Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kika Yi sabo da ya soki ku zauna lafiya,yau kece kike Neman Raina,Rai fa Kamla, idan kin kashe Ni ke dawwama zakiyi a duniya? Ni wallahi ban San rashin Imanin ki ya Kai haka ba,nayi nadamar saninki Kamla,Amma ba komai ki kwantar da hankalinki ko Zan mutu bazan auri Nadeer ba duk da cewar Ina sonsa na Gane so Ba a kyau yake ba,badan Kyau nake son Nadeer b,amma kije gashi Nan yau Zan bar Muku gidanku,Kuma na godewa Allah da naji kince dama tun farko Baki taba Sona ba,tsanata kikayi ba Wai Dan nayi Miki snatching din Ibaad bane kawai tsana ce yanzu naji Dadi.

Kamla ba kunya tace ae naji ki barmin gidan miji na ki Kara gaba bani ba Ke,idan mun koma Hutu mun hadu a school karki min magana karki nuna kin sanni bani ba Ke taja tsaki tayi ficewarta ta bar Iman a Nan tana mamaki.
Wanka Iman tayi ta shirya cikin Wani Danyen Lace Black and White dinkin Riga da skerta ne, tsayawa tayi taci uwar kwalliya Kamar wata Amarya,ba karamin kyau ta zuba ba,dukkan abin amfaninta da Kaya ta zuba a akwatinta tana zuba kamshi ta fito tana Jan akwati,Nadeer baiyi mamaki ba sabo da yaji komai abinda ya faru tsakaninsu da Kamla Yana jikin kofar kawai magana ce baiyi ba,kuma shi yasan Iman ta Dade da warkewa kawai kyaleta yayi.

Kusa da Nadeer Iman ta zauna a nutse tace Yaya Nadeer na war....kafin ta karasa yace na sani Iman kawai kallonki nakeyi har irin aikin da kike Yi kice Kamla ce,kunya ce ta Kama Iman na karya da tayi,Shuru tayi tace yau Zan koma gidan idan ka Amince,Ban Amince ba ya Bata amsa Direct,matar....ba ruwanki da ita,Dan Allah Yaya to muje ka kaini gida ya kamata su Umma su San na warke,sai yau Kika San da haka?.

Sanda Kika warke nunawa kikayi Kamla ta fisu muhimmanci,suna can suna fama da bakin ciki yarsu Bata da Lafiya kin warke fine ai ya kamata a sanar musu ko Dadi sai suji Hankalinsu ya kwanta yarsu ta samu lafiya kin San kuwa me iyaye ke ji idan yayansu Basu da lafiya suna wani Hali musamman irin lalurarki?

Anyway zamuje gida kowa yasan kin warke Amma Ni Zan aurar Dake tunda kyauta aka barmin ke, ke Kika ce Lallai sai a wajena Zaki zauna Kuma na karba kowa ya Amince kin Zama Kamar yata yanzu sai abinda nace,Kuma wallahi idan Kika sake Muka je gida Kika ce baza ki dawo ba sai na Tsine Miki Kuma binki zata Yi, Hhhhhhhhh Iman Bata San sanda ta fashe da dariya ba,Wai ya Tsine Mata Kamar ubanta,Ok kina mamaki ko? Ki zauna kina mamaki sai Kinga na daga Miki nono tukun zakiyi me dalili.
Dariya Iman ta sake kyalkyalawa da ita Wai zai daga Mata Nono.
Kamla ce ta fito a fusace taja wani wawan tsaki ta shige kitchen.










AsmaBaffa.
[11/4, 11:17 PM] Sis Asma: πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ



FREE PAGE






31-35







Official







By
AsmaBaffa









ADDU'AR KAWA SADAUKARWA NE GA
🚨'YAN KWANKWASIYYA🚨






RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku 300 ne


ADDUAR KAWA
Naira dari biyu 200 ne
Ga masu bukatar Shiga Group dinsa.


Masu son siye ta Bank ga Accnt number

0175487861,Asmau Garba Muhammad,Gt bank.

Masu tura katin MTN ta WhatsApp,Transfer ko Vtu ga number da zaku tura.
08033933642.

'YAN NIGER
KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39.






Page naku ne

AISHAT ADAM
KHADIJA DANDUME
MINERH
MAMIE IMAM
MAMEN SABEER
AUTAR MAMA
HAUWA U USMAN
UMMUL
HADIZA MUKHTAR
KHADIJA A HAMZA










Da Hannu yayi wa Iman alamar ta maida kayanta Babu inda zata je,Bata iya Yi Masa Musu Haka ta maida komai sannan fito,Sanye cikin 3qrt da t-shirt me gajeren Hannu kowa ya kalle shi sai ya Kara,Mikewa yayi tare da furta muje kawai,Bayansa ta bi Suka wuce,suna fita Kamla ma ta shirya ta shiga motarta ta bar gidan ba tare da Nadeer ya sani ba,Kamla Irin danginsu da yawa Haka suke basa son zaman lafiya,basa kauna suga ana Zauna lafiya,kullum a Neman masifa suke.

Bata Dade da fita ba Mamanta tace ta koma gida ga Yan uwansu Nan sunzo daga kauye zasu ga gidan aurenta,Dole Haka Kamla ta dawo ta Iske 'Yan Matan kauye su Uku Laure, Usaibatu da Jummala zasu Kai 17yrs, Dake Yan uwansu ne Bata wulakantasu ba sauka tayi musu ta ban girma,yan aiki tasa Suka Yi musu girki kala kala.
Su Iman kuwa gida ya kacame da Murnar ta warke Yan Uwa da abokan arziki sai tayasu murna sukeyi,Baba yace Amma ta dawo gida kenan tunda ta warke,Nadeer yace ta Dan warke dai ai Bata gama warkewa ba, a kwai sauran Rina a kaba.

Baki Iman ta Bude tace ban gane na dan warke ba? Na warke Ras Ina Gane komai,Mama tace kyaleshi ai kin dawo gida shi yaje can da Amaryarsa kina gida, Umma tace ai Alhmdllh tunda Abu yayi kyau sai ki dawo gida,Baba da Abba da shigowarsu kenan Suka ce ai Zama Kuma ya Kare sai ki zauna Kai Nadeer Ka kawo Mata kayanta.
Zumbur Nadeer ya mike yace to Iman dai da kuke ganinta Bata Gama warkewa ba,kawai a Haka zaku ganta kamar lafiya Amma Sam Bata warke ba,Ai kwakwalwar ce ta hargitse Ciwon ya motsa shi yasa tace ita sai an kawo ta wajenku,Karka Raina Mana hankali Mana yarinya ta warke kace Bata warke ba cewar Abba,Wato Ni gaba Daya na Gama ganewa a gidan Nan abinda ake so ake Yi min duk wata marar hankali da ita ake hadani, an bani wacce bana sonta wacce gwara marar kwakwalwa da ita,an hadani da Iman marar lafiya yanzu Kuma ta warke ance ta dawo gida,Ni shike Nan a Haka Zan Kare? To tunda abin Haka ne Iman Bata Gama warkewa ba gata Nan na bar muku idan tayi kisan Kai Kar a Nemo Ni,juyawa yayi zai tafi Da Gudu Iman ta Suri Jakarta da mayafinta tana cewa Umma na tafi sai watarana,Wuce Nadeer tayi ta juyo suna facing juna a Haka take tafiya suna dariya,Su Abba suna kallo Suka shige mota tare da barin gidan zuwa gidansu.

Kasancewar sunci sun koshi a gida Basu tsaya siyen Abinci ba gida Suka karasa Ba tare da wani yayiwa wani magana ba,Nadeer Yana gaba Iman tana bayansa Suka Shiga Palo dauke da Sallama a bakinsu,Fuska Kamla ta Daure,Ga su Usaibatu sun sa tv a gaba suna kallo sun saki Baki da hanci kamar zasu shiga ciki,Laure ta kwalalo Ido,Ganin Nadeer Suka firgita tare da gudu Suka boye a bayan kujera suna Kiran Aljani,Su Basu taba ganin me kyau haka,Sai da Kamla ta zagesu Dalla malamai ku fito wannan ne Mijina banzaye,A hankali Suka fito suna washe Baki Suka gaida Nadeer da Iman,a Palo Suka yada zango, suna zaune Babu Wanda yayi magana,sai Muryar Jummala aka ji tana magana ta Mika hannunta jikin plasma tv tana cewa wayyoooo Kunga Baturiya tana yanke gashinta Ina Nan Ina fama da Gwigwiyayyen nawa, Dan Allah ke kuwa karki yanke Mana,Dariya Iman tayi, Usaibatu tace wallahi kuwa Yar Uwa Iman kike ko? Yanzu ki duba ki gani sabo da Allah yanda turawa ke zaftare gashinsu mu Muna Nan muna fama da namu Kamar Shekar kurciya, Aunty Kamla ma Baki ga nata ba inda kisan Hammatar me tsiren Garin mu,Dariya Suka saki harda Nadeer, kallon Nadeer Jummala tayi tace ai wallahi kaga gashin Kan Nan naka to yafi na Kamla Sau malala gashin Tinkiya,Allah ya jarabce ka Kai Kam da Auren mace me Gwigwiyayyen gashi,Nadeer Yana dariya yace ai kullum idan Zamuyi bacci Dankwali take sawa ta Daure abinta,Karaf Laure tace to ka Bari idan tana bacci cikin dare ai dankwalin zai warware ka lallaba ka gani Billahillazi kaf danginmu bamu gaji gashi ba,Allah ya gani mu ba jinin gashi bane.

Kamla ji take Kamar ta Hadiyi zuciya sabo da takaici,Kowa dariya yakeyi a palon Kamla sai Iman ta Raina ta Fara zazzagawa Iman masifa,Murmushi Iman tayi tace Kamla karki kaini bango wlh Baza Kiji Dadi ba,naga Baki San mutunci ba,daga yau na daina daga Miki kafa,ai Ni baza ki birgeni ba Iman sai Naga kin Auri Nadeer, Jummala tace Heeeee Yawwa ke kuwa Iman Aure shi wallahi mu gani.

Laure ta kalli kamla tace Anty Kamla ai ki godewa Allah kin samu miji Haka,Ni wallahi nasan sai dai a Bawa Nadeer ke Sadaka Haka kawai saurayi kamarsa bazai ganki ya soki ba,Jummala ta karbe zancen da cewa musamman idan Kamla tayi dariya ai ko waye guduwa zaiyi idan yaga hakoranki wargatsatsu Kamar karshen Brushi irin Brush ya tsufa din Nan,Nadeer duk iya daurewarsa sai da ya fashe da dariya,Usaibatu tace wallahi kuwa shegen hakora Kamar karshen Brushi,Mikewa Kamla tayi ta Fara kwadawa Jummala Mari,Iman tace me tayi Miki Kamla? ya Isa Haka Iman ban son Hayaniya cewar Nadeer.
yanzu na Fara tunda Bata San mutunci ba,na fiki iya shege Kamla gwara ma kiyi biyayya.

Sai dai Uwarku ko Ubanku suyi Biyayya,Ido Nadeer ya zaro Ransa bace yace Iman dakko min Biro da paper nasan Me take bukata,Kin tashi Iman tayi tasan me Nadeer Yake Niyyar Yi,Tsawa ya buga Mata me tsananin razanarwa Wanda Ba Iman kawai ba har su Jummala sunji tsoro, Kamla tace idan Uwar wani ta Haifi danta da jini a sakeni, Ba shiri Iman ta je ta kawo Masa Nan take ya dankarawa Kamla saki Daya tare da jefa Mata, tashi ki tattara tsumman kayanki ki bar min gida na,kije ki auri duk Wanda kike so Allah ya gani ba abinda banyi ba na ganin na danne zuciyata, Baki da Amfani a wajenmu gaba Daya,bazan zauna kina zagin Iyayena ba.

Kamla duk rashin mutuncinta sai jikinta yayi sanyi Bata San sanda ta fashe da kuka ba, su Usaibatu ma Suka saki kuka me jiniya, Jummala tace yo wannan ai mu Kika cuta, mu ya Dace mu fashe da kuka,Nima da tuni na barke da kukan Nan dannewa kawai nake Yi cewar Laure.

Bayin Allah bamu ga ta Zama ba anci uban shugaba saura mu yaran Ogar, sai kuzo mu zargawa karenmu Igiya
,Muna murna munzo cin arziki zamu huta a Habuja (Abuja) Bakin Halin Kamla
ya jawo mana,Dan shayin Nan me kauri da muke jira mu zuka gobe Haramiyar mu cewar Laure, Hmm ke dai Bari Dan lemon Nan baza mu Sha ba sai dai Kunun Zaki na kauye musha mu barke da zawo,Iman tace ku kwantar da hankalinku mu zauna tare kafin muma mu bar gidan,Shewa Suka saki Heeeeee wallahi mun gode Ai kinfi Kamla kirki ma,Kamla ce ta kwaso akwati sun Kai goma Sha na kayanta gaba daya tana kuka, su Usaibatu ta kalla tare da furta

Kuzo mu tafi ai gidan bana ubanku bane, ke dai da aka saki ki tafi Amma mu munyi sabuwar Anty baza mu koma gidanku ba sai Jarabar rowar Abinci wajen Mamanki ba ruwanmu Naji Dadi shine Gari su Jummala Suka Furta suna tafi da Hannayensa.
Haka kuka ce? Ae duk bakin cikin shayi da Bredi kike Mana Kuma sai mun Sha,Laure ta kalli Iman tace ai Zaki dinga cika Mana babban Kofi ko? Sosai ma harda kwai da dankali ga farfesu,Dariya Suka saki to kinji gidanku kuwa a Dan mitsil din Kofi ake zuba Mana kamar mun roka tsakani da Allah Kamla mu bama ci Muna koshi a gidanku sabo da rowar Gyatimarki tayi yawa, Wai ku Yan gayu turawa shegen ciki duk yunwa Ina wani gayu ciki da yunwa to mu muna Nan ke aka saki Banda mu.
Kwafa Kamla taja tayi waje tana Hawaye.

Koda Kamla taje gida Karya da gaskiya ta shirya sannan taki nuna takardar sakin tace itace tayi yaji kawai,Mamanta tace zauna wlh ko yazo Biko baza ki koma da wuri ba sai yasha wahala a hannunmu kyaleshi zanyi maganinsa Iyayen nasa sai na raba shi dasu sun kore shi sun Hana shi komai sai yasha Talauci.
zanyi maganinsa da malamai Zan Yi maganinsa.

Murna Kamla tayi tace Ba damuwa.
Nadeer kuwa Sabo da Gudun sharrin su Kamla ya shirya ya tafi gidansu tare da Tara dukkan Family Banda Iman wacce tana Gida tare da su Usaibatu suna ta girke girkensu suna kallon finafinai.
Nadeer a nutse ya bayyanawa su Abba halayen Kamla duk abinda take Masa tun farkon aurensu,Mama tace zata aikata,Abba yace Karshe me ka yanke? Na sake ta Abba,Babu Wanda yaga laifin Nadeer Nan Take Abba yace maza Kira Min Iman tazo,ba waya a hannun Iman sai driver aka sa ya dakko Iman tsabar Shishigin su Usaibatu Saida Suka biyo Iman tare Suka Zo,Abba ne ya kalli Iman yace Iman kina son Nadeer? Wani banbarakwai Iman taji Maganar,idan tace Bata sonsa tayi karya,Nadeer kallonta yakeyi kawai gumi Yana keto Masa Kar Iman tace a'a itama shi take kallo,A hankali yanda Iman kadai ta Gane me yake cewa yace kice Yes daga baya zamu warware matsalar,Kar a bani wata Banzar pls.... Nan take Iman tace cike da kunya Ae Abba,Ihu da tafi su Laure Suka saki Kamar Kanwar Ubansu ce Iman suna yeeeeeeee Ayyiririririri su Mama sai dariya Suke Yi.
Makwafta Abba ya Tara Yan Dattijai a gaban shedu,Baban Iman Shine ya karbi Waliyyi na Nadeer Ita Kuma Iman Abban Nadeer tare da wasu mazan Aka hada komai,Nan take Nadeer ya biya sadaki dubu dari Aka daura Auren Iman da Nadeer, A gaban Iman da sauran Family aka Daura,Iman tafi kowa murna,Yau auren gata akayi Lallai Nadeer Dan lele yau ka saki Mata a daura maka Aure da wata.

Bayan an Gama komai iyayen Nadeer Dana Iman sunfi kowa murna,Sai bayan anyi komai aka dinga bige bigen waya Nan take labari ya watsu, Bayan komai ya lafa Nadeer ya Shiga part din Su Umma ya iske Iman wacce yanzu Kamar Wasa ta Zama Matarsa,a hankali yace ki zauna a gida daga yau,Ai baka Isa ba yaro sai ka dauketa ku koma Inda kuka fito cewar Mama Dake shigowa.

Usaibatu tace wallahi kuwa ai yau party zamu tayasu a gida Ayiririri yau akwai Shagali,zamu Sha lemo mu more,Iman dai kunya take ji yayin da Nadeer tuni ya shiga mota ya bar gidan shi a Dole Yana Gadara Ango ne ya Gama samun Iman.

Ba a Dade ba Kamla ta samu labari Har Nadeer yayi aure,ya sake ta da safe da yamma an daura Masa aure da Iman,a yau Kamla ta tabbatar da Iman tayi Phd a snatching,a fili tace Allah ya Isa, kamar zata Yi hauka ta fesawa Mamanta Labari,Ko Gama ji Maman Kamla Bata Yi ba ta figi gyale sai gidan Kawarta Nan Suka wuce gidan Boka tana haba na gaji da Gafara sa banga kaho ba,Ina ta wahala gwara na shiga malamai naci uban yarinyar Nan Iman,Abinda yake so bazai samu ba,Wallahi ko Zan tafi tsirara bani kyalewa.

Wani kauyen Fulani matsafa Suka shiga Dake kauyukan Abuja, wani Mutum Suka Iske Kamar Mahaukaci a cikin Bukka jikinsa gaba Daya layu ne da guraye.

Bayan sun Karasa Inda yake,tun kafin suyi Masa bayani ya Basu labarin me ya kawosu,Maman Kamla tace Lallai wannan ya shahara ji yanda ya lissafo abinda ya kawo mu, Mijin Yarki yanzu so kike Yarki ta koma gidansa? A'a ba burina ta koma ba,wulakancin da yayi Mata nake so na Rama,Ni bana Yafiya malam sabo da Haka a sa Mata lalurar da baza ta haihu ba,Shi Kuma a raba shi da Iyayensa su koreshi shi da Matarsa ya zauna a Talauci shike Nan.
Dariya Bokan yayi yace bazai ko Sadu da ita ba bare ma yaji Dadi har ya haihu ki bani kwana Uku Zaki ga aiki,bana bukatar sisinki sai aiki yaci,Amma idan aiki yayi duk abinda nace shi Zaki bani kin yarda? Kai ta daga tare da furta na Amince Dan Allah Boka ko a birni Kar a Bari Nadeer ya zauna sabo da Kar Wani me kudi ya taimaka Masa,a cillasu can kauye suci wahalarsu da Matarsa.
Baki da matsala cewar Boka.
Bayan sun Gama tafiya sukayi suna jiran aiki yayi.

Shi kuwa Nadeer Yana can wajen Frnds suna ta tayashi Murna Bai dawo ba sai 8pm Lokacin Umma ta takura Iman tana Shan kayan gyaran jiki,har sunyi ma Iman Hadi sosai zata tafi dashi,Iman Haka kawai sai Murna takeyi ta Auri Nadeer shima Haka,Sai wake wake takeyi tana faman washe Baki,Su Jummala suna ta kallon ikon Allah.

Wanka Iman ta sake taci kwalliya cikin Wata Turkysh Abaya me shegen tsada da kyau,ba karamin Haduwa tayi ba.
Kamar ka sace ta,Kayanta da yawa ta zaba ta bawa su Usaibatu suna ta murna da godiya.
Tana kitchen tana Hada Fruits salad Nadeer ya shigo Palon Umma Yana duba Iman zasu tafi gida, da Ido Laure ta nuna Masa kitchen tana murmushi,Kitchen din ya shiga,Kamshinsa kawai da Iman taji shi yasa taji Zuciyarta tana wani uban bugawa Kamar zata fito ga wani tsoronsa da kawarjini da ya sake shigarta sabo,Motsi ma kasa yinsa tayi.

Ku zauna da wannan yaran anan kafin mu koma gida Mama tace sai Nan da sati daya zaku koma lokacin wannan yaran su Laure sun tafi kauyensu.
Dadi Iman taji har Bata San sanda ta juyo ta kalle shi ba,Yana gaf da jikinta tana juyowa sai da jikinsu ya Hadu wani shock Suka ji gaba dayansu da sauri Iman ta matsa duk ta diririce.
Usaibatu ce ta shigo Kitchen zata dauki ruwa kamar gidan Ubanta,Nadeer ta gani kamar zai shige jikin Iman da sauri ta juya ba tare da sun ganta ba,Cikin su Laure ta koma ta zauna tana Ni Na shige su Yau saura kadan na makance, me Kika gani? Jummala ta tambaya tana son Gulma ,Laure tace Iskanci ake tayi a kitchen daga daura aure in fada muku Yana makale Lallai na yarda Yan Birni Yan iska ne,Muma Bari mu leka mu gani cewar Jummala ta mike tana lallabawa a hankali ta leka kitchen sai ta hango Iman da Nadeer Yana tsaye daf da ita kamar zai shige jikinta,Baki Jummala ta Bude ta dawo da baya cikin sanda ta radawa Usaibatu bariki ake bugawa a can Yasin ki bawa idonki Abinci tun kafin a barki a baya,itama Usaibatu da sauri ta lallaba ta leka kitchen ta hango Nadeer da Iman suna kokawar daukan Spoon Hannunsa ta rike zata kwace Amma ta kasa,Hannaye Usaibatu tasa tare da rufe bakinta ta dawo inda take tace Wallahi Allah da gaske ne na gani Kinga yanda ya rike ta,Bari na sake lekawa na gani Da Rarrafe Laure ke tafiya a kasa taje ta sake lekowa ta dawo da Sauri.

Nadeer Bai bar gidan ba sai dare bayan su Umma Sunyi musu Nasiha sosai,Yayin da Maman Nadeer ta Fara shiryawa Iman Kayan lefe,kudi Kare magana indai da kudi yanzu za ayi komai a wuce wurin.

Kamla kuwa Babanta ne ya dinga cin Ubanta fada ba irin Wanda baiyi ba,karshe yace ga gidan Nan sai kizo mu zauna kici uwar da ake ci a cikinsa tunda bakin halinki bazai Bari kiyi biyayyar Aure ba,Ita kuwa Kamla da Mamanta fadan da Daddy yayi ko a jikinsu Wanda yayi nisa baya Jin Kira.
Washe Gari kwana Daya da Daura Auren Iman Su Raees da Khadija sai tsiya suke yiwa Iman Wai ta sake kwacewa Kawarta miji ta Zama cikakkiyar Snatcher yayin da su Usaibatu suke Jin dadin Zama dasu Iman kamar sune 'yan Uwansu.
Cikin kwana biyu Mama ta Hadawa Iman Lefe akwati Takwas Kaya masu tsada sannan aka kaisu can gidan su Iman Dake Maitama.
Har sabuwar waya me tsadar gaske Abba ya siyawa Iman,Raees Kuma laptop ya canja Mata sabuwa dal.
Tunda Nadeer ya bar gida har kwana biyu Basu ganshi ba.

Gaba Daya sai Iman taji tana kewarsa shi kawai take son gani ko taji sanyi a ranta, Me Lalle Umma ta Kirawo aka zanawa Iman na Amare gashi Tasha gyara ciki da waje na kwana Uku tayi kyau matuka,Lallenta ya zanu matuka abinka da harkar manya gata Yar Fara Kyakyawa sai ta koma Kamar a sace ta.

Abba Ne ya shigo gida a matukar fusace Yana ta masifa,Shima bangaren Baba Haka su Iman Suka ga ya shigo Yana zazzaga masifa,Taya ke Iman Zaki Raba Nadeer da Matarsa Kamla? Abin naki ya Kai Haka burinki ya cika kin korar Masa Mata to wallahi bazan zauna da 'ya maciyar Amana ba,Ashe fasikanci kukeyi ke da Nadeer to wallahi karki sake na sake ganinki a gidana har Abada kije can wurin Mijin naki ku karaci rayuwarki,Baba ban gane....Tasssss ji kake Baba ya wanke Iman da Mari tare da nuna ta da yatsa yace Bari kiji Ni da Yayana munje har gidan su Kamla munji komai abinda Kika Yi,Umma ce ta fito da sauri tace lafiya Baban Raees? Gata Nan Yar iska marar mutunci ta zubar Mana da kima a Idon duniya,Wai Ashe yarinyar Itace tasa Nadeer ya Kori Iman sannan Ashe ta Dade da warkewa Bata fada Mana ba tana can suna kwana tare da Nadeer Suna tafka masha'a, Umma da farko Bata yarda ba Amma ta Rasa dalili sai taji kawai ta yarda itama hakane Nan Suka budewa Iman Wuta,Su Usaibatu sukayi Miki Miki ,Laure tace wlh karya Kamla da Mamanta keyi wallahi itace ta jawo aka saketa,a gabanmu aka Yi komai Iman da Nadeer Basu da Laifi,Rufe min Baki ko na karyaki kema cewar Umma,Baba da kansa ya budewa Iman kofa tare da furta fita ki bar min gida,Sum sum Iman ta dauko abin amfaninta da take bukata a wata jaka karama ta fito tana Rusa kuka tana Rokon Umma da Baba tana Basu hakuri Amma Ina Asirin su Kamla ya Kama su Baba,Raees da Khadija sun San su Iman Basu da Laifi Amma sai bakinsu yayi nauyi Suka Gaza ko magana suna kallo Iman ta fice,Baba ya kalli su Usaibatu yace ku bisu ku tafi munafukai masu son abin duniya,kunji dadi ta Baku cin Hanci Kun guji Yan uwanku na jini,Usaibatu cikin tausayi tace ayi Hakuri Baba Allah sarki shayi ne me kauri ya tsaida mu, miyar Dage dage da jar suya yasa Muka zauna Amma mun tafi muma Suka ebo Yan kayansu a ledar Viva Suka biyo bayan Iman.

Suna fitowa compoud Suka hango Nadeer Shima da Abba a compound ga Mamansa suna ta masifa kamar zasu ci Babu,Abba yace daga yau komai Dana baka na kwace abina har gidan da kake ciki ai bada kudinka ka Gina ba,motoci ma duk nawa ne na siya maka,motarka Daya ce tal Marcedes Benz ita nasan ka siya da kudinka sabo da Haka ka ajiye komai nawa ka dauki matarka ku bar min gida,Asibitin ma Zan bawa wani Likitan yaci gaba da aiki tunda baka San kima da darajar mu ba,Mama ta kalli Iman ta furta kin bani kunya Iman Dama baki canja Hali ba to kun yiwa kanku,Iman da Nadeer kawai mamaki abin ya Basu Wai har Su Kamla ne zasu fada musu karya su yarda,Godiya yayi ga Allah sai da aka Daura musu Aure da Iman sannan hakan ta faru,Mamaki ya Hana Nadeer cewa komai da yasan Kiran da Abba yayi Masa a waya kenan da Bai Zo yaga wannan bakar Rana ba.

Abba Ne ya kwalawa me gadi Kira Bude musu gate su bar min gida,Usaibatu tace wayyo mu Kam bamu da rabon Jin Dadi

Please Login or Register in order to submit comment