Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu koma gida ba a nan zamu zauna harda gyara parking,farin ciki yasa Raudat ta Kara narkewa tace please kayi hakuri,Affan tsigar jikinsa tashi takeyi idan tana Masa Shagwabar nan tana tuna Masa da Nabeela,Murfin robar ruwan ya balle ya balli paracetamol biyu ya zuba a cikin murfin ya dan zuba ruwa ya wani narka maganin sai kace zai bawa dan yaye yace tsaya na baki to Yana kallonta,sabo da shine zai bata kalau take amma tace to tayi wani kasa da kai lagaf, Hannu yasa tare da dago kanta a hankali harda cewa haa ta bude ya zuba Mata ta shanye ji tayi kamar ta Sha alawa sabo da shi ya bata, ruwa ya bata a baki ta shanye abinta ta wani kwanta a saman kujera Yana cewa sannu yaki tashin mota sai data kwashe 30mnt tace naji sauki har na daina ji sannan ya yiwa motarsa key

yace me kike son ci? tace Ice cream ai Kuwa ya tsaya ya siya Mata wata katuwar roba guda biyu da su yogourt me sanyi ya dawo ya leko ta windown ta yace abinci fa ranki ya dade Hajiya Aunty? tace naci a wajen Hafsat,duk da haka sai da ya siyo Mata tsire lafiyayye sannan ya shiga mota Suka tafi, ana tafiya tana Shan ice cream dinta Yana driving yace ni bazan Sha ba? tace Sorry gashi yace tuki nake ai tace to sai munje gida,yace ki bani a Baki ,Ido Raudat ta zaro taji kunya tace bazan iya ba,yace kaji locality me nake ji ba dadi haka sai kace wani suna Siyama,dariya tayi taki bashi bai ce komai ba har ya kawota gida tayi godiya ta wuce part dinta shima ya shige wajen Sayyeed,tana zuwa tayi sufa akan gadonta tana tsalle da murna.

Siyama kuwa bayan ta Gama kukanta har kwana uku bata ga Aslam ba tana ta faman tunaninsa katsam ta fito daga wanka da Yamma yaro ya shigo yace Wai ance Siyama tazo inji Aslam,da sauri tace kace gani nan, ai ko Mai bata shafa ba ta zura skert da riga na material ta saka hijab me Kama da doguwar riga har kasa ta tafi wajensa,tana zuwa yaga fuskarta duk ruwa tayi wani fresh yace daga wanka Kika fito ne? Siyama tace ae Ina yini ya amsa da lafiya lau,tace rannan kazo Wanda ka gani ba Saurayina bane ba sonsa nake ba,yace in ma kina son abinki Charity me zance ni zuwa nayi na duba lafiyarki tunda yanzu kin watsar dani kinyi hadadde,Siyama kamar zata Yi kuka tace ba Saurayina bane tiryan tiryan ta bawa Aslam labarin Affan,yace hmm kice miji aka miki,a'a nifa ance maka sai na yarda za ayi auren idan bana so shike nan Kuma bana sonsa,Aslam ya sake cewa bari mu Fara ja baya Siyama tace kash kajika da wani zance akan Affan din me aka yi aka yi shi wani banza da shi zaka bani kunya Allah yawa kake yi,Aslam yace to shi kina ganinsa me kudi,kudin me wa yake ta kudinsa nawa ya tara,Aslam Yana ta bugar cikin Siyama bata gane ba,sai da ya gama Jin komai sannan yace to Hajiyar wanka in tafi ko na tsaya akwai labari? Siyama tace jeka,yace oh korata ma kike Yi kenan,Siyama tace nayi Fushi sai ka dinga min wasu maganganu haka marasa dadi,Aslam a hankali yace Ina sonki Siyama.....Baki ta bude tace so kuma Aslam? Yace ae ba sai kin so ni ba Kawai na fada Miki mind dina na gaji da hiding, idan Kika bari Kika auri wani laifinki ne na daina kulaki Kuma har abada ko a hanya gwara ma ki aure ni,Siyama ta rasa wanne irin murna zata Yi ta boye tace tun tuni sai da ka bari aka turo min wani wajena yanzu ya zanyi da Kawu? Yace ki San yanda Zaki yi please I love you,ban taba son wata haka ba sai ke sai Ina kusa dake nake gane ni Namiji ne tun tuni tun farkon zuwanku gidana na zaci ba so bane Kawai yasa Naga Nusaiba tafi min na aureta,Siyama ta rufe baki a ranta tace zuki ta mallen maza kenan sabo da ba Nusaiba,ganin bata da Niyyar bashi amsa ya juya ya Mata sallama ya tafi,Siyama Kuma ta Shige gida da sauri tana zuwa tayi ball da bahon wankansu ya fashe fas,Aunty tace Yar nan lafiya? Siyama ta kankame hannu tace wayyo Yana sona dadi kasheni cikin farin ciki ne, Aunty rungume ni dan Allah Zo ki rungumeni, Aunty taki kulata zuwa tayi ta rike jikin bango tana zan sume Iska zata daukeni wayyo Sanyi dadi Allah na gode maka tayi ihu,Aunty tace wallahi sai kin siyo Mana sabon baho akan Namiji Kika fasa Mana baho,za a siyo karki damu ta fada dakinta harda rawar sanyi tsabar farin ciki sai kace tana Jin sanyi haka take karkarwa.

Aisha watanta biyu a gidan Bashir duk ta rame tayi baki ta fita a hayyacinta gashi Hariji sannan Kuma Babu abincin kirki Yana samun kudi amma ya daina bata ci na kirki,a wata biyun ta samu ciki amma shi Bashir baya son haihuwa,ga mijinta can Farooq Yana son haihuwa basu samu ba taje tayi aure Kuma inda ga haihuwar amma ba a son yaran,gaba daya Bashir ya tsaneta sabo da ciki,ko ya ta bashi haushi sai duka a Haka cikin nata ya zube Aisha tayi barin Yan biyu twins,tayi kuka sosai ga rama ta kekashe ta bushe,Farooq Kuwa har wasu lokuta baiyi aure ba ya kasa kula kowa har ya gaji Mamansa ta hada shi Nabeela bazawara ita Kuma Maman Farooq kawar Maman Sabeer ce a can taga Nabeela,Aisha sai labari taji Farooq yayi aure tayi bakin ciki tayi kuka ta gode Allah har ta samu wani cikin,Bashir tsana ta dawo sabuwa dal

Nusaiba bayan ta Gama Idda da kwana uku Sufyan yazo gaida Shehu,Shehu ya sauke shi yace yaro daga yin iddarta da kwana uku har yaushe ta sanka da zaka ce zaka turo wannan ya nuna cewar tun tana da aure ka Santa dama kana sonta ko karya ne? Sufyan yayi mukus yace bazai yuwu ace daga Gama Idda da kwana uku Wai har kazo daga wata uwa duniya kana sonta Kai ba dan unguwar nan ba a Ina ka ganta sai dai idan dama tun tana da aure kana zuwa,Mama tana ji tayi gatsal tace yata shi take so kuma shi zata aura,Shehu yace ba matsala Kai Sufyan gaka ga Nusaiba duk abinda tayi maka karka soma kawo min kara ba ruwana ya tashi ya fice abinsa,Nusaiba ce tazo tace karka damu dashi Indai Mama tana sonka an gama,Sufyan Yana murna sosai ya tafi,Bayan kwana uku ya turo da kudin aure cikin sati biyu Mama ta yanke aure za a daura,Shehu ba ruwansa a ciki sai da daurin aure yazo sannan ya shige gaba Sabo da yarsa ce ba yanda zaiyi aka daura auren Sufyan da Nusaiba

Nusaiba takanas ta tafi gidan Aslam ta kwankwasa ya zaci wani ne ya bude sai kuwa ta shiga ciki tana yiwa gidan kallon banza harda cewa to Ina Aslam Dan karya gashi na riga ka aure Kuma na sake samun wani me kudin Allah ba Azzalumin bawansa bane bazai barni cikin wahala ba na sake tafiya gida me ac sai naga ta tsiya Kai Kuwa gaka nan tsiya tsiya kalli wannan dirty smelling House din naka nafi karfinka tana Jan tsaki ta juya ta bude kofa ta fice tace aci gaba da Shan talauci lafiya,Aslam baki ya tabe ko a jikinsa yace Wanda ya kulaki shine banza baki da ajin da Zan saurareki,Nusaiba tana jinsa ita Kam tayi gaba abinta.








Masu sharhi Ina Matukar godiya






AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

46-50


Official



By
AsmaBaffa





Page naku ne

MRS SAS
YAR AUTA









Sufyan Isa,Dane ga Isa Yan garin Ajingi ne Kano amma a cikin Kano suke danginsu ne a Kauye amma uwarsa da ubansa da kannensa guda bakwai suna Kano kofar Ruwa,Sufyan shine Babba a gidansu talakawane, Allah yasa Sufyan yayi degree ya samu babban aiki na gomnati yayi aiki da shekara hudu haka Kawai ya ajiye aikinsa ya fito takarar Chairman ya koma siyasa,bayan anyi zabe ya Sha kasa ko kansilan nadi ba a bashi ba,karshe talauci ya sake baibaye su ya Shiga Neman aikin kamfani bai samu ba sai da ya kwashe shekara biyar sannan ya samu aiki a wani kamfanin shahararren me kudi ya bashi C.E.O ga Albashi me tsoka yana aikinsa sosai bai da wani aibu sai dai dan Adam kowa Yana da Hali me kyau Kuma ba a rasashi da hali na banza ko ya yake,ana haka ya ginawa iyayensa gida me kyau shima ya gina nasa gidan me kyau sosai amma bai Kama kafar gidan Aslam da bank Suka kwace ba Babu hadi ma,
ya mallaki motarsa me kyau har ya hadu da Nusaiba ya aureta Kuma.

Kwana uku da daura aure Nusaiba ta Sha gyara ta ko Ina tayi kyau sai kamshi take yi,ranar Kuma aka Kai amarya gidan mijinta me kyau kana gani kasan ba gidan talaka bane,zaune take a saman gadonta dake dama Kawai daga ita sai lefenta da kayan sawarta Amma komai na furniture ya zuba abinsa.
Sari ne a jikinta Riga da skert maroon ta yafa mayafinsa kyau Kam tayi,9pm angon ya shigo da Sallama hannunsa dauke da ledar kaji da kayan makulashe,Zama yayi a gefenta yace Alhmdllh Ni Kam nafi ko wanne Namiji dace a duniya,yau na mallakeki burina ya cika,Nusaiba tayi Murmushi tare da bude mayafin data rufa a kanta,yace tashi kiyi Alwala,mikewa tayi ta sheka wanka da Alwala ta fito shima ya shiga,shiryawa tayi cikin kayan baccinta masu daukan hankali sannan ta daura zani tasa hijab har kasa bayan ya fito shima ya shirya ya sa jallabiyarsa sannan Suka gabatar da duk abinda akeyi na addini da na al'ada,ledar ya jawo ya bude musu kaji ne da su Yogourt da sauran kayan makulashe da fruits

Plates ya dakko ya zuba musu ta kalli Naman tace Wai brolas ne ko Maja? Sufyan yace Ina Zan sani ni da na gansu a gashe na siyo,tace maza dai har abada baza kuci gaba ba,tunda aka halicci iyaye da kakanni kowa kaza kaza dai ankonta kuke Yi ko wanne ango ankon kawo kaza,Sufyan Yana Murmushi yace to me kike so? tace Ina laifin ma tattabara tana magana Yana bata naman a baki tana lamushewa amma tana kushewa,sai da suka koshi suka gama komai sannan ya dauketa suka haura saman bed abinka da bazawara tsagera zagewa tayi Suka farantawa juna rai Suka jiyar da juna dadi sosai Sufyan sai yabonta yake yace Yan unguwarku sunyi sakaki na daukeki shike nan,Rungume shi tayi tana I love you a haka har bacci ya kwashe su.

Siyama ce ta zubo shinkafa da wake da Mai da yaji sai salat ta toza wani katon plate kamar mutun uku ne zasu ci tasa a gabanta zaune a tsakar gida saman Sallaya da yamma sanye take daga ita sai vest fara da English skert wani me kyau brown Mai adon fulawowi fari,jikin nan nata sumul sumul komai Masha Allah,ta sa Hannu tana ci baza ma tasa cokali ba,Kawu ne yayi sallama ya shigo sai ga Aslam ma a bayansa sun shigo yasha farin wani yadi me kyan gaske yayi kyau Kamar baza a mutu ba,ya shigo Yana takunsa na Izza,Aunty ce ta amsa sallamarsa,Siyama kunya ta kamata sabo da irin abincin data zuba tana ci ya kamata,Aunty ce ta dakko tabarma tare da shimfida Masa ya zauna Suka gaisa

Siyama tace Ina yini amsawa yayi Yana murmushi,ta mike ta kawo Masa ruwa pure water Yana faman binta da kallo,Kitchen ta Shiga ta zubo Masa abinci a plate ta rufe ta kawo plate din salat da Maggi star ta ajiye komai sannan ta koma ta zauna a gaban abincinta,sabo da kunya Siyama tace Aunty kin siyo min maganin tsutsar cikin nawa Kuwa? Aunty tace wanne tsutsar ciki sai dai ki boyewa Aslam amma kowa yasan irin mugun cinki,Siyama baki ta turo tace to ba tsutsar ciki ce ba suke tashi suna neman abinci,Indai suka farka daga bacci to sai na Fara Jin yunwa shike nan ba zaman lafiya idan ban ci ba Kuma fa,Aslam Murmushi yayi ya kalleta ya kalli abincin Siyama tana cin abinta,da Ido tace kaci mana,juyawa yayi ya kalli Aunty da Kawu yaga ai hirarsu suke Yi hankalinsu baya wajensa ya kalli Siyama da Ido ya fada Mata bazai ci ba harda makale kafada,Murmushi tayi tana leka su Kawu sabo da Kar su Kama ta,tashi Aunty tayi da Kawu Suka Shige daki suka basu waje,Siyama ce ta leka palon taga sun shige bedroom da sauri ta jawo abincinsa gabanta ta tona gefa tasa salat da su tumatir ta ebo a Spoon ta Mika masa a Baki ya tsaya Yana kallonta bai bude bakin ba,cikin muryar rada tace kayi sauri kafin su fito fa bazan iya baka a gabansu ba,Baki ya dan bude ta zuba Masa Yana ci ta sake lekawa dakin su Kawu taga dai basu da niyyar fitowa taci gaba da bashi a baki yana ci,sai da ya koshi Yana Shirin cewa ya koshi Kawu da Aunty Suka fito ai da sauri Siyama ta tura plate din Gaban Aslam tana basarwa taci gaba da cin abinta,Aunty ta fito sanye da hijab tace Aslam har ka koshi dan Allah ka cinye ta nan fa ba wajen Kara bane,Kawu yace ke Siyama ku tashi ku koma dakin zaure ko yafi sakewa a.....kafin ya karasa Siyama ta mike tsaye ta kwashi abincinsa da ruwa,Shima mikewa yayi ya zaro dubu biyar ya mikawa Aunty yace gashi Aunty Kya sa ko Kati ba yawa,Aunty tace harda kokari haka to fa an gode an gode Allah ya Kara sutura yace Ameen Suka koma dakin zaure Wanda ya Sha gyara sai kamshin turaren wuta yake Yi.

Suna shiga Siyama ta dawo ta dauki nata abincin ta wanke hannayenta tare da daukan wani spoon din ta shiga daki ta saka hijab me hannu ta koma wajensa,tana shiga ta iske shi a tsaye tace baka zauna ba,yace tsutsar cikina ce ta tasheni,dariya Suka Yi gaba daya suka zauna tace dan Allah kaci da yawa nasan baka ci komai ba,yace indomie naci Mana,indomie abinci ce? please....ta karasa da shagwabar da hankalin Aslam ya tashi Yana Mata wani irin kallo cike da so Wanda yasa yace kin San me tace sai ka fada yana kallonta Ido cikin Ido ya furta Ina sonki Charity na matsu na jiki kusa dani, Charity tayi Murmushi tace hmm ban baka labarin wata kawata ba Haleesa wata daya da aure jiya naje gidanta na samu tana sheka amai nace haleesa lafiya? Charity tana wani magana ana Yi da hannaye ana style da hannaye Wanda sun Sha lalle me mugun kyau Wai dan Aslam ya gani,tace Ina fada maka ta sake daga hannayen tana jujjuyasu tace dan ubanki Charity ciki ne dani, ai tunda na bude baki kasa rufewa nayi,tana bawa Aslam labarin shi Kuma ita yake kallo kamar tv Yana dariya tun dazu yaga lallen amma ya nuna Kamar bai gani ba shine yanzu labarin ma Sai an sake nuna Masa lallen.

Magana yayi yace ya birgeni haka ake son Namiji kema Watarana haka Zan Miki naki,Charity ta bude baki kunya ta kamata ta rufe Ido da tafukan hannaye tace ba ruwana ni dai Kawai sai a ga Yar Baby ta ace Yar gidan Charity ce wallahi haka zance duk Wanda taji yace da mamanta Charity Kar ta sake ta yarda,Aslam yayi Murmushin Jin dadi yace har na hango kanmu,Ki fadawa Kawu Zan turo a kawo kudi,Siyama tace da wuri haka? Yace kin San Kuwa yanda hankalina ya tashi da naga kina zance bazan iya ba wani yazo a samu matsala,Siyama tace Ina tsoro Kar Kawu yaki yarda sabo da Nusaiba,Aslam yace karki yarda a hanaki aurena kinji dan Allah bance ayi musu rashin kunya ba dole muyi musu biyayya abi a hankali amma ki dage kice sai ni,Aslam Yana yiwa Kansa campaign yace wasu tanadi da na mana sai dai munyi aure,Siyama tace duk abinda ake ciki ka dawo jibi,yace gobe Zan dawo ni ban gaji da ganinki ba tace Allah ya kaimu,mikewa yayi yace zanje wurin Mum,tace kace Ina gaishe ta yace zata ji itama ya zaro dubu biyar ya bata taki karba yace bana son musu,ta karba tare da furta na gode ka manta ledarka da ka shigo da ita tana kusa da Aunty,Aslam yace wayarki ce,waya na siya Miki Zaki ga Simcard din a cikin ledar ki saka sai na kiraki anjima ya rike hannunta ta zame a hankali yace Ni kike ma Haka Yana Murmushi tace muna yin aure kazo kayi ta rikewa,an gama ya furta Suka fito ta rakashi da motar Sabeer yazo ya shiga abarsa ya tafi ta koma ciki taci gaba da dura abincinta.

Washe gari da safe taje gaida Kawu Aunty tana dakin tace Kawu ya amsa tana kunya tace Aslam yace zai fito,Kawu yace daga Ina zai fito? Takara zai fito ko kuwa daga daki? tace zai turo nake nufi,kawu ya gane fa yace baro zai...a'a fa kawu zai turo da manyansa neman aurena ,Kawu yace Yar jakar uba ai na gane so kike ki jawo Mana zagi da abin kunya a unguwa,yanzu idan aka ji mijin kawarki Zaki aura ai mun shiga uku a layin nan da zagi,Aunty tace sai ace ma itace ta rabata da gidan mijinta gashi Yanzu ta aure mijin nata ai ki auri Affan yafi Miki Siyama,Kawu yace rabu da Yar banza Ni baza ayi haka dani ba ki jawo min zagi,Baban Nusaiba Yana ganina da mutunci ace haka ta faru ai ba mutunci,Kece fa babbar kawarta kaf unguwar nan tare aka sanku yanzu sai aji kin aure tsohon mijinta bazai yuwu ba sannan naga Alama kina son Aslam baki son Affan zanje na bawa liman hakuri abin bazai yuwu ba amma ki sani bazan aurawa Aslam ke ba,nasan ya cancanta mutumin kirki ne amma ya auri babbar kawarki ya dawo ya aureki haba Siyama ai da kunya

Siyama tace to ni shi nake so bazan taba son kowa ba sai dai na mutu ba aure Kuma ai lokacin da yake baku kudi karbewa kuke Yi baku ce mijin kawata bace bai Dace ba sai ku karba ko musu bakwa Masa Sabo da lokacin Yana da kudi Sanda zanje gidansa wanke wanke da shara kune kuka Amince baku gano rashin dacewa ba budurwa dani katuwa naje gidan best friend dina wanke wanke da shara bakuyi tunani haka ba kuka Kora ni naje can yanzu Muna son juna shine zaku ce mijin kawa ne Kuma ai ya saketa tayi Aurenta Kuma ita tace a saketa tazo ma tace idan na gani Ina so naje ayi Dani sabo da haka na gani Kuma Ina so a aura Masa ni Yana so na shima Kawai in Kuna son zaman lafiya ku bashi ni a huta,rufe Mana baki shashasha abinda babba ya hango yaro ko ya hau bushiyar rimi bazai hango ba, wallahi wani yaron ba amma ni abinda babba bai hango ba na hango cewar Siyama,zageni ki huta Siyama cewar Kawu, Siyama ta mike tsaye tana hawaye tace da Ina da iyaye ai baza suyi min Haka ba Dan anga ubana ya mutu uwata ma ta mutu shine ake ta nuna min iyakata ta nufi kofa zata fita ta sake cewa Kuma Allah Matukar a watan gobe ba ayi aurenmu ba sai naje ya min cikin Shege,sai na jawo muku abin kunyar da yafi na auren tsohon mijin kawata da wancen abin kunyar gwara na wannan ta juya ta fice ta sake cewa Kuma za a gani kwana nan Zan Fara amai,Kawu da Aunty Suka saki salati Aunty tana yau ga zamani karshen duniya kaga Dauda ka barta ta aure shi wallahi yaran yanzu basa Jin magana basu da hankali ba irin yaran da bane masu biyayya yaron yanzu sai hakuri da addua duk inda ka kai da tarbiya sai addua,Siyama dai bata Mana musu tana Mana biyayya tsakani da Allah tunda kaga ta dage a wannan gaskiya da matsala.
Kawu yace ke har kin tsorata karya take baza ta iya ba ni nine ubanta bazan yarda ta jawo min zagi a gari ba,Aunty tace gaskiya ka ba yarinya zabinta mene aibun Aslam kaima wallahi butulu ne tunda har ya baka jari ka tsaya da kafafunka yanzu bama cikin wahala amma yanzu akan wata banzar Nusaiba da mutanen gari za kayi butulci,Dan Adam ai ba a iya Masa ko kayi ko kar kayi sai ka samu masu zaginka da masu yabonka haka duniya take bare Nusaiba da uwarta Wanda kowa yasan me Suka aikata ai Bari kaji ba a birge dan Adam
Kawu tashi yayi a fusace ya fice daga dakin gaba Daya.

Siyama an kifa Kai a jikin katanga ana sharbar kuka tana Jin fitowar kawu ta Fara Zan mutu ubana mahaifi da zaka dawo duniya bakin cikin yayanka shi zaisa ka Fadi ka sake mutuwa ta biyu,idan da zaka dawo duniya kaga yanda yayanka ya rike yarka gudan jininka da nan take zuciyarka zata sake bugawa,Ummata kiyi fatalwa kizo kiga yarki za ayi Mata auren dole yarku ana Mata rikon sakainar kashi,Kawune yazo zai wuce ta kusa da Siyama tace sai nayi cikin Shege Aslam Zan dinga zuwa,Kawu Yana fita ya samo bulalar dalbejiya ya dawo ya hau tsulawa Siyama ta sake barkewa da kuka Yana tafkarta yace Dan ubanki sa'anki ne ni,har kin Isa ki dinga furta mummunar kalma akan Namiji Zaki je ya Miki cikin Shege da Amadou na raye na tabbatar dukan da zai Miki yafi nawa,Siyama taji duka ba sauki Kawu ba wasa zaneta yake ta fada dakinta da gudu ta kulle,Aunty tace ka bani kunya Dauda wallahi ka daina Dakar min yarinya ai da gaskiyarta kowa yasan Aslam mutumin kirki ne mene laifinsa,Siyama tana daga daki ta leko ta window Ido duk hawaye tace dan ma ka samu suruki me addini

Siyama yau yini tayi ba ci ba Sha sai kuka a daki,Aunty tayi tayi ta fito taki,Kawu Kuma ya shirya ma ya tafi Kauye sai bayan kwana biyu zai dawo,Aunty tana son yarta tace Siyama so kike Hawan jini ya kamani ko bari to na Kira Aslam a waya yazo idan yazo shi ai Kya bude ki fito,Siyama ta bar Wayarta tun safe a dakin Kawu Aslam Yana ta Kira ba'a dagawa,Aunty tana daukan Wayar Infinix Kiran Aslam ya shigo taga an sa My life,dagawa Aunty tayi Suka gaisa da Aslam yace Aunty Ina Siyama fa?Aunty tace dan Allah kazo kaga tun safe gashi har magriba tayi Taki Fitowa ta kulle kanta a daki ba ci ba Sha,Aslam yace sabo da me? Kazo gidan zan fada maka komai,Aslam yace gani nan,ya taho da sauri.

Affan ne ya dawo daga Office Raudat ta fito tana tafiya a durkushe ta rike mara zata shiga mota tana cije lebe, Affan har zai wuce ya dawo yace lafiya? Yaga Raudat tana hawaye tace asibiti zanje bani da lafiya ciwon mara nake yi, Affan ya bude baki yace ahh kice Kawai abin ne yazo,ke Haka kike naki? Rushing day ne? Raudat taki kulashi tana Jin kunya shi ba kunya ce da shi ba,key din motar ya karba yace na gaji amma muje asibitin na kaiki da kaina fatan kin Sa pad karki bata motar,Raudat ta shiga da sauri ya Shiga Suka tafi Suna tafiya yace Allah ya taimake mu da ba maza ne suke abin nan ba ai da mun Shiga uku,Raudat tana fama da kanta bata magana shi kadai yake surutunsa.


Na gaji bakwa sharhi yau









AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

51-55


Official


By
AsmaBaffa





Page naku ne

~s97863205
Aeesha








Har Suka isa asibiti bata magana private ya kaita ya bude mota

Please Login or Register in order to submit comment