Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bukatar siye ta hanyar tura numbobin waya ta WhatsApp ko ta Sms ga number.
08033933642.

Ta hanyar Transfer Kati ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Masu bukatar biya ta accnt ga accnt number
2177560408, Yahaya Garba Muhammad, Zenith bank.

'YAN NIGER masu bukatar siye ku Nemi wannan number
+227 90 79 59 39





AIDA MMN TASNEEN and MMN LAYLA and JANNA.
Page naku ne na hannun dama.










Har dare ya kusa Yana ta baccinsa hankali kwance,Ni kuwa Hannayena a kumbure suke suna min zogi da zafi, kallonsa kawai nakeyi gaskiya Aabid ya Hadu Allah ya Masa baiwa, kwata kwata banyi bacci ba kallonsa nakeyi Ina Jin wani Dadin kallonsa na musamman Wanda bana Jin hakan ga kowa sai shi, banji haushinsa ba sabo da nasan Ni nayi laifi asiri na ne ya tonu,naji kunya nayi nadamar Hali na,Hawaye ne ya shiga sintiri a kumatuna, sai Kusan Magrib ya farka a hankali ya bude idonsa ya mike Zaune Ina jinsa Yana Addua ya tashi a bacci,sau Daya ya kalle Ni yaga Ina uban Hawaye ba ko magana ya wuce Toilet tare da dauro Alwala ya tafi masallaci abinsa,lokacin Umma tana Kano wajen Yan Uwanta ba yau zata dawo ba.

Bai dawo ba sai bayan Sallar Isha sannan yazo ya kwance min igiyar yace kinci sa'a Daya Faruk Yana sonki,Kuma best frnd Dina ne Amma wlh da sai kinyi sati guda kina Shan wahala a hannuna, tashi ki bar min room, da kyar na iya Mikewa Hannayena ko gyalena baza su iya dauka ba ko Ina a kumbure,Haka da sauri na sa takalmina nace na gode Dan Allah kayi hakuri ka yafe min ka rufa min asiri pls bazan Kara ba,Dan Allah karka fadawa abokinka,Ina fadin Haka na fice da sauri.

Gidanmu Hankalinsu ya tashi ganin har dare ban dawo ba,Sai da Suka ji sallamata a gidan sannan hankalinsu ya kwanta,Inno tace Raudat Lafiya? Mami ta tambaya da Abba,
Kame kame na Fara na kasa karyar ban boye ba nace kudi na gani na tsinta kawai shine wani yace ni Barauniya ce ya yanka min Hannaye Kun gani, kowa ya kalli Hannun yace Kai Kai wanne mugu ne Haka? Mami tace wlh ko waye ya birgeni karya kikeyi ba tsinta kikayi ba sata kikayi,wannan ko waye Allah ya biyashi na gode masa, Baki na turo gaba nace ai na daina daukan Kayan kowa daga yau ,wata wuka yasa me kaifi Nasha wahala Allah bazan Kara satarwa kowa komai ba ban taba ganin mugu irin wannan ba, Inno tace wanne Dan iska ne wannan? Nace Abida Mana,wannan Aabid din me irin sunan Abida, Inno ta Rike Baki tace da gani zai aikata bashi da Fara'a ko kadan.

Ai Inno abokin Faruk ne Wanda Zan aura sabo da Faruk ya kyaleni yau Amma da cewa yayi sai nayi sati Yana cin ubana,Abba ya Nisa yace laifin kine Raudat yan Uwanki su da basa daukan Kayan wani sun zauna lafiya ke kuwa ai gashi,bana son sata, duk abinda zaka Yi karka saci kayan wani,Ku Iskancin naku a Ina ya tsaya,bakuyi komai ba,ai baza kuyi irin abinda mukayi ba,duk tsagerun yanzu a bayan uwarsu suke bacci idan dare yayi,mu kuwa da dare sanda Muna samari wa zai ganmu, bakuyi komai ba Iskancin banza kukeyi,Baku je ko Ina ba.

Inno ta kalli danta Abba tace kaci ubanka Nan me kake fada Haka a gaban yaranka? Nufinka fada kake musu ko me? Sai lokacin Abba ya tuna tabargazar da yayi yace ai nufina yanda muke aikin Addini idan dare yayi duk wajen Wa'azi muke tafiya tafsir acan muke raba dare.
Raudat tace kaji Abba wa zaka yiwa wayo mun girma fa, You are very stupid I'm talking and You are talking, Abba baiyi Boko ba Amma yawon duniya da zuwa Lagos yasa ya iya turanci dai dai gwargwado kadan kadan, komai yace zaiyi turanci shi a dole Dan gayu,indai turancinsa ne sun Saba da dashi kullum.
Rufaidat tace kyaleta Abba ja zatayi da Kai,Abba yace Who is she,ya kalleni yace Raudat your too legs will enter my one leg trouser (Wai zai sa kafar wando daya da ni?)

Mami tace sai kizo Raudat na gasa Miki Hannayen ko Kuma su rube ki huta,Da Sauri naje wajen Mami da ruwa me uban zafi a Bowl,tace Abban Ayman kaje chemist Dan Allah ka siyo Mata Magunguna,What? Abba ya furta da karfi yace ni nace tayi sata? Kwandala ta bazan iya kashewa ba,a gasa Mata sosai zanje wajen Malam Shehu na karbo Mata na gargajiya yafi araha Naira ashirin dita ta biya bukata, Amma ai da Kai ake cin kudin satar ko? cewar Mami
Karki min sharri my Hands are clean wooo Abba ya furta ya fice abinsa.

Mami ta Fara gasa min Hannayena tana sani take min da zafi itama,tana dannawa sai na saki Kara da karfi, Kuka nayi sosai Hannayena sun kumbura sosai ko Leda bazan iya dagawa ba,Zazzabi me zafi ya kamani,Allah sarki Inno tasan danta bazai siya min ba ta fita da kanta sai gata da Magunguna ta siyo.
Wanka ma bazan iya ba Dole Mami tayi min da kanta da ruwan dumi,Abinci ta bani naci,da magani ta bani Nasha sannan ta shafa min magani a wajen Ciwon na Kwanta bacci ya kwashe Ni.

Kullum Mami da Inno ke kula Dani har na warke Faruk Bai sani ba Yana can Abuja Wajen aiki sai dai muyi waya dashi,wayar ma sai dai cikin sisters Dina su rike min.
Soyayya ce sosai ta kankama tsakani na da Faruk Ina kaunarsa shima Haka.
Ina jinya har nayi sati guda lokacin Hannuna ya warke saura kadan.
Aabid saura Shekara Daya ya Gama University.

Gida Aabid ya shigo da Murna yau Saturday,Umma tace Aabid lafiya? Naga kana ta murna, Zama yayi a nutse yace Umma Scholarship din da Muka je Exam Abuja to na Samu scholarship zuwa British karatu acan zan Karasa karatuna,Umma tace Alhmdllh Federal Scholarship ce kenan,Amma kana ganin ba matsala ka kusa gamawa fa anan? Ae Umma ba matsala 1yr zan Karasa a can kawai sai ko Masters idan Ina so,Amma bazanyi masters ba sai Nan gaba idan na Samu hali sai nayi Amma Ni dai zanje Kuma ga kudin da zasu bamu da yawa Zan iya Kama business da wasu,To Alhmdllh Haka ake so ai,yaushe ne tafiyar? Next WK Umma dama Shuru nayi ban fada Miki ba sai komai ya Zama ready har Visa anyi mana, mashaallah...Hamisu ne ya kwada Sallama ya shigo tare da gaida Umma ko kula Aabid baiyi ba.

Umma tana murna tace Hamisu kaji Aabid ya samu scholarship zai tafi Burtaniya karatu, Baki Hamisu ya tabe tare da cewa a dawo lafiya,ya canja Zancen ma yace Umma yanzu baza ki fada min Inda Gidan su Raudat yake ba Allah Ina sonta,Ba a Neman aure cikin aure Hamisu na fada maka Kamar baka je Islamiyya ba,da matarka Kai ba wani Babban aiki ba da me zaka rikesu,ranka zai baci karka sake min Zancen Nan idan ba so kake na saba maka ba, Fuska Hamisu ya Bata ya mike ya ficewarsa ba ko sallama.

Ina Kwance a palonmu Sai ga Umma tazo har gidanmu Wai kwana biyu Bata ganni ba,Mami taji Dadi tace ai ta danyi rashin lafiya ne Amma ta warke,Umma tace Allah sarki Allah Kara lafiya Dama zuwa nayi na duba ko lafiya,Raudat ya jiki Ina dariya na zauna kusa da Umma nace lafiya Lau Umma da sauki,a hijab na boye Hannuna Dan Kar ma Umma ta ga shatin wuka ta tambayi dalili,ta Dade a gidanmu sannan tace zata tafi na Rakata na dawo har Lemo da Ayaba ta kawo Mana da yawa Kuma Aabid tasa ya siyo Mata Bai San Ina zata Kai ba.
ban sake Zuwa wajen Umma ba sai da Ciwon ya warke sosai tabon ma saura kadan yau na shirya naci kwalliya cikin material pupple me kyau cikin kayan Faruk na hadu cikin doguwar riga,takalmina Half shoe me kyau na yafa gyale da takalmi na same color nayi sallama dasu Mami na taho gidan Umma gabana Yana faduwa na shiga gidan a tsorace Allah yasa Umma kadai na Iske a tsakar gida tana gyara wake,Aabid Yana kitchen Yana Jin Muryarta ya gane nice,Ina Jin Motsinsa a kitchen gabana ya Fadi gumi ya shiga shatato min,a Raina Ina cewa kamar mace kullum a kitchen, Umma tace kinyi kyau yata ko dai Yau za ayi babban bako? Dariya nayi tare da rufe idona da tafukan hannayena sannan nace Umma Wajen Aabida kawata naje shine na biyo ta Nan,Aabidar ma tana kitchen Wai aiki takeyi shi yasa nayi tahowata wajenki, Umma Bata gane da Aabid nake ba tace kin kyauta sai watarana ki koma idan tana free,Baki na rike nace ba Lallai ba Umma Aabida Bata da halin kirki ,ba mutuniyar arziki bace,Bata San mutunci ba sanda aka raba shi tana bacci,muguwa ce ta gaske Kuma zata ga abinta a kanta,Aabid kasa jurewa yayi tabbas yasan dashi nake,ya fito a fusace Umma sai gani tayi yayo kaina,da sauri ta dakatar dashi sarkin Masifa Abida tace ba Aabid ba,baka ji dai dai ba,baka San Abida ba Sunan mace? Ko Kaine macen?
Wlh Umma baza ki gane ba da Ni take ki Bari nayi maganinta,Nace yo daga nace Aabida kawata sai kace da Kai nake.
Kwafa yaja ya barni sabo da umma.
Umma tace naga ranar da zaka canja Hali wannan zafin zuciyarka Amma ace sabo da Allah Matar da abokinka Zai aura aboki ma irin Faruk kana yiwa budurwarku Haka,yanzu idan ya gani zai ji Dadi?
Kitchen ya koma yaci gaba da girkinsa,Umma tace Shiga ki dakko lemo a fridge Zaki ga har snacks ki ebo yanda zai isheki Raudat.

Ba a son Raina ba Haka na maze Ina tsoro da fargaba na shiga kitchen din,shi kuwa Murna yakeyi, Na Shiga Ina tsoro sai yayi kamar Bai San Dani ba Ina zuwa Zan Bude Fridge ya fisgoni tare da zare min idanunsa masu tsananin kyau da kwarjini,da sauri na saki Kara na fito da gudu,Umma tace lfy? Nace umma Ni dai ki dakko min da kanki dukana zaiyi, ki saki ranki Raudat ba abinda zai Miki jeki dakko ki daina jin tsoro, to nace gabana na dukan uku uku na koma kitchen din Ina ja da baya, Aiko ya taho zai kamani na sake fitowa da gudu Ina Ihu wayyo Umma kin ganshi ko,Ita Umma dariya abin ya Bata tunaninta nice kawai nake Jin tsoro na,fuska ta Bata tace Raudat Ina Wasa dake ne?

Kai na girgiza Kamar zanyi kuka na kalli kitchen din cike da shagwaba nace Ni dai Umma sai dai ki dakko mini, Idan Baki dakko ba ba ruwana dake Raudat,Haka na sake tafiya Ina rabe rabe na shiga kitchen din, Aiko Yana ganina ya juyo naje na bude Fridge din a tsorace, Hannuna ya Fisgo tare da juyani ta baya yasa Hannu ya rufe min Baki Tam inda bazan iya ihu ba a hankali yace Dan ubanki wace Abida? Kai na girgiza Hawaye Yana zubo min,Hannuna ya murda sosai Zafi ya ratsani Hawaye Yana zuba,Dan Kar Umma taji tsabar mugunta ya zame dankwalina ya zuba min rankwashi me zafi ga yatsansa daya da zobe,sai da yayi min sau Uku zafi har kwakwalwata sannan ya hankada Ni jikin fridge din na bige,Hawayena na goge na saita kaina tare da Daura dankwalina na kwashi Lemon Dana ke so nayi hanyar Fita sai da na Bari naje bakin Kofar kitchen din nace Abida muguwa da gudu na fice,Umma ta ga na fito da gudu,Bakya rabo da shiririta Raudat yanzu Aabid kike jin tsoro ke da yake Yayanki ne gashi abokin saurayinki.
Hmm kawai nace na zauna Ina Shan lemons Ina cin Snacks,Lokacin ya Gama girkinsa ya fito a kimbure ya wuce Room dinsa.

Sai bayan 5pm nayiwa Umma Sallama na fito Zan tafi,Ta zauren gidan Window din Aabid na leka kadan na iske ya Gama hadewa cikin wani Yadi me azabar kyau fari tas, Abida muguwa Allah Yana Nan dai na furta da karfi,kafin ya juyo na fice da sauri na bar gidan,kwafa yaja yace kinci sa'a kawai Faruk Yana sonki da har gaban Uwarki zanje.

Faruk ya dawo murna nakeyi sosai nasan Zan washe da Kaya masu kyau da kudi, Ranar Daya zo Kd ranar yazo gidanmu da yamma,kwalliya naci cikin sabon lace din Daya dinka min na hadu sosai Brown and Orange,Takalmi da mayafina duk iri Daya,Yana cikin mota na fito da fara'a Ina zuba Murmushi abin mamaki sai Naga shi da Aabid ne sunsha wanka cikin Shadda Yar gaske,Aabid light blue Shi Kuma ogan nawa Milk color.
Zuciyata sai bugawa takeyi ganin yanda Aabid yasha kyau abin bazai misaltu ba,Faruk Dina ma yayi kyau Amma bai Kama kafar Aabid ba,A Raina nace kaga Aabid Dan me dadin kallo gaskiya Yana da dadin kallo,sharewa nayi na koma bangaren Faruk Dake mazaunin driver ya bude motar nace barka da zuwa ranka ya Dade,i miss u so much na furta Ina fari da Ido, Muka hada Ido da Aabid da sauri ya kalleni sabo da Jin kalamai na, a ransa yace Lallai yarinyar ko kunya Bata ji ba,Baki ya tabe tare da Kara Hade Fuska,Faruk yace Miss u too Babyna ga Frnd Dina Yayanki yau nazo dashi dole yazo ya gaida gimbiyar Mata,Murmushi na saki me kyau nace ka kyauta gaskiya da kawo min shi ta Dole,ace best frnd guda Bai zo wajen Babynka ba ai abin baiyi dai dai ba,Aabid ji yake kamar ya shakeni, a fili kuwa Murmushi yayi kadan sabo da Faruk Kar ya zargi wani Abu, Ina yini ya Umma na? Na furta a nutse Ina wani kwalmade murya da iyayi kambun gidanmu,Harara ya galla min a boye Wanda Ni kadai nasan ta mece,Ido daya na kashe Masa Nima a sace,Ina kallo yaja kwafa a hankali sannan yace Lfy kowa yayi shuru, Kaifa Dan Iska ne Aabid ya zaka dinga shawa Babyna kamshi, Shuru nayi na juya wajen Faruk Dina na kafeshi da Ido nace kayi kyau Darling yau kafi ko yaushe kyau kana jin dadi ka manta Dani ka barni da tunaninka zai hallaka Ni,Aabid Yana daga Mota ya bude Baki kadan sannan a ransa yace Lallai yarinyar a haka Kamar batidajiya Ashe Shuuma ce,Bai Gama tunaninsa ba Yaji nace Yaya so na ya karu ko raguwa yake? Kasan soyayya fa da Dadi take My Faruk, son ka ya Gama min illla sai ka dinga tafiya kana Bari na na furta da sigar Shagwaba Ina narkewa kamar zanyi kuka,Faruk ma yace aiki ne ya rike Ni My Honey bakya kusa ai babu Jin Dadi, Ina Sonki Kalamanki suna narka min zuciya,kin hadu ta ko Ina Raudat,ban taba haduwa dame iya love irinki ba,Horn Aabid ya Danna Wai Yazo su tafi yaji kalaman banza Faruk yake furtawa yarinya karama ya kawoshi zai zubar Masa da mutunci,Faruk ya kalleni yace kiyi hakuri jibi zan dawo ni kadai zan Dade Muna Hira yanzu Aabid ya gaji,ba komai Allah ya kaimu kaje kawai ku tafi Sai munyi waya.
Leda manya guda biyu ya Mika min da kyar na karba,kudi ya Miko min yayi yayi naki karba sabo da kunyar Faruk nake ji Yana hidima damu da yawa, Aabid a mota yace munafuka Ana Bata kudi Taki karba sai na sata barsuniyar banza ta sameni Dan marayan Allah tana tafka min sata ko tausayi Babu.
Faruk shiga yayi yaja mota Suka tafi Nima na Shiga Gida.

Ko Nisa da layinmu basuyi ba Abba ya tsaida su,Suka tsaya kuwa a mutunce Suka fito daga mota tare da gaidashi dama Aabid yasan abinda Abba keyi a Gari,Aiko sai suka ji yace Daga Wajen Raudat din kuke ne? Faruk da Bai San abinda Abba keyi ba yace ae Yana Murna,Abba yace Allah sarki to an gode kunji yarana kuci gaba da zuwa,ai Raudat duk gidan Nan Babu me hankalinta yarinya ce Nutsatsiya,Faruk zo mana Ina son magana da Kai,
Faruk yaja gefe yace Dana wlh dama Man gyada da manja ne babu a gidan,na rasa yanda zanyi sai Kuma Naga kazo ma nace Bari na fadawa Dana,Dan Kaine kawai na fada maka naga Kai mutumin kirki ne,Aabid mamakin Abba ya kamashi Nan take yaji Mutuncin Abba ya zube a wajensa shi iya Rayuwarsa Bai taba ganin mutum Haka ba,duk abin arzikin da yayi Masa Bai gani ba Haka ya zaro dubu Biyar cash ya mikawa Abba yace gashi Abba,Na gode nagode Allah Kara budi,Ameen Cewar Faruk ya shiga mota wajen Aabid Suka tafi Abba kuwa Bai tsaya ko Ina ba sai Cenema kallon film da wasanni kala kala,sannan ya tsaya yaci abincinsa me Rai da Lafiya yasha nama su Kuma gida ya barsu da Garau Garau.

Aabid dariya ya dinga shekawa Faruk ba ji ba gani harda Hawaye yace dama Bari nayi ka gani da kanka saura halayen Uwar gayyar taka Nan gaba Lokacin Too late to cry, Faruk yace kayiwa Allah ka fada min halinta? wlh ba ruwana yarinyar kirki ce Amma a Musulunci ya Yarda idan mutum zaiyi aure ya tambayi halin yarinyar ko ta tambaya a Fadi gaskiya baka da laifi a wajen Allah idan mutum Yana so ya aura a Haka Amma Faruk nasan kana sonta Raudat Bata da wani hali na banza Indai kana sonta Kar halin iyaye ya shafeta ka aureta wlh yanzu halin ya ko da ake dubawa bana iyaye ko Yan Uwa ba Tunda kowa da Halinsa.
Duk yanda Faruk yaso Jin halin Raudat Aabid Bai fada Masa ba sabo da yasan satar ma da takeyi da kuruciya da Kuma talauci.

Suna tafiya a mota Sai ga Aymana ta siyo Kayan Miya itama zata shige Napep tana jira a bakin titi,Faruk sarkin son Mata Bai gane Aymana bace sabo da sau Daya ya taba ganinta a gidansu lokacin yaje gaida Mami, Ihu Faruk ya saki Wanda Aabid sai da ya tsorata yace kaga wata hot Baby Kai Kai...Kai.....wow.....kamar taso tafi Raudat Dina tsayi gaskiya wannan tayi min Dole na nemeta itama na dinga zuwa ko ba komai na danyi Romancing nata ita Kuma Raudat dita sai na boyeta na auri abata,Aabid ya kalli Faruk da mamaki yace Faruk baza ka gyara Halinka ba Wai ka girma fa Kai kowa taka ce a turai ka koyo wannan Lagutse yaran mutane wlh ba kyau Bai Dace ba Kamar marar Ilmi,kana son Raudat ka tsaya iya ita Ina jiye maka wlh.
Kaga duk me irin Halayenka wlh basa samun ta Gari,ka Zama na gari ka samu ta Gari,sai kazo kana son aure Ido rufe ka rasa matar Aure.

Kai Dalla Aabid Ina ruwanka just common Romance sex ne? Sau nawa na Taba sex sau hudu ne ko sau biyar Kuma na daina tun a turai ne just Romance kullum nakeyi, ka dameni da Wa'azi idan bakin ciki kake min ni na hanaka ka nemi budurwarka ka daina takura min Kai a dole na Gari Malam baka da lafiya kaje ka nemi magani can,Raudat kake so na ajiye ita kadai akanta zan daina kula Mata? Ita din banza kucaka ma duk ba Ni na taimaka musu ba Suka farfado a ya na samesu? Baki Aabid ya bude yace Oh dama badan Allah kayi musu ba? Gaskiya ka bani mamaki har ka Fara musu Gori tun ba a je ko Ina ba? Banyi zaton zaka Yi Haka ba Faruk akan kawai kaga wata a titi,Karka yaudari Yarinya me yasa ka Bari kasa yarinya ta kamu da sonka shine zaka ci gaba da Neman matanka wlh Allah sai ya saka Mata,gaskiya nake fada maka kafin kayi Nadama gaba,Idan zaka taimaki wani kayi don Allah Faruk gaskiya ce bazan fasa fada maka ba,sannan yarinyar da kake tunanin zaka je wajenta yanzu Aymana ce yayar Raudat ce, tsaki Faruk yaja yace to sai Yaya Wlh indai zata dinga kulani Ni Kuma zanje Muna haduwa da ita a wani wajen daban,Allah ya bada Sa'a tsaya na fita a nan cewar Aabid,Zage zage Faruk ya shiga Yi ya tsaya da mota Aabid ma dake kwallo ne zagin ya antayawa Faruk iri iri da turanci suke zagin juna ya fice Daga motar a fusace Ya buga murfin motar tare da cewa stupid idiot.
Faruk yace shima fuck you Nonsense.
Basu taba fada ba sai yau,Napep Aabid ya shiga ya tafi gida,shi kuwa Faruk juya motarsa yayi ya Nufi wajen Aymana dake tsaye tana jiran Napep.

Aymana tana tsaye sai gani tayi an tsaya a gabanta tare da sauke glass,Tana dubawa taga Faruk Saurayin kanwarta ta biyun karshe Raudat, da Murmushi ta gaida shi Bata kawo komai ba,yace Anty shigo na kaiki gida Rana tana dukan babbar Anty, Aymana ta shiga ba tare da komai a ranta ba kunyar ma Faruk take ji.
Kida ya kunna a motar har wani rawa yakeyi da kafada Yana kallon Aymana Kamar maye,ita tana tunanin abin nasa da Wasa ne sai taga da gaske ne,Ba zato taji Hannunsa a habarta Yana shafawa yace eyeeee You are Beautiful, kina fa da kyau sai nake ganin kinfi Raudat kyau ma, Aymana jikinta ta kankame waje Daya tace ai kuwa Raudat tafi mu kyau kowa ya sheda mu bamu Kama kafarta bama,idonka ke maka gezo Kuma karka sake taba min jiki Ina ganin mutuncinka ba Haka muke ba, Murmushi yayi na yan duniya Yana kallonta Yana tuki Yana wani washe Baki a ransa Yana ayyana irin dadin da jikin Aymana zaiyi yasan Raudat tana da kyau yanda take da wayo baza ta Bari ko hannu ya rike Mata ba,ya taba gwada hakan ta daina kulashi shi yasa yake ganin zai gwada wajen Aymana.

Yana kokarin sake taba fuskar Aymana tace Malam wait saukeni a Nan ko na maka ihu,ba shiri ya gangare ya tsaya ta bude mota ya irgo kudi ya mika Mata tace bana bukata tayi tafiyarta,yace zanzo gidan Aymana Dole ki kula Ni.
Aymana har Hawaye tayi tasan Abbansu ne yake zubar musu da mutunci kowa yazo sai dai iskanci yake so yayi damu,Faruk ne dama muke tunanin na Gari ne ashe shima ba Haka bane.

Aymana Addua tayi akan Allah ya tsallakar da kanwarta Kar Faruk ya yaudareta ko ya aureni Yana iskancinsa da Mata, gashi ba dama ta fadawa Raudat sabo da tasan zance bakin ciki take min ko muyi fada Dole ta bar abin aranta.
Kwana Uku tsakani naje gidan Umma na Iske Aabid yayi Shirin tafiya ya hade cikin kana Nan kaya ga Trolley dinsa zai tafi British karatu, sai naji ba Dadi a Raina,Kallonsa nayi Yana ta murnarsa shi, Ido Muka hada yace ya akayi ne? Daina kallona to mayya, wannan Lokacin Dariya kawai nayi,ya kalleni kadan ya dauke kansa can gefe Yana Bata fuska,Umma tace sai yaushe idan ka tafi? Sai bikin Faruk Inshaallah zanzo Umma,Allah ya kaimu Ameen ya furta,Alex ogansa shi zai Kai Aabid airport a motarsa me kyau ba laifi ta me karamin karfi,Alex Yana zuwa Ya dauki karamar jakarsa Umma harda kuka,dariya ma ta bawa Aabid Yana Lallashinta Yana dariya shima Bai son Barin Umma zaiyi missing nata,Ni Raudat Karan kada Miya Nima Ina gefe na fashe da kuka Wanda yasa Aabid ya kalleni da sauri,Umma tace kaga Raudat ma ta Saba da Kai Dole tayi Kuka,katanga na rike Gam naci gaba Rusa kuka na Wanda Aabid Bai San sanda dariya ta kwace Masa ba yace ko Ubanki ne zaiyi tafiyar Nan ai sai Haka harda rike katanga munafuka,Kuka

Please Login or Register in order to submit comment