Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwansa,Raudat sai satar kallonsa takeyi ga kamshin kwai ya cika gidan tuni taji yawunta ya tsinke,sai da ya Gama soyawa sannan ya shiga wanka,Umma tace Raudat Kinga miyata can Kan Gas zata zube Dan juya min ita Bari na ninke wasu Kaya,Umma tana shiga Daki Raudat tana kitchen tayi maza ta bude kwan Aabid ta dauki Kwai fai fai Daya ta tura a Baki ta cinye tas ta juya miyar Umma ta fito ta zauna inda suke da a tsakar gida saman tabarma tayi wani lakwas tare da langabe Kai kamar mutuniyar kirki,Aabid Bai ko kalleta ba itama tana satar kallonsa Amma Bata kulashi ba.

Cikin 3qtr ya fito da t-shirt Yana kamshi ba karamin kyau yayi ba,Raudat tana gani ya shige kitchen tare da bude kwansa da sauri ya jefar da murfin ya kwala ihu,Umma ta fito da gudu tana tambaya lafiya Aabid? Aabid yace Umma wlh yanzu na tabbatar Aljanune Dani dama ance suna sata Dole na Nemo malamai gidan Nan Yasha karatu musamman dakina,Kinga Kwan ma an sace Abu daya Dame zanci abincin nawa,Raudat da kyar ta danne dariyarta ta mugunta, Umma tana salati tace gaskiya a kirawo Malamai manya yanzu kayi hakuri ka soya wani kawai Allah kawo maganinsu.

Ina daga zaune ina boye dariyata ba zato Aabid ya kalle ni kadan tare da galla min Harara Bai kawo ni bace kawai dariyar dayaga ina yi ne kasa kasa yasa ya harare ni, ina zaune ya fasa wani Kwan ya soya abinsa sannan naga ya zuba jullof din shinkafa ya tafi dakinsa,a Raina nace abincin ma sai anci da kwai Dan Iyayi,Tafiyar ma da kyar yake yinta Yana wani zuba sarauta da mulki.
Yau dai kwai kawai naci banyi sata ba na tafi gida.

Washe Gari kuwa kwalliya naci cikin kayan da matar Dan Majalisa ta bani na Yarta,ba karamin kyau nayi ba Cikin lace din Maroon color and black, Napep na hau na tafi Unguwar sarki wani katon gida na Samu na gaske na Samu da kyar Masu gadi Suka barni na Shiga gidan sabo da kyawuna, wata me aiki na samu nace kice Dan Allah Hajiya tayi bakuwa Yar uwarta daga garinsu,me aiki taje jiki na rawa tace Hajiya Yar Uwarki tazo tace a fada miki Amma yarinya ce budurwa.

Hajiya Kaltum tayi zaton da gaske ne daga garinsu ne sai gata ta sakko da kyar daga sama tana wani gadara da yanga,dama Hajiya Yar wulakanci ce Bata da mutunci ko kadan, gani na kyakyawar gaske Itama Hajiya Kaltum duk danginsu kyawawa ne farare sai tayi zaton da gaske ne Yar danginsu ce, Zama tayi tana karkada kafa na gaisheta ta amsa da kyar, tace ke Yar gidan wace a dangina? Na shiga tunani nace Hajiya ta Makkah, Aiko anyi a Sa'a a danginta akwai takari masu Zama a Makkah,tace Yar gidan Hajiya Karimatu ce ko Yar Hajiya Hafsatu ce?
Da Sauri nace Yar Hijiya Karimatu ce, sannu da zuwa yaushe Zaki koma? Nace anjima da yamma lis tace Kar na kwana,Hajiya Kaltum tana Shan kamshi tace ok,Zama nayi Hajiya tasa aka cika min gabana da kayan alatu na ci,naci na barshi Ina ta dariyar mugunta a Raina naci banza,yamma tana ji nace Zan tafi,Hajiya tace ai garin da nisa Jigawa ai da nisa gwara ki tafi da wuri tana uban yanga ta bani dubu biyar tace gashi ki hau mota,ta kawo Turmin atamfa sabuwa ta bani tace ki gaishe da Hajiya Karimatu nace Inshaallah na fice abina daga gidan cike da Murna,Ina fita bakin gate wata galleliyar mota ta danno,Glass naga an sauke da sauri wani kyakyawa yace ke wajen wa Kika zo? Murmushi nayi nace wajen Hajiya nayi tafiyata da sauri na shige Napep sai gida.








AsmaBaffa
[4/16, 9:29 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙










3










Official







By
AsmaBaffa







NA KUDU NE

RASHIN SA'A COMPLT ga me bukata 300 ne, zaku iya Neman a wannan number ta WhatsApp
08033933642.


NA KUDI NE

TA GYARU Naira dari biyu ne 200 masu bukata

Masu son tura nubobin Katin MTN ta WhatsApp ga number ki min magana
08033933642.

Masu bukatar siye ta Hanyar Transfer ko Vtu ga number da zaku biya
09032409668.

Wanda Kuma ta banki suke bukatar siye ga accnt number
2177560408, Yahaya Garba Muhammad,zenith Bank.




Page naki ne Ummy Manga.








Ko da na Isa gida cewa nayi gidan dana ke aiki ne Suka bani kudi da atamfar, Mami Bata yarda ba amma Inno da Abba murna ma sukeyi ba ruwansu,Su Aymana duk Basu yadda da kudin ba Amma talauci yasa aka karbe haka.
Abba harda cewa Ina Alfahari dake Raudat duk cikin yarana babu me zuciya irinki ba irin wannan kartan banzan ba ya nuna su Aymana da yatsa, Inno ta karbe zancen da cewa yo aini shi yasa ko harkata bana hadawa dasu sabo da ba abinda Suka iya sai iyayi su ba Yayan kowa ba.
Mami kuwa da Hannu ta yafito Ni zuwa dakinta,na bita kuwa ba tsoro sabo da nasan ba wani fada ta iya ba,kallo na tayi tace Raudat Wai a Ina kike samo kudi da Abubuwa ne? Nace Mami Ni aiki nakeyi a gidan masu kudi gumi nane, Hmm Mami tace a sanyaye tace to dai ki Bari bana so koma a Ina kike samowa ba kyau Raudat, to kawai nace nayi Mata Shuru.

Hamisu da Matarsa Hauwa'u tare da yaronta Karami Daya Suka zo ganin Umman Hamisu,Aabid suna zaune tare da Umma a tsakar gida tana goge Masa kayan sawa Suka ji Sallamar Hamisu da Iyalansa,Aabid da Fara'a yana musu sannu da zuwa Amma Hamisu wani banzan kallo yayi Masa me cike da tsana,Hauwa kuwa tsaki taja ma kawai,Umma tana kallonsu wannan Abu yana Kona Mata Rai,Hamisu ya kalleta yace Haba Umma yanzu kamar wannan banzan Zaki dinga wahalar da kanki har Kina Masa guga,Hauwa tace ba Imani ya zauna Yana kallonta,Tsawa Umma ta daka musu ya Isa idan abinda ya kawoku kenan ku tashi ku Kama gabanku Ni da Dana mutu ka raba,Hamisu ya kara Jin haushi kamar ya fashe,Aabid kuwa wani kallon kaskanci yayi musu ko kallonsu Bai sake Yi ba dake shi dama baya daukan raini da wulakanci sabo da yasha cin mutuncin Hamisu,Kuma Umma cewa takeyi ba komai yayi dai dai.

Mikewa Aabid yayi da Niyyar fita sai yaji Karar mota a kofar gidan Yana fita ya iske Faruk abokinsa yazo gari, da fara'a ya fito Suka tafa suna dariya irin na abokai yaushe ka shigo,?Aabid ya tambaya yace kwana biyu kenan room din Aabid suka shige suna hira Bayan Faruk yazo ya kwashi gaisuwa wajen Umma,Hamisu da Matarsa sai Harararsa sukeyi akan kawai abokin Aabid ne shima kiyayyar ta shafeshi.

Raudat nice na shigo gidan nayi kwalliyata da atamfar da matar Dan Majalisa ta bani nayi matsanancin kyau Kamar Yar wani Chairman na Local Government,Umma tace Yan Mata Raudat yau shigar Rana akayi min,dariya nayi Haka kawai nake Masifar kaunar Umma,Kusa da Umma naje na gaisheta har kasa,sannan na gaisar da Hamisu dake ta uban kallo na kamar Maye,dare daya yaji mugun son ni Raudat ya shigeshi sabo da kyawu na kawai yaji Yana sona,Ita Kuma Hauwa ganin kallon da Hamisu yake mini gani da uban kyau Kishi ya shigeta ,taji tsana ta me zafi, ni kuwa Raudat Ban San sunayi ba gaisar dasu kawai nayi nace Umma dama zuwa nayi na gaisar dake Bari na tafi.

Ai kuwa Baki Isa ba Raudat sai yamma Zaki tafi Kamar yanda Kika Saba matukar ba a gida su Mami Suka ce ki koma da wuri ba,Caraf Hamisu yace gaskiya ya kamata ki yini ko aiki kya Taya Umma,Umma dama itace Raudat din da rannan Kika ce itace tayi wani Abinci me Dadi Dana ci? Umma ta Harari Hamisu sabo da tasan halinsa da son Matan jaraba ga Matarsa Kuma ko kunya baya ji,Shareshi kowa yayi Umma tace Raudat Jeki kitchen ki ebo lemo da abinci Zaki gani ki kaiwa Yayanki Aabid dakinsa yayi bako.
Tsoro ya kamani nasan yanda Aabid ya tsaneni ko kallo ban ishe shi ba na shigar Masa Room abin fa da wahala.

Haka kawai gumi ya shiga keto min ta ko ina na mike jiki na ba kwari,Umma naji tace muje na shirya Miki abincin kawai sai ki Kai Masa,Jin Haka kishina ya Kama Hamisu ya Hade Rai yace yaushe za a tura budurwa baliga wajen Samari Umma,ai ga Hauwa aikin me takeyi ita ta Kai musu Mana,Dake nice baka kauna ko? Ina matarka ta sunna budurwa ta fini? Hauwa ta furta ranta a bace,Umma ma ta dinga yiwa Hamisu Fada ta inda take shiga Bata Nan take fita ba,Amma sai cewa ma yayi to Ni kawo Umma na Kai musu abincin,Tsaki Umma taja tace zoki karba Raudat wannan bashi da hankali.

Karbar katon tire din nayi zuciyata tana bugawa,gumi ta ko Ina yake keto min tsoron Aabid nake ji ga kwarjininsa ko sunansa naji tsorata nakeyi, Haka na tafi a hankali, bakin kofar na tsaya nayi knocking suna ta Hira da dariya ban San Ma Aabid Yana magana Haka ba sai yau,Shigo naji Aabid yace Bai San ni bace.

Kofar na Fara budewa sannan na dauki tire din na shiga dakin a hankali da sallama a Baki na,Yana ganin nice ya Hade Rai ya Bata fuska kamar yaga Mutuwa,Faruk dake saman katifa a kwance Yana latsa waya yace you? Yana nuna Ni da yatsa, da sauri na zuba Masa Ido Nan take na gano Wanda na gani ne a katafaren gidan da naje nace Yar Uwar Hajiya Kaltum ce Ni aka bani atamfa da kudi Ina Fitowa na ganshi a bakin gate zai shiga da mota, tsoro ya kamani, Faruk yace Kinyi Shuru kece ko? Da Sauri Na girgiza kaina nace Yaya tace? Ban fiye karya ba nace Bani bace, Faruk yace Kece wlh ba yanda zaayi na kasa ganeki, Amma me Kika je Yi a gidanmu? Aabid ko Yar Uwar Umma ce? Da Sauri nace Kakata ce ta aikeni gidanku na Kai wasu Kaya,Amma Kika ce ba Ke bace? Wasa nakeyi nice na furta Ina goge gumin dake keto min da mayafi na,Dakin Aabid Da ac Amma bana Jin sanyinta, da sauri na fice Daga dakin.

Aabid Yana ta Hararar Faruk Ina fita yace banza zaka zubar Mana da mutunci Ina ruwanka da wani taje gidanku,Faruk ya kalli Aabid yace wlh tunda na ganta naji Ina sonta sosai tun lokacin nake Neman Ina Zan ganta Yar Uwarku ce? Aabid ya bude Baki yace Faruk nasan son matanka kowacce kace kana sonta wannan ba Yar uwarmu bace Amma a unguwar Nan gidansu yake kawai wajen Umma naga tana zuwa.

Faruk ya sake gyara kwanciya yace That's nice Alhmdllh Umma sai ta shige min gaba na aure ta da gaske nake wlh dama naji a jikina na kusa aure,shekarar aure na ce ta Kama, fuska Aabid ya Bata yace wannan kucakar zaka aura? Bata wuce 17-18yrs ba? Ina sonta Haka Cewar Faruk, Allah ya taimaka Amma wlh Ni bazan shiga safgar ba,ko zance bazan rakaka ba,ba ruwana,ae naji indai Umma ta wuce min gaba an Gama Cewar Faruk, Aabid ya kalli Faruk yace daga Kunga Fara sai kuce kyau, ko wacce Fara me kyau ce a wajenku, dariya Aabid yayi yace wlh Raudat ta daban ce Kuma kaima kasan gaskiya karya kakeyi kawai ka tsani yarinya Aljanna ta aureka ka barmu masu lafiya muyi aurenmu,Murmushi Aabid yayi kawai yace ayi lafiya masu lafiya.

Dukkan aikin gidan Ni nayiwa Umma shi Hamisu yaki barina na huta da uban surutunsa,Ina gamawa nayiwa Umma Sallama na tafi Gida, Ina tafiya Hamisu yaja Matarsa suka tafi gida Suma.
Faruk a ranar ya samu Umma da Zancen Yana Sona,Umma taji Dadi Na samu Miji Managarci kamar Faruk,murna tayi sosai tace karka damu Faruk idan tazo zan fada Mata sai ka nemi soyayyarta Raudat yarinyar kirki ce baza ta ki Yarda da Kai ba,Aabid Yana gefe Yana tabe Baki har suka Gama ya raka Faruk mota ya tafi.

Haka kuwa akayi washe Gari Ina zuwa Wajen Umma ta sanar min Komai da farko gaskiya banso tace Faruk bane nafi son tace Aabid ne da sai na gyara halayena na nutsu na daina abinda nakeyi Marasa kyau Amma Faruk Bai dameni ba duk da cewa ya hadu shima sosai ga kudi gashi da hankali.
Bazan iya yiwa Umma Musu ba nace na Amince ya Fara zuwa zance wajena,Umma tace Allah Miki Albarka.

Aabid Napep ne ya saukeshi a cikin schl dinsu Abu Zaria ya shiga ciki Yana taku dai dai ka rantse jinin kudi ne,gashi ya dauki wanka cikin kana Nan Kaya na zamani black Jin pencil da Riga t-shirt Fara sai wata baka top marar kauri karama dai dai shi me dogon hannu yasa,da takalminsa half shoe Black, gashin Nan Yasha gyara dagwas dashi kowa ya ganshi sai ya sake kallonsa.
Yan Mata duk sun wani rude Ana Aabid ya shigo schl har waya wasu ke bugawa frnds nasu akan su fito ga Aabid ya shigo schl,ko kallonsu bayayi bare yasan me sukeyi.
Haka ya Gama lectures dinsa sai 4pm ya Gama kusan ko yaushe baya nacin lecture kullum ba ko yaushe yake zuwa ba Amma dake Allah ya bashi basira har yafi masu zuwa kullum kokari,ranar Daya zo Yana Gama lecture din da yake saurara zai tafi gida a ranar duk da akwai nisa,lokacin Exam kawai yake kwana a schl sai ko idan suna da test ta sassafe, baya zuwa lecture din 8 ko 9am ko wacce ce ba zai je ba bacci yake sha abinsa.
Da frnds Suka gaisa maza suka Dan tafa tare da Hira sama sama yace zai wuce gida,ya kusa bakin gate kenan wata tsaleliyar Mota red ta perker a gabansa, wata matashiya codediya Yar gayu baza ta wuce 25yrs tana kamshi ta fito da iyayi tana yanga tare da makale Murya tace

Aabid Manya Ina yini? Sai ayi ta Binka Kai ko a jikinka na Dade Ina fada maka Ina sonka kayi min kyanka Yana tafiya Dani,kasan soyayya Kamar mota ce wacce Bata da birki,Sam bata jin birki,kawai zagawa takeyi a zuciyar Wanda ya kamu da ita,Ina da kudi,Babana akwai Naira ka Soni ka huta,Yana tsaye har buduwar ta Gama yaja tsaki ya canja hanya ya barta a wajen kamar gunki Yan Schl din suna tayi Mata dariya taji kunya.

Kwana biyu tsakani da yamma Ina gidanmu Ina wanke wanke naji yaro ya shigo yace Wai Raudat tazo inji faruk, su Rufaidat ne Suka Fara min dariya Ana inye Yan Mata anyi goshi munji kugin mota,hannu na na wanke tare da gyara fuska ta nasa Hijab na fita,Faruk ya tausaya mana ganin irin gidan da muke ciki yasan akwai talauci, da Yar Fara'a na Karasa inda yake cikin katuwar motarsa, ganina yasa ya fito da sauri tare da cewa ranki ya Dade,tare da naka na furta sannan na gaidashi a mutunce na shigar dashi Dan zauren gidanmu kusa da kofar buhun Leda Muka tsaya.

Yace Raudat Manya fatan Umma ta fada Miki komai? Ae na furta Sannan nace Amma kasan duk Wanda yace Yana son mutum farar Daya to yayi karya,aure ba abin Wasa bane sai dai muci gaba da tafiya a Haka Muna tare ta Haka zamu Fahimci juna,sai kaga ko a farko ba a son mutum muamula da halayensa masu kyau baka san ma sanda sonsa zai shigeka ba har ka Amince ka auri mutum,so mu tafi a Haka Har Allah ya tabbatar da Alkhairi hope ka Gane nufi na? Tunda nake magana Ni kawai yake kallo har na Gama yace Uhm Malama Raudat Tsari,dariya mukayi Baki daya yace gaskiya kin birgeni,kin nuna min ke wayayya ce,nayi alkawari Zan jure komai yanda kike so Haka za ayi, ba komai na gode,Hira Muka shiga Yi Yana tambayata schl da sauran abinda ya shafi rayuwata na fada Masa Wanda Zan iya na bar sauran.
Allah Allah nakeyi ya tafi Kar Abba ya dawo ya tareshi a Hanya ya rokeshi kudi,Naci Sa'a har Faruk ya tafi Abba Bai dawo ba.

Room din Mami na shiga tare da sanar Mata komai Taji Dadi tace Allah yasa da gaske Faruk din yake sai ki aureshi a samu a rageku a gidan sabo da kunyi yawa dama Ina ta Addua Allah ya fito muku da Mazaje na gari,Inno ma sai Murna takeyi, Su Aymana kuwa harda cewa da sune Suka samu ko wata daya baza su sake a gida ba zasuyi aure abinsu.
Ko da Abba ya dawo ya samu labari shima yaji Dadi Amma ya ciji yatsa da Bai ga Faruk ba da ya samu na shagalinsa.
Kallo na yayi yace Raudat tawa idan zai dawo ki sanar Dani Ina so nayi Masa screening ko zai ci jarabawata, mun gano Abba kudi zai roka zai Ce wani screening Amma sai nace to Abba.

Tun daga wannan Rana idan Faruk zaizo wajena zance sai nace Abba gobe ne shi Kuma sai ya tafi sha'aninsa ya bar gida yace sabo da gobe Ina gida surikina zaizo, Ranar Kuma sai Abba ya zauna a gida sai na fada Masa nace Baya Gari ya canja lokaci,Haka na dinga yiwa Abba da taimakon Yan gidan.

Faruk Haka ya dinga kyautata min Yana kashe min kudi da yan gidan mu gaba Daya,hakan yasa talaucinmu ya ragu kaya masu tsada yake dinka min, Haka yasa aka Yi Mana katanga me kyan gaske ya gyara Mana room da ko Ina na gidan har Tiles aka Yi mana ya dawo sabo, Kayan Abinci da sauransu,Su Aymana yanga ta karu,a Unguwa kuwa sai gulmarmu akeyi mun samu gara muna tatsewa,duk abin Nan da akeyi naki yarda Abba yaga Faruk sabo da zai zubar Mana da mutunci, tun ban damu da Faruk ba har naji sonsa a Raina ,da kaina na fada Masa Ina sonsa Zan hadashi da Abba,Faruk sai Murna yakeyi.

Tunda na Hadu da Faruk Allah ya taimake Ni na daina sata da zuwa gidan mutane Ina hada karya Ana bani kudi,Inno ma ko Maula Bata cewa muje mun canja sosai Banda Abba.
Ranar da zai gaida Abba na fadawa Abba ya zauna Jiransa,Faruk ya dauki wanka na musamman yazo, Abba ya fice fit wajensa,Faruk ya zube gwiwo Yi a kasa tare da kwasar gaisuwa,Abba Yana ta washe Baki tun kafin yayi rokon nasa Faruk ya bashi kudade masu yawa Abba sai godiya yakeyi da abubuwan da yayi Mana a gidan.
Har waya babba Faruk ya siya min..
Bayan Faruk ya koma wajen aikinsa Abuja
Na Dan kwana biyu banje wajen Umma ba, yau na dauki wanka na cikin Arabian Gown Black me adon Golden Nayi rolling da mayafinta ga gashina nayi acuci nasha kyau,Kayan duk Faruk ya siya min har takalmi golden me tudu kadan na saka na sanarwa Mami sannan na tafi.

Tunda na shiga nake kwala sallama ba kowa a gidan Umma ta sawa room dinta key alamar Bata Nan,ban kawo komai ba na murda kofar Aabid naji ta bude na leka kaina naji Babu kowa ba ko motsi sai na shige room din abina,Har zan fita idona ya hango kudinsa Yan dubu dubu saman katifa, A fili nace shege Dan Iyayi na Samu Wanda nake so zan aura Bari ma na sake raba shi da kudin Nan,shi a dole ya tsaneni Baya so na, dariyar mugunta nayi nace Bai sani ba nice duk nake Masa sace sace yayi zaton Aljanune Allah sarki to na yau gaba Daya zan daukesu,Kudin na Irga cas dubu goma na Samu na tura su cikin Bra dita,Na bude gongonin Madara na cika Baki na tare da rufe gongonin,sai da na shanye Sannan na gyara bakina na juya da niyar tafiya kawai naci Karo da Mutum a bayana ya harde Hannayensa kawai Yana kallona alamar ya Dade tsaye a bayana ya Gama gani da Jin duk abinda nakeyi nake Kuma cewa.

Tsoro ya kamani gabana ya Fadi gumi ya jika min Kaya,jikina ya dauki rawa karrrrrr...karrrrrr..Kamar mazari, nayi nayi na tsaida rawar da jikina yakeyi na kasa sai ma Karuwa da yakeyi kafata tana karkari Ni kadai na rasa Bakin magana,durkushewa nayi a kasa kafin kace me Hawaye ya wanke min fuska tas ta ko ina.

Fita naga yayi tare da kulleni a dakin yayi da key nayi zaton mutane zai Tara min sai naga ya shigo da Igiya me tsayi da Kauri,farin seletape me Fadi ya dakko a Drower dinsa,ya dakko wuka tana sheki,Nan take na barke da kuka, seletape yasa ya manne bakina Kam sai Hawaye ba sautin kuka, wata kujera ya jawo ta Dining table ya daukeni Kamar tsinke ya jefa Ni saman kujerar ba Imani yasa Igiyar Nan ya daureni ta ko Ina Tam bana ko motsi ba Baki Kuma,Wukarsa ya dakko ya rike ransa a bace Ya tura Hannunsa ta wuyan rigata Ina ta so nayi magana ba dama Ina ji Ina gani ya shigar da hannunsa cikin rigar ba mutunci har cikin Bra din naji Hannunsa Yana yawo a Dukiyar Fulanina harda mugunta ya hada da na shanuna ya Fisgo kudinsa,wani zafi ya ratsa ni na barke da kuka Amma ba damar ji sai Hawaye.

Kudin ya ajiye a gefe ya kalleni da muguwar tsana yace Dama kece barauniyata munafukar banza wlh kisa a ranki baza a ganki a gidanku ba sai Nan da Sati Daya Zaki ci ubanki,duk abinda ake sace min Ashe kece barauniyar banz.

Ina so na bashi hakuri ba dama yace harda zagina ko to zakiga zagi ya fisgi Hannuna Daya dake daure ya samu tafin Hannuna yasa wuka ya yanka da wukar jini ya feso ya kalleni yanda Hawaye ke dildilo min,yace daga yau baza ki sake marmarin satar Kayan wani ba,wukar ya Kara caka min tsininta a tsakiyar hannun na rumtse Ido sabo da azaba Ji nake Kamar na Suma,ya sake yankawa,sai da yayiwa tafin Hannuna kaca kaca da wuka jini tako Ina a hannun Fitowa yakeyi,ya Kama dayan ma ya yayyankeshi, Bai hakura ba yace dama na tsaneki tunda na ganki ya dakko ruwa me uban zafi ya Danna min hannayena a ciki na rushe da uban kuka Amma ba sauti,sai da ya Gama gasa hannun da ruwan zafi sannan ya kwance igiyar daya daureni na Fado jikinsa ragwaf Ina magiya da rokonsa yayi hakuri wasu maruka ya zuba min sunfi uku,ya dakko Belt harda da dage min riga ta baya ya zane min gadon Bata tas sai da fatar wajen tayi rudu rudu ta farfashe sannan ya sake daureni ya barni a daure saman Kujera Baki like ,ya gyara komai na dakinsa Ina kallo yazo yayi wanka yayi Kwanciyarsa bacci ya kwasheshi.
Bai bani ko ruwa ba,ya Riga da yace sai nayi sati guda Ina daure a dakinsa.









AsmaBaffa
[4/16, 9:29 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙








4







Official







By
AsmaBaffa










NA KUDI NE

RASHIN SA'A COMPLT ga masu bukata dari uku ne 300.
Zaku iya nemana ta wannan number
08033933642

YAN NIGER Ku Nemi wannan number
+227 90 79 59 39

NA KUDI NE

TA GYARU dari biyu ne 200.
Masu

Please Login or Register in order to submit comment