Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wiwi na dinga Yi nace sai na rakaka Ni,Dariya ta sake kwace Masa yace Ubanwa zaki raka? Tahowa nayi da sauri na kwace Trolley din dake hannunsa na fisgeta najata kirrrrrrr har cikin Motar Alex Ina Goge Hawayena da gefen Hijab Dina,na saka akwati a boot na zaga bayan motar na zauna daram nace Sai anje Dani,Alex Yana ta dariya shima, Aabid Yana Fitowa Bayan sunyi sallama da Umma yazo ya Fisgo Ni waje na rike rigarsa na cukwikwiyeshi Muna ta kokawa Umma tazo tana subhannallah lafiya ke Raudat sakeshi shi kadai zai tafi ya Hana mu wahalar da kanmu,Ina haki nace sai a barshi ya tafi shi kadai Haka akeyi ai Ana rako zai ce wani ba Wanda zai je Dan ma ya samu za a rakashi to kaje Allah sa ka auri Baturiya ta haifo maka Yara duk Arna,ko ka hadu da Star Terminator yayi maka dukan tsiya ya ballaka ko Horror ya kamaka woooooo na Masa gwalo.
Zan dawo ne ke Zan Fara ballawa, Dariya Umma tayi nace Umma ki tambayeshi yaushe zai dawo? Harara ya zuba min,Saida na Bari Alex ya kusa Jan Mota nace Abida an tafi mugunta ta Kare,Abida na fada Abidede Abida wulluuuuuuu na gudu wajen Umma,Alex yaja mota ya tafi,Umma tana dariya tace na ganeki Raudat Ashe tsokanarsa kikeyi rannan shi yasa kike bani labarin Abida Wai kawarki Dole Aabid ya dakeki,dariya nayi nace ai mugu ne Umma wlh dannan naki.
Faruk Bai San Aabid ya tafi ba tun fadan da sukayi, ba Wanda ya kula wani sai da yazo wajen Umma yaji labarin.

Gidanmu Faruk yaje Ina Fitowa yace yau dai ya kamata a Kira min Aymana babbar Anty mu gaisa,Ban San komai ba na tafi da murnata wajen Aymana.








AsmaBaffa.
[4/16, 9:30 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙









5-10








Official







By
AsmaBaffa





NA KUDI NE

RASHIN SA'A COMPLT Dari Uku ne 300, ga masu bukata kuyi min magana ta pc a wannan number
08033933642.


NA KUDI NE

TA GYARU Dari biyu ne 200.
Ga masu bukatar siye ta Hanyar tura lambobin katin waya ku tura ta pc na a wannan number
08033933642.

Ga masu bukatar siye ta Hanyar Transfer Kati ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Masu bukatar siye ta Bank ga accnt number da zaku tura kudin
2177560408, Yahaya Garba Muhammad, Zenith bank.

'YAN NIGER masu bukatar siye ku Nemi wannan number din
+227 90 79 59 39.






Page naku ne Malakso and Auta.








Da murna ta na Iske Aymana nace Sis kizo Inji Faruk yace Zaku gyaisa,Wani iri taji Zancen tasan Halinsa Amma Bata so Raudat ta Gane ko Mami kawai Hijab Aymana tasa tace Bari naje,Nace Tnx Bari na Hado Masa lemo kafin ku gaisa,Wajensa ta fita Yana cikin mota kafa daya waje Daya ciki,Bata fuska tayi tayi sallama ya amsa Yana washe Baki Ina wuni tace kawai ta juya Zata tafi,yace Aymana ji Mana pls minti Daya wani Abu zan nuna Miki a waya, Dole ta koma tace Ina jinka Malam,wayar tasa Ya mikawa Aymana yace kalli wani Pics, karba tayi da sauri ta waro Ido hotunanta ne da na Aabid ya hada ya dafata wasu Kuma ta rungumeshi,Kuma tabbas computer ce ta hada domin a wayar Raudat ya saci pics nata aka jona Dana Aabid ya tura.

Wayarsa ya fisge ba zato,yace ko ki Yarda mu dinga haduwa a wani wajen ko Kuma wallahi na nunawa Raudat da Abbanki na Tona Miki asiri, Aymana ta gigice musamman pics din wani a saman bed suke kowa ya gani zai ce iskanci takeyi, Innalillahi wa Innailaihirraju'un ta furta tare da share Hawaye tace ba komai Zan na zuwa ga number ta ka nemeni, ba kunya ya dauki number Aymana karshe tace duk abinda kake so a tare Dani kasa a ranka da ikon Allah bazai faru ba Kuma Allah sai ya bimin hakki na,Baki Ya tabe lokacin Ni Kuma na fito da tire Karami,naga Aymana idonta da hawaye Amma ta goge a boye tayi wucewarta ban kawo komai ba Muka ci gaba da soyewa.

Tun daga wannan Rana Faruk yake Kiran Aymana a waya yace ta sameshi a waje kaza Haka Bata taba musawa ba tana zuwa idan ya kawo Mata Maganar banza tayi Masa rashin mutunci tayi tafiyarta.
Shi kanshi ya rasa ta ya zai bullo mata.

Yau ma Yana wani eatery na masu kudi ya Kira Aymana ta shirya ta fice da yamma lis Wanda kwana Nan mun kasa gane kan Aymana sabo da Bata fita kullum tana gida Amma yanzu kusan kullum sai ta fita.
Gefe guda Kuma Saura kwanaki kadan Faruk zai turo da kudin aurensa daga Nan sai naje na gaida Ummansa, tsoro ne ya kamani na tuna cewar gidan da na taba zuwa na damfari Hajiya Kaltum naje a matsayin Yar uwarta itace Maman Faruk, a fili na furta chaiii ....asiri ya tonu,wayyo ya zanyi Innalillahi, da sauri Rufaida ta kalleni tace me ya faru ke Kuma?
A hankali na sanar wa Anty Rufaida Komai,Baki ta bude tace Raudat wannan Risk ne fa Kika dinga saka kanki ciki yanzu idan da ta gano ki fa? Tsaki naja nace ke fa Banza ce Anty bakya ganewa Ni Bata baya nakeyi ba ya zanyi naje gaishe ta idan Faruk ya turo kudin aurena,da wanne idon Zan kalleta zai iya fasa aure na fa wlh Kuma a gaskiya na rasa Faruk to mutuwa zanyi kawai Bazan iya rayuwa Babu shi ba,sonsa yayi min yawa ya gama ratsani.

Dariya Rufaida ta dingayi tace kice sonsa yayi Miki mugun kamu,kin kurbi madarar kauna ko?
Idan kina cewa kurba kada kenan ai kwankwada nayi bazan taba son wani irin Faruk ba,gashi Yana matukar Sona Yana kula dani iyayena da Yan uwana me ya kamata nayi Rufaida? Tace ki soshi nace yawwa kin Gane ashe to yanzu ya zanyi da Mamansa? Rufaida tace inye Raudat anyi miji an kusa aure za a ji dadi, dariya nayi tare da fari da Ido na mike tsaye Ina taku dai dai Ina juyawa da iyayi na sagale hannu daya nace za a kwashi love Kinga ban taba Kiss ba Rufaida ranar da aka kaini gidan Faruk sai mun kusa tsinke lips dinmu sabo da kiss idan kuka Zo Gidana sai dai kuga lips Dina yayi jajir sabo da azabar da zaiji,Dariya Rufaida tayi tace Banga laifinki ba Amma Raudat Ina ma kece Kika samu Aabid Kun Dace wlh,tsaki naja nace ke raba Ni da mugun banza ga Faruk Dina Dan Albarka.

Aymana ce tayi Sallama ta shigo Fuskarta murtuk Kamar ma Kuka tayi tambayarta mukayi lafiya? Tace kaina ke ciwo ta fada saman bed tayi kwanciyarta Baki Muka tabe Muka ci gaba da Hurar mu.
Bayan wasu Kwanani Haka Faruk yakeyi yazo wajena musha soyayya Yana kashe Mana kudi,daga gefe a boye Kuma Yana Kiran Aymana a boye Yana Blackmailing nata Dole take zuwa inda ya kirata,ko taje sai ya dinga tsarata akan ta yarda dashi yayi Xxx da ita Amma Aymana Taki yarda ko Hannu ta Hana ya rike Mata,hakan ya Kara fusata Faruk ya Kara daukan pics dinta ba tare data Sani ba sai ya hada Dana Aabid karshe ma pics din wata ya samu tsirara yasa Computer ya Hada da pic din wani Shima tsirara ya saka fuskar Aabid ya hada Kamar gaske suna room a saman Bed.

Yau nida Rufaida Muka shirya sabon saurayinta zai kaimu wajen shakatawa,Mun fadawa Aymana ta shirya tace unguwa zata je ita,shi yasa Muka share ta.

Faruk Kiran Aymana yayi wani Wajen shakatawa sabo da yasan idan yace Hotel baza ta je ba,Haka da yamma likis bayan mun Fita itama ta fice a boye, taje ta hangoshi saman Wata kujera a cikin korayen flowers Yana nishadi, cike da takaici sai ji yayi tace gani ya akayi Kuma? Murmushi ya saki tare da zuba Mata Ido Pics din ya nuna Mata yace kin gani matukar Baki Amince min ba sai na sake su a duniya kowa ya gani,Ran Aymana ya baci tace ai banyi mamaki ba sabo da Kai Dan Akuya ne Dan Karya,marar tsoran Allah,Maci Amana best frnd naka Aabid kake nufi da sharri,ace Wai Aabid zaka dinga yiwa Haka to ai ko Uwarka ce haka zaka mata,Ni Kuma Yayar Budurwarka da zaka aura zaka yiwa Haka wlh kaji tsoron Allah ka tuba,Allah sai ya saka Mana daga Ni har Aabid da Bai San me kake yi ba,Kuma wlh na gaji da zuwa wajenka kaje ka saka a duniya uban waye ya sanni? Jikina Kuma yafi karfinka Dan Akuya kaje ka nunawa Abba ma karewa kenan Allah shine zai tsaya min dashi na dogara tana Gama fadin Haka tayi tafiyarta ta barshi kerere a tsaye ta juya da Niyayyar zata tafi Ya Fisgo Hijab dinta, Dai dai lokacin Muka zo wucewa ta wajen Ni da Rufaida Da Saurayinta ya kawo mu, muma zamu huta mu shakata,a idonmu Muka ga Faruk ya Fisgo Aymana tare da Zabga Mata wani uban Mari,a tare Muka hada Baki mukace Aymana me ya kawoki Nan?

Faruk yace Babyna kiyi hakuri abinda nake ta so na fada Miki kenan Ina Jin kunyar hakan Kamar Aymana itace zata dinga Bina tana cewa Wai na Aureta sabo da Allah Wai Kar na aureki na Aureta nace a'a Akan taji zan turo da kudin aurenki tazo tana ci min mutunci tsautsayi yasa na mareta kuyi hakuri pls,Hawaye tuni ya cika min fuska nace Aymana shi yasa Muka ce kizo muje unguwa Kika ce kina da wajen zuwa?,haba gaskiya Mana shi yasa kullum Bata da sukuni daga tunani sai ta fice mun kasa Gane mata cewar Rufaida, Pics din dake hannun Faruk na kwace na duba idona na runtse da sauri,Rufaida ma ta gani ban San dalili ba ganin pics din Aymana da Aabid yafi komai daga min hankali,kuka na saki me karfi hankalin mutane ya Fara dawowa kanmu,pics din na dukunkune Baki daya nace Rufaida jeki inda Saurayinki yake Ni na tafi gida,Aymana Allah sarki Bata da bakin magana Bata San me zata fada a yarda da ita ba sai Allah kawai,Napep na shiga Ina ta kuka har naje gida Ina kuka,Inno,Abba,Mama da sauran Yan gidanmu gaba Daya Suka fito Fadeela tace lafiya? Ina kuka na shiga bada labari tiryan tiryan yanda Faruk ya fada sannan na nuna musu pics kowa ya shiga kunci Abba ne kadai yace ban yarda ba Raudat,wlh Aymana baza ta aikata Haka ba,akwai lauje cikin Nadi Amma nasan Aymana akwai Kamun Kai da hankali sam bazai yuwu ba,ba ita bace gaskiya kamar Baku da Ilmi,wannan Hoton wlh hadawa akayi ko Aabid Dana sani bazai aikata Haka ba,Dan Allah ku nutsu kuyi hakuri Abi komai a hankali Allah zai warware gaskiya.

Mami tana Hawaye tace Haka zakace dama Mana tunda Kai son kudi ya maka yawa,duk Kai ka watsa min Yara ko me sukeyi Kaine ka zubar musu da mutunci Dole Haka ta faru,Abba yace Shut up Addua Zaki Yi min Amma Ni me nakeyi in Banda Kallo a Cenema da gidan wasanni me nakeyi kuma? Aikin Banza ko kunya baka ji Haka surukanka zasu ji Halinka? cewar Inno, Abba yace Dan Allah ku fadawa Surukan nawa suzo muje kallon tare Mene a ciki,anji kunya cewar Mami,Raudat kuwa tuni na fada daki na boye pics din Ina rusar kuka ba ji ba gani har Rufaida ta dawo,Aymana kuwa kawai daga Nan gidan dake nesa damu ta wuce sabo da tana da kawa Zeenatu a gidan sannan Mamansu me hankali tana mugun son Aymana sabo da tasan gidan su ma Yanzu an tsaneta,Shi kuwa Faruk sai Bayan abin ya tabbatar ya hada tsiya ko a jikinsa ya tafiyarsa gida.

Kwana Uku ba Aymana ba labarinta sannan Kuma muma hankalinmu ya tashi rashin ganinta,Abba yace Dan Allah a bar Zancen ya wuce kawai a daina tashin tashin idan akan Faruk ne Raudat nice zan aureshi,sannan pics gaskiya Abba yaki yarda cewar Aymana ce,shi kuwa Faruk ba kunya yaci gaba da zuwa wajena harda Lallashina Akan na bar Zancen kawai,Nima na yarda na hakura na bar komai Amma pics din da Aabid ke jiki Yana Raina Ina kokonto ko shine ko ba shine bane.
Su kansu gidan da Aymana tayi kwanaki Basu San komai ba Bata fadawa kowa ba kawai tace laifi tayiwa Abba.

Ana Haka Baban Zeenatu da kansa ya dawo da Aymana gida taga ba Wanda ya canja Mata sai ma fada da akayi Mata akan taje gidan wasu tana kwana,zance ya wuce an bar komai taje zata ba Abba labarin komai yace Bai son tone tone kawai a bar Zancen yasan koma Mene Aymana baza ta aikata ba,Haka ta bar abin a ranta ita ma tana murnar Allah ya kubutar da ita.

Bayan Sati biyu Faruk ya turo kudin aurena dubu Dari aka kawo,Nasha murna ranar mun san Abba ne zai cinye kudin auren.
Bayan sati Uku Faruk yace zai zo ya kaini jibi Sunday na gaisar da Mamansa,a Nan cikina ya duri ruwa,ba yanda na iya ranar ya kaini har Wajen kwalliya Kayan da zansa ma wasu masu tsadar gaske Ready made gown Dark blue Nasha kyau Ina kamshi nayi rolling da mayafi ya daukeni Muka tafi a motarsa Ina faman hada gumi zuciyata tana dukan Tara Tara Ina Dana saninin halina,dama duk abinda zakayi ya kamata kayi hangen nesa baka san a Ina zaka hadu da Mutum ba Wanda ranarsa ce.

Gidan kuwa shine ya shiga da mota Yana min Hira Amma ko iya amsawa bana Yi uhm uhm kawai nake cewa,Bayan yayi parking a gidan Muka fito tare da jerawa Yana ta kallona da sha'awa sabo da na hadu gaskiya,Palonsu katafare Muka shiga ba kowa sai kamshi da Ac tana zubo da sanyi,Bari na Kira Mama Baby ya Haura Sama da sauri,Sun Dade Basu fito ba,sannan sai ga Faruk ya fito Yana zuba Murmushi yace gata Nan,Nan take Yan aiki suka cika min gaba da abinci,lokaci kadan sai ga Mama ta fito tana zuba mulki da Shan kamshi tazo ta zauna kaina yana kasa,da sauri na zube kasa na kwashi gaisuwa, ta amsa da kyar sannan tace Ni bana wannan surukantar ta mutanen kauye ki bude Ido kawai,Dagowa nayi da sauri Muka hada Ido,tace Kai...ke Dago again na ganki,kadan na Dago kaina na maida abina kasa da sauri Dan Kar ta ganeni tace wow,Gyalena naji kawai Hajiya ta fisge tace wlh kuwa itace,ke Yar damfara Barauniya dama na Dade Ina nemanki Ni Kika shimfidawa karya Barauniya,Faruk yace Lafiya Mama? Mama tace wlh baza ka aureta ba, ka karbo kudin aurenka Nan Hajiya ta bashi labarin komai,Faruk yace zata aikata wlh Mama Raudat Allah ya kamaki cewar Faruk,ki sani na fasa aurenki wlh bazan auri Yar damfara Barauniya ba,shine kike rufe min munafuka harda cewa kin taba zuwa gidanmu Ashe damfara Kika zo,kije na bar muki kudin ku je da marokin ubanki, taimakon da nayi muku kuje an bar muku matalauta.
Bani da bakin magana Mikewa nayi da gudu na fice Ina kuka sai da naje Bakin kofar fita nace Uwarka ce marokiya ba Ubana ba,sannan Kuma bada arziki aka haifeku ba,Dan iska Maci Amana ai mun San komai kana so ka lalata Aymana,Kuma pics din da ka hada Da Aabid sai na nuna Masa watarana.
Wani kyau ne da Kai da har zaka zagi iyayena arzikin naka Bai Kai ya kawo ba,Faruk ransa a bace yace ke karki Soma wlh a tafin Hannuna kuke ba abinda ban sani naku ba,Baku da aiki sai Maula,gida duk rubabbe Ni na taimaka muku matsiyata, Nima nace yo daka gyara Mana kyauta kayi Mana ganina kayi kana sha'awata Dan kuwa dama ba Sona kakeyi ba,shaawace ta kawoka,sannan ubanka ne yace Ka bamu kudin? Nima idan haka ne ka biyani maganata,Zancen danayi da Kai,dadadan kalamai,dariya da murshi,fari kissa da kisisinar, Shagwaba,kwalliya,girki da Hada maka lemo duk Dana Yi maka kaji Dadi ka biyani, muma sai mu biyaka kudinka kaf, zobon Dana Hada maka rannan,Abinci me Dadi Dana dinga dafa maka kazo muyi lisaafi a gida, Kai karamin Dan iska ne, ke Kuma Mama Wlh kinci darajar girmanki Amma kaf gidanmu ki tambaya kiji ba a taba mu, atamfa ce da dubu Biyar idan Yazo munyi lissafin idan da canji za a biyaki, Ina Gama Fadar Haka Tsaki naja nayi tafiyata.

Tun a Hanya na tafi Ina kuka Ina Hawaye sabo da ba karya Ina son Faruk sosai, ba karamin kokari nayi ba Dana iya Rama zagin da yayi ma Iyayena,na tabbatar dama ba Sona yake ba idan Yana Sona da gaske bazai min Haka ba,Jikin bishiya na samu a gefen wani gida na zauna na dinga darzar kuka wiwi Saida na kusa kaiwa dare na mike idona jajir a kumbure nace Allah ka saka min,Saida na shiryu na Gyaru yanzu Jarabta ta Fara Hawa kaina Allah kenan a Haka na shiga Napep.

Gidanmu na shiga Ina kuka, Dukkansu kowa Yana gida na shigo da ihun kuka,Mami ta rikeni da sauri tace lafiya Raudat? Mutuwa akayi? Ina Basu labarin duk abinda ya faru tun Daga farkon zuwa damfara ta da abinda ya faru da muka je gidan.
Kowa yayi shuru,Inno tace Allah ya saka Miki kiyi hakuri ba kanki farau ba,Allah yasa Haka shine Alkhairi Raudat Ni dama wlh Hankalina Bai kwanta da yaron ba,Mami tace kema Raudat da laifinki magana ta gaskiya ba Wanda zaiji halinki ya aureki tunda mutane baza su gane kin shiryu ba,ta sanadin Aabid kin shiryu Amma abinda mutane zasu fada akanki baza su san kin daina kin Gyaru ba,ga irin abinda ya faru gareki,yanzu Kinga Illar abinda Kika aikata kin girbi abinki a hannunki.
Wlh dama baya sonta kawai jikinta yake so Cewar Aymana,Abba kuwa Jin irin gorin da Faruk yayiwa yarsa ya taba Masa zuciya,shima ya gane ba son yarsa Faruk keyi ba duba da irin abinda yayiwa Aymana.

Rufaidat da Fadeela ne suke Lallashina suna bani hakuri,Abba kuwa Cewa yayi Allah ya Baki Wanda ya fishi yayi ficewarsa bashi da niyyar gyara halayensa na Maula.
Inno ce ta kaini dakinta Ina ta kuka suna Lallashina,zazzabi me zafi ya cafkeni na kwanta Ina rawar sanyi.

Aabid kuwa tunda ya Isa British wani hadadden gida shi kadai ya Kama,sati daya Suka Fara lecture,ya wani irin Kara kyau da gogewa ya sake Zama Dan gayu na gasken gaske Turawa da bakakenmu rubibinsa sukeyi Amma shi ko kulasu bayayi sai dai Frnds da yayi babaken fata yaran manya da Turawa suna harkarsu,Ko da yaje Yana Kiran Faruk sun shirya normal suna waya ko yaushe Amma Aabid Bai San abinda ke faruwa ba tsaka nin Raudat da Faruk ba, Umma kuwa kusan kullum sai sunyi waya da Aabid,labari ya watsu an fasa Auren Raudat kowa yasan maganar Amma ba Wanda yasan Mene Asalin fasa bikin sabo da Abba ya Hana fadawa kowa yace ko Yaya muke da Mutum Kar mu fada mu rufawa kanmu asiri sabo da Bakin mutane.

Na kasa cire Faruk daga raina,Aikina kullum kuka da tunaninsa duk na rame sosai kowa ya ganni yasan Ina cikin damuwa,a Haka Haka jini na ya hau duk sati sai Munje asibiti ganin Likita da karbo magani,gashi yanzu Talaucinmu ya dawo sabo da dama Faruk ke tallafa Mana Muka daina Talaucin sosai yanzu kuwa bama ganinsa.
Na dage Ina Shan Magani sai dai sauki Amma jinin yaki sauka,Umma Taji Labarin tana yawan zuwa duba Ni,Har Aabid ta bashi labarin komai a waya yace Amma Faruk bashi da Imani wlh ya yaudari Yarinya Allah sai ya saka mata,ita Kuma Allah ya Bata lafiya kawai.

Haka na kasance daga kuka sai tunani kullum a Haka nake har Islamiyya Abba yasa na koma ko Zan rage Tunani Amma a banza.
Yauma muna class har malami ya Gama hadisinsa ban San me yace ba,gida na dawo nayi sallar Isha da Adduoi na Kwanta naci gaba da tunanina ko Abinci sai anyi yaki Dani nake ci.
Na dawo wata silent ko Hira na daina bare Wasa da dariya Dana Saba duk ba wannan sai kunci da Shuru Shuru Nima na koma Yar Uwar Aabid.

Washe Gari Mami ta sameni a kwance da yamma tace Raudat yanzu baza ki samawa kanki lafiya ba ki daina wannan haukar shi Yana can Yana harkarsa ya manta dake,Kuma kin San irin zagin da Kika Masa a gaban uwarsa bazai hakura ya dawo gareki ba,kin yanke Hukunci cikin fushi ya zageki kin Rama Wanda a matsayinki na ya mace me mutunci Bai Dace ba,uwarsa baza ta Bari ba kin nuna halinki a gabanta akan ranki ya baci an zagi ubanki,jin Mami tace ya manta Dani na fashe da kuka,Ikon Allah to tashi kiyi wanka ki shirya ki tafi gidan Umma ki tayata kwana ta kirani a waya tace kije can,nasan Mami ce ta fadawa Umma halin da nake ciki,To nace na mike Ina Goge Hawayena nayi wanka na shirya tsaf na saka Hijab na dauki kayan sawata kala uku a jaka na fito nayi musu Sallama na wuce gidan Umma.

Koda naje gidan Umma Nasiha da fada ta dinga Yi min tana kwantar min da hankali Amma bana daukan ko Daya a Raina, Ina son Faruk sosai,Hauwa matar Hamisu ce ta kawo Danta zai Kai 5yrs tace Hutu ta kawoshi da kayansa ta tafi, Dan Hauwa Hammad bashi da kyuya Muna ta Wasa dashi lokacin na Dan manta da abinda ke damuna tare mukayi aikin gida da Umma har girki nice nayi Mana na dare,Mukayi Sallar Isha Umma tasa mukayi karatun Qur'ani naji mugun Dadi da sanyi a Raina dake duk gidanmu Munyi karatun Addini sosai Aymana ma tayi sauka da sauran Litattafai na Musulunci, Ni kuwa dasu Fadeela mun wuce Izu Arba'in gamu da Hadda a ka,sauran littafai ma ba laifi munyi,Allah ya zuba Mana kokari da basira a ko wanne fanni Boko da Arabic ko Umma Tasha mamakin Ilmi na.
Ana zafi sosai shi yasa Umma ta fito Mana da Katuwar katifa waje Muka Kwanta Muna ta Wasa da Hammad Yana kyalkyala dariya wayar Umma tayi Kara kirrrrrr...tana dubawa taga Hamisu dagawa tayi Suka gaisa.

Jin Hayaniya yace Wai wace ne kusa dake Umma? Raudat ce Wlh Tazo kasan an fasa bikinta Nan Umma ta fadawa Hamisu Amma ko Umma Bata San Dalilin fasa auren ba,Hamisu farin ciki ya kamashi yace gobe zanzo Umma na fada Miki Raudat Rabona ce,Kai ban son Shirme cewar Umma ta datse wayarta.

Ina Jin abinda Hamisu yace a Raina na yanke Hukunci ko Hamisu yace Yana Sona yanzu duk da bana sonsa aurensa zanyi sabo da Nayi auren huce takaici,Faruk yaji nayi aurena yasan ban damu dashi ba, Ina Tunanin Haka Kira ya sake Shigowa wayar ta duba taga Aabid.

Dagawa tayi da murna tace mutanen Burtaniya,Ina Jin Haka gabana ya Fadi nasan Aabid ne Haka kawai Kuma sai naji Farin ciki ya kamani,Muka ci gaba da wasanmu Ina yiwa Hammad Wasa a cikinsa Muna ta dariya,Aabid ta waya yaji Hayaniyarmu sai yaji Kamar muryata shi kanshi gabansa sai da ya Fadi, yace Umma waye ne suke cikawa mutane Kunne? Umma tayi dariya tace mutuniyarka ce Raudat da Hammad an kawoshi Hutu suke ta Wasa gata Bari na Bata ku gaisa,Yace ni Ummi

Please Login or Register in order to submit comment