Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ[11/4, 10:56 PM] Sis Asma: BISMILLAH
COPY BY ZAINAB BUTALAWA





πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ
ADDU'AR KAWA
πŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺπŸŸͺ




FREE PAGE







1





Official






By
AsmaBaffa






ADDUAR KAWA GABA DAYANSA NA
🚨YAN KWANKWASIYYA NE🚨







ALHMDLLH Allah ya kawo mu sabon Novel Kamar yanda Muka fara lafiya Allah yasa mu Gama lafiya Dani da ku fans.



SANARWA....

NA CANJA ACCOUNT NUMBER,KAR WACCE TA TURA KUDI A TSOHO NA DA.



RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne.

'YAR KWANGILA COMPLT
Naira dari Uku ne.


ADDUAR KAWA
Domin shiga Group dinsa kullum za a ga posting
Naira dari Biyu 200 ne.



Masu bukatar siya ta Bank ga account number

Accnt number 0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gt bank.

Ga masu son tura katin MTN ta WhatsApp ko masu yin Transfer na Kati ga number da zaku tura ko kuyi min magana Kai tsaye ta wannan number...
08033933642







Yawan comment yawan Posting.









Page din na farko naku ne gaba dayanku MASOYANA.











Raees fito Mana ku tafi sai Iman ta makara yau kasan tana da lecture 8am ga Driver Yana jiranku idan Kuma halin naka zaka Yi ka jira kayi driving kanka school ita ta wuce,matashiyar da aka Kira da Iman kyakyawar gaske Fara Amma ba irin fal ba,fari ne me kyau kamar ita tayi kanta,cike da Gadara ta dauki handbag dinta tana cuno Dan jajayen lips dinta tare da furta Umma kyaleshi Ni nayi gaba Yana Bata min lokaci kin San halin Ya Raees baya shiri da wuri,to ai shike Nan Iman a dawo lafiya.

Mota ta zaba a cikin motocin katafaren gidan ta shiga ko Driver Bata nema ba ta tuka kanta zuwa school,tana shiga kawayenta Suka fito suna jiranta,Hanan ce ta Fara Furta kin fa hadu Yan Mata,Kamla ta amshe da furta waye ya kaimu a school din Nan ga kyau,ga Ilmi ga kudi ,Jawahir tace yes oooo,Murmushi Iman tayi tana wani Shan kamshi tana basarwa tace mu wuce Frnds, sanye Iman take cikin Wata dakakkiyar Shadda Brown Tasha uban dinki me kyau,takalminta da Jakarta designers milk color ta yafa mayafi Karami me tsada.
Gaba Daya kawayen Su Uku yaran masu kudin gaske ne domin iyayen kawayen Iman duk sunfi Baban Iman kudi kasancewar shi a karkashin yayansa yake.

Yanda Iman ke ji da kanta tafi Yar shugaban kasa ma,wasu suna zaton ko Dan tana da kyau ne, Ashar Iman ta dura tare da Jan tsaki Wai kunji Malamin Nan ba zaizo ba yau yasan Kuma shi kadai muke da lecture yau a school din Nan sabo da shi Muka Zo,wannan wanne jaki ne? Dariya su Kamla sukayi tare da furta mu a dadinmu sai mu fita yawo dama nayi sabon wani Handsome guy Yana so na sai na kirashi ya kaimu yawo,Motata ya zanyi da ita? Iman ta furta tana turo lips irin na masu kudin Nan,Driver yazo ya dauka Mana,no Umma kin San halinta fada zata Yi min,To Mene Muna son chilling Amma iyaye wlh suna takura mana,Hausawa kwai matsala ba freedom cewar Hanan,ajiye motar a Nan idan mun dawo sai a daukeki a Nan ki wuce gida Kinga baza a Gane ba cewar Jawahir,Tafawa sukayi, Nan take Kamla ta Kira sabon saurayinta,Ba afi 15mnt ba sai gashi a wata mahaukaciyar mota me tsadar gaske,Iman tace halina da ke Kamla Allah Yana Baki kyawawan samari matasa masu kudi Kuma,Amma Ni jaraba inda kisan na Hadiyi tsaka kowa ya tsaneni duk kyawu na sai shegun tsofaffi masu shirgegen ciki Kamar kwarya,Kullum Addua nake Ina idar da Sallah nake cewa Allah miji fari Kyakyawa me hanci,Ni ko bashi da kudi fari Kyakyawa me hanci me so na Amma Kinga Shuru ,Kai Iman ta daga sama tare da furta Allah ka bani miji Kyakyawa fari me hanci Kamar Aeria Dan gayu,me tsafta,Dan matashi Dan camai camai me iya love,ya Allah me sexy eyes,Dariya su Hanan Suka dinga Yi domin sun Saba da Jin Adduar Iman.

Saurayin Kamla ne ya fito wani Kyakyawa chocolate Dan matashi ga daukan wanka abin gwanin Sha'awa,Iman tana ganinsa a hankali tace Allah ko irin farin wannan ne Ina so,Allah ko kamar wannan ne,Wow Kamla dan ubanki ki aure shi yayi wlh Innalillahi irin nawa ne wannan Dani ya dace,Kai da gani ya iya love,Kamla sai dariya Suke yiwa Iman duk ta gigice da ganin me kyau haka.
Da kyar Iman ta iya saita kanta kafin su Karasa inda motar take suka shiga,suna baya Kamla tana gaba,Iman ta mudubi sai kallon Saurayin takeyi Kamar mayya,Kamla tace Iman sunansa Ibaad,Ibaad ga frnds Dina Iman,Hanan da Jawahir,Nan Suka gaisa da Ibaad,Jin muryarsa Iman ta sake zaucewa a ranta tana furta mun Dace dashi wayyo sunansa Ibaad Ni Kuma Iman ai daga ji ma mun Dace tun a suna,Ga Ni Iman me Imani kenan,shi Kuma Ibaad Ibada kenan,Wai ga Imani ya Hadu da Ibada ai sai tafiya Aljanna Kuma, Haka Iman ke ta Zancen zuci Har Suka Isa wani Hadadden park Dake Birnin Tarayya Abuja.

Kamla ta fito cikin shigarta me kyau,Haka su Hanan ma,Kamla tana kusa da saurayinta Ibaad sun jera suna tafiya sune a gaba,Iman tace Kai mu gwauraye mu bisu a baya,dariya sukayi gaba Daya har Ibaad tun a mota yake kallon Iman kamar Bata da nutsuwa sai Abu takeyi kamar cartoon duk da cewar yaganta yarinya ce sosai kawayen nata sunfi ta shekaru.

Abinda kowa ke so ya Yaci a wajen sannan ya kaisu shopping suka zabi abinda suke so Banda Iman ko tsinke Bata dauka ba,Sai da zasu fita Ibaad ya kula yace ke Iman ya Baki dauki komi ba? Uhm mu da ba saurayinmu ba Dan son banza ka ciyar damu lunch Kuma muzo mu dauki Abu a siya Mana,rashin Imanin ai yayi yawa Ni ba Haka nake ba Ina da Imani sunana na amsa shi Iman.
Murmushi Ibaad yayi yaji wani kaunar Iman yaji tayi bala'in birge shi,ba tare da kowa ya Ankara ba Iman ta Masa Signa da Ido,da sauri Ibaad ya dauke idonsa a kanta Jin wani Yarrrr tsigar jikinsa ta tashi.
Mota Suka shiga ya sauke Iman a schl ta shiga motarta tayi gida,su Kuma su Kamla har gida ya maida su abinsu.

Iman ce ta shiga gidansu da motarta tana sake sake a ranta yayin da Tayi parking side din Yayan Mahaifinta ta shiga Alhaji Ahmad Dan Ali, Mama ta iske ta Tara Yan aikin gidan tana musu Nasiha,har kasa Iman ta duka tare da gaishe ta,ta amsa da fara'a tace Iman an dawo? Ae Mama Ina Khad? Bata dawo daga schl ba kin San ita Exam sukeyi a University dinsu,ae na Gane to Ina Auta Na'eem? Dazu ya dawo daga schl ya tafi Islamiyya, ok Wai Mama Sai yaushe Ya Nadeer zai dawo daga Uk ne? Very soon Inshaallah,Kin San kuwa an Gama Gina Masa Hospital dinsa da komai shi kawai ake jira,Wai za a ga Iyayi wajen Ya Nadeer idan ya dawo zai ganmu mun Zama yan mata sai aure ko? Oh Iman tafi ki bani waje kin addabeni,Da gudu Iman tayi part dinsu Raees ta iske a Palo Yana buga game,sallama tayi ya amsa tana zuwa ya rankwashe ta,ta saki Kara,yace karki Mana karya Ina gani Namiji ya fita daku yawo,Baki Bude tace wlh abinci ya kaimu Muka ci Saurayin Kamla ne Dan Allah karka fadawa Umma pls,Dariya Raees yayi yace to kinji har na kure ki dama wlh ban gani ba kawai fada nayi gashi kin tonawa kanki asiri.
Sama ta Haura da gudu tana dariya tasan Ya Raees bazai fadawa Umma ba.

Da Yamma Lis Iman Tasha wanka cikin Wata Atamfa super green riga da skert fadin irin kyan da tayi Bata Baki ne,Iman badai iya daukan wanka ba,Umma ta Iske tana lazimi ta sharara karya tare da Furta Umma zanje wajen Kamla Zan karbo wani littafi gobe muna da Test,Jin harkar karatu ce Umma tace a dawo lafiya Amma kisa Driver ya kaiki ban son tukin gangancinki,Ok Umma, Driver tasa ya kaita gidan su Kamla, securities sun rigada sun San Iman direct ta shige,A main Palo ta hango Kamla ita kadai tana kallon film,Ihu Kamla ta saki Jin Sallamar Iman da ihu Suka wani Rungume juna ,Kamla tace kamar kin San ba kowa a gidan Nan su Mummy sun tafi biki sai dare zasu dawo sai Ni Daya kamar mayya,Iman ta zauna kusa da Kawarta tace ya garin Mene labari? Oya Gist me ko babu latest? Kamla tayi wani farrr da Ido tace akwai Mana kin San Guy din Nan Ibaad wani mugun sonsa nakeyi wlh shima Yana so na,yace aure zamuyi soon Wai na Karasa karatun a gidansa,Hmm Yayi kyau ai cewar Iman,Wayar Kamla ce ta dauki Kara,tana dubawa ta fadada fara'arta tace wow Dan Halak Kinga Ibaad ne ma ke kirana,Iman Kamar zata shige wayar tace kice Ina gaida shi,Kamla ta daga waya,tare da furta Hello Ranka ya Dade,My Queen ya kk? Me kikeyi yanzu? Muna tare da kawata Iman yanzu tazo tace ma a gaishe ka,Bani ita mu gaisa,Kamla Bata ji komai ba ta mikawa Iman waya.

Abin mamaki sai ko Iman ta lankwashe murya ta canja murya gaba Daya ta koma me uban dadi,a hankali ta radawa Kamla karki damu kawata ban son a Raina mu ne a ganmu wasu Yan kauye kin san mu wayayyu Dole Muna da mahassada da Yan sa Ido a ko ina gwara mu dinga Ankara Muna komai na Yan gayu don Haka Zan Dan yiwa muryata faci idan ba damuwa? Kamla taji tsari cikin rada tace Haka ne kawata baki da damuwa,Iman ta sake lankwashe murya tare da Sallama cike da nutsuwa da tsantsan ladabi ita a Dole me tarbiyya sabo da ta Gama karantar Ibaad mutum ne me son Addini da Tarbiyya.

Honorable Allah ya Kara maka tsawon Rai Ka wuni lafiya? Murmushi Ibaad yayi shi dai tarbiyyar Iman tana tafiya da shi,Ga murya me Dadi tafi ta Kamla,Iman tace Allah yaja da ranka Ana kular min da kawata sosai ko? Sosai ma ai kin San itama tana ji Dani Dole Nima naji da Abata,Iman tace Haka ne to a dage da Addua kasan Addua itace komai sai Allah ya shige Mana gaba akan komai,a rage bacci Dan Allah,Nan ta jawo aya da Hadisi ta fassara dai dai, gaba Daya ta kwancewa Ibaad kwakwalwa Jin irin addinin Iman shi a duniya me Addini yake nema dama,Kuma gashi Kamla dinsa Bata da wani addini sosai sai kadan tafi ga Boko.
Sun Dade suna Hira da Iman kwata kwata ya Hana a bawa Kamla wayar sai da dare yayi sannan sukayi Sallama Iman ta Gama kashe shi da salonta,ko Kamla Bai nema ba ya kashe wayarsa tare da fadawa saman bed dinsa ya shiga tunanin Iman.

Kamla kuwa Allah sarki har ta gaji da jira tayi bacci a saman kujera,Iman tashinta tayi ta rakata tare da wucewa gida abinta cike da farin ciki.
Tun daga wannan Rana kullum Ibaad ya bugo wa Kamla waya Iman yake Fara tambaya,Yayin da Iman ma Haka tun Kamla tana sharewa har ta Fara nuna kishinta karara,ganin haka sai Iman ta daina Maganar Ibaad shima ya daina tambayar Iman,Yau suna class sun Gama lecture Iman tace Kamla bani wayarki na tura wakar Nan Mana,Kamla ta Mika Mata tana cewa ki tura min Nima wannan Dana fada Miki,Number Ibaad Iman ta duba taga Ansa King Ibaad,da sauri tasa number a wayarta sannan ta tura wakarta ta Bata wayar.

Da dare Iman ta Gama Shirin baccinta 10pm ta Kira wayar Ibaad Bugu Daya ya dauka,Iman ta kashe Muryarta tace da fatan ka Gane wace? Yaso ya gane Muryar Amma ya kasa tace to Iman ce kawar Kamla,wani farin ciki ya mamaye Zuciyar Ibaad har Bai San sanda yayi tuntsira gudi gudi ba tare da Hantsilawa a saman bed dinsa dama ba abinda yake son ji sai Iman,ba abinda yake son gani sai Iman,Haka Suka raba dare suna hira kafin su gaji suyi bacci,Tun daga wannan Rana Iman suke waya kullum da Ibaad,shakuwa me karfi ta shiga tsakaninsu,har ta Kai ya Fara zuwa zance wajen Iman yayin da gaba Daya ya share Kamla.
Kamla tayi kuka har ta gaji Bata San dalilinsa na daina kulata ba.

Suna schl Hanan tace Kamla ki share shi Banga amfanin damuwa da Wanda Bai damu da ke ba,duk kin wani Rame sai kuka ko Abinci bakya ci akan wani Ibaad Ni wlh Banga abin so a Nan ba,Jawahir tace wlh kuwa Ibaad din banza maza nawa ne Suka fishi komai,Iman tana zaune Waka take ji tana rawa da kanta tare da furta harda yin kishi dani akan Yana Tambayata ai gashi Nan dama na fada Miki Namiji ba Dan goyo bane,Kamla ta fashe da kuka tace wlh kuwa sai da Kika fada min naki ji gashi sai da ya Bari na fada sonsa,ki daina Bata Hawayenki Yan Mata Yana can mayaudarin tare da wata cewar Iman.
Hanan tace ku tayani da Addua Nima Ina ruwa na fada son wani Ameer,Baku ganshi ba wlh fari tas dashi kwara ne ya Hadu Dan kawar mamanmu ne muke soyayya,daga Jin ance Kyakyawa fari Iman tace Yana da hanci? Wlh Kamar Anja Aeria ma cewar Hanan,zumbur Iman ta mike tace Kira Mana shi mu ganshi kyan nasa ya Kai a so shi? Yanzu Zan Kira shi ya maida Ni gida sai ku ganshi,yawwa Kira shi cewar Iman,Haka shima Hanan ta Kira shi 30mnt yazo ya Hadu a wata Benz tun a cikin mota Iman ta hango shi sai kawai ta rude tace kut ai ya take Ibaad a komai,Hannu ta daga sama ya Allah ka bani miji ko irin wannan ne Ameer,Me hasken wannan da farin Nan, Hanan Haka itama ta gabatar musu da nata sannan ta shiga motarsa suka wuce.

Nan take Iman ta koma kaunar Saurayin Hanan,Daga Nan ta koma zuwa gidan su Hanan kullum har ta sato number Ameer,Ameer dama shi Dan duniya ne Mata yake bi ganin Pics din Iman ta tura Masa ta WhatsApp yaga tafi Hanan ta ko Ina kawai ya koma wajen Iman shima,gaba Daya ta hada Ibaad da Ameer tana ta buga Soyayya da kowannensu ita kawai Dadi take ji ganinta da kyawawa.
Hanan Kamar tayi canfi sai gashi Ameer itama ya tsere.

Ko a gida ba Wanda yasan me Iman ke Yi,ga Ameer har ya Fara kawo Mata Zancen Iskanci Amma ita Sam ba Haka take ba hasali ma Namiji in dai ba Dan Uwanta ba ba Wanda ya taba ko rike Mata Hannu.
Ko film ne Ilham ita sai na star me kyau,Haka Yan Ball ma duk kyawawan sonsu take,kowa idan me kyau ne to tana sonsa,ko a gida an San halinta na son maza masu kyau, suna main Palo gaba daya Mikewa tayi zata Haura Sama kenan aka hasko wakar wani balarabe Kyakyawan gaske ai sai Iman ta dawo ta zauna tace Bari na kalli saurayina,Ina son wannan gashi me kyau,Raees ya kalleta tare da Furta yawwa ai nasan Hali,Baki Umma ta tabe tare da furta,duk samarin naki da kike kawowa kina cewa masu kyau Basu Kama ko yatsan Nadeer a kyau ba Amma kinbi kin damu mutane,Baki Iman ta cuno tare da furta Umma ai shi ya cuci kansa da fushi,ba fara'a,ga Iyayi da uban gadara wace zata auri wannan, tsaki Umma ta ja tare da furta Allah ya shirye ki.

An kwashe wata Biyu da kwace samarin su Hanan da Iman tayi Jawahir itama tayi Gam da katar da wani Dan gidan gomna ya Hadu ga kudi ga kyau,Shima tunda Iman ta ganshi a Hoto kawai sai da ta sace number dinsa ta San yanda zatayi ta kwace ya koma wajenta gaba Daya su ukun ta hade su love kawai take buga musu,Khadija ma Kanwar Nadeer Yar kanin Babanta mate din Iman ce,Tunda Saurayin Khadija yazo zance Iman ta ganshi me kyau sai da ta shige Masa,idan yazo zance wajen Khadija ko suna waya ba wacce yake tambaya ko ya dinga zancenta sai Iman,ganin Haka Khadija sai ta daina kulashi ta barwa Iman,Iman tace ita lafiya Shar Amma duk cikinsu Halayen Ibaad sunfi birgeta.

Su Kamla Basu San meke faruwa ba suna ta zuwa Schl suna kawancensu Basu San Iman taci Amanarsu ba cikin Dan kankanin lokaci ta gama dasu gaba Daya.
Ana Haka katsam Iman ta samu rashin lafiya dare Daya,Wani tsiro ne ya fito Mata a gabanta HQ ko Zama Bata iya yi, hankalin kowa ya tashi Nan aka yayeta zuwa asibiti,bayan gwaje gwaje Likita yace aiki za ayi Dole sai an cire,Amma za a bata Magunguna sai Nan da wata Biyu Dole za ayi aikin.

Ko da ta Fara Shan Magunguna tana Jin sauki sosai Amma har makaranta tana zuwa,yau Monday suna garden na makarantar Ibaad ya Kira Iman gefe ta koma suka Sha wayarsu,Kamla tace Iman kin bar mu a duhu saurayi Kika yi ne yanzu naga kullum Baki da aiki sai waya,Murmushi Iman ta saki tare da Furta hmm frnds ne kawai Kamla.
Baki Suka tabe wa Iman ba tare da sunce ehem ba.
Karku ga Ina gyara muryata tana Dadi ba saurayi bane na sanku da zargi Kuna keta Haddin musulunci,Baku da aiki sai zargi,idan saurayi ne ai sai Kun Riga kowa sani,to mu muka ce miki kiyi abinki Ina ruwanmu cewar Hanan.

Tsaki Iman ta ja,Kamla tace Iman karki ga ke kawar mu ce Muna kulaki kice Zaki kawo Mana Raini kin San dai min girme ki nesa ba kusa ba,Mu ba mate naki bane kamar Kanwar mu kike don duk cikinmu mun girmeki da five years so ki kiyaye mu baza ki Mana wayo ba.
Yarinya da ita ma ta Isa tace zata Mana wayo ko ta Raina mu ai wlh kinyi karya cewar Jawahir.
Iman tana jinsu dama sun Saba Mata gorin sun girmeta ita yarinya ce sunfi karfin ajinta,Hakan ya Kara tunzira Iman tace Lallai sai ta nuna musu Basu da wayo.

Washe Gari da yamma Iman Bata da Ismiyya tana gaban tv tana kallon film Maman Nadeer ta shigo tace Iman taso da Allah ki raka Ni gidan kawarki Kamla Babansu bashi da Lafiya Ana zaman mutunci ya kamata Muje duba shi tunda duk abinda ya faru suna zuwa Mana Suma,Zumbur Iman ta mike tare da Furta dama yanzu nayi wanka Bari kawai na dakko mayafi na,Umma tayi wa sallama Suka tafi ita da Mama,Wata kafceciyar Motar Mama ta hau,Iman ke Driving Maman Nadeer tana gaba suna Hira har suka Isa gidan su Kamla,Lokacin Kamla Bata Nan sun tafi gidan wani bikin Dangin Babansu sai Maman Kamla da Yan Uwanta dake kula da Alhaji,Maman Kamla muguwar Yar karya ce duk da suna da kudi sosai Amma sai ta Kara da karya,burinta a San su masu kudi ne komai ita ce me kudi bayan ko yatsan Baban Nadeer Basu Kama ba a kudi.

Ganin Masu kudi ne su Iman ba wulakanci ba yanga ta tarbe su tana haba haba dasu tare da kallon wasu manyan Mata yan Uwanta masu Gadara da takama tace Hajiya Attine ga kawar Kamla ga Babarta matar Alhaji Ahmad Dan Ali ce? Da sauri Matan Suka ce wow Dan Ali dai da ake labarinsa of course shi fa cewar Maman Kamla,Hajiya Attine tace gaskiya Maman Iman Shaddar Nan Taki tayi kyau matuka Amma Dinkin Senegal ne ko ta birge Ni that's really nice,Mama dai kallonsu take Yi domin ta san Halin Maman Kamla da son karya.

Maman Kamla ta Gyaru farin glass dinta tare da cewa Mama Ina Danki kuwa Nadeer naji ance Yana Uk ko? Ae Yana can Amma yanzu Yana Greece yaje Hutawa Sunyi Hutu,sam Bai son zaman kasar Nan nayi fadan har na gaji cewar Mama,Maman Kamla tayi dariya wakekiyar wushiryarta wacce tayi yawa Kamar Hakori guda ne ya Fadi a saman tsakiyar Hakoran tace Nima Kinga nayi nayi ya tura Kamla Ko Banzar kasar Nan ce Dubai yaki da kyar na Samu ya Kai Abdullah Cypros,Amma wannan kasar tamu me za a ci da ita kawai Wai a Haka ma Dan Muna Abuja ne, Ni yanzu idan ba Abuja ko Lagos ba Ina Zan iya rayuwa a kasar nan,Iman ta kalla tace Iman tashi ki Karo min karfin Ac din Nan zafi yayi yawa.

Mama Baki ta tabe kawai tace to ya za ayi Allah yayi mu anan,mun gode Masa ma da yayo mu musulmai shine farkon abin godiya ga Allah,Maman Kamla tace wlh fa sannan Kuma Allah yasa muka zo a yaran sunna yanzu Hajiya Salima da a 'ya 'yan shegu Muka tashi Yaya zamuyi kenan Allah ya taimake mu,Hajiya Attine tace Hajiya Salima ita Maman Kamla a can kauyen Nasarawa Alhaji ya ganta yaji Yana sonta?,saura kwana Uku Bikinta tana ganinsa ta fasa auren

Please Login or Register in order to submit comment