Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki kalli kanki Low class da ke in Banda Albarkacin Aabid kin Isa Ki ganni bare ki iya Bude babakinki da babu Brush kiyi min magana.

Maganar Mufeeda ta Fusata Ni duk Tsafta ta ko Ina a kalkale tace bana Brush ai ko na cire mayafina nace ke bafa tsoronki nake ji ba,banza Yar Tasha gwara ni ke tunda Kika zo gidan Nan Kika kashe kamshin gidan da warin Hammatarki, Mufeeda taji Haushin nace Mata me warin Hammata, tace kanki akeji,nace a'a kan Ubanki akeji Yar Tasha Me warin Hammata du gashi cako cako kamar Allurai...Muna Haka Aabid ya shigo ya dau wanka cikin kana Nan kaya black and White t-shirts me gajeren hannu da hula a bayan rigar, Wandon pencil black, Sumar Nan tana sheki Yana bulbula kamshi,Mufeeda tana ganinsa ta dinga kallonsa kamar Mayya,shi Kuma Yana wani shareta Amma Bata ganewa,Zama yayi a gefenta Suka Kama Hirar schl, nace Ya Aabid Ina yini? Lfy yasu Mami? Lafiya suke na amsa Masa muna harar juna Ni da Mufeeda.

Mufeeda tana so ta fadawa Aabid tana sonsa tana kunya sabo da na ki tashi na Basu waje,hakan yasa Taji haushina tace ita zata tafi tana da wajen zuwa zasu Yi waya Da Aabid kawai, Umma ya Kira Mata tayi Sallama yace Driver dinki Yana kofar gida,Murmushi Mufeeda tayi tace ae cewa yayi ba sai ya shigo da Motar ba,Suna Mikewa nace Bari na rakaki nabi su a baya,ita da Aabid suna gaba Kamar zata shige jikinsa, Ya Aabid na furta a hankali, ya juyo a hankali Muka hada Ido da Hannu na nuna Masa gefe Wai ya matsa gefe,ya gane me nake nufi Amma ya juya abinsa Suka ci gaba da Tafiyarsu.

Aabid iya bakin gate ya bar Mufeeda yace ki gaida gida sai munyi waya,tace Alright thanks. ya wuce Wajen Umma, Ni kuwa naki tafiya Muka fice har bakin gate nida Mufeeda inda Driver yake,
Harara ta balla min tace ke Wai Ina ruwana dake ne? Nima ramawa nayi nace an biyo Namiji mayya to yafi karfinki,Mari Mufeeda ta kawo min Allah yasa Bata sameni ba na kauce,Zuciya ta zo min na cakumi wuyanta Ina zaginta na hada ta da jikin Motar tare da maka ta jiki da karfi ji kake gwaraf.

kokawa Muka Fara sosai yakushi da cizo mukewa juna a fuska,duk mun jiwa kanmu rauni a fuska har jini,Tace Allah ya tsine miki da Uwarki,zuciya ta Kara kamani nayi kukan Kura Nace Iyaaaaaa....nayi tafiyar ruwa da Mufeeda ta Fadi a kasa na haye ruwan cikinta na dinga dirmarta kamar na samu jaka tana ihu,Driver ne ya fito da gudu Yana rokona da kyar ya bani hakuri na kyaleta na mike a Samanta Ina haki Fuskata duk rauni, Itama ta mike ta fada mota tare da cewa Allah ya isa shegiya,Driver yaja mota Suka tafi tana ta faman zagin Dattijon Driver akan Wai Bai zo ya CeCe ta da wuri ba Allah sarki Ni Kuma na koma ciki Umma taga Fuskata duk yakushi,cizo gasu Nan a fuska ta abinka da farar Fata duk gurin yayi ja.

Aabid Yana kwance a 3seater kusa da Umma tace Raudat Lafiya kike kuwa? a Ina Kika ji wannan Uban Raunuka Haka? Fada Kika yi da wata ko wani? Ga fuskarki Nan duk cizo da yakushi? Shuru nayi Ina Wasa da yatsu na,Aabid ya kalleni yace Umma ba Wanda ta Sani a street din Nan ita ba Hatsari ba sai dai idan Mufeeda bakuwata ta Tsokana Suka Yi fada sabo da naji hayaniyarsu sama sama,Kuma nasan Mufeeda itama kamar Damusa Haka take wajen masifa da fada,ita Kuma wannan ya nuna Ni da lips dinsa wannan Bata da kunya ga Tsokana na tabbata ita ce tayi tsokanar ai gashi Nan kinwa kanki ta cijeki ta yakusheki jiki duk tabo wa zai kwasheki a Haka ya Kai gidansa Aabid duk shine yake ta fada Haka, Umma ta Goya Masa baya Cewar ba Shakka Raudat ayi bakuwa ki hakke Mata sabo da Allah Haka akeyi ko ba komai ko Dan Aabid ai Kya kyaleta ko tsokanarki tayi Bai kamata ki Rama ba,Lips na cuno gaba nace to Wai Umma ni sai na kyaleta?

Baza ki kyaleta ba ai ta girmeki Cewar Umma,Kukan Shagwaba na saki Ina Doka kafafu nace wlh Ni bazan kyaleta ba ta zageni ai da kadan ta girmeni har zata zageni Ni dama bani da hakuri Baki ji ba Umma yanda ta dinga tsine min Haka kawai daga nace sannu da zuwa Bakuwar mu ke Budurwar Ya Aabid ce? Da fara'a na tambayeta Amma sai ta Kama masifa Allah ya kiyaye min me zanci dashi,nafi karfinsa,Iyayena Ni masu Arziki ne,sannan ba kalata bane shi sabo da bashi da Naira,nafi son Wanda zai kaini Kasashen waje,Amma shi Aabid yaushe ma yayi kudin ai sai rufin Asiri,naji Haushinta Umma nace haba ki kalli wannan gida ga mota me kyau gashi da kyau ga iya wanka,ai Umma kin San me tace? Umma tace sai kin fada Raudat,Nace sai ko ta bude Baki a gabana na matso kwallar karya naci gaba Wai ta kalli Kamar Aabid tace Shafe shafe yakeyi ba farinsa bane na Allah kanti yake shiga,Umma tace Amma wannan Yar iska ce gwara da Kika jibgeta Ina ma a gabana ta fada da ta kwashi Kashinta a hannu.

Farin ciki naji a Raina Umma ta Yarda sai na samu kwarin gwiwa,Ai Umma harda cewa me zai iya Yi min wannan Kamar mace Haka yake Ina zai iya aikin karfi,yanzu ma shigowa kawai nayi sabo da mutunci Amma wannan dan Iyayin ga jiji da Kai shi a kudin nasa ma Bai je ko Ina ba,Nace haba Mufeeda a gabana ai cin Fuska ne, shike Nan ta Fara zagina,sai da kuka fito tayi Shuru tana waye waye shi yasa Kika ga Umma na bisu Rakiiya, kin San To nima idan Rashin mutunci ne A nake ba Z ba na Kama shegiya a waje Nima Kunga fuska ta to wlh Tata tafi tawa rauni sannan na zauneta nayi Mata duka,Umma taji Haushi an zagi Aabid dinta tace iceko taji jiki? Nace ai zunkuli da Naushi Tasha a Hannuna Kya rantse Salman Khan ne ya Kama Boss a fadan karshe.

Umma tayi dariya tace kin birgeni tunda ita tayi laifi,Aabid yaja tsaki yace Umma ke yarda Kika yi da ita? Ni nasan karya takeyi wlh Mufeedan da take mugun so na,Ni baza ki Raina min hankali ba kawai kin fake da Mufeeda kin ci min mutunci nine me Kama da mace Allah Umma Ina kyaleta ne sabo da ke Amma wlh zan Fara zaneta a gidan Nan ta Gama Rainani Dan Ubanki Ni Sa'anki ne? Aabid ya mike a fusace zai Dukeni na gudu wajen Umma,Kai fa baka san arziki ba,an zageka yarinya ta tare maka ta Kare maka mutunci shine zaka juya Maganar a kanta Ina laifi ma, Aabid ransa a bace ya daga Hannaye sama yace Allah ka kawo Almajirin Kauye ya auri yarinyar Nan naga karshenta,Ko Allah ka kawo Dan dako,ko tsohon tuzuru Wanda bayan rabuwarsa da Matarsa ya Kai Shekara a Shirin Bai sake aure ba yanzu ya Kara da ke.

Dariya mukayi harda Umma Wai shi takaici ya Masa yawa bashi da hanyar Ramawa,Aabid ya sake cewa Allah ko Dan garuwa,ko me tallan Agwalima,ko me Kwakwa a samu Daya ciki ya aureta, Kuma kwandalata kin daina ci,Dariya muka sake kyalkyalewa da ita har Umma,Nace Allah sai naci dama Uniform din Islamiyya ta ya yage Ina ta so Zan fada maka gwara daka tuna min,ga Takalmin makaranta ya tsinke shima, Kije Babanki ya siya Miki ai kinwa kanki yarinya ciki duk Koko, dariya nayi Dana tuna sanda nake Kai Masa Koko na kullum, Umma tace to sai me Dan baka Bata ba akan kayi Mata anko shike Nan, ki kyaleshi Umma Allah sai kayi min, tsaki yaja tare da ficewa ya bar gidan gaba Daya ya shiga mota tare da tafiya wajen Faruk.

Fadeela da Rufaida Suma sun samu samarinsu Allah yayi Basu damu da halin Abba ba a Haka Suka ce zasu auresu,Fadeela Nata Dan kasuwa ne matashi zai Kai 35yrs ya taba aure Matarsa wata biyar da biki tayi Bari ta Rasu, Yana samun kudi a kasuwa sosai ba laifi Sabeer kenan,shine zai auri Fadeela ya kawo kudin aurensa Ansa Rana wata Biyu kacal kasancewar ya shirya bashi da matsalar Muhalli da kudin aure.

Shima Abba yanzu baida matsala sabo da abokinsa Dan majilasa shi zaiyi Kayan daki da komai, Rufaida kuwa Nata shima Ya Gama komai na aure bikinsa saura wata Daya da wata Allah yayi aka fasa auren sakamakon yarinyar tace ita Dole sai tayi aikin Gomnati idan bazai yarda ba ta fasa auren, shi Kuma Yana aikin Gomnati Babba,ga kasuwanci Yana da Hali baya son Matarsa tayi aikin Gomnati yafi so ya Sa Matarsa a kasuwanci ta dinga Yi Amma yarinyar tace ita Bata yarda ba iyayenta ma Suka ce a'a baza su yarda ba yarsu aiki zata Yi, bayan ya hakura Allah ya hada shi da Rufaida Wacce yanzu shima ya Kai kudin aure da sadaki biki Rana daya Dana Fadeela,Saurayin Rufaida ma Matashi ne 30yrs Dan gayu Fulanin asali Ammar kenan.

Muna ta Shirin bikin su Fadeela angwaye Suna ta kashe kudi hakan yasa ni da kanwata Khairat aka dinka Mana Kayan bikin har kala biyar,ga Takalma da jaka dai dai kudinmu an siya Mana da jaka kala biyy, su kuwa Amare nasu daban, suna ta gyaran jiki mu kuwa sai dai kallo kawai.
Fadeela tace Raudat da tuni kin riga kowa aure a gidan Nan yanda Kika Fimu samun samari Wanda da gaske aurenki zasu Yi,gashi Kuma sai ta Allah ta kasance mu bamu samu matsala ba abin sai Allah ya kawo Mana shi a layi,Rufaida tace Allah kenan Haka ya tsara,biki saura kwana Uku aka Gama jere da komai a gidan Amare,gidan ko wacce ya Hadu,mu da ake rainawa Ana ganin ba kowa bane sai Allah yake azirtamu da samun mazaje na kirki Kuma masu hali,
Ga Dan Majalisa abokin Abba kaya na Alfarma yayiwa Su Fadeela Kaya na kasar Dubai,komai yaji.

Haka Rayuwar ta kasance Har Allah ya kawo mu bikin su Fadeela Kamu Muka Fara Sha Alhamis,sai Party ranar Friday yau kenan mukayi angwaye sun kashe Kudi sosai,Umma ma taje ba yanda Umma batayi da Aabid ba akan yaje Dinner yace shi bazai je ba Mijin Rufaida dai abokinsa ne suna kasuwanci tare Yana siyen kaya a wajen Aabid idan yayo order Dan Haka Yana cikin abokan angwaye,iya Daurin aure ya isheshi.
Anji Dadi an rakashe ansha Rawa da liki tare da angwaye,Dinner tayi kyau sosai,Umma a gidanmu take ta kwana Ana Shan biki da ita.

Washe Gari Da safe 11am Daurin aure munyi wanka anci kwalliya har Amare sun Sha Shadda,Ni kuwa Atamfa Sky blue and black na saka Riga da skert dinkin me Masifar kyau,kayan sun kamani daf, Hips din Nan gasu Nan manya kyau Kam nayi shi ba a magana,nayi kwalliyata sama sama,Daurin Ture kaga tsiya nayi abina,Gidan dake Facing gidanmu a Nan Amare suke Zama tare da Frnds nasu, ni kuwa a gidanmu na kwana, Muna gida Ni da kawata Habiba Muka ji an daura Auren Fadeela da Sabeer, Rufaida da Ammar Kan sadaki dubu Hamsim ko wacce.
Ina jin Umma Suna Waya da Aabid Wai ya shigo tare da Angwaye yayiwa Mami Allah Sanya Alkhairi.
Jin hakan yasa na tsaya a jikin Kofar Aiko Bai biyo angwaye ba sai gashi shi kadai, yasha Shadda light Blue kyau Kam yasha yau na daban ne ka rantse shine Angon,Wanda Basu sani bama har tambaya suke ko shine,Mata da yawa a gidan yasa ya tsaya a bakin kofar tare da yafitoni da Hannu nazo,a nutse na Tako gabansa,Ni kaina nasan nayi kyau matuka.

Murmushi nayi naje wajensa tare da gaidashi yace Kira min Mami mu gaisa a Nan,Uhm kunyar Mata kakeyi? Harara ta yayi yace Dalla Kira min Ita sauri nakeyi, dariya nayi a hankali nace Kayi kyau Yau Alhaji Aabid na wuce Na Kira Masa Mami da Umma Suka gaisa yayiwa su Mami Allah Sanya Alkhairi sannan yace Umma yau kwananki biyu a Nan Dan Allah kizo mu tafi gida,Kullum yanzu Indomie nake ci har na gaji ba abinci,Ni Kuma kin San abincin Restaurant Bai dameni ba.

Umma tace ai kuwa sai jibi zan dawo,gobe za a Kai Amare mune zamu Kai gara,Kaine da iyayi kace abinci baza kaci na Restaurant ko gidan biki ba,ga Raudat Nan Zan Turata taje ta girka maka a gidan Aymana ta Kai maka gida,Wannan kazamar ce zata iya wani Abinci cewar Aabid, Iyayin banza Naga Sau nawa ita take min girki kana cinyewa har da Santi yanzu zaka ce kaza kaza to tafi ka zauna da Yunwa,To Umma tazo mu tafi tayi a gidanmu part dinki Ina kallo a idona inda Bata Yi dai dai ba sai na gyara Mata,Abinda ka iya girkin ma wanne girki ne baka Yi Aabid,Amma tunda kaje turai ka lalace, ga Raudat Nan ta dakko mayafi ku tafi, Nace Umma Ni dai idan na bishi masifa zai ta Yi min,idan yayi Miki ki dawowarki,ga kudin Napep rike ko bakar magana ya fada Miki ki taho gida,To na furta na karba tare da dakko jakata da Mayafi na bishi, gaban motar na Shiga yace koma baya Malama da ace naga wannan mummunar fuskar Taki gwara na Zama Driver ki, dariya nayi na shige baya na zauna,motar ga kamshi a ciki gata Tasha wanki tana kyalli,ga sanyin Dadi na ac kida na tashi kadan.
Ina bayan mota Yana gaba,na tsokaneshi a hankali nace Driver...Me kike cewa? Nace wakata nakeyi ba da Kai nake ba.
Abinda yasa na biyo shi so nake na lallabashi ya bani kudin Uniform sabo shi yasa na yarda,sosai na Kulla a zuciyata zan masa ladabi.








AsmaBaffa.
[4/16, 9:53 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙








31-35








Official








By
AsmaBaffa





NA KUDI NE

RASHIN SA'A COMPLT dari Uku ne 300 ga masu bukata.

NA KUDI NE

TA GYARU na kudi ne dari biyu 200 ga me bukatar shiga Group din.

Masu bukatar siyen wannan novels guda biyu zaku iya siye ta wannan Hanyoyi Kamar Haka:

Masu son biya ta hanyar bank ga accnt number da zaku tura
2177560408, Yahaya Garba Muhammad, zenith bank.

Transfer Kati ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Idan Kuma number Katin MTN zaku tura ta WhatsApp ko Sms ga number da zaku tura
08033933642.

'YAN NIGER masu son siye ku nemu wannan number
+227 90 79 59 39.






Page naku ne

Haulatu Bawa kamba
Choice
Momyn Sabreen
Maryam
Nafeesat Umar Muhammad
Minerh
Maman Fahad
Mrs Farooq
Ummu Amatussalam
Aceryer lame
Shakee Ross
Maman Irfan
Maman Alamin and
Oum Aman.

Godiya gareku

Maman faty, Maryam Mg
Alhmdulillah,Maman Umma, Murja Suleiman kkr, UmmuHaneephart, Roukayyah Bello, Zainab Dinawah, Aisha Adamu, and Maman Aareef.

Fatan Alkhairi gare ku

Jikarkulu, Jannat, Mmnm Muazzam, Maman Irfan,Niimatullah,Zarah Dandagazau,Maman Husna,Saudat,Rukayya Muhammad and Islam.








Nutsuwa nayi sosai ban kulashi ba,Yana ta tukinsa a nutse har muka Isa gidan,yayi parking na fito Muka nufi part din Umma ba tare da wani yayi ko tari ba, shi ya bude min part din Umma ba Dirty ba komai nace waye yake gyara gidan Nan gashi ko Ina Neat,Shuru yayi min har Muka shiga kitchen shima ko Ina tas, me Zan dafa maka?na tambayeshi Dan ya wahalar Dani yace Pounded yam with Egusi Soup, ban nuna komai ba nace ok Sir, Zan Fara dakko Nama a fridge ya wani nemi kujera ya zauna yace karki taba Fridge din Nan dawo ki wanke hannunki tas first.

Bance komai ba na dawo sink nasa liquid soap na wanke wanke tare da wanke Hannuna Ina ta dirzawa sai da Naga ji sannan yace ya wanku to yanzu Fara girki, banyi musu ba na dakko Kaza zan yanka na Fara kici kici na kasa tayi min karfi na hada zufa Zan share Fuskata da Hannun da ke rike da wukar, muryarsa na tsinta yace kazanta Zaki Yi ga gumi ga wuka, Mikewa yayi tare da Miko min Hannu yace Bani wukar, da sauri na Mika Masa Zan goge gumin yaja tsaki yace ke kazama wlh karki sake ki goge gumi da hannu idan ba Haka ba bazan Ci girkin ba, Tsayawa nayi a gefe Ina kallo ya yanka min Kazar sannan ya wanke Hannayensa ya miko min Handkerchief me kamshi, Murmushi nayi zan karba yace a'a kazama a taba handkerchief ayi min girki bada Ni ba, tsaya sosai na goge Miki,tsayawa nayi Kamar gunki ya daura a saman goshina tare da goge min da kansa.

Ina ta kallon Iyayi ya Hana nayi girkina sai yace shi zai koya min Dole bana Yi daidai, a Haka Na Gama girkin yabi ya takura min komai na taba yace ba Haka ba, Ina gamawa yace saura ki gyara kitchen, ba Musu na gyara kitchen Yana tsaye,Ina gamawa yace Serve Me
Ya Furta tun a kitchen din, zuba Masa nayi ba musu, a tsaye ya saka Loma Daya yaji shegen Dadi Yana taunawa yasan girkin yayi sosai Amma sai ya Bata fuska harda turo lips waje da kyar ya Hadiye,na kafe shi da Ido Ina so yace yayi Kar ya kushe Ni kar yace sai na sake dafa Masa wani abin,Bai ce komai ba ya sake yankar Loma yasa a Baki ya Bata fuska Karo na biyu,Ina ta kallonshi ba ko kyafta Ido nayi Murmushi tare da cewa da Dadi ko? Harara ya galla min yace ba dadi,Dole zanci maganin yunwa,har abada baza ki iya abin duniya ba,komai Baki iya ba,mace kamarki Baki iya girki ba tun yanzu to sai yaushe kenan a Haka a ganki Shar Amma tir da halayenki fice ki bani waje, Nasan yayi Dadi kawai bakin cikin Aabid ne, Biyayya nayi na fito Palo na zauna tare da abincina a plate Nima Ina ci,Shi kuwa tuni ya zauna a kitchen din ya cika tumbinsa Yana Santi a ransa,sai da ya Gama sannan ya gyara hannunsa da Bakinsa ya fito kamar Bai ci komai ba.

Yana Bata fuska ya karaso inda nake Nima na Gama cin nawa,Plate nawa ya kalla yaga Pounded yam guda har Uku Allah ya gani Ina da cin Bala'i, Baki ya bude yace duk ke kadai Kika cinye? A hankali nace ae, ya girgiza Kai yace Lallai rikonki sai Federal kin Wuce Karamar Hukuma,Tashi ki tafi girki ba Dadi Mene amfanin zuwanki ma,biyayya nayi nace kayi hakuri kaji,duk yayi zaton ladabin Allah ne, a Aljihu naga ya zaro dubu Biyar yace ungo kudin Uniform din badan halinki ba,Dan kawai Uniform ne na taimaka miki tafi gida kin dameni da kallon banza.

Durkusawa nayi kasa na karba da hannu biyu tare da cewa na gode Allah ya Kara budi,Allah yasa kafi Haka,Ina Gama Addua ta na mike tare da yin hanyar ficewa daga Palon Ina ta farin ciki, har Zan fita sai Kuma na dawo gabansa harda tsugunawa irin me ladabi din Nan,Mene Kuma? Ya tambaya Yana kwance a saman Kujera Yana kallo,nace Alhaji Aabid Dan Allah idan na samu miji zanyi aure Kaine waliyina, Aabid da kyar ya danne Dariyarsa yace sabo da na Baki kudi? Ai me baka shine abin a Rike nidai Dan Allah Kaine Waliyina sai ka yarda Zan auri ko waye Kaine zaka Yi Masa screening, Dariya yayi ba shiri yace Lallai kin shaku da kudi Ke imanin ki kudi ko? Tafi ki bani waje, Dariya nayi kadan nace ai Zan tafi dama Amma Kaine waliyi na,ranar auren idan yazo Dan Allah kazo da wuri goro da Alawa Kai zaka rabata kazo da katuwar babbar Riga sabo da bin layi layi kana rabawa bayan ka daura auren, Robar ruwan Daya shanye ya jefo Mini Yana dariya, na yafa Gyalena na fice Ina daga Masa Hannu.

Napep na shiga na koma gida inda ake ta kida Dj Ana rawa,ko gida ban shiga ba na shige filin rawa naji kida sosai Hannuna Yana rawa Ina so nayi liki bana son taba kudin Uniform Dina,cikin kudin na dangwali yawu a yatsa na tare da zaro dubu Daya da kyar, naja me bada canjin sababbin kudi gefe, nace bani Yan biyar biyar na Naira dari ka bani canjin dari Tara, Mutumin me Kama da Dan daudu ya Rike Baki yace Haba baiwar Allah Gaki a Haka kalar kudi,ba ruwanka bani canji idan akwai, Haka ya bani Yan biyar biyar na Naira dari na koma cikin fili Amare suna ciki Ana ta Yi musu liki, Ni kuwa nace Haka kawai nayi musu liki su Sha dadin banza gwara nayiwa kaina tunda kudi nane, naje wajen me kida nace zanyiwa kaina Liki Dj ka Samin kida me Dadi Ni kadai zaka kira filin Nan,Dj yayi zaton wasu Yan dubu dubu Zan likawa kaina.

Mc yace to Alhmdllh Amare su fita yanzu...zaiyi magana naje na rada Masa sunana da zai fada,ai kuwa Yace Yanzu a wannan Fili Muna bukatar Kanwar Amare ita kadai Hajiya Raudat kanwar Alhaji Aabid me Naira,aka dinga dariyar sunan,Su Umma duk suna wajen sai dariya sukeyi kowa da Yan Mata An zuba min Ido a ga bajintar da zanyi, na shiga fili aka saki sauti me Dadi na Fara rawa ta na dan iya kadan,daga baya na ebo Yan biyar biyar Dina na naira dari Ina likawa Kaine Ina rawata, Dj da Mc suna gani jikinsu yayi sanyi dariya ta kama Yan kallo har Amare, kafin kace me kudi sun Kare Naira dari,Dj Yana ganin ba kudin kirki bane ya canja kida tare da Kiran iyayen Amarya,na fita Ina cewa Dan anga bani da kudi to Ni dai bazan sake asarar kudina ba,Naje wajen Aymana tana Rike Da Handbag ga danta Kato a kafadarta, ke Aymana kina auren mekudi Amma Dan kudin liki ya gagareni na kwace Jakar na zuge na samu yan Hamsim da Yan ashirin na liki na kwasa da Dan yawa dake ba nawa bane na shige Fili na likawa kawayen Mami da Inno tare da wasu Kawayen Amare.

Haka biki ya kasance bayan laasar aka Kai Amare gidajensu masu kyau,zuwa dare muka dawo gida lfy anyi an Gama, Baki na kusa duk sun tafi,washe Gari su Umma suna Kai gara Suka koma gidajensu,Gidanmu ya koma ba kowa daga Ni sai Khairat Kanwata sai Kuma Inno da Mami,da yamma Abba ya shigo gida Yana Murna yace Kai Alhmdllh Mami Kinga Na sauke nauyi da yawa Allah yasa sunyi auren Nan kenan sai dai mutuwa,Mami da Inno Suka ce Ameen, Abba ya washe Baki yace Allah ya rufa min asiri yanzu Sanwa ta ragu a gidan Nan, Amma Yara sun cike gida zagada zagada Haka yanzu sai suje ayiwa miji yanga acan,Kunga da Sallah atamfa Turmi biyu kacal zan siyawa su Raudat sai Kuma Inno dake,haba har naji wani sakayau Dani,Inno tace Kai dai Bari dannan da kyar nake iya bacci sabo da yaran Nan da Suka ki auruwa Rida Rida gasu kyawawa ga talauci Ina tsoro Kar Allah ya jarabcemu Daya tayo Mana ciki yaran zamani ba a sakin jiki dasu,Addua nake ba dare ba rana to Gashi yanzu sai labari, Abba yayi dariya yace shinkafarmu cofi uku yanzu ta ishemu da Yar Taliya Daya da rabi badan ma Raudat ba me cikin Zani ai da kashe kudin bazai Kai Haka ba, Abba ya kalle Ni yace Dan ubanki ki Nemo naki kema naga kina wani yake Baki yar buhun uba me ciki Kamar mangala.

Dariya mukayi gaba Daya Abba yace ah ai da gaskiyata Dan namanmu yanzu na dari biyar sai muci da yawa ya kalli Mami ya zaro Mata ido tare da cewa yanka Goma Zaki dinga zuba min yanzu, Inno

Please Login or Register in order to submit comment