Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fito ya zaga ya bude Mata kofar hannunta ya riko ta fito da kyar Suka Shiga ciki,dake private ne komai kudi dandanan suka ga doctor,suna shiga namijj ne likita ya tambayi meke damunta,tace period ne duk wata nake fama fa ciwon mara Kamar Zan mutu da dai na daina amma yanzu ya dawo,Nan take likita ya rubuta wasu gwaje gwaje suka je aka mata Affan ke biyan kudin da komai,suna dawowa wajen likita ya karbi test din ya duba yace ah kina da aure? tace a'a yace budurwa ce ke? tace ae,yace ai ke ba matsala ma kina yin aure Zaki warke, magunguna ya rubuta Mata yace ki dinga siyen wannan duk wata idan Zaki Fara,tace to Suka fito,takardar ya karba ya siyo magungunan kala biyu tana cikin mota tana jiransa Yana kawowa ta balle ta sha dake wannan ciwon bana karya bane
Mota yaja Suka wuce gida tun kafin su je gida Taji sauki sai gata tana cewa kaini gidan wata kawata ba wacce Muka je rannan ba,yace ba inda Zaki je ke kullum a gidan kawaye gida zakije ki huta,Baki ta bude tana kallon ikon Allah kamar ubanta yace na gama magana bana Kuma magana biyu ya wuce gida direct,Shuru tayi har Suka dawo ta fito garau da ita yace take your medications properly ya wuce bangarensa itama ta Shige palonta tana hutawa.

Sai dare ya leka ta window palonta jin kida na tashi yasan tabbas kallo takeyi a zaune ya hango ta a kasa ta mike kafafu tana cin gyada tana bushewa kallonta yake sosai ya furta liman me yasa baka zaman abokin Baban Raudat ba sai ka Zama abokin Baban Siyama,ko a suna ba hadi Raudha wow inda Manzon Allah ke kwance haba wa ma zai hada,Liman bazai yuwu ba dole mu tafi Oyo state daga nan ma har Ondo duk ba matsala,Raudat ce taji Kamar ana magana kasa kasa window ta kalla ta ganshi harda dage Mata labile mikewa tayi a hankali ta karaso jikin window ya zama tana palonta yana. Nasa shima Suka tsaya suna kallon juna babu kyaftawa,juyawa tayi da niyyar komawa yace ya jikin a hankali,da sauki ta furta tana Murmushi tace na gode,ko Oyo zamu tafi ne? Harda rera waka wai Affan Ina zaka je ne.....Ni zani Oyo na kwana....tana ta dariya tace da gaske zaka rakani? a ranta tace ai kuwa da jibi jibin nan zamu tafi idan Kuwa baza ka raka Ni ba to gwara nayi zamana a nan Ina ganinka kullum,katse Mata Maganar zucin yayi yace da gaske nake yi Indai babu matsala ni sai nayi masauki a hotel ke kije gidanku,tace ae da gaske gwara naje gida naga Iyayena jibi ka shirya mu tafi,yace an gama zanje wajen ogana na sanar masa tace to tare da komawa ta zauna shima ya juya cikin palonsa ya zauna cike da farin ciki

Aslam ne yayi sallam a gidan su Siyama Aunty tana zaune a bakin kofar Siyama Kamar me jira a fito a bata wani abu,Shigowa yayi gidan Aunty ta mike tana cewa sannu da zuwa Aslam,yace yawwa Aunty ya durkusa ya gaida ta da fara'a ta amsa masa sannan tace yarinyar nan daga magana tace Wai zaka Aiko da manya,Kawunta yace shi gudun abin kunya yake tunda ka auri babbar kawarta Kar a zage shi a gari,nace tunda Yara suna San juna ayi abin nan yace shi zagi yake gudu yanzu sabo da Allah ta bari Mana abi abin a hankali Kuma shine sai ta tashi hankalin mutane shine ta kulle kofarta tun sassafe ko ruwa bata Sha ba,Aslam a ransa dadi yaji yace a ransa ta min dai dai a fili yace zata fito ne kiyi Hakuri Aunty Ina kawun fa? Ya tafi Kauye sai jibi zai dawo ta window ya leka dakin Siyama ya ganta ta mike tsaye Kamar an kulle barawo a daki,Murmushi ta sakar Masa shima haka da Ido yace ta fito,jigin windown ta karaso cikin rada tace na fito? Yace ae,tawaye nayi fa,ba a yiwa iyaye tawaye ba nace abi komai a hankali ba,kasa control nayi my anger tayi rising yace to tayi falling down please come out, tace a siyo min Madara a hada min tea Kamar koko sabo da kauri,yace naji fito Aunty ta ganki,na Basu hakuri? Aslam yace a'a ba yanzu ba sai sun Amince sai kice kawu Nima nayi kuskure ka yafe min kin gane tace ae tana dariya tazo ta Bude kofa,Aunty tana ji suna ta kus kus ba a Jin me suke cewa sai gani tayi Siyama ta fito tace marar ji wlh Siyama bakya ji,Aslam yace a Ina za a siyi madarar?Aunty tace wacce madara? Ya kamata ta Sha Abu me zafi hanjinta ya warware,Aunty tace Indai kayan shayi ne akwai na Kawunta karka bata kudinka,Yace ai ba a shanyewa Kawu nasa ba ya juya ya fita a wajejen ya tambayi kanti aka nuna masa ya siyo mulu madara,Milo,Lipton,da duk wani kayan tea manyan gwangwani kobwanne,Sugar cube ma wurin kwali goma ya siya musu ya kawo,Anty ta bude baki tace wannan hidimar fa? Yace naki ne ke da Siyama Aunty ku kyalewa Kawu nasa,Aunty tace dan nan duka haka an gode Allah ya bar zumunci,Ruwan zafi tazubowa Siyama a cup da spoon ta kawo Mata,harda siyowa da bread me kwakwa,Siyama ta loda Madara da Milo na musamman ta hada abinta murtuk tana yagar bread me kwakwa da ya hado dashi Yana zaune ta shanye ta cinye rabin katon bread din,yace dole ki dinga kiba wannan duk a cikin ki, tace ya zanyi da tsutsar ciki ta min yawa ba ni kadai bace,Aunty abincin rana a zubo min tun jiya banci komai ba azumi Kawai na kusa yi saura kadan,Aunty ta zubo Mata tuwon shinkafa miyar gyada, ta sake kawo na Aslam again,Siyama tana sanye da t-shirt dinta me gajeren hannu da skert wata kalar dark green da ado a jiki,hula ce ta zamani me kyau a kanta taci abincinta,Aslam kuwa ya koshi yau bai ci ba,sai wurin magriba ta rako shi kofar gida yace Zan tafi sai nazo,Banda rigima a bisu a hankali,Siyama tace baka San kawu ba idan yayi magana baya canjawa, Inshaallah a kanmu zai canja akwai rabo tsakaninmu

Siyama tace yanzu da ka Haihu da Nusaiba da yanzu tana da cikinka,Allah ya taimakeni bata samu ciki ba ta haifar min masifar jininsu,Siyama tayi dariya ya juya yace Zan makara a masallaci ya ja hancinta kadan ya wuce Yana dago Mata hannu bye,Siyama ta tsaya tana cewa nace ya dinga hakuri sai anyi aure baya ji,ta koma ciki bayan sunyi Sallar Isha Aunty ta zaunar da ita tayi ta Mata nasiha da fada kamar ta dauka tayi luf da ita tace shike nan Aunty Zan gyara,Aunty tace ko kefa Haba Siyama kin girma ke ba yarinya ba ki dinga yi Mana haka tace na daina to,Aunty tace kinyi alkawari? Charity a ranta tace bayi ba a fili tace nayi Aunty tana murna...

Satin Nusaiba biyu da aure tayi kyau ta Kara kiba duk da cewa tana nuna Hali amma Sufyan wani abin Yana Dan biye Mata,Mama ce tace ta fadawa Sufyan Kar ya fita yau zata zo tace to,Yana zaune tana kwance tayi pillow da cinyarsa tace Honey Mama tace karka fita zata Zo yau,yace ai kuwa ya Zama dole na fita Sabo da Ina da aikin da zanyi yau a Office in tana so tazo da yamma ko ta jira ni,Nusaiba tace what Honey Mama ce fa yace to sai na fasa zuwa aiki kin San muhimmancin aikin nan a wajena Kuwa mikewa zaune Nusaiba tayi tace kaga Malam saurara aure fa ba hauka bane, Dan Kana mijina baka da damar taka ni yanda kake so,dama Ina Jin haushinka nace muje Kasar waje Honey moon kace na jira sai ka Gama wani aiki na hakura Ina jira Shuru na dawo nace tunda America baza ta samu ba ka kaini Moroco Nan Africa Abu yaci tura okay na dawo nace ka kaini nan Niger ko banza maga Sahara,ga Sefa dinsu me daraja sabo da bakin Hali kana min story story, kace muje yawon shakatawa ka wani siyo min English gown me araha kana nufin na saka na fita ga latest nan da ake kawowa daga manyan kasashe na fada maka ka dauki rigarka ka kaita inda zaka kaita ban sakawa wani muje Abuja nayi me a Abuja,a Abuja Zan bude Ido mene a ciki na gida Nigeria fa,yanzu Mama baka kyale ba zaka ci min mutuncin uwa wlh kaci mutuncin uwata sai na rama a Kan taka,Tsaki Sufyan ya ja yace kina haushi Kamar karya kullum haushi wan wan wan banda lokacinki na fuskanci ke kanki na rawa ko jahilci yana taba ki ya dauki wayarsa da key din mota ya fice ya barta tana zage zage

Tana haka Mama ta shigo tace lafiya Nusaiba daga aure? Tayani ji Mama wannan Sufyan din,Mama tace ki kwantar da hankalinki har yanzu fa bamu ci kwandalarsa ba ki Bari tukun mu Fara morarsa Mana zai ci ubansa kyale shi kin San fa wannan Bai kai Aslam kudi ba haka bai Kai Aslam kyauta ba,jeki ki shirya min girki me Dadi ki tabbatar yaji nama,Nusaiba tace Kai Mama suna dariya su a dole duniya ta samu sabuwa,Bayan Mama taci ta koshi tace Karo min karfin ac na Sha kafin na tafi,tana karewa gidan kallo tace oh God ta turawa yata kinyi dace Allah yasa ki Haihu da shi danki ya samu gado me tsoka,Nusaiba tace Ameen Mama kuma namiji Zan Haifa

Sai Yamma likis Sufyan ya dawo ya iske Mama a Palo,Zama yayi tare da gaisheta da ladabi Yana Mata Sannu da zuwa,Mama tace dama yanzu nake Shirin tafiya gida sai gaka,dama zuwa nayi Naga gida sannan na muku Nasiha,Dan Allah ka zauna da yata lafiya Ni nasan yarinyata Yar albarka ce bata da matsala Matukar ka kiyaye hakkinta kayi Mata abinda ya kamata abinda ya dace tayi Murmushi hehehe abinda ya dace wato duk abinda ta nema kana yi to zaku zauna lafiya zaka sameta me biyayya,Sufyan yace Inshaallah Mama,mikewa tayi zata tafi ya bata dubu goma ta karba tana tabe baki suna signa da yarta Nusaiba Wai baiyi abin arziki ba dubu goma kacal haka Mama ta tafi,tana tafiya Nusaiba ta rungumeshi tana shafa kirjinsa tace Kamar kudin da ka bawa Mama sunyi kadan,Sufyan Yana son Nusaiba shi yasa in tayi wani abin shi baya ganin laifinta yace karki damu idan munje gaida ta sai a Kara mata yafi haka tace sai mijina Suka haura sama suna dariya cike da so da kauna.

Aisha bayan barin da tayi bata fi wata ba ta sake samun wani cikin,ai Bashir Yana ganin ta Fara laulayi ya sameta a zaune duk ta gama lalacewa,yace Aisha tunda ke baki da kwakwalwar ganewa na nuna Miki haske kin kasa fahimta bari na fito kuru kuru kiji bana son haihuwa dalilin da yasa na auro ki naji labarin tunda Kika Yi aure da tsohon mijinki baki taba haihuwa ba ni nafi son mace juya,tunanina ke juya ce shi yasa na aureki sabo da na huta da jikinki amma ana taba ki sai samun ciki daga anyi abu sai ciki bazan iya ba,idan kina so mu zauna tare ki zubar da cikin nan idan Kuma bakya so to kije na sawwake Miki,Aisha tana kuka tana nadamar barin gidan Farooq tace ina son cikina,ya nuna Mata kofa yace jeki na sakeki saki daya ya rubuta takarda ya Mika mata,Aisha tana kuka ta hada kayanta sai gida.

Ummanta tana ganinta gabanta ya Fadi tace Aisha me Zan gani ba dai an sakeki ba? Aisha ta fashe da kuka,Umma tace ba kece da kuka ba nice da kuka Aisha,yanzu Zaki zo ki addabeni ki buwayeni ki damu rayuwata,ki dinga wulakantani nayi nadamar rabaki da gidan mijinki Farooq,Nice na zugaki laifina nane dama ance Indai yarinya ta wuce zaman gaban iyayenta to idan ta dawo sai ta kusa dukan uwarta,Aisha tace ai kece Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala kalli yanda na koma sai kace Jimina,wa yace ki yarda da shawara ta,ai da kina da hankali tunda ni Kika ga na kauce Hanya sai ki gyara min ai Nima ban wuce ayi min fada ba tunda na Fara manyanta kullum kwakwalwata sake kwancewa takeyi Saura kadan Aisha tayi dariya yanda Umma tace kwakwalwarta ta kwance, Aisha ta kwashi kayanta ta koma ciki wani sanyi taji a rayuwarta.

Farooq Kuwa da Nabeela amarci suke Sha amma zuciyar Nabeela Babu dadi tunanin Affan takeyi Ina zata ganshi ta nemi yafiyarsa sanna son Affan take kamar hauka ko sex sukeyi da Farooq sai ta tuna Affan take gamsuwa sunayi tana ganin Farooq kamar Affan ne ke Mata sai tayi ya jin Dadi,Indai bata tuna Affan ba to baza ta gamsu ba ranar, gashi kunyar Affan take tunda yazo ya samu an daura Aurenta da dan Uwansa bata sake farin ciki ba a rayuwarta wannan yasa ta tsani Yusuf gaba daya basu zauna lafiya ba,ta dinga nunawa Yusuf halin ko in kula tun Yana binta har ya gaji Suka Fara fada kullum basu da kwanciyar hankali har ya koma wulakantata karshe ma ya saketa hakki ne ya Kama su kwata kwata Allah bai bari sunji dadin auren ba,Farooq Kuwa zuciyarsa tana ga Aisha Kawai gangar jikinsa ce a wajen Nabeela nan ma dai Nabeela bata Yi dace ba.

Kamar yanda Raudat tace Affan ya shirya suje garinsu ranar na zuwa wani wanka Affan ya dauka da jakarsa ta kaya me kyan gaske in ka ganshi ka rantse turai zai tafi,Raudat kuwa wata doguwar Riga tasa na leshi dinkin manyan Mata masu ji da kansu ta Sha dogon takalmi da Jakarta ta kayan sawa sai hand bag komai coffee and white,tana Fitowa ta mikawa Affan flight ticket,wani yaron Affan ne yazo a motar Affan ya kaisu airport suka shiga jirgi ranar farko kenan da Affan ya Shiga jirgi tsabar gayu sai kace Wanda ya shekara dari Yana shiga yanda yake tafiya Yana gabatar da komai nasa,ga sit dinsa ga na Raudat suna zaune idan ya saci kallonta sau daya sai ya dauke Kai itama sai ta juyo ta saci kallonsa haka suke faman Yi har suka sauka lafiya,suna zuwa wani driver ne da mota me tsada Yana jiranta,suka Shiga mota da Affan ta Fadi sunan wani Hotel a garin ta rigada ta Masa booking Bai kashe kwandala ba,suna zuwa Hotel ne me tsada da kyau har room dinsa sannan tace Zan tafi zan dinga kawo maka abinci daga gida idan Kuma kaci a nan baka bukata ka fada min a waya tana kallonsa tana Murmushi,yace to sai ki ta min abu da kudinki karfa Watarana a min gori ni bana so nasan halin Mata bana Jin Dadi ki dinga kyaleni Ina biya Mana please bana so idan ba Haka ba Zan koma gida Kawai kin maidani yaro,Dariya tayi tace afwan to ka huta ,yace karki kawo min abinci nifa ba yaro bane ba Kuma duhun Kaine dani ba sannan Ina Jin turanci,tace to sorry na daina tace zanzo da dare muje yawo ta Kai hannu zata ja Masa gemu ya goce yace wannan fa raini ne ke ba matata ba sannan ba budurwata ba Zaki lalatani ya juya tare da rufe kofarsa,ta tafi tana Murmushi dama tsokanarsa tayi tasan fadin ransa.

Yau Kawu yana dawowa Siyama ta masa Sannu da zuwa ya amsa ta karbi kayansa ta Kai daki sai tsarabar Kauye lafiyayyen nonon shanu kindirmo cikin katon wani bowl,Kwan zabi,etc Aunty tace Sannu da zuwa Suka shiga daki Siyama kuma ta Kira Aslam,kashewa yayi tare da kiranta back sallama tayi ya lumshe Ido yanda muryarta ke tafiya da Imaninsa,inyini yaya ya aikin,lfy Alhmdllh ya furta Yana gyara kwanciyarsa saman kujera tace Kawu ya dawo yanzu,yace Allah mun gode maka tunda ya dawo lafiya daga nan Suka fada hirarsu ta masoya har Kawu ya fito yayi wanka tare da gabatar da Sallar Isha Yana Jin Siyama ta makale murya tana ta yiwa bawan Allah shagwaba,bata San yana jinta ba,tana kwance a tsakar gida suna Palo shi da Aunty ita Aunty ma bata ji me take cewa ba amma Kawu hankalinsa na kanta,karaf yaji tana cewa kasan Ina sonka nima amma sai kayi ta cewa Kai kadai kake so na gobe zaka Zo da Yamma,yace bayan kin daina zuwa layin mu ma,tace zanzo ne ,Kawu ya zaci Siyama gidan Farooq take shiga bai san ko taje unguwar ba a waje suke Zama Kuma tunda Nusaiba ta bar gidan sau daya taje,Kawu a ransa yace wato Siyama ba Wasa take ba zuwa zatayi ya Mata cikin shegen amma gobe zai gani idan zata fita, gajiya yayi da ji ya fito,Siyama tana ganin ya fito da Fushi tace Zan kiraka Yaya ta kashe wayar amma sai tayi kamar bata kashe ba taci ga da cewa ka jirani gobe zanzo gidanka da Yamma,Dariya tayi tace hmmm sai dai na zo,kawu yace Siyama zo magana tayi Aslam Kawu na kirana ka kirani anjima
Kawu ne ya daka Mata tsawa Allah yasa dama ta kashe wayar, yazo ya fisge Wayar tunaninsa wayar suke da Aslam ya Kara Wayar a kunne Yana masifa yace duk abinda ya samu yata Kaine wallahi Matukar aka lalata min yarinya Kaine ya Danna wajen red ya kashe bai kula ba dama a kashe take,yace ke Kuma Siyama duk abinda zaku yi kuyi bazan bashi ke ba ya juya ya koma daki.

Siyama ta fashe da kuka kasa kasa karshe ma ta koma dakinta ta kwanta,washe gari Kawu ya kafa ya tsare Yana jira yaga ta Ina Siyama zata fita,4pm yaga tayi wanka ta shirya ta saka hijab tace Aunty zanje karbo Miki Humrar, Kawu yace gidan ubanwa Zaki je,Ashe da gaske kike Siyama gidan Namiji Zaki je,tace nife ba can Zan je ba jiya ma kawai fada nayi amma na kashe wayar,Ni kike tsokana sabo da ni sa'anki ne ya taso zai sharara Mata Mari tace a'a bada Kai nake ba da Kaina nake tsokana,yace to daga yau ba inda Zaki je na hanaki fita ko kofar gida Kuma ki fadawa Aslam din Kar ya sake zuwa min gida tunda ba alheri kuke shukawa ba,ke Zaki iya sani inyi abinda banyi niyya ba.

Siyama bata ce komai ba tace kayi hakuri kawu ta koma ta zauna a dakinta,Aunty ta fito tace wallahi abinda kakeyi ba tsari gaskiya duk abinda yaron nan yayi maka idan yaji ka hanashi zuwa gidan nan ai mutuncinka zai zube dan Allah karka Yi haka ai da kunya,Siyama baza ta aikata ba wlh ba abinda zai faru me yasa kake haka wai,Kawu ne ya mike ya fice,Yana fita ya hadu da Maman Nusaiba ta dawo daga unguwa ta Masa kallon banza tace oh Mallam Dauda sai muka ji Kuma wannan matsiyacin zaka aurawa Yar rikon ka sabo da ba yarka bace za a zalunci yarinya a bata me karayar arziki,da yarka ce ai da baka yarda ba,Kai Kam juya marar amfani,ai Kai hoto ne a duniya mutum mutumi tunda baka haihuwa mene amfaninka baka San ciwon haihuwa ba baka San zafin da ba,in Banda Kai kwangiri ne kana gani 'yata ta fito sai da muka sa ya saketa sabo da bakin talauci shine Kai zaka Kai Yar wani sabo da zalunci me za aci da Aslam,ka duba Nusaiba yanzu ta shiga daula fantamawa takeyi yanda take so, tsohon banza ta juya ta wuce,Mamaki ya Kama Dauda ya bude baki haka Kawai shi ba kulata yake Yi ba ta bude baki taci mutuncinsa haka ta tafi,yace irin wannan annoba ne ga al'ummar duniya wannan matar Shehu Yana fama ai fasa fitar yayi ya koma gida,Yana zuwa ya fara bawa Aunty labari kaf har gwadawa yake yanda Mama tayi Masa,Siyama ta kyalkyale da dariya ta dinga dariya tace hakkin marainiya ne,hakkina ne wlh a guji batawa maraya rai gashi Allah ya saukar da aya,wlh Kawu Ina jiye maka Kar rabo ya kasheka lokacinka baiyi ba,rabo kisa yake watakil sai baka raye za ayi,gwara ka hakura Kar lokacin zuwan 'ya'yana duniya ya matso kazo ka hana zaka iya mutuwa,Kawu tunawa yayi yanda akace rabo na kisa tsoro ya kamashi Kar ya mutu,Shuru yayi tare da lulawa tunanin duniya,Siyama ta dinga dariya ta mike ta ebo kindirmo ta zuba sugar tana juyawa tana cewa rai ,Kawu yayi Shuru Aunty tace ayi bawa da kafiya haba Dauda.










AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️


56-60



Official



By
AsmaBaffa







Page naku ne

UMMY M
MARYAM BASHIR
MBELLO








Dauda Yana zaune bai ce komai ba,Siyama tana kallonsa ko zata ji zai ce ya yarda amma sai ji tayi yace idan na mutu ma kwana na ne ya kare dama Allah yayi kwanana ya kare sabo da haka Ina Kan bakana Kuma karki sake yazo min gida,kwana uku Kawu ya hanata fita Kuma ya hana Aslam zuwa zance,Siyama duk ta Shiga duwa,Aslam ma Sai dai suyi waya a boye kasancewar yace sai ya kwace Wayar in ya sake ji suna waya,ai Kuwa Watarana Kawu ya Kama Siyama tana waya da Aslam,tana tsaka da waya sai ga Kawu Katsam ya Miko Hannu yace bani Wayar,Siyama tace Yaya Aslam karka kirani idan kaji Shuru Kawu yazo zai kwace Wayar,Aslam yace alright bashi I love you karki yarda a raba mu please,tace Inshaallah Muna tare har abada,Wayar Kawu ya fisge ya kashe ta gaba Daya ya juya ya tafi da wayar, Kawu Yana Fitowa ya fice daga gidan,Siyama ya bari tana kuka Aunty ce ta shigo ta zauna a gefen katifar Siyama tace kiyi hakuri Siyama,duk aure da Kika gani idan aka Yi sak ba wani kalubale to bai ma fiye Danko ba ko Mene zaka Nema idan da nasara sai an samu matsaltsalu sai an Sha wahala,abinda nake so dake kici gaba da addua idan Aslam ne Alkhairi Allah ya baki shi idan Kuma ba Alkhairi ne bane Allah ya zaba miki mafi Alkha....ba wani mafi Alkhairi Aslam ne Alkhairi na Kawai idan ana son zaman lafiya a bashi ni tun kafin na kangare na daina Jin magana gwara ma ki fadawa mijinki tun kafin na Fara fetsara a gidan nan,Aunty tace to fa ku Yara idan kuka tsunduma bakwa Jin Kira ai sai kiyi tunda bakya Jin magana..

Siyama ranar haka ta yini sukuku ko aiki bata taya Aunty ba,Aslam kuwa gidan da Mum take yaje ya sameta a Palo ita Daya,bayan ya gaida ta,Mum tace Aslam kamar kana cikin damuwa kwana biyu Naga Kuma kamar ka Dan rame lafiya? Marairaicewa yayi sannan ya Fara bawa Mum labarin komai,ita Mum Murna takeyi danta ya samu mace,yace Mum kina murna baki ji me nace ba Kawunta yace bazai bani ita ba Kuma ya kwace Wayarta sannan yace Kar na sake zuwar Masa gida,Mum ta kalli Aslam tace Inshaallah zai hakura karka damu ka kwantar da hankalinka,Mum taya hankalina zai kwanta idan ban sameta ba fa ya zanyi,Ni ban taba son wata haka ba,ka kwantar da hankalinka nace Inshaallah zai hakura Kuma ko waye haka zaiyi a matsayinsa na uba babbar kawar yarsa dole ya hana,Addua zaka Yi sosai,Aslam yace yanzu Mum baza kije min ba? Wannan yakin naka ne Aslam ka dage kawai,Shuru yayi Kawai ya zuba tagumi ya tsinci muryar Mum tana cewa Amma na maka sha'awar Siyama,Ki daina sha'awar min Mata Ni kadai nake son abata Wai yaji haushi tace baza taje Masa ba, Mum ta dinga dariya tace to aci gaba da sonta lafiya,tashi ma yayi ya bar gidan.
Bayan kwana uku Aslam duk ya wani fututtuke ya tashi hankalinsa ya rasa inda zai sa Kansa rashin Jin Siyama,itama bangaren Siyama haka.

Zuwa Yamma Siyama da Aunty Suna tsakar gida saman katuwar tabarma suna Jin radio Kawu Yana zaune saman kujera aka sako wakar soyayya Siyama ta mike zaune tana saurar wakar
Mawakiyar tace kaine

Please Login or Register in order to submit comment