Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fara bushewa ma,suna Isa Bedroom dinta ya zabo Mata wata English gown Yar siririya marar nauyi yace gashi shiga Toilet kiyi fitsari ki canja Kaya ki fito maza, murya a shake tace Ah...Ah...tsawa ya buga Mata ba shiri ta shige ta canja Kaya ta fito, Abinci ya tura Mata dama yunwa take ji ta ci ba laifi sai Kuma tea na kayan kamshi Wanda me aiki Amintu yasa ta dafa ta Bawa Iman ta shanye sannan ya Sa Mata Drip.

Iman sai kallon Ruwan takeyi tana mamaki wannan Mene ne? Abinci yaci shima sannan yayi wanka ya saka Kaya Marasa nauyi ya fito Yana kamshi,Dakin Iman ya shiga ya Iske ruwan saura kadan ya Kare,Idon Iman a bude tana ta faman Atishawa,Yana karewa ya zare mata, Bata Dade ba bacci ya kwashe ta.

Ko da Nadeer ya fita masu Aiki su Amintu da Raliya ya Kira su,Da sauri Suka tsuguna a gabansa Dattijai ne,Nadeer yace ko Kun San me ya faru da Iman? Aminatu tayi niyyar fadar gaskiya domin a gabanta komai ya faru Amma tana tsoro Kar ace ta hada miji da Mata fada sai tace bamu sani ba Alhaji yanda ka ganta Haka Muka ganta,Okay ya furta kawai Suka tashi zuwa part dinsu.

Kamla ce ta fito taci uban kana Nan Kaya tana zuba kamshi,kusa da Nadeer ta zauna bai ko kalle ta ba sannan Bai ce Mata komai ba,Gajiya tayi da Zaman tace Ashe Iman ce Bata da Lafiya? Ai ban sani ba me ya faru da ita? Ban sani ba me yasa Baki Zo kin gani da idonki ba tun farko,wani haushi ya Kama Kamla tace Kai Malam karka fada min magana ai bani na kawota gidan ba wallahi ko mutuwa Iman tayi ba abinda ya dameni ko gaisuwa sai naga damar zuwa,Kuma tunda baza ka bani hakkina ba wallahi Allah ya isa bazan yafe ba,macuci azzalumi,a Haka Namiji har namiji Ashe baka iya komai ba,ga mutane can Sunyi aure suna ta Uban Balbala soyayya Ni kuwa ko rigata baka taba rikewa ba wallahi sai na fadawa Tsohuwarka na daina daga maka kafa,Akan wata banza Ni ba mace bace Albarkatu ne Dani iri iri Kamar me,To wlh sai na tona maka asiri,Ya Allah kasa Ko Abbanka ko Mama a cikinsu Daya ya Tsine maka,Nadeer Yana jinta Bai ko ce Mata kala ba har ta Gama ta mike tsaye tare da furta idan kaji haushi ka harbo min saki Uku yau karewar Bakinciki tana tafiya ta ja tsaki tayi Tafiyarta.

Mamakin rashin tarbiyyar Kamla ya Gama kashe Nadeer Wanda har ya kasa motsi,Bai taba zaton Kamla rashin tarbiyyarta ya Kai Haka ba,kamarsa me kwarjini,kyau,kudi,cikar sura da Haiba Amma yarinya karama tayi Masa irin wannan,Bai taba Jin Kamla tayi Addua me kyau ba,Bata yiwa mutum fata na Gari,sai Adduar nemawa mutum bala'i ta iya,Ana so mutum ya dinga Addua me kyau a ko yaushe,ko wani zaiwa yayi me kyau sakamakon ko yaushe Allah na iya karbar Addua idan mutum yayi Addua sai a Dace a lokacin Allah ya karbi adduar Nan take a zartar, tabewar Kamla tayi yawa.

Kamla tana Shiga Bedroom tace yanzu duk jikin Nan me kyau na Nadeer haramiyata bazan ko Dan rungumeshi,wata zuciyar tace Kika sake ma Kishiya zai Miki ya auro wacce yake so su dinga soyewa,Kamla ta girgiza Kai tare da furta gwara na dinga Addu'a Kar Allah yasa yaga wata ya so ta,wata zuciyar ta Kamla tace ai kudi shike sawa a Karawa mace kishiya idan talaka ne kuwa Yana fama Dana Abinci ma Ina yaga ta Yi Miki kishiya ai kawai kiyi fata ya Zama talaka ya Talauce kuyi zamanku tare a dinga taimaka muku,ko Iyayenki sa dinga Baku Abinci.

Wata zuciyar ta Kamla tace to ai Ubansa Yana da azabar kudi Taya zai Talauce? tace af akwai abinda yafi karfin Allah sanda yaga dama dare Daya zai iya maida su talakawa gaba Daya,Ni Kuma tunda Nayi karatu na sai na Samu Aiki na koma nice Hajiya Ina juya Nadeer yanda Naga dama sai abinda nace sabo da Ni nake ciyar dashi, rawa Kamla tayi a jikin mudubi tace yeeee na Zama Hajiya.

Tun daga wannan Rana Kamla ta Fara wannan Addua,Allah yasa Nadeer ya Zama talaka ita Kuma ta Zama me kudi, gashi tana ganawa Iman azaba kullum Idan Nadeer ya fita sai ta samu muguntar da zata yiwa Iman gwanin ban tausayi.

Nadeer ya Fara fahimtar akwai abinda Kamla Ke yiwa Iman,Yau Sunday Yana gida ya Kira Kamla ta fito Palo sanye cikin Shadda maroon Tasha dinki na manyan hajiyoyi ba karya ta iya gayu,Iman tana kusa da Nadeer.
Zama tayi tana wani Bata fuska,Kallonta Nadeer yayi yace Kamla me kike so daga wajena a matsayinki na matata? Kamla tunaninta Nadeer ya fada sonta sai a ranta tace sai naja Masa aji shege yaga mace Hadaddiya Zama ka dawo Hanya indai Kamla ce sai kayi kuka a kaina,Cike da yanga ta kalleshi tace ba komai,Yace ki Fadi gaskiya Ina zargin kina cutar min da Kanwata idan bana gida,sabo da Haka mu ajiye magana Zan biya Miki dukkan bukatunki da kike so ke Kuma Dan Allah na roke ki Dan Allah ki daina taba min Iman,Amana ce a wurina,Tsaki Kamla taja tace au dama sabo da ita ka yarda zaka biya min bukata ta ko? Badan kana so na ba? Direct Nadeer yace bazan Miki karya ba Kamla kiyi hakuri bazan iya sonki ba Amma Zan Hakura na Baki hakkinki ko badan Iman ba sabo da Allah Kar Allah ya kamani da hakkinki Zan biya Miki bukatunki wallahi harga Allah sabo da Umarnin Allah ne Dole Zan Baki hakkinki,Fuuuu Kamla ta mike tsaye tana Huci tace Oh wato ka Gama da Iman ka gaji da dandanata ka Gama Jin Dadi da ita yanzu ka dawo wajena zaka dandana Ni ko? To bana so,bana son ragowar Iman,bazan taba yarda da Kai ba fasiki,wallahi kaji tsoron Allah ka tuba,Ni da kake ganina akan na yarda dakai gwara naje na Samu Mahaukaci a cikin bola na bashi kaina,yanzu Ni ba ruwana da jikinka,tana Gama fadin Haka ta mike tayi ciki ta bar Nadeer da Iman,tana Shiga room dinta Kamla ta daka tsalle ta fada saman bed tana ihu tana murna tace Ya mato,wallahi ya fada so na,Ai Haka Zan ta wulakantashi har sai yayi kuka a kaina sannan Zan yarda da shi,Wayarta ta jawo ta Kira Mamanta ta fada Mata itama mama ta yarda,Kamla harda cewa Mama ke Kinga yanda yake rokata ya kusa kuka fa,Dariyar Jin Dadi Maman Kamla tayi tace to yanzu ki lallaba ya barki kije gidansu ki fadawa Uwarsa baya kulaki ki hada gurmi yanda zai rasa Jin Dadi a duniya,Dariya Kamla tayi tace to Mama an Gama,Maman Kamla tace ahaf ai yanzu a duniyar Nan duk Wanda ya zauna lafiya shi ya so,mu duk inda zaman lafiya yake bama Zama,nafi so kullum naga tashin hankali sabo da shine take na, da shi na Saba Kuma shi na iya,A shi nayi Degree da masters, mutum Bai Shiga gonar mu ba ma ya ya iya bare ya shiga,duk abinda yayi Mana sai mun rama, sai da Suka Gama wayarsu sannan Kamla ta canja shiga cikin wasu matsiyatan Kaya sharara dasu komai nata a waje Wai zata fita ta firgita Nadeer ta motsa shi sannan tana so ya sake haukacewa a kanta Kuma ta hanashi komai.

Palo ta fito ta Iske shi da Iman da Aminatu me aiki tana gyarawa Iman gashi,Iman sai kuka takeyi Wai Bata so ita shi Kuma ya kafa ya tsare sai anyi Mata,Ko kunyar me aiki Bata ji ba tazo ta zauna kusa da Nadeer, Iman ta hango Boobs din Kamla Sunyi Sujjada a Rigar sharara Ana kallon komai tayi zaton abin Wasa ne,Zumbur ta mike,Babu Wanda yasan me Iman zata yi.
Iman ta kalli Nadeer tare da furta laaaa Kawana kaga irin nawa,wallahi Ina da irinsa na nuna maka Nima ka gani? Shuru ba Wanda ya kula Iman kunya ta lullube Aminatu da Nadeer,Iman ta kalli Kamla ta kyalkyale da dariya tace Allah naki bashi da kyau,Remote Iman ta dauka tare da jifan Kamla dashi,a fusace Kamla ta mike tsaye tana durawa Imana zagi,Tsawa Nadeer ya daka Mata uban waye yace ki fito da shi kije ki tattara abinki cikin kaya na mutunci ya fiye miki,.
Kwafa Kamla taja tace Haka Naga damar Zama Kuma zan kamata ne wlh sai ta Gane kurenta.







AsmaBaffa.
[11/4, 11:16 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ




FREE PAGE










21-25






Official







By
AsmaBaffa







ADDUAR KAWA NOVEL
SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨






SANARWA..

NA CANJA ACCOUNT NUMBER.





RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne


'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

ADDU'AR KAWA
Ga me son shiga group dinsa dari biyu 200 ne.



Ga masu bukatar siya ta Bank ga Accnt number

Accnt number 0175487861
Asmau Garba Muhammad, Gtbank.

Masu tura katin MTN ta WhatsApp, transfer ko Vtu ga number da zaku tura
08033933642.

'YAN NIGER
KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39.







Page naku ne Yan Albarka

Zainab Garba Butalawa
Marcycool
Y lame
Basmam Glam
Maryam Hamza
Ummi Khadija
Ummin Saddeeq









Dariya Iman tayi kawai sabo da Bata Gane me Kamla Ke nufi da masifa ba, Aminatu tsaf ta gyara Iman ka rantse Bata da Lalura.

Iman ce ta Kalli Nadeer tace Ni dai zanyi kuka na,kuka nake son Yi Allah,Dariya Nadeer yayi tare da Furta Yi abinki kinji, fadar Haka ke da wuya Iman ta saki jiniyar kuka ranar yini tayi cir tana rera kuka kala kala wayayayaya...yiiiiiii...wayyooo...woooooo...Haka kawai,Shi kanshi Nadeer Bai kula ta ba bare su Kamla da Tausayi Bai ratsasu ba,washe Gari ma da safe tana Gama karyawa tace Ni dai Dariya ta zanyi, Nadeer yace Good for you,Kamla tana zaune tana kallonsu Iman ta zauna a kasa gaban Nadeer da yake saman kujera Yana kallonta ai ko ta Fara Dariya Hahahaha,yiiiiiiiiihahahahaha,Ahhhahahhahhh,Owwwhahaaha....Ehehehehw....uhuhuhuhu,Tana dariyar Nan Kamla Bata sanda ta fashe da Mahaukaciyar dariya ba ko tausayi babu,Shi kanshi Nadeer da kyar ya iya danne tasa sabo Da Iman dariyar ma style style takeyinta Kuma sai tayi kyau komai tayi me kyau ne.

Satin Kamla biyu da Aure Amma kullum muguntarta kara karfi takeyi,ko Nadeer Bata yiwa magana gaba takeyi dashi, Kamar ba matar aure ba Babu abinda takeyi sai chat, duk Inda taga dama fita yawo takeyi makwaftansu masu kudi gida gida take shiga idan Nadeer ya fita itama fita take Yi, yau Saturday Sallamar Sameer da Hussain Suka ji abokan Nadeer, Suna shigowa Iman ta mike a tsorace sabo da tsoron mutane take ji sai Idan ta Saba da mutum,Kusa da Nadeer ta koma tare da boye Fuskarta a gefen Damatsan Hannunsa,Dariya Su Sameer sukayi ganin yanda Iman ta tsorace,Kamla tuni Dama tana bedroom dinta daga Iman sai Nadeer a palon, Sameer ne ya mikawa Nadeer Hannu Suka tafa ai sai Iman ta mike da gudu tare da Haura sama.

Dai dai lokacin da Iman zata shiga Room dinta Kamla tana labe dauke da katon Sanda kamar zata daki Doki haka ta dage Iya karfinta ta kwadawa Iman a kanta Nan take Iman Ta Fadi kasa sumammiya,tunanin Kamla ta mutu Alhmdllh ta furta ta koma room dinta tare da boye sandar a kasan bed dinta tayi kwanciyarta tana ta murna ta huta da jaraba.

Sai da Su Sameer suka Gama kwasar hirar su tare da Nadeer,da kansa ya kawo musu kayan motsa Baki,sun Dade sannan Suka tafi abinsu,Nadeer saman ya hauro ya Iske Iman kwance kanta sai jini yake fitarwa,a gigice ya Karasa Inda take Bai ko tsaya Bata lokaci ba ya dauke ta zuwa Hospital dinsa,Nan suka bawa Iman agajin gaggawa har Allah yasa ta farfado Sai bacci take kwasa,Su Mama Basu San me ake ciki ba sabo da Bai sanar musu ba Dan Kar Hankalinsu ya tashi.
Sai Da yayi Sallar Isha ya dawo kusa da Iman wacce ke bacci ya zauna a gefen Bed din da take kwance tare da rike Hannunta Yana kallonta ba ko Kyafta Ido Yana Tausayawa Iman Kuma ya tabbata Kamla ce tayi Mata Haka,Yana cikin tunaninsa Iman ta farka a hankali sai taga Nadeer a kusa da Ita ta Gane shi sosai,Kanta taji Yana Mata ciwo Nan take tun daga Hatsarin data yi ya Fado Mata,sai ta Fara tunanin abinda ya faru a baya har Wanda take a halin rashin hankali,Wani So da Kaunar Nadeer ne ya sake shigarta irin abubuwan da ya dinga Yi Mata yasha wahala da ita,godiya tayi ga Allah data warke.
Iman ta warke, Nadeer sai gani yayi tana Hawaye.

Bata Bari Nadeer ya gane ta warke ba,Abinda ya Bata mamaki yanda Kamla ta dinga Neman ranta,Amma Bata ga laifin Kamla ba itace take da laifi ita ta kwace Mata saurayi taci Amanarta,Amma ai ta tuba ta Kuma Bata hakuri ,Nadeer ganin tana kuka yayi zaton halinta ne na ciwon hauka sabo da ta Saba kuka ko dariya.

Ganin kukan nata na daban ne da gaske takeyi sai Kuma yaji Tausayinta, ko alamar ta warke Bata nunawa Nadeer ba,Allurar bacci yayi Mata kawai ta koma bacci, wayarsa ce tayi Kara ya duba sai yaga bakuwar number, dagawa yayi tare da furta Hello who is on the line? Muryar Kamla yaji tace Hello ya jikin Iman din ko ta mutu? Wani bakin ciki Nadeer yaji ya tsani Kamla Bata da halin kirki,tsaki yaja tare da kashe wayarsa.

A hospital Suka kwana Iman taji sauki sosai Bai San Iman ta warke ba sabo da baiga ko Alama ba,Sai 11am ta farka jikinta da sauki sosai,Ganin Babu kowa a room din sai ta mike ta shige Toilet komai na bukata Nadeer ya kawo Mata sabo,Brush tayi sosai tayi wanka tare da daura Alwala tayi Sallah tare da kwarara Azkhar sannan ta shirya sosai tana farin ciki ta warke sai Allah take wa godiya,Wata sabuwar Arabian Gown Peach color tasa ba ko digon kwalliya a Fuskarta ta koma saman bed ta kwanta abinta,tana kwanciya Nadeer ya shigo room din,baiyi tunanin komai ba sabo da yasan tana wanka da Sa Kaya ba sabon Abu bane,Ita kuwa Iman kunyar Nadeer ce ta lullube ta Kamar yanda ta Saba tun tana da Lafiya wani kwarjini yake Mata,ga tsoronsa da take fama dashi,duk sanda Taji ko kamshinsa ne sai Zuciyarta ta buga,yanzu ma ganinsa yasa Iman Ta daura Hannunta a saman kirjinta tana danne Zuciyarta sabo da yanda take bugawa da matukar karfi.

Ta manta cewar ta barwa Zuciyarta cewa baza ta nuna ta warke ba Amma Kash sai ta manta tace Ya Nadeer Ina kwana tana boye Fuskarta a jikin pillow,A firgice ya kalleta da sauri tare da Furta Iman kin warke? Da sauri ta tuna sai tace Mene Kuma warkewa? Kan Nadeer ne ya daure yace Amma Taya Kika San sunana harda gaisuwa? Wata Nurse tace Wai Nadeer ne sunanka Na daina cewa kawa na,tace kuma Wai Ana cewa mutum Ina kwana.

Okay cewar Nadeer Amma shi sai tunani yake yi ba Haka yasan Iman Mahaukaciya ba,sai kawai a ransa yace ai dama Mahaukata watarana suna Abu Kamar masu Hankali ai normal ne kawai ya share zancen yace Tashi mu tafi gida kinji sauki ai,Yana juya baya Iman ta zaro harshe tayi Masa gwalo kasa kasa ta furta na warke wullu,Ina Nan a gidanka Zama daram sai naga me Kamla zata Kulla maka.

Juyowa yayi tare da cewa dakko waccen Jakar kayan,Dire diren kafafu Iman ta Fara na Shagwaba tace Ni na San wata jaka ne,ai dai jaka tana daji kawata ce ma fada mukayi da ita na dawo wajenka na barta can,Bai kulata ba ya dauki Jakar kayan Suka tafi,Koda ya bude Mata mota zata shiga Don ta tabbatar Masa Bata warke ba sai ta shiga ta baya maimakon ta shige ta gaba ai sai ta Fara tura bayanta ciki,Fisgota yayi tare da zaunar da ita a cikin mota yace Haka akeyi ki koya daga yau,Gaba ya shiga Suka tafi gida.

Jawahir da Hanan Basu ji gargadin da Nadeer yayi musu ba Haka Suka Kara zuwa Wajen kawarsu Kamla, suna Hira Hanan tace wlh Bai Isa ya raba mu ba,Suna main Palo sai Hira sukeyi gaba Daya gulmar Iman da Nadeer sukeyi suna zaginta,Jawahir ce Bata cika magana ba tana Dan Tausayawa Iman,Kamla tace me Zaku ci me aiki ta dafa muku? Jawahir tace Ke yanzu me aiki ke dafa Miki Abinci? Kuma Haka kike barin Mijinki da yunwa kullum gidanki kayau a bushe baza aji kamshin girki na tashi ba,wannan ba tsari bane,kin San Kuma ba sonki yake ba ai tunda kina sonsa dagewa zakiyi ki dinga kyautata Masa ko bazai ci ba ki dafa ki dinga Masa hidima ko ba komai kin sauke Nauyin Dake kanki Kuma a hankali zai dawo ya soki sabo da zaiga kina da Halaye masu kyau,Amma fada,kishi da wulakanci wallahi Namiji bazai soki ba,ke ko ace Yana sonki sai ya daina sonki tunda Baki da halin da za a soki,Tasssss kake ji Kamla ta zubawa Jawahir Mari tana kumfar Baki tare da furta ke har kin Isa kizo har gidan Mijina ki zageni,Jawahir Kai ta girgiza Tare da furtawa kin Mari banza Kamla kinci darajar gidanki na Zo Amma wallahi watarana sai kinyi nadamar halayenki.

Iman taci Amanarki Allah ya saka Miki da mafi Alkhairi domin Nadeer yafi Ibaad komai Allah ya Baki Amma ki yi yanda Zaki zauna lafiya dashi kin kasa,Kuma Sai na tona Miki asiri abinda kikewa Iman,Hanan tace Baki kyauta ba Kamla da Kika Mari Jawahir me fada Miki gaskiya mu wallahi mun yafewa Iman yanzu mun Gane gaskiya tayi laifi ta bamu hakuri mun Kuma hakura,Ibaad idan ba mijinki bane Allah yayi ko mutuwa zakiyi wallahi baza ki same shi ba,idan kuwa mijinki ne ko kin tsofa sai Allah ya sake hada ku,irin wannan Banga abin tashin hankali ba,Mijinki duk tsiya shi Zaki Aura komai Dade wa.

Dariya Kamla tayi tace daga yau to bani ba ku,Ni dama Kun Isheni to wallahi ko a Hanya karku nuna Kun sanni,ba Ni ba ku,na canja kawaye Wanda suke wayayyu ba irinku ba banzaye,Ke Kuma Jawahir da kike cewa Zaki Tona min asiri karki manta har kanku zaku tonawa asiri,an fada muku bani da kwakwalwa? To Bari kiji sabo da Haka dama nayi yanda Dole da Sa hannunku a Hatsarin Iman da tayi,Na farko Hanan Dake muka je wajen Driver trailer har kinyi magana Cewar ayi Mata yanda baza ta mutu ba,kin ga video a wayata Nan take Kamla ta kunna video record da maganganu Hanan yanda za ayiwa Iman.

Duk abinda mukayi daku wallahi akwai video nasa yaro na ya dauki komai sabo da bacin Rana irin wannan,sai da nayi lissafi,Sannan ke Jawahir kece nasa Kika Kira Iman Kika ce tazo an tafi Wani company acan za ayi lecture,Kinga video dinki, Nan ma Jawahir ta ganta Kiri Kiri,Dariya Kamla tayi tace idan kun sace wayar nan a kwai wasu copies da yawa ba a Hannuna kadai ba,sabo da Haka kuyi yanda kuke so.

Kirji Jawahir ta dafe tare da furta wayyo Lallai bazan taba Bari Asiri ya tonu ba,nayi nadamar yiwa Iman Haka banyiwa kaina Adalci ba,Dariya Hanan tayi tace Ni kuwa kamar na fallasa asiri duk abinda zai faru to ya faru,wallahi Baki Isa ba cewar Jawahir,duk yanda zanyi Baza ki Tona ba,Tsawa Kamla ta buga musu tare da furta daga yau Kuma na daina kawance daku ku kama gabanku bani ba ku, Jawahir tace wato ke kin Koma Boss kenan ko? Kwarai kuwa cewar Kamla,Hanan ta Furta to Dan Uban Boss munga Bugyambo ma be karewarta ,Nadeer ne suka shigo tare da Iman,Iman ta ga kawayenta Bata nuna ta Gane su ba,Allah ya Baki lafiya Iman cewar Jawahir,Hanan tace Ina Yini Ya Nadeer ko kallo Basu Ishi Nadeer ba yayi gaba abinsa,Iman a ranta sai taji Tausayin Kamla yanda take son Nadeer shi Baya sonta,a ranta ta kudurce a ranta Lallai zata Yi Amfani da Ciwon Haukarta na baya ta taimakawa Kamla yanda zata samu Nadeer ya so ta ya karbe ta a matsayin mace.

Kitchen ta wuce Direct tana tsalle tsallenta Dan a tabbatar fa Bata warke ba,Cokali ta dakko da plate tana kida sai buga spoon din takeyi a jikin plate din da karfi a Haka ta taho tana dariya har gaban Kamla tana kada Mata,Ba zato ta kwala cokalin a goshin Kamla,tana dariya tana kida da Waka,Jawahir ta kalla tana cewa ke Yar ficika tasa kasan cokalin a hancin Jawahir tare da tambaya wannan rijiya ce? Tana zuwa Kan Hanan ta sheke da dariya tare Fisgo Dankwalin Hanan Dan gashin Hanan ya bayyana, ai Shekar Ungulu ce wannan cewar Iman,Ihu Suka kwala tsoro suke ji Kar Iman ko tana duka Basu sani ba, da gudu Suka bar gidan,Kamla kuwa Room dinta ta arce suka bar Iman Ita Daya tana ta dariya ita tasan ta warke dama tana sani tayi musu Haka.
Sai da Iman ta koma dakinta taji kewar iyayenta Babu Wanda take son gani sai su taya zata gansu oho.

Washe Gari Iman tayi Sallar asuba tare da Azhkar a hankali ta lallaba kitchen sai da ta shiga dakin Nadeer ta tabbata Yana bacci,Kamla kuwa dama Bata yin Sallar asuba sai Rana ta fito,ko Ina sai da Iman ta kulle Dan Kar Yan aiki su shugo su kamata,Haka kitchen ma ta kulle ko Ina,A gurguje ta soya dankali da kwai tayi Farfesun kaji me shegen dadi,ta dafa shayi yasha kayan kamshi yanda tasan Nadeer Yana so Haka tayi komai ta shirya Dining sannan ta gyara kitchen kamar ba Wanda ya shiga,da sauri ta koma room dinta Bayan ta bude ko Ina,Yan aiki Suka Fara aikin gyaran gidan Banda dakin Kamla,Iman Dana Nadeer, sai sun tashi a bacci ake gyara musu abinsu.

Nadeer sai kamshin girki yake ji ya cika gida,wanka yayi ya shirya cikin wasu kananan Kaya masu tsananin kyau da tsada kamar wani Bature Haka ya koma,cikin takunsa na Isa da takama ya fito Palo,Iman ya hango a Palo yanda ta Saba Zama tana kallon cartoon yau ma Haka ya ganta sai dai yau tafi kyau yanda tasa kayan na masu Hankali ne,Inda take ya tako,Kallo Daya tayi Masa kunya ta lullubeta ta kasa ko motsi shi dai Nadeer sai yaga Iman kamar me hankali tun jiya yake ganinta Haka, da kyar ta danne abinda takeji ta mike zumbur tana Sosa jiki Kamar me cutar karzuwa,Kawana kaga ta nunawa Nadeer Dining ya hango Abinci a jere, ki daina ce min kawana Yaya Nadeer sunana,To Yaya Nadeer Iman ta furta kamar me koyon yaren Hausa, yace waye yayi girkin? dakin Kamla ta nuna ma'ana itace ta dafa,Baza muci ba Bari mu siyo namu ko? Kafada Iman ta makale zata Yi kuka ita Dole sai anci abincin Kamla,Suna Haka sai ga Kamla ta sakko ko wanka Bata Yi ba,da Yar rigar baccinta tana Hamma,Bata kula kowa ba Bata tambayi waye yayi girkin ba kawai ta zauna a Dining ta zabi Wanda take so ta shiga ci hankalinta kwance. Nadeer ya yarda Itace ta dafa ganin yanda ta Riga kowa cin Abinci,Hannunsa Iman taja Zuwa Dining Suma Suka zauna,Hannu Iman tasa zata dauki Spoon Kamla ta daka Mata tsawa keeeee......Karuwar Mahaukaciya girkin ubanki ne ya dafa da Zaki ci? Shegiya kina nunawa ke mahaukaciya ce Amma kin San kwana da namijin wata,kwartuwa a Haka Zaki Kare munafuka,Iman taji Haushin kalaman Kamla matuka Amma ta nuna Bata ganewa ma

Please Login or Register in order to submit comment