Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai dadi sosai.
Su Usaibatu ne Suka Fara Fitowa da jakankunansu Ghana must go,Yayin da Mutane maza da Mata manya da Yara suka Fara cincirundo wajen kallon motar Nadeer da Kuma kallon su Nadeer.

Su Usaibatu kuwa gidan me Gari suka Shiga tare da kiranshi,Jin me mota ne yazo nemansa sai ya fito da sauri,Ganin su Nadeer yasan masu kudi ne harda Durkusawa har kasa Yana gaida su,Nadeer Mamaki ya kamashi dattijo harda Durkusawa,Da sauri me Gari ya dakko katuwar Tabarma ya Shimfida musu,Su Usaibatu suna tsaye Nadeer da Iman Suka zauna.,
Me Gari ne yayi magana bayin Allah daga Ina haka ko Gomnati ce ta turo ku zaku raba mana Tallafi?,Ido Iman da Nadeer suka hada me Gari da son abin duniya,Murmushi Nadeer yayi tare da Furta ba Haka bane,tsarin garin ne yayi min,naji labarinsa wurin su Laure shine nace Zan siyi fili nayi gini,Me Gari yaji harka tazo da sauri yace Alhmdllh ai fili akwai shi dama ba a Dade da yanka wani fili ba har an Fara siyarwa,Sai muje kaga girmansa yayi ko yayi kadan sai a Kara maka,Ba damuwa cewar Iman,da su Usaibatu aka tafi can wajen karshen Gari a wajen Ginin Amare ne sababbin gidaje wasu na kasa wasu na siminti a Nan me Gari ya nunawa Nadeer katon fili,me Gari Yana washe Baki yace kaga idan ka Gina Nan yayi wallahi gaku ga Amare kusa akwai mutane a wajen,Nadeer da Iman Suka murmusa,Usaibatu tace Me Gari Suma Amare ne ko sati ba ayi ba da Aurensu kawai Amarci Suka Zo ci a Nan kasan mutanen birni sun Saba da Honeymoon Inji Bature.
Iman tace a Ina Kika San Honey moon? Wajen Kamla mayyar maza Muka ji ta fassara mana.

Nadeer Yana jira yaji kudin fili me tsada sai yaji me Gari yace dubu dari,shi me Gari a Haka ma cutar Nadeer yayi,Nan take Me Gari ya Nemo shedu,Nadeer Kuma Su Usaibatu Suka Kira Iyayensu su Hudu harda Yayan Laure Kamisu Suka Zama shedun Nadeer aka rubuta Takardu da komai sannan su Usaibatu Suka Yi sallama da su Nadeer Suka tafi gidansu.

Iman kuwa da Nadeer sai wurin Magrib sannan suka Shiga Mota Suka koma Cikin Birnin Kebbi Masaukinsu Hotel,Dakin Su Usaibatu ta shige Wai baza ta hada daki da Nadeer ba,Ta Iske masu Hotel sun gyara komai,Shima Nadeer Yana room dinsa sai dai yasa a kawo Mata Abinci yayin da ya nemi Hamshakan maginansa ya Basu aikin Ginin gida dake Garin Shanaye, tuni gini yayi nisa aiki akeyi sosai ba dare ba Rana,Su Usaibatu kullum sai sunje sunga yanda gini yayi kyau.
Kafin sati Daya An gina room biyu da katon Palo har wurin Dining,ko wanne room da Toilet dinsa sannan akayi toilet daban a tsakar gida ta Baki,rufin kwanon gidan Dark brown ne, ciki yasha pop,tsakar gida akayi rijiya aka rufeta tare da Sa katon Tank Wanda zai na jawo ruwa cikin pampuna kasancewar Babu Ruwan pampo a garin Amma akwai Wutar nepa,ciki da wajen gidan yasha tiles har jikin bango ko Ina,Tsakar gida Kuma Interlock sai Yan flowers da aka sa,gidan ba karamin kyau yayi ba,idan ka shiga ka rantse a Abuja ma kake,Dan karamin gida sai shegen kyau,ya tsaru,Yan kauye sai kallo sukeyi suna murna garinsu yaci gaba ko banza za aga gida me kyau Suma,Wutar Solar aka saka Wanda idan ba Nepa ga Solar Nan, komai an saka,gaskiya gida ya Kai gida cikin kwana takwas aka Gama komai,Ba tare da Iman ta sani ba Nadeer Yana yawan zuwa kauyen ganin gidan,Har furniture masu tsada ya zuba a gidan,sai kayan Abinci ya cika store dashi,duk wani abin amfani an saka a kitchen,Babu abinda zaka nema ka Rasa sai abinda ba a Rasa ba,Su Usaibatu ne Suka zage Suka gyara gidan tas ko Ina kyalli yakeyi,iya kudinka iya shagalinka wato ko a kauye ne indai da kudi an wuce wajen,idan kana birni ba kudi to fa baka da bakin magana.

Su Laure kuwa Nadeer Yana zuwa suke zuwa wajensa sabo da yana raba musu kudin Shan shayi.
Har kwana goma Iman Bata ganin Nadeer sai Idan ya leko duba ta,hakan ma a jikin kofa zai tsaya suna gaisawa zai juya ya tafi abinsa,Ita Kuma sai kunya ta kasa tsinana komai ta zauce.

Yau Sunday da safe Bayan sun karya,Iman tana kwance tana game da wayarta taji kwankwasa kofa,budewa tayi da sauri tasan Nadeer ne, Tana budewa ta sadda kanta kasa,Dakko Kayanki mu wuce kauyenki, an Gama Gina gidan ne? Da Ido ya Mata Alama da Yes, Jakarta ta dakko da komai nata Suka jera,Nadeer ya ajiye musu key Suka tafi,sai da ya shiga wani store a Garin ya jibgar musu siyayyar abinda Babu sannan ya sake tsayawa a bank,a ATM machine ya Ciri kudade Suka wuce,1pm Suka Isa kauyen da zasu zauna,tun daga nesa gidan Nadeer kawai ake hangowa kowa ya kalli gidan yasan gida ne, Iman sai faman murna takeyi Nadeer Yana satar kallonta Cikin gidan ya nufa su Usaibatu suna kofar gidan Dama yace musu yau zasu dawo gaba Daya,ganin motar Nadeer suka dage tare da tura gate din ya Shiga ciki suka rufe,Iman taga gida neat sai faman washe Baki takeyi Bata taba tunanin Haka za a kera gidan ba,Ko da Suka Shiga ciki Tasha mamakin irin furniture din da aka zuba, ko Ina sai da ta duba na gidan,gashi yasha gyara sai kamshi yakeyi gwanin birgewa.
Su Jummala kuwa sallama Suka Yi musu zasu tafi gida,Iman tace kuzo da dare za muyi party yau ai sai kun gaji da Shan shayi da lemo,Farin ciki ya Kama su Laure Suka ce to sai Munzo,Nadeer kuwa tuni ya wuce bedroom abinsa.

Iman ma Daya room din ta zaba ta shige ta Fara shirya kayanta,tana Gama wanka ta silla tare da Hadewa cikin wani creazy pencil Jean fari t-shirt tasa me shegen kyau Black,gashinta yaci gyara, ba karamin kyau tayi ba.
Kamar wata Baturiya Haka ta fito kamar a sace ta,Nadeer ta Iske a palo, shi kuwa wando ne 3qurt a jikinsa ba ko Riga sexy jikinsa me shegen kyau da sheki ya bayyana,Kallon tsaf Nadeer yayi Mata a ransa ya Furta Ashe dai tana da kyau ta iya kula da kanta,a fili kuwa nunawa yayi Bai ma gani ba,Gefensa ta samu ta zauna tare da yin shuru.

Kallonta yayi yace akwai komai a kitchen kin San Nan ba a siyar da Abinci so sai ki zage ki Fara Abinci ba ruwana ke Kika ce sai an zauna a Nan garin,Murmushi Iman tayi tana Wasa da yatsunta cike da kunya ta Furta to kanta a kasa sai Murmushi take Yi ita Daya sabo da wani farin ciki dake ratsa ta,Kallonta Nadeer keyi ba kyaftawa sabo da ba karya tayi kyau,muryarsa me Dadi ta tsinta Yana cewa Ni Kinga ki daina wannan gulmar Taki ta kunyar banza ba birgeni takeyi ba Hasali ma nafi sonki sanda kina da Lalura sabo da ba wani kunya a tsakaninmu, Kunya ta kike ji nayi Miki operation Kuma na aureki shike Nan 1-1 kenan ban gani a banza ba,Da sauri Iman tasa tafukan Hannayenta tare da rufe Fuskarta ji take Kamar ta nutse,Baki ya tabe Yana kallon ikon Allah.

Kitchen ta mike ta Shiga taga akwai komai Gashi harda Gas kayan Abinci kuwa komai akwai a store,Fitowa tayi tace kana cin tuwo Ya Nadeer? Harara ya Balla Mata tare da Furta kin sani ai sai dai kiyi kici abinki,to me Zan dafa? Shuru yayi mata,da kanta ta koma kitchen tayi miyar kwai Tasha nama sai tayi Sakwara,Gefe kuma taga kaji a fridge sai tayi Farfesun Naman kaza,Bata Gama ba sai kusan Magrib,gidan ta sake gyarawa ko Ina Yana sheki da kamshi,Wanka ta sake yi ta shirya cikin Wani arnen material doguwar Riga tayi kyau matuka,Sallar Magriba ta fito zatayi sai taji ta Fara period,Hankalinta ne ya tashi kasancewa Babu pad a gidan,Da sauri ta fito tuni Nadeer baya gidan ya tafi masallacin kauyen har Sallar Isha an idar Amma Bai dawo ba, Su Usaibatu ne Suka shigo tare da rangada Sallama, Alhmdllh Iman ta Furta tare da amsa musu Sallamar su,a Palo Suka zauna,Iman tace Laure Dan Allah a Ina Zan samu pad a garin nan? Mene Kuma Pat? Iman tace Baku santa ba? Audugar mata idan suna Al'ada fa,Usaibatu tace ohoooo mun Gane ai Bredin Mata Zaki ce,akwai a wani kanti mutum Daya ne ke siyarwa duk garin Nan Allah yasa ma mu samu,To kuzo muje ku raka ni mu siyo,Hijab Iman ta saka ta manta tana da aure kawai suka fita zasu tafi,Suna fita bakin gate Suka hadu da Nadeer ya dawo gidan, Ina zaki? Ina Ina ta Fara Hannunsa ta rike tare da jansa gefe Zo kaji,Gefe Suka matsa Wai za ayi sirri,Period dama na Fara yanzu shine zamu je na siyo pad,Su Usaibatu kunya ce ta kamasu suna gefe Jummala tace mun shigesu ta fada Masa shike Nan munji kunya yanzu yasan mune zamu rakata siyo Auduga,ya zamuyi da kunya? Yanzu yasan muma Muna Yi shike Nan mun Kade har gayyenmu cewar Laure,Usaibatu tace ai wallahi kawai mu maze kamar bamu san zancen ba,Muyi Masa wayo yasan ba ruwanmu,Sai ko Laure tace Matar Nadeer kizo muje gidan namu Mana ko kin fasa zuwa ne? An fasa zuwa cewar Nadeer kuzo muje ku Sha shayinku,Sum sum Suka koma ciki,Room dinta Iman ta shige Nadeer yabi bayanta,cikin sip ya bude ya nuna Mata wani Side taga pad ce da yawa a ciki yace gashi Nan,Mamaki da farin ciki ya Kama Iman,a hankali ta Furta Thank you,Ko kulata baiyi ba ya fice zuwa Dining,Jummala da shishigi tace ka Kira ta tazo ta zuba maka Mana Babu kyau mutum yayi girki wani yazo ya Fara ci baza ta ji Dadi ba,Karaf Laure tace a'a ai shi ya siyo komai shi ya kamata ya raba abincin,Ke Dan Babanki Haka yakeyi shi ke raba abinci,Jummala ce ta kwalawa Iman Kiran ta fito,Mijinki da kansa yake zuba Abinci Wai ke Haka ake yin aure ne? Ni Yasin ban taba ganin matar Aure wacce Bata kula da mijinta ba irinki,Sanda aka Daura auren Nan muna kallonki ranar yini Kika Yi kina wake wake kina murna,Amma yanzu kin kasa rike minjinki ko a kauye ba ayin Haka bare Yan Birni to wlh Kika sake kina gani wata zata Aure shi ko ya dawo da Kamla tsohuwar matarsa,.

Iman ta manta Nadeer Yana jinta kishi ya rufe Mata Ido tace ta Allah ba Taki ba,Kuma yarinya Bani ba kishiya sanda Zan Masa soyayyar a gabanki zanyi Kika San me nake Masa Mata da miji sai Allah,Nadeer dariya ta bashi ya murmusa,A'a mu bamu gani a kasa ba idan kina kula da shi to baza muga Haka ba,idan bakya sonsa kiyi magana da wuri mu Hada shi da wata Barira tana Nan Kyakyawa ce a garin Nan tana Nan Kuma Yasin mayyar maza ce taje birni ta waye,ki kiyaye Kar mijinki yaga Barira, Bariran banza Ni Kun San irin yanda nake kwace samarin wasu Allah ne ya shiryeni Amma hmm,munga Alama ga Kamla Nan kin sa an saketa cewar Usaibatu,ganin su Laure sun dameta tace kuzo kusha shayinku ku tafi gida dare Yana Yi akwai Kare a garin Nan,Usaibatu tace fatan Baki da Tsoro matar Nadeer sabo da Nan gidan naku gaba Daya Aljannu ne a yankin Nan,Da dare Hana mutane bacci sukeyi sai ki kiyaye,Iman Ido ta zaro tsoro ya kamata Dan Allah da gaske? Ki Bari da dare Zaki ji da kanki sai ki bamu labari,tsoro ya Kama Iman.

Sai da Suka cika cikinsu suka koshi sannan Suka yiwa su Iman Sallama,Iman tace gobe kuzo da yamma zamu dan zaga Gari,Allah ya kaimu Suka Furta sannan suka tafi Nadeer ya kulle gidan gaba Daya.
A Palo ya zauna Yana kallon DStv Iman tazo ta zauna itama,sabo da su Laure sun tsoratata sunce Aljanu ne a yankinsu, Har 10pm sannan Nadeer ya kashe komai na wuta ya wuce Bedroom dinsa,Iman kamar jela tabi bayansa,Wando tasa tight har guda biyu,tasa bra,vest tare da Sa wata karamar Riga a ciki sannan tasa Hijab gashi Ana uban Zafi Wai a Haka zata kwanta Dan Kar Nadeer yayi Mata wani abu shine tasa security a jikinta,Da mamaki yake kallonta ta kwanta a saman bed dinsa tare da dunkulewa wuri Daya ta kankame waje Daya,tana Hada uban zufa Amma Bata ji,Bai kulata ba daga shi sai boxers ya kwanta gefen bed tare da kashe light,motsi idan Nadeer yayi sai yaga Iman ta farka a firgice Bata bacci a tsorace take.

Sabo da tsokana a hankali yasa Hannu zai rage Mata kayan jikinta firgit ta farka tare da gyara Hijiba dinta tare da dunkulewa waje Daya taci gaba da baccinta.
Cikin tsakar dare 2:30 sai da Iman ta tabbatar Nadeer baccinsa yayi nisa ta tashi tare da lallabawa ta Rungume shi ta daura kanta a bayansa tayi luf,da taji zai farka ko zaiyi juyi sai ta sake shi ta koma can karshen bed tayi likimo ta Hana kanta bacci gaba daya.
A Haka har Bata San bacci ya kwashe ta ba.

Washe Gari da Asuba ta Riga shi tashi Toilet ta shiga tayi brush sosai tare da daura Alwala tana Fitowa ta Iske ya tashi Yana jiranta,Murmushi ta sakar masa,Toilet din ya Shiga shima brush da Alwala yayi a gurguje ya wuce masallaci sai da Gari yayi haske sannan ya dawo gidan sanye da Jallabiya Fara,Kana gani kasan Nadeer a cikin damuwa yake, Iman kuwa Bata koma Bacci ba gyaran gidan ta shiga Yi sannan ta daura Karin safe, sai da ta Gama komai sannan ta fada wanka tare da cakarewa cikin Wata Atamfa Me shegen kyau Brown and black riga skert ba karamin fito da Surarta tayi ba Tasha kyau tayi Daurin ture kaga tsiya.

Dakin Nadeer ta Shiga ba tare da ta kwankwasa ba,Lokacin ya cire towel zai sa Kaya yayi zigidir Iman tana shiga ta saki Salati tare da juya Masa baya da sauri tace kayi hakuri ban San Haka kake ba na shigo Ur breakfast is read....hhhhhhh...kafin ta karasa ta wani fashe da dariyar da Bata shirya ba,ta kasa danne ta Bata San ta fito ba,da gudu ta fice tana dariya,Shima Dariya ce ta kamashi yace Idan kin Isa ki tsaya,Tana dariya tace Ina Sam ba ruwana Ni Kam,cikin kana Nan Kaya ya hade blue trouser shirt Fara, fadin irin kyan da yayi Bata Baki ne,karshe ya Gama Hadewa Yana bulbula kamshi ya fito, sai da numfashin Iman ya dauke na Dan wani lokaci ta kasa daina kallonsa ta zuba Masa Ido a ranta tana nayi Dace Allah na gode maka.

Mikewa tayi tsaye suna facing juna tana murmushi,Baki ya tabe sabo da shi dai ya gaji da Murmushin Nan nata Wanda ya Gaza Gane dalinta na yin haka.
Bayan sun karya kamar wasu kurame basa magana da juna,Ita kunya shi Girman Kai,yamma likis su Usaibatu aka ci gayu zasu raka Iman Yawo Nadeer ma yaga zaman ya ishe shi ya bisu Suka tafi sai da Suka Gama zaga ko Ina na garin,Karshe sai da su Jummala Suka raka su Nadeer gidajen Iyayensu suka gaida su,ko Ina kallon su Nadeer akeyi kamar watan Ramadan sabon kamawa,sai kusan dare Suka dawo gida,Iman ta shirya musu Hadaddiyar jullop din taliya Tasha Kifi,suka ci tare da yin Sallar Isha.

10pm Suka Yi Shirin bacci Iman yanda ta Yi jiya Haka ma yau tasa tight har biyu ga bra ga Riga sai Hijab,Gefen Gadon Nadeer ta rabe har 2am Bata Yi bacci ba shi kuwa yayi baccinsa,A hankali ta dauki wayarta ta lallaba tare da haske fuskar Nadeer,Dan Jan lips dinsa ta kalla ta zaro harshe waje ta mayar a hankali tace wannan kyansa Kiss me zafi,zanji dadinsa kuwa,hancinsa ta kalla tare da Furta sai kace biro Yatsanta ta daura saman tsinin hancinsa ta Dan lakuta,hannu tasa a hankali ta gwale Masa Ido Kamar Madara ta Furta tana dariya kasa kasa,girarsa ta shafa tace Wai ya akayi tafi tawa yawa ai kyan wannan girar ace nice da ita.

Jikinsa ta shiga haskawa ba Riga a jikinsa sai sheki fatarsa keyi,Hijab dinta cire ta cire rigunan daga ita sai Bra sannan Wai tayi Hugging dinsa tace Skin to skin ko banza na yini Ina tunawa,Motsi ya danyi da sauri ta kashe haske tare da maida kayan jikinta, idonsa ya bude a ransa Yana dariya domin duk abinda Iman take Masa Yana jinta,Kamar Bai gani ba yace lafiya kike ta damun mutane da juye juye,Iman tana Mika da hamma Wai ita a Dole me bacci tace jikina ne naji kamar kaikayi sai Kuma Wai ta koma baccinta harda Mafarkin karya tana cewa Laure yawo zamuje,ki Kirawo su Jummala.
Murmushi ya saki tare da Kwanciya ya matsa gefe can a Haka bacci ya kwashe shi ba tare da ya farka ba sai Asuba.

Kamla soyayya tayi karfi tsakaninta da Kamal,soyayya sukeyi sosai suke kaunar junansu har ta Kai ga Kamla ta takura Masa ya turo manyansa,ba a dauki lokaci ba ya turo wasu manyan mutane Wanda da ganinsu kaga masu kudi,Sunzo da motoci na Gagara,Maman Kamla ta Rasa inda zata sa kanta sabo da murna,Kudin Aure suka kawo dubu dari da Hamsim,Ango yace a shirye suke kawai a tsayar da Rana,Daddyn Kamla shima Bai wani ja magana ba aka sa Rana cikin gaggawa wata Daya bikin Kamla sannan Daddyn Kamla ya Hana wani shagali Ana daura aure za a Kai Kano state inda gidan Ango yake.
Tuni Kamla aka Fara shiri da Gyaran Jiki,Su Jawahir dake Neman miji Ido rufe abin ya Basu mamaki yanda Kamla take da sa'a tana samun mazajen aure,Ibaad kuwa tsohon Saurayin Kamla da Iman ya koma Kasar waje da Zama inda yake Business a can ya samu wata Yar Ghana Kyakyawa ya aura bayan ya samu Kamla akan ta yafe Masa irin yaudarar da yayi Mata Amma tace ita wallahi Bata yafiya, Kamla ita Sam Bata yafiya a rayuwarta,a gaban Idon mutum zata ce ta yafe Amma a Bayan idonsa sai tace ita baza ta yafe ba.

Kwanan Iman da Nadeer biyar a kauyen Shanaye Sam Iman ta kasa gane Nadeer kullum sai ta ganshi cikin damuwa Babu walwala a tare da shi Wanda ba komai ke damunsa ba face Iyayensa da abinda ya faru tsakaninsu,Yana Palo zaune Yana kallon news Wanda a zahirin gaskiya ba News yake kallo ba hankalinsa Yana gida yana tunanin meke damun Iyayensu oho,Iman Cikin tsantsarariyar kwalliyarta ta zuwa club ta fito sanye cikin Wata Yar Guntuwar gown ko gwiwa Bata rufe Mata ba,kafafunta masu kyau santala santala Suka bayyana,gashinta yasha gyara tasa wata hula ta zamani yayinda gashinta ya kwanta a gadon bayanta Kamar baturiyar kasar England Haka ta fito,Nadeer kuwa Sanye yake cikin wani shegen yard fari sharara ba Karim shegen kyau yayi ba Kamar bashi da damuwa.

Hannun Iman dauke da Tire Wanda ta jero kayan ci da Sha a kai har ta ajiye a gaban Nadeer ma Bai San ta ajiye ba ya Lula tunanin duniya,a hankali ta zauna a kusa dashi,Lips dinta ta dauka a kunnensa Kamar me rada tace Sannu da tunani,da sauri ya dawo Hayyacinsa ya Dan kalleta kadan yayi murmushinsa me tsada itama martini ta maida Masa yayin da take Kallon labbansa masu kyau suna birgeta.

Lemon kwakwar data hada Masa shi ta tsiyaya Masa a glass cup ta Mika Masa ya karba Hannunsu ya Hadu dana juna wani yarrr Suka ji a jininsu da sauri ta janye Hannunta farar shinkafa da miyar jajjage ta zuba Masa a plate sai Hadin salat dinta,Yana ci Yana Santi a ransa Iman ta iya girki sosai,ita kuwa kallonsa takeyi tana Allah yasa abincin ya birge shi,Yayi Dadi? Ta tambaye shi,Tsokanarta yayi da a'a girkin Nan kamar a prison daurewa kawai nakeyi ki tattara ki bawa kawayenki su Laure,Fuska Iman ta Bata kamar zata Yi kuka jikinta yayi sanyi,Muryarsa ta tsinta yace I'm kidding you very Delicious.
Thanks ta Furta tana murna.
Kallonta yake Yi tana ta wani murna.

Kwana biyu Nadeer ya Fara canjawa Yana Dan sakarwa Iman fuska har Hira sukeyi,Har yawo suke fita cikin garin,5pm Iman ta fito sanye cikin Atamfa Riga da skert bedroom din Nadeer ta shiga Yana kwance sai Danna laptop yake yi,sallama ya amsa mata,saman gefen gadon ta zauna tare da cewa kayan miyar mu ya kare zanje na siyo ko kazo muje a siyo,kin fiye son yawo kullum sai kin fita a garin Nan,Shagwaba ta Fara tana doka kafafu a kasa Ni...Ni..Allah zaman gidan ba Dadi ne,Tsigar jikinsa ce ta tashi Yaji wani Dadi Ana Masa Shagwaba Kai Shagwaba tana mugun birge shi ga Iman dinsa ta haddace ta kullum sai tayi Masa ita.

Biye Mata yayi ya mike tare da canja kayan jikinsa yasa wata shadda ta gasken gaske,Baki Bude Iman ke kallonsa,Yatsansa Daya ya daura a kasan Habarta ya dago habar ya hade da bakinta,bakin ya rufe gam sannan yace rufe bakin to,dariya tayi tace Ni me yasa baka Yi min kwalliyar Nan ba sai zamu fita? Ai ke shigarki ta daban ce ban Fara Yi Miki Taki kalar ba sai nan gaba,Iman Bata Gane me yake nufi ba ta juya tana gaba Yana bayanta har suka kulle gidan.

Duk inda Suka ratsa kallonsu akeyi Ana labarinsu,Nadeer Kuma ga Iya muamula duk inda ya Iske mutane a kauyen sai ya musu sallama tare da daga musu hannu,baya nuna musu ya fisu sabanin wasu da Basu iya muamula da mutane ba Dole sai sun nuna banbanci,Nadeer sai yayi farin jini kowa sonsa yakeyi,gashi da kyauta duk inda ya zauna to fa sai sun Mori Nadeer,Iman gani tayi kawai Ana ta gaida Nadeer ko Ina suka zaga.
Haka Suka je Suka siyo Abinda suke bukata Suka koma gida.

Washe Gari Nadeer fita yayi Wata Majalisa ta matasan kauyen ya zauna Yana jinsu suna ta Hira,Wani matashi zai Kai Sa'an Nadeer Wato Aliko, Aliko yace Mata Mata ai Mata Sam ba Yan goyo bane matukar baka gamsar da matarka to ko duniyar Nan zaka Bata baza ka birgeta ba,cikin Mazan Audu ya tsomo Baki yace Haka mukayi da matata Rahina Billahillazi Aliko sai da na koma abin tausayi,Rahina har dungure min Kai takeyi sabo da bani da lafiya bana iya komai,sai da naje Kasar Niger na samu magani Ina fada maka sai ga Rahina Wai harda canja min suna daga Audu na koma Wai Milk candy,Aliko ya kyalkyale da dariya tare da Furta sai kace yaron yayi a Rasa Sunan da za a sa maka sai Milk candy shegiyar Alewar Yara,aini na Hanata sa min suna ta Kira Ni da Aliko na,Dan kuturin munafunci kana tsufa zata koma kiranka da Malam ba ruwana da wani canja suna,shike Yakubu yace Ni kuwa Wai a littafi ta ji Ana Kiran jarumin ciki da chakulety shike Nan na canja daga Yakubu na koma Chakulety,Su Aliko sai dariya Hhhhhh Ai Mata Sam Basu Yi ba,Dan Adam me daraja,Wanda Allah yayi shi da daraja Kuma aka zabi sunaye na kwarai aka sa mana,Yakub Sunan Annabi ne guda aka sa maka,Ni kuwa Aliyu Sunan sahabi Amma Suka kaskantar damu Muka Kare a shegiya Sunan Alawa.

Na Gama gano Mata wulakanci ne yasa suke canja Mana suna ba Wai wani soyayya ba,Audu yace Kuma abin Haushin ma duk harkar Zaki ake sa Mana shegiya alawar Naira biyar goma a Kira Dan Adam guda da Sunanta,Ina laifin su toron Giwa ko Zaki,ai sai ace dama dama,Amma sai wata

Please Login or Register in order to submit comment