Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma wajensa tana kuka tare da boyewa a bayansa,Kamla kuwa bayan ta Gama mutuwar tsayenta kafa ta daga zata gudu caraf Nadeer ya damko ta,ta Fara Ihu tana na tuba wlh bazan sake ba,Ko kallonta baiyi ba Mari da duka ta ko Ina yake Mata yace dama Ina sani tarko na Dana Miki,Dan ke muguwa ce kawar taki Kuma Marar lafiya Zaki doka Haka,Sai da ya tabbatar ta daku sannan ya kyaleta yace mayya me kambum baka wallahi indai wani Abu ya samu Iman bazan daga Miki kafa ba,wanne irin Rashin Imani ne Dake Haka?

Amarya washe garin Aure taci duka,Hannun Iman ya riko zasu sauka kasa kenan Suka ji Sallamar Baki,Kanwarsa Khadija da Kawayen Kamla su biyu Jawahir da Hanan,Khadija da sauri tace Ya Ina kwana? Lfy Alhmdllh ya furta da fara'a Khad dinmu kece a gidan? Ae Yaya Mama ce tace nazo na gano Mata lafiyarka,Murmushi yayi Yace lafiya Mana yanzu ma daga wajen Amarya muke kuje Dan Allah ku lallasar min ita tun jiya take Abu Daya kamar a kanta a ka Fara Abu, kunya ta Kama su Hanan,Khadija kuwa dariya tayi tace Lallai yaya, Su Hanan kamar Basu San Iman ba Suka haura sama abinsu dakin Kamla,a saman bed Suka hango Kamla tana Rusa uban kukan dukan data ci,Su Kuma Sunyi zaton kukan first night take Yi Kamar yanda ango yace.

Hanan ce ta kwashe da dariya,Allah me iko Kamar akanki aka Fara,Ni nayi mamaki wlh duk Girman Kan Nadeer har ya sakko da wuri Haka ya bada Kai Lallai Kamla Ke me sa'a ce, Khadija tace ai Yaya Nadeer me kirki ne sai Idan Wanda Bai San Halinsa ba zai ce Yana da Jin kai ba,Kamla cike da shesheka ta Furta D...d.. dukan..tsiya..y...yayi...min wallahi....dariya su Jawahir sukayi tare da cewa Lallai kinji maza Kamla mu Dama zuwa mukayi muji ya ake ciki sai gashi Kuma Abu har ya dau saiti komai na tafiya lafiya Alhmdllh,Khadija tace uhmm Ni na tafi gida Mama tace a gaida ki tayi waje,Khadija tana fita Kamla ta kwashe abinda ya faru ta sanarwa su Jawahir,Lallai Dan rainin hankali ne wannan guy din akan Iman zai Dake ki ko dai Sex yake yi da ita? Jiya ma tsakar dare Naga ta shige room dinsa sai wajen karshen dare Naga ya rakata dakinta Basu San Ina kallonsu ba,Salati da tafa hannu su Hanan ke Yi,Hanan tace gashi Likita ne bazai yarda tayi ciki ba,ai an shiga matsala ki mike tsaye Kamla Zama fa Bai ganki ba,ki sanarwa Mamanki tun lokaci Bai kure muku ba....garam Suka ji an banko kofa da karfi,Nadeer ne a fusace yace ku tashi ku bar min gida munafukan banza munafukan wofi wallahi duk ranar Dana sake ganinku ko a layin Nan sai na daure ku,Da gudu su Hanan Suka bar gidan,Suna fita Nadeer yace kije ki fadawa Kakar Mamanki ma nafi karfinku Marasa tarbiyya,mukus Kamla tayi ya Gama cin Ubanta yayi waje,gidan ya Bari Baki daya ko Iman Bai saurara ba a Palo ya barta tana kallo abinta.

Bai zarce ko Ina ba sai gidan Iyayensa,Umman Iman tana Palo tana Sallamar Baki Nadeer ya shigo da fara'a ta tarbe shi Suka gaisa Umma tace Ina Yar gidanka? Fatan dai lafiya Bata takura muku ba? Ban so aka tafi da ita da wuri ba ya kamata ace kunyi ko wata Daya ne da Amarya,Gashinsa me yawa ya Sosa yace Haba Umma to Iman ba inda zata zauna a hakan ma Bata ko kallon Amaryar tsoronta take ji duk da Ina kusa,Oh Kamla Kawarta guda Kai Ciwon hauka baiyi ba mutuwar tsaye ce badan Kar nayi sabo ba da mutum yayi Ciwon hauka gwara mutuwa,Haba Umma ki daina fadar Haka kaddara ce komai Allah yayi shine me kyau Dan Allah karki sake furta irin wannan ai Haukar Iman me sauki ce,idan ba fada akayi ba ai wani a Haka idan ya ganta zaice lafiyayya ce to Kuma har take abubuwanta dai dai ai sai a godewa Allah cewar Nadeer.

To Allah ya Bata lfy ameen Umma Ina Baba? Ya fita Office,Mikewa Nadeer yayi tare da wucewa Part dinsu,Mama ya Iske tana bedroom dinta saman lafiyayyen gadonta tana kwance tana huce gajiya,tana kallon Nadeer tace Ango wannan irin kyau Haka lallai,Murmushi yayi cike da kunya ya gaida Mama Yana wani Jin kunya, sun Dade suna Hira tana Masa Nasiha kafin tace ka shirya wacce kasa Zaku tafi Honey moon din?

Baki ya turo Haba Mama wanne Honey moon Kuma da 'yar zaman dakina Iman,Ana Honeymoon da Yar zaman daki ne? Duka Mama ta Kai Masa tana marar kunya, Yana murmushi ya bar gidan.
Tun da Kamla ta tabbatar Nadeer ya fita ta fito ta Kama Iman da duka ta ko ina har sai da ta gaji Dan kanta ta daina dukan ta,Haka ta hana Yan aiki aikinsu na yamma tasa Iman Dole tana koya Mata aikin,Iman Kuma ba Kai tunda ta gano Kan aikin ba ko gajiya take abinta iya karfinta,Kamla kuwa taci kwalliya tana hakimce a kujerar Palo tana tauna chewgum tana chatting a waya sai dariya takeyi ita Daya.

Sai wurin Magrib motar Nadeer ta kutso Kai cikin gidan parking yayi tare da Fitowa da ledar shopping a hannunsa,Iman ya Fara hangowa kanta ba dankwali ga Magrib ta kusa a compound tana ta faman shara ta rike kugu tana cije Baki alamar ta gaji,mutuwar tsaye yayi kawai cike da Tausayawa kamar ance ta juyo tana juyowa ta ganshi a tsaye a bayanta,ihu ta buga tayi uban jifa da tsintsiya Nan take tsintsiyar ta wargaje a kasa dai dai lokacin Kamla ta leko Jin ihu sai taga Iman ce ta daka tsalle tare da fadawa Kirjin Nadeer,Tana ta tsalle ta cukwikwiye shi ta ko Ina Kamar yau ta Fara ganinsa,Murmushi ya saki me tsada ya janye jikinsa da sauri,zata Kara cakumoshi ya matsa da sauri,sai taga Kamar Wasa yake mata,Sai tazo zata cakumoshi sai ya matsa da sauri Haka Suka dinga Yi suna dariya,Ledar Dake hannunsa ta fisge ba zato,Ledar ta Bude taga snacks dasu Icecream kawai dama yunwa take ji Nan ta dakko ta Fara ci hannu baka hannu kwarya wannan ya nuna tun safe Bata sake cin komai ba,kwace snack din da take ci yayi tare da icecream din ya zuba a Dustbin yace kinyi shara hannunki Babu wanki akwai Dirty kina cin Abu dashi salon cuta ta kamaki,wani ya dauko a ledar ya bude da kansa ya Shiga Bata a Baki tana ci,Nan take ta cinye cake manya uku da Icecream roba Daya,Kamla tana kallo yayin da hawayen kishi ya wanke Mata fuska a fili tace sai na kashe Iman da Hannuna.

Kamla tana kallo ya shigo tare da Iman ba tare Daya kalleta ba ransa a bace yace a ko yaushe munanan halayenki Kara tunzira Ni sukeyi Ina Jin matukar tsanar ki,ba da haka ake karban zuciyar mutum ba,halaye masu kyau na kwarai suke sawa a so mutum,rashin sa kuwa shi ke Kara Haifar da kiyayya,ki sani Kamla ban taba Jin digon sonki ba kinsa Iyayena sun aura min ke,ke da iyayenki sun musu karya ki sani bakya sahun Matan da Zan iya so a duniya,bukatarki baza ta biya ba,da ace kina da Halaye na kwarai watakil zai sa na canja Amma ki sani wallahi duk abinda Kika shuka shi Zaki girba,Iman idan kin gaji ki kwantar da ita ki yanka ta kiga wacce riba Zaki samu, Zan iya jure komai Amma Banda Cin zalin Iman da kikeyi,tana da lalura,kin San Amana ce a wajena yanzu Iman a Hannuna take,komai nata Yana Hannuna,'yar uwata ce,jini na ce, Baki kula da ita ba ai idan da kunya baza kizo ki dinga azabtar da ita ba,nayi Miki warning na farko karki sake nayi Miki na biyu na uku kuwa hakan zai sa ki karbi sakamako mummuna a hannuna,bana sonki bazai yuwu Haka kawai Ina Zama na lafiya kizo ki dinga sa min Ciwon Kai ba, Yana furta Haka yaja tsaki suka wuce tare da Iman,Kamla na tsaye sororo karshe wayarta ta dauka ta Kira Mamanta ta kule a daki suna sirri.
Yanda Za ayi Nadeer ya sota.










AsmaBaffa.
[11/4, 11:16 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ


FREE PAGE






16-20







Official






By
AsmaBaffa






ADDU'AR KAWA NOVEL
SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨








SANARWA..

NA CANJA ACCNT NUMBER.






RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

YAR KAWANGILA COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

ADDU'AR KAWA
Masu son Shiga group dari biyu ne.


Ga masu son siya ta Bank ga Accnt number

0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gt bank.

Masu tura katin MTN ta WhatsApp,transfer ko Vtu ga number da zaku tura
08033933642.








Page naku ne

LEEMAT
NAFEESAT UMAR MUHAMMAD
UMMIN SADDIQ
SWEETY BELLA
MARIYA HABU
MATAR FILLO.














Kamla ce tace Cikin kuka Mama ki taimaka min,me ya faru Dake 'yata? Idan sirrinki ne na kwanciya karki ce komai Kamla ai abin Haka yake,Karki damu kinji kiyi hakuri zuwa wani lokaci Zaki Saba,Ma..Mama bafa Haka bane tunda nazo gidan Nan Ubana kawai yake ci,Ke Kamla ban son sharri fa, I'm serious Mama ko bacci bana Yi sai masifa bashi da mutunci ko kadan,Ga Rashin tausayi,Wannan Jarabar yarinyar Iman itace kawai a gabansa,jiya ma Sai da ya fyalfyallamin mari a kanta,gashi komai yace baya so na,Ni dai Mama Ko gurin Boka ne kije,ke ko shirka ce muyi idan bukata ta biya sai mu tuba Nan gaba,ke mu mun ga yau munga jiya ba sai da Boka ba, Tuggu da munafunci kawai ya ishe su ,gashi Kinsan tuggu Muka hada har Kika samu ya aure ki,to ki nutsu Zan fada Miki yanda Zaki bullo masa sai zuwa dare Zan kiraki,ki kwantar da hankalinki Kamar tsumma a cikin Randa.
Farin ciki ne ya Kama Kamla sukayi Sallama da Mamanta.

Sabo da farin ciki ai Kamla sabon wanka ta sake ta cakare cikin doguwar Rigar green Material,tayi kyau sosai tana baza kamshi ta fito main Palo tana wani nishadi da Gadara tana hango kanta kawai ta samu Nadeer a Hannu, a palon ta Iske Nadeer a zaune Yana zaune a center carpet Yana Typing a laptop dinsa da wasu Takardu a gabansa Yana cin Apple,Kujerar Dake facing nasa Kamla ta zauna tare da tsura Masa Ido kawai tana faman kallonsa Kamar mayya,Bai ma San tana Yi ba,Iman ce ta fito daga kitchen Hannunta dauke da Plate ta ciko shi da ruwa tana kurbar abinta duk ta jika kayan jikinta,Riga ce doguwa marar nauyi,tsakiyar Palon ta zauna tare da ajiye Plate din ruwa a gabanta Kamar zata ci Abinci,Nadeer Yana satar kallon me takeyi Yana kallo tana lasar ruwan kamar mage tana Shan ruwa, Kamla tace ko zaka tayata Sha ne? Wallahi kana cin zalina Allah ya Isa na,Ido ya rumtse sabo da zafin kalaman da Kamla ta Furta Masa,Yau ya tabbatar Kamla Bata samu tarbiyya ba,Bata iya magana ba sam, Iman ya Kira a hankali yace 'Yar zaman daki da sauri ta juyo sabo da tasan yace Wai shine sunanta,Me kike Yi? Abinci nake ci, Hararar Wasa yayi Mata yace kawo mu gani,plate din ta Kai Masa har ta shanye ruwan ma,agogon dake daure a tsintsiyar Hannunsa me tsadar gaske ya kalla,10:30pm je ki canja Kaya kiyi bacci,To Iman ta furta ta tafi Room dinta, ba tare da ko kallon Kamla yayi ba ya mike shima zai Haura sama.

Tsaki Kamla taja tare da furta aikin banza Dan yaga Ana sonsa Wai shi me kyau,Nadeer ya ji tsakin da tayi Masa kawai share ta yayi ya wuce abinsa,Ya Kai Step din karshe kenan Iman ta fito da gudu Suka ci Karo,Tana ganin Nadeer ne tayi sauri ta damki rigarsa lokacin Kamla ta hauro saman Itama da baya ta koma tare da rabewa a jikin bango tana kallon me Nadeer zaiyi, Sake min Riga Mana ya furtawa Iman da masifa,Tsalle tayi da Shagwaba Zata Yi kuka,Mene ne? Ya tambaye ta,Ni.....kallon Cartoon za muyi,Kije ki kalla ke Daya bacci zanyi,Hannunsa ta rike tace to Zo muyi Enter kaji, Mene Enter? Kasa tunawa Iman tayi sai kawai ta Fara tafi da tsalle na Yan Primary tana wakar Enter....Enter, Ohhh Nadeer ya Furta Dan yasan Yara nayi,To kayi kaima,dariya abin ya bashi Yana Namiji Babba ya Fara wata Enter ai shima ya haukace kawai,Dakinsa ya wuce Iman ta bishi da gudu ta cika gidan da wakar Enter, Kofa ya banko a gaban Kamla wacce ta rabe tana kallo tace wayyo Iskanci zasuyi yau ma wallahi bazanyi bacci ba,Munafukai zasu fake da Enter ok na gane wato Enter shine Shiga nufinta Nadeer Enter Her body and scatter her ok wooo ai kuwa yau sai Na gani da Ido na.

Kamla kofar Room din Nadeer ta lallaba ta Dan tura kofar kadan yanda baza suji Alama ba idanuwanta ta leka dasu kawai,Iman ta Hango tana ta birgima a kasan tiles tana wakokin Yan primary Kuma da karfi,Amma Nadeer duk rashin son Hayaniyarsa ba ruwansa Bed dinsa ya gyara sosai kamar mace ya shige Toilet,Wanka yayi a toilet din ya shirya sannan ya fito sanye cikin fararen kayan Baccinsa marasa nauyi ya kwanta abinsa Yana Adduoi,Iman kuwa har yanzu wakarta takeyi tana birgima a kasa ta Gama zage room din,Kamla tana daga kofa cewa take yau sai Na gani jira har dare yayi nisa,Kamla Babu ko gajiya tana tsaye, Taga Nadeer ya jefowa Iman pillow kasa,a Fili Kamar me rada Kamla tace tooooo ya Fara kiranta da wayo wato ta dauki pillow su kwanta Yes Ina Nan Zan gani,Kafin Kamla ta rufe Baki Iman ta mike ta juya kenan zata bar Room din sai Kuma Haukar ta motsa ta fasa Tafiya kafa tasa tana dukan jikin bed din Nadeer duk ta hanashi bacci,Tsaki yaja tare da danne kansa da Pillow alamar Iman ta Dame shi,Ganin abinda yayi sai Iman tayi Sufa ta fada saman Nadeer dake saman Bed, Baki Kamla ta Bude tare da yin ihu kadan sama sama tace eho kwartaye Ina Nan wlh, Mintsinin Nadeer Iman tayi da karfi a kafarsa,Zafi ya ratsa Nadeer ya kasa controlling kansa kawai ya samu ya hankado Iman kasa ta Fado tare da mikewa zata arce,Kamla farin ciki ya kamata tace yau Baya Mood Iman,Fitowa Iman tayi taci Karo da Kamla, bul Kamla Fado room din Nadeer tace ya zaka koreta sai da ka lasawa mahaukaciya Zuma ta Saba zaka dawo ka tsaneta,tunawa tayi da Bata so Nadeer ya gane tana Masa labe sai ta fice da gudu,tsaki Yaja ya juya abinsa.

A tsorace Iman ta raba ta arce da gudu zuwa Room dinta itama,sai lokacin Kamla ta koma dakinta ta kwanta tana jira dare ya tsala ta sake lekawa ko zata ga Iman da Nadeer sun Jone tare.
A Haka har bacci ya kwashe ta Bata fito ba yayin da Iman da Nadeer suke shakar baccinsu hankali kwance kowanne a dakinsa.

Washe Gari da sassafe Iman ta tashi Kamar yanda aka koya Mata Haka tayi brush da wanka,Sallah kuwa Babu batunta kawai Doguwar Riga ta zura sakamakon Nadeer gaba Daya su ya ebo Mata sabo sune zasu Mata dadin sawa ba wahala, ko haske gari baiyi ba Iman ta dawo main Palo tare da kunna kallo ta kamo tashar cartoon tana kallo abinta ,Nadeer ne ya dawo daga masallaci Sallar asuba ya iske Iman tana kallo sai kuka takeyi Wai Tausayi Cartoon suke Bata,Baiyi mamaki ba ko kadan yasan ba hankali ne da Iman ba, Kitchen Ya wuce da kansa ya hada Mata lafiyayyen Tea sai Bread and Egg,a wani Dan Faranti ya shirya komai ya kawo Mata gabanta ya ajiye yasan Da wuri take karyawa,Ganin Abinci sai ta Fara murna tare da kafa Kai tana kwankwada Bata ajiye cup din ba sai da ta shanye shayin tas sannan ta dauki kwanta soyayye ta cinye sai bread shine na karshe ta dinga kasumar abinta har ta cinye yanka uku sannan ta Mika Masa abinsa,dariya yayi ganin tana Lashe lips hakan ya nuna ta ji dadinsa.

Wayar Kamla ce tayi Kara,Ganin Jawahir ce Kawarta ta dauka da sauri,Hello Jawa ya kike,lfy Amarya kinsha Mai,ban son tsokana fa cewar Kamla,To ya mutuniyar Taki ne wai? Hmmm Iman tana Nan shegiya na Rasa yanda Zan bullowa yarinyar Nan naga karshenta,Jawahir dariya tayi sannan tace Ni a ganina da kin hakura kin kyaleta Haka tunda ta saduda ta bamu hakuri ya kamata mu kyaleta Haka Dan Allah ko Dan Darajar kawacen mu da yanda ta Gane gaskiya ta Fadi laifinta a gare mu ta Kuma bamu hakuri har ta dinga bamu kudade tana kyautata Mana sabo da mu hakura mu yafe mata.

Mutum yaci Amanarka Kuma ya dawo ya fada maka ya baka hakuri kin San Abin Babba ne,ba kowa ne zai iya wannan abin ba,yayi laifi ya tonawa kansa asiri ba kowa Allah ke bawa wannan baiwar ba,ko banza Iman tana da zuciya me kyau,ko Allah aka yiwa laifi idan ka tuba yana yafe mana bare mu Dan Adam.

Tsaki Kamla taja tace Dama akan wannan Kika kirani? To wallahi bazan hakura ba,ke Jawahir Bari kiji abinda ban taba fada muku ba tun farko haduwata da Iman a school ban taba kaunarta ba,na tsaneta sabo da Ni indai mutum zai fini ba kaunarsa nakeyi ba,kawai danne zuciyata nakeyi,Yanzu Kamla duk kawacen Nan muma badan Allah kike Zama damu ba? Ana aikin banza ne yanzu,Use people and get what you want Haka akeyi yanzu,Ni fa yanzu Jawahir ba sa'arku bace karki ga Muna mutunci kice Zaki dameni da wata Nasiha,Haka Kika ce Kamla? Ae idan a gidanku ake ciyar Dani kisa a daina...kit ta kashe wayarta.

kwalliya Kamla tayi sosai Tayi Kyau Cikin Kayan lefenta ta sa wata Atamfa Red Riga da skert,ganin yau Bata ga Iman ta fito ba ta tabbata tana garden, Direct Garden ta wuce a can ta Iske Iman tana ta Wasa da ruwan da ake bawa Shuke Shuke ta jika jikinta sharkaf,Ganin Haka sai Kamla tace Allah ameen Allah yasa Mura ta sarke Miki Numfashi,tsabar mugunta sai Kamla ta karbi Abin ruwan ta Shiga fesawa Iman tana cewa Ruwan sama ake Yi maza Yi Wanka kinji,Iman kuwa sai abin yake birgeta ta tsaya Kamla ta dinga sheka Mata ruwa Kamar tana wanke mota Allah sarki Iman Sai Tsalle takeyi ta samu abinda take so.

Dama ba Dankwali a Kanta kawai sai Kamla ta dawo saitin Kan Iman ta Shiga wanke Mata gashi da karfi take fesa Mata ruwan,sai shidewa Iman takeyi, Sai da Kamla ta tabbata ta Sha wahala domin tun Iman tana Jin Dadi har ta daina sai rawar Sanyi take Yi,Kamla kanta ta daga sama Karaf ta hango Katon Miciji a saman Bishiyar Mango,Sai ta kalli Iman wacce ke rawar sanyi tace Ke jeki Hau saman Bishiyar can ko naci ubanki da miyar Tattasai, Iman tace Mene Hau?

Mari Kamla ta kwada Mata sosai tace Dan Uwarki ki hau Bishiyar can yau sai kin kamo min miciji can,gwadawa Iman tayi yanda ake Hawa,ita Kuma Haukar Tata ta son Wasa ce,Sai ta Fara kokarin Hawa ba hankali sannan Bishiyar karama ce me saukin Hawa sai ga Iman ta haye sama miciji na samanta kadan a wani reshe, Kamla sai ta shiga Nunawa Iman Miciji tana kamo min wannan kinji,kallon wurin da Kamla Ke nunawa tayi sai taga Abu Amma Bata Gane Mene ne ba,Hannu Iman ta Kai zata kamo miciji sai ko miciji ya fasa Kai ya kawo Mata Sara Allah yasa Bai sameta ba,firgitar da Iman tayi yasa ta Fado kasa sai Kamla ta sheke da dariya tana Jin Dadi Iman ta Fado har gwiwoyinta sun kurje a kasa.

Abinda Zan tayi Miki kenan har sai Iyayenki sun gaji sun maida ke gidan Mahaukata sun Barni daga Ni sai Mijina,Nadeer Bai San me sukeyi ba tuni yayi shirinsa ya wuce Hospital abinsa yayin da Su Kamla Suka koma ciki tare da shiga kitchen ta hada cornflakes ta Sha,Bata kaunar yin girki ta Iya girki Amma kyuya Bata barinta tayi sai dai Ta dinga cin Cold abu,ko tasa Yan aiki su Aminatu su dafa Mata,Iman kuwa bedroom din Nadeer ta shiga nemansa baya Nan ta shiga Duba shi Amma Bata ganshi ba,kayanta sun jike sosai Bata Yi hankalin cirewa ba sai ta dawo Palo ta kwanta a saman doguwar kujera ta kankame jikinta tana rawar sanyi.

Kamla ganin yanda Iman ke karkarwa sai tazo tana murna ta kunna Mata Ac ta kure volume dinta karshe,Sanyi ya cika ko Ina,ta kulle ko Ina na Palo sanyi gauraye Palon shegiya ki mutu ma ba Imani ne Dani ba Ni bani da mutunci,inda mutunci ma yake banje ba,ni na kashe mutum ba komai bane a wajena matukar za a shiga gonata to kuwa tuggu da makirci ya ishe shi,Halayen Uwata na gado bamu da Imani Cewar Kamla ta furta tare da shigewa room dinta tayi kwanciyarta bacci ya kwashe ta,Iman Bata Yi hankalin barin wajen ba ta kwanta a Haka abinta.
Kamla Mamanta ta Kira a waya,tace Umma na Fara aiwatar da abinda Kika ce Bari yazo yagani da kansa zai dauke ta daga gidan Nan ya maidata gidan Ubanta ko gidan Mahaukata.
Mamanta tace yawwa yanzu kina ji kije kiyi Mata turaren Nan to Mama an Gama cewar Kamla.

Tun safe Iman ke kwance tana uwar karkarwa har Karfe Daya na Rana lokacin Kamla ta fito Ta sake tabbatarwa ta rufe ko Ina,sai ta fita tace me gadi ya samo Mata garwashin wuta zata Yi turaren wuta,15mnt me gadi ya kawo Mata wuta a palon Kamla ta zuba Barkono a ciki ta kawo inda Iman ke kwance ta Fara turara Mata ta koma bedroom dinta da gudu, Hayaki da yaji ya turnuke Iman ta Fara tari idonta yayi jajir Amma abinka da ba hankali Bata iya tashi ba a Nan wajen ta sume,Sai da Barkono ya cinye sannan Kamla ta fito ta lallaba ta dauke abin turaren,ita kanta tari takeyi data shaka, Sai yamma zai dawo Allah yasa ya iske kin mutu ma cewar Kamla, 5pm ya tuna Iman maybe bata ci Abinci ba,Asibitinsa ya bari silverbirds yaje ya musu take away ya nufo gida, Motar Taufeeq ce Tayi parking a gaggauce ya shigo Da ledojin take away ya kawowa Iman abincin.



Palo ya shigo dauke da Sallama a Bakinsa,a kwance ya hango Iman kamar gawa Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba,Da sauri ya Karasa inda take kwance,Palon Kuma Babu wani alamar yajin Barkono ko wani Abu tuni Kamla tasa Yan aikin sun gyara ta saki Ac tare da Bude ko Ina yasha Iska sannan ta kulle ko Ina a gain ta bar Palon,gashi ta Hana ko wacce me aiki taba ko yatsan Iman.
Nadeer tashin Iman ya Fara Yi ya girgiza jikinta yaji Kamar gawa ya rike Hannunta Shuru,Hankalinsa ya tashi gashi yasan tana raye ba mutuwa tayi ba,ruwan sanyi ya ebo tare da zuba Mata Nan take ta farfado tana tari,Magana tayi da kyar Kawana sai ta fashe da kuka,Muryarta yaji a shake kamar mura ta kamata me karfi da kyar take Jan numfashi,Hannunta ya rike Yana tambayarta me ya faru dake waye? Shuru tayi Bata da hankalin da har zata iya fadar me ya faru da ita,Kuka kawai take Masa,wuyanta ya taba da Bayan Hannunsa yaji zafi jikinta alamar mura ce ta kamata,Munafuka Kamla tana Labe a lungu tana kallonsu sai dariya takeyi kasa kasa,wani room ya shiga ya kwaso kayan Allurai da Drip,Allurai ya zuba a cikin Ruwan sannan yace Tashi mu koma room dinki a sa Miki ruwa a can,Tana kukanta ta mike tsaye da kyar Suka Haura sama tana gaba Yana binta a baya,Sai yanzu ya kula da kayan jikinta a jike sharkaf da ruwa har ya

Please Login or Register in order to submit comment