Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba daya,Hannunta rike da spoon ta zubawa Nadeer Dake zaune kamar gunki shi mamakin rashin Imanin Kamla yake yi,Itama Iman ta zubawa Kanta,ba Wanda yayi tunanin Iman ta warke sabo da dama tana zubawa Nadeer Abinci yanda shima yake zuba Mata ta koya.

Abincin yaci a Bakinsa wani mugun Dadi yaji a ransa yace Amma dama kamla ta iya girki Haka Bata Yi,sai Santi yakeyi a ransa yaci ya koshi,Iman tana ta faman satar kallonsa,har ya Gama ci ya mike tare da kwasar wayoyinsa ya wuce Hospital abinsa.

Yana fita Kamla ta tabbatar ya fita sai ko ta mike ta damki Kwalar Iman ta shiga dura Mata Ashar kala kala,Iman ta tsaya dagalolo Haka tana ji tana gani Kamla ta dungure Mata Kai ta tallafe Mata keya tare da zunduma Mata zagi,Bata iya yin komai ba har Kamla ta Gama ta koma room dinta,Tana tafiya Iman ta girgiza Kai ta hada kwanikan ta wanke komai ta maida shi inda ya Dace ta gyara Dining sai ta wuce Bedroom din Nadeer ya danyi Dirty ba a gyara Masa sai masu aiki su Kuma basa yin yanda ya kamata, Zagewa Iman tayi sai da ta dawo da dakin Nan sabo duk da cewar Nadeer Yana gyara abinsa Amma na yau na musamman ne,Kayansa ma Daya cire a washing machine ta wanke Suka bushe ta goge Masa su,kamshin da dakin yakeyi na daban ne,Haka toilet dinsa ma,Dakinta shima ta gyara sannan ta shiga room din Kamla,Lokacin Kamla tayi wanka ta fita makwafta gidan sabuwar Kawarta Matar Wani Ambassador, can take Kara koyo wasu halayen na banza,Haka Dakin Kamla ma Yasha uban gyara kamshi kawai yakeyi,gaba Daya gidan sai da Iman tayi gyara na musamman Allah yasa Yan aiki Basu ga Iman ba suna can part dinsu.

Girkin Rana Iman ta Dora ta shirya lafiyayyar Friedrice da soyayyar kaza,sai couslow tare da fruits salad ta hada ya dau sanyi, Har 5pm Kamla Bata dawo daga yawonta ba,Kuma Nadeer Bai sani ba ta fita, tafi karfin ta tambaye shi cewar ta,bashi da matsayin Daya Isa ta tambaye shi Unguwa cewar Kamla.

Dai dai lokacin da zai dawo gida sai ga Kamla ta Riga shi dawowa har tayi wanka ta shirya ta wuce Dining,Tunaninta 'Yan aiki Nadeer yasa suke dafa abinci yanzu,da Kuma yace Babu Yar aikin da zata dafa mata Abinci idan baza tayi ba ta zauna da yunwa,a fili ta furta munafuki ta Kai Loma Daya bakinta taji Dadin gaske Bata taba cin Abinci me Dadi Haka ba sai jiya da yau.

Nadeer ne yayi Sallama ya shigo ko amsawa Kamla Bata Yi ba Wai gaba takeyi da Nadeer, Mamaki ya Kama Nadeer ganin gidan gaba Daya ya canja sai kamshi da kyaIli,Iman ce ta fito da gudu ita a Dole marar hankali,Murmushi ya sakar mata,Ba tare da tayi magana ba ta karbi ledar hannunsa ta Bude Ice cream ne da abubuwan ciye ciye,Da sauri ta Bude Icecream Daya ta Fara Sha abinta sannan da yatsa ta nuna Masa Abinci a Dining,yace na koshi,Kuka ta saki Wai sai yaci Dole,Yasan tana daukan Zafi zata sume kawai sai ya hakura ya zauna a Dining,Kamla tsaki taja ta mike tare da Haurawa sama tana zage zage Babu Wanda ya kulata,Iman kuwa abincin ta zuba masa,yace waye ya dafa? Still Kamla ta nuna da yatsa wacce ke Haurawa sama.

Uhm kawai Nadeer ya furta ya shiga cin abincinsa,Yana Mamakin Wai Kamla ce ta gyara gida Haka ta Kuma Yi girki me Dadi haka.
Kamla kuwa tana shiga dakinta tunani ta Fara me zata yiwa Iman yanda zata raba Iman da gidan Baki daya, can wata dabara ta Fado Mata,Nan take ta dauki wayarta ta duba Messages Nan ta kamo Messages na NCDC hukumar yaki da cutar Corona virus, kiransu tayi a waya,Allah ya Bata sa'a Bugu Daya Suka dauka.

Kamla tace Dan Allah kuzo Yar uwata ce ta kamu da cutar sarkewar numfashi Muna tunanin Corona virus ce ta kamata kuzo ku tafi da ita a killace ta Dan Allah,Ncdc suka ce taje kasar waje ne ta dawo a satin Nan? Kamla tace yau kwananta uku da dawowa daga kasar China, Kuma Saida ta tsaya tayi kwana uku a kasar Italy sannan tazo Nigeria,Bamu Address din gidanku yanzu cewar NCDC,Nan take Kamla ta bada Address Din gidan Nadeer.











AsmaBaffa.
[11/4, 11:17 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ


FREE PAGE








26-30






Official






By
AsmaBaffa.



ADDU'AR KAWA SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨






RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku 300 ne


ADDU'AR KAWA
Dari biyu 200 ne ga me son shiga group dinsa.

Masu Bukatar siye ta Bank ga Accnt number

0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gtbank.

Masu tura katin MTN ta WhatsApp, Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
08033933642.

''YAN NIGER ku nemi wannan Number
+227 90 79 59 39.






Page naku ne

Zeemah
Ummu Aiman
Farida Yusuf Bashir
Precious Nauwar
Bilkisurabiuado5.










Misalin karfe Hudu na yamma Lokacin Iman tana ta faman kallon cartoon din Dole Nadeer Yana ta aiki a system dinsa,Me gadi ya shigo a gigice yace Ranka ya Dade Ga masu aikin Corona can a kofar gida sunzo ai Ni a tunanina an hakura Babu Corona yanzu to gasu can zasu shigo wai dole sai an Bude musu gate,Karaf Kamla ta fito tare da furta ce musu su shugo Mana,Da sauri me gadi ya juya Nadeer ya daka Masa tsawa karka sake su shugo min gida na fada maka, Iman kamar tayi magana Amma babu halin hakan,Ita kuwa Kamla ji take Kamar ta kashe Nadeer sabo da bacin Ran Dake damunta, a gaskiya Abinda kake min ya ishe Ni wallahi sai na fadawa babanka komai zanyi sai ka hanani sai Idan Iman ce tace shine tayi dai dai.

Baki Nadeer ya tabe tare da Furta Ni Baki ga Abinda kike min Ina kyale ki ba sai ke? Kyaleki kawai nake yi Amma har zagina kike Yi idan kin Isa ki Bari Ncdc su shugo gidan Nan kiga yanda zanyi kasa kasa Dake wallahi ko bana gida Ncdc suka shugo min gida sai Kinga abinda Zan Miki, Kina Abu Kamar Tinkiya wacce Bata San me takeyi ba,Iman kawarki Kuma kin San halin data tsinci kanta ko tausaya mata ai kyayi,Hawaye ne ya kwacewa Iman Ba tare data shirya ba, Da sauri ta share Hawayenta Dan Kar Nadeer ya gano ta Amma ya rigada ya gani,Kallonta yayi a nutse Sai ko yaga ta daga Kai sama tana share kwalla, da mamaki ya kalleta tare da Furta Mene ne 'yar zaman daki? Baki ta washe tare da yin karya tace Allah sarkiiiiiiyiiiiiiii Wannan cartoon din na tuna me abin tausayi Maman sa ta Duke shi, Murmushi Nadeer yayi,Iman tace Yaya Nadeer Ka kaini yawo gidan Tom and Jerry na kwashi gaisuwa,so nake na gaishe su sai naji Dadi na,Dariya Nadeer yayi yace Tom and jerry Ni ban San gidansu ba gaskiya,Ni ban yarda ba Sai ka kaini Allah ta furta tana shagwaba,Alright Amma sai Idan Kinga mutane baza kiyi kuka ba,sannan karki ji tsoron mutane duk inda Muka je zakiyi shuru,Iman tace to na yarda bazan ji tsoro ba,Nadeer Bai San Iman ta warke bane,Kamla ya kalla da take faman cin chewgum tana das das,sabo da Kar a zargeshi baya kula Matarsa yace Ki shirya 5pm zamuje gidanmu ku gaisa dasu Mama,Allah ya kiyaye bazan je ba Kuma gaisuwar bazan gaida su ba, Baki Nadeer ya tabe tare da furta dama su Suka Nemo aurenki Ina ruwana Ni dai Kika sake Kika zageni yau Dukan tsiya Zaki ci,Ka kashe Ni ma karka barni da Rai Bazan je gidan naku ba gidan Iyayena zanje,A dawo lafiya cewar Nadeer.

Yau Iman Bata iya dafa musu Abinci ba kasancewar Nadeer Yana gida zai iya gano ta,Bai damu ba tunaninsa yau Kamla Bata Yi niyyar dafa abincin ba kawai Yaronsa ya aika yayi musu Take away na sharwama da sauran abin ci Dana Sha Kuma har Kamla yasa aka siyo Mata itama,Masu aiki kuwa dama sune suke dafa abinda suke so a part dinsu.
5pm ya kalli Iman wacce ke wasan Dole a Palo yace je ki shirya mu wuce,Da Gudu ta fada room dinta taci wanka sosai, lotion ta shafa sannan ta zabo doguwar Rigar wani lace me tsadar gaske dark green and milk, gashin ta gyara sosai sannan ta shafa Powder sama sama sabo da Kar Nadeer ya gane ta warke,Dankwalin lace din da mayafi milk color ta rike a hannunta a Dole Bata warke ba Fitowa tayi ta Iske Nadeer Yana jiranta a Palo yaci Uwar wanka cikin Wata Shadda milk color ba karamin Haduwa yayi ba,Kamar a jikinsa aka dinka kayan,sumar Nan Tasha kyau sai sheki takeyi Yana kamshi,Ba karamin kyau Yaga Iman tayi Masa ba sai da zuciyarsa ta buga,Murmushi yayi Yace kinyi kyau sauri ki yafa mayafin mu wuce,Ni bana so cewar Iman,Mayafin ya fisge tare da yafa Mata,zata cire yace kina cire mayafin Nan na fasa zuwa Dake,Kukan karya ta saki Hannunta ya rike tare suka fice,Kamla tana daki ta tuna Iman fa ta kware wajen Snatching gwara ma ta bisu ayi komai a gabanta,Mayafinta ta sura a saman bed tasa takalmi tabi bayansu da gudu Kamar mahaukaciya,Kafin Nadeer ya shiga mota ta bangaje Iman ta shige gidan gaba ita a Dole me miji,Nadeer Bai kulata ba ya budewa Iman bayan mota ta Shiga shi yayi Driving nasu zuwa gidansu.

Yana parking a harabar gidan Iyayensa Direct Part din su Iman yace su Wuce,Kamla tace ai ba uwata bace bazan Shiga ba ehe,Da Sauri Iman ta kalli Kamla sabo da lafazin Daya fito daga bakin Kamla,Ae nace ai ba uwata bace Uwarki ce ko? Ko uwata ce ? Kamla ta tambayi Iman,Nadeer yace ai Umman Iman baza ta taba Haifar 'ya marar tarbiyya irinki ba, Ai idan ta Haifo 'ya irinki to na tabbata gidan raino zata kaiki sabo da ke shedaniya ce Babu Wanda zai so ya Haifo 'ya irinki, Kuka Kamla ta saki Wai ya zagi iyayenta sai ta juya ta wuce part din Maman Nadeer da gudu tana kuka.
Tsaki Nadeer yaja Suka wuce bangaren Umman Iman, a Palo Suka Iske Umma da Baban Iman tare da Raees suna Hira,Cike da mamaki Suka amsa sallama ganin Iman Bata gudu ba Kuma Bata nuna alamar tana tsoronsu ba,Cike da farin ciki a zuciyar Iman take Kallon iyayen nata da Dan Uwanta Raees Kamar tayi musu magana Amma Kash yanzu Babu damar yin hakan.
Umma cike da murna tace Nadeer yau kune harda Yar gidan naka? Murmushi yayi tare da furta Ae Umma,Baba Yana Jin Dadi yace gashi bata gudu ba yau gaskiya an samu ci gaba,Ai na fada Mata idan ta gudu bazan kaita gidan Tom and Jerry ba shi yasa ta tsaya, Ni nasan da Dalili cewar Raees Yana Murmushi ya furta.

Iman Bayan Nadeer ta koma tare da buya bayan ta Gama kallon Iyayen nata taji Dadi ganin suna lafiya,Zama Nadeer yayi saman Kujera itama Iman ga kugunta ga nasa ta zauna tana Dan nuna tsoro kadan,Da Nadeer kadai Suka gaisa Iman ko kulasu Bata Yi ba sai kalle kalle da take Yi,Kayan Sha aka kawowa su Iman,Umma tace Nadeer asha lemo Mana,Iman ce ta dauka tare da bude kwalin exotic ta tsiyaya tare da mikawa Nadeer Umma da Baba suna kallo Lallai Iman ta samu sauki cewar Raees, Nadeer ya kalleta yace kema Kisha,Baki ta tabe tace Dodo ne a ciki,Babu Wanda ya matsa Mata Haka sukayi ta Hira da Nadeer tana jinsu Iman Bata ce komai ba sai da Suka Dade tana ta Jin Dadi taga Iyayenta sannan tace da Nadeer Gida tana Jan rigarsa wai su tafi gida ta gaji.
Kuje wajen Maman taka karta gaji ta hanaka Zama Kuma,To Nadeer ya furta tare da Mikewa tsaye ya musu sallama Iman hannu tasa tare da rike rigarsa Kamar jela suka bar part din zuwa na Mama, a Nan Suka Iske Kamla ta Gama shirya Karya Allah yasa Abba Baya Gari Yana kasar Qatar,Ko Zama Nadeer baiyi ba Mama ta balbaleshi da fada akan me zai zagi iyayen Kamla,Nadeer ya zauna tare da fayyacewa Mama abinda Kamla tayi,Mama kanta sai taji Kamla ta Bata haushi tace to indai Haka ne Kamla Baki kyauta ba,wannan ai shashanci ne, Nasiha tayi musu sosai Amma Kamla sai tabe Baki takeyi tana cewa Allahu Akbar da wulakanci, duk abinda Mama tace sai aji Kamla tace Allahu Akbar....Duk shareta sukeyi suna daga Mata kafa,Na karshe Mama tace Ai a satin Nan ma Abban naku zai dawo Allah yasa dai Kuna Zama lafiya ko? Allahu Akbar....Kamla ta furta da karfi tana Tauna chewgum, Baki Bude Mama ta kalleta tana kallon rashin kunya zalla a wajen Kamla,Nadeer zaiyi magana ya Gama harzuka, Mama tace kyaleta Nadeer karka Soma, Budar bakin Kamla sai tace Yo Ni a fada Mana zuciya, tunda ya aureni me ya taba yi min,Bai taba kwanciya Dani ba bare ya bani hakki na,Danku bashi da Lafiya ku nema Masa magani,idan Kuma kunce kalau yake to very soon zaku ga Iman da cikinsa domin ita yake aure ba Ni ba,Baku da hurumin fada min naji, Kamla tana Gama fadin Haka ta mike ta fice Fuuuu ta bar gidan Baki daya,taxi ta shiga tare da komawa gidan Nadeer.

Nadeer dai shi Mama ya kalla yace Kun gani da idonku,Kunga abinda nake fada muku to abinda takeyi yafi Haka,kawai Dan Baku sani bane Amma da ace tare muke daku yanda kuka Aurota ku zaku koreta da kanku,shi yasa ban Mata komai ba sai Kun gani Kuma yanzu Ni wlh ba abinda zanyi Mata ko fada bazan Yi Mata ba sabo da tun farko na fada muku gaskiya,Amma Nan gaba gaskiya zata Yi Halinta ai.
Shuru Mama tayi tasan sune da laifi.

Mikewa Nadeer yayi ya rike Hannun Iman tare da yiwa Mama sallama Suka wuce gida abinsu,Ko da Suka koma gida Yana kallon Kamla Bai ce Mata kala ba,Iman kuwa ji tayi Kamla ta fita a kanta sakamakon iyayenta data wulakanta abin baiwa Iman Dadi ba Amma a Haka zata Yi kokari taga Nadeer ya so Kamla sun zauna lafiya duk da cewar tana son Nadeer ita ta hakura ta barwa kawar ta.

Haka Iman ta dage take gyara gida,tayi girki masu Dadi,Abubuwan data Sa Nadeer na so su takeyi Masa a boye sai tace Kamla ce tayi ba ita bace,Hakan Bai Sa Nadeer yaji Yana son Kamla ko digo ba duba ga yanda Kamla Ke Masa rashin kunya kullum har Iyayensa,mamakin Nadeer shine Yanda Iman ta daina Shiga dakinsa idan Yana ciki,Bata Zama kusa dashi Kamar yanda takeyi a baya da take hali na hauka,Duk ta canja Masa ba irin da ba ko yaushe tana jikinsa ta rungumeshi ba ruwanta,Amma yanzu ko da Wasa Bata Yi sai ma kunyarsa da take ji tana biye kanta idan ta ganshi,sannan Kamla tana zuwa inda yake Iman zata mike ta shige Bedroom bazai sake ganinta ba,Wannan shike ciwa Nadeer tuwo a kwarya,Ko banza Iman tana debe Masa kewa Yana Jin nishadi a ransa,tana bashi farin ciki, Hira da ita abin a so ne Haka ganinta Yana jefa shi nishadi,Itama bangaren Iman Haka abin yake bala'in kaunar Nadeer takeyi fiye da komai Amma Kamla ta Riga ta aurarsa ita Kam Bata da sa'ar auren me kyau Kuma Wanda take so,duk sanda zata so wani to Kawarta ta rigata,sai yanzu ta Gane Bata taba son kowa ba sai Nadeer a kansa tasan so gashi Kuma yayi aure Kuma Kawarta Babu amfanin zamanta a gidan Nadeer Dole ta hakura sabo da so take Nadeer yaso Kamla su zauna lafiya ko ba komai zata goge laifinta ta huta da Jin Haushinta da Kamla keyi.

Wannan dalili yasa Iman taci gaba da Zama a gidan Nadeer tana yiwa Kamla Bautar girki da Gyaran gida tare da kyautatawa Nadeer a matsayin Kamla ce ke Yi,Sai da Iman ta kwashe Watanni kusan hudu tana Bautar aiki, Wanda a sace takeyi Bata Bari Nadeer ko Kamla ta kamata tana aikin,Tasha wahala sosai,gashi ta kuntata kanta tana Pretending a matsayin mahaukaciya,ta Hana kanta ganin Iyayenta,Sallah ma a boye takeyi duk sabo da Kamla Amma Kamla Bata gani, hasali ma kullum sai ta zagi Iman ko ta shirya Mata mugunta iriri.

Nadeer kuwa Kiba ma yayi da kyau,Sannan Bai taba Jin son Kamla ba,duk da cewar Iman tana cewa Kamla ce tayi girkin Amma a zuciyarsa Bai yarda ba Kuma Bai Jin son Kamla Haka Allah yayi sabo da so Allah ne ke sawa mutum,Ita kuwa Iman kullum so da Kaunar Nadeer karuwa yake a ranta.
Yau Saturday Iman,Nadeer da Kamla suna palo,Kamla tana doguwar kujerar da Nadeer yake,Iman Mikewa tayi tazo gaban Nadeer ta zauna,Hannunsa ta kamo ta kamo Hannun Kamla ta hada wuri Daya tare da Furta Yaya Me yasa bakwa kwana tare Kuma kace min matarka ce ko? Kamla hannunta ta fisge da karfi tare da furta Uwarki ce Matarsa munafuka,indai har kece Zaki sa ya Soni bana so,Kuma wallahi matukar sabo dake zai kwana Dani bana so gwara ya sake Ni, Baki Nadeer ya tabe Bai kulasu ba, Iman kuwa Mikewa tayi ta wuce Bedroom dinta,tana shiga ta fada saman Bed dinta tare da fashewa da kuka Wiwi,Sai da ta gaji kafin bacci ya kwashe ta a Nan tayi bacci.

Haka Iman ta kasance kullum cikin aiki take a gidan idan suna bacci ko sun Fita, Yau Da Asuba tana kitchen tana ta aikin ta tana soye soye,Nadeer dama ya taba Kama ta wurin sau biyar Shuru yayi Bai nuna ya San ita ke yin aikin ba,yau ma ya Dade a kofar kitchen Yana ta kallonta tana aikinta Yana ta zuba Murmushi sannan ya wuce Gym abinsa ba tare da ta sani ba.

Da Dare ma Yana sani yake fita sai ta Gama girkinta sai ya dawo gida,Yau ma Haka yayi Yana dawowa ta jashi Dining tana cewa Yaya yawwa Zo kaga Aunty tayi maka Girki Abinci me Dadi,Zo kaci biye Mata yayi ya zauna yaci ya koshi Yana Santi yace Lallai naga Alama sai an budewa Kamla Restaurant a kasar waje,girkin Nan nata yafi karfin a Nigeria sai dai kasar waje,Iman sabo da farin ciki Nadeer ya Yaba abincinta ta manta Bata San sanda ta kyalkyale da dariya ba wacce ta tafi da Imanin Nadeer Baki daya ya lakace Yana kallonta kawai.
Tunawa tayi da sauri ta Sha kunu tace Ni kuka zanyi,kafin kiyi kukan Kirawo Aunty ayi Mata godiya yau Zan fara kwana a dakinta tunda tayi min wannan girkin me shegen Dadi,Wani kishi ne ya turnuke zuciyar Iman, hankalinta ya tashi sosai,Tsoro ya shige ta Nadeer ya Fara son Kamla kenan ita shike Nan,dabara ce ta Fado Mata tace ai ko ka kirata baza tazo ba,Kuma baza ta yarda da Kai ba bare ku kwana tare kawai a kyaleta,Dariya ce ta Kama Nadeer sabo da Iman ta Kama kanta ta nuna ta warke tunda har ta iya tunani, a fili yace ba komai Kirawo ta Haka Zan lallashi Abata zata yarda yau Hakkinta Zan Bata yau Zan angwance,Iman a ranta tace wayyo Allah na shiga uku a fili Kuma tace Yaya yau fa Saturday wannan ranar Bata sa'a bace a musulunci ka bari sai ranar Friday sai ka angwance itace Rana me daraja,Au a Ina Kika san Sunan juma'a? a wajen Tom and Jerry fa naji, uhm to tunda baza kije ba Bari zanje da kaina, da sauri Iman ta mike,Kamar kwai ya fashe Mata a ciki, Wai Dan Kar taje da wuri idan tayi tafiya Daya biyu sai ta tsaya ta huta sannan taci gaba da tafiya a Haka har taje dakin Kamla,tana shiga tace Kamla kizo Inji Yaya,Tsawa Kamla ta buga Mata ke Mahaukaciyar banza bace min da gani,da sauri Iman ta bar dakin Kamla ta fito tana kuka.

Lafiya? Nadeer ya tambayeta,tace na bar Mata dakinta shine tayi tsawa....munafuka gani na fito cewar Kamla tazo gaban Nadeer, Malam gani Kamla ta furta tare da tsayawa kerere a gabansa,jeki na fasa cewar Nadeer,tsaki taja tayi Tafiyarta inda ta fito,Iman kuwa dariya tayiwa Nadeer ta gudu itama room dinta.

Iman da Karfin Hali Bata daina aiki a matsayin Kamla ce keyi ba,kullum Haka takeyi Wanda Nadeer ya Gama Gane Iman ta warke ita ke Masa komai,Bayan sati Biyu Kamla ta gaji taga Iman baza ta bar gidan ba kawai sai ta tafi gida ta tambayi Nadeer a matsayin Kawai iyayenta zata gaisar Amma a zahiri gida ta tafi dakko Darasi wajen Mamanta.
Da kuka ta Shiga gida tana bawa Mamanta labari,Mamanta tace Zan fada Miki Mafita ta karshe da Zaki Yi kawai ki samu guba ki sawa Iman taci ta mutu uban kowa ya huta da jaraba,Mama idan aka Kai Gawar asibiti aka gwada fa? Ai ni za ace,Haka ne kinyi gaskiya Kamla, Amma ki shammace ta idan tana bacci kisa pillow ki danne Mata fuska har ta daina numfashi sannan ki tafi kinga ba Wanda zai Gane za ace kawai ta kwanta bacci lafiya lafiya aka ga gawarta kawai da safe,za ayi tunanin cutarta ce ta kasheta ko ya? Dariya Kamla tayi tace Alhmdllh, Kinga sai na sake daga Ni sai Mijina Dole ma ya hakura ya so ni.
Sun Dade suna Hira sai dare Kamla ta dawo.

Sai da Kamla ta Bari dare ya tsala wurin 2:30am ta tura kofar Iman a hankali,sai ta hango Iman saman Sallaya tana ta Nafeela cikin dare,Tsaki taja a hankali ta lallaba tare da komawa dakinta.
Ranar Monday karfe biyu na Rana Nadeer Bai je ko Ina ba Yana gida,Iman tana so tayi Masa girki Babu dama tana tsoro Kar ya kamata sai taga ma yasa an kawo Abinci iri iri Suka ci Suka koshi sannan tayi sallah a boye ta kwanta zata Yi baccin Rana.

Kamla tasan Iman Tana yin baccin Rana karfe biyu take kwanciya hudu ta tashi,Sai ko Kamla ta zauna tana jira taga karfe Uku tayi tasan lokacin baccinta yayi nisa yanda baza ta farka ba,3pm tanayi Kamla ta lallaba a hankali ta Bude dakin Iman ta Shiga,tun sanda Kofar tayi Kara Iman ta farka sai tayi lambo tana kallon Kamla a hankali tazo ta dauki Pillow Daya ta danne fuskar Iman da karfi,Iman tana sani tayi Shure Shure ta saki jiki kamar gawa,Lokacin Kamla ta dauke Pillow tana murna ta ajiye pillow a gefe tana dariya tace shegiya na tsaneki Iman tun farkon ganina Dake,Tarrrrr Iman ta Bude Idanunta a cikin na Kamla,tsoro ya shigi Kamla,Iman tayi Murmushi tace Kamla kenan nasan Baki San Iman ta warke ba,tunaninki Ni mahaukaciya ce har yanzu,To Bari kiji duk abinda kikeyi Ina sane,yau watana Kusan hudu da warkewa,kece sanadin Haukacewa ta kece sanadin samun lafiyata na warke Ras,Kece Kika Yi silar da nayi Hatsari kece Kuma Kika kwada min sanda a kaina na warke na dawo normal.

Watana uku kenan da warkewa watana uku Ina Bauta Miki sabo da nasa Nadeer ya soki ku zauna tare har abada,Kamla wulakanci,da Rashin mutunci Bai Sa mutum ya soka sai kyautatawa,da ace kina yin abinda ya Dace da tuni Nadeer ya fada sonki,Allah ya gani yaga zuciyata nasan a farko nayi muku laifi yes na Karbi laifina na tuba, a lokacin kuruciya na ibana ban San so ba ma,Ina tabbatar Miki ba son Ibaad nakeyi ba,ban taba son kowa ba a duniya sai Nadeer,Amma na Hakura na sallama sabo da abinda nayi Miki nake kokarin goge laifi na Kamla,Amma bakya gani,ki sani Duk aikin da nakeyi da girki Nadeer nake fadawa cewar kece

Please Login or Register in order to submit comment