Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Volume Dan Kar naji,Affan yace wanne irin rage Volume nu ban danna komai ba kina gani waya Kawai nake,Raudah ta sake manne jikinta a nasa tasa hannunta tare da sakalo shi ta wuyansa tace ni na gani Sanda ka Danna Kaine baka kula ba,Ohhhh Wai me yasa kike min haka,Raudah tsoron fadansa taji tace okay naji amma dai ka kula saurayine da ita fa ba Miji ba,Affan ya girgiza Kai Kawai yace to aiki nake koma ki kwanta,Raudah tace oh korata kake Yi sabo da kayi waya da mace har ka Fara gajiya dani kwana daya,yanzu laushin kirjina fa kake ji duk ban kyauta ba because of that useless girl Mardiyya, Affan yace yi hakuri ni ba korarki nake Yi ba Yi zamanki a Haka,Raudah ta gyara sosai tare da makalkale shi a haka yake danna system din,Yana gamawa ya juya kanta,ta jawowa kanta Yana ta kokarin barinta sai ta warke amma ta jawo sha'awa baza ta bari ya kyaleta ba ya koma tare da hakkewa a kanta tana kuka tana rokonsa amma Ina Sam babu daga kafa.

Suna ta soyayyarsu da Raudah kamar zasu lashe juna har sati daya sannan ya koma aikinsa shima badan ransa ya so ba,5pm Raudah gida yaji gyara ko Ina ya dauki sheki da kamshi ta gama girki ta shirya a dining taci uban gayu na musamman,Yana shigowa ta tareshi tace Kai da kace 5 zaka dawo kalli time 5:30pm fa Ina ta jira,yace wani dan aikine ya rikeni,kayan jikinsa take karewa kallo taga wani waje yayi Kamar Kalar Powder ta Mata,tace mene wannan Kamar powder din mace,bani hannunka ta jawo Hannun Affan ta shinshina tace bani dayan naji shima ta shinshina tace yawwa babu komai,Raudah tayi kasa ta Fara kokarin janye Masa wando tace tsaya na gani,Affan ransa ya baci cikin tsawa yace Raudah tsorata tayi ta sake shi da sauri ta Fara bashi hakuri,yace Kamar fa kin Fara haukacewa kishi ne zai haukataki idan baki Wasa ba,wallahi idan nayi niyya ke baki Isa ki hanani kula wata ba,daga auren zan Fara kula Mata,ki kwantar da hankalinki ke kadai nake da ita,tace to ni ko mene kazo wajena ko me kaji kana so ka dawo gida Zan baka, Affan ya samu salon wayon da zaina Mata dama tana damunsa da kukan zafi da kyar take yarda da shi, tunda hakane shi yaga hanya,Murmushi yayi Yana Jin dadi yace ke nake bukata Ina cin abinci,tace ka Bari Mana sai 10pm ni wlh zafi,yace okay so kike na fara yin Yan Mata...Raudah da sauri tace ba damuwa muje ko Mene Zan maka Kawai ka fada zanyi,yace Kuma har 10pm din Zan sake round 2 tace to da sauri, Wai ita Kar yayi budurwa,idan zai fita da kuka suke rabuwa ita bazai fita ba sai dai su zauna tare a gida.









AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️


86-90




Official

By
AsmaBaffa





Page naki ne
AIDA MAMAN TASNIM









Nusaiba tana cika Iddarta ta shirya a boye sai gidan Aslam tana zuwa taga gidan ya sake haduwa komai an canja Masa new design,a bakin gate ta tsaya ta kasa shiga gida tasan ba halin shiga idan ta tuna abinda ta aikata gate din take shafawa da hannayenta tana zubar da hawaye ta Dade a haka har ta gaji ta juya gida inda ta fito,washe gari gidan Sufyan ta shirya taje gidan ta zaci gwauro ne bata san Yana sakinta da wata daya ya koma ya nemi gafarar Iyayensa ya auri tsohuwar budurwarsa Zahrau sun rabu tana sonsa Yarinyar kirki Yar tarbiyya ai Kuwa Yana aurota bai Dade ba ya samu Offer a land and housing sai dai albashinsa ba Kamar na Aslam ba amma ba laifi,yanzu iyayensa da Yan Uwa duka komai Yana musu,Zahrau har Kara takura Masa takeyi akan dole yayi musu abubuwa,Nusaiba tana Shiga gidan taga Zahrau tana gyarawa Sufyan kwalar rigarsa suna dariya cike da so ai kasa karasawa tayi tasan yayi aure ta juyo da sauri ba tare da sun ganta ba,ta dawo gida sai kuka Wanda ba shiri Mama ta shirya ta tafi gidan da Mum take ta manta irin wulakancin data Yi Mata lokacin da Mum tazo a gyara.

Mama gidan da Mum take ta shiga tana ta kwada Sallama Hajiya Zainab ta tafi gidan biki sai Mum,Mama tana ta sallama ba ji ba gani Mum ta fito sai taga Mama Fuska ta daure cike da bala'i Mum tace Wai wace ne ta damemu da Sallama taki ci taki cinyewa,Mama ta marairaice tare da langabar da kai tace surukata...ohhhhh da baki san ni surukarki bace sai yanzu dan Allah malama Fadi me ya kawoki sauri nake yi Ina da aikin yi,Mama tace zuwa nayi Dan Allah Surukata ki taimaka kisa danki ya maida Nusaiba dakinta dan Allah kuyi Hakuri komai ya wuce zamu gyara Inshaallah dan Allah ki taimaka Mana,Mum wani kallo ta Mata up an down sannan ba tare data furta komai ba ta tofar mata da yawu tuf ta juya tare da komawa ciki ta bar Mum a tsaye kikam,gajiya tayi da tsaiwa ta juya ta koma gida dabarunta sun Kare dama duk Shirin da tace shine kawai zata yi,Nusaiba ana gida zaman gida Wasa farin girki, bayan wasu Yan lokuta Shehu baya dagawa mama da Nusaiba kafa baya sakar musu fuska da Mama da Nusaiba wahala suke Sha sauran yaransa yake yiwa abinda suke so kawai,suna haka katsam sai ga Aslam,Shehu Yana gida yace a'a dana yau Kaine a gidan? Aslam yace ae Abba ya zauna kusa da Shehu a tabarma ya gaisar da shi ko kallon Mama da Nusaiba baiyi ba Wanda gasu nan a tsaye sun taho da sauri sun tsaya musu a kai suna magana kasa kasa da ita da Nusaiba,Shehu yace ashe haka arzikinka dama yana nan ya dawo naji labari Ina ta so ma nazo har gidanka Allah mun gode maka,Aslam yace Abba Kai na daban ne nasan me kaunata ne Kuma babban mutum ne Kai idan ba damuwa bana Inshaallah zamu tafi aikin Hajji tare da Kai,Shehu yace wayyo Allah dadi kashe ni Aslam ya dinga dariya,Nusaiba da Mama harda murna tunanunsu bikon Nusaiba zaiyi shi yasa ya Fara kashe musu kudi irin da,Aslam yace Kawu ba iya Makkah zaka tsaya ba Paris da Dubai zaka je inda Nusaiba take mafarkin zuwa yanzu gashi Shehu Babanta shi zai je Kuma Aslam Yana sani yayi hakan Sabo da farkon aurensu haka tace sai an kaita honey moon Paris ko Dubai,yace sannan duk Sanda kaji kana son hutawa Abba karka damu ka hada kayanka kazo gidana ka huta,ko me kake bukata Kawai ka kirani a waya,Shehu Kamar yayi suman dadi haka yake ji gani yake Kamar a mafarki,yace Kuma tare da abokinka zaku je Baban Siyama Kawu da Aunty,Shehu yace Alhmdllh na gode na gode ya dinga godiya Yana murna,Aslam yace Maganar shirye shiryen visa Zan kiraka a waya ya mike ya zaro Yan dubu dubu ya mikawa Shehu yace gashi kayi amfani da wannan,Mama ta dafe kirji,Nusaiba Hawaye ya Fara antayo Mata a kumatu,Mama tace surukina dan Allah kayi hakuri abinda Muka maka,Nusaiba tace dan Allah ka yafe min ka dawo muyi aure,Aslam yayi hanyar barin gidan ya juyo yayiwa Nusaiba da Mama kallon banza yace mugaye kawai yaja Tsaki ya juya shi da Shehu Suka fice,har mota Shehu ya rakashi ya tafi sannan ya dawo Yana taku dai dai Yana doro,Shehu yace Alhmdllh Yana takama a gidan ya zama Dan gayen dattijo aka bar Mama da Nusaiba da bakin ciki.

Aisha tuni an maida Aurenta da Farooq suna zamansu lafiya yanzu duk Karya da fadan da sukeyi sun daina sai mutunta juna kowa baya so wani Abu yazo ya shiga tsakaninsu,soyayya suke me tsafta abinsu su,Nabeela kuwa tana yin Idda ta samu miji wani babban mutum ne me Mata ta hakura da Affan tasan babu aure a tsakaninsu ma tunda Dan Uwansa Yana raye amma ta take gaskiya yanzu Kam ta hakura ta auri me Mata Kuma tayi zamanta babu Neman rigima,Sabeer ma yayi aure ya auri zankadediyar matarsa Habiba.

Raudah da Affan suna soyayyarsu sosai matsalar Raudah kishin tsiya,yau tana zaune a gida Affan ya fita sai ga Wayar Landlady ta shigo tana ta kiranta dagawa tayi tun kafin tayi magana Landlady tace Raudah maza maza fito ga mijinki Affan da wata sun shiga shopping zo ki gani da idonki,Raudah tace what? Na fada Miki maza basu da amana mijina haka ce ta rabamu da shi na aminta da shi Ashe maci amana ne,gani Ina ShopRite maza kizo kafin ya bar wajen, Landlady tayi gaskiya domin Affan ne da wata zasu shiga ciki ita Kawai dan ta ganshi da mace shine tace budurwarsa ce bata San cewar Amaryar liman bace ogan Affan Kuma Liman dinne yasa Affan ya kaita wajen wata Mata suna business tare da matar Liman,matar daga kasar waje tazo shine Affan ya kaita.

Raudah hijab ta zurma ta fito da uban gudu tare da bude motarta ta shige ta Mata key motar taki tashi tayi tayi motar taki ta fito da sauri daga gidan sai ga yaron Affan da machine yazo gidan zai karbi takardu,da sauri tace dan Allah kaini ShopRite sauri,ya zaci ma wata masifa ce ta faru ya juya machine ta hau da sauri tana cewa kayi gudu Yi sauri Salahu dan Allah Yana tambaya lafiya Hajiya? Kayi sauri please duk ta gigita me machine suna ta fyalla gudu a titi tana kayi sauri ka Kara wuta Yana tsinka gudun gaske a rude yaje ya daki mota Suka watse a gefen kwalta Raudah ko motsi bata Yi kanta ya fashe daga gefe Yana jini,me machine din Kuwa Suma yayi Yana farfadowa yasan inda yake sai raunuka da yaji,mutane sun taru akansu aka kwashi Raudah da Salahu yaron Affan zuwa asibiti,lokacin Affan ma ya koma Office Kawai yaji Kira Yana dagawa ya mike Zumbur a gigice Yana tambaya a wanne asibitin ya tafi da sauri figi motarsa sai asibitin,matarsa Kawai yake cewa dakin da Raudah take aka kaishi Yana Shiga ya iske ta farfado amma ta karye baras a kafa sai kanta an nade daga gefen da bandage,tana ta kuka a kwance Affan bai ma tambayi me ta fito Yi ba Kawai ta lafiyarta yake Yi,ganin tana ta kuka ya Fara lallashinta,a gefenta ya zauna tare da maida kanta jikinsa Yana lallashinta tana hawaye yace Inshaallah Zaki warke kinji,anjima kadan za ayi aiki a dora min ke,ya Isa haka kukan Affan ko aiki sai mataimakinsa yayiwa magana ya kula da komai ya tafi jinyar matarsa sai ta warke zai dawo ya sanarwa liman gaba Daya family Suka Zo dubiya har Liman,a ranar aka dora Raudah ana ta zuwa dubiya har Yusuf da matarsa sunzo,shi kuwa yaron Affan tuni ma an sallame shi sai da Raudah ta kwashe sati biyu a asibiti Affan shike jinyarta shike Mata komai bai bari ma yan uwan Raudah sun zauna ba tunda suka zo dubiya,mamanta ce ma ta dage sai da tayi sati guda a asibitin sannan ta koma.

Wheelchair aka bawa Rauda da sandunan koya tafiya lokacin da aka sallameta,Raudah tana tuna dalilin fitarta daga gida sai hawaye da kukan takaicin halinta tana nadama da Dana sani,gashi Affan din yand a yasan bata tambaye shi ba ta fito amma ko zancen bai Mata ba ta lafiyarta yake Yi ya daina zuwa aiki sai jinyarta shike Mata komai ita Kuwa me zata ce da wannan bawan Allah tayi dacen miji da wani ne sai dai a kaita gidansu in ta warke a dawo da ita, motar Affan ce ta shigo gidansa ya fito ya Bude dayan bangaren sannan ya bude booth ya dakko wheelchair ya dakko Raudah tare da dora ta a Kai tare da rufe motar ya turata a hankali zuwa ciki,Raudah tana ta zagin kanta a zuciyarta abinda ta aikata,Affan gwani ne wajen gyara da tsafta sai da ya gyara gidan nan tsaf sannan ya yiwa Raudah wanka shima yayi ya dorata saman kujerarta suka fito,ya shiryata cikin gown gajera marar nauyi,abinci yayi order aka kawo musu har gida suka ci sannan ya fita masallaci ita Kuma tayi sallah a zaune saman kujerarta.

Washe gari tana Palo tare da Affan suna kallo Landlady ta shigo bayan sun gaisa Affan ya koma bedroom ya basu waje,Rauda ta kalli Landlady tana hawaye tace kin cuceni ke ba matar kwarai bace Kuma ba abokiyar zama bace,sam bakya Dora mutum a hanyar gaskiya gashi nan abinda Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala,Ina zamana da mijina lafiya ke kin kasa aure kinzo kina zugani bakya taba yabon maza sai dai ki Fadi sharrinsu shi yasa da yawa wasu matan idan Suka taru basu da aiki sai fadan sharrin maza basu fadan alkhairinsu a haka wasu Wanda suke zaune lafiya da mazajensu shike nan an gurbata musu zuciya sai su Fara zargin nasu in ba a yi sa'a ba rashin zaman lafiya ya Fara kenan,Mata in Suka taru basu da aiki sai zagin maza da halayensu ki sani wata idan bata dauka ba wata dauka zata Yi karshe auren ya mutu ma,ba kowa ce take auren miji me kule kulen mata ba Kamar mijinki da Kika taba aure Bmbai yuwuwa kiwa maza kudin goro,na Zama sakarai da ilimina da hankalina na zauna Ina daukan shawararki landlady kiji tsoron Allah kije kiyi aure ki daina lalata Mana namu,kuma Indai zugace zata kawoki gidana karki sake zuwa inda nake bani ba bake har abada,kin girmeni babbar mace ce ke amma baki da tunani, Landlady tasan itama bata kyauta ba tace kiyi hakuri Raudah wlh aurena dana Yi na fuskanci halin mijina kenan sai nake tunanin kowa ma haka yake wannan yasa na kasa kara yin aure amma Inshaallah nima na gane gaskiya,Raudah tace oho Miki ni dai in bada alheri Zaki Zo ba karki sake zuwa gidana yanzu ma ki tashi ki tafi, Landlady ta mike jiki ba kwari ta tafi,Raudah tana hawaye Affan ya fito yace Wai me yasa kullum sai kinyi kuka ne kina Jin sauki fa kin kusa fara tafiya da kafafunki Inshaallah.

Raudah tana kujerarta ta miko hannu tare da rike hannun Affan tana hawayenta tace dan Allah ka yafe min na tuba bazan sake ba,ta bashi labarin komai zugata da Landlady keyi tace karshe gashi ta kaini ta baro na karye ta fashe da kuka,Affan yace ai Raudah tunda naji kinyi hatsari nasan kishi ne ya fito dake shi yasa ma ban tambayeki ba nasan baki da wata matsala face kishi,abinda yasa Kuma bana damuwa so ne a kaina akeyi Kar wata ta kwace ni to ni ai na Zama dan gata gashi kin jawa kanki kin karye Allah ya takaita ma,haba wifey babu izinina Kika fito haba Raudah kishi fa idan yayi yawa zargi yake kawowa,da sauri tace wlh bana zarginka Kawai in ta zugani ne sai naga kamar haka ka yafe min kayi hakuri bazan sake ba babu ruwana yanzu gashi na karye a banza,Affan ya kyalkyale da dariya tana hawaye ta duke shi a kafada,yace ai Ni Kika jawa aikin,ki sani bazan taba cin Amanarki ba na Sha fada miki,to yanzu idan ta kasance Zan Kara kishiya yaya kenan Raudah? tace ai ma Inshaallah baza ta faru b,to idan ta faru fa? Mutuwa zanyi Kawai,yace kin gani wannan halin naki sai ke Kika ce kin tuba kuma? Baki ta turo tace ae na tuba bazanyi fada ba bazan ce komai ba Kuma bazan bibiyeka ba sai dai Kawai aga na mutu,Affan yayi dariya sosai tace ai kana da kyau ko wacce sonka zata dinga yi ni Kuma bana sooooo....ta karasa da kuka,To yanzu Raudah nifa ba ni nayi kaina ba Nima tashi nayi na ganni haka,Raudah tace ka kakalo shi Mana tunda kana ta gyara jikinka kana daukan wanka kullum kayi ta matso kyawunka kana fita gashi nan sai kafi 1h a toilet kana wanka duk ka goge fatarka kullum fari kake sake Yi kullum gashi nan bature kake Zama,Affan dariya Kamar me yace to na daina wankan sai na zauna miki a kazami gobe kice Nima Ina warin hammata,yanzu sai kince kin tuba kin daina ko? Raudah tace Zan dinga yiwa kaina Addua kaima ka tayani,Affan ya sake sakin dariya tace wannan ba abin dariya bane kaje kullum kayi ta gyara Suma ba ji ba gani ko wacce Yar iskar budurwa tana zare Ido gashi nan gaf ake da yaye dalibai daga Yan secondary zasuyi candy gashi Yan University sun kusa gamawa naji a labarai ance final exam zasu zana Kuma Yan Service sun gama miji suke jira wallahi ta Allah ba tasu ba, Affan har wani dadi yake ji ana kishinsa yace to ya Isa me Miji,Raudah tace kayi hakuri na tuba Allah kishi irin na baya da nayi bazan sake ba amma zan dinga dan yin kadan kadan shi yasa nake baka hakuri kayi hakuri dani Dan Allah har Allah ya yaye min,Affan yace to an gama Raudah,no your love zaka ce ta gyara masa Yace Okay My love,My one and only, My Heart,My soul my life Kuma Queen dita,Raudah Murmushi tayi tana Jin dadi tace ga mijina me jinyata me so na wata tazo itama Watarana ayi jinyarta haka dole naji haushi,kwana nawa baka Yi komai dani ba lafiya iceko? Affan yace Baby rigima baki da lafiya a karyen zanyi wani xxx dake,Raudah tace a'a in kana so kayi Zan maka komai Zan daure ai na Fara Jin sauki kafar basai a lallabata a gefe daya ba,Wai wayo take wa Affan Kar ma yaji Yana so ya Karo aure tunda bata da lafiya ko yayi sha'awar wata ita bata da lafiya baza ta iya Masa komai ba akan haka gwara ta daure tunda tana gani idan Yana Mata wanka Yana shiga yanayin bukatar mace daurewa Kawai yake yi shi yasa gwara ta tari abin.
Affan da wuri ya amshi tayin Raudah yana murna yau zai gagije,ai Kuwa da dare haka kafa aka sata a gefe Suka jiyar da juna dadi.

Washe gari Raudah tana kallon labarai a tashar hausa suna zaune da Affan taji ance gomnati ta dage jarabawar waec da dalibai zasu zana Yan secondary school an Kara wata uku nan gaba,Raudah tace Alhmdllh Yan banzan Yara aci gaba da shiga aji,Me labarai tace kungiyar Asu jibi Monday zasu Kara tafiya yajin aiki na Sai baba ta gani,Raudah ta kyalkyale da dariya tace maga karyar gama degree dan ubanku,Affan Yana jinta waya yake dannawa amma sai da ya tsaya kallon Raudah tana bashi dariya matuka.

Bayan kwanaki ya Fara koyawa Raudah tafiya har ta iya ta Fara takawa da kanta har ta dawo tana tafiya normal Kamar bata taba karyewa ba,likita yace ta dinga Dan zaga unguwa tana tafiya a kafa me dan nisa,tare da Affan Suka fito sunyi gayu sosai Affan sanye da 3qrt da t-shirt komai fari,ita Kuwa Abaya ta sa silver color me shegen kyau tayi rolling suna tafiya a layin suna zancen soyayya suna nishadi kamar saurayi da budurwa ka gansu gwanin birgewa,Suna ta nishadi yana tsokanarta,wata Yar budurwa ce tazo wucewa Raudah da sauri ta koma ta bayansa tare da rufe Masa idanu da tafukan hannayenta dariya sukeyi musamman Affan, sai wurin magriba Suka dawo gida.

Siyama kwance suke da Aslam a makeken bed dinsu sun gama soyewa suna hutawa ta juya tare da hugging din Aslam tace My Sugar dan Allah ka biya min makaranta na koma Nima nayi karatu,marairaicewa tayi da shagwaba please ko ba degree ba ko NCE ne dan Allah kaji, Aslam yace ni bana son fitarki aje a gurbata min Mata Muna zaman mu lafiya,Siyama tace Ina da hankali fa Inshaallah babu abinda zai faru wace ma ta Isa ta zuga ni na yarda ilimi Yana da dadi kaga Zan sake wayewa sex dinnan ma Sai kaga albarkacin makaranta da gogewa nazo Ina maka style har na tintsira gudi gudi,dariya Affan yayi ba shiri yace ba wayon da Zaki min Yar nan,Siyama ta sake cewa to yaran mu fa ko Dan yaranmu da zamu haifa zai musu Rana,Yan dagwai dagwai dinmu jikokin Mum, Yan fararen yaranmu masu Yan kunnuwa Affan yace naji amma sai kin samu ciki Zaki fara yarona tun a ciki ya dinga Jin turanci,Siyama tace Indai ciki ne Ina da shi fa,watanmu biyar da aure Ina da ciki,Aslam yace haka ake cikin,da gaske fa nake idan baka yarda ba muje asibiti gobe,ta ya Kika sani? tace Sanda na dinga zazzabi rannan na siyo wannan tsinken na pt na gwada Allah ya nuna Ina da ciki,shine baki fada min ba? gobe Zan kaiki asibiti ai,gari na wayewa Suka shirya sai asibiti bayan an Mata gwaji nagartacce aka tabbatar tana da ciki na wata uku dai dai,Aslam sai Murna harda kissing dinta a kumatu Suka dawo gida murna taki karewa,Siyama tace ai mu irin jinin haihuwa ne ana taba mu muke samun ciki,dariya yayi sai Murna yake zubawa daga nan ya Fara musu Shirin barin kasar.

Su kawu,Aunty da Shehu sai Wanda Affan yasa zai rakasu ko Ina suna filin jirgi,Landlady ma tazo zata tafi Umrah tana filin jirgi a nan Suka hadu da su Shehu,Shehu yaga dai dai shi yaji Landlady ta masa harda cewa sannu,tace yawwa sannunku,sai ga Shehu ya zage Yana yiwa Landlady tambayoyi kema Makkah Zaki? tace ae Umrah zanyi yace ke Kuwa ki karasa ladanki Mana kiyi aikin hajjin gaba daya amma kiyi Umrah Kawai ki dawo sabo da rashin rabo,Landlady tayi Murmushi bai san me kudi bace,Shehu ya zake suna ta hira da Landlady,Shehu harda cewa daga nan mu Paris zamu wuce sai Dubai, Landlady ta zaro Ido ta zaci wani shegen me kudi ne Shehu ta saki jiki harda bawa Shehu labarinta kaf amma bata nuna Masa me kudi bace, tun a nan Suka kulla soyayyarsu in sun dawo zasu Yi aure, Landlady a ranta tace gwara ko talaka ne Indai na samu me so na Nima nayi auren nan na huta kullum sai dai na rungumi pillow na gaji,Shehu Yana ta murna ya samu matar aure shi kam.








AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️


91-95





Official

By
AsmaBaffa







Page naki ne
Bk








Affan yau zai koma aikinsa cikin shiri ya fito tare da Raudah tana shagwaba ta rakashi har mota tana kumburo baki irin na Yan Shagwabar nan da sangarta,Affan ya zaro kudi Yan dubu dubu na dubu goma ya Mika Mata ta karba tana cewa na mene? yace baki nayi ki kashe,duk da tana da kudi bata da wata matsala sai da taji dadi yace sabo da wasu mazan tunaninsu Kawai ci da Sha zasu bawa mace basu iya bawa mace dan kudi ko Yaya ne gwargwadon samunsa Watarana haka sabo da ba iya abinci da sutura bane matsalarta,in ka bata kudi maybe a danginta akwai Wanda take so ta yiwa kyauta ko ta kyautatawa kawaye ko Yan Uwa bare uwa uba iyayenta kuma,zata kyautata muamularta da Yan Uwa da abokan arziki amma mazan da yawa basa ganewa, Raudah tana shagwaba tace to ai Ina da kudi Kuma ma Ni ka dawo da wuri yafi min muhimmanci,nasan kina da su ai amma kudinki daban nawa daban wannan naki ne kiyi abinda Kika ga dama da abinki, tace to na gode Allah ya Kara budi yasa kafi haka,karfe nawa zaka dawo? 5pm ya furta Yana kallonta,dire diren kafafu ta fara tana kukan tabara yayi nisa gaskiya ni ka rage, kina aiki fa My life kin San Kuma ka'ida kiyi hakuri tare fa muke bacci kin San da Ina gida ba aiki dole Ina gida, Alright ta furta Allah ya tsare a nemo mana halali Banda haram, Inshaallah ya furta Yana cewa am gonna miss you,me too yace come here..dan kanta ta shigar cikin motar yayi kissing dinta tace ko na zo nayi driving naka? Kina amaryar Zan bar matata ta fita, dariya Suka

Please Login or Register in order to submit comment