Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[6/28, 1:46 PM] Sis Asma: BISMILLAH

🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮


1️⃣

Official



By
AsmaBaffa
Copy By Zainab Butalawa

Littafan Dana rubuta

GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MA'AIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
ME MAGANI
TUBABBIYA
HADIN KAI
RASHIN SA'A
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
TA GYARU
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA
DANGIN RABI
DUNIYATA AMNA
MAFARKIN FARIDA
WARE BAIKO.....


INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA SABON NOVEL DINA KAMAR YANDA MUKA FARA LAFIYA ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA TARE DA NI DA KU FANS ALLAH YA BAMU LAFIYA DA TSAWON RAI MAI AMFANI.

WANNAN NOVEL BANA KUDI BANE DAN NISHADINKU FANS ALLAH YA BAR KAUNA

DAN ALLAH A DINGA ZUBA SHARHI MUNA RAKASHEWA KAMAR YANDA AKA SABA🤣

WANDA SUKE GROUPS DINA DA WANDA NAKE GROUPS DINSU DA MA WANDA BAMA GROUP DAYA DUKKAN MASOYA NOVELS DINA INA MIKO GAISUWA INA DANNO MUKU GODIYA ME TARIN YAWA.

WANDA NA BATAWA RAI A YAFE MIN NIMA DUK DA NASAN AN FITAR MIN DA NOVEL DIN KUDI NA YAFEWA KOWA 🤣

WARE BAIKO KACOKAN SADAURKARWA NE GA KAWATA 'YAR ARBARKA
🌹AIDA MAMAN TASNIM🌹


Page Dinku ne manya manya

UMMI DEEJAT
AUTA
BESTYNBEELAT
MAMAN SAMHA
UMMUN SADDEEQ
MOMCY
MAMAN SADIQ
FANCY HONEY
RAHMA



Gudu take Yaya Sulaiman na binta da katuwar bulala Yana tsula Mata,ihu take tana gudu cikin masifa Sulaiman yace wallahi kinji na rantse sai kinje makaranta,Yar iskar yarinya kullum sai da duka za a raka ki school,Bata fasa gudun ba shima Bai fasa binta Yana duka ba tana haki Hadi da ihu Tace wallahi bazan je ba nace muku bana son makaranta bana so amma baza ku saurareni ba,Ni da Makaranta bama mutunci ba kawaye bane bana sonta.

Zanci ubanki cewar Sulaiman mutane suna ta kallonsu wurin 10am lokacin da a ake rakata da bulala makaranta in da sabo mutane sun Saba gani sabo da basa ganin budurwar a mai hankali shi yasa bata Shiga safgar kowa itama ba a kulata.

Shaffff....Sulaiman ya shabda Mata bulala again a Haka ya rakata har School,tana wallahi bazan Gane komai ba,na fada muku bani da kwakwalwar karatu ko wanne iri ne,ni karatu baya shiga kwakwalwata bazan Gane ba tana fadan Haka har ta shiga aji,Malam Yana ciki ko kulashi Bata Yi ba ta fada ciki da kalar tafiyarta wata iri ta saki jiki wani shakwaf sannan ta rankwafa gashi ko Ina jefa kafarta take haka take tafiya ita ba tafiyar maza ba kuma baza ace tafiyar mata take yi ba babu Wani gwalli ko yanga.

wuri ta samu ta zauna Jakarta tana saman cikinta hijab din ya karkace gefe,a jikin window ta zauna ta bude tare da zura kanta waje tana kallon compound,Malaman sun rigada sun Saba da halinta ba Wanda ke kulata Haka Malam ya gama darasinsa na mathematics

Zai fita ta juyo ta zabga Tsaki tace Sannu sai kaje ka Nemo X din da kanka,kullum kuce 2a-2b = 2ab find x waye zai nemo muku x din ita x din gidan wa take tafiya? Kullum a,b,s suna aji suna hutawa a saman allo ita x da kullum ake cewa a nemota Ina take tafiya ko yawon banza ita take tafiya? Idan mutuniyar arziki ce tayi zamanta a aji mana mu dinga kallonta,Malamin Takaici yasa ko kulata baiyi ba ya fice abinsa,Yan aji suna ta Dariya Amma ko kallo Basu isheta ba sabo da bata da kawa a makarantar,A babban kauyen nasu ma kawarta Daya ce Sakina Shekarunsu Daya Amma Sakina ita bata tsaya Wasa ba da wuri ta gama karatun secondary tuni ta Kama sana'a,ita Kuwa Har yanzu a Ss3 take nna ta Mata repeating har takai shekara 21years yanzu a haka,sabo da garinsu babban Gari ne na gaske sai dai Kawai local government din nasu ba a cikin birni take ba a wajen garin Adamawa take shi yasa gaskiya da wayewarsu da ci gabansu sosai kamar ba Yan Kauye ba banbancinsu babu yawa Dana cikin birni.


Yarinya ce karama Yar Fara kyakyawa a kalla zata Kai 6yrs,saman bene ta hauro da gudu sanye da Yar gown iya gwiwa me siririn Hannu pink cikin kyakyawan gidan take tafiya da gudu har ta shige wani lafiyayyen bedroom Wanda ya gaji da tsaruwa,tana Shiga tayi Sallama tare da cewa Yaya Nabeel Wai me ya sameka? kyakyawan Matashin Wanda aka Kira da Nabeel Amma kowa yafi saninsa da Lele sabo da Haka Iyayensa ke kiransa, juyi yayi a saman makeken bed dinsa ya sake kankame pillow tare da lumshe Ido ya bude tarrr saman Yar Yarinyar nan da alama kanwarsa ce

Yace Fadila Jeki ki fadawa Mimi da Affa ki basu shawara kice ayi min aure na girma,na Gama degree Ina da aikinyi me Zan jira Kuma, Yar yarinya Bata ganewa ta kyalkyale da dariya tace Yawwa Yaya Nima daga Nan sai a hada da nawa, muyi tafiyar mu tare ko,wanda aka Kira da Yaya ya hade rai yace nine na girma ke yanzu me Kika sani,kunya nake ji kije ki fadawa Affa da Mimi karki sake kice Ni na turo ki shawara Kawai Zaki basu,kice ya kamata a Fadawa su Kawu tunda Kinga sune Yan Uwan Affa sune zasu wuce gaba sai kice a fada musu su wuce gaba ayi auren Nawa,Dariya Yarinyar Fadila tayi cikin maganarta da ba Wani fita take ba sabo da yarinya ce sosai tace Yaya Yar karama ce fa Ni ai Mimi baza su yarda ba

Bazan sake kulaki ba Indai Baki je kin fada ba,Yarinyar Haka ta kwashe da gudu harda faduwa tana cewa Zan fada Yaya,part din Affa tayi ta Iske Mimi a can tana Shiga tace Affa Wai ayiwa Yaya Nabeel aure amma Ni dai bazan fada muku shi yace ba,gaskiya ba shine Yace ba,Dariya ta basu Affa Kuwa Nan take ya hade rai yace shine ya turo ki,na rasa me yake damun Yaron Nan Ina so yayi Ilimi me zurfi amma shi ba yaso shi yasa nace Yan Uwana su Kara maida shi kasar waje karatu Ya koma yayi Masters

an waye yanzu bai Isa ba a sati biyu Inshaallah zai bar kasar Nan Zan samu yan Uwan nawa,har yaushe Nabeel ya girma,har yaushe ya San wani aure me ya sani yaro ayi Masa aure Dan Kawai yaga Allah ya hore mana,a banza Muka Tara kudin yasan wahalar da Muka Sha,Ina laifin ma idan ya Kai matakin masters ya gama a yaso aure da wuri yace ayi Masa amma ko Degree biyu babu comon degree da kowa Yana da shi..

Ka bi a hankali dan Allah ai ba haramun bane Kuma Nabeel ai ya Isa aure akan a barshi Haka ayi Masa Mana ai karatu baya Hana aure,29yrs fa Tunda kaga Yana Haka akwai dalili cewar Mimi,Affa da Bala'i ya tasowa wa Mimi ai dama ke kike lalata shi to wlh ko me zaiyi bai Isa na janye maganata ba karatu zaiyi Likita nake so ya zama,Taya za a kaishi waje a kashe kudi akan ya Zama likita Dan iskan yaron Nan sai yaje ya karanta Engineering ya dawo, Kuma nace Kar ya fara sana'a sabo da Matukar Yana Kama kudi bazai ilimin ba amma karshe sai gani nayi ya hada gwiya da turawa ya kawo motocin aikin titin kwalta gashi Nan yanzu yaje Yana ta faman tara kudi baya Jin magana ta,sai kyale kyale da Hawa motoci Yana Wasa da kudi ga Kanina can Yana Gina Masa tankasheshen asibiti,to idan ba nan ce hanyar cin Abincinsa bafa Haba Affan Fadila ku dinga rage wannan yahudancin Kar ya halakar da ku,Tsaki Yaja tare da furta sai Naga Wanda ya Isa nace ae yace a'a ya fice abinsa.

A bakin kofar Palon ya Iske Lele ya Sha wata kafirar shadda milk ga Uwar suma taci kudi,Baffa ya kalle shi ya tabe baki yace Lele kalleka a haka Kamar wayayye Kamar Dan boko Kalar Ilimi, zubin Doctor Allah ya maka Amma ka Raina baiwarka ka zabi aure ka Isa kasa nayi abinda banyi Niyyar ba,ko da kudinka zakayi wallahi baka Isa ba bare ace Ni Zan maka dole, karatu zakayi kayi shiri Us zaka tafi verysoon bani da arzikin fitar da Kai waje nasan kana da kudi kaima Nabeel Allah ya baka amma Yan Uwana zasu yi,matsa ka bani waje shashasha ba abinda kuka sani sai aure kuyi ta yiwa Mata ciki kuna sakinsu to ba a gidana ba,yaro da Kai 29years kace Aure.

Nabeel har Affa ya Gama Bai ce komai ba har ya tafi ya shiga shirgegiyar motarsa driver Yaja,Nabeel ciki ya Shiga wajen Mimi dinsa.
Nabeel lele Yana shiga wajen Mimi kunya ta lullube shi sabo da Yana da kunya shi kam,Lele meke damunka haka?Kamar zai narke yace Mimi wlh aure nake so ki Masa magana please ni ko da wace ayi min tunda bani da budurwa,

Fadila ya cafka yace haka nace kice ba shawara nace ki basu ba ya zuba Mata rankwashi ta saki ihu ya tashi ya fice abinsa cikin Fushi da zuciya shima wata damfareriyar mota ya Shiga wacce tafi ta Affa tsada da kyau gata Fara driver ya tukashi ya fita sabo da Yana da meeting,a gidan motoci ne sunfi shida Guda hudu na Nabeel ne,Daya ta Mimi,biyu na Affa.

Sai dare Bayan Affan Nabeel Lele ya dawo ya huta yaci Abinci Mimi ta samu mijin nata cike da kwantar da Murya take Masa Nasiha tace Dan Allah Affan Fadila kayi Hakuri a fara yiwa Yaron Nan auren Nan tunda Yana so Kuma Allah ya hore mana tunda kaga ya matsa wlh akwai dalili Kar mu Bari ta sanadiyar Haka tun Yana Hakuri ya Gaza ya fada wani shashancin daban kasan dama fa ya koyo Shan giya a turai Yana Sha sama sama,yaran zamanin Nan sai Allah,Affa yace bashi da hankali Dan ubansa yayi iskancin Mana ai duniya ce,a'a kayi tunani a duba abin Nan fa,a Haka ta dinga lallaba Affa har ya Amince akan Nabeel ya Fadi wace yake so zai aura masa,ranar Nabeel murna kamar sai dai Kash bashi da wacce yaji Yana so a duniya Kuma babu macen da suke shiri da ita sai Basma Yar gidan Kanin Babansa sun danfi mutunci tunda Haka ne shi ba Wai auren soyayya zaiyi ba auren rage zafin sha'awa zai dinga manage da ita kafin Nan gaba ya samu nutsuwa ya Nemo wacce yake so a sake daura Masa aure ya rike Mata biyu,Nan take Kawai yace ai Basma yake so,Affa yaji Dadi Haka da ya sanarwa Kaninsa da Yan uwa sunyi murna

Bayan kwanaki aka Kai kudi tare da yin baikwo...
Nabeel sai murna yake zaiyi aure,Basma Kuwa ta Dade tana kaunar Nabeel tunaninta bazai so ta ba shi yasa tayi Shuru yanzu Kuwa ji take tafi ko wacce mace sa'a a duniya,sabo da samun Miji irin Nabeel sai yarinya me yawan azumi da Sallar dare,Haka Nabeel Kam yake nishadinsa Amma Bai damu da wata Amarya ba a Haka gani yake wani mugun so ne ya kamashi.

Yana gida abokinsa Ammar ya shigo yace Wai da gaske auren za ayi maka? Maganar da na fada maka a waya baka yarda ba kenan? No Lele yanzu dama soyayya kake? Baka da hankali ammar baka San love ba,Kuma Nifa kasan Sha'awa ce dani,lafiya tayi min yawa badan ma Ina mafarkin na dan rage ba ai da tuni sai ta Allah,ayi min auren yafi tun kafin na Fara barbare Yaran wasu.

Wai Affa Kuma a kaini turai kasan Allah bazan iya tsallakewa ba Ina ganin turawa da Mata kyawawa wallahi sai na Yi wannan Karon,Dariya sukayi Ammar yace tun baka San hanyar wajen ba kenan Ina ga ka dandana,Lele yace uban waye yace Zan kasa Gane Hanya,gashi Nan muna ganin jarirai Mata ba Kaya idan ana musu wanka nasan hanya Ina zuwa nasan inda Zan bi.

Ammar Yana ta Dariya yace Ni Kuwa kyankyamin Mata nake idan na tuna ta Nan suke jinin haila sai naji Takaici,Dariya Nabeel Lele yayi kyawawan hakoransa Suka bayanna,ya shafa dogon hancinsa tare da motsa Dan madaidaicin lips dinsa jajaye dasu abinka da fari yace Ni bana kyankyami wlh,Nifa jinin ma birgeni Ni yake musamman idan na tuna ta hanyar da yake Fitowa sai Naga shi Kam jinin yafi kowa sa'a a duniya duk wata zai ta sintiri a wajen,Da nine ai ba Haka ba,Ni so nake ma naji mace tanayin period sai naji wani kaunarta Naga tana wani birgeni har wani kyau suke karawa,Ammar ya dinga dariya harda buga kafa,inda Nabeel yayi sa'a akwai addini da tsoron Allah kowa yasan wannan duk maganarsa a wajen abokinsa yake Masa Wasa amma Mata ma basu isheshi kallo ba.

Ammar yace mamaki kake bani Nabeel yanda kake da tsananin kyau ga class jibi yanda Mata ke son alaka da Kai,Kai da zaka ji Mata Basu dameka ba sai kafi kowa son Mata Kuma ka bani kunya,Nifa ba wali bane Dan uwarka Ammar ni Kawai Ina so a min aure idan ba Haka ba wlh na Fara bin mata Ina da kudi ka sani,Allah ya tsare cewar Ammar, Yar hirar da sukayi da Ammar shi Nabeel tuni ya fada wani yanayi,suna Haka sai ga Yar school din su Nabeel tazo Meena,Tare sukayi secondary da su Nabeel tana mugun kaunar Nabeel,Meena kyakyawa ce baka da ita Masha Allah,tana zuwa wurin Mimi ta wuce Suka gaisa sannan ta fake da gaisar da Mimi tazo amma a zahiri wajen Lele take zuwa.

Sai da Mimi tace Bari a Kira Miki shi,Meena tace da kin barshi ma,Haba ai ko gaisawa sai kuyi a waya ta Kira Lele kazo ga Meena tazo,Takaici ya lullube Nabeel Haka Kawai shi baya son Ana Shiga harkarsa Matukar ba shine ya shiga taka ba,Tsaki Yaja tare da mikewa Yana gyara wandonsa Jean Dake Shirin faduwa kasa sabo da gayu,Ammar yace ba sai kaje ba ku gaisa ko Dan Kugunta ta goga maka ka samu yau ka samu bacci,Allah ya kiyaye ance ma Dan Iska ne Ni Dan Ina son Abu sai na lalata kaina,Haka yaje suka gaisa da Meena ba sakin Fuska ko kadan.

Daga lecture ta fito a birnin Abuja,Mota ce tazo ta dauketa me kyau, har taje gidansu Ranta a bace yake,cike take da Jin haushin Dan class dinsu Nabeel Wanda yanzu Haka da shi suke zana final year exam,ta kulle a Ranta yau sai taci Masa mutunci,Dan Kawai tace Yana Dan birgeta shine zai zageta a wajen kawayenta shi yasa Tace to wlh yau dole na nuna Masa ni waken suya ce na gagari kwari,Wayarta me tsada ta jawo tare zagawa bayan garden inda babu Wanda zai ji me zata ce,a zuciye ta shiga Neman Number Nabeel Amma bata samu ba,Nan take ta Kira kawarta bata jira me zata ce ba tace Turo min number Nabeel please,Maryam tace Allah yasa nima Ina da ita,ai Kuwa idan duk Kano Zaki zage sai kin Nemo number Nabeel a garin Nan..

Dariya tayi tare da kashe wayar tasan Halin kawarta Kawai data tashi turo mata number Nabeel sai ta canja number karshe ta turo mata da wrong number, bata sani ba kawai ta Danna Kira sai da ta Kira sau biyu Bai daga ba kafin daga bisani aka kashe Kiran aka kira ta back,Tsaki taja tace karyar banza wai su masu kudi.

Gabanta ne ya yanke ya Fadi Jin wata Murya me Dadi da taushi Sam ba irin muryar Nabeel din Data sani ba,Tsaki taja cike da ruwan masifa tace Malam ka Bude Murya aikin banza Dan Iyayi Kai har ka kana da damar da zageni waye Kai,Hey pls who are you? Basma ce dan iyayenka,Dan kaga Family Dinku masu kudi ne Kai kana da damar kace Wai kaga Alama sonka nakeyi,me zanyi da Kai samari Nawa ne ke bi na,daga yabonka sai kace sonka nakeyi harda cewa me zaka ci Dani talakawa ai shi yasa Naga Kai Ubanka da arziki aka haife shi,waye pls aka sake cewa ta waya,cike da bala'i tace nace Basma ce,what? Na cikin Wayar ya furta shima,shima yace Basma Ni Nabeel kike zagi Haka? Ita ma Basma bata gane ba Nabeel din da take Nema bane, tace ae an zageka Kai din banza akan na yabe ka sai aka ce sonka nakeyi Kai ka Isa na soka waye Kai,yaro da Kai me zaka tsinana min mutumin da ko tsaiwar minti goma baka iyawa jiki duk a lankwashe Kamar Dan daudu banza gara ajawo kit ta kashe Wayarta.

Nabeel ransa ya baci shi Basma zata zaga sabo da Yace zai aure ta ai Kuwa ko sama da kasa zata hade ya fasa wlh,Fitowa yayi a fusace sai dakin Affansa Yana zuwa yace Affa na fasa auren bana kaunar Basma yanzu ko kadan Kawai a ware baikon da aka Yi wlh ko Zan mutu bazan auri Basma ba,Affa dama dan Nabeel ya nace ne Amma shi Bai son auren ga Basma Yar Kaninsa ce sai yace,Kai kace kana so ka sani bazan iya tunkarar Yan Uwana da Maganar ba kaje ka samu shi Kawunku da kanka ka fada Masa dalilinka ba ruwana
Nabeel yace ai Kuwa zanje yau sai an ware baiko

Tunda Basma ta Kira classmate Dinta Nabeel taci mutuncinsa sai washe gari tana zuwa makaranta suka ga Nabeel shi da abokansa su Uku suna hira,tare suke da friends Dinta Yana ganinta ya yatsina kyakyawar bakar fuskarsa Nabeel din Basma na school wankan tarwada ne kyakyawa,Kawarta Maryam ce ta Masa magana Malam Nabeel Baki ya washe tare da furta Yan Mata sai kace wani Babban mutum haushi ya bawa Basma ta Masa wani kallon banza sai Kuwa yace Basma ba magana? Ko kallonsu Bata Yi ba,su Nabeel suna tafiya ta kalli kawayenta tace shege ai yaci zagi na Gama da shi nayi Masa fata fata,mamaki sukeyi yanda take da shariya ba komai take tsayawa ta saurara ba amma akan Nabeel ta zauna tana masifa.

Maryam ta kalleta da zolaya tace Kuma Nabeel din shine Wanda Kika Kir....kafin ta rufe Baki tace shine Mana harda wani makale murya Yana min yanga Ni Kuwa na Masa gaja gaja na kashe wayata Wai harda tambaya what...Basma ni Nabeel kike zagi? Ni Kuwa zagi ta Uwa ta uba na Masa shine fa Kika ga ya tsorata yanzu Yana washe min Baki,kin San ni ban iya Fushi,Maryam tana ta mamaki sabo da ita tasan tabbas ta canja number Daya a number din Nabeel amma gashi Basma ta tabbatar ta samu Nabeel a waya, tunanin ko dai data ji Wrong number ne ta nemo wajen wasu Haka Maryam ta bawa kanta amsa.

Basma tace ai Nabeel ya shiga Uku Dani ya tsokano tsuliyar dodo yanzu Bari na kirashi da Daya layin Nawa na Raina Masa wayo,Wayarta ta zaro tare da Nemo number data Kira jiya,sai data Yi bugu biyu kafin a dauka sai taji an kashe an Kirata back,muryar Nan me Dadi ta sake dukanta Tace Nabeel ka daina wannan Iyayin kasanni na Sanka Ni ba birgeni kakeyi da wannan muryar ba ka fito min a mutum,Nabeel ya Gane muryarta Kawai Yaja Tsaki tare da kashe wayarsa lokacin Yana tare da ma'aikatansa Yana musu bayani akan wani aiki, Engineer kenan.

Adamawa state matashiyar budurwar ce ta sake fitowa sanye da uniform maroon and white wow kyakyawa da ita karshe,skin dinta chocolate me haske baza kace Fara Kar ba Kuma baza kace da ita baka ba,yanayin dirinta gwanin birgewa Haka fuskarta da komai nata me kyau ne, da kuka ta fito daga Dan kyakyawan gidansu na bulon siminti,kaf kauyen ba gida me kyan nasu gidansu na bulon siminti a sumulmule yasha paint green, ciki harda tiles zata Kai 19yrs wuyan Hijab dinta ya karkace Bari daya,jakar makarantar nata ta ratayota ta Gaban Dan guntun hijab din nata,tana gudu tana kuka matashin yayanta Yana binta da bulala suna ta gudu a Gari ana kallonsu.
Tana gudu tana magana wallahi bazan je makaranta ba,nace muku bana son makaranta Ni,ai ba Dole bane,ko dole sai anyi karatu ake samun ci gaba,Wanda yake binta da bulala yace wallahi dole sai kinje makaranta Dan ubanki,Ni bazan je ba wlh ka rabu Dani bana son makaranta Ni Kuma ko ka kaini sai na gudo,saurayin Allah ya bashi sa'a ya cafketa ya dinga tsula Mata bulala tana ihu amma tana kuka tana cewa bazan je makaranta ba Ni bana son makarantar ta sake kwashewa da gudu ya bita Ana ta kallonsu dama an Saba ganinsu kullum da safe sai ya rakota da gudu suyi ta gudu Amma baza taje ba,sai da ya Rakata har makaranta da bulala suna gudu tana ihu sannan ya dawo gida Yana masifa.

Wani dattijo da matarsa suna zaune a tsakar gida Yana bala'i Papa wannan Yarinyar
dole sai an dau mataki a kanta,ka duba girmanta mate dinta duk wasu sun Gama secondary da 3yrs Amma ita 21yrs har yanzu tana ss3 sabo da rashin zuwa makaranta gashi har yanzu Bata iya karatu da rubutu ba ko sunanta Bata iya rubutawa ba.

Sai lokacin Wanda aka Kira da Papa yayi magana yace Abita a hankali Dan Allah kaga bani na haifeta ba Yar Dan Uwa na ce marainiya ce Bata da Uwa da uba nine komai nata bana so ta kalle mu a

Please Login or Register in order to submit comment