Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da aure ba Wasa,Wani farin ciki ne ya mamaye Zuciyar Kamla, na farko ta samu miji Mafi tsadar samu a duniya ba ko wacce mace zata ga Nadeer Bata so kasancewa tare da shi ba,na Biyu ta samu hanyar Kuntatawa Iman,domin yanzu Bata da makiyya sama da Iman,Bata kaunar Iman ko kadan,Kamla Murmushi ta saki tare da Furta Allah dai ya zaba mafi Alkhairinsa,Iman ta wani fannin tana so ta hada Kamla da Nadeer sabo da ta kankare laifinta da ta yiwa Kamla,a hankali Iman tace sai Munzo zance,Allah ya kawo ku lfy cewar Kamla.

Bayan sun Gama wayar Iman kanta a kasa tace Ya Nadeer Kamla ta Amince yaushe zamu je Zancen? Dariya ta bawa Nadeer daga Wasa Amma sai yace ke Zaki dinga zuwa min kafin naje da kaina idan kin warke, Alright Iman ta furta Zuciyarta ba Dadi.
A hankali tace Me kake ganin zanyiwa Hanan Da Jawahir Suma na goge laifina a wajensu,Khadija Yar uwata ce Bata rike Ni da komai,Ban sani ba Ni nace kije ki kwace musu saurayi cewar Nadeer.
Shuru Iman tayi tana tunani a ranta har ta samu amsa, a fili Kuma tace to Wai Ni Ina ruwana kyansu ne ya ja musu, hakan kuwa ta Fara kyautatawa Hanan da Jawahir ta hanyar Tura musu kudi a accnt kyauta,Farko dubu ashirin ashirin ta Basu,ta Basu 30k, 15k, sai ta karbi kudi wurin Abban Nadeer ta turawa su Jawahir Amma ko sun gani ko godiya Basu taba yiwa Iman ba.

Satin Iman Biyu ta warke sosai tana Hospital ta wani Kara ja da Yar kiba tayi kyau, Wanka tayi ta shirya cikin Arabian Gown Black,ta rolling mayafinta Baki,tasa takalmi fari tare da jaka Fara duk Umma ta sa ta kawo Mata kayan, Driver tasa ya fita da ita daga Hospital din ganin ba kowa a wajenta,su Umma sun tafi gida sai date zata dare zasu dawo, tafiya tayi zuwa gidan su Kamla zance zata yiwa Ya Nadeer, Fitarta ke da wuya Nadeer ya shigo dubata ya iske Ba kowa,Umma ya Kira tace ta fada min ta tafi gidan Kawarta,Haba Umma Bata fa Gama warkewa ba zaku Bari ta fita,ya zaku Bata Mana aiki,Idan wani Abu ya faru fa,Bari ta dawo sai ayi Mata fada.

Ran Nadeer ya baci Bayan ya kashe wayar a fusace ya Furta jiki magayi wlh bazan kirata a waya ba,taje duk inda zata je,Kuma wani Abu ya faru ba ruwana,Iman kuwa a gidan Kawarta Kamla Driver yayi parking,Har katafaren Palon gidan Iman ta shiga,Suka gaisa da Maman Kamla sannan Maman Kamla tace Kamla tana ciki dakinta,Sama Iman ta Haura har Bedroom din Kamla,Kamla ganin Iman ce da kyar ma ta iya amsa sallama ko wurin Zama Bata bawa Iman ba,Gefen bed kusa da Kamla ta zauna sannan cike da fara'a Iman tace Kamla Naga Kamar har yanzu laifin danayi Baki yafe min ba? Kiyi hakuri ga Yayana zai maye Gurbi Kuma kin San Yafi Ibaad komai,Baki Kamla ta tabe sannan tace na hakura Mana ya kike so nayi Dake ko goyaki kike so nayi, Hmm to Wlh Ya Nadeer yace kinyi Masa Yana sonki Kuma da aure ya kike gani? Yace zaizo da kansa zance Amma na Fara sanar Dake muyi magana abinda Kika ce na sanar Masa,Kamla tana murna tace ai nace na Amince,sai ya Fara zuwa da kansa,Murmushi Iman tayi tare da Furta na goge laifi na ko? Kai kawai Kamla ta daga Mata tana wani yatsina fuska tana yiwa Iman kallon Banza,Daga Nan Iman ta Fara Bawa Kamla labarin kyawawan halayen Nadeer har kusan Magrib sannan tayi Mata sallama,Kamla ko Rakiya Babu haka Iman ta wuce gidan su Hanan Suka gaisa taje Wajen Jawahir ma sannan tasa Driver ya maida ta Hospital.

Tana shiga room dinta ta Iske Abban Nadeer,Babanta,Nadeer,Umma da Mama sai Khadija suna jiranta,Gaban Iman ya yanke ya Fadi,a tsawace Abba yace Ina Kika tafi Dan Ubanki? Mahaukaciyar Ina ce ke kina asibiti Zaki tafi yawo You are very stupid, Iman Rau rau tayi kamar zata Yi kuka tace Abba Ya Nadeer ne ya aike Ni naje Masa zance zaiyi aure kwana Nan kawata yake so,Kowa a cikinsu sai farin ciki ya Kama su Kuma,Dama suna so suji Nadeer ko budurwa yace Yana so,suna so yayi aure,Masha Allah cewar Abba cikin kawayen naki wace ce? Abba sunanta Kamla Yar Gidan Minister sani Yaka, Ah to idan Haka ne ai Alhmdllh na sanshi mutumin kirki ne muna harka sosai Allah ya nuna Mana lokacin,Nadeer Ransa yayi mugun baci shi daga Wasa yarinya ta hada Masa bala'i Lallai sai yaci uban Iman Yau Bari su Umma su tafi.

Shanye bacin Ransa yayi yace Umma ku koma gida gaba Daya kawai Zan kula da Iman ai taji sauki,Tunda tana tayaka Neman aure ai Dole kace Haka ja'iri cewar Baban Iman,Gaba Daya tafiya Suka Yi gida ya rage daga Nadeer sai Iman.

Iman tana tsaye ta saci kallon Nadeer taga ransa a bace idonsa yayi jajir,Magana ta bude Baki zata furta Nadeer ya Sa Hannu ya damki Wuyanta ya Mata zazzafa damka a wuya,yayin da Iman ta Fara kakarin wahala idonta ya firfirto cak ya daga ta sama ta Wuyanta Da ya Rika,Sai da ya tabbatar tasha wahala ya sake ta fada saman bed din, tana tsoron zata Yi Rauni ta riko Hannun Nadeer ta jawo shi ba zata ya kifo kanta Gaba Daya kirjin sa yana saman na Iman,Bakinsa a saitin nata,Wani Yarrrrr suke ji a tare,da Sauri Iman ta lumshe Idanunta baza ta iya shanye kallon da yake Mata ba.

wani Abu taji Kamar Yana janta kawai a ranta ta shirya Shan duka tace bari kafin Kamla taji kalarsa na rigata,ba zato ta daura Lips dinta a saman na Nadeer ta bashi Wani Yuuuut da sauri ya lumshe Ido ya waresu jajir a Idon Iman,Ihu ta tsala tasan yau sai ya duketa da gudu ta zabura tare da mikewa zata kwashe da gudu,cikin zafin nama ya fisgo rigarta ya jawo ta baya cike da hasala ya shiga Zabgawa Iman Mari ta ko Ina,Wayar charger ya fisgo,Iman ta mike a tamanin ta afka Toilet kafin ta rufe kofar ya Sa Hannu ya fito da ita Yana furta How Dear you ya Fara tsula Mata Wire,Iman ta saki kuka tana Dan Allah kayi hakuri Ya Nadeer wlh tsautsayi ne bazan sake ba,shedan ne ya nuna min wata Flower a bakinka,Ni Flower na gani ba Lips dinka ba,Okay Flower ko? Nadeer ya tambayeta Yana Huci,gaba Daya ta gigice tace Ahm...am...ah...Awara da kwai na gani bakinka ya koma,Awara ce Tasha kwai shine ta birgeni ban sani ba Ashe lips dinka ne, Allah Ni Awara nake gani gata Nan har yanzu shedan ita yake nuna min bakinka ya koma ita,wani bacin Rai ya tasowa Nadeer tace Bakinsa me Kamar Awara, shine na gwada cinye ta nayi maka da Wasa wallahi bazan sake ba, Nadeer yace Awara ne lips Dina ko? Da sauri Iman tace Ae Tasha yaji ma kuwa,Gashin kanta yaja ta saki Ihu.

Jin Ana ta ihu Nurses suka shugo da gudu da kyar Suka kwaci Iman a hannun Nadeer,jikinsa har rawa yakeyi,nurses suna rike da Nadeer,Iman tuni ta goge Hawayenta Karo na farko kenan da ta dago jajayen idonta ta daura shi a cikin na Nadeer budar bakin Iman sai tace Ya Nadeer Da Dadi Awarar kuwa.

Ido ya rumtse sabo da takaici,Kafin ya motsa tace Ni ko Dadinsa naji wlh Lallai Kamla ta more ko dai Nima na shigo takarar ne? Fisgewa yayi ya nufota a fusace zai sake kamata ta fada toilet ta kulle tare da Sa key, tana ta tsalle a ciki tana uban dariya da Jin Dadi,Nadeer Yana jinta a fusace ya bar Room din Bai sake dawowa ba,a Hospital ya kwana,Washe Gari da Sassafe ya nufo room din Iman sabo da yayiwa Umma Alkawarin kula da ita Hakan yasa yazo duba ta,Yana shiga ya Hango ta Zaune Saman Bed daga Ita sai vest karama me siririn Hannu Da skert Blue,a hankali ta kalle shi sanye cikin Jallabiya Fara yayi kyau,kullum Nadeer me kyau ne shi,Ina Kwana ya Nadeer ta Furta da fara'a ko kulata baiyi ba Yana kallon Damatsan Hannnun ta da Suka tashi yayi rudu rudu sabo da dukan da yayi Mata jiya,Yana tsoro Kar Umma ta gani.

Muryarsa taji yace canja wannan rigar kisa me dogon Hannu,Dole sai dai ka Miko min akwatin wlh yau da kyar na tashi sai nurse ce tayi min komai, me ya same ki Kuma? Wurin da aka Yi min aikin ne yake ciwo Kamar ma kumbura yayi Kuma Yana kaikayi Ina sosawa ya kumbura,Uban wa yace ki Sosa,kin San da Haka ba ki fada min ba tun wuri? To ai jiya ne da ka bani wahala ya Zama worse, Kin jawa kanki Dole sai na duba wajen sai a San me za ayi Miki,Kuka Iman ta fashe da shi,Tsayawa yayi Yana kallon ikon Allah,a hankali tace Ni na shiga Uku na,sai kallo na kake Yi Kai ba Mijina ba Ni wlh na gaji a barshi idan rubewa ma zaiyi shike Nan na Mutu kawai na huta da wannan wahalar duniya,Idan Haka ne kasa Doctor mace ta duba sai ta baka labari kawai,Murmushi Nadeer ya saki Wanda Bai shirya ba,wannan fannin na karanta Na kalli na Matan da Suka fiki class ma,ba bako na bane har na gaji da ganin na Mata kala kala bare wata ke kucaka.

Dariya Iman ta shiga Yi tace ah Lallai ya Kace kawai dai abinda yasa ka karanci fannin kenan,sai na zuga Kamla idan kunyi Aure ta hanaka aikin Nan,Zan mareki wlh idan kina hada Ni da wannan kazamar kawar taki,akwati ya tura Mata ta zabi Riga me dogon Hannu ta daura a saman Vest din sannan ya fita ya turo Mace ta duba Iman ta koma ta sanar Masa wani dinki ne wacce ta cire ta barshi Bata cire wani ba,Haka yasa Doctor tazo ta cire a nutse duk da Haka Iman sai da tayi kuka,Umma da Mama sune Suka Zo suna kula da Iman har ta cika Sati Uku a Hospital ta warke Ras kawai Nadeer ya sallamesu aka koma gida da Iman lafiya Lau.

Tun daga wannan Rana Iman bata sake ganin Nadeer ba harkarta takeyi tana fita yawonta ko ina har Driving tana Yi da kanta,Kamla ta gaji da jiran ganin Nadeer har yau Bai Zo zance ba,yau ta yanke zata je wajen Iman taji ya ake ciki ne.
Iman tana Kitchen Umma da Mama sun tafi Biki har Khadija,Ita Daya ce sai masu aiki,Nadeer ne ya shigo sanye cikin kana Nan Kaya ba karamin kyau yayi ba,Fitowar Iman daga kitchen kenan wani sabon kamshin Nadeer na musamman ya daki Hancinta,Ina Yini Ya Nadeer Umma da Mama sunje biki Iman ta furta,na fiki sani Umma tace ta hada min Kunun gyada dauko min a Bina,Kitchen din Iman ta koma tare da dakko katon Glass Bowl da cup ta kawo gabansa a nutse ta ajiye a gabansa,,mikewarta ke da wuya Kamla ta rafka sallama,Iman ta amsa tana Mata sannu da zuwa,wani farin ciki ne ya Kama Kamla ganin Rabin ranta a zaune cikin shiga ta Alfarma,Kamla Zama tayi a kujera tana wani kallon Nadeer cike da so,Sai taji Ashe Ibaad ma aikin banza ne a Kan Nadeer.

Iman tana zuba Murmushi ta furta yau dai ga Zara ga wata Ya Nadeer ga Kamlan taka,tsaki Nadeer yaja ko kallonsu baiyi ba yaci gaba da Shan Kunun sa,jikin Iman yayi sanyi kusa Da shi ta koma ta zauna tare da furta Dan Allah karka Bari naji kunya ya Nadeer,Tsawa Nadeer ya bugawa Kamla Ke wannan tsokanarki takeyi ba abinda zanci da ke,ya kalli Iman yace You better tell this Thing,This Trash ta bar Nan gidan,ko nayi Kama da Wanda zai so ki ya furta Yana Kallon Kamla,fitar Mana a gida Ya furta a tsawace.

Da gudu Kamla ta mike tayi waje,Iman tabi bayan ta tana Bata hakuri,Kamla cikin karaji tace dakata malama makaryaciya munafuka wato shine Kika hada min tarko Dan kuci min mutunci to wallah Bari kiji Iman sai naga gatanki a duniya,sai naga Karshenki,abinda Kika Fi karfi sai yafi karfinki,In Allah ya yarda Haukacewa zakiyi kamar yanda na fada Miki a baya Inshaallah sai Ciwon Tabin kwakwalwa ya kamaki,Tana furta Haka ta shige motarta ta bar gidan,Iman ta juya jiki ba karfi,Nadeer ta gani a bayanta duk Hirarsu ya ji har Adduar Kawar Iman.

Tsaki yaja tare da komawa cikin Palo abinsa inda ya bar kununsa ya ci gaba da Sha,Iman a sanyaye ta shigo tare da Neman kujera itama ta zauna ta rumtse Ido tana Dana sanin Abinda tayiwa su Kamla gashi yanzu sun daina sonta sun daina yarda da ita,abinda ya fiye Mata kawai ta daina shiga harkarsu.

Hawaye ne masu zafi ya silalo wa Iman a saman kumatu ba tare da ta sani ba,Nadeer Yana kallonta akan wata banza kawa kike kuka?ya furta ba tare da ya kalli Iman ba, Ko Dan tayi Miki Addua me zafi? Ai ita ce mahaukaciyar,Iman Hawayenta ta goge da sauri Amma gaba Daya tunani takeyi.

Bayan sati Biyu su Iman Suka koma makaranta,Gaba Daya Su Kamla sun takura Mata sun hanata sakewa,sun hada Kai da Yan Iskan schl sun sa Iman a gaba,ko Ina ta gifta a makarantar sai ayi ta jefar Mata da maganganu Ana zagin ta watarana Kuma har dariya ake mata,Hakan yasa ta daina Sha'awar karatu gaba daya a Dole take zuwa school din.
Tun iyayenta Basu Gane ba har Suka gano Lallai akwai abinda ke damun Iman.

Yau suna da Lecture 9am ta dau wanka tayi kyau sosai tayi parking da motarta tana Fitowa Kamla ta watsa Mata Yogourt a kayanta,sauran kawaye sunfi su goma Suka Fara ihu da dariya,Iman ganin so suke ta kulasu su Zaneta sai tayi Shuru ta juya zata tafi Hanan ta fisge gyalen da Iman ta yafa,nan ma maza da Mata suka Fara Dariya ta wulakanci,Daga nesa Jawahir ta jefe ta da katon cake fasss a goshin Iman,da yawa matan suna cewa Snatcher sai su dungure Iman,Ga Raees shi ya bar schl din ya Gama bare ya tare mata,Bata da kowa,Bata ce komai ba idonta yayi jajir tace Hanan bani gyalena,Ba musu ta jefa Mata ta sunkuya zata dauki abinta Kamla ta hankada Iman ta fada cikin ruwan saman da akayi ya taru a katon Rami,Iman Hancinta ya fashe ta saki kuka,suna ta faman Yi Mata dariya,Wata Rantsatsiyar mota ce ta karaso dai dai inda Iman take kwance cikin ruwan,Su kansu Basu taba ganin mota irin wannan ba,Driver ne ya fita tare da Bude Masa baya tun daga Kafafunsa Daya zuro Suka firgita da kyawunsa bare kayan jikinsa Shadda ce me azabar tsada Sky blue,Nadeer kenan ya fito cike da Izza da takamarsa,Kamla Ya Samu ta tsaya tana kallonsa kawai sai Mari take ji ta ko Ina,sai da ta durkushe a kasa,Iman ya mikawa Hannunsa ta Kama ya jawota tsaye ta jike sharkaf, Me Suka Miki? Nuna min duk wacce tayi Miki wani abin,Iman ta nuna Wanda suka takura Mata gaba Daya,Yace kin San ko wacce ko? Ae tace tana sheshekar kuka,wace tafi takura Miki? Iman ta nuna Masa Kamla tace jiya ma Mari na tayi, ba kunya Nadeer ya Yace Ina tsaye a nan Rama duk abinda tayi Miki,Iman Bata hakura ba ta samu ta dage iya karfinta ta kwadawa Kamla Mari,ta Dawo ta bayanta Ta durma Mata Dundu a baya tace kin tuna a aji last week,Sannan ta dungure Mata Kai ta hankada Kamla cikin Ruwan yanda tayiwa Iman,Su Hanan zasu gudu Nadeer yace wlh duk Cikinku wacce ta taka kafarta sai ta bar makarantar Nan har abada,Cak Suka tsaya ga Kwarjini da Kyawun Nadeer ya Gama ruda su sun kasa ko motsi,suna kallo Sai da Iman ta Rama duk abinda Suka Mata Daya bayan daya,Sannan Iman tace Yaya akwai wasu ma a class jiya harda su suka tureni na fadi,Hannun Nadeer ta rike suka je har class ba teacher kawai Surutu sukeyi,Sai Dukan Iman Suka ji kawai a kansu,A fusace Suka dago ganin Nadeer sai sukayi mukus, Suna fitowa kofar Aji wasu Yan Mata su biyar Iman tace ke Halima kallo Nan wooooooo....yeeeee....Ahhhh...na rama Ihun da kuka Yi min jiya,wallahi da ace Kun taba jiki na sai na Rama ga Yayana duk wacce ta Isa tayi magana,Shuru sukayi suna kallon Ikon Allah Kamar Yan primary school ko secondary Wai Dole Iman sai ta Rama komai.

Daga Nan Hannun Iman Nadeer ya figa Zuwa Office din shugaban makarantar, Kara ya shigar yace ko a dauki mataki ko ya shigar da su kara kotu sun bar student suna abinda Suka ga dama,Hakuri Suka dinga bayarwa sannan Iman Gaba Daya ta bada da sunansu aka dakatar dasu da zuwa makaranta har na sati biyu sannan Ana neman Iyayensu.
Motarsa Nadeer ya nufa Iman ta bishi da sauri,a fusace ya juyo tare da Mata wani mugun kallo,Baya ta koma da sauri ta tsaya a firgice.










AsmaBaffa
[11/4, 11:15 PM] Sis Asma: SABUWAR ME EDDITING NA BAWA TAKE TA MIN SHIRME FANS,NA KARBE EDITING DINA DA KAINA.
🟪🟪🟪🟪🟪🟪🟪🟪
ADDU'AR KAWA
🟪🟪🟪🟪🟪🟪🟪🟪


FREE PAGE







5






Official






By
AsmaBaffa.









SANARWA...

NA CANJA ACCOUNT NUMBER.





RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300

'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari uku 300 ne

ADDU'AR KAWA
Naira dari biyu 200 ne
Ga masu bukatar shiga Group dinsa.


Ga masu bukatar siye ta Bank ga Accnt number

Accnt number 0175487861,Asmau Garba Muhammad, Gtbank.

Ga masu son tura katin MTN ta WhatsApp,Transfer ko Vtu ga number ta
08033933642.





Ana Yi Ana Sharhi Dan Allah fans.







Page naku ne Yan Albarka

OUM AMATULLAH
UMMA KURSUM
AUNTY NICE
AUNTY BABY
MURJANATU ISMA'IL
MARYAMKABIR
UMMU ELHAM.










A hankali Iman ta furta Yaya Wai me kazo Yi a schl din Nan? Baba ne yace Raees ya fada Masa abinda ake Miki shima Raees wasu ne Suka kirashi a waya Suka sanar masa,shine Baba yace nazo na gani,Na gode Yaya Nadeer cewar Iman,ko kulata baiyi ba, tafiya yayi ita Kuma Haka ta zauna lecture har suka tashi ta koma gida,tun daga wannan Rana Iman Ta samu lafiya ba Wanda ke shiga safgarta.
Kamla kuwa Mamanta ta sanarwa Abinda Nadeer yayi Mata,Hajiya Baraka Maman Kamla tace shi din banza har ya Isa ya taba min 'ya,to wlh ba a Haifi ubansa ba ma karewa,Kuma Mama Ina sonsa Amma yaki yarda Dani,Murmushi Hajiya Baraka tayi tace kwantar da hankalinki Kamar ya soki an Gama,nice fa da Ni yake Zancen Babu boka ba Malam tuggu kawai shi zai aiki a kansa, ta sama zamu biyo masa,Kamla sai Murna takeyi zata mallaki Nadeer.

Kamla ce ta Kira Hanan da Jawahir tace to ya zamu shirya yanda za ayiwa wannan yarinyar mu kawo karshenta,Jawahir tace Ni baruwa gaskiya idan ta mutu fa mu ce me? Hanan ma tace Nima tsoro nake ji,Tsaki Kamla taja tare da kashe wayarta ta Kira Wani matukin Babbar mota Trailer ta bashi aikin da zai Mata da kudade masu yawan gaske, Sai da ta sa Jawahir ta Kira Iman tunda suna Dan gaisawa sama sama da Jawajir, Allah sarki Iman,ganin Kiran Jawahir da sauri ta daga,Jawahir tace kin taho schl ne? Ae yanzu ma Ina Kan Hanya dai dai super park, ok To makaranta fa an fita za aje wannan Company Dake hanyar Suleja ki same mu a can gaba Daya Muna can,Kuma malamin yace Idan baka je ba baza ka ci Exam dinsa ba,Iman tace Dama yace kuwa za a je Ashe yau ne ko? to gani Nan na taho,Haka Iman ta saki Hanya ta mike har ta bar garin Abuja ta hau Babban titi tana ta sharara gudu a titi,Kawai Me Babbar motar Nan na Kamla yazo ya kwashe motar Iman Gaba Daya.

Motar kawai juyawa tayi ta kifa a titi,Kafin kace me mutane sun zagaye motar Iman wacce tayi rugu rugu ba Wanda yayi zaton za a samu mutum da Rai a ciki,ga me Babbar motar ya gudu gaba Daya an neme shi an Rasa.
Cikin gaggawa Aka zaro Iman Wacce take sume Kuma ikon Allah jikinta ko Ina kalau ba wani rauni da ciwo sai kawai Hannunta da ake tunanin ya karye,ganin Haka sai hankalin mutane ya kwanta.

Police aka Kira suna zuwa Suka Kira last call History nata wato Jawahir,Jawahir a tsorace ta Kira Kamla tace Ni dai ba ruwa na kinji Iman tayi hatsari,Murmushi Kamla tayi tace Bari a sanarwa Iyayenta,Nan take ta Kira Baban Iman ta fada Masa abinda ya faru,gaba Daya gidan ne Suka dunguma asibitin da aka Kai Iman Umma da Mama Har Khadija kuka kawai suke Yi,Ganin Iman Bata ji wasu rauni ba sai Hankalinsu ya kwanta har Doctors cewa sukeyi da sauki kawai karaya ce a Hannu.

Nadeer kawai Transfer ya karba Suka koma da Iman Hospital nasa,duk wani Abu Daya Dace anyiwa Iman, a kwana na biyu gaba Daya gidan Suna dakin sun kafeta da Ido ana fatan ta farfado,a hankali ta motsa kafarta,Umma da sauri ta matsa kusa da ita,Ido Iman ta Bude Tarr tana bin su Umma da kallo,Wani razanannen Ihu ta saki ko Karayar Hannunta Bata ji duk da an daure zumbur ta mike tsaye tana cewa Kai wannan Animal dinfa wa ya kawoku nan? Fuskar Umma ta rike ta shafa tare da furta kai....Hahahaha wannan ai Damusa ce,Ina Kika baro su zaki? Fatan dai duk su barewa da Giwa babbar gayya suna Nan lafiya? Idan kin koma Dan Allah ki gai she min su kinji Damusa.

Wurin Abban Nadeer ta nufa tace Wannan ai rago ne Kai harda Kai aka zo gaishe Ni? Ina Yar uwarka tinkiya? Khadija ta kalla tace ke Yar Autar kurege sannu,Nadeer ta karasa Inda yake tana ta faman kallonsa sai da ta dauki lokaci me tsawo tace wannan kawa na ne tana furta Haka ta fada Jikin Nadeer ta Rungume shi kam sai Kuma Suka ji ta fashe da kuka tana cewa Ni Ina Mijina ya tafi ne? kuka Baban Iman ya fashe da shi kawai ya fice waje,Haka Abba Ma,Umma kuwa Dama kukan takeyi ita da Mama,Khadija ma Sai hawayen Tausayi,Raees kuwa tunda ya kife kansa kasa motsi yayi,Nadeer ne kadai me Dan karfin gwiwa ma.

Janye Iman yayi a jikinsa sai ko ta Fara tsalle da ihu tana faman dariya tana tafi,Allurar Bacci Nadeer ya Mata ta zube a gadon tayi bacci sannan ya fita wurin su Abba Yana lallashinsu da Basu karfin gwiwa,Abba ya kalli Nadeer yace Yanzu Mene abin Yi? Za ayi Mata Test mu ga meke damun kanta tunda naga a kanta ta Bugu kawai ku Taya mu da Addua,kuka ba shi bane Addua take bukata a halin da take ciki, Inshaallah zata samu lfy.

Iman ko ta farfado Umma ta Bata Abinci baza ta ci ba sai Idan Nadeer ne,Bayan kwana Uku duk wani gwaji Daya kamata anyi wa Iman Result ya fito,Nadeer Bai boyewa kowa ba a gaban kowa ya Furta sakamako cewar wasu jijiyoyi dake kwakwalwar Iman sune Suka hade waje Daya,Wanda da kansu ma watarana zasu iya komawa yanda suke da kansu,idan Kuma Basu koma ba Dole sai anyi Mata aiki,aikin Yana da Hadari shi yasa gwara a kyaleta Har muga Ikon Allah,Yanzu dole Hospital za a canja Mata zuwa asibitin masu Rangwamen hankali sune suke da kwarewa a wannan fanni,akwai private me matukar kyau sai mu maida ta can,Kuka Umma ta saki tare da cewa kace kawai asibitin Mahaukata za a Kai 'yata wanne wani Na masu Rangwamen hankali.

Raees Dake tsaye Kamar gunki shi ya shiga bawa Umma Baki,Baba yace ba komai Nadeer

Please Login or Register in order to submit comment