Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da tsugunawa har kasa na Mika Masa tare da cewa ranka ya Dade gashi,Tnx ya furta tare da karba Yana min wani kallon so,Aabid na zubawa shima na ajiye Masa a gabansa na koma na zauna,Muka Fara kalamai na kauna Wanda Aabid yaji Fauzan Yana bashi kunya ya fita yace idan kun Gama Ina waje Ni,ai kuwa tashinsa ya bamu dama sosai.daga Nan Fauzan yace kwana Nan za a kawo kudi Inshaallah Ina komawa Zan fadawa Ammi na,farin ciki ya riskeni nace Allah ya kaimu,mun Dade Muna Hira sannan na rakashi ya gaida su Mami Aiko Munsha kudi Ranar na raka su mota,Fauzan ya bani kudi zasu Kai dubu Hamsim sannan Suka tafi Aabid ya maida shi Airport ya tafi gida.

Bayan Kwana Uku Fauzan ya samu Amminsa a dakin mai martaba yace Ammina Ina so na fada Miki na Samu matar Aure,Nan take Ammi ta Bata Rai tare da cewa ai kuwa kayi a banza don mun rigada mun Yi maka Mata Yar kanin Mai martaba Rumasa'u ita zaka aura tun Kuna jarirai me martaba yayi alkawari sannan Babu kishiya ko zakayi sai Ruma ta Fara manyanta,Maimartaba Yana ji yace Haka yake Fauzan kasan Kuma ba a ja dani, Fauzan baya son Ruma,shi Raudat yake so Amma Haka yace na gode Maimartaba ya mike ya wuce part dinsa.

Ban san Zancen ba naji dai wayarsa Bata shiga har 4days lokacin Fauzan Yayi Bakin ciki har ya gaji karshe ya yanke Hukuncin sanar min gaskiya kawai bazai iya tsallake kudirin Iyayensa ba,Yana Sona Haka ya hakura Dole ya sawa zuciyarsa hakuri da juriya ya Fara Kiran Aabid a waya Ring Daya Aabid ya daga.
Labarin komai ya bawa Aabid,Aabid yace Bai San zance ba,ya dinga Bala'i Kamar Zai kashe Fauzan,yace kasa na zubar da mutunci na jawowa yarinya,yanzu me zance Mata,Kuma sai dana fada maka tun farko karka sake cutar da yarinyar Nan da iyayenta,na fada maka kace baka da matsala gaskiya baka kyauta min ba ko kadan,Yarinya sai wasan Kura akeyi da ita wannan ai wulakanci ne,Fauzan yace ikon Allah Aabid sai kace Kai ne Raudat to ai Kun dace ka aureta Mana Kai shike Nan ka taimakemu,Tsaki Aabid yaja yace Ni ai ba sa'a ta bace nafi karfinta, sai ka kirata a waya ka sanar Mata halin da ake ciki akan iyayenka ya kashe wayarsa ya bar Fauzan da mamaki.

Ina Daki saman gadon Mami a kwance Ina karatun Islamiyya wayata tayi Kara nasan Fauzan ne burin rayuwata,Farin ciki ya kamani na daga tare da kashe murya nace Ranka ya Dade My Soul ya gida yasu Ammin mu? Kasan kuwa I miss u,pls yaushe zaka zo na ganka,Fauzan zuciyarsa ta karye,jikinsa yayi sanyi,kunya ta kamashi akan abinda zai fada min,ya daure da kyar yace Raudat kiyi hakuri ki yafe min Ina so ki sani kaddara ce Allah ne ya kaddaro Mana, Wai me kake nufi ne ban Gane ba? Yace Raudat ki yafe min ya fada min duk abinda iyayensa Suka ce akan aurenmu,nace karshe dai kaima ka fasa sabo da Umarnin iyayenka,Kiyi hakuri Dan Allah Na fadawa Aabid akan Haka yayi fushi Dani Yana masifa,a hankali nace ba komai Allah yasa Haka shine Alkhairi Nan na kashe wayata na bude bayan wayar na zare layina tare da karkaryashi na watsar,na bude tsohuwar akwati can kasa na jefa wayar a ciki,nace Allah ya gani na Gama soyayya auren ma bazanyi ba na hakura gaba Daya Inshaallah bazan Kara kula kowa ba na furta ina me fashewa da kuka me ciwo har na gaji na daina tare da Fawwala Allah na fadawa Su Mami Suma su daina sa Rai.

Banyi kuka ba Amma Jinina ya sake Hawa cuta ta kamani me zafi muka koma zuwa asibiti duk abinda akeyi Umma Bata sani ba,Aabid ma Bai San bani da Lafiya ba, cuta har ta Kai ta kawo aka kwantar Dani a asibiti aka bamu gado gashi Abba bashi da kudi Dole kudin wasu Kayan dakina da aka siya aka siyar dasu Ana Yi min magani.
kwana na Uku Mami ta sanarwa Umma,Aabid bai ji Dadi ba sabo da shi ya hada abin.
Umma ya dauka a mota suka taho asibitin Gomnati da muke ciki zasu duba Ni.







AsmaBaffa.
[4/16, 9:51 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙







21-25








Official







By
AsmaBaffa






NA KUDI NE

Ga masu bukatar RASHIN SA'A COMPLT Dari Uku ne 300 ku nemeni a pc ta Number ta 08033933642

YAN NIGER ga masu nema ku Nemi wannan Number
+227 90 79 59 39.


TA GYARU dari biyu ne 200 ga masu bukatar a sasu a group dinsa
Zaku iya tura number katin MTN ta Pc na a wannan number
08033933642

Masu son siye ta hanyar Transfer Kati ko Vtu zaku iya Turawa a wannan number
09032409668.

Masu bukatar siye ta banki ga accnt number da zaku tura
2177560408,Yahaya Garba Muhammad,Zenith bank.

'YAN NIGER Ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.






Page naku ne
Mrs Mukhtar
Mmn Beelal
Batty
Aysha Humaira Mk and
Zainab.





Naji sauki ba laifi Inno tace tashi kije kiyi wanka ki shirya sai kici Abinci kinji, yau Ina period nace Fadeela taje siyo min pad yanzu zata dawo ai,Kafin na rufe baki Fadeela ta shigo da Pad a hannunta ta mikawa Inno a bakar Leda tace to Inno ke Daya zamu Bari Har Mami mun tafi gida zamuyi Wanka muyi Abinci sai dare zamu dawo sai ke ki tafi,To Allah ya tsare maza ku tafi,Fadeela da sauri ta fice zuwa Wajen Mami da Rufaida, Mijin Aymana ya kwashe su a mota suka tafi gida.Abba kuwa kullum sai yazo yayi min fada akan nayi hakuri.

Inno ta fito kenan zata siyo Mana ruwa taga Umma da Aabid sun fito daga Motar Aabid, Inno tace sannunku da zuwa Suka gaisa tare da Yi Mata ya me jiki tace da sauki kuzo na rakaku dakin da muke Sai na barku naje na siyo abinda Zan siyo,Suna Baya Inno tana gaba Suna Baya tace ga dakin tana ciki,Umma ta shigo sai Aabid na Gama baje Pad a saman Bed na dauki Daya na juya zan shiga toilet naji Sallamar Umma,Kunya ta kamani Yanda na bude pad na fito dasu dawowa nayi na zauna Saman Bed,Umma tace Raudat Ashe Haka Abu ya sake faruwa Kuma? Kaina na sadda kasa sai Hawaye sharrrrr ya Fara zubowa a saman Hannuna Umma ta rike Hannuna da Tausaya tace Raudat Hakurin da Kika Saba Kaddara ce Allah zai Baki Wanda yafi su,Kuka na fashe dashi tare da rufe idanuwa na naci gaba da Yi,Inno tace Haka takeyi duk Wanda yazo dubiya sai ta sake tashin ciwonta gashi Bata cin komai sai Dan ruwa take kurba,Umma tace gashi ai na gani duk ta lalace ta karmashe Ni 'yasu sai Dan kashin wuya, Likita me Allura ne ya shigo yace my patient Ana ta kuka,ke kullum sai kinyi kuka,Idona jage jage da hawaye nace Ni baza ka sake min Allura ba na gaji ga magani kullum a dirka min, Likita ya Fara Lallashina Yana zuko ruwan Allura, Inno tayiwa Umma signa Wai ta taso su bar dakin, suna ficewa tace ki kyaleta Aabid yana wajen Kuma taga ba Mata zata tsaya ayi Mata Amma idan muna Nan Bata yarda sai Shagwaba Iri iri.
Murmushi Umma tayi Suka tafi siyayyarsu da Inno.

Ina Zaune Doctor yayi yayi na bude Duwawu yayi min naki,yace nafa gaji wlh Nonsense kina Bata min time, kunkuni na Fara nace me kuka iya ku har abada likitocin Nigeria baza ku waye ba ace kun kasa koya Allura da Kaya a jikin mutum,Bature kuwa da Jean ma tsirawa zaiyi, Doctor ya gaji ya tafi da niyyar ya rikeni yayi mini na mike tsaye derere a saman Bed din,Aabid Yana kallonsu Dr yace Malam kaga kanwarka abinda takeyi wlh zan tafiyata Kuma bazan dawo ba,Aabid ya mike tsaye tare da gyara hannun rigar shaddarsa Fara,ihu na saki na zauna a saman bed din,Aabid ya karaso kamshinsa ya cika min ciki,daukana yayi kamar yanda ake yiwa Yara Kamar jaririya Haka yayi min gashi yayi min rikon gaske Amma na dinga wutsil wutsil,Dr yace bafa zata tsaya ba ka sabata a kafada,Aabid ya sake juyani ji kawai nayi wani shilll ya sabani a kafa ya danne kafafuna da Hannuna kaina ma ya danne da hannu Daya,Dr ya bude skert Dina kadan ya tsira min Allura na kwalla Kara sannan ya fice abinsa, Aabid kuwa saman bed ya jefa Ni Kamar kayan wanki tare da cewa idan kin ga dama ki mulmula,Harara na watsa Masa nace anje turai an koyo iskanci Allah ya kiyaye ka taba Haramun Wuta Bal bal.

Murmushi yayi yace ae naji ke Kuma 3-0 aka sake Yi Miki,ta Kuma lekowa ta koma, Nan take Hawaye ya cika min Ido muryata tana rawa nace ai koma Mene Kaine ka cuceni tunda Kai ka hadani dashi, yanzu ke akan Namiji kike kuka? Kina bani kunya cewar Aabid,kuka na saki da karfi ya kyalkyale da dariya yace Dan Allah ki daina kukan nan Haka a samo wani sabo ko Almajiri ne a hada ku, gashi dama Ina da wani me gadin makarantar boko zan hada ku,Hawaye Yana zubar min sai Kuma dariya ta zo min Ina Hawaye Ina dariya, Aabid yace da gaske nake wannan bazai Yi ta leko ta koma ba ya furta yana dariya yace kina bani dariya yarinya ko 20yrs har yau Baki Kai ba kin damu kanki sai kinyi soyayya da aure,to Wai me kike so a auren ne? Ko love baki iya ba,Ga Dan Hamisu ma ko a Bari Hamisu ya dawo nan gaba? Ka Bari na warke kaga acting maza sun shiga Uku ba tausayi ba Imani duk Wanda yazo wajena kudinsa zanci na yaudari shege.

Dariya Aabid yakeyi min yace Haushin Rashi ne dai Kowa sai ya daga Miki red card Allah sarki poor Raudat,Haushin Aabid yasa na mike tare da daukan pad dita na shige wankana.

Ina shiga wanka yaje cikin mota ya dakko abincin da Umma tazo min dashi,Zama yayi a gefen bed din inda yake, a hankali ya dauki pad Daya ya bude dama Bai taba dauka ya gani ba,Jin motsina yasa na ajiye da sauri tare da basarwa.
Har na fito da shiri tsaf har kaya a toilet na canja gefe na Samu Nima a gadon na zauna na dakko Dan Vaseline na shafa a kafafu da Hannuna, ko anyi sabo ne Doctor? Ta gefen Ido na harareshi,yace princess ta Dan sarki,shike Nan ya wuce ya jikin naki? Gani ai ka ganni sai yanzu zaka tambaya ya jikina, to ga abinci nan Umma ta kawo miki, flasks din kala uku masu kyau sun birgeni.

Da kansa ya bude min Flask Daya babban Fried rice ce da soyayyun kaji harda su hadin salat,dayan Kuma Farfesun Naman Rago,Daya Kuma faten wake da Hanta, sai naga wani Almajiri ya shigo da manyan caton na lemuka kala uku da ruwan roba tare da kayan tea su madara da Milo gasu Nan dai, Aabid yace ga nawa kayan dubiyar Allah ya Kara lafiya,Ganin kayan Dadi nayi Murmushi na nuna Masa Farfesun nace ta Kan wancan zan Fara,Aiko ya zuba min a plate da kansa,na karba Ina cin abina a nutse, Santi yasa na manta nace Umma ce ta dafa wannan? Uhm kawai yace,na dakko wata tsoka na lukuma a Baki nace Wai da gaske Allah ba Umma ce ba ta haifeka? Yace Umma ce Mana Yana boye dariyarsa,na dauko soyayyar Kazar na yagi Mamanta sai naji tafi Farfesun ma nace to ya kuke da Hamisu ne? Yayanka ne?Aabid dai yace Ae Yana murmushi,na kalleshi kadan nace Ni dai nafi karfinka bazan taba sonka ba ehe, Baki Aabid ya tabe yace Asiri kawai zance kin min gwara da Kika fada min Kinga Zan fadawa Umma idan taga nace Ina sonki kawai ta nemar min magani,Yarinya Baki Isa na soki ba nima Gwara ma ki samawa kanki lafiya,to Ni me zanyi dakai Daga na maka warning kallonsa nayi nace zuba min Faten waken to, ki Bari Cikinki ya huta Mana kinci wannan kinci wancan kamar rainon kauye,Ina ruwanka da cikina Ni ka zuba min pls, kadan ya zuba min a plate Yana cikin Zuba min su Umma Suka dawo,Inno tace taji girki da nama gashi taci Amma namu Bata ci munafuka,Murmushi nayi kawai na karbi abina Ina ci.

Ina cikin ci na jawo Wani karamin Paper ta Magunguna a gefe na rubutawa Aabid Kamar Haka:
Karka Manta da kudin Ankon saura 3wks, idon su Umma na faka tare da Dora Masa a cinya,ya dauka ya karanta,shima ya Rubuta min Kamar haka:
Nawa ne?
Karba nayi na karanta Nima na sake rubuta Masa
Kala biyu ne nace dubu biyar,atamfa dubu uku,sai gyale Banda takalmi Ina Dasu,karantawa ya sakeyi yayi Murmushi ya rubuta
kin saci rabonki yarinya
Kyaleshi nayi na ajiye paper da rubutun.

sai Ga Hamisu ya shigo Umma ce ta takura Masa Dole yazo dubani
Yana zuwa ya gaida Inno yace sannu Raudat Allah sarki Raudat kiyi hakuri Nan gaba na gani ko Zan iya taimaka Miki,Fuska Umma ta Bata tace jeka dubiyar ta isa zai sake magana tace bana son ji jeka kawai kaba mutane masu hankali waje.
Dole ya fice ya tafi gida su Umma sai dare sannan suka Yi Mana sallama zasu tafi Umma ta bani dubu biyu, Sun fita gaba Daya har Inno zata rakasu Ni kuwa na Kwanta tare da lumshe Ido,Aabid yace Kash nayi mantuwa,na manta key na ya sharara karya ya dawo dakin da nake, da sauri na mike Zaune ganin Aabid, dubu goma naga ya ajiye min a gefena yace gashi Nan badan halinki ba Dan kawai Abinda abokina yayi Miki ne Amma da sisina baza ki gani ba,Dadi naji na samu kudin anko nace na gode Allah ya Kara budi, yaje bakin kofa nace Baka ce Ameen ba Aabida, da sauri ya juyo yace me Kika ce? Nace baka ce Ameen ba jajirtaccen Namiji Aabid na Umma ikon Allah Alhaji Aabid me hadarin Naira, zanyi maganinki ya furta fuska ba Rahma yayi waje.
Ni kuwa ajiyar zuciya na sauke tare da boye kudina.

Bayan kwana biyu har Faruk yazo ya dubani Fauzan kuwa ko keyarsa ban gani ba har na warke aka sallame mu Muka koma gida.
Rufaida ce ta shigo gidan da Jarabar Iyayin data Saba,tana wani tsuke Baki magana kasa kasa ba a ji sosai tace Raudat tunda kin warke ki kawo kudin ankon naki a siyo a Kai dinki,kudin na Mika Mata,sai ga Aymana Hashim dinta ya kawota zata sake duba Ni Aymana yanzu iyayi ya karu sabo da ta Auri miji me sonta me Hali Kuma,Kaya masu tsada take sawa itama Eggs da yawa ta kawo min na dubiya.
Tunda na boye wayata ban sake fitowa da ita ba har na warke Ras Dani Wanda yanzu bani da burin da ya wuce naga nayi samari Wanda Zan dinga Yaudarar su Nima na Rama abinda akayi min.
Haka kuwa Ranar da Zan koma Islamiyya wani Babban Banza ya tsaya a mota tare da tareni,Banyi ko musu ba na bashi number wayata Dana sake sabon layi.
Yace Address dinki fa Yan Mata? Sai na bashi Address din gidan su Aabid Muka rabu.

Ina dawowa daga Islamiyya na shirya kayana na tafi Gidan Umma zanyi kwanaki acan daga can Zan dinga zuwa Islamiyya,sannan Target na hada yanda zan dinga zance da Samarina ba tare da sunga Abba ba bare ya koresu da Halinsa.
Washe Gari na kwana Daya gidan Umma Alhajina Dattijo yazo zance, Muna cikin Hira a cikin gidan saman kujeru na Yar rumfa Aabid ya dawo daga kasuwa,Yana ganin Wanda na jajibo yayi Murmushi yace wato a Nan za ayi damfarar kenan to zanyi Miki bakin ciki matukar Ina Nan sisi baza ki samu ba,yarinya har abada Bata Kulla alheri, wa zai aureta a Haka.
Yana Gama fadin Haka ya fito a motarsa fuskar Nan ba kwayar fara'a kamar zai dakemu ya karaso inda muke Hira nida Alhaji Yahaya, sallama yayi sannan yace Malam karka Kara zuwa Nan wannan da kake gani saura sati daya bikinta yaudararka zatayi kawai ta cinye maka kudade a banza.

Alhaji Yahaya ya mike yace Raudat Amma Kika ce Baki da kowa kina min kalaman soyayyar banza Allah ya kamaki dama jarabata ta kawoni Ina da Matata da yarana,Aabid yace Ka koma ka rungumi abinka ya fiye maka Baba.
Kallon Aabid nake kawai Kamar zanyi kuka na Gama hada Target zan wanki Alhaji kudade Aabid ya cuceni,Ina kallo Alhajin yaja motarsa Rai a bace ya bar gidan Bai bani ko sisi ba,Aabid ya tintsire min da dariya yayi tafiyarsa,da karfi nace bazan kawo ma Abinci dare ba yau ko Umma ta aukoni zubarwa zanyi, Hannu ya daga min Yana tafiya Bai ko juyo ba,haushi yasa nace Aabidede Aabida....Bai kulani ba.

Bayan kwana biyu sai da na tabbatar Aabid ya tafi Kasuwa nace sabon saurayina yazo zance,Matashi ne wannan ko mota bashi da ita,a kafa yazo shima Muna zaune nayi Masa girki na hada Masa lemo Ina so na fanshe kudina kawai sai ga Aabid ya dawo yayi mantuwa, Hankalina ya tashi nasan korarsa zaiyi Dan Kar na samu kudi,direct wajenmu ya nufo na tsaya da Ido nake rokon Aabid Ina nuna Masa abincin Dana Hada Dan Allah ya Bari na fanshe wahala ta Amma Aabid yace Malam wannan Sati me zuwa aurenta idan baka sani ba ka sani Dan Haka ka tashi ka tafi,Matashin zaiyi magana Aabid yace bana son ji Fuska ba rahma,Aiko shima ya tafi abinsa Yana Jin haushina,Aabid ya juya Yana tafiya na bishi da Sauri Haba Dan Allah kalli wahalar Dana Sha na hada girkina ya cinye a banza ba ko sisi Ni ba sonsa nake ba,ka koreshi Wai me na tare maka ne? Ba tare da ya kalleni ba yace ki koma gidanku ki Tara mazanki Amma wlh ba a Nan ba,idan Zaki Tara dari matukar a gidanku ne ba ruwana dake, kallonsa nayi Ina binsa Muna tafiya cike da Shagwaba nace Ni...Ni...ahhhhh....uhmmm....na Fara Kukan Shagwaba Ina Doka kafafu a kasa.


Ayi hakuri da wannan









AsmaBaffa.
[4/16, 9:53 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙









26-30







Official








By
AsmaBaffa





NA KUDI NE

RASHIN SA'A COMPLT dari uku ne 300 ga masu bukata ku Nemi wannan number
08033933642.

'YAN NIGER ga number da zaku nema
+227 90 79 59 39.


TA GYARU ga masu bukata dari biyu ne 200

Masu bukatar siye ta Hanyar Tura kudi ta banki ga accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad,zenith bank.

Masu son yin transfer Kati ko Vtu ga Number da zaku iya turawa
09032409668.

Masu son Siya ta hanyar Tura number katin MTN ta WhatsApp Dina ko sms ga number ta
08033933642.

'YAN NIGER Ku nemi wannan number ga me son Siya.
+227 90 79 59 39.





Page naki ne
MOM ABDALLAH
JAMEELA SANI
FANCY HONEY
HAJIYA ABOU
JIDDERH BABANGIDA &
ANTY NURSE ZARIA.


INA GODIYA MASU SHARHI😍😍😍😍🥰😘







Tafiyarsa ya karawa sauri tare da shigewa cikin bangarensa ya banko kofar sa harda sa key,Dole na koma na kwashe kwanika na maida kitchen sannan na kaiwa Umma Kara, nace Umma kin ga Ya Aabid ko kiyi Masa magana gaskiya ba ruwana dashi Taya Zan kawo samarina ya dinga korar min su, a'a bazan Masa fada ba Raudat ke duk Yaudarar Nan da maza suka Miki bakiyi hankali ba kike Kara kwasosu sai sun yaudareki su Tafi Aabid yayi min dadai, Bedroom na shige kawai Ina fushi.

Abbanmu a cikin Manyan abokansa Allah ya azurta Daya ya Zama Dan Majalisa,mutumin kirki ne Bai Manta da abokai ba,yasa aka Kira Masa Abba,Yaje har gidansa Suka tafa suna Wasa da dariya abokai an hadu,Dan Majalisa Hon Danjuma yace Mutumina me kake so na baka na jari ka Kama babbar sana'a tunda Allah ya hore Bai Dace na barka Haka ba, gaka da Yara suna bukatar kudin makaranta,Amma yanzu mu Fara Maganar Jari me kake bukata Wanda zaka huta ka dinga samun kudi? Abba farin ciki ya kamashi yace Danjuma duk duniya idan mutum Yana so ya birgeni to ya siya mini mota Yar kurkura akori Kura ita nake so kawai ko Makkah bana so irin Kurkura,Danjuma ya dinga dariya harda buga kafa,yace Haba haba mutumina ga Abubuwa masu tsada Wanda zaka samu kudi Amma Kurkura ai duk Kanwar Ja ce ka zabi wani abin dai,Abba yace to Ni dai ka siya min Kurkura ta kawai ta isheni sai Kuma ka bani kudi na bude gidan kallon Ball ko Dambe, Danjuma ya kada ya Raya Amma Abba yace shi abinda yake so kenan Dole yace to ba komai Amma nasan Halinka bazan baka kudin a hannu ba kashewa zakayi,sannan idan auren yaranka ya tashi ka turo Min Mami tazo ta karba da kanta kudin kayan daki bazan baka ba na San Halayenka,Dariya sukayi Suka ci gaba da Hira sannan Abba da yamma yace zai tafi Danjuma ya bashi dubu Hamsim.

Lokacin Ina gidanmu sai gani mukayi Abba yasa matasa sun shigo da karamar Dstv, gaba daya ya kashe kudin Daya samo, alhalin gida Babu ko geron koko ya dakko me gyara ya hada Masa tare da kamo tashoshi a Tv din dake Palo, Abba yace tashar Dambe da Ball kawai nake so ka hada min bana son ko wacce,me gyara yace An Gama,haka Babu wata Tasha Daga ta ball sai Dambe, kullum Abba yana makale a gida Yana kallo indai ance Akwai nepa,tun bama kallo har muke Shiga Ana kallo damu Ball Bata wuce mu, premier,Laliga,FA cup, champions leaque, European cup,karago cup,seria A, Bundesliga etc Haka muke kallo muma mun Saba,Inno da Mami ne kawai basa kalla.

Tunda na dawo ban koma gidan Umma ba sabo da yanda Aabid ke takura min sabo da Ina kawo samari sai da Umma ta Nemo Ni a waya naje sannan na tafi gidan bayan naci kwalliyata nayi kyau.
Ina zuwa naga Motar Aabid a gida tabbacin Yana Nan,Palon Umma na Shiga na hango wata Kyakyawar budurwa Chocolate da ita taci wanka Na gaske da gani Kasan Yar masu kudi ce,nayi kwalliya Amma sai dana Raina kaina akan Budurwar da baza ta wuce 23yrs ba.
Da fara'a na Karasa kusa da Umma Dake saman Kujera suna Hira da Budurwar jefi jefi,Sai Iyayi takeyi tana Shan kamshi,tana ganina ta Kara wani Bata fuska tana tauna chewgum a hankali tana Shan lemon da Umma ta kawo Mata,ganin irin Kallon banzan da take min nima ban kulata ba nayi zamana,Umma tace Bakuwar Aabid ce fa tare Suka Yi karatu a Turai tazo Nigeria jiya shine tazo wajensa,Baki na tabe nace Uhm tare da gallawa Bakuwar Harara,Umma tace sunanta Mufeeda nace Mufeeda? Mene kuma Mufeeda? ko Dadi ji Babu haka,Mufeeda bakuwa ta kalleni ta Kara hararata tare da yatsina fuska ganin kyau na tana tunanin Aabid zai so ni,dama ita ce take sonsa sosai,Umma ta mike tare da cewa Aabid ya tafi wanka Raudat zauna wajen Bakuwar Bari naje nayi Sallah na fito,to kawai nace Ina Danna kwakurar wayata minti Daya Daya sai na kalleta naja tsaki, Muryar Mufeeda naji Tace nifa na tsani kallo irin kallon kauyawa,kawai ayi ta kallon mutum, Baki na tabe nace Ina abin kallon? Me za a kalla a Nan wajen hanci Kamar gajeren Wando, Mufeeda Taji Haushi tace ai gwara Ni shegiya kodaddiya da ganin farin Nan harda Mai Kika Kara, Nima nace Ubanki ne yake bani kudin idan yazo zance wajena, Ke Ni ba sa'arki bace

Please Login or Register in order to submit comment