Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a Habuja,Kusa da Nadeer Iman ta karasa tare da Rike Masa Hannu tana Hawaye murya na rawa tace muje kawai gida ka dauki motarka mu bar garin nan abin Nan ba na lafiya bane,Watarana zasu neme mu.

Ba musu ya juya Suka fita a kafa su Laure suna take musu baya,Jummala ce ta tare taxi Suka shiga su Hudu Mata a baya har Iman Nadeer Yana gaban Mota.

Gidansu suka je Suka kwashi iya Kayan sawa da duk wani muhimmin abinsu Suka zuba a motar Nadeer wato Marcedes Benz,a tsakar gidan jikin motar Suka tsaya Iman tace wanne Gari zamu tafi kenan? Karaf Laure tace kuzo mu wulla kauyenmu Dake garin Kebbi state,garinmu Yana da girma sosai,kaga Kai Mijin Iman Likita ne sai kaje can ka Bude mana Chemist a garinmu dama Babu me chemist,Allah sarki Mijin Iman daga babban Likita an koma Me Chemist shike Nan ka hau motar Rebas (Reverse) a rayuwa kaci gaba Amma dare Daya kayi you turn ka juya Haka tsarin Allah yake watarana na gaba ya dawo baya,na baya yayi gaba cewar Jummala.

Duk halin da Nadeer yake sai da yayi Murmushi Haka Iman ma,Nadeer ko a waya Bai sanarwa kowa ba kawai Mota ya shiga mazaunin Driver Iman tana gaba,Jummala,Usaibatu da Laure suna bayan mota,Iman tace baza kuyi sallama da Maman Kamla ba? Laure tace Taci Ubanta shegiya muguwa tayi kadan muyi Mata sallama ku ja mota kawai muyi tafiyarmu.
Yamma likis Haka su Nadeer Suka Yi Tafiyarsu tuki kawai yakeyi su Usaibatu suna ta Basu dariya yanda suke zuba kauyenci.

Laure ta kalli wani symbol na tallan sabulu matar jiki wata Kyakyawa fara tace lallai Ana cutar Mutanen birni Wai sai a samu hoton wacce dama Haka Allah yayita me kyau a samu a mannata a kwalin sai kaga Ana ta rubibin siya Suma Wai zasu Zama irinta Tirrr ai man Shanu yafi wannan sau dubu, Ai Malam ka samu Man Shanu ka lafka shine magana, Dariya sukayi Har Nadeer.

Sai da su Nadeer suka Yi nisa cikin duhun daj wurin 9pm Motarsa ta tsaya Dole ya gangare yin duniya mota Taki tashi,Su Usaibatu sun Saba da daji ko a jikinsu cewa sukayi mu fito a tura motar Nan cikin dajin Nan tunda ga hanya a ciki sai mu kwana a Nan da safe sai muci gaba da tafiya idan an gyara Amma idan Muka bar mota a gefen titi aradu Yan daba ko Yan kidnapping suna Nan wlh idan Suka Kama mu to fa sai Lahaula, Nadeer yace hakane yarinya waye to zai tura motar? Gamu sai mu tayaka,Nan take su Laure aka ci danmara za a tura Mota,Iman itama ta gyara zata sa Hannu Nadeer ya rike Hannunta tare da furta Banda ke mu zamu tura,Iyye wato na wani banza naka dukiya ko ita baza Tasha wahala ba sai mu Yan kauye da muka Saba da wahala cewar Laure,Nadeer yace itace ai zata sauke handbrake ta ciki mu Kuma mu tura,Haka suka Fara tura Mota Jummala tana Nishi tace Sama dai Me Chemist Iyaaaaa.......Yiiiiiii..Haka kuwa mota akayi cikin daji da ita yanda baza a hango ta ba a gefen titi.

Iman sai tsoro take ji Nadeer Yana kallonta,Laure tace a fito da Sallaya mu Shimfida Mu kwashi bacci,Nadeer yaja baya tare da Furta Haka kawai miciji ya sare mu ba ruwana,Iman kamar jela ta koma ta mannewa Nadeer.










To Fans Yanzu labarin zai Fara,salon Novel zai canja, Yanzu za a Fara Shan dariya, soyayya tare Tausayi zalla.
Wannan salon Novel din na musamman ne,Labari biyu ne a Novel guda Daya, labarin me tsayi ne sai Wanda yaji.

Ga masu bukatar samun Nishadi ya bi novel din Nan, Inshaallah ba asarar kudi zai Nishadantar.


NAN NA KAWO KARSHEN FREE PAGE.










AsmaBaffa.
[11/4, 11:18 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ



FREE PAGE






36-40




Official






By
AsmaBaffa






ADDU'AR KAWA SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨







ADDU'AR KAWA

Ga masu bukatar shiga Group dinsa
Naira dari biyu 200 ne.

Masu son siya ta Bank ga Accnt number

0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gt bank.

Masu tura katin MTN ta WhatsApp,transfer ko Vtu ga number da zaku
Tura
08033933642.

YAN NIGER
Ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.








Page naku ne

'YAN ADDUAR KAWA GP










Ganin suna tsaye Nadeer Yace to a shiga Mota mu sauke glass,Haka kuwa sukayi Suka shige mota tare da sauke Glasses su Jummala suna baya Nadeer da Iman suna gaba abinsu.
Nadeer sai wani share Iman yake yi a Dole shi ba sonta yake Yi ba.
Jin shurun yayi yawa Usaibatu tace Bari na Baku labari, Iman da Nadeer Suka kasa kunne suna sauraren Usaibatu ta Fara labari.
Wata Rana ce dai akwai Wani Babban Likita a Garin Habuja,Likitan Nan Kyakyawa ne na gaske jinin Larabawa ne, likitan ga gadara gashi me kudi,Katsam sai aka bashi sadakar wata Baiwar Allah me Gwigwiyayyen gashi, watarana ya saketa,sakinta ke da wuya aka aura Masa zukekiyar mace me Kama dashi,Ashe me farar kafa ce ba'a sani ba,kwana Uku kacal Ya Rasa komai nasa daga aurenta gashi zai Kare a kauye bashi da kudi zai koma me Chemist,Dariya Nadeer yayi,Iman tace wato nice me farar kafa ko? Kamla me Gwigwiyayyen gashi ba komai zaku ga farar kafa,baza mu taba Talauci ba ko a kauye Muka zauna Sai Ilmi yayi Rana.

Nufinku Zama zamuyi a kauye Sam gida Zan Gina lafiyayye a kauyen Wanda ko ku idan Kun shiga zaku ce a birni kuke, Idan zamu Sha shayi ai mu Alhmdllh cewar Laure, Amma ku Yan uwan Kamla ne baza mu taba Zama a garin su Kamla ba cewar Iman,Ai kauyen su Kamla daban,mu Yan uwan kamla ne Amma a wani kauyen Iyayen mu sukayi aure aka haife mu garinmu daban,mu fa kakanni muka hada da Kamla,kauyen su Kamla Yana da matukar nisa da namu,Okay yanzu naji magana Cewar Iman.

Mu dai gaskiya fita zamuyi mu zauna a waje muyi bacci,Katuwar Sallaya Iman ta Basu guda biyu Suka shinfida a jikin motar ba tsoro Suka Fara bacci,bayan mota Iman ta koma tare da kwanciya abinta,Nadeer kuwa kujera ya kwantar ya Fara bacci me nauyi.
Basu farka ba sai da Gari ya waye yayi haske tar sannan Su Jummala Suka farka sunyi wani futu futu dasu ga kayan jikinsu kodaddu,Sai lokacin Suka karewa wurin kallo Suka hango harda katon kogi na ruwa,ai can Suka nufa har Iman,Nadeer kuwa da ruwan Roba yayi brush da Alwala tare da gabatar da Sallah,Iman ma Brush da toothpaste ta dawo ta dauka,Su Jummala kuwa aswaki Suka balla a jikin wata bishiya suka goge bakinsu tas tare da wanke jikinsu harda sa sabulu a fuska irin Yan Matan Nan,Iman ma da sabulu ta wanke Fuskarta sukayi Alwala tare da yin Sallah,Hamma Laure tayi tace saura Abinci yunwa zata karasani,da Sassafen Nan Nadeer ya furta,kaji mu da Me Chemist mu ba irinku bane gaskiya,to ku Bari mota ta tashi first sai a siyi shayi a wani Gari Murna ta Kama su Jummala harda tafi,Usaibatu tace Yasin takarar kansila zamu tsaida Kai a garinmu,ba shiri Nadeer ya saki dariya Kamar cikinsa zaiyi ciwo,Iman ma Haka,Laure tace Honorable-Honorable sai kayi da ikon Allah,Iman tana dariya tace Allah ya tabbatar na Zama matar Kansila,Bakin titi Suka fita suka tare wani me mashine ya kira musu me gyara kuwa Dake tsakaninsu ba nisa da wani Gari,Me gyara Yana zuwa yayi gyara mota ta tashi,Kudin gyara aka biyashi suka Shiga Mota tare da ci gaba da tafiya,Basu Yi nisa sosai ba Suka tsaya a wani Babban Gari me dauke da katafariyar Tasha,Ciki suka Shiga Nadeer yace gaskiya kunya nakeji Ni Ni na tafi siyo shayi Gaskiya bazan iya ba,Usaibatu tace kawo Naira mu yanzu muje da kanmu abin kunya mu gaba Muka bashi ba Baya ba,mu da muke zuwa Tasha Talla,Laure tace sai muyi cinikinka mu sai da Kai a gabanka ba tare da ka sani ba,Kudin ya Mika musu, Su Uku Suka shige cikin Tasha, Gaban me shayi Suka karasa kowacce tace ayi Hadin Kauri,Haka aka hada musu me Kauri Harda Iman da Nadeer Haka Suka dinga kawo cups cikin mota har guda biyar shake da Tea hadin kauri,Jumma ta tsaya tace bread zaka bamu na Dari biyar manya guda biyu Yan dari biyu da Hamsim,me shayi sai washe Baki yake yaga ciniki,Miko Mana Butter waccen ta ledar Yar Dari da Hamsim ya Basu Butter Yar sachet,tace Miko min chanji na,Yana Bata chanji ta koma wajen me Doya da kwai, Ta siyo ta dari daban ta dari hudu daban,sannan tace bani kwai a cikin kwai guda goma,Haka a zuba Mata egg in to Egg guda goma cif ya Kama kowa biyu kenan su biyar,kudin da Nadeer ya Basu sai da suka Karar dashi sannan Suka dawo cikin Motar Suka kulle.

Kansila ga naka Laure ta Mika Masa,Nadeer yace bazan Sha ba kazanta kowa yasa Bakinsa a cup,Ke Iman Haka ake kula da miji? To wlh tun wuri kisa yaci ya koshi Dole idan ba Haka ba ya tintsirar damu a motar Nan,Yana Jin yunwa Ina zamuje gida lafiya,ki sani samun lafiyarsa samun lafiyar mu,so kike yunwa tasa ya dinga ganin Jirgi a Kan Hanya yayi zaton ko mota ce garin kaucewa ya Afka mu kasan Gingimari Trailer, dariya Iman tayi Usaibatu tace yo sabo da Allah fa Muna so mu koma muga iyayenmu lafiya ke da anyi magana sai dariya Baki kamar murfin buta,Dariya sukayi gaba Daya harda Nadeer,Jummala tuni ta Fara Kora shayinta tana lafkawa bread Butter ga Doya da kwai,ga Kuma Kwai cikin kwai,Su Usaibatu ma ko Bismillah Babu Suka Fara aika nasu,Iman gaskiya itama fa taji yunwa daukar nata tayi ta Fara da Bismillah tana ci taji Dadi kuwa,Laure Jakarta ta zuge da Hannu dayan da Bata taba kwai ba ta dakko yaji me yawa a jaka,Iman tace Ina Kika samo yaji? Bakin Laure cike da kwai tace a kitchen din Maman Kamla ranar da zamu Zo gidanku naci yajin naji shegen Dadi gata da rowa idan nace ta sanmin baza ta bani ba shi yasa na Samu Leda na juye yajin gaba Daya na gudo dashi,gaskiya Iyayenmu kawai daka yaji sukeyi Amma ba Dadi sai uban gishiri,Laure tace Musamman Inna ta Allah yagi ba Dadi girkinta.

Usaibatu tace Ahayye aini madarar peak ta Gari na sungumo na juye a katuwar Leda,Jummala tace Ni kuwa Dambun Naman da Kamla tasa akayi ranar da aka saketa shi na juyo Zan dinga ci a hankali abina, Usaibatu ce ta kyaftawa Iman Ido Wai ta bawa Kansila Abinci yaci,Kafada Iman ta makale Wai a'a,a hankali Laure tace a Baki Zaki bashi da kanki zai ci maza munafukai ne,soyayya yake so,Nadeer Yana jinsu Wai a Haka rada sukeyi.

Iman Wai ita irin taji Shawara ta juya zata Yi magana,Usaibatu ta radawa Jummala munyi Mata wayo yanzu zamuga Iskanci soyayya,Iman Tana wani sanda ta daura Hannunta a na Nadeer dariya ma ta bashi,Rasa me zata ce Masa tayi,shima Bai tsaya ya jirata ba kawai ya karbi Doyar dake saman cinyarta,yace a bani tea and Bread Banda Butter,Da sauri Usaibatu ta Mika Masa tana radawa Laure shu'umin yaji soyayya,Kinga Kamar asiri daga Dora Masa Hannu, Baki gani ba tana rike hannunsa yayi wani karkarwa Alqur'an Ni na gani da Ido na,Iman Dariya ce ta kwace mata sabo da ana Jin abinda suke cewa, cin abinsa Nadeer ya Fara Yi,Jummala ta zunguri Iman da Hannunta tace a Baki Zaki bashi irin na Yan film din turawa Wai ke ya kike Haka ne kamar daga daji aka kyankyashe ki,sai kace ba rainon carpet da madara ba cewar Laure,Usaibatu tace Ke wallahi Iman Durin Gona ce, kina yawa fa gaskiya baza ki taba cin marki a soyayya ba,0 kan jaki Zaki na ci kullum Yasin.

Iman tace Kai Na iya to ganin dama ne banyi ba,Rada Laure tayiwa Iman tace zamu fita maidawa me shayi kofinansa kafin mu dawo kiyi Masa Tausa yasha wahalar tuki Kafafunsa zafi zasuyi,Nadeer Yana jinsu Yana ta dariya a ransa wato su Usaibatu Lallai sai sunga soyayya zasu hakura.

Abincin gaba Daya sun cinye tas har Iman da Nadeer sunci,Suka zubar da ledojin,Jummala harda gyara cikin Motar,Iman ta wani fesa carfreshner,Suka fice zasu maida kofunan me shayi.
Har Suka dawo Iman da Nadeer ba Wanda ya kula Dan Uwansa,Iman kunyarsa take ji shi Kuma Girman Kai,Suna shiga ya fisgi mota da karfi,Laure tace uhmmmm kaji tuki daga Jin kalarsa anci an koshi ba yunwa a cikin Driver, kalar na dazu kuwa ka rantse wahainiyace ke tafiya sadaf Sadaf Kamar zamu saci kayan wani,Ana Jan mota Wani sakadaf sakadaf, Hhhh Suka Fara Dariya, Nadeer da Iman har sun gaji da dariya yau Kamar cikinsu zai ciwo.

Su Abba kuwa tunda Suka kori su Nadeer Suka ji wani sanyi a ransu sai lokacin Suka samu nutsuwa Hankalinsu ya kwanta Suka ci gaba da harkokinsa Kamar Basu Haifi wasu Yara ba,kawai Khadija da Raees suke iya tunawa sune yaransu,yayin da Khadija da Raees ko a jikinsu Basu Yi tunanin Nadeer da Iman ba bare ma suyi zancensu.
Maman Kamla kuwa dama sai da tasa yaronta ya bincika Mata komai,har Lokacin dasu Iman Suka bar gida sai da yabi bayansu a mota yaga Ina Suka dosa sannan ya dawo ya Bata labari,Murna a wajenta ba a magana,tace Kamla na godewa Allah da Bai taba saduwa dake ba bare ki samu ciki dashi,yanzu sai ki samu wani ki aura inda Zaki huta muma hankalinmu ya kwanta,Daddyn Kamla ne ya shigo sai yaji Sunyi dif sun daina Zancen Dan Kar yaji,kallon Maman Kamla yayi yace a sannu Zaki girbi abinda Kika shuka komai dadewa akwai ranar kin dillanci,Shuru sukayi shiko ya wuce ciki.

Bangaren su Jawahir kuwa sunji labarin komai sai dai ba a San dalilin korar su Iman ba,Sun Tausayawa Iman da Nadeer,Yayinda abokan Nadeer Suka dinga gwada kiransa Amma Bata shiga bare Iman data sake sabuwar waya da simcard.

Kwanan Kamla biyu da saki ta Fara daukan gayu tana yawo itace club da party iri iri a can ta hadu da wani Kyakyawan saurayi Dan 30yrs wankan tarwada Kamal,taga Kamal cikin hadaddun Kaya da gani kaga Dan manya,ga kudi da yake nunawa ba karya,Kamla farar Daya taji tana bala'in kaunarsa,shima ji yayi Yana son Kamla matuka, cikin Rana Daya Suka Saba da juna Suka shaku, har ta Kai ga Sunyi exchanging numbers waya,Kamal yace Kamla Ina matukar sonki Kuma wallahi da aure nake sonki idan har kin Amince,Babu komai a kanki kasancewar bakiyi kwanciyar aure da mijinki ba,Kamla tace Hmm Kamal kenan Nima Ina sonka Amma ban San Kai waye ba sannan da sana'arka,Naga dai sheda daya Kai me Addini ne sabo da ko club zaka Zo sai na ganka da katon carbi Wai Mene dalili ne? Hmm Ni Kamla da kike ganina Dan gidan malamai ne dake kauyen Funtuwa wato garin Dan Tintire,babana hamshakin Malami ne Nima Kuma Haka,Kawai nishadi ke kawo Ni club,kin San rayuwa ko Malam ne sai da nishadi,Ni nayi karatuna har Degree babban Lawyer ne a High Court Dake Abuja,Ina da kudi sannan idan ta Kama Ina yiwa masu kudi Addua a biyani, bazan Miki karya ba kinji asalina,Iyayena Kuma suna katsina idan Kun shirya Zan kaiku kuga asalina,Kamla tace ai na yarda da Kai ba damuwa Inshaallah hakan ma yayi Ina sonka Nan gaba sai muyi aure zanyi Shawara da iyayena,Kamal a zuciyar murna yake yi karyarsa ta hau,A ransa yace Zaki ga Lawyer sai Nan gaba.
Kamla gaba Daya ta fada son Kamla ta gigice Haka taje ta fadawa Mamanta komai,Daddy da Mama Suka ce ai in kina so mu bamu da matsala zamu bashi lokaci ya turo manyansa.
To Wai waye Kamal? Labarinsa gaskiya ne ko karya?

Jawahir da Hanan aure suke so suyi ruwa a Kallo Amma Babu Mijin aure,duk samarin da suke samu Babu na Aure a ciki, sau da dama suna haduwa su biyu su tattauna matsalolinsu Dake damunsu,Kamar kullum Hanan tana gidan su Jawahir suna Hira,Ga radio tana faman Yi,Malam Kabiru Gombe Yana waazi yazo karshe Yana kwararo Addua yace Matan da suke son aure Basu samu mazajen Aure ba Allah ka Basu miji na gar... Kafin Ya Kai karshe Hanan da Jawahir sun hada Baki da karfi wajen cewa Ameennnnnnnn....har ta Kai ga mutanen gidan harda Mummyn Jawahir sun fito a tsorace suna tambaya lafiya? a kunyace Hanan tace lafiya Mummy wlh Addua muka amsa da Ameen kawai,Yayan Iman tsaki yaja tare da Furta banzaye wallahi bazai wuce akan Mijin aure ba duk sun tashi Hankalinsu kamar zasu Kai kansu,Mukus su Hanan sukayi Basu ce komai ba.

Nadeer kuwa har gajiya yayi da tukin Iman tana kallonsa tasan ya gaji tace Yi parking na Karbi Driving din sai ka huta,Laure tace wani tukin kirki Kika iya salon ki jefa mu cikin Trailer, Mata tukinsu ai bana Babban titi bane,Suna gani Nadeer ya gangare Usaibatu tace Allah yaji kanmu yanzu wannan Yar Iman dince ta iya mota matar da ko zata girmemu Bai Fi da Shekara daya ba,Jummala Karaf tace kai kuyi Shuru na rabaku da Matan birni wannan da kuke ganinta tsohuwa ce maybe ta wuce Shekara ashirin gyara kansu sukeyi shi yasa basa tsufa kullum Yara Zaki dinga ganinsu,Karya kukeyi wlh ban Kai 20years ba Kar kuyi min sharri cewar Iman taji za a kushe ta a gaban mijinta,Kuma wlh indai Kuna min Haka baza ku sake Shan shayi ba,Munyi Shuru Yasin kiyi hakuri ai kamar jaririya Haka kike,nasan baza ki wuce Shekara Sha biyar ba cewar Jummala,Nadeer inda Iman ta tashi ya koma ya zauna ita kuma ta Fara tuki cikin kwarewa da nutsuwa har Allah ya kaisu Kebbi, cikin Birnin Suka Nemo lafiyayyen Hotel,Nadeer yace a Nan zamu zauna da Iman ku Kuma zuwa yamma Zan kaiku kauyenku tsalle Iman tayi ta dire ita wallahi baza a zauna a birni ba sai kauye,Bai kawo komai ba Nadeer Bai San asiri ya Kama Iman ba itama,Yace wanne irin kauye Ni Taya Zan iya Zama a kauye,ban taba ko yini a kauye ba bare na zauna cikinsa,Kuka Iman ta saki wiwi Kamar zata mutu, ganin Haka Su Jummala Suka dinga Rokon Nadeer su tafi kauyen su kawai shayinsu suke ji,indai Nadeer baije ba shike Nan Shan shayi ya Kare,Dole yace to shike Nan zamu zauna a can sabo da Iman Amma Ni gidana Zan Gina me kyau na Yan Birni kin yarda? Da sauri Iman ta goge Hawayenta tana dariya tace na Amince yace to muje,cikin Hotel suka dunguma ya Kama Musu Room biyu,su Jummala daki daya shi da Iman daki Daya,Nan ma Sai Iman tace ita fa Dole a dakin su Jummala zata kwana,Usaibatu ta Bude Baki cike da mamaki Amma sukayi shuru.

Ganin lafiyayyen bed su Usaibatu Suka dinga tsalle a Kai suna birgima Suna oh yau Wai mune a Otel harda kukan Dadi,Abinci lafiyayye me tsada aka kawo musu Suka ci Suka Sha sannan sukayi Sallah sai Kuma wanka,suna ta layin Toilet Wai sai sunyi Fitsari da Kashi a Shaddar Hotel sannan Suka tabbatar da sun ci Kudinsu ba ayi asarar kudi ba,Iman tana ta kallon ikon Allah,Ko wacce ta shiga wanka to fa sai ta hada da Kashi, Sunki Gamawa su ba Iman tayi wanka,ko sun Gama wata sai tace zata Yi fitsari itama,Jummala tace gwara ki koma dakin mijinki Iman mu Kam yau sai mun Kafa tarihi, Hakan da taji yasa Iman ta kwashi kayan da ta zabo a mota zata sa ta nufi Room din Nadeer, kofa ta kwankwasa, Bude kofar yayi,Iman ta kalleshi tun Daga Dama har kasa daure yake da towel a kugunsa kasa dauke idonta tayi sai kallon surarsa takeyi.

Ya akayi ya Katse Mata tunaninta,wata kunyarsa da sonsa ne ya sake shigarta,Iman Doluwa take Zama matukar tayi Ido biyu da Nadeer to fa Bata iya komai sai abinda aka ce Mata,gaba Daya wayonta guduwa yake yi,a hankali ta furta ban samu na shiga wankan ba sun hanani shiga sunyi wanka Amma sai layin Toilet suke Wai baza su Bari kayi asarar kudi ba sai sun Mori Kudinsu,Murmushi ya saki tare da matsa Mata ta wuce ciki tana tafiya tana waiwayensa ba tare da ta shirya ba ji kake kum ta bige goshinta,Kunya ce ta sake lullube ta ya kamata tana kallonsa ai sai ta fada toilet da sauri.

Shiryawa yayi cikin Wata Arniyar Jallabiyya fitted marar Nauyi yanda bazai ji zafi ba,Iman kuwa a toilet ta shirya kanta cikin Wani lace Maroon and Golden Riga da skert tayi kyau karshe,har Yar kwalliya tayi sama sama ta fito tsaf da ita, kayan data cire Yana hannunta,Nadeer a zuciyarsa yace Wai Dan Kar a kalli jikinta,Mene ban sani ba,Yana kallo ta Bude kofa zata fita yace kice su fito mu wuce Gashi har 4:30pm.
Koda ta shiga dakin su Usaibatu sun Gama shiryawa har sun fice suna jikin mota,Nadeer ta sanarwa shima ya fito Suka hadu tare da Iman Suka jera har compoud,Su Usaibatu suna ta faman kallonsu,Laure tace kallesu yanda suke taka kasa Kamar su Suka Halicceta sai uban gadara da yanga sukeyi,Ai Ana karya a birni cewar Jummala,Uhm kalle su ka rantse da Allah basa Kashi cewar Laure.
Nadeer Yana Karasowa Suka shiga mota Iman ya mikawa Mukulli ta shiga gaba ita zata ci gaba da tuki, Usaibatu tayi magana to dai a kula da gingimari motar katako Kar a rotse Mana Kai,Nadeer yace Kai kuyi Mana Shuru Surutunku yayi yawa Kuna sa min Headache ku bakwa rasa bakin magana ne Wai? Mudai Allah ya kaimu lafiya cewar Iman taja mota Suka tafi Su Jummala suna nuna musu Hanya har aka zo wani Dan kauye,Laure tace ga kauyen su Kamla,Kar ku sake tayi muku yanga ko Dan gaba Kunga kauyensu tana muku Iyayi ku Tona Mata asiri,kalli to gidajensu Basu Fi guda goma ba,Amma duk gida Daya sai an samu mutane sunfi dari a gidan,Lallai Ai kuwa ga Gari Nan mun ganshi cewar Iman.

Sunyi tafiya me matukar Nisa sannan Suka Isa kauyen Su Usaibatu,Usaibatu ta shaki Iska tare da furta kaji Gari me daraja iskarsa ma ta daban ce,

Nadeer ne ya Katse su da cewa yanzu Zan samu fili na siya a garin Nan? Sosai ma wajen me Gari zamu je ai,Iman tace da gaske gidan zaka Gina Mana? Kwarai ma kuwa Bari ki gani Nan da sati daya an Gama komai,Allah ya kaimu cewar Iman,Ameen Nadeer ya furta,Suna Hira sama sama har Suka karasa cikin Garin Kofar gidan me Gari.

Wanne Gari ne wannan?








Karshen Free page kenan fans, page Daya na Kara muku.








AsmaBaffa.
[11/4, 11:18 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ



NA KUDI NE







41-45






Official






By
AsmaBaffa






ADDU'AR KAWA SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨






Page naku ne

UMMU LATEEFAH
HADIZA
HALIMASCO









Garin Su Usaibatu me suna Gidan Shanaye,garin Fulani ne Gari me kyau zagaye yake da korayen Shuke Shuke da kayan marmari,ga wasu koramai Wanda suka zagaye garin,sanyi da Niima ke tattare da Gidan Shanaye,Garin akwai kyau da tsari Kauyen Fulani ne masu Wayewa da Dan Ilminsu dai dai gwargwado suna da makarantar primary ta Mata da maza,da Kuma secondary School na Gomnati,sai Kuma makarantun Allo da Islamiyya kwaya Daya tal,ko Ina ka kalla Shanu ne a garin shi yasa ma garin yaci Sunan gidan Shanaye,Ginin gidaje akwai na kasa,akwai na Bulon siminti da Kuma bukkoki na Fulani,garin

Please Login or Register in order to submit comment