Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Furta cike da Shagwaba Kallonta yayi Suka hada Ido yace Zanje na dawo ne yanzu Ina da aiki a gida, Kai ta daga Masa da Tausayi tare furta idan baka dawo ba Kuka Ni dai zanyi, Alright kiyi kukanki kinji idan ban dawo ba,Kai ta daga Masa to zata Yi kukanta,da sauri ya fita ya barta a tsaye,Da gudu ta leka ta window tana kallonsa zai Shiga Mota kanta ta zuro ta window ta kwalla uban Kara da sauri ya dago ya kalli window din nata ya hango ta tana daga Masa Hannu, Hannu ya daga shima ya Shiga Mota ya wuce abinsa.

Kamla murna ta ishe ta zata Auri Nadeer Iyayenta ma sai Murna sukeyi Yar su zata auri Me kudi Dan me kudi,sun Gama shirinsu na biki Kamla sai rabon Iv sukeyi da su Jawahir,Yau ma suna motar Kamla sun Fita Hanan tace wlh Allah ya karbi Adduarki Kamla kamar Wasa Kika fada Kika ce sai ta Haukace gashi ta tabbata Kuma kince sai kin auri Nadeer gashi kin samu Wanda ya dace,Allah yasa dai kema Kyakyawa ce kawai hasken fata zasu nuna miki,Hasken ma yanzu zasu daina nuna min na siyo Mai me tsada Zan na shafawa kwana Nan zaku ganni na dawo Fara tas Nima,Jawahir tace Yanzu gashi ance Iman da Angonki take yarda shike kula da ita Kuma gidanki za a kawo ta ku zauna tare,Dariya Kamla tayi tace ai Yar aiki na zata dawo wlh,ba ruwana da Haukarta Ubanta zata ci a hannu na,ai Ina fada muku Alkawarin karya nayiwa Iyayenta Kan cewar Zan kula da ita,abinda Dole zai fita daga Ni sai Iman a gidan ai ta Zama baiwa ta,Ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli yaci riba,na dauki fansa,matukar Ina Raye Iman baza tayi rayuwa me Dadi ba.

Ina tsoro karfa Nadeer ya so ta? Hmm ai ba dai ya sota ba sai dai ta soshi Kuma baza ta same shi ba,Ina Adduar Allah ya jarabci Iman da son Nadeer sannan ya Hanata shi sai Ni kadai Zan zauna da abina, A Haka zata Kare shegiya ai Iman ko a kabari taga me kyau sai ta soshi mayya,Kinga dai a haukace take Amma ta mannewa Angona shi kadai take yarda dashi,Kuma wallahi Dan Yana da matsiyacin kyau ne,da ace Wani garan ne Iman baza ta kalle shi ba,Dariya sukayi gaba har suka je gidan da zasu Kai Iv, Jawahir ta fito daga Mota tana cewa Ango yace bazai Attending ko wanne Event namu ba ko? Hmm ai Kamu kawai zanyi a daura aure a kaini Nima ban damu da wasu Dinner etc ba Tunda burina ya cika an Gama cewar Kamla.

Bangaren su Umma ma Sun Gama Shirin bikinsu da komai ba wani Shagali za ayi ba,Haka su Abba ma,Nadeer ne kawai frnds nasa sun sani su Sameer ne Suka gayyato abokai gaba daya iya Daurin aure Suma sunce baza su hada Event ba sabo da suna Taya abokinsu bakin cikin auren dole.
Ita kuwa Kamla idan Mama suka Kira su tambayeta suji ko Dansu Yana zuwa zance,sai tace Ai kusan kullum sai yaje zance,wayon Kamla dan Kar tace Baya zuwa su tabbatar baya sonta a fasa auren sai tace ai Yana zuwa sosai.
Haka Ma Maman Kamla sai ta Kira Mama tayi ta Mata godiya Wai Nadeer yana musu Sha Tara ta arziki bayan shi Bai San komai ba.

Ango harkar gabansa yake Yi,Ana saura kwana Daya bikin Nadeer Yaje Hospital wajen Iman a zaune ya ganta da Handle a hannunta tana game na cartoon a Tv masu kula da ita Suka hada Mata ganin tana so,ganin Nadeer ya shigo tayi jifa da Handle din ta mike da sauri tana faman dariyar Jin Dadi,Ido ya lumshe Mata Yana murmushinsa me tsada.
Zama sukayi a gefen bed, Daga Haka Babu Wanda yayiwa wani magana,Nadeer yayi Shuru ya tafi duniyar tunani za ayi Masa Auren dole.

Hannunsa Iman ta rike tare da matsawa da sauri ya juyo ya kalle ta Murmushi ta saki tare da cewa Mene ne? Gobe za a daura min Aure,za a baka Mata?Kai ya daga Mata,dariya ta kyalkyale da ita tare da cewa gobe Zan bar Nan mu tafi ko? Kai ya daga Mata,Allah yasa a baka Matar Adduar Iman kenan itama a halinta na Mahaukata.

Handle din game ya dauka ya mikawa Iman ya dauki Daya suna yin game Iman Bata iya ba shirmenta ma take yi sai koya Mata yakeyi Amma Bata ganewa sabo da yanzu ba hankali ne da ita ba.
Yau Nadeer Bai koma gida ba sai Tsakar dare 3am Abba tunaninsu Duk Shirin biki ne,Mama tace kaga yaran zamani ko? Ashe Yana so gashi Nan kullum baya Zama Ana ta Shirin biki,dariya Abba yayi Ni nasan Halin Dana Masifar zurfin ciki da pretending a wurin Nadeer ai yayi yawa,Allah ya kyauta.

Washe Gari 11am za a daura aure 10:30am Ango Yana ta fushi da kyar Sameer ya lallaba shi ya shirya cikin dinkin da Abba ya dinka Masa na Daurin aure,Shadda yasa fara taji uban aiki me tsada da kyau harda babbar Riga irin ta matasan zamani Hula yasa dai dai shi ya Dora ta sosai ba karamin kyau Nadeer yayi ba,kowa ya kalle shi sai ya sake Kamar a sace shi,Yana zuba Kamshi Wayarsa ya dauka ya Kira yace ya kin Shirya ta kuwa? Alright wurin makeup din Zan same ku? Ok ya furta tare da kashe wayar.

Masallacin da za a daura Auren suka je, an cika makil manyan mutane sun cika ko Ina sai jibgan motoci,Ango Basu Dade da zuwa ba aka Daura auren Kamla da Nadeer Kan sadaki dubu dari ko tsayawa Nadeer baiyi ba bare ayi wani pics sabo da Baya son wani tarihin da zai tuna wannan Rana kawai mota ya shiga ya bar wajen,Abba yaji Haushin abinda yayi Amma ya share,Bai wuce ko Ina ba sai wurin make up inda ya Iske Iman tana ta tsala ihu da kuka Taki yarda a shiryata,Tsawa taji Nadeer ya buga Mata,Shuru tayi ta koma wajensa da gudu tana ajiyar Zuciya,Harara ya watsa Mata tace to Animal ne a Nan Allah wannan Aladiya ce,idan Baki tsaya ba sai na zaneki a Nan Kuma tafiya zanyi na barki bazan sake zuwa ba,komawa tayi ta zauna a inda taga Ana zama,Kusa da ita ya koma ya zauna yace Ina kusa ki tsaya,Kai ta daga kamar zata Yi kuka,a Haka aka Yi Mata kwalliya tayi Masifar kyau,sanye take cikin Shadda Silver and white dinki aka Mata na Allah Tsine uwar me karya ko ita ce Amaryar sai Haka.

Daurin da aka nada Mata na musamman ne, takalminta da jaka suka Silver harda mayafinta Amma ta rike a hannu a hannu Bata so,Ana gamawa ta mike tana cika tana batsewa wayarsa ya mikawa wata tayi musu pics,Haka ta dinga Yi musu pics kala kala, Iman tana ta Shagwaba tana turo lips Bata so ba Karamin kyau Suka Yi ba,kanta ta daura a Kirjinsa Wai ta gaji Nan ma aka daukesu, wayar ya karba ya biyasu Kudinsu harda karin wasu na kyauta,a gaban mota ya sata,Ya Shiga yaja Suka tafi zuwa gidansu.

Anyi anyi yaje gidan iyayen Amarya yaki yarda tun Sameer yayi naci har ya kyale shi,Umma tana cikin mutane sai ganin Iman tayi da Nadeer sun shigo Iman Tasha kyau kamar me hankali,ganin su Umma da mutane Iman ta gigice ta rude,hankalinta ya tashi jikinta ya Fara rawa Kar Kar da sauri Iman tace zanyi Kuka,Idan Kika Yi ko magana tafiya zanyi na barki ba ruwana da ke cewar Nadeer,Hannunta ta kwace da gudu ta fada wani daki,taga mutane ai ta fito da Gudun tsiya again tayi sama da gudu da kukanta gaba Daya ta fada dakin Umma taga Wasu Yan uwan Umma,kanta ya dauki zafi sai kawai ta silale a kasa ta sume,dama damuwa tana yiwa Iman yawa sai Suma.

Da sauri Umma da Nadeer Suka karasa Inda Iman ke kwance rasha rasha,Ruwan Sanyi ya yayyafa Mata ta farfado
Amma Bata iya Gane su waye ta tashi again da gudu ta fada dakinta Wanda Bata San dakin waye ba,Nan ta samu ba kowa,Saman bed din ta Haura ta lullube kanta da Bargo jikinta Yana rawa karrrrr karrrrr tana uban nishi.

Nadeer yace Umma ki barta a room dinta ita Daya,idan wani Abu ya faru ki sanar min a waya,To Nadeer wannan kwalliyar fa? Murmushi yayi Yace Umma na biki ne Mana nasa akayi Mata,Oh to an gode Allah ya saka da Alkhairi irin wannan hidima Haka ko gajiya baka Yi,Ficewa yayi kawai abinsa,Yan Uwan su Kamla sunzo suna wajen Mama,Ya wuce su abinsa ko kallonsu baiyi ba ya Isa wajen Mamansa yace Mama abincina fa? Yana part dinka an Kai su Sameer suna can suna jiranka,Yana Jin Mama tana cewa kayi kyau Ango Bai ko juyo ba,ya wuce abinsa,Yan uwan Kamla suna shine ango,Kai Amma tayi sa'a sai dai Bai da mutunci ko kadan,kalli ko kallonmu baiyi ba a Haka Wai ya auri Yar uwarmu suruki ne, cab za ayi ta Ashe.

Iman a dakinta ta boye data Ji motsin mutum sai ta fada toilet tasa key,har aka Gama biki ba Wanda yaje wajenta Umma ce kawai take Kai Mata Abinci Amma Iman Bata ko kallon abincin bare taci ma,Ganin Bata ga Nadeer ba har dare yayi sai ta fashe da kuka ta Fara farfasa komai data gani na dakin,Kayan kwalliya dake Kan mirror gaba Daya watsi tayi da su,Da Gudu Umma ta shigo Iman ta saki Ihu da Kara hakan yasa ta Fadi a kasa tana ta Suma,Hankalin Umma ya tashi ba shiri ta Kira Babanta a waya yace Bari na turo Nadeer,Ka manta Yau za a raka shi dakin Amaryarsa, ae Haka ne Amma Bari dai a sanar Masa,Nadeer Yana can Su Sameer sun wani takura Masa Dole yayi wanka ya shirya cikin Wata dakakkiyar Shadda sea blue,yasha kyau Kam,sun fito zasu wuce kenan Kiran Baba ya shigo,Dagawa yayi Bayan sun gaisa Baba yace Iman ce dama take ta Suma tana lalata kayan room dinta,Ok Baba Bari Naje wajenta,Abokansa ya kalla yace Ina zuwa,Da sauri ya Karasa wajen Umma Wacce ke tsaye a palon sama ta daga a Kanta sama Tana nazari,Bedroom din Iman ya wuce room din yabi da kallo,Ba karamin barna tayi ba, gashi taji ciwo a Hannunta,wata Allura ya koma ya dakko yazo ya tsira Mata tana sume,Ko minti biyu ba ayi ba ta farka abinta,ganinsa kawai yasa ta mike zumbur da sauri ta taka zuwa inda yake jikin mirror,kirjinsa ta fada tare da rungumeshi Kam,jikinta har rawa yake Yi ta Rasa ya zata Yi da ranta sabo da murnar ganinsa,Dariya yayi Yana kallon idanuwanta ita kuwa fuska ta Bata tana doka kafafu na Shagwaba ya tafi ya barta.

Ki zauna gobe zanzo na dauke ki kinji,Kafada ta makale Wai Bata yarda ba,Rigarsa ta rike sosai Kam,ganin Haka yasa yace muje rigarsa ta rike Kam suka fita a Haka,Umma ce ta taresu tana murna tace Alhmddlh Amma ai Kuma karka tafi da ita yau za a Kai maka amaryarka fa,ba komai Umma tunda tare zamu zauna dama Dole akan ta dinga damuwa Haka gwara mu tafi kawai.
Iman ya rikewa Hannu kanta ba ko dankwali tana ta sauri su bar gidan.
Abokansa Babu wanda Bai Tausayawa Iman ba ganin halin da take ciki,Ko magana Babu Wanda yayiwa Ango Kan me yasa zai tafi da wata tun yanzu,kawai motocinsu Suka Shiga tare da barin gidan Abba zuwa katafaren Gidan Ango dake Maitama Abuja,Gida ne na gagara,gida ne Wanda ya amsa sunansa gida,ba karamin kudi aka kashe ba wajen tsara wannan gida na Nadeer ba,Ko a kasar waje sai Haka,Babu abinda Babu na more rayuwa,komai an tanada,Yan aikine maza da mata ke zagade a ko Ina na gidan.

Gida ya dauki uban kamshi ta ko Ina,Sai Wanda Suka kawo Amarya da Yan Mata sai Yan Uwanta Mata shakikai duk gasu Nan a gidan Suna jiran isowar Ango,ganin gidan a cike abokan Ango ko shiga gidan basuyi ba Suka tafi gida abinsu Ango rike da Hannun Iman ya kutsa Kai cikin part dinsa, gidane sama da kasa part biyu,Yana yin sallama kawayen Amarya Suka Fara shewa da guda,ganin Ango rike da wata tsaleliyar budurwa me Kama da shi sai suka Yi Shuru,Hanan da jawahir ne kadai Suka san Wace ce kusa da Ango Wanda Nan take suka Fara gulma suna bayani,Ganin fuskar Ango ba Rahma kowa suka tattara Suka bar gidan Baki daya,Kamla Amarya itace ta Bawa Yan aiki Umarni Kan su gyara Mata gida,Jin ance Ango yazo Bai nemeta ba sai kawai ta wuce bangaren sa.
Knocking tayi Masa Shuru lokacin Sallah yake Yi ta fada room din.

Mamaki ne ya kashe Kamla ganin Iman a gefen Gadon Nadeer tana zaune sai Wasa take faman Yi da yatsunta,Nadeer Yana kasa saman Sallaya Yana Adduoi.
Kamla kishi ne ya tokare Mata makoshi,ita tana Matarsa Amma wata shegiya ta Riga ta Shiga dakin Ango har saman bed din mijinta.






Yanzu za'a Fara








AsmaBaffa.
[11/4, 11:16 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ


FREE PAGE







11-15





Official






By
AsmaBaffa









ADDUAR KAWA NOVEL
SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨




SANARWA...

NA CANJA ACCOUNT NUMBER.





RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku ne 300


ADDUAR KAWA
Dari biyu 200 ne ga masu bukatar shiga Group.


Ga masu bukatar siya ta Bank ga Accnt number

0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gtbank.

Masu tura Katin mtn ta whatsApp, transfer ko Vtu ga number da zaku tura
08033933642.





Page naku ne

FANCY HONEY
RUKIEY MUAZ
AMYYNA MEENASH
MAMAN HIBBATULLAH
NABILAT ABUBAKAR
COOL LIFE H@WEE
DR MEENART.









Wani mahaukacin tsaki Kamla taja Wanda yayi sanadin dagowar Iman,Ganin Wata Bata santa ba sai kawai Iman ta saki Ihu ta buga uban tsalle ta koma Bayan Nadeer ta boye kanta tana ta ihu da kuka Bata son ganin kowa matukar ba Nadeer ba.
Tsaki Kamla taja sai Kuma ta sheke da dariya tana yiwa Iman kallon kaskanci ta Furta hmm yau Ni naga Yar iskar Mahaukaciya katuwar banza,miji ba naki ba shegiya mahaukaciya,Ido Iman ta tsurawa Kamla tana sake rirrike Nadeer,Ai na sanki Iman ai ke ko a lahira Kika ga me kyau sai kin makale masa,Indai kece mayyar masu kyau to a Kabari ma da Zaki ga me kyau to sai kin so shi Algungumar banza.

Mikewa tsaye Nadeer yayi Iman ta sake buya a bayansa tare da rike Masa Hannu,Ganin Haka Kamla tace ai Mijin ba naki bane munafukar mahaukaciya, zuwa tayi itama Kamla ta rike Daya Hannun Nadeer Suka sashi a tsakiya,Iman ta kwalla Kara,itama Kamla ta saki Kara Kamar an kunna Handdrier sai da Nadeer ya toshe kunnensa,Iman dawowa tayi a tsorace gaban Nadeer ta Rungume shi,Kamla kishi ya motsa itama ta saki hannunsa ta hada da Iman din da Nadeer ta Rungume Wai itama ta Rungume mijinta.
Tsawa ya dakawa Kamla, Iman tayi zaton da ita yake ta sake shi da sauri tare da matsawa baya,Kamla ma tuni taja baya,Iman ya kalla yace let's go,Yana gaba tana binsa a baya,Kamla itama ta rufa musu baya sai taga kwakwaf.

Room din Iman dake kusa da Nadeer yace shine na Iman,Kamla tace ai idan ta Isa Allah ya dau Raina ga room Dina ga naka itama sai a kawo ta sama,ai kamata yayi a barta a can kasa ita din banza,ke wace da Kika Isa Ni da gidana ki sa min doka? Ko kinzo da tsinke gidan Nan face kayan sawar ki? Ko nace Ina sonki? Na taba zuwa zance wajenki? Kwandala ta na taba kashe Miki? Kuma karki ce ban fada Miki ba wallahi ba Ni nasa a daura aure ba sabo da Haka ko room Dina karki sake na ganki again,abincinki karki sake kiyi Dani,Karki sake ki taba min Kayan Daya shafi part Dina,Mind ur fucking Business munafuka mayya kawai,tunaninki Aure na shine zai sa na soki? Kinyi kuskure har abada wallahi bazan soki ba.

Kamla cike da Fitsara tace ok haka kace? To zamu gani Ni Kuma sai kayi kuka a kaina sabo da so da kauna ta,Murmushin kasaita Nadeer ya saki yace maitarki baza ta ci Ni ba nafi karfinki,Ni Nadeer sai 'yar Zaman dakinsa,Kamla tace oh yanzu naje gano,Ki wuce Rano ma ba Gano Kika je ba cewar Nadeer.

mahaukaciyar Kwartuwa kake so kenan,waye Bai San karuwanci kuke Yi da Iman ba,Dama tunda kayi Mata aiki kaga Tsaraicinta muka San Dole a dinga lallabawa,saukar Maruka kawai Kamla taji a kumatunta hagu da damanta,Ihu ta saki tayi waje da gudu,Iman Ido ta rumtse tare da Sa Hannayenta ta toshe kunnenta tana Hawaye, fita yayi abinsa ko Iman din Bai kula ba ya koma room dinsa tare da Shirin bacci ya kwanta abinsa,har ya Fara bacci yaji bugun kofa bana hankali ba,Bude kofar yayi sai yaga Iman kanta a kasa ta Fara magana karatun zaka koya min,Kamla tana labe ta leko da kanta Baki bude Jin Iman tace Nadeer zai koya Mata karatu sai Kamla ta hangame Baki tare da Kara turo kunnenta tana saurara a hankali tace karatu cikin dare? Nadeer Bai San Kamla tana labe ba ya kalli kudu da Arewa sannan cikin zafin nama ya fisgo Hannun Iman wukil ta shige room dinsa ya banko kofa,ai Kamla sai ta barke da kuka a wajen taja kafarta tare da komawa bedroom dinta Daren farko na Amarya Bata Yi bacci ba Kuma Babu soyayya sai kuka.

Nadeer kuwa Iman ya lallaba ta Bari zai koya Mata karatun da safe harda Littafinta da Biro,Kamla tana Jin Karar Bude kofa ta leko da kanta a hankali ta kofarta sai taga Nadeer ne ya raka Iman Room dinta kuma Bai tsaya a waje ba ya Shiga har ciki suna dariya,Allah sarki shi Iman ce ta bashi dariya da Haukarta Kuma kawai light ya kashe Mata ya fito Amma Kamla zargi take Yi anyi wani Abu.
Yana Fitowa ta koma cikin room dinta ba tare Daya ganta ba.
Washe Gari da sanyin safiya Nadeer ya fito sanye cikin kayansa na Gym farin 3qtr da Riga Armless Fara yayi Masifar kyau ga pcap a kansa, Ganin zai fita Iman tana tsaye a Palo tana kallon cartoon zumbur ta mike tana murna sanye take cikin Arabian Gown black kanta ba dankwali ba ko digon kwalliya a hakan ma Sai tayi Masifar kyau.

Kamar Walkiya sai ga Kamla ta fito sanye da Gutun wando da kadan ya rufe Mata mazaunai zata birge miji, da wata Guntuwar Vest red and white ko gaisuwa Bata Furta ba tace Nima Zanyi Exercise din,kallonta Nadeer yayi Wata Yar lukuta da ita cinyarta duk nankarwa,Ko kula Kamla baiyi ba ya juya zai tafi yaji an rike Masa Hannu tunaninsa Kamla ce kawai Yana juyowa ya kwarfeta da uban Mari ihu da kukan Iman yaji Ashe ita ya Mara ita ce ta rike Masa Hannu,wata mahaukaciyar Dariya Kamla ta saki Hahahahaha hakki ne tukunna ma, Tsaki yaja ya juya zai tafi Iman ta sake fisgo hannunsa Yana sani ya wani taho ya fada jikinta kansa ya sauke a kirjin Iman ya wani kwantar da abinsa, Ahh...Kamla ta furta a fili da karfi, Nadeer yace tafiya zanyi ya juya again Iman ta sake riko Hannunsa ya sake fadowa jikinta wannan lokacin Kamla Baki Bude take Kallon Nadeer tana gani Yana lallaba Iman akan ta jira shi zai dawo, Yana fita Iman ta juya baya tana kallon Cartoon Kamla ta dakko wani Plate tare da kwadawa Iman a kanta da karfi,Kan Iman ya fashe Nan take jini ya shiga biyowa ta Kan Iman zuwa Fuskarta,Allah sarki Iman kawai bin Kamla take Yi da kallo ko jinin ma Bata kula da shi ba,kunnen Iman ta Kama ta furta shegiya munafuka wlh duk ranar Dana ganki a wajen Mijina in ya bar gidan Nan sai na kashe ki Mahaukaciyar banza ta hankada Iman ta Fadi a kasa,duk kukan Iman Bata Yi ba yanzu jini Yana ta zuba Amma tana a kwance kallonta takeyi a Tv tana dariyarta,Haka har Nadeer ya dawo ya hango Iman a kwance a kasa tana kallo,Tsallake ta yayi zai Haura sama da ruwan roba a hannunsa, Iman ta rike kafarsa tana daga kwance a kasa,Juyoya yayi Salati ya saki ganin jini ya Gama wankewa Iman fuska,Mamaki ya kamashi a Ina taji ciwo,Kamla ya Shiga kwalawa Kira Amma Taki Fitowa,Shareta yayi ya dakko first aid box,Iman binsa takeyi da kallo ganin yanda ya tsorata, Fuskarta ta shafo taga jini Baki ta bude tace Laaaaa Aboki shayi ne ke zubowa a Kaina, dariya da Tausayi ta bashi ganin ko a jikinta sai ma cewa da tayi shayi ne ke zuba a kanta.

Pls Iman talk to me waye ya fasa Miki Kai? Dariya tayi kawai ba abinda take ganewa,yasan ma Kamla ce a fili ya furta Zanyi maganinki ne, a Haka ya Mata Dressing ya Haura sama a gurguje ya dauki wankan sugar ya fito cikin Wata Shadda zai fita, Kamla ya kwalawa Kira ta fito sanye cikin 3qutr da Yar rigarta ko cibi Bata rufe ba, a matsayinki na Aminiyar Iman ki tafi da ita ki shirya ta Zan Kai ta asibiti cewar Nadeer ya Furta cike da Izza,Ayiriri nanaye Allah sittiri bukwui Inji kishiyar me doro Ni na shirya wannan mahaukaciyar Allah ya kiyaye,Lalura ce kema Baki fi karfinta ba idan har kina so na daga yau ki dinga Yiwa Iman komai idan har kina so na soki na nuna Miki kauna, kana nufin idan har Ina kula da ita zamu dinga kwana tare? Yeah na Miki Alkawari Amma sai Naga canji,an gama jira yanzu zaka ganta fes Amma kayi Mata magana karta ce zata dakeni ko tayi min ihunsu na Mahaukata,Kai kadai take kulawa Kai din ma mayya Dan taga kana da kyau ne,Alright Iman je wajen Wannan ta shiryaki ki barta zata Yi wanka da kanta ta iya Kaya kawai Zaki tayata sawa,sannan karki kallar Mata tsaraici kin San ba kyau ko ke mace ce Yar uwarta Bai kamata ba ehe,wlh Kika kallar Mata jiki sai kin Gane kurenki.
Baki Kamla ta tabe sannan tace ai gwara Ni Kai fa? Ka manta sanda ka gama kalle Mata kana Namiji sai ni zaka gargade Ni, Murmushi Nadeer yayi yace har kin tuna min da farin gani yau yini zanyi Ina hasko shi a kwakwalwa ta hakan kadai ya gamsar Dani ko na shekara dubu ba Aure iya wannan ya ishe Ni,Ran Kamla ne ya baci kishinsa ya taso Mata tace me ya Hana yanzu ka dinga shiryata da kanka? Ai kin San Zan iya,Hannun Iman ta Kama Kamla ta fisgi hannun muje Kuma wallahi Kika min ihu sai na ci Uwarki harda ubanki,Iman Bata San me ake Yi ba,rau rau tayi zata Yi kuka tana kallon Nadeer, da Hannu ya Mata Alama da Kar tayi kuka ta bi ta suje,Kuka ta fashe da shi tana waiwayen baya tana kallon Nadeer.

Sai da Kamla ta tabbatar sun shiga Bedroom ta samu Iman tare da Dirka Mata duka a gadon bayanta,Ba ruwanta da raunin da take da shi a Kai Haka Kamla taja gashinta da karfi sannan ta samu ta falle ta da Mari tana Ni Zan Miki bauta shegiya mayya,watarana nice ajalinki sai na kashe ki Mahaukaciyar banza hannu ta daga zata sake dukan Iman Nadeer ya yayi gyaran murya,A rude Kamla ta juyo ta ganshi a jikin kofa ya harde Hannayensa a kirjinsa da Alama ya Dade da shigowa dama Yana binsu a baya yaga komai a idonsa ya faru,Da gudu Iman ta

Please Login or Register in order to submit comment