Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakushinta ma Wai dadi ba zafu,Raudat har yau bata bashi amsar tana sonsa ba sai aji take ja Masa tun Yana tambaya har ya gaji.

Aisha wannan karon tana hakurin dannewa basa fada da Mahaifiyarta suna zaune lafiya Sabo da sunyi nadama Matukar gaske,aikin gidan kaf kusan Aisha ke yinsa,tana son cikin nan nata duk da uban dan baya so amma ji takeyi da cikin nan,har tayi kyau ta Fara murmurewa, Farooq yayi murnar fitowar Aisha amma yaji haushi da aka ce tana da cikin wani ba nasa ba,Aisha tana ta murna zata samu danta ko ya Kawai tana wanke kayanta dana Ummanta ta Fara zubar da jini,ta tsorata sosai Suka tafi asibiti har da Baban Aisha aka je, lokacin cikin Aisha ya zube gaba Daya har ma sai da aka Mata wankin ciki,sabo da taji jiki kwanan su biyu a asibiti sannan suka dawo gida taci kuka ta koshi sai da Babanta yayi ta Mata nasiha sannan ta hakura,Ciki na zubewa mutane munafukai suka kaiwa Farooq gulmar cikin Aisha ya zube ta wani bangaren yaji Mata ciwo ta wani bangaren yaji Dadi.

Bangaren Siyama kuwa sati Daya Kawai dangi aka fadawa Suma kawu yace ba taro Yan daurin aure ne Kawai zasu Zo,Dangin uwar Babar Siyama ma haka ya fada musu,Babu Wanda aka ce yazo sai iya maza Yan Uwa,shima Aslam ya fadawa Mum, Mum tace amma nayi maka farin ciki son ai gwara ma haka ba sai da taron ba babu komai an gode amma duk da haka ayi order abinci a Kai musu su bawa danginsu Suma mu dai ta bangaren mu tunda dama wannan iftila'in ya fada maka dama bamu da Niyyar taro sai na Yan daurin aure Kawai Nan Suka Yi kulla kullarsu da Mum dinsa yanda baza suji kunya ba,Haka aka tura manya da kudin komai da komai ko Siyama bata sa rai da lefe ba,Aunty dai ta dage tana ta gyara yarta sannan tana zuwa gyaran jiki, Saura kwana uku biki aka kawo lefe sunyi mamaki akwatina goma cif Kaya na gani na fada ba abinda babu,aka dinga zuwa kallon lefen a unguwar,Maman Nusaiba taji labari ta kyalkyale da dariya tace dan karya ne haka yakeyi yanzu ana kaita zaice yaci bashin bank ba kudi sun shiga uku ta sake sakin dariya,Shehu yace kinyi asarar halinki ke dai Kam tir.

Aslam ne ya fito tare da Siyama yazo zance Suka Yi kicibus da Nusaiba mijinta ya kawota a mota ya juya,Aslam bai ma ga ko motar ba lokacin yayi nisa tuni ya bar layin,Nusaiba ansha wanka kana ganinta kasan tana hutawa ko kallonta Aslam baiyi ba ta gefenta ya wuce, har da kallon Siyama tayi dariya tace an kusa cin bashin banki ki daina murna an kawo Miki akwati goma Nawa kusan guda ashirin ya kawo amma karshe a ya na kare da talaucinsa, Siyama tsaki taja,Aslam yaja hannun Siyama yace let's go My Heart Suka wuce,Nusaiba ta bisu da kallo tace a hau taxi lafiya nasu ko kalleta ba abin Kuma ya Mata mugun ciwo a rai wato Aslam Kamar ma bai taba saninta ba haka yake nuna Mata ta wuce gidansu dai tana takaici.











AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️


61-65




Official

By
AsmaBaffa





Page nakuli ne
Rukey Muaz







Ana gobe daurin aure Siyama tasha gyara sai kamshi take zubawa Kawai ta Sha lalle,Kawayenta ta gayyata Zulfa'u,Sakna,Raihanatu da Nana sune Kawai a gidansu suke tayata Zama,sai bangaren Dangin mahaifiyarta Mata su biyar,sai bangaren dangin Aunty Mata su wurin goma haka bangaren Kawu da Mahaifin Siyama Suma sun kai goma gida ya cika tam duk da Kawu yace bazai taro ba dole sai da aka zo Masa,haka Aslam ya dinga dariya Jin Kawu yace bazai taro ba amma iya dangi sun cika gidan haka ya Aiko musu da kayan abinci shinkafa ta dafawa da danya ta tuwo,mangyada manja,Maggi iri iri,kayan Miya buhu biyu,su Alayyahu,kabewa, Albasa,Taliya macaroni komai sai da aka kawo da yawa su Aunty Suka dinga mamaki kamar me kudi haka ya aikowa da Kawu dubu dari biyu,ya bawa Aunty dubu hamsim haka Siyama ma ya Aiko Sabeer ya kawo Mata kasonta sai,Kawu ne yaga mutane sun cika gidan ya Kira Aunty gefe yace nace fa ba shagali ba biki ya akayi Yan Uwa Suka cika min gida to wlh babu wacce zata Kai Amarya ko wacce gobe ta bar min gida,Aunty tace to tunda an sanarwa Yan Uwa ai ba wacce zaka kora idan Kuma zaka iya bismillah,Kuma biki babu wacce aka yiwa aure ba dangi sabo da Haka itama Dole Yan uwanta suzo Amarya Kuma ba komai ango yazo ya dauki matarsa ai dai an daura aure ko to Alhmdllh,Kawu Yana magana kasa kasa Kar dangi suji yace Ni dai ba wacce na gayyata biki,Kai ka sani cewar Aunty ta juya ta koma suna ta girke girkensu Kuma ta gayyaci Yan unguwa Wanda suke mutunci da kawayenta.
Washe gari daurin Aure ranar asabar karfe 11am,Aslam shi Kam yayi gayya sosai Suka Zo da danginsu na jini Yan uwan Uba dana uwa aka taru a masallaci Shehu ma shine wakilin Aslam shi ya karbi auren Aslam aka daura akan sadaki dubu dari,ana daura Aure Aslam Yana cikin abokai yaga Affan da liman sunzo Yana sani Aslam da abokansa yace Dan Allah a nuna Mana Wanda na kasa a samarin Amarya,Sabeer yace waye Muka zo muka kasa Muka cinye shi da yaki? Affan ya gane da shi suke,yace gani nan ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa yace Congratulations a zauna lafiya,Aslam yace Kar ma a zauna lafiya,Affan yace to fa Yana dariya yasan kishi ne kawai,Sabeer yace Wanda Muka kasa ayi Hakuri banda gaba,Affan ya dinga dariya shi ko a jikinsa ya tashi Yana kwambonsa ya wuce,Liman ma ya taya Aslam murna sosai ,Aslam yau anji shadda ta musamman Fara tasha aiki da babbar riga da hula yayi kyau kamar a sace shi ga abinci da yayi orda fried rice da rabin kaza har da masu rabawa ana ta bawa mutane a ledar take away a zuwan gidan Amarya ne Suka kawo.

Siyama kuwa ta Sha leshi dan ubansu golden and white,Kawu yace babu batun shagali ko angon bai je wajen Amarya ba Kawu ya Hana,Amarya tana zaune cikin Yan tsirarin abokanta suna cin abinci Kamar ba Amarya ba komai bata akeyi tana lashewa da ance gashi zata ci abinta, sun Kuna Bluetooth speaker suna Jin kidansu suna nishadi tunda ango ya bugo Mata waya yace sai na Zo daukan Amarya,Siyama tana Jin kunya tace ka daina zumudi fa period na Fara jiya da dare,Aslam yace ba komai bukatar maje hajji Sallah tunda an daura yanzu hankalina a kwance yake nasan kin Zama tawa,Murmushi yace 4pm zanzo daukan abata ki shirya da wuri,Siyama Wayarta ma ta kashe duk sai taji ba dadi abinka da wacce bata taba barin gida ba kullum kana tare da iyayenka dole idan za a rabaka da gida kaji ba dadi,Siyama kuka ta Fara Yi tun da wuri kawaye suna tsokanarta ta dauki pad dinta ta Shige toilet tana hawaye a cikin toilet din ta fashe taci kukanta ta koshi duk ta bata kwalliyar tata sai fuskar ta wanke gaba daya ta fito idonta yayi alamar Kuka,Aunty tana Sallamar baki ta kalli Siyama Suka hada Ido tace ke Kuma meye na kukan duk rashin kunyar tana ina? Yan Uwa Suka saki guda da shewa Siyama sai sabon kuka ya taho,dangi Suka Yi caaa a kanta da tsokana sabo da kowa ya Santa da baki amma yau Kamar ba Siyama ba,kawaye suna Mata tsiya Kawai ta kwanta a katifa ta juya musu baya tun tana hawaye har bacci ya kwasheta kowa yazo Ina Amarya sai aga tana shakar uban bacci tun 12 har kusan 3pm bacci takeyi,ana ta posting pics din ango da na Amarya a online Wanda suka Zo bikin duk da cewar ma basu dauki hoton tare ba, ai Yan layinsu suna fara zuwa bikin Suka tasheta da tsokana wata tazo ta Dana Mata duka a gadon baya ke dalla tashi Amarya da bacci ki tashi kiyi wanka aka taru akan Siyama sabo da mutane da yawa ana Wasa da ita ta ko Ina caccakarta akeyi,4pm Aunty tasa tayi wanka tare da canja Kaya wani material ta sa me shegen kyau na lefe,suna bikinsu dai Kafin dare aka Kai Yan biki gidan Amarya duk me son ganin gidan Amarya Aslam ya turo wasu bakin abokansa sun kaisu a mota har Aunty taje taga gidan yarta komai yayi Mata itakam,Yan bikin ma suna ta yabawa da yan uwa,na nesa sun tafi ma tuni sabo da Kawu dama ya fada musu ba taro shi yasa Basu zauna ba,Aunty Kuwa dama ta fadawa mutanenta Kawu ne zai Kai Amarya da Kansa shi yasa babu macen data zauna zuwa magriba kowa ya watse sai Yan uwan Aunty su Uku suna ta aikin gyara gidan,Sabeer ne yazo ya kwashi kayan lefe duk wani abinda Siyama take so ya tafi,Aslam ce Masa yayi ya bar kayan a motarsa da ita zai dakko Amarya idan sunje gida ya cire kayan gaba daya,Kamar Aslam bazai Zo daukan Siyama ba sai dare Aunty tace tayi wanka ta shirya ya yo waya yace gashi nan,Siyama tace ban dade da yin wankan ba fa to ai na Amarya ne idan Kika Yi yanzu ai kin huta Yi a can,Siyama haka ta fesa wanka tazo ta Gama shafe shafenta ta saka wani Leshi da Kawu ya dinka Mata na biki me shegen kyau sea blue and black mayafinta me shegen kyau Kalar kayan da takalmi da jaka komai same color tayi kwalliyarta me kyau ta shafa turaruka tana shiri Kawu da Aunty Suka shigo Suka zauna a dakin Suka Fara Mata nasiha iri iri tana ji ta fashe da kuka suna Yi tana kuka kanta a kasa har Aslam yazo tana kuka,Aunty itama harda hawaye ta fada bedroom dinta ta kwanta tana ta kuka Aunty zata rabu da yarta,Kawu shi ya tasa keyar Siyama tana kuka kanta a kasa ta rufe kanta da mayafi tana kuka ya kaita har mota inda Aslam ke mazaunin driver sanye cikin wata shaddar Yar ubansu ruwan kwai,Shiga tayi gefe ta zauna Kawu ya rufe dama ya yiwa Aslam tasa Nasihar tuni,Siyama ta sauke glass din motar tana shesheka tace Kawu..... Kawu yace a'a Siyama karyar rashin kunya ta Kare ki daina nemana gaki ga Aslam aje ayi ta samun ciki idan Kinga dama ki Haihu sau goma a shekara Allah yasa Albarka,Aslam Murmushi yayi Kawu ya yiwa Aslam godiya yace su tafi Aslam yaja mota Suka tafi Siyama na kuka.

Affan dawowa yayi gida daga wajen daurin Aure Raudat ta tsaya a jikin window tace Ina kaje ne haka? Yace yau ki tayani jaje an min gora,Nasha Sanda da Kaye an min mugun Kaye budurwa ta aka daurawa aure Bata so na wani take so,Raudat taji wani farin ciki tace amma ya Naga baka damu ba? Juyowa yayi Yana kallonta yace sabo da ke nake so,Raudat baki ta bude yace yes ke nake so fa na fada Miki kince sai kin duba shike nan ai rayuwa ce harda yin Kalar tausayi,Raudat tayi dariya tace ai zan baka amsa ne nan gaba,Affan ya girgiza Kai a ransa yace zanyi maganinki.
Washe gari da Yamma wata budurwa ce Yar kwalisa Fara ta dau wanka ta sa key ta bude part din Affan kawai ta Shige a gaban Raudat dake Compound,Raudat ta bita da kallo yarinya Shuru Shuru bata fito ba har Raudat ta gaji ta shigo ranta a bace tace ke wai wa kike jira? Yarinyar tana yanga tace Affan, Raudat tace a Ina Kika samu key dinsa? tace shi yaje gidanmu ya bani yace na jira shi, Fitowa Raudat tayi cike da kishi hankalinta a tashe ta zaune a compound Affan ya dawo da sauri ya fito ya shiga part dinsa Kuma ya rufo kofa,Shuru Shuru ta ga bai fito ba shigowa tayi ciki ta same shi a zaune shi kadai bakuwar Kuma tana kitchen tana girki kamshi na tashi,Raudat zuciyarta ta jagule ta rasa inda zata sa kanta a duniya taji san yi fita tayi cikin fushi ta koma bedroom dinta ta kwanta a saman bed dinta ta Fara hawaye kafin kace me ta fara ciwon kai ko Hussain bata taba sonsa haka ba bare ma tayi wani ciwon Kai a kansa amma Affan bayan ciwon Kai harda zazzabi ya lullubeta,Affan Kuwa Yana ganin Raudah ranta ya baci ya mike ya shiga kitchen yace Safara'u zo ki tafi gida kin gama aikinki, Safara'u ta fito tace Yaya Affan ka manta sakon da zaka bani na bawa Mallam,Yace af na manta ya mike da sauri ya dakko Mata kudi yace gashi kice ragowar kudin gidan Mai ne da nace Zan kawo tace to tare da ficewa,tana tafiya dan Masifa kunnen Raudat taji Sanda tayiwa Affan Sallama tashi Raudat tayi tare da saka hijab sai palon Affan.

Kishi ya gama cika Mata zuciya ta banko kofar ya mike zai shiga bedroom tace waccen wacece? Yace wa? Who is she? ta furta da fada tana rawar sanyi yace baki da lafiya ne? Ban sani ba mayaudari kace min Ni kake so kana zuwa ka kawo wata macen mene baka fada min ba,Affan yace Yar Liman ce fa uban gida na a'a Yar gidan sarkin musulmi ce karewar limanci si ba muharramarka bace da zaku kebe dan ubanta tazo tace zata maka girki Kawai kace sonta kake yi Kuma bana sonka bana bukatarka gaba daya ta juya ta fice Kamar zata tashi sama.
Affan yaji Dadi yace yawwa kin Kama kanki ya zauna Yana murna sosai tana sonsa,washe gari ogan Raudat yazo zai dauketa zasu tafi aiki,taji sauki ta fito cikin shirinta da simple doguwar Riga marar nayi ta fito da takardunta,Affan yau hutawa yake a gida yaga Raudat an dauketa a dalleliyar mota ya zaci saurayi ne ya kule sosai Kamar zaiyi duka.

Yamma nayi ta dawo Affan ya tareta a Hanya waye wancan? wa? Wanda ya daukeki a mota,abokin aikina nane ai gwara ni ba namiji na kawo dakina ba,Tambayarta yayi a nutse Raudat mu daina irin wannan kina so na ko bakya so na? Tsayawa tayi tana tunani Kawai ya juya ya Fara tafiya abinsa tace wait bai tsaya ba ta bishi da sauri tace Ina sonka kayi hakuri,tsayawa yayi cak Yana murna,gabansa ta dawo ta tsaya tace Ina sonka wlh kayi hakuri,sabo da murna ma kasa magana yayi,takardunta ya karba yace mu je na Zama mijjn Kan tace suna tafiya abinsu Suna hira abinsu amma kishin masifa ne da Raudat duk da haka tana zargin Affan ko suna shiri da Safara'u.

Aslam kuwa tsohuwar unguwarsu yaje unguwar masu kudi ita Siyama tana ta faman kuka a lullubeta cikin Mayafi har age gida bata sani ba sai da yace fito ta dago da kanta Mamaki ya kamata tace me za muyi a wannan gidan ta kalli gidansa ne katafaren gida na da Wanda ta sani Sanda Yana me kudi,Kuma duka ga motocinsa nan har da wasu sababbi ma,masu aikin gidan tsofaffi Wanda ya sallama ta gani ya dawo dasu kenan,ga inda an Kara gyara shi ya koma wani irin mugun hadadden gida har ya da a baya tsaruwa,baki ta bude yace Baby fito Yana Murmushi ya jawo hannunta ta fito tace ba dai duk talaucin da kace ba karya ne? yace ki saurareni Baby kiji ba abinda ya faru da dukiyata tun daga lokacin da nace Nusaiba ta ebi kudi a cikin kudina ta bawa Mamanta ta kwashe kudin duka na Fara zargin sabo da kudina ta aureni badan Allah ba shine nayi Mata haka Kuma ko Mum da Sabeer ban fada musu komai ba tunaninsu da gaske na talauce,Siyama ta Fara mamaki tace yanzu kana nufin duk banki da kace sun kwace komai karya ne? Yace ae,Fuska ta bata tace amma ka dauki hakkinmu hawaye ya zubo mata tace me yasa kayi Mana haka, rudewa yayi ganin ranta a bace,tace ta ya za ayi ace dama Kawai fada kayi ka shirya zance Muka dinga Shan wahala a kanka muna Jin tausayinka hawaye ya zubo Mata,yace please Baby kiyi Hakuri ke kin San dalilin da yasa nayi haka sabo da na San me so na tsakani da Allah kuma gashi na sani ya karasa Kamar zaiyi kuka kiyi hakuri muje ciki ta shiga yasa me aikin ta shigar Mata da kayanta kaf bedroom din Amarya,ya zauna Yana aikin lallabata ya Sha fama kafin ta hakura ta sakko hannunta ya rike kin zauna a Palo Baby muje sama Suka haura sama jikinta a sanyaye tace ya akayi Naga motar da Nusaiba ta siyar maka Wanda tace Wanda ya siya ya gudu bai bata kudin ba? Yace ai Wanda ya siya motar yarona ne tunaninta ban me nake ba ni na tura shi ya siyi motar ya gudu Kuma,Saurayinta data aura ne kadai ban sani ba ban ma taba ganinsa ba amma komai da takeyi Ina sane

Suna Shiga bedroom dinsa ya rungumeta a jikinsa yace ko za a hanani yanzu? Murmushi ta saki tace yaci gaba da rungumeta Yana shafa wuyanta,tsigar jikinta ce ta tashi Wanda ya jawo ta lumshe idonta,yace kinyi wanka a gida ko yanzu zamu Yi Yana magana yana goga Mata Hajiya Babba wacce ta mike sosai,tace yanzu nayi wanka yace Nima Haka, toilet dai ta Shiga taci gaba da kukan barin gidansu ta wanke fuskarta ta fito tare da zabo rigar bacci ta gaske ta saka shi yayi shirinsa ma,kayan makulashe Suka lashe sannan Suka Yi brush ta Fitowa ya dauketa sai saman bed ya kwantar da ita a hankali...

Nabeela ce ta samu ciki a gidan Farook murna wajen farouk ba a cewa komai,Kamar gaske sabo da bata son Farook taje a boye ta zubar da cikin aka Mata Allura,Bayan ta dawo gida cikin dare ta fara bleeding yayi yayi ta bari a tafi asibiti taki yarda sabo da Kar a ganeta sai da ta kusa mutuwa Farook ya kasa jurewa ya dauke ya dauko Mamansa Suka tafi asibiti,ai Kuwa bayan komai ya lafa likitoci sun samu nasarar ceto ranta, likitan yace Farook ya same shi a Office,bayan Farook ya shiga ya zauna likitan ya dago ya kalli Farook ya Fara fada taya za ayi a Mata allurar zubar da ciki me karfi haka,Farook yace Allura Kuma?likita yace Kai mijinta ne ko kuwa cikin Shege ka Mata sakamako ya nuna Allura ce me karfi ta zubar da ciki,idan matarka ce ka binciketa gaskiya,Farook duk da ransa ya baci amma ya danne bai nuna ba Sam Sai da aka sallamesu bayan kwana biyu taji sauki sosai ta warke ya sameta a bedroom tana zaune,Yace Nabeela wacce Allura Kika yi na zubar da ciki? dama kin San bakya kaunata Kika aureni,kin San wani kike so Kika zalunceni na aureki, Nabeela tace waye ya fada maka? Wayo ya Mata yace Wanda Kika je ya zubar Miki cikin,tunani tayi Kawai da gaske an fada masa tace Ni bana son haihuwar, gau kake ji ya kifa Mata Mari hagu da Dama yace amma ke azzaluma ce Ina son yaran Kika zubar min da ciki, ya zari zai Fara zaneta ta gudu Daya dakin ta saka key tana Cewa Allah ya Isa,idan ya zageta haka ta rama Kawai takarda ya dakko ya saketa Saki daya ya bata takardarta ya sallameta,ita duk Affan take so akansa take kashe aurenta har da murna zata je ta nemi Affan dama taji labarin inda yake Zaune can zata tafi ko Idda baza ta bari tayi ba.

Nusaiba Kuwa soyayya suke bugawa da Sufyan abinda take so yake Mata komai ya samo a gindin Nusaiba da uwarta yake karewa,duk ta rabashi da danginsa Wanda da shi Suka dogara shike Basu ci da Sha amma Nusaiba tasa yanzu ok gaida iyayensa sai yaga dama yake zuwa,Basu da cin yau bare na gobe amma yaki ya taimake su,Ummansa ce ta gaji ta shirya ta tafi gidansa,Lokacin ya tafi Office tana zuwa ta shiga palon Wanda ta iske yar aiki tana ta gyare gyare,Yar aiki ta gaisheta Umma ta shiga ta zauna tace me aikin ta Kira Mata Nusaiba,Nusaiba tana sama taci gayu ta kishingida a saman gado tana latsa Wayarta ac na ratsata,Me aikin ce ta shiga da sallama ta durkusa a gaban Nusaiba tace Kinyi bakuwa Hajiya,Nusaiba da aka Kira da Hajiya tana yatsina tace wace? umman Alhaji ce,uwarsa ce Maimuna Wai?Me aiki tayi mamaki uwar miji guda ake Kira da sunanta gatsal haka,me aikin tace ae itace,tsaki Nusaiba ta ja tare da furta je kice Ina zuwa,tunda me aiki tace gata nan Nusaiba tafi hour guda bata fito sannan sai gata tana sakkowa daga bene tikasai tikasai tana taku dai dai tazo ta zauna tare da furta gani naji ance kina nemana,Uwar miji tace dama Sufyan nazo gani ko Yana gida?kin San Yana wajen aiki bai dawowa sai dare in kuma Zaki jirashi to ta mike tana kunkuni tana cewa miji ma sabo da Masifa baza a barka ka zauna lafiya ba uwar mutum tabi ta isheka ta Shige kitchen,tana zuwa kitchen ta samu me aiki tace idan Kika sake Kika Bata ko ruwa sai na koreki yau,Umman Sufyan tana ji a kunnenta mikewa tayi ma kawai ta bar gidan ta koma gida inda ta bawa Baban Sufyan labarin irin wulakancin da aka Mata,Baban Sufyan yace kyale shi ai Allah shike ciyar da mutum Kuma shi ke raya bawa kyale shi zaizo ya same mu watarana tunda shi mace tafi iyayensa.

Bangaren ango Kuwa Nafila yayi shi daya da adduoi Siyama tana zaune a gefen bed tayi Shuru tana tunani da farin ciki yau itace a gidan nan tangameme haka,gida na gagara,mijinta hadadde ga kudi duk natane Allah take godiya har ya idar Yana sallamewa ya juyo Yana kallonta cike da farin ciki Yana Murmushi ya mike tare da haurawa saman bed din ya jawota jikinsa









AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️


71-75



Official

By
AsmaBaffa






Page naki ne

Bestynbeelat










Suna dawowa gida mota ya bude ya fita ya zaga tare da bude mata kofa hannunta ya riko ya fito da ita sannan ya bude bayan mota tana rike a hannunsa ya dakko take away nasu Suka shiga ciki ba kowa me aiki ma tana bangarenta,waist dinta ya riko suna tafiya Murmushi tayi tana kallon gidanta Kamar mafarki take gani ta kalli gidan ta kalli mijinta sai farin ciki takeyi tana tunani dama Yan uwanta da akai kaisu ganin gidan Amarya nan aka kawo su Suka kalla da yabawa suna cewa me kudi ne ashe tunaninsu Kawai zuzutun Mata ne, daukan Siyama yayi Suka karasa sama Bedroom dinsa Yana cewa gaskiya wannan rashin tsarkin naki ya min cikas da ace na San Haka ne tabbas sai na roki kawu a daga bikin a Kara sati daya,Kai fa kace baka damu ba auren shine me wahalar,kayan jikinta ya fara cire Mata Yana cewa ki daina sa min bra Indai Kika fahimci Ina mood,kallon sa tayi tace da Ina maka kallon kamili ashe kaima guda ne,na taba ce Miki ni Kamili ne? no na taba cewa bana son wagga harka? Da wani ustaz kike ganina? Siyama tace ae har tausayinka nake,Murmushi yayi yace to ki daina sarkin musulmai ma Yana son sex da Zaki ga Liman dinku sai kin daina binsa sallah,Dariya Suka yi tare da Mika Mata hannu Suka tafa

Yana kallonta yace Ina sonki tana Jin kunya yace bari nayi Sallah ya mike yayi Alwala zai tada Sallah ta mike tare da dagewa ta ture shi tana dariya tace yau baza kayi Sallar Isha da wuri ba sai na karya ma Alwala ta rungume shi,Zama yayi ba shiri saman Sallayar ta koma gefen bed ta

Please Login or Register in order to submit comment