin ya shige ɗakin da sauri da gaske da babu ita

Dafe kai yayi kawai sai ga ƙwalla "Me yasa zakiyi mun haka Nuratu?!"

Haushine ya kawo ma Fauza wuya "And so fucking what in ta tafi ,dama karuwancin tafi so tayi sai taje tayi me ye na kuka akan karuwa..." Wata bahaguwar mari ya sakin mata a kunci

"Karki sake ce mata karuwa in ma ita karuwace to nine kwarton ,kuma ke ce kika janyo ,kuma dole zan bita don tsira da martabar gidan mu da Ni kaina!!!"

Dukda zafin mari da alaajabin yau ita Ahmed ya mara bai kai mata abun mamaki ba yatankacin kalmomin da suke fitowa daga bakin Ahmed

"Ahmed Ni ka mara akan fasiƙar ƴar aikina ? Ahmed kasan ko me kake faɗi? Rashin haihuwa haukane da har zaka ringa magana kamar taɓaɓɓe?"

"Kece taɓaɓɓiya Ni a hayyacina nike ,wallahi bazai yuwu inga samu inga rashiba dole sai nabi Nuratu yau yau dinnan kafin ai mun flushing din yarona yabi rariya don sarai nasan halin annobar Kishiyar uwarta INNA ABU!....."






FLASH BACK✨
(Mafarin komai...Tushen labarin)



Kitumirmira akwai ƙatoton lauje cikin naɗi ,labarin nan dai ba'a soma komai ba ,gashi wannan shine page din kusa da ƙarshe ,ki biya kuɗin ki ta daya daga cikin wannan hanyoyin
7782217014
Mohammed Hassana
Fcmb

Ko katin MTN ta wannan Number 09065990265
Ƴan Niger katin Artel ta wannan Number na sama.
[11/30, 15:20] أم افنان✍️💞: *🫧SUGAR MUMMIES🫧*

Na
Hassana Bamalli
Oum Aphnan
🔟

_Crazy In_Law😄⛹️‍♀️_
#Fun🥳
#Apathy
#Village Islamic kingdom👑

NASSARAWA GRA

Tamfatsetsen Gidan sama ne mai kyawun gaske ,amma tsabagen bala'i har gilasan windinan gidan girgiza sukeyi

Arc. Abu-jafar cikin bala'i ya kalli matarsa Suwaiba yana nuna ta da yatsa

Shekara ta ɗai..ɗai..ɗai takwas ina biyan kuɗin hayan gidan nan da kaina ,ba wanda ya taɓa ji sai don yau kin cika mun dubu Ashirin ...Only twenty thousand kinje kin fada ma uwarki ,kalan gori da cin mutumci ya..."

Ɗaɗɗaga masa hannu ta ringayi alamar yayi shiru kar taji saboda daga dinning area ɗin da suke ta hango shigowar Inna Abu gidan riƙe da hannun ƴar ɗakinta Nuratu ,ta glasses ɗin windown kicin dake facing tsakar gida

Haba tsiya ya rufe ma Abu_Jafar Ido ko kallon matar bai yi sai da yaji an doka masa tsawa

"To mugu ! mai zaisa bazata faɗa mun ba.? Nice nan uwarta dole ta faɗa mun mashiga da mafitar dukiyarta kodon halin rayuwa da mutuwa. don tanada uwa da uba da yara ko da ta mutu kwabo ! baka samu gadonta!"

Kauda kai Suwaiba tayi tana fifita hannu cikin tarin jin kunya

Abu_Jafar sunkuyar dakai yayi ya ɗauki cinyar kazan dake kan abincinsa ya soka a baki zai gutsura

"Dallah jibeka mai mataccen zuciya ji yanda ka luma wani gabza gabzan haƙoranka a cikin kaza ko kunya babu anacin cefanen mata!,haba gaskiya kullum kake mulla ƙiba ɗiyata ke rama!"

Suwaiba miƙewa tayi kamar zata fasa ihu "Haba Inna surukinki ne fa ,kuma bani nayi cefanen ba ma ƙaninsa na Japan yazo ya kawo mana kajin ƙwara hamsin da miliyon guda muyi cefane ga kajin ashirin can ma Abu_Jafar ɗin ya ware a mota za'a kawo maku gida"

Ba kunya ta washe baki "Allah sarki Amadidi,na daɗe rabon da in gansa tun bayan da yayi bautar ƙasa a ƙauyen mu ,Nuratu Abokinkine ya kawo mana kaji ,kice zamuja dabge ,Yina ina Amadun?" Ɗaga mata kai Nuratu tayi tana murza yatsun hannunta,tana washe baki itama tayi kewar Ahmed

Ɗaure fuska Suwaiba tayi bata amsa mata tambayarta ba ,sai Abu_Jafar ne ya haɗiye naman bakinsa da ƙyar yace "Kina nan zakiga ya shigo yaje kai amaryarsa wankin gashine can plazan ƙasan mu"

Washe baki tayi "Allah srki kaji sha'anin su na Attajirai ,Abu jafar gwara dai kayi zuciya tunda an koreka aikin ba komawa zakayi ka maƙale a wuyar mace ba ,kaima dai ka nemi ko sana'ar ƙarfine in na gwamnatin ya kasa samuwa ,ga gidajen bulo nan ko dubu biyu suka baka a rana dame ka manta?"

Ƙwallane yaji ya kawo masa ido

Jan kujera yayi ya mike "To Inna ki neman mun in kinsamo zanyi" Yana gama magana ya juya ya shige ɗakin dake kusa da su .

Waigawa tayi ta kalli Suwaiba ,tana ƙasa da murya kamar munafuka

"Da gaske yike zai iya aikin gidan bulo?"

"Haba Inna aikin fini sani ,ya za'ayi babban mutum kamar abu-jafar kice yayi leburanci ,wannan cin fuskane yana fa raga makine Albarkacin keɗin surukansa ne"

Tafa hannu ta shigayi tana salati "Suwaiba ?! To don Allah kisa abu-jafar yayi ƙuli ƙulin kubura dani ,in yaso akai gawata gida ,kinga mun shahararriya! Nine kike wulaƙantawa akan miji? Aah lallai kin riƙa ,Ni ina kokarin kwatar maki ƴancinki sai ki barbaɗa mun ƙasa a ido?"

"Wannan shine ƙwatan ƴancin Inna? Kullum kina lilo a unguwarnan ko gate ɗin gidan nan ya shaida kalar bugun ƙofarki ,wallahi inna bai dacewa ,ni yanzu ma ya akayi Abu-jafar yasan na fada maki na ranta masa dubu ashirin ya cika ya biya haya?"

"Mai martaba na fada ma wa ,gwara ayi ma tufka hanci kafin ya tatike ki da bashi ki kasa ƙulla abun arziki ,ga Ƴan uwankinan duk da gwalagwalansu na aure ke ga faƙara'u Alal lalurati ,fataralle Sarkin fawan lahira kin siyar kinba miji wallahi bazai yuwu ba ko kinaso ko kina ƙi sai na ƙwatar maki ƴancinki gaba zaki gode mun ko ƙasa ya rufe mun ido,kuma zuwa gidan nan bazan fasa zuwa ba har sai abu-jafar yayi zuciya ya nemi sana'a .
Inyaso in nazo ki gaggaɓe kafafuwana!"

Sunkuyar da kai tayi batace komai ba "Kiyi magana mana ,Allazi miji,Indai namijine kasheki zaiyi ki gode ma Allah da ya baki tsayyayiyar uwa irina!.....Ni wuce muje a bani kajin nawa in wuce dashi don da ɗan taxi nike a waje ,in ma da ɗan agade (plantain) ki zubo mun a leda mu sama na kalacin gobe (Break fast) "

Cije baki tayi ,ta kalli Nuratu "ƙanwata a zubo abincine?"

"Aah saidai ki zuba mun a leda anjima zanci"

"Ku komai a zuba muku a leda sai kace baƙin Mayu?! Kowa sai yasan daga kauye kuke?"

"Allah sarki Suwaiba haihuwa tayi gardama Ni kike zagi ko? Lallai kinyi aure a burni...Nuratu tashi mu sa kai" ta ja hannunta fuuuu suka fita da gudu ta bi bayanta tana kira amma bata tsaya ba

Suna zuwa suka faɗa taxi dinsu yayi reverse zasu tafi ,Gararaf taxi ɗin ya buga ma gaban wata shimfidediyar baƙar mota sai sheƙi takeyi .

Take ya fasa masa madubin gaba
Cak yaja ya tsaya
Daga baya Inna ABU ta fara dannawa mai wancan motan zagi "Shegu ƴaƴan ɓarayi Allah ya isan mu kudin talakawa huhum da ikon Allah yanda ka dakar masa mota sai kayi rani saboda talauci....Ɗan nan wuce muje"

"Aah Baba Ni ne fa mai laifi ki tsaya in basa hakuri karki ja mun ɗauri"

"Kaji lusari ku kukeja ana wulakanta mu ka wuce nace"

A zuciye Ahmed ya fito daga Mercedes GLK ɗin saye yake cikin cream ɗin filtex mai sharara yayi askin funck gashinsa sai walƙiya yake a hasken rana ,fuskarsa manne da shade baƙa kalar takalmin sa da agogonsa masu azaban tsada.

"Hello Mr Idiot bazaka iya fitowa bane shashasha?"

"Kaima shashasha ɗan akuya ƴaƴan ɓarayi wooooo macuta wooooo masu shan jinin talaka"

Damtse mata baki Nuratu tayi "Ya Ahmed ne fa"

Daidai ya fincike hannun taxi ɗin ya buɗe
Cikin borin kunya ta soma bige bakinta "Subhanallh dara taci gida ,ɗan nan i_Haƙuri ban gane ka bane " murmushi yayi fuskarsa ta washe daga ɓacin ran da yake ciki

"Inna ABU laluwa bala'i gida za'a koma da tsakar ranar nan?"

"Eh wallahi maraba na da ganinku baƙin turai,ka ganmu a mota ƙarfe ƙarfeee,Ko muzo ka kaimu a waccan zazzafan motanne irin na ministoci?"

Dariya yayi "Ai dole na kumuje in kaiku Amma zan fara kai Madam gidan Yaya "

Fitowa sukayi suka koma motan ya yi ma mai taxi ɗin ihsani mai taxi ɗin nata basa haƙuri

A mota baya suka ɗuru sai zuba ƙauyanci sukeyi a haka suka gaisa da Fauza mata mai fara'a dason mutane "My love ga Nuratu ,besty ta da nake baki labari na wannan village din da nayi bautar ƙasa ,yarinyar Sarkin garin,itakuma wannan step mom ɗin ta ce kuma ƙawar mamanmu ce tun na yaranta surukuwar Ya abu-jafar"

Washe baki tayi "wow nice meeting you sannunku ,Love yana bani labarinku" caɓe baki Inna Abu tayi "ki saki jiki kiyi Hausa zalla ƴan ƙauye ne nan ,ki bar lanƙwashe murya sake shi ras"

Dariya suka fashe da shi a maimakon suji haushi sun maidata kamar cartoon

"Inna bala'inki na nan?"
"Allah ya rabani da bala'i gaskiya ne dole In faɗi hali zanen dutse ba abinda ya sauya mun sai wanda ya daɗu"

Haka suka isa har ƙauyen su Nuratu

A ƙarƙashin rungujejen bishiyar durumi dake ƙofar gidan suka riski sarki da mutanensa an shimfida manyan taburmi da dardumai ana ta fadanci ya tokare akan kujera kai yasha rawani.

Inna Abu itada da Nuratu da suka fita sarki bai sani ba ta ƙofar baya suka wuce siriri suka shige gida ,shikuma ya tsaya da Anty Fauza suka gaisa ya turota cikin gida suka gaisa da mutanen gida
Da zasu tafi ne ya ɗan kebe da sarki ya ciro kudi mai kauri ya masa ihsani sannan ne ya ɗaura da roƙonsa "Ranku ya daɗe a ƙara kula mana da Iyayenmu don Allah kar kuna nan aje ai masu duka a hanya!"

"Me yafaru malam Amadu?"

Nan ya zayyane masa duk irin tujaran da Inna Abu taso yin masa ya daura da cewa "inda Ni ba dan gida bane me kake gani? Tuni na aikata caji ofis"

Kakabi ya shigayi yina tafa hannu
"Amadu ina nan bansan sun fita ba Ni maganar da Abu take jawo mun ya isheni kamar ba gimbiya ba! ɗaiɗaikun matan ƙauye nan ne batayi fada dasu ba wohohoo"

***
Gidan Sarkin Musulunci Aminu ɗan isiyaku,Ƙauyen iyanbu (Ƙirƙirarren ƙauye a Kano Nigeria)

Gidane babban gidan sarauta Ginin tubali an masa kwalliya da hannun magini ,mai ɗauke da zauruka takwas ,da fankacecen tsakargida,da sasuna uku,na waje wajen shine sashen mai martaba sai cikon biyu na matan sarki,.
Inna ABU wacce ta kasance uwargida mai yara biyar duk mata. Babbansu saude tayi aure a Lagos sai saratu a Kaduna ,suwaiba a Cikin garin kano sai cikon biyun Wasila da Rafa'atu sune ƴan mata

Sai kuma Iya Talatu wato amarya mai yara biyu Nuratu da ɗan autan sarki Nuraddeni.

Akwai kyakkyawar zaman lafiya tsakanin zuriar wannan gidan ,ba kishi lafiyar Allah,kullum tare ake cin abinci sannan kowa yana kaunar dan uwansa

Nuratu wanda suke saanni da Rafa'atu gaba-daya ta dade da zama ƴar ɗakin Inna Abu ,kayan sallanta yina dakin Inna Abu tare suke zuwa don haka ɗaiɗaikun sirrin Inna Abu ne bata sani ba ,ta ɗauke ta tamkar aminiya

8pm
Lokacine da sarki yake tara rankatakaf iyalansa ya masu karatun addini In an gama mai tambaya yayi

Yau ma haka ta kasance kowa ya haɗu a baranda da littatafansa harda Iya Talatu Inna Abu ne kaɗai babu ita .

Falfalfal sarki ya fara fallo littafin gabansa ,kafin ya soma shafa gemu yana hamdala

"YAWWA ina Abu?" Nuratune tayi karaf tace "Tana ɗaki taje sallar ishai"
"Maza kirawota wannan darasin da ita ya dace"

Saida abu ta gama laƙaiƙaitan ta ta fito don ta tsani karatun nan na dare.

"Yawwa zauna nan gefene kisa kunni da kyau kowa ma yasa kunne" akace "To"

"Wasallalahu Alal nabiyyil Kareem Amma ba'a da yau BABUN ISTIGIFARI...Babi akan neman gafaran Ubangiji!"

"Shidai tuba yana tabbata ne bisa sharaɗi _Annadamu Ala ma fata_ yin nadama akan abinda ya wuce ,dakuma niyyar bazaka sake aikatawa ba daganan in ka cutar da wani da bakinka ko aikinka sai ka rokeshi ya yafe maka ,sannan kayi ISTIGIFARI Ubangiji ya yafe maka ,kinajina ko abu?"

"Kai mai martaba na gaji wai karatu kake koyawa ko ci mun mutunci kake son yi ? Kai koyarwanka mana ka daina sa sunana"

"Aah nidai bance ga tijaran da kikayiwa Ahmadu a hanya ba,kuma bance kin fita kinje kinci mutuncin mijin Suwaiba ba tareda izinina ba kawai karatu mukeyi"

Ras gabanta ya fadi sai kuma ta fuske tana muzurai haka ya dinga zuba karatu itakuwa sai raba ido takeyi tana tunanin hanyar neman kudi sam bata jinsa ma

Saida akwa kwashi kusan awa biyu kafafun kowa yayi tsami wasu ma sun fara barci duk an gaji an daina fahimta kana,ya ɗago ya kallesu a tsaya anan ko a cigaba?"

Kowa bazai iya cewa ya gaji ba don haka sukace a cigaba

Zabura inna ABU tayi "Kwarankwatsa na gaji a tsaya haka nan ,ke Nuratu zo muje ki kiramun Madam Kareema a waya na kar dare yayi ban sameta ba ,yau sai naci mutuncin Ahmadu da Abu-jafar sai na nuna masu ba sune sa'oina ba uwarsu ce daidai dani "

Taja hannun Nuratu fiii suka shige ɗaki

Kwance zani tayi ta ciro wayarta a lalita "karɓi nan Latso mun karima Madam"

Da sauri ta karba tana murna za'a tuzarta su Ahmed dama taji haushinsa wai bai kulata ba

Sallaman BABA ZULAI Ne ya karaɗa gidan

"Sallamanku dai masu gaida Aminiya kina ina?"

Washe baki inna Abu tayi ta buɗe murya "Maraba lale marhabin SARKIN NOMA da kanki(ta kirata da sunan mijinta) shigo mana"

Tafawa sukayi nan suka sarƙe da hira

"Ke ban baki labari ba ,tafiya Habuja danayi Allah ya hadani da taƙadiran ƴaƴansu ,kinsan me sukayi mun ? Wai na gansu sunata tsalle wai kamfanin MTN tana bada kyautan kudi ,jikina na ɓari na miƙa wayata nace a sa mun lambobin suma su zuba mun ....kinsan Allah suna sa numbobin sai ga ɗari biyar saaaa
Nan na mike na fara rawa ,abun mamaki sai suka fara dariya wai ai bashi suka bani,nan murna ta koma ciki ,ABU kinsan dai yanda na tsani bashin mtn ɗin nan ,don haka da sauri na kwaɗa ma kamfanin kira ,watanan jairar matar ta ɗauka,nan na ce mata

"Ranki ya dade naga an bani bashin dari biyar , Madam don Allah ku kwashe ,bada sanina bane na dannan lambobin kuka turo bashin" kinsan me jairar tace

Kostoma kayi hakry in baka gane abuba ka ringa kiran numbobin agajin mu don karin bayani "

Ai bansan sanda naja tsaki ba na hau surfa mata bala'i "to wallahi zaku sani,ɗari biyun baya ma da kuka bani haka kuka sa duk na urunce da kyar na biya,yanzu kun lafto mun 500₦ bayan kunsan bashi da ruwa kuke badawa ko ,zaku sani Kwarankwatsa ban biya"

Fashewa da dariya ABU tayi "hhh komfuwutan kike tsiya da ita ? A banza man kare to ya kuka ƙare?"

"Kashe wayar nayi,ai batasan ƙaryan mugunta ba kiran mutane nikeyi muyi ta hira a cinya kudin ƴan asara bazan biya ba dai"

Waigawa ABU tayi ta kalli Nuratu dake gefe tana dariya "Ke kiramun kariman mana ko sai tayi barci?"

Zulai waro ido tayi "yawwa maganan karuwa fa nazo dashi wallahi Nomau ma baisan na fito ba ,ke Nuratu bamu waje"

Tana fita suka manne suka fara ƙusƙus
Abun Alkhairi nazo maki dashi,akwai kasada amma akwai riba ga samu yanzun nan sai ki kuɗance"

"Menene wa zamuje mu zane a bamu kuɗi?"
Zaro penis (Bura) na roba da pant mai haɗe da gadil tayi a jakan hannunta

"Kinga wannan shi ake kira da gadil shi yake flatning tummy....kiga rusheshiyar mace da ƙaton tumbi amma tana sakashi sai ta tsuke ta dawo ƴar yarinya ,matan birni sunyi nesa wajen sai dasu ,wannan kuma..." Ta daga Buran

"Hmmm baa magana bazakisan amfaninsa ba amma su matan Alhazan sunsan aikinsa ,wallahi daga zuwana Habuja karkiga camaman da nayi na kalmaso kudina na dawo ,shine fa nace wannan abun alkhairin bazan samu in cinye Ni kadai ba sai na gayyaci ƙawata ko ya kikace ?"

"Zulai wannan ai kayan karuwai ne ina Ni matan sarki ina wannan harka?"

"Baga Nuratu ba sai ki hadani da ita ki zuba mata,su da kayan maganin mata irinsu karya gado ,kwallin me gida idonka idona ta soma zaga maki dashi akwai fa Alkhairi yanzu zaki siya gidaje da gonaki in kinyi karfi mu fara

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment