Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na farko da wata ta Bata masa Rai ya kalleni kallo daya tare da zuba Min Hara ta masifa, duk Rashin kunyata Shuru nayi na kasa hada Ido dashi, Ita kuwa Khairat tunaninta sabo da ita nayi hakan Bata San target nake hadawa ba yanda Zan sace shi tas,Har wani Babban yatsa ta daga min aboye, ni kuwa na naje tare da rada Mata ki Sha kuruminki yanzu na karbi case din Dole Zan hada Masa tarko sai ya soki,dariya tayi da jin Dadi Muka tafi Yana ta Isa da takama,duk Iyayin su Khairat sai Muka ga ai ko gefen rigarsa Basu Kama ba,Khairat harda sauri ta wani jera dashi,sai ko ya Kara ja baya,ni kuwa Ina bayansu Ina wakata Ina Cewa Abida shegiya,Abida ga yanga,Abida sai Iyayi eh..eh...Abida ga Girman Kai,Abida ba sisi sai gyare gyare, Yar Abida me Jan lips,Yar Abida me gashin Dokilolo, Kaga Abida Abida sai karya Abida ga Mulki, sauti na Kara tare da cewa Yar banza Abida Kai lalle Yar banza Abida.

Aabid Yana jina wlh yasan da shi nake kawai Bai son ya yanke Hukunci ne akan wata banzar yarinya karama shi yasa ya share ni Kamar baya ji.
Aabid yasan Basu da kudi Amma gidansu mugun Aljannar Duniya ne akan nasu Khairat, gidanmu ginin Bulo ne Amma ka rantse kango ne,ko Kofa Babu sai ledar buhu ce aka daura,Haka rabin katangar ya zube da Langa Langa aka gyara, saidai Aabid ya yaba da Tsabtarmu tayi Masa.
A tsaye da gadara ya gaida Mami tare da Inno, Abba Yana dakinsa ya fito da sauri Jin Muryar Namiji ko zai samu hanyar Maula, Aabid ya gaida shi fuska ba Rahma,Abba yaga Bai samu fuska ba sai ya koma daki yayi lakwas Jin ance me gyaran speaker ne.
Wasu tsofaffin speakers muka Fitowa da Aabid Wanda ya kusa dariya ta kwace masa ya danne.

A wulakance ya Fara gyarasu,Mami ce ta kawo Masa kujera harda Ruwa,yaji Dadi kuwa yace na Gode,Ni dai Ina gefe Ina ta tunanin Taya Zan bullo Masa na Samu rabo na, Khairat tana gefe tana ta faman kallonsa kamar zata cinyeshi Haka su Fadeela ma sai kallonsa sukeyi musamman Ayman mayya an Dade ba miji.

Bamuyi zaton speakers din zasu tashi ba sai gashi a kankanin lokaci sun farayi ya jona da wayarsa sannan ya zare, Yeeeeee na furta nace wakar Abida Zan kwana jii yau shegiya Abida Ah..ah...ah..na juya Ina Rawata,Yana jina Kamar zuciyarsa ta fito Haka yake ji.
Bacin rai yasa ya Mana wayo yace Miko min speakers din na gyara wani Abu na manta ya furta Yana Bata Rai, Khairat jiki na rawa ta Mika Masa,ya karba ya sake kwancewa ya tsinke wayoyin Daya hada sai da ya tabbatar ya Kara lalatawa yanda har abada baza tayi ba sannan ya hada ya tashi yayi tafiyarsa Muna kallonsa tuna ninmu ya gyara da gaske,sai da muka kunna yin duniya Taki yi.










AsmaBaffa
[4/16, 9:22 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙








2







Official








By
AsmaBaffa







NA KUDI NE

Kamar yanda kuka sani Allah yasa an gama RASHIN SA'A lfy, ga masu bukatar Complete Dari Uku 300 kuyi min magana ta pc a wannan Number
08033933642.


NA KUDI NE


TA GYARU na kudi ne Naira dari biyu 200 ne ga masu Bukata.

Ga masu son tura number na katin MTN ta WhatsApp, Zaki iya turawa ta wannan number
08033933642.

Masu son siye ta Hanyar Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Masu son biya ta hanyar bank ga accnt number
2177560408, Yahaya Garba Muhammad, zenith bank.





Page naku ne Marcycool and Adala Flower.







Tsaki naja Khairat ta dunguremin Kai tace Yar iska wlh ke Kika jawo yaji Haushi ya gane dashi kike banza Yar iska,Baki na murguda Mata nace Ina ruwana Dan nayi wakata ko shine Abida?
Inno ce ta dakawa Khairat dake zagina tace karki sake zagar min Raudat akan tayi wakarta sai kice dashi take ko sunansa Abida? Ubanwa yace Iyayensa su sa Masa Aabidar.
Ke Raudat shirya mu tafi gidan Alhaji Na Allah Kansila yace mu koma yau da yamma Yana gida.
Abba ne Ya fito Jin za a fita Nemo kudi Yana washe Baki yace za a fita Neman ne Inno? Inno tace wlh kuwa Dan Nan ai gwara muje ma samo na abinci geron koko ya Kare daga nan gobe Babu,Abba yace hakane Amma ya kamata Ni a Dan bani wani Abu na Rike a hannuna ko naji karfin jikina,Inno ta kalli danta me matacciyar zuciya tace Allah yasa a samu da yawa,Ameen yace.

Inno da Raudat Suka yi Shirin zuwa gidan Kansila,Raudat sanye take cikin wani jemammen yadi ya kode yaci duniya Brown color ne Amma sabo da yaji jiki ya koma Red, doguwar Riga ce a Haka ma sune masu Dan kyau a kayan Raudat sai na zuwa Unguwa kala biyu ba a sasu wannan sai gidan biki.

Abbanmu Fitowa yayi kofar gida tare da kwanciya a jikin bishiya Yana Hutawa Muka wuceshi da Inno Muna Hira yanda zamu hada plan mu samu kudin.
Inno ta kalleni tace Raudat wacce basira zamuyi mu samu ne? Na kalli Inno nace ai Inno muce Wani ne baida lafiya kin san rashin lafiya Dole a samu ko ba yawa,Dadi ne ya Kama Inno tace yawwa Haka zamu ce maza muje Yar Nan shi yasa nake sonki.
Dariya nayi nace Inno kwana Nan Zaki Fara ganina da kudi,Amma dai bana sata ba? Haba Inno wani aiki na samu a gidan masu kudi Zan na zuwa lokacin danake da time,Masha Allah Raudat wanne Me kudin ne? Alhmdllh Kuma aikin ne sai kina da time Zaki je?
Kai na dagawa Inno tare da furta Haka aikin yake Inno Wai suna da Yan aiki da yawa,Haka Inno ta dinga murna,Ni kuwa dariya nakeyi Dan nasan karya nakeyi Aabid Zan lallabawa na dinga yiwa sata ko yaushe idan na kawo gida za ace aiki nake zuwa.

Da dare Abba Yana kwance wani matashi Hashim da bazai wuce 26yrs ba ya zo wajen Aymana zance a Lifan ya yazo ta fito Suka sha Hira sannan ya Bata 2k yace gashi Kya sa Kati,karba tayi tare da godiya,Abba Yana labe Yana ganin komai Basu sani ba,Sai da sauri ya fice fit yabi Hanyar Daya san Saurayin Hashim zai bi da Lifan dinsa ya wuce, Yana Dan tafiya a kasa Hashim ya taho da Lifan zai Wuce da sauri Abba ya tsaida shi,bayan ya tsaya Abba yace sannu samari Suka gaisa sai yace Dan Allah can gaba kadan zaka saukeni zanje Chemist ne,Hashim ya gane Abbanmu ne, a mutunce ya daukeshi Suka tafi.
Suna cikin tafiya Abba yace Sannu Yaro Allah ya maka Albarka Dana, wajen Aymana kake zuwa ne? Hashim yace ae wlh Abba,to yayi kyau Haka ake so kaci gaba da zuwa kaji,Ai yarinya ce me hankali Aymana kaci gaba da zuwa kaji,Hashim yace Inshaallah.

Bayan sunzo kusa da chemist sai yace a Nan zan sauka Dana,Hashim ya tsaya da machine sai da ya sauka sannan Abba yace kaga Dana wlh cikin Yaran ne Daya ba lafiya Zan siya Mata magani gashi da tsada kudin da kyar zasu Kai min sai kuma naga gaka Dana Alhmdllh sai ka cika min,Hashim yaji wani dam Amma sai ya zaro dubu biyu yace gashi Abba ba matsala, Abba ya karbe da sauri Yana Murna Yana godiya na gode Dana Allah ya maka Albarka,ai Kai Dana ne kaci gaba da zuwa kaji.
Hashim Yana tafiya Abba ya dauke Hanya ya bar Wajen Chemist Bai tsaya ko Ina ba sai gidan rawa da wajen kallon Dambe a Daren.

Ni da Inno kuwa tunda muka bar gida Muna cikin gidan Kansila yace mu jirashi zai zo ya ganmu,a cikin gidan mukayi Sallah Muna jira har sai Bayan Isha ya dawo gidansa sannan ya kalli Inno yace me Kika ce ne bukatarku? Inno tace Wlh Hon Jikata ce Bata da Lafiya tana kwance ranga ranga abin ba Dadi an rubuta Mana magani har na dubu Biyar shine nazo ka tallafa Mana.
Nima Raudat na Kara langabewa Muka koma abin tausayi dubu biyu ya zaro yace gashi kuje ku cika, wannan mulki da muke ciki ba kudi wlh ba a sakar Mana muna cikin wani Hali, Inno tace ba komai Dana an gode Allah ya saka daga Nan muka ce da matar Kansila zasu tafi tace ga tuwo na Gama ku tsaya kuci,Aiko Muka zauna Muka Lashe tuwonmu tas sannan Muka Mata sallama, munzo tafiya zamu wuce ta jikin igiyar shanya gaba Daya wanki akayi an ciki igiya da shanya,Inno Bata Sani ba na sa hannu na zari wani gyale me kyau sabo yellow nasan na Yar kansilar ce budurwa, na boye cikin zanina Muka tafi gida.

Duk wahalar da Muka Sha muna komawa Inno ta dauke Dubu Daya ta bawa Abba ta dauki dari biyar tace gobe dai a Sha Miya da Nama, ta bani Naira dari,ta dauki sauran ta bawa Mami tace ayi cefane sisi Inno Bata dauka ba.
Washe Gari da yamma Ni aka bawa dari biyar din naje na siyo Naman Miya.

Sanye nake cikin Wata atamfata green and yellow na yafa mayafin Dana Sato gidan Kansila yellow, Atamfa ta kodaddiya jemammiya taji jiki matuka Gaya atamfar, Mami cikin sanyinta tace a Ina Kika samu wannan gyalen me kyau sabo Raudat? Zai wuce na sata ne abinda ta Saba Cewar Fadeela, Harara na zuba mata,Rufaidat Kanwata tace wlh ki canja Hali Tam, Mami tana ji tace ki daina ba kyau bana so Raudat, shike Nan fadan Mami, ficewa nayi da sauri nasa flat takalmin Aymana green na tafi siyo nama tas Dani ba kazanta.

Ina zuwa gaban Me Naman Sai Ga Aabid yazo shima siyen na gidansu,wani azabar kyau da yayi cikin wani yadi Milk color sharara dashi me tsada duk Faruk ke dinka musu.
ga kamshi Yana zubawa,Nima naje wajen ko kallona baiyi ba,Ni kuwa kyawunsa yasa na dinga kallonshi da kyar na saita kaina, Kudin Daya zaro masu yawa yasa na rude ji nake Kamar na fisge su Amma ba Hali, wuya na shiga mikawa Kamar na rakumin dawa Ina leka kudin hannunsa Ina Jin inama nawa ne, dubu biyu ya zaro a ciki tare da mikawa me nama yace gashi, Aiko me nama Ina Mika Masa nawa, ganin na dari biyar ne ga me dubu biyu sai ya Fara karbar na Aabid, nace Halilu Me nama Mene Haka ai na riga shi zaka Fara karbar nasa wannan ba adalci bane,Halilu ko kulani baiyi ba ya yankawa Aabid harda Kara Masa da yawa yace gashi, Ni kuwa ya karbi kudina ganin nice Raudat me Kyau ya washe Baki ai ban San ke bace Raudatu kawo a baki,Haka ya dinga kallona Yana tilka min uban Nama Yana washe Baki ya bani da yawa yace jeki da kudinki Yan mata, Aabid haushin me nama ya cika Masa zuciya akan Yar yarinya karama zai dinga bada Kansa Haka Yana washe uban Baki harda Bata kyauta,tsaki yaja yayi tafiyarsa,a Raina nace Dan bakin ciki Ina Nan zuwa kanka sai na daina satarwa kowa komai Zan dawo kanka.

Washe Gari kuwa da Sassafe Muka tafi gidan Wani tsohon Dan Majalisa aka ce baya gida ya tafi Abuja,Gidan Muka shiga Matarsa me kirki ta bamu ruwa harda Abinci Muka ci Muka koshi, tace daga Ina kuke? Inno tace Yan gudun Hijira ne mu daga Niger muke,Ni Kuma ban iya karya ba Haka nake zai wahala nayi karya,ko laifi nayi indai Ni nayi Zan fada, fakat nace Nan garin muke Rigasa,Inno ta samu ta dinga dirka min uban duka a bayana, Dan ubanki Ni Zaki karyata,Matar tace daina dukanta Allah ya tona Miki asiri Iya,kina tsohuwa ko kunya bakya ji ki dankara karya wlh kiji tsoron Allah Yar Maula,dama irinku ne Bata Gari tashi ku bar min gida,Inno taji kunya matuka Haka ta mike da sauri tayi waje,Matar Dan Majalisa tace tunda Kika Fadi gaskiya Yan Mata ke tsaya na Miki kyauta Albarkacin gaskiyarki, Murna da Dadi Suka kamani, Ina tsaye ta kawo min Riga da skert kala uku kusan sababbi ne ma dai dai Ni,lace Daya,atamfa kala biyu tace na Yarta ne tana turai karatu kije kisa,na karba Ina godiya ta kawo dubu Uku tace gashi kuje,Godiya na dingayi na fita na iske Inno, da Inno tayi fushi Amma ganin matar ta bawa jikarta kyauta sai Murna tana Mata Addua,Muka tafi gida.

Abba Yana kusa da gidanmu wani Dan matashi Bashir Yana mutuntashi a Unguwarmu yake, ganin yaron Yana Sana'ar gwanjo Kuma ta karbeshi shike Nan Abba kusan ko yaushe idan ya ganshi sai ya tambayeshi kudi, yau ma ya gaidashi yace Dana Zo mana,tuni Bashir ya Saba da rokon Abba yace gani Abba,Yawwa Alhmdllh da Allah yasa na ganka Dan Allah kaga wlh itacen da za ayi girki ne gidan yau Babu,ka siya min ko na dari biyu ne, Murmushi Bashir yayi tare da cewa ba komai Abba Bari na siyo maka na dari biyar ma, Haka Yaje ya siyo da kansa ya kawowa Abba ya karba Yana murna ya kawo Mana gida Kuma da gaske babu itacen ko Daya bare ayi girkin dare.

Washe Gari da Sassafe Babu inda zamu fita yau Ni da Inno da wuri na zurma Hijab tare da daukan kwanon Koko na nayi dabara tare da sadadewa daga gidan na tafi shagon Alex inda Aabid ke aiki, ko da naje Alex yace ai Yana schl sai anjima da yamma zai zo idan kina son ganinsa ki Bari sai Saturday Sunday da safe Zaki sameshi, ok nace na juya jiki ba kwari.
Da Rana kuwa Tuwon masara mukayi miyar kuka ba a Gama girkin da wuri ba,Ana zuba min nawa na sake sace jiki na tafi shagon Alex,Ina zuwa Dai dai lokacin Aabid ya dawo daga Schl harda littafi a hannunsa,ya shiga shagon ko kallo ban isheshi ba duk kyau na abin Nan Yana bani mamaki.

Kusa dashi na Karasa nesa kadan nace Ina yini Bai ko amsa ba sai ya akayi yace? Jin muryarsa yasa na rude na Fara hada uban zufa da kyar na ajiye Masa wani lalataccen kwanon mu na abinci nace gashi Inji Anty Khairat tace a kawo maka, tsaki yaja a fusace yace tashi ki bani waje da abincinki dauke tarkacen banzan ki da wofi an fada muku Ni irin ko wanne banza ne da har zanci abincinku, ba shiri na dauke kwanon cike da kunya gumi Yana keto min ta ko Ina Haka na koma gida.

Ranar Saturday da wuri naje lokacin yazo wajen aiki tuni,Jiki na Yana rawa na ajiye Masa kofin silver Kato shake da Koko na na safe,Ina tsoro Ina ja da baya nace gashi Inji Anty Khairat tace batayi zuciya ba,Mikewa tsaye yayi a matukar hasale yayin Dana saki kofin kokon ya Fadi a kasa na kwala ihu kadan nace wayyoooooo nayi waje da gudun tsiya, mutane na kusa sun tsorata tunaninsu Wani abin ne sai Suma Suka tashi da gudu sai da sukayi Nisa sannan Suka ga na tsaya Ina hakki, tsaki Suka ja Suka koma suna dariyar abin kunyar da sukayi.
Washe Gari ban hakura ba na sake Kai Masa na gudu Haka na dinga Yi kullum sai na Kai Masa kokon safe na,ko abincin rana ko na dare,Haka Khairat Bata San Ina Yi ba sabo da taga bazai so ta ba ta hakura bata ko zancensa yanzu Amma Bata San ni Ina ta Kai Abinci Ina cewa inji Khairat ba.
Duk yanda naso ya dinga ko min magana yaki Haka Koko na yanda nakai nake dakkowa Bai taba daura Hannunsa saman kwananmu ba.
Duk tunaninsa Dan ya Soni nake Masa Haka Bai San Ni sata nake so na samu dama nayi Masa ba,ko Inno bana bi yawon Maula sosai burina na samu dama akan Aabid.

Rana ta karshe Dana Kai Masa kokon safe Ranar Saturday sai Allah Yasa naji yace Zazzabi yakeji zai je gida yayi wanka ya Huta,Alex yana ta Yi Masa sannu, ya tashi ya dauki hanyar gida, a hankali nabi bayansa Ina labewa a Lungu Ina binsa Sadaf sadaf ba tare da ya sani ba har Muka Isa gidansu me Dan kyau na talaka me rufin asiri, Yana shiga gidan na bishi ciki na makale a zaure,gidan a sumulmule yake da siminti ko Ina cikin Dakuna Kuma da kitchen da Toilet duk tiles ne, Umma ya iske a tsakar gida tana Jin Radio, har ka dawo Aabid? Ae Umma bana jin dadi Hutawa zanyi Amma Bari na Fara wanka, dakin dake jikin zauren ya dawo ya shige Wanda shine dakinsa,akwai Window ta cikin zauren Daya window din Kuma ta cikin gida, a hankali na dage kafafuna tare da leka dakin,kamshi ne ya daki Hancina,Dakin nasa yasha tiles harda plasma tv,ga wata katifa katuwa kamar gado,komai na dakin na Yan gayu ne ba tarkace ya tsara dakin sosai,harda Fridge Kato.

Da Ido daya na sake lekawa na iske Yana irga kudi zasu Kai dubu Biyar,a hankali nace eho...Ashe me kudi ne,dama da gani nasan ya Tara kudi ai kuwa Dole na yagi rabo na,ya shiga cire kayansa,ganin irin kyawun surarsa na kasa dauke idona a kansa a hankali nace kaga mutum da dadin kallo,wannan Dole Yan Mata su soshi baza a gaji da kallonsa ba,Ina Haka ya zare Boxers dinsa da sauri nayi kasa da kaina Banga komai ba,sai da na dauki lokaci sannan na leka na hango shi Yana dafe Kai irin zazzabi yakeyi ga Towel ya daura a kugunsa Alama wanka zaije.
Yana fita Tsakar gidan Naji Umma tana cewa Ga ruwa can me dumi na hada maka sai ka Kai Toilet dinka,Baki na tabe nace Kato dashi Ana Kai Masa ruwan Wanka,Umma na hango ta mike ta shige dakinta,shi Kuma ya dakko ruwan ya shige bayinsa dake cikin room dinsa,Toilet din ta hadu dai dai misali komai Kal Yana kamshi, Ina ganin ya shige wanka, Nima nayi wuf na fada dakin Aabid a hankali nakeyin komai yanda ba Wanda zaiji motsi na.

Cikin kudin Daya ajiye gefen pillow na dauka na saci dubu Daya a ciki,sannan na duba gefe naga ragowar dambun nama a roba na dauke Robar gaba Daya,har na fita da sauri na sake dawowa hango gongonin Madara da milo dana Yi, na bude gongonin da kyar na ebi kamar cokali hudu hudu na zuba a wata ledar bread Dana tsinta a dakin,Yana can Yana ta wankan Iyayinsa,Ina gamawa na fice fit daga gidan na tafi gida Ina murna yau an samu harka.

Tun a Hanya Ina tafiya Ina Shan Madarata da Milo a cikin hijab nake sa kaina na Ina lasar madarata da Milo har naje gida, Ina shiga Naga kowa a gidanmu ya shige daki an kwanta anyi Shuru ba Wanda kewa Dan uwansa magana, ga gida rafai ba ko tukunya akan Murhu da gani Babu abincin dafawa kowa yunwa ce ta cinye Masa ciki, Abba kuwa baya ma gidan,yasan halin da ake ciki Amma yayi ficewarsa, ganin Haka kawai nayi sauri na fita wani gida naje tana shinkafa da Miya da nama harda salat, ta dari biyar Na siyo Mana da yawan gaske da nama na shigo gida nace salamu alaykum da kwarin gwiwa, Mami na kaiwa kawai abincin ta ganni da Katon kwano nace gashi a raba kowa yaci kafin na dare, a Ina Kika samu abincin? Kudin Dana ke Tarawa ne na gidan da nake zuwa aiki,Inno ta sani ma,Yunwa na damun Mami ko tsaurara bincike Bata Yi ba ta Raba abincin kowa aka zuba Masa,Inno harda shewa tace Raudat Allah dai ya Miki Albarka,Ana Haka sai ga Abba ya shigo bai ko tambayi ya akayi aka samu ba kawai yace a zubo min nawa, su Aymana Suka kalli Abba da mamaki kawai Suka ci gaba da cin abincinsu, shima aka bashi nasa, kafin kace me ciki ya dauka an cika gida da Surutu Ana Kaya Kaya Ana Hira da dariya Amma dazu kuwa kowa luf ko motsi ba a Yi.
Dari biyar din kuwa ragowa Mami na mikawa nace a San ya za ayi ayi na dare ko Yaya ne,sai Murna akeyi Amma kowa yasan bazai wuce kudin sata bane Hali irin na talauci yasa Mami ta karbe Bata Yi fada ba,sabo da nace aiki nakeyi.

Aabid kuwa Yana Fitowa daga wanka mamaki ya Kama shi ganin gongonin Madara a bude Kuma duk an zubar a kasa,Babu dambun Naman Daya Bari, kudinsa ya duba Babu dubu Daya a ciki gashi kudin suke Nan ya hada zai biya kudin Wasu littafai da zasu siya,da kyar ma ya hada dubu Biyar din,Wajen Umma ya nufa yace Umma wani abin mamaki ne, Dafe kirji Umma tayi tace Mene ne fa,? Aabid ya Bata labarin abinda ya gani,Umma tace bazai wuce Almajirai ba sabo da yanzu sune barayin Gari da ka ajiye kudi da abinci zasu sace Allah ma ya kiyaye ba duka Suka Dauke ba, Bari Ina da dubu Daya Hamisu ya bani rannan Bari na baka ita sai ka cika, Aabid yace ok Yana mamakin sata Kiri Kiri da ranar Allah,ai kuwa Allah ya hada shi da wannan barawo ko waye ya kamashi zai gane shayi ruwa ne.

Washe Gari salon dabara Raudat ta canja, gidan su Aabid ta shiga direct wajen Umma,ta kwada sallama,Umma ta fito tana amsawa da fara'a sai dai Kyawun Raudat ya gigita ta, Yan Mata shigo Mana Umma ta Kai Raudat har Palo, Raudat ta duka har kasa tare da gaisar da Umma,amsawa tayi Raudat ta birge ta, Lokaci guda taji tana kaunar Raudat,Raudat tace bamu da Nisa daku kawai na shigo Mu gaisa, Umma taji wani dadi tace masha'allah na gode,Raudat Haka ta yini a gidan tana ta yiwa Umma Hira tare suka Yi girki da sauran ayyuka kaf,Umma tana ta Jin Dadi matuka,ka rantse sun Shekara da Umma Haka suke Hira,Sai da Raudat taci Abinci tayi Sallar laasar sannan tayiwa Umma Sallama ta tafi gida,Umma tana ki dinga zuwa kinji Muna hira,Raudat tace ba komai kusan kullum zanzo.

A zauren gidan ta labe Umma tayi Alwala ta shiga Daki,wuf Raudat ta dawo ta lallaba ta murda handle din kofar Aabid kawai taji ta bude Aiko ta shige da sauri dakinsa, ta sake kwasar Madara da Milo,ta sace wani lemo da ayaba data gani da yawa a cikin katon fridge dinsa dake dakin,taga wasu snacks ta kwashe ta hada Leda Viva guda da kayan ci tayi waje ta bar layin Baki daya ta tafi gida.
Aabid yauma Haka yaga barna yaje ya fadawa Umma,Umma tace ka dinga sa key kullum sai nayi maka fada Almajirai ne kawai ka kiyaye gaba, sanda zasu shiga Ina daki ban sani ba.

Washe Gari da yamma lis Raudat taci kwalliyarta tayi kyau sosai sai dai Kayan jikinta sunji jiki ta Shiga gidan su Aabid wajen Umma ta dinga kwala sallama,Umma ta fito tace Raudat kece tafe sannu da zuwa,Aabid lokacin Yana kitchen sai soye soyensa yake Yi, Ya juyo da sauri Jin ance Raudat ga Kuma murya ya gane ta,Hira yaga suna ta Yi da Umma suna dariya Kamar sun San Juna, Baki ya tabe yaci gaba soya

Please Login or Register in order to submit comment