Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waccen ta aure Baban Kamla ,ke fa Kema Baban Iman a kauye ya gano ki? Mama tambayar ma dariya ta Bata Kamar wasu Yara tace a'a Ni a birni na girma, Dariya sukayi har Iman ta tabbatar Maman Kamla hankalinta ragagge ne.

Maman Kamla Hajiya Baraka tace Amma kina sana'a kina fita kasashen waje ko? Don yanzu ba a Zama Babu sana'a,Kinga Ni har kiwon dabbobi nakeyi,ga Business Ina fita Dubai Ina kawo Kaya,ga harkar noma,Ina siyan kayan Abinci lokacin da yake Araha da yawa sai na ajiye shinkafa, wake,masara,dawa,Gero etc buhu dari biyu,dari biyar,dari uku ko Fi ma,idan yayi tsada sai na fito dashi na siyar wlh riba Zaki ci me yawa, Subhannallah wannan ai ba sana'a bace Dirty kike durawa a cikin ki,matukar ba Ke Kika noma ba to Bai halatta ki siyi Abu a Araha ba ki ajiye sai ya Dade sai yayi tsada ki fito dashi ai wannan ba sana'a bace,duk me yin Haka wlh ba sana'a yake ba Dirty da bala'i yake durawa kansa.
Ke ai yanzu yaki Halak yaki Haram akeyi an daina wannan bin wani gaskiya,Kinga noma ma yinsa nakeyi sosai Ni,Bana Zama inje Hajji inje Umrah,in Shana da kudi na,Mama tace Allah ya bada sa'a,Suna zaune Maman Kamla tana zaune da tarin kudi a gabanta taci kwalliya ita a Dole me kudi,In dai Kai baka da shi ko kallonka baza tayi ba,shi yasa take so Yarta Kamla ta samu Dan hamshakin me kudi ta aura.
Su Mama bayan sun duba Mijin nata yayi godiya kawai Suka musu sallama Suka tafi abinsu.

Iman tana Driving suna hanyar komawa gida wayar Mama tayi Kara,Da fara'a Mama tace Nadeer ne fa,Da murna Iman tace idan kin Gama ki bani shi mu gaisa na Dade banji ko kalar muryarsa ba.
Gefen Hanya Iman ta gangare tare da yin parking tana Jin Mama cike da so da kauna irin na Uwa da danta suna ta Hira Nadeer Yana dariya mutumin da sai yayi Wata guda ba a ga ko da Murmushinsa ba.
Iman tana ji Mama tace ga Iman Bari na Bata ku gaisa,Kyale ta Mama Ni me Zan ce Mata Wai,Kai ka kiyaye Ni Kai da Yar Uwarka kanwarka ce fa,Iman karba tayi da fara'a tace Ina Yini Ya Nadeer,Shuru yayi Mata Yana sani,Karo na biyu Iman tace nace Ina Yini Ya Nadeer? Shuru ba amsa sai ma Tsaki da taji yaja,Da kyar Ya iya furta kina da Bukata ne? Wani Yarrrrrrrrrrrr Iman taji a jikinta sanda Taji muryarsa me shegen dadi,Dan ta sake sashi magana tana so taji muryarsa me Gardi,tace ae Bukata ce Dani iri iri ma kuwa shi yasa ma nace Mama ta bani number dinka na fada maka,Ina jinki bani da time ya sake furtawa,Iman a ranta ta Furta Na shiga Uku Dadi Muryarsa Zan mutu,Da kyar ta Fisgo nutsuwarta tace Da...dama so nake ka siyo min Laptop iPhone ita kawai nake so,Ban iya daukan Kaya ba ya furta tare da kashe wayarsa a can yana ta masifa shi kadai ta Gama Bata min lokaci Yar iskar Yarinya.

Mama Dariya tayi tace naga sanda Nadeer Dina zai canja,Kuyi Masa aure idan ya dawo wallahi mace ce kawai maganinsa Mama yanda zata Ci ub.....da sauri Iman ta toshe bakinta,Mama tace sai na fada Masa ai ya kusa dawowa,Dariya sukayi sannan Iman ta fisgi mota ta Fara fella gudu da Mama a mota tana uban ganganci a titi,Mama Tana mota sai faduwa take tana tashi,har hanjin cikinta ya juya ta Fara kakarin Amai,Iman kuwa Dariya take Mata,Mama tace Zaki ci ubanki Iman hallaka mu Zaki Yi?
Gudu Iman ta rage a nutse har suka karasa gida.

Washe Gari Iman tana Palo tana kallo abinda ta Saba idan ba school abinta hankali kwance.














AsmaBaffa.
[11/4, 10:57 PM] Sis Asma: GYARA AKA YI FANS
WURIN EDITING NE.





πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ






FREE PAGE








2








Official










By
AsmaBaffa.





ADDU'AR KAWA NOVEL NA
🚨'YAN KWANKWASIYYA NE🚨.








SANARWA...

NA CANJA ACCOUNT NUMBER.







RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

ADDU'AR KAWA
Ga masu bukatar shiga Group kullum kuga posting
Naira dari biyu 200 ne.


Masu Bukatar siya ta Bank, ga account number..

Accnt number 0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gt bank.

Ga masu son tura katin MTN ta WhatsApp,Transfer ko Vtu kuyi min magana Kai tsaye a wannan number
08033933642.






Comment pls fans.



Page naku ne 'Yar kwangila fans Group.











Iman tana Palo a zaune Umma ta fito tare da furta Iman kije Inji Babanku Yana dakinsa,Da sauri Iman ta daura dankwalin lace din Dake jikinta ta Haura sama part din Babansu, a palonsa tayi sallama ya amsa Yana zaune a 2seater a kasan Kafafunsa gabansa ta zauna tana zare idanu sabo da tasan ba Wasa, Baba ne yayi magana Iman wanne samari kike Tara mana a gida ne? Ko aure kike so? Da sauri tace Baba Ni ba Aure nake so ba wlh kawai abokai na ne Yan school dinmu,Tassss kake ji Baba ya kwashe Iman da mahaukacin Mari,Da sauri ta dafe kumatu tare da sakin Kuka,mu Zaki mayar Yan Iska? Ai nasan duk irin mazan da kike kawowa bana hanaki kula samari ba? Yar iska kike so ki Zama?to wlh ki kiyaye mu tun kafin na fadawa Yaya Kuma kin San Halinsa,Jin Baba yace zai fadawa yayansa Iman ta gigice tana bashi hakuri,Na daina Baba Dan Allah kayi hakuri Allah bazan Kara ba na tuba wallahi
Tashi ki bani waje ko na tattaka ki stupid kawai Zaki zubar Mana da mutunci,sabo da Kinga Nadeer baya Gari ko?,Da gudu Iman ta fice.

Tunda Iman ta fita Bata tsaya ko Ina ba sai part din Maman Nadeer can ta Iske Khadija,ko kallonta Khadija Bata Yi ba sabo da Iman ta kwace Mata Mijin da zata aura,a duniya ba Wanda take so sama da saurayinta tana tunanin zai zamo mijinta Amma Iman tabi Rana tabi dare tare da rabata da shi,suna Yan Uwa ko kunya Bata ji,Tsaki Khadija ta ja tare da barin Palon,Iman kuwa ko a jikinta sai ma cewa tayi Kyawun Rausayinki ne ya ja miki,Duk Wanda yake da kyau to kyawunsa ya jawo Masa domin sai ya so ni Dole,Muryar Mama ce ta daki dodon kunnen Iman tace Iman ki gyara halinki ba Abu ne me kyau ba kici amanar kawayenki da Yan uwanki,duk cikin samarinki Khadija tace gaba Daya na kawayenki ne Kika Yi snatching nasu ba Abu ne me kyau ba,ki roki Allah sai ya kawo Miki naki,Baki Iman ta cokalo tare da cewa Ai Adduar tawa ce ta karbu shi yasa Allah ya hore min na Samu dama har na kwace su,Kuma Mama ai laifin samarin ne idan da gaske suna son Su Kamla ai sai su dage Suki kulani ya kamata ma yayi suci mutunci na,Amma fa Ina yin wayo sai kawai su dawo wajena,Ni Kuma nawa duk da nake samu tsofaffi ne sun Haifi Ya Nadeer ma gasu Basu da kyau.

Ok ke yanzu kyau Zaki Aura? Mama ta tambaya,Mama waye yaki kyau a duniya kema ba gashi ba Kyakyawa ce ke Abban Nadeer jiba kyansa jinin larabawan moroco da Algeria sannan kuce mu baza mu zaba ba ai wlh Nima kyau kawai,Dariya ma ta Bawa Mama ganin da gaske Iman take, Allah ya shiryeki Iman,Ameen Mama Baki da aikin girki na Taya ki? Bani da burin Daya wuce yanzu Naga na Iya girke girke masu Kara lafiya sabo da idan na Auri me kyau yasha girki yanda kullum kyawunsa zai ci gaba da Glowing Yana wani shining,Tafi ki bani waje Da banzan a
Surutunki Kamar Aku,Tv ta kalla Ana Highlighting din Ball Neymer ta kalla tace Ina ma zanga Neymer din Nan Allah da shi Zan aura,Biron dake Hannun Mama ta jefa Mata tashi ki tafi Wlh na gaji da fitsararki kin San Kuma Abba Yana Gari yanzu Zan Kira shi,Da sauri Iman ta bar part din Jin Abba Yana Gari.

Bayan sati Biyu Magungunan Iman suna karewa Ciwonta ya dawo sosai Bata iya Zama Kamar zata haukace Haka take,kuka takeyi sosai Dole aka koma ganin Likita ya rubuta Mata wasu taci gaba da Sha Amma Ciwon Yana Nan Yana damunta, su Kamla kullum suna hanyar zuwa dubiyar Iman, Yau su Kamla su Uku Suka shigo katafaren gidan su Iman da labebiyar motar Kamla,Suna fitowa Zasu shiga ciki kenan katsam sai ga Motar Ibaad shima yazo gidan duba budurwarsa Iman.
Yana fitowa sukayi Ido biyu da Kamla Dake Dan duniya ne ko a jikinsa,Kamla kuwa mamaki ne ya rufe ta me ya kawo Ibaad gidan su Iman,Wani sabon son Ibaad ne ya lullube Kamla,Kasa share shi tayi,Zuciyarta wani bugawa takeyi kawai tace Sannu Ina wuni,da Fara'a ya amsa ko a jikinsa yace ya gida kwana da yawa? Wani sanyi ya ratsa zuciyar Kamla tace lfy Alhmdllh sannan suka wuce ciki su Hanan ko kallo Ibaad Bai ishe su ba sabo da ya yaudari kawarsu. Bayan sun gaida Umma Sun iske Iman a bedroom dinta Wanda ya gaji da Haduwa komai na ciki Sea blue and white.

Iman gabanta ne ya yanke ya Fadi tasan Ibaad yace yazo duba ta Yana compound ga su Kamla Kuma,Wayar Iman sai Kara takeyi Ibaad Yana kiranta ta kasa Dagawa,wayar ta dauka tace Ina zuwa ta shige Toilet dinta sannan ta daga tare da Furta Hello My Hero? Ya amsa cike da farin ciki Yana Jin zuciyarsa tana bugawa a duk sanda yake waya da Iman dinsa,nasan kazo ko? Ka bani 3mnt zaka ganni,Nan take ta kashe wayar tare da Kiran me aiki Rakiya ta Bata Umarni Kan ta Kai Ibaad Palon Baki sannan ta fito tana Murmushi ta kalli su Kamla tace Ku Dan jira Ni Wai Ibaad ne yazo Zan hada shi da Abban Nadeer zai Masa signing a wasu Document,Kamla Ashe Ibaad yayi mugun sanin Abban su Nadeer, Kamla farin ciki ya kamata tace Alhmdllh Iman Dan Allah ki lallaba min shi ya dawo gareni wlh Ina kaunarsa,Hanan da Jawahir suka ce wlh Kamla Baki da zuciya akan namiji, da Sauri Iman tace nasan mutuncin kanmu bazan ma yarda na dawo Mata da shi ba,duk irin wulakantaki da yayi Amma kike sonsa wlh kin bani kunya Kuma wlh bazan iya ba ganin Abban Nadeer ma daya dameni na taimaka masa da kyar na yarda,na tsani Ibaad tunda yayi Miki Haka kawata, kiyi zuciya ki rabu dashi kawai,Da sauri Hanan tace wlh kuwa.


Gaban Iman ne ya Fadi ganin Kiran Ameer Saurayin Hanan,Wayar ta daga a hankali Suka gaisa su dai Su Kamla sunji tace sai zuwa dare kazo,Wannan Kuma waye? Jawahir ta tambaya,Hmm wani Dan Uwan Umma ne yace zai shigo da dare ya dubani Wai so na yake, dariya sukayi gaba Daya Iman tace me zanci dashi bafa Kyakyawa bane.
Duk iskancin Nan da kike Dan Kinga Ya Nadeer ya koma Uk ne cewar Hanan,Iman tace wlh kuwa kawata baya Bari kowa yazo zance wajen mu,Ina zuwa Bari Naje na raka Ibaad wajen Abba,Mayafinta ta dauka ta shiga bedroom din Umma can taci uban kwalliya ta wuce Palon Baki inda Ibaad ke jiranta.

Kamshin turarenta ne ya daki Hancin Ibaad Wanda yayi sanadin dagowarsa da sauri ya kafe Iman da kallo zuciyar sa tana bugawa sabo da irin tsananin kyan da Iman tayi gaskiya ba karya Iman ta hadu karshe,Sanye take cikin Wata Shadda gezna maroon, kusa da Ibaad ta zauna Wanda yake cikin hadaddun kana Nan kaya,Ranki ya Dade kinyi kyau cewar Ibaad, Fari Iman tayi da Ido tare da furta thanks,Hannunta ya rike ya Fara Wasa da yatsunta sabo da Ibaad Yana birgeta tasan ba Dan Iska bane Bata hanashi kawai iyakar ya rike Mata Hannu, samarin yanzu masu rike Hannu da Hugging sune na Gari mutane sun lalace,sun Dade suna Hira sannan ya ajiye Mata kudade masu nauyi ya wuce.

Sai da ta shiga bedroom din Umma ta canja kayanta na dazu tare da wanke Fuskarta tasa Katon Hijab sannan ta koma wajen su Hanan Dake room dinta,Kamla ta saki Murmushi tare da Furta Iman da wannan Hijab din Ibaad ya ganki? Ah ae Mana to uban me Zan Masa saurayina ne Dan uwarsa ya yaudarar min kawa a banza Zan zauna yaga kwalliyata ai bani ba shi,Dariya suka dinga Yi Iman ta birge su.
Sai dare su Kamla Suka fito zasu tafi Iman tace ya makarantar ai Malaman sun yarda munyi Miki har Test da Assignment Baki da matsala cewar Kamla,na gode kawayena Ina kaunarku cewar Iman,Har mota ta raka su,Sun juya da motarsu zasu fita motar Ameer Saurayin Hanan ya shigo da tasa motar,Hanan da sauri tace wancan kamar motar Ameer Dina, ke Dalla uban kowa ma Kika gani kice Ameer dinki me zai kawo Ameer Nan Kamla ta lullube Hanan da fada,Hanan tayi mukus Suka bar gidan Ameer shima yaga Hanan Amma ya share tunda Allah ya taimake shi Bata ganshi sosai ba.
A compound Iman ta tsaya Suka danyi Hira da Ameer,Sam Bata damu dasu Ameer ba sosai ba kamar yanda take son Ibaad ba,tana mugun son Ibaad Yana birgeta.

Kwana biyu Iman taji sauki sosai da dare 8pm ta shirya zata fita Wai karbo dinki kasan layinsu ba nisa da gidansu,Umma tace kiyi sauri Kar Babanku ya dawo ko Abban Nadeer ya ganki a waje ba ruwana,Iman tace ai yanzu Zan dawo,Raees Yana zaune yace sai ki kula wlh Goody mahaukaci a Nan yake Zama Kuma kin San dukan mutane yakeyi ko jifa,Iman tace na sani Ya Raees ai tambayar ma mutane zanyi inda Goody Mahaukaci baya Zama na wuce lafiya Lau abina,idan Kika Dade wlh Zaki ji ajikin ki Ya Nadeer ya dawo yau Yana gida,Yaushe Nadeer din ya dawo ban sani ba? Tun safe sanda ya shugo Nan Baki ji shi ba? Cewar Umma,tunda Iman taji a bakin Umma tasan da gaske ne,Hijab dinta me hannu ta saka ta fice da sauri ta bar gidan, sai da tazo layin da Goody mahaukaci yake zama,Iman tace Uhm Bari na tambayi wancan bawan Allah din layin Nan duhu ba haske ya nuna min hanyar da Zan bi inda bazan ga Goody mahaukaci ba har naje na dawo.

Cikin duhu Iman ta samu mutumin Wanda ba a Gane waye tace Bawan Allah Dan Allah wacce Hanya zanbi wacce bazan Hadu da Goody Mahaukaci l ba? Kasan Goody a mahaukakatan ma karshe ne,Shege Dan Iska,wallahi da ace Ina da Dama da sai na sa an karairaya wa Goody Kafafu, Iman Bata sani ba Ashe Goody Mahaukacin ne da kanshi shi ta tare ta tambaya,Goody Yana Huci da gurnani yace Dan kutmar ubanki nine Goody...(Afwan fans nayi zagi) Ai Iman ta kwashe da gudu tare da ihu tayi Reverse ta koma Inda ta fito,Shi ko Goody ya bita shima da uban gudu Yana jifanta da manyan duwatsu,Iman gudu take shararawa da ihu gaba Daya Goody ya rufa Mata baya,Wani jifan ya sameta a kafa,Har karfinta ya Kare ga lalurarta taji wuya ta tashi kasa tafiya tayi ta Fadi a wajen,Goody ya karaso Inda take da manyan duwatsunsa Yana Dura Mata Ashar,Iman Tana cewa Goody tsaya kaji wlh Kai mutumin kirki ne,Gaka kyakyawan Saurayi,Dan gayu me kamshi, sonka nake Yi dama na Dade Ina sonka Wai Wayo zata yiwa mahaukaci, cikin karaji Goody ya Kai Mata duka a fuska, Bai Kai ga dukan ba wata Rantsatsiyar mota ce ta haske wa Goody Fuska,Goody Kuma baya son haske da Gudu Yana ihu ya koma Inda ya fito cikin duhuwar unguwar da yake Zama.
Sai lokacin Iman ta samu damar kuka ta fashe da kuka sosai gashi ta kasa tashi.

Mutumin Dake mota ne ya fito,Wow wani farin balarabe ne,Kyakyawan gaske na ajin karshe,ga Kyawun fuska da sura fari tar da shi,duk da dare ne hakan Bai Hana ganin irin tsananin kyawunsa ba,ko a garin Turawa da larabawa sai an Tona a samo irinsa,Cikin tafiyarsa ta takama da Izza ya karaso Inda Iman ke kwance, ke ubanwa ya fito Dake daga gida a wannan Daren? Taji Muryar Nadeer me Dadi ta daki dodon kunnenta,Nadeer ya Kara girma da kyau ya Zama cikakken Namiji Daya amsa sunansa,yanzu dama Ya Nadeer Haka yake da kyau kamar Aljani, tasan Halinsa yanzu zai zaneta,Kuka kawai ta sake saki tace Wal...Wal...wallahi Allah...ba Haka kawai na fito ba...na rantse da Allah dinki na Zan karbo kuma na tambayi Umma...Shut up ya daka Mata tsawa tashi ki wuce gida Kuma bazan daukeki a Motata ba,Wlh bazan iya tashi ba,kasan lalurar da nake da Ita bazan iya tashi ba,Ya Nadeer Bai San Iman tana da lalura ba tsaki yaja tare da juyawa abinsa zai shiga mota ya wuce,Da karfi Iman Tace dan Allah ka taimaka min idan kaje gida kace Ya Raees yazo ya daukeni cuwona ya tashi,Duk da dare ne sai da ya juwo tare da Balla Mata Harara sannan ya dauki katuwar wayarsa me shegen tsada ya Kira Umma, a hankali yace Umma Iman ta kasa tashi dama tana da wata lalura ne? Da sauri Umma ta fashe da kuka tana Salati tace ai baka sani ba lalura ce a gabanta dare Daya ta samu lalurar aiki za ayi Mata Nan da wata Daya,Dan Allah Nadeer ka dakko ta, ok kawai yace ya kashe wayar,Yana zuwa ya fisgi Hannun Iman Dan wulakanci a kasa ya jawota kiiiiiiiiiiiii Kamar kayan wanki,gefen Cinyoyinta duk sun kurje ya jefata a bayan mota sannan ya shiga ya fisgi motarsa zuwa gida,Iman ba damar kuka tasan Halin Ya Nadeer sai ya mareta,tun kafin yaje gida ya Kira Khadija a waya ta fito,Yana yin parking ya fice a motar yayi tafiyarsa tare da furta khad taimaketa ki kaita part din su.

Khadija dai Haka da kyar da wahala tana yiwa Iman sannu ta kaita side nasu,Ya Raees Jin Goody ne ya tumurmusa Iman Haka ya dinga dariya,Umma ma abin ya Bata dariya,Iman kuwa haushinsu take ji Ana ta Yi Mata dariya.

Bayan kwana Biyar Nadeer ya Fara aikinsa a hospital nasa dankareren gaske tare shararrun likitoci harda turawa,asibitin sai manyan masu kudi ne ke zuwansa,Nadeer baya son wahala ba sosai ma yake zuwa aikin ba,dama masters ya koma yayi a uk. da dare sanye yake cikin Wata Arniyar shadda Saka Grey color tayi mugun kyau ba karamin kyau yayi ba kamar Wanda yaje Daurin Aure,Hadadden Part dinsa ya Haura minti kadan ya fito sanye da Jallabiya fitted milk color, Yana uban kamshi ya nufi part din Abbansa Wanda ya Gama gajiya da Haduwa an narkar da dukiya komai na daban ne a gidan.
Kwankwasa kofa yayi Abba ya furta shugo,Palon Abbansa ya shiga dauke da Sallama a bakinsa,Mama Dake gefen Abba itace ta amsa Sallamar,Khadija tana gefe a kasan center carpet, Shima Nadeer a kasan ya zauna cike da ladabi ya gaida Mama da Abba Suka Amsa,Abba yace Nadeer so nake naji tunda fannin Tiyata ka karanta me zai Hana tunda Kai na gida ne Dan Uwan Iman ne,Kayi Mata aikin da za ayi Mata,Ni da Dan Uwana mun yanke Shawara akan wani banza bare ya kalli alaurar mace gwara Kai kayi aikin idan yaso sai ka Nemo likitocinka Mata kuyi aikin tare,Nadeer baya son wahala ya turo jajayen lips dinsa Dan cut yace Abba Ni....Ni...gaskiya wasu suyi Mata aikin nan....tsawa Abba ya daga Masa yace har Ni in baka Umarni kayi min musu?yaushe ka girma har ka Isa kayi jayayya dani You are very stupid,da Sauri Taufeeq yace kayi hakuri Abba zanyi,Mama tace taurin kanka na masifa ya ja maka,zaka taimaki Yar uwarka ka zauna kana shirmen banza,Karajin Abba Suka ji Allurarsa ta tsohon Soja ta motsa yace on your kneel, Oya kneel down before I give you a Dirty slap, Ba Shiri Nadeer yayi kneeling down,Handsup Abba ya Furta,Mama ce tace Dan Allah kayi hakuri Kato da shi ya Isa Haifar Yara kana sashi Kneel down ai zaiyi Mata aikin ko,Ae..Ae...Nadeer ya furta da sauri,Get out Abba ya Furta da sauri ba shiri yayi waje,Khadija ta bi bayansa itama da sauri Dan Kar Allurar Abba ta motsa a kanta again.

Komai na Iman na asibiti sai da Nadeer ya tura Khadija ta karbo Masa yaga komai da komai,yaje wajen Likitan ya sake Masa tambayoyi sannan ya dawo tare da Sa ranar aiki idan Iman ta Karasa Exam ta Gama level 2 dinsu saura sati Daya su Gama.

Bayan kwana Uku Nadeer ya gano yanda samari kyawawa masu kudi suke layin zuwa wajen Iman idan tasan Abba da Babanta basa Gari,Yau ma da dare bayan Sallar Isha Ibaad yazo Nadeer Yana compound a kujera Yana kallonsu Iman Bata ma San da shi ba za suyi sallama da Ibaad Yana kallo Ibaad ya riko Hannun Iman Bai taba Rungume Iman ba sai yau yace sau Daya kawai Baby ya rungumeta a Kirjinsa sannan ya shiga mota ya tafi sukayi Bye.
Tana juyawa zata tafi taga mutum a gabanta,ba karamin tsorata tayi ba,Ga kwarjini da cikar zatin Nadeer yasa Iman duk ta gigice,ta Rasa Dalilin da yasa Bata iya kallon Nadeer,ta Rasa me yasa take Jin tsoronsa? Ba tare da tace komai ba ta ratsa zata wuce ta gefensa Maruka taji har biyu a Fuskarta masu zafi,Iman ta dafe kumatu tsoro ya shigeta ta kwashe da gudu Dan tasan laifinta.

Tunda su Kamla suka ga Ibaad a gidan su Iman Hankalinsu ya kasa kwanciya Suka Fara binci ke har sai da Suka Gane komai,mamaki ya Kama su Wai Iman ce ta musu snatching,Ana Haka Kuma Iman taga za ayi Mata aiki ko ta tashi ko ta mutu wannan Dalilin yasa tayi tirr da halinta na banza tace Dole naje na Basu hakuri su yafe min ko wacce ta koma wajen saurayinta, Bata San su Kamla sun Gane me tayi ba tuni,Amma Basu nuna Mata ba ko a fuska,yau Thursday zasu zana Exam ta karshen Gama level 2, 12pm Suka fito daga Exam,Iman cike da kunya ta ja su Kamla garden din schl din, Zama sukayi suna kallonta kawai, a hankali ta Bude bakinta me kyau tace Uhm...Ahm...dama ba wani Abu ne yasa nace Ina son magana da ku ba Kawaye na,Ku yafe min ta furta idon na zubar da Hawaye ta Basu labarin yanda tayi ta kwace musu samari,Kamla wacce ke tsananin son Ibaad tace kin cuce Ni Iman,ba komai kanki Kika cuta mun yafe Miki ai ke kawar mu ce,Jawahir tace kinyi asarar halinki,Hanan Kam cewa tayi na yafe Ni ma Iman tana Jin Dadi tunaninta da gaske sun yafe Mata tayi godiya tare da Yi musu Sallama ta tafi gida cike da nadama.

Iman tana tafiya Kamla ta sheke da dariya tace ikon Allah Dan kawai ta fimu kyau shike Nan ko wanne saurayi sai ya bita,to idan ku Kun yafe Ni ban yafe ba sai na dauki fansa, yanda ta Yaudaremu muma Yaudararta zamuyi sai mun Rama,Wallahi wallahi kinji na rantse Iman sai ta Haukace sai kwakwalwarta ta hadu da jini,Hanan tace wlh kuwa Banga laifinki ba ai tare zamuyi aikin Dan ganin Bayan Iman,Ko Alama Kuma Kar mu nuna Mata ko a fuska mu ma cewar Jawahir,sun Dade da Gama Tattaunawa sannan Suka tafi Suma.














AsmaBaffa.
[11/4, 10:58 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ



FREE PAGE







3







Official








By
AsmaBaffa.





ADDU'AR KAWA NOVEL
SADAUKARWA GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA NE🚨









Please Login or Register in order to submit comment