Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kaita can din,Ka tabbatar me kyau ne Hospital din? Abba ya tambaya,Sosai ma Abban Nadeer Yana da kyau na San asibitin cewar Mama.
Ok ba komai sai muje a kaita.
Umma da Nadeer ne Suka Shiga Room din Iman Sunyi sa'a ta farka ta tsurawa tafin Hannunta Ido tana ta kallo Kamar zata dakko Abu a ciki,Sosawa ta Shiga Yi tana dukansa tana cewa ka fita baza ka fita ba ko sai na mareka,Nadeer da kyar ya daure saura kadan Hawaye ya zubo Masa,Umma kuwa kukanta kawai take Yi,a gabanta Nadeer ya tsuguna Hannun ya kalla Yana Murmushi ya kalli Fuskarta yace Iman Mene a ciki? Miciji ne gashi Nan a ciki,Yana dubawa sai yaga tsagun tafin Hannunta ne Wai miciji ne,Murmushi Yayi ta tsura Masa Ido tana ta kallonsa Kamar ta sanshi , Iman...Kai Ni ba sunana Iman ba ta furta cike da Shagwaba Ni,Alright to ya sunanki? Da sauri ta bashi amsa Jaka,Ni jaka sunana ok to tashi muje Unguwa Zaki je? Kai ta daga Masa ta mike da sauri sai taga su Umma Nan take ta saki Ihu da karaji ba shiri Suka Yi waje da sauri.
Nadeer Hannunta ya rike tare da yafa Mata mayafi ta cire tayi cilli da shi,Sai ya kyaleta kawai ya jata tare da Sa ta a bayan mota shima baya ya Shiga Driver ya jasu zuwa Hospital din da za a canjawa Iman,su Umma motocinsu suna bayan ta Nadeer har Asibitin Suka Isa Suma.

Already Nadeer ya Gama komai dama kawai Room Suka bawa Iman Ita Daya sabo da Nadeer ya kashe kudi komai na Iman na daban za ayi Mata har masu kula da ita,Iman suna shiga Room din ta Fara tsalle da murna tace Kai Zan ji Dadi,Laaaaa Harda Hoton Biri,wannan ai Aboki na ne tun Ina yarinya ko baka sanshi ba ne? Dariya ta Kama Nadeer domin hoton shugaban Hospital din ne ta gani shine tace Biri ne,katuwar plasma ya kunna Mata ta Fara kallo ganin Cartoon movie tace tsaya a Nan ai nasan wannan garin,sai Kuma ta Fara Hawaye Wai Tausayi cartoon suke Bata,Nadeer yace to Bari na kashe tunda kuka zakiyi,dariya ta saki tace na daina.

Mikewa Yayi zai tafi da gudu ta shako wuyansa ta baya ta daka Uban tsalle ta haye Bayan Nadeer,ya zaka tafi Ina zaka je? Ba Nan bane gidan mu? Yanzu Zan dawo Abinci Zan kawo Miki,To kayi sauri,to sauka a bayana,a Haka zamuje Mana,Murmushi yayi ya kaita saman Bed ya kwantar da ita karki tashi sai na dawo idan Kika tashi a Nan idan na dawo sai na zaneki,Kai ta daga Masa alamar to,yace to yi bacci,da sauri ta rufe idonta tace nayi baccin ka gani ko? ae na gani,a hankali ya bar dakin Suka sake magana da Doctors sannan ya lallashi su Umma Suka tafi gida gaba dayansu har Nadeer.

Ko da Nadeer ya koma gida,Abinci yaci yayi wanka tare da kwanciya bacci bayan yayi Sallar Isha,Gaba Daya Iman Yake tunawa musamman yanda ta kwanta mishi a baya,da kyar yaja tsaki tare da kautar da tunanin Bacci ya kwashe shi,Sai 9am ya tashi,wanka ya shiga ya Dade kafin ya fito ya shirya cikin Wani yard me azabar kyau da tsada shara shara fari,Ba karamin kyau yayi ba ga dinkin dai dai jikinsa kamar a jikinsa aka dinga ,Sumar Nan tana shining ya fito Dining ya wuce kawai ya cika cikinsa sannan ya je Suka gaisa da Mama,Abba Yana zaune a gefen Gadon Mama yace Nadeer ya kamata ka tafi ka gano mana yarinyar Nan Duk na Hana kowa zuwa tunda kuka sukeyi sai sati sati zasu dinga ganinta,Kai ka dinga zuwa Kullum kana dubata,Hakan ma yayi Abba,Bari Naje yau bazan je Aiki ba,Uhm Haka ka Iya Dama burinka kaki zuwa aiki,da badan Iman na cuta ba ai Hospital baza ma su ganka ba,Dariya sukayi gaba Daya,Abba yace to me zuwa Yi maka Zance wajen budurwa ta kwanta rashin lafiya yanzu ya za ayi kenan? Murmushi Nadeer yayi yace Abba sharri tayi min dama Yana Fadin Haka ya fita abinsa zuwa Wajen Umma Suka gaisa harda Baba,Umma tace ya za ayi da abincin Iman? Zasu Bata a can,a'a Ni dai a Kai Mata taci nawa tafi Jin Dadi Amma abincin Hospital wani Dadi zaiyi,Ba musu Nadeer yace kawo Umma tunda so kike Dole sai taci naki,a basket ta hada Masa komai Driver ya dauka tare da Sawa a motar Nadeer, Umma yayiwa Sallama ya tafi,kafin ya fito Har Driver ya Gyara mota kawai hakimcewa yayi a baya cikin sabuwar motarsa Fara tas.

Yana Shiga ciki Wani Likita ya tare shi Suka gaisa yace Doctor Nadeer patient dinka tun jiya daka tafi Taki tashi tana Nan a kwance Wai tace kawanta ne yace ta kwanta karta tashi sai ya dawo,munyi munyi ko Zama tayi taki yarda tace ma Baccinta takeyi ita,Muna zuwa tashinta zata saki karaji tace a fita bacci takeyi.
Dariya Nadeer yayi yace Allah me iko wayo fa nayi Mata yanzu ko fitsari Bata Yi ba? Taki tashi ko zaune tun jiya a Haka take.

Room din Suka shiga, Jin motsin mutum Iman da sauri ta juyo tana ganin Nadeer sai ta rufe idonta tace Ina ta baccina ka ganni? Tausayi ta bashi yace to bakiyi ko fitsari ba? Kai ta daga Masa tace ai kace Kar na tashi,Ok to tashi kije kiyi wanka da Brush ai kin tuna yanda na koya Miki ko? Kai ta daga Masa irin ta Gane din Nan,Toilet din wani clean Yana sheki ya bude Mata tasa slifas ta shiga ya rufe Mata kofar ta Bude tace tsoro nake ji ka barta a bude kana kallo na Ina kallon ka,Harara ya watsa Mata sai ko ta kyalkyale da dariya tace idonka irin na Dan dodo,Toilet din ya rufe Karo na biyu ta sake budewa tana kokarin tube kayanta ya daka Mata tsawa,Idan Kika tube Allah sai na mareki dakikiya Ina Wasa da ke?

Ko wani ya shigo karki sake kice Zaki cire kayanki kinji ko? to ta furta a sanyaye sai Kuma ta fashe da kuka Toilet din ya rufe Mata yace kiyi sauri Kuma kin tuna abinda na koya Miki ko? Tana daga ciki tace Uhm...kamar me hankali yanda ya koya Mata komai Haka tayi ta fito,Zanin Atamfar nata ta dauro ta fito da daura kirjinta,Kayan data cire suna Hannunta gabansa tazo ta tsaya, yace Oya Haaa muga Hakoran naki? Tace Uhm Mene Hakori? Your Teeth ya nuna Mata nasa tace ohh Injin nika zaka ce min ko Injin markade sai na Gane ta bude Masa Hakoran harda zaro Masa Harshenta tace yasha wanki Kamar Zan cire shi saura kadan har jini yayi,Aiko yaga duk taji rauni a dasashinta,Haka na koya Miki? Kuka Ta saki tare da furta to Ni ban iya ba.

Haka na koya Miki? Ya furta Yana kallonta Fada ya Fara Mata ta saki Kara tare da toshe kunnenta tana maganganu ita daya tana bazan ji ba yeeeeeeeeee....yiiiiii....Shuru yayi sannan itama tayi Shuru,Zo muga gashin ko ya fita kanta ta turo Masa ya Buda gashin kadan yaga ya fita Yana kamshi yace shike nan,Busar da gashin yanzu,Iska ta Fara hurowa da bakinta Kamar tana hura Abinci Huuuuuuuuuuuuu Wai a Haka gashin zai bushe.
Oh Allah Nadeer ya furta tare da Dora Mata towel Karami a kanta ya Fara goge Mata gashin Yana tsane Mata yace Haka zakiyi kin tuna?

Kallonsa tayi Ido cikin Ido Wanda sanda tana lafiya Bata iya kallonsa,Idonsa ya janye daga gareta,ita kuwa gashin kanta take dirzawa da Towel kamar zata cire kanta,Mai ya Mika Mata ta shafa a kafafu da Hannu, tana ta faman dariya ita kadai,doguwar Rigar Atamfa ya Bata ta sa ba ko Bra, Mikewa yayi da kansa ya zabo Mata Bra cikin kayanta ya Mika Mata tare da cewa cire rigar ki Fara sa wannan, kallonsa ta tsaya Yi kawai.

Fisgar Bra din tayi tare da yin jifa da ita tana dariya,Tsaki yaja ya daka Mata tsawa tare da cilla mata towel,ta Gane me yake nufi Towel din ta daura sannan ta cire rigar da ta sa tayi jifa da ita Wai taji Haushi, Umarni ya Bata Kan ta juya bayanta,Juyawa tayi sai faman tsalle tsalle take Yi,sama ya daga kansa Yana rufe Ido ya Sa Mata bra akan Towel din Dake jikinta,sannan ya rufe Ido sosai ya zare towel din,shi ba abin ya gyara Mata ba,idonsa a rufe ya Sa hannu Yana lalube a duhu Wai zai gyara mata,garin laluba Hannu ya Dora a saman kirjinta,wani laushi yaji da sauri ya janye hannunsa kamar ya taba wuta,Ihu Iman ta saki ta Shiga kwala Kara me karfi,da sauri idonsa Yana farfari shi Bai Bude ba Bai Kuma rufe ba ya Bata rigarta ta saka abarta bra a karkace Boobs Daya a cikin bra Daya Bai Shiga ba,Koda ya bude idonsa dariya abin ya bashi sai ya danne ya kyaleta haka kawai,Abincin Umma ya zuba Mata a plate ta karba Kamar wata karya bakinta ta dumbula a plate din kawai ta ci tayi dama dama da fuskarta,Dole ya kaita toilet tare da wanke Mata fuska sannan Suka fito,Zama tayi gefen bed dinta tana kallon cartoon dinta tana Hawaye Wai Tausayi,Why are you crying? Ya tambayeta kamar me hankali tana shesheka tace abin...abin...Tausayi...ga Kawanta ya daina kulata,Ba kawanta bane fa Yayanta ne yace ta raka shi yawo shine Zaki ce kawanta ya daina kulata bakya ganewa Iman cewar Nadeer.

Dariya ta kyalkyale Masa da ita kawai ya tsaya Yana kallonta yanda tayi Masifar kyau,Tagumi ya zuba kawai Yana kallonta kamar Tv sai Tsalle takeyi tana dariya tana Wasa da tsokali,Ba zato ta kwada Masa Cokali a goshinsa da karfi,Da sauri ya dafe wajen jini na fita, A fusace ya kalleta sai yaga dariya ma take Masa,tissue yasa ya danne Dan wajen da ya fashe Allah yasa kadan ne, Mikewa yayi zai bar asibitin Baki daya,da gudu ta riko Hannunsa,ya fisge yayi waje abinsa, da gudun tsiya Iman ta bishi tana uban kuka har jikin motarsa ta Kama rirrike shi ta ko Ina Wai bazai tafi ba,Doctor ya kira ya sanarwa sai ga Nurse tazo Nan take ta tsirawa Iman wata Allura jikinta ya saki ya Zama so Weak Nan ta Fadi ragwaf a kasa sai wasu ne suka Zo tare da dauketa suka maidata room dinta, Nadeer kuwa cike da Tausayawa ga bakin ciki ta fasa Masa goshi Yana zamansa lafiya ya bar Hospital din zuwa gida.

Yana zuwa Umma ya maidawa kwanikanta ta kalli goshinsa an manna plaster,Me ya sameka Nadeer? Hmmm yayi Murmushi kadan yace Umma Yarki ce Iman,Baki Umma ta Bude tace oh Allah dai ya Bata lafiya sai hakuri kaci gaba da hakuri kaji Nadeer, ba komai Umma yayi waje abinsa.

Washe Gari Nadeer Yana gaban Abba da Baba sun neme shi,Suna saman kujera Yana kasa Abba yayi gyaran murya yace Nadeer na tura an tambayo maka Auren kawar Iman Wato Kamla, munyi magana da iyayenta Kan zaka Aureta ka dauki Iman ku zauna tare a gidan tunda kawai Iman ce suna kaunar juna,Kuma Bincike ya nuna Iman tana so ka aure yarinyar tace kana zuwa zance ma Kun Gama daidaitawa, Maman Kamla ma tayi Mana godiya yanda kake kula da 'Yarta kana musu Abubuwa na kyautatawa, Kuma Kamla tayi Mana Alkawari cewar zata rike Iman da Amana tunda Iman Bata yarda da kowa,munyi tunanin aura maka Iman sai Muka fasa sabo da Idan munyi Haka mun zalunceku,Iman Bata da Lafiya,Kai Kuma idan Muka baka Iman mun zalunce ka a halin da kake ciki,shi yasa Muka je da kanmu da yawun Mamanka da Umma zaka auri Kamla Dole tunda tana sonka kana sonta zaku Rike Iman kasancewar Bata so Kowa ya rabe ta sai Kai,asibiti ba abinda suke Mata bamu ga amfanin zamanta a asibitin Mahaukata ba.

Tunda Abba ya Fara magana Nadeer Hankalinsa ya tashi,a nutse yace Abba Ni wlh ba son Kamla nake ba,hasali ma na tsaneta Babu wacce na tsana a duniya irin ta,wlh ko Kun aura min ita sai dai tayi zaman kunci,Dan bazan iya rayuwar aure da ita ba,akan Haka ai gwara ku Aura min Iman kawai Amma wata banza Kamla wallahi Ni karya take min ban taba zuwa inda take ba,ko gaisawa bama Yi da ita,Tsawa Abba ya daka Masa to baza a aura maka Iman ba sabo da Idan ta warke Bata kaunar ka fa? Ni nasan zata so ni ma,ubanka Kai Ana magana kana magana cewar Baba,Shuru Nadeer yayi zuciyarsa kamar zata fashe,Abba yace Kai ka daina batawa kanka lokaci yaro mun rigada mun Kai kudin aure ansa Rana Nan da sati Biyu bikinka kaje kayi shiri mun Gama shirya komai,Mikewa Nadeer yayi tsaye yace to tunda Haka ne a hada na aure su gaba Daya su biyun Mana dama Iman Muharrami take bukata me kula da ita Wanda zai Mata komai,Abba Ni ba mijinta bane ai bani da ikon Yi Mata komai Amma Abba Kana gani yau Dana je Bra ma kasa sa Mata nayi da matata ce fa Bai sai na sa Mata abarta ba,Baki Abba ya bude ya Suri Wani agogonsa ya jefi Nadeer da shi kaga fitsararre marar mutunci abinda ka koya kenan a turai? Kai ba Dan Uwanta bane? Kuma ga Mata Nan baza ka Nemo ba su kula da ita,Kasan Bata yarda da kowa,to ai lalura ce sai ka taimaka Mata Lada zaka samu.

Nadeer Yana daga bakin kofa yace Haba Abba Kuna fa da Ilmi Ni ai ba muharraminta bane ko Raees Bai Dace ya kula da Iman ba bare Kuma ni, Ni wlh dama Bata yadda Dani gaba Daya Nima kowa ya huta,Amma ace Abba Kun kasa fahimtata,Kamla wlh baza ta kula da Iman ba,karku Yi kuskuren da zaku yi Dana sani,Zaka ci Ubanka wallahi Nadeer Ana magana kana magana Cewar Mama,Shike Nan na yarda ayi duk yanda kike so Amma duk abinda ya faru karkuyi kuka Dani,sannan Kuma Nan gaba ko kunce na Auri Iman bazan aure ta ba tunda na Fadi gaskiya Anki ji,Nima ai Taimako zanyi ba sonta nake Yi ba Amma har za a ce idan ta warke zata ce Bata so na,Ni bance bana sonta ba sai Iman ce zata Bata so na? Shike Nan Ni dama Taimako zanyi amma
Ki duba Mama wace ta Isa tace bata so na Hadadden Handsome iri na,ga kyau na larabawa,ga sura,ga class,ga Ilmi,ga Naira,ga hankali, ai wlh Ni ya kamata nayi yanga ba Dan nace a aura min Iman za ace wani za a cuceta ba,za a cuceta ko za a cuceni Ni Idan na aure ta.
Abba cikin Salama yace Nadeer zabi kasar da kake son tafiya Honey moon,Dama kana son Zama a kasar waje ka zabi ko wacce kasa ku tafi da Amarya da Iman,burina ka kular min da Iman.

Nadeer Yana uban fushi ya Furta idan ba Ni ba waye a yanzu ake Kai Masa 'yar zaman daki,yarinya kursumemiya irin Iman ace da ita za a tare ba Aure ba komai nace a Aura min ita Anki Ana Zancen Na tafi dasu Honey moon,Dan Allah Mama wanne Honey moon za ayi da 'yar zaman daki gansamemiya a kusa,Ko a jahiliyya period da ake tura Yar zaman daki ai tarihi ya nuna yarinya ake bayarwa Yar 7 to 9years Amma Ni ace Yar 19-20yrs,Dariya Nadeer ya bawa su Abba gaba Daya,Baba yace Look Nadeer ai Iman ba zaman daki taje ba,Bata da hankali,a halin yanzu ai Yar 2yrs ma tafi Iman Hankali so ba Yar zaman daki bace patient dinka ce Doctor.

Kuyi Hakuri Abba na yarda kuyi duk yanda kuke so Amma wlh Kamla room dinta ma bazan shiga ba,Kai Allah zai Kama da Rashin bawa Matarka Hakkinta cewar Abba ya Furta cikin fada,Nadeer yace Ni nace a aura min ita Ni wlh ba ruwana yayi waje Fuuuuuu ya bar gidan gaba Daya.
Da mamaki su Abba suka kalli juna,Yaushe Nadeer din namu ya lalace Haka? Shi yasa na fada maka Yaya Kar a kaishi turai karatu to yanzu ga Abinda ya koya fito na fito da Iyayensa.

Nadeer Bai zarce ko Ina ba sai gidan su Sameer,a palon Sameer ya kwanta Yana ta mita,Sameer Yana taya abokinsa bacin Rai,Sameer yace abokina yanzu da wannan Banzar Kamla ai gwara Iman Mara hankali,yanzu da ace ka samu Iman ai lafiya Lau ko ya kace mutumina? Zanci uwarka karka Bata min Rai,itama an fada maka sonta nakeyi kawai ban son tana taba min jiki Ni ba muharraminta ba,idan da aure ko ta taba Ni kaga ba matsala,dariya Sameer ya Shiga Yi yace shike Nan to ka hakura Haka idan ta taba ka kaji wani Abu sai ka koma wajen Kamla Amarya ka kwashi gara,Ashar Nadeer ya durawa Sameer tare da Mikewa ya bar gidan gaba Daya a cikin fushi.









AsmaBaffa
[11/4, 11:16 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ

FREE PAGE







6-10





Official






By
AsmaBaffa








ADDU'AR KAWA NOVEL
SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨








SANARWA...
NA CANJA ACCOUNT NUMBER.






RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku 300 ne


ADDU'AR KAWA
Ga masu bukatat Shiga group dinsa Dari biyu 200 ne.

Masu Bukatar siye ta Bank ga Accnt number

Accnt number
0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gtbank.

Ga masu son tura katin MTN ta whatsApp, Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
08033933642.



Bana ganin Sharhi.






Page naku ne

HUMAIRA MK
MAMAN HUMAIRA&IKRAM
RUKY MUAZ
-M
FATIMA
MARYAM HAMZA
SU..SY
UMMI










Tunda Nadeer ya fita sai dare sannan ya dawo gida abinsa,kwanan Iman Biyar a Hospital Bata ga Nadeer ba sai su Umma da suke zuwa,idan sunje ma Ihu da karaji zata dinga Yi baza ta taba Shuru ba sai sun tafi,hakan yasa basa iya ko rabar Iman sabo da har jifansu takeyi Umma sai dai kuka,Su Abba ma sunje sosai Amma Iman Nadeer kawai take nema, har Fitowa takeyi compound na Hospital tayi ta faman duba Nadeer ko Allah zai sa ta ganshi Amma shuru.
Ko wanne Maaikaci ta gani sai ta Fara cewa Kawana....Kawana....sai da Iman ta cika sati Daya Bata ga Nadeer ba,yau Saturday yaji yayi missing shirmen Iman da yamma ya dauki wanka cikin 3qtr fari da Riga me tsada ruwan kasa yayi mugun kyau,Wata sabuwar motarsa baka ya shiga zuwa Hospital din da Iman ta ke.

Yana parking ya hango ta a jikin windown room dinta tana ta kallon bakin gate,Yana Fitowa a motar sukayi Ido biyu da Iman,Bata Gane shi ba a hankali ya tura kofar tare da shiga room din,Kin juyowa tayi sabo da tasan ba shi bane Likita ne, kafadarta ya dafa,Baki ta turo gaba taci gaba kallon Window,Muryarsa taji yayi Sallama,da mugun sauri ta juyo taga shine da gaske ai sai ta Fadi a kasa tana birgima da kuka Wai duk murna ce,dariya yayi ta mike ta fada Kirjinsa ta kankame shi ta ko Ina,Shuru sukayi Babu Wanda yayi motsi sai a hankali Iman ta zare jikinta,Da karfi tace Dan Allah tambayarka zanyi? Ina jinki ya Furta da nutsuwa a Dole zai ji zance, Shuru tayi tana kallonsa sannan tace Wai a Ambulance nazo gidan ko a Keke? Shuru ya Mata tace to a machine? Ko Taxi ce?

Ganin yau ba yanda ta Saba ganinsa ba tayi Shuru ta juya ta koma gefen Bed dinta ta zauna,Biro da Wani littafi ya mika Mata,karba tayi tace Mene ne wannan? Rubutu akeyi karatu Zaki dinga Yi Muna karatu,jefar da littafin tayi tana Ahhhhhhhhh.........Ni...Ni.....bana so...Mene Kuma rubutu? Tunda tayi Haka yasan baza tayi ba,Ok...tunda bakya so shike Nan,bani labari to Ina jinki,Mene labari kuma? a hankali yace ya sunana? Kawana Mana sunanka,Na gaskiya fa? Ni dai ban iya ba ta furta tare da daura kanta a kafadarsa tayi Shuru,Yace to Ni Bari na Baki labari.
Yawwa Ina jinka ta furta Kamar me hankali,Auren dole za ayi min, Mene Aure Kuma? Wata kawata za'a bani zamu zauna gida Daya,Dariya Iman ta kyalkyale da ita tace naji Dadi itama Zaka na Bata labari? Kai ya daga Mata yace bacci ma tare zamu Yi da ita a bed irin wannan zamu na kwana,Baki ta bude sannan ta makale kafada tasa yatsu tare da toshe kunnenta tana Kara Ahhhh....Ahhhhhhhhh Wai baza taji ba,Dariya yayi sosai tace to Ni ya baka kwana a nan? Ai ke ba matata bace Kawata ce ko? Ohhhh da Mata ake kwana? Kai ya daga Mata,Ni Kuma ka daina kulani? No tare zamu koma da ke da matata zamu zauna,Murna Iman ta Fara taci gaba da cewa Bana son matar ka ni, ai Dole ki zauna da ita,Waye zai baka Mata? Babana? Waye Baba? Ni Ina nawa Baban? Allah yasa a baka matar to.

Ganin Bata Gane komai kawai yayi Mata Shuru bayanshi ta koma Yana zaune ta koma Bayan shi ta kwanta a Bed dinta ta lumshe Ido sai bacci ya kwashe ta,Bai San tayi bacci,sai nishinta yaji tana kuka sannan sai wani karkarwa take Yi alamar mafarki takeyi me ban tsoro gaba Daya ta hada zufa ta ko Ina.

Yana zaune gefen Gadon Da sauri ya juya yaga Halin data ke ciki, a hankali ya Sa Hannunsa cikin Nata,A firgice ta farka ta Fara kuka jikin ta Yana rawa, tana tsakiyar bed din a zaune ya Rungumeta a Kirjinsa,Yana shafa gashin kanta a hankali,Ido ta lumshe suna a Haka Suka dauki lokaci me tsawo sannan ta dawo cikin nutsuwarta , Zame jikinsa yayi a hankali Yana Jin wani iri jikinsa ya Zama so Weak kwanciya yayi a saman bed din,Itama komawa tayi ta kwanta a gefensa tare da daukan kafarta Daya ta daura Masa a jikinsa dariya ta bashi ya murmusa kadan.

Tunani ya tafi akan Auren da za ayi Masa da Kamla me kambun baka cewar Nadeer Kamla kambum baka ne da ita,ita ce tace Iman zata haukace gashi ta tabbata, Iman Tana gani ya tafi tunani ta kafe shi da idanu tana ganin tsananin Kyawun Nadeer ita Bata San Mene kyau ba Amma sai ta ji kawai tana sonsa shi kadai take iya samun nutsuwa idan ta ganshi, sun Dade a Haka sannan ya mike da niyyar tafiya,Kuka ta fashe Masa da shi tare da rike Hannun sa Wai bazai tafi ba,ganin kuka takeyi sosai sai ya rike Hannunta suka fita ya zaga da ita Compound din Hospital din ko Ina har garden ya kaita Yana rike da Hannunta suna tafiya,ita dai binshi kawai takeyi Bata Gane komai.

Hadari ya Gama Hadawa sosai Ruwa daf yake da tsugewa,Ganin Hakan Nadeer yace Let's go ga ruwa Nan za ayi I need to go home,Kafada ta makale tana turo lips,Ido ya tsura mata kafin kace me ruwa ya kece me karfin gaske,Iman Dariya ta Shiga kyalkyalawa tana faman tsalle ruwa ya yazo,Bakinta ta hangame tare da daga Kai sama Wai zata Sha ruwan saman,gashinta ya jike sosai yayi Mata yaraf a gadon baya dama Taki yarda ta daura dankwali, kayan dake jikinta Doguwar Rigar Material ce readymade ruwan da ya jikata yasa ta manne a jikinta surarta ta bayyana sosai gashi Babu Bra a jikinta,Kallo Daya Nadeer yayi Mata ya dauke kansa,da sauri ya juya zai bar wajen kenan ta tafi da gudu tare da Rungume shi ta baya Wai bazai tafi ba.

Wani Yarrrrr yaji a jikinsa Wanda yayi sanadin tashin hankalinsa,da sauri ya zare jikinsa tare da fisgar hannunta ya jata tana cijewa ita baza ta tafi ba,Wanka...wanka...kawai take cewa.

Ganin zata wahalar dashi kawai ya dauke ta Kamar jaririya har zuwa Dakinta sannan yace ki canja Kaya ga Abinci Nan kici please and please Kar ki Bata bakinki, Ina zaka je? Ta

Please Login or Register in order to submit comment