Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sum sum Suka bar wajen,Nusaiba babu abinda take da buri face ta samu mijjn aure ko ba me kudi ba amma ta rasa me sonta yanzu duk irin farin jininta yanzu babu ko wani ya fara tunanin zuwa a unguwar za a fada Masa gaskiya halin Nusaiba da uwarta sai mutum ya fasa zuwa,akwai mutum biyu ma sunzo amma tun daga zuwa daya Nusaiba bata sake ganin sun Zo ba an zuga su a unguwar ,wannan karon Ido rufe take Neman miji ko ba me kudi ba ma amma talakan ma ta rasa shi.

Yau tana part din Amarya tana Mata uban aiki Landlady taga tana hawaye,tace Nusaiba lafiya? Nusaiba ta zauna ta bawa Landlady labarin abinda ta shuka kaf tana kuka tace yanzu miji nake nema ko talaka ne wlh Zan zauna na rike mijina amma Kinga talakan ma na rasa duniya me yayi, Landlady tace wlh kin bani takaici ko Mene ke Kika jawowa kanki Nusaiba yanzu ai an waye kina gani yanzu manyan mata ma kula suke da mazajensu bare Yan matan yanzu,shawarar da Zan baki ki yiwa iyayenki Biyayya har Maman taki ki samu Wanda Kika batawa ki tabbatar sun yafe miki sannan ki dukufa da addua ba dare ba rana Allah zai kawo Miki miji kin samu dama me kyau har biyu kinyi watsi da ita ai gashi nan yanzu son kudi da son zuciya da hauka sun kaiki sun baro yanzu wa gari ya waya? Nusaiba tace Inshaallah zanyi yanda Kika ce,Nusaiba haka ta sake gyara halinta tana ta Addua tana yiwa mahaifinta biyayya amma ta kasa zuwa Neman yafiya wajen Sufyan da Aslam sabo da kunyar abinda ta aikata.

Mama tana Kauye lokacin da Nusaiba ta kwashe kudin tsohuwa Yan gidan Suka samu Mama Suka zo Suka tasa ta gaba lallai sai an biya su kudin me daddawa Suka kwace karamar Wayar Mama tare da siyar da ita dubu hudu Suka dauke dubu Uku dubu Daya Suka jefawa Mama canjinta,ita kanta Mama wahala ta isheta baza ta iya ba gashi lokaci Yana ta tafiya haka ta hado komatsanta ta dawo ta tafi gidan su Siyama tana rokon Kawu yasa baki Shehu ya maidata wallahi ta gane kuskurenta baza ta sake ba,Kawu yace ai Kinga irinta yanzu gashi kalleki dan girman Allah kin dawo sai kace dodanniya ,kin ganki Kuwa sai kace horror ba kyan gani da ace da dare ne na ganki ai sai na Suma idan nayi arba da kamanninki sabo da zance gamo nayi,Kawu ya gama Mata tatas sannan yaje ya samu Yan uwan Shehu ya lallabasu aka Kira Shehu aka zauna dashi akan yayi hakuri ya maida Mama,aka buga aka buga Shehu yace bai yarda ba,an rasa inda za ayi da Shehu har Mama ta kwashe kwana uku gidan su Siyama Shehu bai San da zamanta bama,sai da ta daidaici Sanda yake dawowa daga masallaci da sassafe da sauran duhu ta fice ai Kuwa taci sa'a ya dawo ta tare shi,zubewa tayi a kasa tace dan Allah Shehu ka yafe min wallahi bazan sake ba na tuba kayi hakuri dan girman Allah, Shehu ko kulata baiyi ba ta rike rigarsa tana kuka tana rokonsa ya fisge rigarsa ya shige gida bangaren Amarya,haka ta dawo jiki a sanyaye.

Duk dangi da duk me fadawa Shehu yaji yaje wajensa akan Maganar maida Mama dakinta Shehu yaki landlady da kanta tayi Masa magana yayi hakuri ya dawo da Mama ko dan yaranta amma Shehu yace ba ruwanta wannan tsakaninsa da Mama ne dole ta kyale shi.
Kawu ne yace yanzu shawara ta karshe ki tafi gidan Aslam ki roke shi yayiwa Shehu magana Indai Aslam ya sa baki to aurenki zai koma dai dai amma Indai ba Aslam ba Sai dai na fada Miki ta bature Sorry Sorry.
Mama tsoro ya kamata tace Aslam din da ya tsane mu ko naje bazai kalleni ba karshe ma ya ci min mutunci Aslam baya kaunar mu ko daidai da kwayar zarra ne,ai yayi dai dai mene ne baku Yi Masa ba lokacin Yana auren yarki idan zaki je kije idan baza ki je ba to gobe ki bar min gida na gaji cewar Kawu,Aunty tace idan tsoro kike ji zan rakaki,Mama tace dan Allah ki rakani wallahi idan naje Ni kadai Aslam zai iya harbe ni da bindigarsa ni tsoronsa nake ji yanzu ban taba sanin Shu'umi bane sai da ya rabu da yata sai da ya rama abinda Muka Masa babu irin bakanta Mana zuciya da baiyi ba abin nan ya min ciwo karshen cin mutunci Aslam ya kashe kudi me yawan gaske aka Yi min kishiya kalli gidanta kalli namu ta fashe da kuka Aunty sai da abin ya bata dariya Aslam yayi dai dai cewar Aunty.

Washe gari da Yamma Sunday Aslam Yana gida Yana zaune a center carpet Yana shan lemo Yana aiki a system Siyama kwance take a cinyarsa tayi dai dai da dan cikinta tana ta Wasa da botin din rigarsa Suka ji door bell sai da dan cikin Siyama ya motsa sakamakon karar da yaji ba zato,Siyama tace wash dan cikina zai fasa min ciki ni bana son karar nan tsoratani take yi yace Zan cireta to tunda baki so amma idan muna sama fa taya za muji knocking? ai idan na haihu sai a maida yace to ba damuwa,tashi ki bude kofa Siyama direct tace bazan iya ba wlh na gaji kayi hakuri,dariya yayi yace wannan ciki Ina ganin ta kaina da shi,tashi to na bude Siyama tace bazan iya ba dan Allah karka tashi naji dadin kwanciyar nan Allah kace su shigo mana,Aslam yace yau baza kiji kunyar ba kenan? Tace ko Kawu ne sai dai yayi hakuri bazan tashi ba,da Kansa yace ku shigo Aunty ta bude kofa tare da shigowa bayanta Mama ce sanye da Hijab,Aslam Yana ganin Mama ya daure Fuska tam ba mutunci,Siyama kuwa bata tashin ba kamar yanda ta fada,Aunty ce ta harareta ba shiri ta mike zaune a gajiye ba dankwali ma a kanta doguwar rigace a jikinta Yar kanti tace Aunty Sannu da zuwa,ta gaishe da Aunty ta gaisar da Mama ta amsa tana washe baki harda cewa Siyama Allah ya raba lafiya,Kitchen ta shiga ta kawo musu lemo da snacks ta zauna kusa da Aunty ko minti daya bata Yi ba ta kwanta a cinyar Aunty,Aunty tace ke dagani a kanki aka Fara ciki da kinzo waje ki kwantawa mutum a jiki,Siyama kin tashi tayi har Aslam ya gaida Aunty Kawai ko kallon Mama baiyi ba ya mike zai haura sama Aunty tace Aslam wajenka nazo fa,dawowa yayi ya zauna yace Aunty gani,Aunty tace wata Alfarma nazo nema wajenka dan Allah Aslam abinda Mama da Nusaiba Suka maka ka yafe musu kayi hakuri Allah ma Yana yafe Mana bare dan Adam ka yafe Mata,Mama ta karbe harda durkusawa a kasa dan Allah Aslam ka yafe min nasan munyi maka laifi ka yafe min dan Allah,Aslam ya kalleta shekeke bai ce kala ba,bazai yafe ba,Aunty tace kayi hakuri Aslam Allah Yana son bawa me hakuri da yafiya,ganin Aunty ce take ta rokonsa Kawai yace to amma fa bai ce ya yafe ba,Aunty taci gaba tace dama Shehu ne tunda ya saketa yau wajen watanta hudu yaki ya dawo da ita babu irin hakurin da bata bashi ba yaki yarda kowa a dangi da Yan Uwa har abokai sunje wajensa akan Maganar yaki amincewa,Kuma wlh ta tuba ta gane gaskiya a matsayinta na Yar uwa musulma akace yau Allah ya shiryata ai abin farin ciki ne ga mu musulmai to dan Allah ka sa baki kayiwa Shehu magana ya maidata Kaine kadai zaka fada Masa yaji dan Allah,Aslam ya gama Jin Aunty yace ni Aunty mene hadina da iyalin Abba Shehu,Ina yaro me zai kaini shiga zancen manya in yaga dama ya dawo da ita idan bai ga da ba ta hakura ta koma Kauye inda tafi wayo ni ba ruwana da ai bata san dan Adam me daraja bane bata taba zaton ma Zan Mata rana ba a rayuwa,Aunty tace bana son taurin Kai Aslam ya Ina rokar ka kana botsewa,yace Aunty shike nan taci darajarki albarkacinki Zan Masa magana amma bata da matsayin da Zan taka har can wajensa Zan dai kirashi a waya kawai in ya yarda tayi murna idan bai yarda ba ruwanta mutum dai abinda ya shuka shi zai girba Kuma Alhmdllh ko yanzu tun a duniya ba ayi nisa ba sun Fara girban nasu hukuncin,bazai yuwu ka shuka gero kace zaka girbi shinkafa ba bazai yuwu ba kowa yayi yanda yake so to bazai ga yanda yake so ba, idan Kuwa kayi abinda baka so to kuwa zaka ga abinda kake so haka rayuwa take,basai Yar taki ta auri me kudin ba jarinku kuci gaba da cin duniya gashi nan talaka ma ta rasa yanzu sai ku nema Mata hatimin annabi Yusuf ta sha ko ta samu ko talaka ne abinda bakwa so din dai...Aunty ce tace ya Isa haka Aslam idan baza kayi ba ka Mana Shuru ni ban ma San haka kake da mugun riko ba,Aunty baki San me aka Masa bane har uwarsa sun zageta babu wulakancin da basuyi Masa ba cewar Siyama,Aunty tace bana so Siyama gyara nazo bana son tone tone ke me Miji Zaki zake ki tare masa Maman Nusaiba ai uwarki ce kema,Mama tace Siyama kiyi hakuri ki yafe min,Siyama tace ni baki min komai ba zagina nane da tsine min da kuka yi Kuma kanku ta koma to haushin me zanji,Aslam yace ko ma dai mene dan kanku Kuma ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba Zan Masa magana,Aunty tace yawwa ko Kai fa Basu dade ba Mama tana Jin tsoro ta damu sai an tafi Aslam tsoro yake bata,ai Kuwa Suka tafi Suna tafiya Aslam yace lallai Aunty ai Kawai lallaba su nayi ba inda zanje ko waya bazan Masa ba ta shekara dari bata koma gidan Miji ba,Siyama tace a'a fa ka riga ka fadawa Aunty yanzu jiranka zata yi kayi hakuri dai kayi Masa waya sabo da Aunty idan baka yi ba ka raina min Iyayena fa Kuma ni nasan mijina ba haka yake ba Wanda na aura me yafiya ne da hakuri yace naji Mrs Aslam zanyi ku kyaleni na Sha ruwa please,Jikinsa ta koma ta kwanta.

Yaran Mama Kuwa tunda Suka ji tana gidan Kawu kullum suna gidan Wajen uwarsu Yara da mahaifiyarsu akwai shakuwa ta musamman sabo da yaran Aunty da Kawu Suka dage Shehu yayi hakuri ya maida Mama sai Nusaiba itama duk da Shehu Yana Mata fada haka take bashi hakuri bata gajiya amma Shehu ya kafe yaki abinka da me hakuri bai iya Fushi ba, Landlady ce ta siyowa su Nusaiba kayan sawa harda takalma da kudinta ganin Basu da suturar arziki Musamman Nusaiba da Sufyan ya kwace Mata sutura gaba daya ya hanata shi yasa bata da kayan sawa,Aunty har Raudah ta bugawa waya tace dan Allah ta hado Mata kayan da zata bayar kwance ta Aiko Mata zata bawa Yar mijinta bata da kayan sawa,haka Raudah ta ciko Leda da Kaya masu kyau kusan ma sababbi ne Landlady ta bawa Nusaiba kala bakwai a ciki sai Ihsan da take Yar budurwa itama aka bata wasu a ciki kala hudu, har takalma kala hudu Raudah ta bada da mayafai duk aka bawa Nusaiba,Nusaiba tana murna sosai wani bangaren Kuma idan ta tuna tsiyar data shuka da daular da ta shiga ita da sutura ma Sai dai ta bawa wani yau ta dawo gidan jiya ita ake bawa kwance a rayuwarta ta baya talla ne Kawai bata dauka ba,Watarana cikin dare sai kuka take tilka ta koshi.

Tunda Aslam yace zaiyi ma Shehu magana ya manta ma da batunsu har an wuce Sati biyu Mama tana jira a gidan Kawu,Kawu ma yaji Shuru Shuru waya ya bugawa Aslam da Kansa yace bayan sun gaisa yace Aslam kaci gidanku Ina batun Maganar da kace zaka yiwa Shehu akan matarsa,Aslam sai yanzu ya tuna ma da batun Yana Office ma yace Kuyi hakuri wlh na manta,ka manta ma kace cewar Kawu,Aslam yace Bari na kirashi yanzu yanda Muka Yi zan sanar da ku,Aslam Shehu ya Kira bayan sun gaisa yace Kawu dama magana zamuyi,yace Ina jinka Aslam,yace Alfarma nake nema a wajenka Abba,Shehu da sauri yace Fadi Aslam ko Mene shi Inshaallah zanyi maka,yace akan Mama ne dan Allah kayi hakuri Allah ma muna Masa laifi Kuma Yana yafe mana bare dan Adam musamman ma Wanda yasan yayi laifi ya tuba ya gane kuskurensa,ko dan yaranta ma kayi hakuri yaran zaka duba,Shehu ko musu bai iya yiwa Aslam sai yace dama Ina sonta ai iskancinta ne yayi yawa bata da mutunci ko kadan amma zata dawo Inshaallah tunda kayi magana Inshaallah Zan dawo da ita amma ka kyaleta ta Kara Shan wahalar rayuwa tukun nima sai na gama amarci na sannan ta dawo yanzu Kam kace ta koma Kauye zan Mata magana,Aslam Yana dariyar Shehu Wai sai ya gama Amarcinsa a fili yace to Abba za a fada Mata na gode,Aslam nan take ya Kira Kawu ya fada Masa yanda sukayi da Shehu,Kawu yace Alhmdllh kaga kaima ai ka samu lada yanzu bari na sanar mata.

Kawu Mama ya samu yace ki godewa Allah Aslam yayi Miki rana Wanda duk duniya babu me miki irinta ya sa Shehu zai maida ke dakinki amma yace ki koma Kauye zai Miki magana da Kansa,Mama ta fashe da kukan farin ciki tace dan Allah ku barni a nan ku taimakeni Kauye wahala inda kasan Ina cikin wuta,Kawu yace ai yace Indai a nan kika zauna bazai dawo Dake ba ai da sauri Mama ta Fara tattara kayanta zata tafi kauyen nasu haka,Kawu yaji tausayinta amma gwara ta Sha wahala sosai yanda ko ance ta sake yin wani abin baza tayi ba,Haka ta koma Kauye taci gaba da Shan bakar wahala a gidansu tunda ba iyaye ne da ita ba a gidan Yan Uwa ne Kuma Yan uwansu kaf basu da mutunci kowa dan iskan Kansa ne kudi Kawai shine mutuncinka a idon su,Gashi idan tana so ma a San Mata abincin sai taje anyi aiki da ita a gidan surfe da daka sai tayi dole,hannun Mama yayi kanta yayi kaushi sabo da wahala,gashi Shehu Shuru har ta sake yin wata guda a kauyen su Nusaiba sai rokonsa suke Yi har kuka sai da Suka yiwa Shehu sabo da Ameer yaje yaga halin da mahaifiyarsu take ciki,Shehu sai lokacin ya nemi yan uwan Mama maza Suka Yi magana za a sake maida aure sabo da ta gama Idda tuni,bata sani bama sai Yan uwanta ne Suka sanar Mata an maida Aurenta da Shehu,Zabura Mama tayi gwanin tausayi tace yazo ne? Yace ae yazo ya koma ma yace idan kin shirya ko yaushe zaki iya tarewa a dakinki,Mama tace yau Zan koma ai tsofaffin gidan Mata Suka ce ai Kya tsaya dai ki gyara jikinki,Suka hana Mama Sai lokacin suke bata abinci ishashe sabo da sunji taci gaba zata koma birni lokacin abinci sai ta ture,har kyautar Sabulai da su Omo suke bata Kuma ta daina taya su aiki amma abinci sai ta ture,kowacce sai ta bata kyautar magungunan Mata na gyara jiki,Mama sabo da an Mata kishiya ta dage da Sha tana ta gyara kanta bata aiki kaushin Hannu duk ya gudu babu tayi Yar kibarta da haske,sai da tayi gyaran sosai sannan ta shirya wasu dattijai su biyu Suka rakota gidan mijinta,Yaranta sai rungumeta da murna Kamar me,Su dai dattijai suna kawota Suka koma Kauye abinsu,Yaran Mama sun zagayeta suna ta murna yau sun rasa inda zasu saka kansu,Nusaiba ce ta kawo Mata abinci a plate da cokali harda siyo Mata lemo, Mama ta bude abincin ta ga shinkafa da Miya da nama harda salat,Mama yaushe rabo tace haka kuka ci gaba a rayuwa? Nusaiba tayi dariya tace Mama ai yanzu Abba abinda muke so muke dafawa,haka yake cewa mu zabi abinda muke so,Ameer yace kinga shagon Abba da kasuwancinsa ya bunkasa sosai, Mashaallah cewar Mama ta Fara antaya loma sai da taga bayan abincin nan tas,Nusaiba tace a Karo miki? tace na koshi Alhmdllh,duk da haka Nusaiba sai da ta tsamo Mata nama a tukunya kusan guda goma tace Mama cinye nasan yanzu kina yiwa mutum baki ko tsinuwa zata Kama mutum sabo da rashin cin nama akwai dafi me zafi yanzu a yawunki,Mama tayi dariya tace sai ku kuka da kanku amma ai kullum Albarka nake saka muku ko laifi kuka min naji haushi a bayan idon ku sai nace na yafe muku Allah ya muku albarka,Nusaiba tace badan Aslam ba shike nan Mama baza ki dawo ba,Mama tace ke dai bari Naga rayuwa yanzu fatana ki samu miji ko talaka ne, ameen cewar Nusaiba zanje Nima na nemi gafarar Aslam da Sufyan.

Shehu dai a ranar ma Mama bata ganshi ba haka ta kwana ita kadai,washe gari da Yamma Nusaiba ta shirya ita da Ihsan kanwarta ta rakata Suka Fara zuwa gidan Sufyan sun ci sa'a Yana gida dake weekend ne,shima matarsa tana da ciki,matar bata San su waye ba ta sauke su cikin mutuntuwa Nusaiba sai kallon gidan takeyi komai an zuba sabo,Sufyan ne ya fito ya ga Nusaiba abinka da so,Sufyan gangariyar so yayiwa Nusaiba tsakani da Allah bai wani bata Fuska ba tunda yasan shima Yana da laifi tana da aure ya dinga soyayya da ita,gaisawa Suka yi tace zuwa nayi na baka hakuri ka yafe min abinda nayi maka,Yace oh ba damuwa na yafe Miki Nima ki yafe min munyi kuskure Allah ya yafe mana,tace na gode ta mike zasu tafi ya bata 5k taki karba sai Ihsan ya bawa ita Kuwa ta karbe Suka wuce gidan Aslam

Tunda tazo bakin gate ta Fara hawaye ta tuna haukar da tayi da wannan gidanta ne ta cuci kanta,Ihsan tace Aunty kiyi hakuri haka kin Riga kin cuci kanki Siyama ta Shige gidan kunyi change kawa da kawa Kun auri miji daya haka Allah ya rubuta sai kin Fara Shiga gidan itama gashi tazo ta Shige ta fiki wayo da Imani Aurenku Aunty kawaye ko wacce ta dandani zumar Mijin Daya shike nan 50-50,Nusaiba tace yau na shiga Uku ubanki Ihsan wato har kinyi girman da Kika San mene zumar maza zanci Ubanki wallahi sai na fadawa Abba yaci ubanki wato Yar iska kike so ki dawo,Nima fa Aunty na Isa auren nan wlh 18yrs fa komai na hada wlh ina samun miji aure zanyi ni dai,gashi nan a novel nake Jin soyayya idan Muna karantawa a makaranta a Wayar wasu friends, writers da basa tsaftace alkalaminsu wani ka rantse Bf kake kallo,Nusaiba tace ai wasu na daya daga cikin Wanda suke gurbatawa Yara tarbiyya komai fada akeyi gatsal batsa tun farko har karshen novel yawanci ma yaran Mata sunfi manyan matan karatun novels,Allah ya shirya yasa su gane su gyara alkalaminsu wajen rubutu sabo da tarbiyyar yaranmu masu tasowa gaba,Ihsan tace to Aunty da dadi auren? Baki Nusaiba ta bude tace ke in kina da saurayi ki fito da shi gwara a Miki auren nan, Ihsan tace Ina da abina,dariya ta bawa Nusaiba suna rike da hannun juna tace waye? tace Mahmoud wani yayan kawata ne manager ne a bank baki ganshi ba Aunty ya hadu mugun sona yake kin San na fiki haske duk gidanmu nice ziza haka yake ce min Zizata,Nusaiba tace ba karya Ihsan na yarda to kice ya dinga zuwa zance,tace dama ce Masa nayi Kar yazo Abba zai dukeni,kice yazo kina yin candy sai a daura mu Sha biki,Murna Ihsan take yi writers sun ruda yarinya da soyayya.

Suna compound na gidan Aslam sai ga motar Aslam ta shigo ya dawo, door bell Nusaiba ta danna amma Siyama tasa an hanata yin kara,knocking tayi Allah yasa tana kitchen ta fito tace Baby tare da bude kofa ai Kuwa Ihsan ta washe baki tace irin Yan Novels,dariya ta basu Siyama tace kune a gidan ku shigo suka shiga kamshi da sanyi Yana dukan su,Siyama tace yau an tuna da kawancen kenan? Nusaiba tace uhm zuwa nayi mijinki ya yafe min ko na samu hakkinsa ya daina bibiyata na samu mijin aure,Siyama tace Inshaallah ma ya yafe Miki Nusaiba,Duniya kenan Wai Nusaiba ce yau ke neman Yafiyar wani,bana son Iskanci tunda kin aure shi da shegen munafuncinki da kutungwila ai sai ki kyaleni,Dariya Siyama tayi tace kece Kika yiwa kanki fa Nusaiba babu laifina,Nusaiba tana dariya tace da laifinki Mana tunda kece kike kula da shi idan ba shishigi ba Ina ruwan Yar aiki da kula da mijin matar gida,to ita matar wa yace tayi wasarere da mijinta,Kinga mu ki kawo mana kayan dadi muci karki dame mu cewar Nusaiba,Siyama ta kawo musu abubuwan ci da sha sai lokacin Aslam ya turo kofa tare da shigowa,Siyama ta mike taje tana Masa oyoyo oyoyo harda Masa kirari ga hantsi leka gidajen kowa,me karya icen dawa sai giwa,hadarin sama zo da jido ko tsawa,angon Siyama Oga yazo, Kaine da gidan Kaine da dakin, bakaki me karya gada,ko su bi ko suki sai dai su bari, abi oga a zauna lafiya,Oga karya kafafun arna,aje gari ya jima sai kwarya,sunyi bakar tafiya ka kayar,Dan asali kuji babban suna,sai an Kai su tasha ko sunki,dariya yakeyi shi mamaki ma Aslam yake sai kace wata Yar tauri yanda ta iya kirari kamar me Waka kullum da Kalar da take Masa ba irin na baya ba Indai tana nishadi to zai Sha kirari sai dai ya tsaya Yana kallonta Kuma wani Dadi yake ji sai yaji Kansa yayi wani gingiringim, rungumeta yayi tana dariya itama hannunsa ta rike ta kaishi ya zauna ta kalli Nusaiba da Ihsan Wanda Suka zuba musu Ido suna Shan kallo Siyama tace ga Sadauki ku gaida shi,Sadauki Aslam shi Kuma an murtuke Fuska ba raini,Nusaiba tace Ina yini wani kallon banza ya Mata da kyar yace lfy,Ihsan Kuwa tana gaida shi ya amsa da fara'a yace ya school tace Alhmdllh,Siyama tace wannan ba karatu take ba na Santa har gidan kawarta take tafiya karatun Novel soyayya ta sani Kawai,Ihsan tayi dariya Nusaiba tace ta ya Kika sani? tace ni da tayi a gabana naje gidan kawata ce yayar kawar Ihsan basu San Ina wajen ba in Banda zancen aure ba abinda sukeyi wallahi ku aurar da ita da wuri Ihsan Nema take ta lalace,Ihsan Fuska ta boye tana Jin kunya a hankali tace ai Ina da saurayina,Aslam yace ae lallai da gaske ne,Siyama tace kaji ko Baby na fada muku,bakya so kiyi karatu me zurfi? Aslam ya tambaya,tace ai yace zai biya min a gidansa sai nayi a can dakin mijina,dariya ta Kama Aslam Wai dakin mijjnta,Yace to Masha Allah,Nusaiba ce ta katse hirar tace Siyama tana mintsinawa Siyama Ido Wai ta yiwa Aslam magana,Siyama tace Sadaukina Nusaiba fa zuwa tayi ka yafe mata abinda tayi maka shi Kawai take bukata,ke dan Allah saurara karki min wannan zancen bana so ya mike ya haura sama abinsa ya barsu,Siyama tace tab akwai aiki,yanzu abinda za ayi Zan ta rokar Miki shi Inshaallah zai hakura,Nusaiba jikinta yayi sanyi tace dan Allah ki taimaka Kawata,Siyama tace karki damu,Nusaiba tace Bari mu tafi Kar Mama tayi Mana fada kin San yanzu Mama an San annabi ya faku,dariya Suka yi Siyama tace Ina zuwa ta haura sama da sauri ta shiga bedroom ta samu Aslam ya tube zai shiga wanka yaga ta bude akwati tana eban turaruka da kayan make up ya kalleta yace Ina Zaki Kai su? tace Nusaiba Zan bawa,yace bada abinda na siya ba zube yaje ya kwace kayan ya maida akwati ya kulle abinsa,Siyama ta Bata rai tace to ka bani kudi na basu kudin mota,yace badai kudina ba Indai Nusaiba ce baza ta sake cin kwandala ta ba har abada,Wai mene Haka Baby ai ni zaka bawa na basu ba wai Kai ka basu ba,bazan bayar ba bana son musu,tace fine ai na tuna Ina da abubuwan da Aunty ta

Please Login or Register in order to submit comment