Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka fasa,ka tuna yanda iyaye ke wahalar kashe kudi idan ance za ayi auren yarsu,me nayi maka Hamisu? Ko wani ne ya fada maka Ina da halin banza? Dan Allah ko Dan kunyar mutane karka ce ka fasa pls Hamisu,Hamisu ya kalleni yaji wata tsanata a ransa tsawa ya buga min nace na fasa aurenki ko Dole ne? Ina da matata Hauwa ta isheni ita kadai da Dana,Na gane gaskiya Hauwa ta isheni ita ce a gabana yanzu,ki fadawa Iyayenki Wlh na fasa aurenki Kuma duk duniya ba Wanda ya Isa yasa na aureki ko Umma ce,bani da wata Hujja kawai ji nayi na daina sonki na tsaneki Hauwa ta nake so,bazan aureki ba kudi Dana kawo kuje duka na bar muku,Ni abinda ma ya fito daga hannunku ma bana kauna Allah yasa ban kawo lefe ba yawwa,ki fadawa ubanki na fasa aurenki ko a Hanya karki nuna kin Sanni gaisuwarki bana so ya juya yayi tafiyarsa ya barni a tsaye.

Duk abinda Hamisu yace a kunnen Abba,sai juyowa nayi Naga Abba Yana Hawaye shi kadai,ganin Ina kallonsa ya share da rigarsa da sauri tare da daga kansa sama ya shiga Gida.
Ni kuwa bakin ciki yasa na fashe da kuka a wajen ji nake Kamar nayi hauka me zance da mutane kawaye etc, ko gida ban shiga ba na wuce gidan Umma.
Ina kuka na shiga gidan Umma ko sallama banyi ba, duhun magrib ya Fara Palon Umma yayi duhu ban San da Mutum a doguwar kujera ba na fada Kai Ina kuka na sai naji kamshin Aabid yace Ouchchch...jikina ya dauki rawa na mike zumbur da Muryar kuka nace kayi hakuri ban San da Mutum ba Ina Umma....yiiiiii....naci gaba da kuka na.

Umma ce ta fito daga bayi tace naji kamar kukan Raudat Lafiya,Naje wajen Umma da rarrafe na rike kafart ta kenan Suka kawo nepa haske ya mamaye Palon Aabid ya mike Zaune Yana kallon kukan da nakeyi shi tunaninsa Mami ko Abba ne ya rasu, nace Umma Hamisu ne...yiiii ...ya...yace...ya fasa aurena,Umma ta rafka Salati tace me kika masa?..nace yace bashi da Hujja kawai dare..dare...Daya..yaji..ya...tsaneni Matarsa Hauwa yake so..Umma ki duba abin Nan wlh Iyayena da kyar aka samo kudin da za ayi min komai na bikin Nan...munji kunya a idon duniya....Hannayena na daga Sama kamar me Addua Ina kuka nace Hamisu musanye aka Yi Miki a asibiti Umma ba danki bane ayi bincike..munji kunya...Hamisu ya tozarta mu...na juya na kalli Aabid Dake danne dariya nace dama wannan ne yace ya fasa sai nace da dalili Amma Hamisu me nayi Masa yace Hauwarsa ta isheshi ita yake so..Umma tace Hauwa Matarsa? Da Sauri na daga Kai nace Ehhh...Hauwa Yar dukurkura....yiiii...shegiy..tsayinta kamar keken dinki... Umma abin Nan bada Wasa bane Kiyi Hakuri Zan Dan zageshi Amma Hamisu Tsinanne ne... Dan Iska,tambadadde ..sai Daya Bari na hakura das...Muna Haka sai ga Hamisu ya Fado dakin nace yawwa Alhmdllh gashi ma yazo da shegen goshi Kamar taragon jirgi , Baki Kamar Ana busa Algaita,lebe Kamar bututu, Aabid Yana ta dariya a ransa har ya kasa Dannewa Daya kalli Hamisu yaga makeken goshinsa, a ransa Yana Allah ya Kara dama Kamar wannan me kyau Haka kije ki zabo Hamisu idan ba lalacewa ba da shashanci.

Umma ce tace Hamisu fada min dalilinka na fasawa? Hamisu yace wlh Umma Babu dalili Hauwa ta nake so na tsaneki Raudat, Haka kawai naji na daina sonta,Umma tace ikon Allah cab jeka gida to Inshaallah itama Raudat ta hakura ta fasa aurenka kaje da hauwar taka Allah yasa Haka shine Alkhairi....da sauri nace shegiya me Kama da keken dinki.
Aabid ya kwashe da dariya,Hamisu ya Balla Masa Harara Yace Shege Dan Wanda ba ganshi ba ya fice.

Aabid ya kalleni ya sheke da dariya yace ta leko ta koma sau biyu saura na Uku,ke akan wani Hamisu kike wannan haukar aike murna ya kamata kiyi ki samu ki sake zaben wani na kirki kin zauna kina batawa kanki lokaci, Uwaka Aabid maimakon ka lallasheta sai banzan surutu cewar Umma,dariya ya dingayi ya mike tare da fice wa yana ta yi min Dariyar mugunta.







AsmaBaffa
[4/16, 9:31 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙








16-20







Official







By
AsmaBaffa.






NA KUDI NE

RASHIN SA'A COMPLT ga masu bukata dari Uku 300.
Zaku iya nemana ta wannan number
08033933642.

YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.


NA KUDI NE

TA GYARU dari biyu ne 200, masu so a sasu a group din domin ci gaba da karanta Ta Gyaru idan WhatsApp ko Sms Zaku tura lambobin katin mtn ga number ta.
08033933642.

Ta Hanyar Transfer ko Vtu ga zaku tura a Nan
09032409668.

Masu bukatar siye ta banki to ga accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad,Zenith bank.

'YAN NIGER ku nemi wannan number din
+227 90 79 59 39.


Ina matukar Godiya Fans Wanda Suka siya da Wanda Basu siya ba Ina Miko gaisuwa😍🥰 ana tare.





Page naku ne AMINA and NAFI.





Lallashina Umma ta dingayi tana Yi min Nasiha tace Haba Raudat Kamar Baki San kaddara ba,Jarabta ce Allah yake Miki keda Yan gidanku Dan ya gwada Imaninku wasu ma Matan mazajen su ke mutuwa duk Wanda Suka Aura,Kuma idan Kika yi Hakuri Kika barwa Allah sai yayi Miki canji Wanda bakya zato, Nace Gashi na shiryu na daina sabo bare nace laifi nake aikatawa,Allah kenan ai ko kana Masa laifi ko baka Yi Masa zai jarabceka,musamman me Imani,iya Imaninka iya jarabtarka,Allah baya dorawa bawansa abinda bazai iya ba,a Haka da Zaki ji tanadin da Allah yayi Miki sai kiyi mamaki,Dan Yana sonki ne yasa ya hanaki Faruk da Hamisu,kiyi hakuri karki damu kanki Allah zai Baki Wanda ya fisu, Ameen na furta naji zuciyata tayi Sanyi Sallar Magrib nayi sannan nayiwa Umma Sallama na dauki hanya.

Zauren na shigo me duhu Zan fice naci Karo da Mutum ya shigo Aabid ne mukayi Karo kaina ya bigi Kirjinsa naji wani kamshi da laushi, Bai kulani ba yayi wucewarsa shima Nima na tafi gida.
Ina Shiga Gida Suka ganni fes Dani kowa yayi mamaki anyi tunanin za a ga na sume ma,Abba ya Basu labari ashe,Haka Suma Suka shiga Lallashina da Nasiha nace ba komai.

Bayan wasu kwanaki zance ya sake watsuwa an fasa bikina a unguwar sai gulma akeyi iri iri,ko fita bana son Yi sai Dole,
Naci gaba da rayuwata karshe kudin da Suka rage na Fara sana'a dasu Ina yin Snacks ina kaiwa kantin wani Yana siyar min wani Kuma na shiga private schl na Kai a siye Riba nake samu sosai.
Lokaci lokaci Ina zuwa Wajen Umma Haka rayuwar ta kasance Mana yayin da Aymana ke dauke da yaron cikinta.Umma da Yan uwanta Manya har gida Suka je Suka bawa Iyayena Hakuri Kuma kudin da Suka kawo basu Karbi komai ba suka ce sun yafe.

Aabid kuwa Neman kudinsa yakeyi abinsa akwai wani abokinsa Fauzan masu kudin gaske Aabid ya taimaka Masa a schl,Lokacin da ya samu matsala a exam Aabid ne ya tsaya aka gyarawa Fauzan result a turai..
Fauzan Dan sarkin Sokoto ne,suna mutunci da Aabid sosai,Fauzan wankan tarwada ne Kyakyawa matashi 29yrs,Yana zuwa gida ya sanarwa Aabid zaizo wajensa Kd daga Nan zai wuce Abuja.

Ranar da Fauzan zaizo Ina gidan su Umma,tun Aabid baya kulani tsabar zuwa gidansu da nakeyi da Kuma tsokanarsa da nakeyi Dole watarana Yana kulani.
Muna kitchen tare da Umma Aabid ya fada Mana Yana da bako, ai kuwa Muka dage tare da shirya girke girke masu Dadi,Ina yiwa Palon Umma turaren wuta naji Sallamar Su Aabid su biyu sun shigo,Aabid yace ke Ina Umma Sallah takeyi Amma yanzu zata fito,Fauzan ne yasha kayan sarauta ya dau wanka,kasa na duka tare da gaida shi ya amsa da sakin fuska Yana kallona Har Umma ta fito, Suka gaisa Aabid yace shine Wanda nake Baki labari Fauzan, to Alhmdllh mashaallah cewar Umma,gaba Daya idon Fauzan Yana kaina.

Suna fita yace Aabid kanwarka ce? Aabid yayi Murmushi yace kawai zaman mutunci a layin Nan take ya bashi labarina yaji tausayina na rashin masoya biyu,Yace Ni wlh Ina sonta idan zata so ni,wannan irin Kyakyawa kana kallo zata wuceka,baki Aabid ya tabe yace sai dai ku Ni tayi min kadan,dariya sukayi tare da tafawa har suka karasa dakin Aabid Suna ta Hira na Kai musu Abinci a katon Tire na koma na kawo kayan Sha na juya zan tafi kenan Aabid yace Baki zubawa Fauzan ba, Haka na juyo a kunyace na zuba Masa lemon Dana hada kaina kasa na ajiye na mike da sauri na bar Room din Fauzan Yana ta kallo na, Aabid yace to ta tafi rufe Idon naka dariya Fauzan yayi yace ka birgeni abokina daka ce ta zuba min Zanji dadin Shan lemon,Aabid yace Kuna bani mamaki wlh Wai me kuke hangowa ne a jikin yarinyar Nan? Sabo da Kai nace ta tsaya ta zuba maka zaka wani zubar Mana da mutunci Kuma banza Kamar ka me aji da kudi,dariya Fauzan yayi yace wlh baka san yarinyar Nan ba naga Alama makaho ne Kai ko kunun kanwa ne a idonka ko Kuma baka da lafiya Aabid, Hamisu ne ya shigo ko sallama Babu ganin Motoci harda dogarai a kofar gida na Dan sarkin Fauzan.
Umma Waye yazo Haka ? Umma tace Wai yaushe zaka Yi hankali Hamisu ko sallama Babu to Dan sarkin Sokoto ne Abokin Aabid,wani uban tsaki Hamisu yaja yace Ni wlh na zata wajen mutanen kirki Suka zo aikin banza,Fitowa nayi daga kitchen dauke da plate a Hannuna sanye nake da Kaya Yan kanti riga t-shirt baka me gajeren hannu nayi kyau skert din na Jean,na cire Hijab Dina ba dankwali a kaina jelar gashi na har tsakiyar bayana.

Dai dai lokacin Fauzan da Aabid Suka fito zai tafi zai yiwa Umma Sallama, Aabid ne ya Fara kallona naji kunyar shigata komai na surata ya bayyana, a sace ya nuna min da yatsa Wai Ina Hijab Dina,Murmushi nayi na makale kafada da Hannu na nuna masa Iska nake Sha,Baki ya tabe tare da dauke kansa ,Fauzan ya kafeni da Ido Hakan yasa na jawo Hijab Dina a saman igiya na saka, Hamisu Yana ganina a gaban su Fauzan da Umma ya balla min Harara kowa Yana gani, Nima na Rama,ke Ni sa'anki ne? Nace to Ni kaga nayi Kama da Sa'arka? yace aikin banza Ashe Haka kike mummuna Allah ya taimakeni Hauwa ta fiki komai idona ya makance, dariya nayi nace to Ni me zanyi da Kai da dinma idona nane ya makance ance maka sonka nakeyi? Ai auren Huce takaici Zan taimaka nayi da Kai kalleka fa badan jinin Umma ba da ko kallonka ita kanta Hauwan baza tayi ba,Kuma Hauwan da kake fada me ta fini tsayinta Bai wuce Keken dinki ba,gata baka Ana bakake kyawawa Amma Hauwa ita sai a slow,Ni kuwa fa ko me Hassada Dole ya hakura gani zabgegiya,santaleliya,Charkwadediya duk Wanda ya sameni sai ya kwana Yana Nafeela sabo da Murna,Dariya Fauzan yayi sosai,Aaibid kuwa Murmushi yayi Dan shi Hamisu dariya yake bashi da tsokanarsa kamar yaro.
Umma tace bazan hanaki ba Raudat tunda baka ja girmanka ba shashasha ne kai sai kayi ki Rama Raudat.

Hamisu Ransa ya baci yace Umma ke ko kishina bakya Yi Ina danki wata banza tana ci min mutunci kamata yayi ki daina barinta tana zuwa gidan Nan, Akan me? Allah ya hadamu da yata wlh da iyayen Raudat zasu bar min ita Dana karba naji Dadi kuma.
Hamisu ya sake kallona yaja kwafa yace zanyi maganinki ke da wannan Dan Wanda ba a ganshi ba zaku Gane kurenku Kai Dan Me Hatsari wlh idan Ina magana kana dariya zanyi maganinka ya fice fuuuu ya bar gidan,Umma tace Allah ya shirya,Fauzan yayi Murmushi yayiwa Umma Sallama ya ajiye Mata kudade Nima ya bani dubu Goma yan dubu dubu na karba da hannu biyu nayi godiya Ina ta murna,Bayan sun fita yace Aabid ka bani accnt number naka na baka wasu kudi ka Kara jali,Aabid yace na gode nawa sun ishe Ni,Fauzan ya Bata rai yace wlh kayi karya ni taimakon daka Yi min a schl cewa nayi a'a tsaka ninmu Babu Haka Dole Aabid ya bashi Accnt sukayi Sallama ya tafi.
Ba a fi 30mnt ba Aabid yaga 3million a accnt nasa da sunan Fauzan.
Nan take ya kirashi yace na gani na gode Amma kudin sunyi yawa Fauzan kitt Fauzan ya datse wayarsa.

Umma ya samu Aabid ya sanarwa kudin da aka bashi,Ina kwance a tabarma gefen Umma kamar Ni aka Turawa nace kai..Kai...wannan Dan mutunci ne Ina murna Ya Aabid Allah Kara budi ya karo kawo malala gashin Tinkiya Amma zaka Yi min wani ankon Kawata kala biyu ne pls kaji Alhaji Aabid? Umma tayi dariya tace Raudat bakya rabo da Tsokana,Aabid yace kin dauki rabonki ai a can baya yarinya da ace Baki dauka ba da sai na Baki amma tunda kin dauki na Allah ya Isa to kinci rabonki, signa nayi Masa Ina Masa Alama yayi Shuru ya rufa min asiri Kar Umma taji abinda na aikata,Umma naji tace me ta dauka na Allah ya Isa Kai Aabid ku daina yiwa yata Sharri fa to,Mikewa yayi ya bar gidan.
Koda na koma gidanmu kudin na fadawa Mami yanda na samesu sannan na Bata su gaba Daya nace ayi cefane a boye ba tare da Abba ya sani ba sabo da Karbewa zaiyi ya kashe a banza.

Tun daga wannan Rana Allah Bai kaini gidan Umma ba,Ina tsakar gida da yamma Mami ta sani Na tuka Mata tuwo ban iya tuka tuwon Gari ba da kyar nakeyi ga hayaki yasa Ni Hawaye idona yayi jajir,Sanye nake da Yar Vest karama pink da skert ya Dame daga sama kasa ya bude peach color,mota Muka ji ta tsaya a kofar gidanmu,Minti Biyar sai ga Umma ta shigo da Sallama.

Fadeela ta tari Umma da Fara'a tace shigo sannu dake Mami da Yan gidanmu gaba Daya har Inno suna zuwa gidan Umma Ana zumunci, Umma tace Khairat Jeki shigo da Aabid kawoshi nayi a gaisa Yana waje,to tace ta tafi da sauri Mami ta shiga Palo wajen Umma da Inno tare da sauran Yan gidan Ana ta Hira Ni kuwa tunda na Mata sannu da zuwa Ina ta kici kici da tuwo naji Sallamar Aabid sun shigo tare da Khairat, Hawaye ne ya cika min Ido na hayaki na bar Jikin murhun na matsa jikin bango Ina Goge idona Ina Haki.
Aabid kallo Daya yayi min a hankali yace Allah ya Kara kije ki tukawa mutane tuwo Lazy girl ya shige Palo, Muna dariya Ni da Khairat, Ni kuma na Karasa tukawa na rufe tukunya tare da wanke fuska ta Sannan na Shiga wajen Umma da Aabid na gaishesu.
Umma tace Ina Kika shige ne Raudat na daina ganinki Murmushi nayi nace gobe nake so zanzo dama,Allah ya kaimu,ko Aabid yau ya danyi Hira dasu Mami kadan sannan Umma tace Raudat muje ki raka mu,Rufaidat Bata Nan ta koma Islamiyya itama.

Umma na raka naga wata radediyar mota zata Kai ta million biyu ta hadu karshe katuwa da ita baka,Nace Umma motar waye ne? Kwana biyu bakya zuwa ai Aabid ne ya siya Kuma an Gama Zuba furniture da komai a sabon gidanmu an Kai kayan sawarmu ma Gobe zai daukeni mu koma ciki da yamma Dan Haka kizo a tafi dake kiga gidan Kinga sai ki dinga zuwa Kinga waje,dariya nayi nace Mashaallah Allah ya Kara budi Amma Ni dai sai dai ki bani Address din a rubuce bayan kun koma sai nazo a nutse Kamar Nan da kwana Uku Haka sannan kin nutsu,Allah ya kaimu ba damuwa.
Da kaina na rubuta Address din tana fada min sannan suka tafi,Ina shiga Gida na bawa su Mami labari Aabid ya canja musu gida harda mota sabuwa,Khairat tace na ganta ai ta hadu karshe Kinga yanda yayi kyau? Aabid da me kudi ya dace.

Nayi Murmushi kawai nace bashi da mutunci fa wlh wannan idan yayi kudi sai ya taka mutane kina ga inda yake wani takama da gadara ga jiji da Kai,Mami cikin sanyinta tace a'a Haka Allah ya halicce shi karku Yi gulmarsa Babu Kyau Allah ya Hana wlh, Shuru mukayi kawai.

Yau wanka na Sha cikin Wasu Pakistan Riga da wando masu kyau da yake Faruk ya Tara min Kaya da yawa shi yasa nake kwalliyata kudin Napep Mami ta bani na tafi sabon gidan Umma, bakin titi na Isa Ina tsaye Ina jiran Napep wata mota me kyau ta tsaya a gabana tare da sauke Glass din window wani black Handsome ya Hadu ba laifi yace Hi yan mata, Ina zuwa ne? Ko kallonsa ban sake Yi ba na tare Napep Dina na shige na barshi Nan,Napep din yabi a baya Yana ta binmu har Muka je gidan Umma Yana Bina ban sani ba, gidan me Bakin gate yasha kyau sosai tun daga Wajen gidan ya birgeni Ina Sallamar me Napep naga motar dazu ta sake tsayawa a gabana wannan Lokacin motar ya bude ya fito yasha shadda light Coffee color yace haba Yan Mata ba girmanki bane hakan, sai lokacin na tsaya nace Malam sai Bina kakeyi Wai lafiya? Murmushi ya saki yace kinki tsayawa ne ki saurareni tunda na ganki wlh jinina ya Hadu da naki ba sai Lallai ki so ni ba kawai ko Frnd ce ki Zama tawa Muna mutunci kawai ma ya Isa,Jin yace Frnd nace Ni bana wani aboki da Namiji Malam,Haka ya dinga rokata har na hakura nace to iya Friend bana soyayya ni,ok ya furta Yana Murna yace bani number ki,Na zaro karamar wayata Yar dubu uku na karbi tasa na kirashi ta Shiga sannan yace na gode ya shiga motarsa Nima na shiga Gidan Umma gabana ya yanke ya Fadi ganin Aabid danayi ba zato har ya fito yaganni tare da wani ya koma,Ni tsoro naji banyi zaton da Mutum ba,Kansa ya dauke ya koma inda aka tanaji kujerun Zama da wata Yar rumfa kamar ta Yan China me kyau,Wajen sa na Karasa nace Ina yini Ya Aabid wani kallo yayi min sannan yace Lafiya Hannunsa rike da biro da paper Yana duba Business dinsa a waya Yana rubutu,Mikewa nayi zan tafi na tsinci Muryarsa yace Ke zo,Komawa nayi wajensa nace gani yace Irin mazan Nan kike kwasa sai sun sake yaudararki kizo kina damun mutane da kukan banza,ai yace kawai Frnds ba soyayya ba,abin dariya ya bashi idan ba kuruciya ba Taya Namiji zai min wayo kamata Amma sai yace Kin tuna Fauzan Frnd Dina Wanda yazo? Dan sarki? Nima na tambaya,yace ae yace Yana sonki na karbi number ki wajen Umma na bashi kuma Yana da hankali idan ya Miki ki aureshi kawai,Amma baka ganin yafi karfina jibi kudinsu fa ga mulki,ke fa kina birni Kamar yar kauye kije zai kiraki ku karata can idan kun Fahinci juna matsalarku ba ruwana.
Tafiya nayi ciki wajen Umma Ina murna a Raina,ban San gidan ba sai na nufi inda zai kaini bangaren Aabid, Ke ya furta tare da Mikewa juyowa nayi ba tare da yayi magana ba da hannu ya nuna min bangaren Umma Wai can zanyi Kamar me bada Hannu a titi,dariya nayi ya galla min Harara nayi bangaren Daya nuna min.

Ina shiga da Sallama naji Umma ta amsa,Baki Bude na shiga Palon tsananin Haduwarsa komai na Dubai aka zuba ga sanyin Ac da kamshi ta ko Ina, nace Lallai Umma kun Mori gida Allah yasa a zauna lafiya Allah ya Kara lafiya da Nisan kwana, Ameen Ameen cewar Umma muje kiga ko Ina,Haka Umma ta nuna min har kitchen su Toilet Dake cikin Bedroom gidan yayi kyau sosai kamar wani gidan Dan Majalisa Haka yake. A store ma ba abinda Babu na Kayan Abinci,a kitchen na dakko wata Fura me sanyi da Umma ta hadawa Aabid nace Ni Zan shanyeta Ina pitowa Palo Ina kokarin Bude Robar Aabid ya shugo yace Umma Ina Furar tawa? Ina Jin Haka na bude Robar da sauri na Fara Sha da sauri da sauri,Ga Raudat har ta Fara Sha ma Cewar Umma,takaici ya kamashi ya fisge Robar da Furar ke ciki kije ki hada Taki Mana Zaki shanye min daga zuwanki,Oh Aabid ba Kara akan fura? kyaleshi Raudat ebo Taki a Fridge ki hada Zaki ga Nonon a Kato Bowl da Furar a wata silver Umma ta furta, Mikewa nayi na shige kitchen tare da dama tawa na fito nace Umma har Banana da kwakwa na hada a tawa,irin hadin da Aabid ke so Aiko ba kunya ya Mika min wacce ya fisge yace ungo Taki bani wannan,Ni bana son taka tawa nake so kowa yasha Abarsa,Nufinki kazantarki Zan Sha bani Malama ya ajiye tasa a kasa ya kwace tawa yayi tafiyarsa,Umma tace wannan son Kai ne Ina ruwanka da tata, nace kyaleshi Umma yaje.
Sai dare na koma gidanmu.

Da dare Muna kwance wayata tayi Kara Fadeela ta Miko min,Naga new number na daga tare da Sallama,naji Muryar Namiji ya amsa tare da cewa kawata yana fadar Haka na gane mutumin dazu ne Daya dinga Bina, Network ne yasa bana Jin abinda yake cewa sai ya kashe kawai,Ina ta jira Naga ya Kara Kira sai naji shuru shuru.
Washe Gari ma Bai Kira ba,Ni Kuma nace wlh bazan kirashi ba Ashe ma Ni na damu dashi.
Tun Ina sa Rai zai Kira Shuru na manta dashi kawai.

Bayan kwanaki kadan Fauzan abokin Aabid ya Fara kirana Muna waya,kusan kullum sai ya kirani ko ya tura min Text ta soyayya masu dadi, har Muka dawo a Rana sai muyi waya sau uku sau Hudu,text ba yankewa shima Fauzan tun bana kulawa har naji sonsa ya kamani shima,love sosai muke Sha Wanda duk gidanmu an San da zamanshi duk da cewar Bai taba zuwa wajena ba, bani da lokaci sai na Fauzan soyayya tafi wacce mukayi da Faruk nesa ba kusa ba.

Sunday Yauce ranar farko da Fauzan yace zai zo gidanmu, murna duk tabi ta ishine gaba Daya na rasa yanda zanyi da Raina,mun gyara ko Ina na gidanmu tare da yin girke girke iri iri na talaka,Abba anji Dan sarki Harda cewa ya bani palonsa nayi zance a ciki Haka Muka Kara gyara ko Ina mukayi wanka da Kwalliya harda su Mami
Fadeela gwanar iya kwalliya ce, fitted gown nasa ta material Sea blue Wanda itama cikin na Faruk ne,Khairat kuwa ta iya dauri kala kala Haka tayi min Wani me kyau, takalmi nasa flat Blue shima Ina zuba Kamshi.
Muna zaune mukaji mota sai ga wayarsa ya kirani yace kizo muna waje,nace a mota kazo tun daga can? Aabid ne ya dakko Ni a airport a jirgi nazo,ok nace na mike tare da Dan yafa karamin Gyalena na fita, Aabid a ransa yana ganina yace uhm za ayi bako kamar za a je Party.

Jikin motar na karaso tare da gaida Aabid sannan nace su shigo,da kyar Aabid ya shigo Dan Kar Fauzan yace ya wulakantashi, Dakin Abba na kaisu Suka zauna a kujerun mu na masu karamin karfi sannan Khairat ta kawo musu abincin da Muka hada,Aabid Yana jina nace My Man ya gajiya ya Kamata kasha Abu ko yayane,na furta Ina Wani kashe Masa Ido,maimakon Fauzan ya gani sai Aabid Wanda muke hada Ido dashi,Zobo yasha Hadi na tsiyaya Masa

Please Login or Register in order to submit comment