Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace Kai dai Allah ya shirya kanka kawai ka sani,Raudat wlh ki dage ki samo naki ko idan na gaji nayi Miki auren Dole, Khairat kina gani Exam suke zanawa Neco ta kusa gamawa Kuma Kin san Khairat da saurayinta na aure Sufyan yaron kirki Yana taimakona sosai,gashi Doctor ne kwanan Nan ya Gama Yana aikinsa ke kuwa ko Yan samarin ma sun daina zuwa wajenki.
Allah zai Bata ne itama cewar Mami, Abba Yana kallon Mami yace Ameen Nima Haka nake so sarkin son Yaya ba dama ayi musu fada sai kin tare musu ya fice waje Muna kallonshi.
Ni kuwa nace ai da gani Allah ya kadarta Mana a layi ake jero Mana za muyi aure,Kinga yanzu yayye na Sunyi nice akan layi Haka nake ta sawa a Raina, tunanina Dan Allah yasa su Aymana Sunyi aure a jere ai a haka zai kasance nice zanyi sai Yar auta Khairat.

Bayan Watanni Amare suna ta Shan Amarcinsu ni kuwa ko Kare Bai sake zuwa wajena zance ba, Khairat kuwa Sufyan dinta har ya kawo kudin aurenta itama zata tsallake ta barni,wannan yafi damuna ace Kanwata ta tafi Ni Ina gida ai abin da kunya gashi duk nafi kowa kyau da komai a gidan Amma su sun samu Ni kuwa Ina Nan ba kowa ko na rage dare Daga Islamiyya sai gidan Umma,Aabid ma bana ganinsa sosai Business dinsa ya Kara zafi Abu ya bunkasa har kasar waje yake fita yanzu shine China da Dubai,sai kyau yake karawa Yana fesa uban gayu,Faruk ko ya bawa Aabid kudi ko yayi musu dinki Aabid baya karba,cewa yayi yanzu Allah ya bashi nasa Bai kamata ba,Haka da lafazi me Dadi ya zame jikinsa da kayan Faruk sannan shima tunda yake samu yake kyautatawa Faruk sosai da Abubuwa duk da yasan Faruk yafi karfinsu Amma Yana bashi, har yafi Faruk kashe kudi ma akan abinda Faruk yake Masa idan an hada yanzu na Aabid yafi yawa,abinda yasa Aabid ya kiyayi Kayan Faruk tunda yaji yayi Mana Gori akan ya taimaka mana shike Nan ya zame kansa, Fauzan kuwa anyi Masa aure da Yar Uwarsa suna Shan Amarcinsu Amma har yanzu Ina ransa Kuma Yana tunanin Kara ta biyu Dani Nan gaba.

Ansa ranar Auren Khairat itama saura wata biyu, Umma tazo gidanmu wajen Mami da Abba,Tace Dan Allah Shawara tazo da ita akan danta Aabid,Mami tace na me fa? Umma tace Aabid yanzu Allah ya hore Masa Yana samu dai dai gwargwado Yana da komai na aure Amma yaki Nemo budurwa kullum sai yace bashi da time,gashi ko yaushe Yana yawan fita Dubai da China Bai Dace a barshi ba shi ba aure ba Kar shedan yasa ya kauce hanya watarana, babban baligi kamarsa gashi da kyau Mata suna rubibinsa ya kamata ayi Masa aure, Abba yace Haka ne,Umma tace to nayi tunanin na nemar Masa Raudat Amma sai na fuskanci basa shiri da juna naga Sam Basu ko birge junansu tsakaninsu fada,lokacin Ina labe a jikin kofa Ina Jin abinda Umma tace takaicinta ya kamani, a hankali yanda baza suji Ni ba cikin rada rada nace a Ina muke fadan dashi Lallai ma Umma yau nasan bakya kaunata,Ina ji taci gaba da cewa shine nake so Mami ki rakani Muje wajen Yan Uwana Kano akwai Yar gidan wani dangina Madeena na nemowa Aabid, sabo da idan naje wajen bare za a ce ba a San asalinsa ba abin ya Zama rigima, na sake cewa Lallai Umma Zaki jawowa Madeena bala'i Dan sai na targada ta,Ni ya korar min samari na kyaleshi yayi aure ai Bai Isa ba,Mami tace ba komai ai sai muje,Abba ma yace hakan yana da kyau ai Raudat fitinanniya ce, Umma tace Ina so Abba ka zamewa Aabid waliyinsa, Abba yace ah ba komai Yaushe zamu je? Mami tace gobe idan Allah ya kaimu,to Allah ya kaimu Ameen.

Komawa nayi inda nake zaune sai ga Umma ta fito Na dauke kaina daga Yamma inda nake facing Umma na cillashi kudu na kalli can tare da nuna Keyata, Umma tace Raudat sai kace wacce nayi miki laifi wannan dauke Kai Haka ko rakani baza kiyi ba, juyowa nayi Babu wata fara'a dana Saba nace bana jin dadi ne Umma ki gaida gida,Allah ya sawwake sannu Kisha magani kinji? nace to ki gaida gida.

Umma ta tafi gida, da dare Umma ta Kira Aabid Suka zauna tace Aabid na zaba maka matar Aure,Kuma nasan baza ka bani kunya ba, zabina me kyau ne Aabid Dan Allah karka bani kunya nayi hakan ne Dan gujewa shedan kar ka kauce hanya watarana, duk da nasan ma hakan baza ta faru ba Inshaallah, Amma Allah ya hore maka, aure ne ya kamace ka, Aabid baya so a ransa ko wace tunda shi dai Bai ga wacce tayi masa ba a duniya,yasan bazai wuce Umma ta hada shi da Raudat ba don ita ya sani Yar gaban goshinta duk da cewar Bai son Barauniyarsa Raudat tayi Masa karama,Kuma shi wayewarta Bata Kai ya aureta ba,bazai ma iya sonta ba sai dai Umma ta gaji ta Raba auren Nan gaba,ko bed bazai iya hadawa da ita ba, Umma ce ta katse Masa tunani tace Ina jinka Aabid, yace Umma Na yarda na karbi zabinki ko wace ma na Amince Allah ya bada zaman lfy na gode.
Umma ta washe Baki tace na gode Aabid Allah yayi maka Albarka Allah bayyana maka Babanka da Danginka,Ameen yace yana Dan guntun Murmushi,a hankali yace Umma to wace Matar? Madeena Yar Kano wannan Marainiya Yar Dan uwana,wacce take damunka da surutu idan Muka je gidansu, yarinyar Nan da kake cewa sai tayi maka tatsuniya,wacce kake biye mata kuyi ta labari, wani Dukul Aabid yaji wani mulmulen Abu ya soke Masa makoshi ya kasa hadiyar yawu.
Da kyar ya iya cewa Umma yanzu sai kikaga mun Dace da wannan abar kamar....kasa karasawa yayi yace ba komai Umma Allah yasa Haka shine mafi Alkhairi,Ameen Umma tace,ya tashi ya tafi Yana tsananin bacin Rai Kamar Wanda zai shiga wuta.

tun daga ranar ban sake Zuwa gidan Umma ba,Ko ta kirani sai nace zanzo ne naki zuwa har aka kwashe wata guda da rabi bikin Khairat saura sati Uku, Yayin da naga Dangin Umma da Dangin Abba da Mami sun wucewa Aabid gaba Ana ta shirye shiryen na Aabid, Nace Mami Wai Madeenan ta yarda Kuma zata auri Aabid din? Mami tace sosai ma kuwa an Gama komai Dangin Abbanku Dana Umma ne Suka wuce gaba,yanzu Haka an Gama Hada lefe baki gani ba akwati takwas yayi na gani na fada,rabi ma a Dubai ya hadosu.
Baki na tabe nace Kuma ya yarda Yana sonta? Ai shi Aabid yace matukar Umma ce ta zaba Masa Yana so,a fili nace doko wanda Bai San Yancin kansa ba,a Haka kamar Namiji ya Bari za ayi Masa auren Dole, Mari naji Umma ta kifeni dashi Wanda Bata taba yi Mana ba,Kunci na dafe na fashe da kuka,tace ke Ashe rashin hankalin naki kullum gaba yakeyi babban mutum kike zagi, dama na Dade ina taraki Umma tayi tayi kije kinki zuwa uban me tayi Miki duk Abinda take Miki bakya godewa,Aabid Zaki zaga mutumin da yake Miki dinki har Uniform ya siya Miki tashi ki bani waje wacce Bata San arziki ba, Mikewa nayi na tafi Dakin Inno Ina ta kuka,Khairat kuwa Ana ta gyarata Ana tsumata, Abba yace ya gaji da biki wannan ba wani kade Kade da party daurawa kawai za ayi akai Amarya,Nima anyi min dinkuna kala biyar.
An kawo lefen Khairat masu kyau da tsada akwati shida, sai na Aabid ma an Gama hadawa komai Amma ba a Kai ba Wai sai anyi bikin,bikin Aabid Dana Khairat Rana daya ne.

Bangaren Aabid kuwa Yana ta bakin ciki ya rame Baya son Auren Baya son koma wace matar ce saboda yace bazai je zance ba wlh,itama Umma ta kyaleshi tunda dai ya yarda da auren ya Gama Mata komai,Hamisu yana ta masa dariya sabo da yasan Madeenar Mummuna ce,Faruk da Fauzan tare da Sauran abokai ma sai tsokanarsa sukeyi za ayi Masa auren Dole, Ni kuwa tunda naji ance Mummuna ce Na dinga dariya Ina murna tuni na daina Jin wani haushi na shirya na tafi Gidan Umma.

Ina shiga na hango Aabid a zaune jikin Flowers yayi Tagumi Yana ta tunani,sanye nake cikin Lace riga da skert Ina nishadi na harda wakata Ina cewa: ke kikace kina so da Baki ce kina so ba da abaki shi ba.
Karasawa nayi Inda yake tare da rangada sallama nace Angon Madeena kasha kamshi,Alhaji Aabid na Anty Madeena,Kai kake da Madeena Baki daya,aje Dubai aje China,asha ruwan roba a karya Karin safe da kaza, me Sakwara da Miya na Anty Madeena Allah ya kawo Yara masu Albarka.
Yana cikin bacin Rai sai da Na sashi dariyar Dole kirarin da nake Masa, karya nayi nace ai Munje da Mami har Kano wajen Madeena,Aabid yace Dan Allah? Nace sosai ma,yace ta Kara kyau kuwa? Dariya nayi nace tab bazan maka karya ba Fatarta Kamar kalar kashin Shanu,wata koriya koriya, brown Haka,Black, Blacky dai kawai gata Nan, baki ya tabe kawai,nace Amma ance ta iya girki,Girkin banza shi zan ta ci cewar Aabid ya furta da masifa, na sheke da dariya nace kirjinta duk nankarwa(straight) wani layi layi yaja,Aabid ya yace naga ta kaina Amma in ba karya ba a Ina Kika hango nankarwa a kirjinta? Wanki Muka iske tana Yi tasa dinki show me your neck tsohon yayi Aiko riga ta zazzago nace sai na kalle maka komai, Muna zaune tayi wanka ta saka dinki shima tsohon yayi zura hannunka Masoyi, Muna cin Abinci ta daga Hannayenta sama tana Mika ai ko arm dinta Nankarwa tayi wani zirnaniya tabi ta zagaye wajen,Aabid ya rufe Ido Rai a bace yace na Mutu Kawai, na sake shekewa da dariya,yace to sai me Kuma ki gano min? Nace tace bacci takeji ta kwanta da Rana Ina kusa da ita a dakinta sai Munshari kwarrrrrr..Kamar Ana jan rago za a kaishi kasuwa yana kuka,daga Nan sai Yawun bacci malalala akan pillow, Aabid ya sake rumtse Ido yace Hijira zanyi wlh idan tazo gidan Nan, tana yin irin wannan shirmen gwara nayi Gabas, na dinga dariya harda rike ciki nace Gabas Ina kenan? Yace Niger can cikin Sahara yafiye min lafiya, Umma ta fito tana karkade carpet ta hango mu muna ta Hira Ina dariya, Aabid yace zauna Ga kujera ki Fede min labari daga biri har wutsiya naji idan an kawota ta Ina zan Fara daukan matakin Kare kaina.

Nace to Kai baka santa bane? Ya akayi ka bari aka caka maka? da kalar tausayi yace Umma ce ya zanyi? Ranar bikin Ana daurawa Zan tafiyata yawo a Gari nayi ta garari da motata,Dariya nayi nace Zan rakaka mu tafi muyi ta yawonmu, yace to Amma ki lallaba ki sake bin su Umma Kano ki gano min latest labari akan Madeena nace to Amma kudin Shan Lemo fa? Ya kamata ka biya ko lemo Nasha acan zanfi Jin Dadin samo labari, dake yana son jin labari ba musu ya zaro 3k ya bani gashi, na karbe Ina dariya nace Na gode Allah ya biya,Zaka Sha labari har ya aka yi aka haifeta sai na fada maka komai Bari naje wajen Umma.
Umma tana kallonmu ta saman bene Ashe Muna ta Hira Amma Bata San hirar me mukeyi ba tace Raudat yau kuma Hira ce Haka ta motsa dariya nayi na wuce ciki sai dare na tafi gida.

Bikin su Aabid saura sati daya duk wani shiri an Gama shi, Aabid part dinsa an canja komai sabo masu tsada, gaba Daya gidan an gyarashi an sake canja Masa fasali yayi mugun kyau, Khairat ma an Gama koma mun Gama komai,Ana gobe Daurin aure naje Saloon aka gyara min gashina tare da zuba min Lalle Kamar nice Amaryar, Danginmu suna ta min tsiya na zauna ruwan Ido waye waye,Ina jinsu na share su,bangaren su Madina ma Haka,washe Gari har Dangin Umma duk an cika makil a wajen Daurin auren Khairat,har Aabid Ango yaci uban wanka cikin sabuwar Shadda Fara tas,Suka zo da abokansa Ana jira a daura na Khairat a tafi na Aabid, sanarwa mukaji An Fara Daura Auren Aabid da Raudat Kan sadaki dubu Dari, daga baya Muka ji ance An daura na khairat da Sufyan sadaki dubu Dari Shima,Aabid Yana jira da abokai a Gama za a tafi nasa kawai yaji sabon rahoto a speaker, Nima Ina gida na rude Wanda kasa motsi nayi na Zama gunki,Aabid kuwa daga nan Bai kula kowa ba ya koma Gida a motarsa, cikin mutane ya Kira Umma suka kebe a bedroom yace Umma me ya faru Haka naji an daura da Raudat Kuma ba Madeena ba?

Umma tayi Murmushi tace Aabid bazan boye maka ba, Dangin uwar Madeena ne suke ta gutsiri tsoma a Kano ba a San asalinka ba Dangin miji mu zamu cuci yarsu su baza su yarda ba,sannan na duba naga kaima baka son madeena duk da cewar ita tana sonka Amma na hango za a samu matsala shi yasa tun wuri bikinku saura kwana Uku akai lefe na fasa naje na Basu Hakuri Suka dawo min da kudin auren nayi nayi su barshi Uwar Madeena tace Bata so har zagina tayi, abin ya fusata Ni shi yasa Kawai naje na tuntubi iyayen Raudat Suka Amince kawai aka daura da ita,Ina tabbatar maka itama Bata sani ba Amma iyayenta yau Dole zasu fada Mata komai.

Ajiyar zuciya Aabid ya sauke yace Na gode Umma Allah ya biyaki,a ransa kuwa tsaki yaja a rasa wacce za a bani sai wannan barauniyar, ai ko zata Zama Hoto a gidan ko yatsanta bazan rike ba,ta zauna iya side nata yarinya karama ba wani karatu me zurfi ya tafi abinsa kawai wajen su Faruk.

Kamar inda Umma tayiwa Aabid bayani Haka Nima su Mami Suka fayyace min komai Wanda Suka San waye Aabid Ana ta tayani Murna matuka, Ni kuwa na fashe da kuka an hadani da mugu nasan wlh wahala zansha kawai baya so na,Haka na yini a dakin Inno Ina kuka,Inno ta dakko Bulala ta koroni waje na dauki jakata nayi tafiyata gidan Aymana,tana gidanmu Amma nayiwa Hashim waya ya kawo min key ya koma kasuwa na bude bangaren Aymana na fada saman bed dinta Ina ta kuka na.
Da yamma Ana ta nemana za a Kai Amare ba a ganni ba, Hashim Wanda shima Yana daga cikin Yan daukan Amarya yace tana Gidana fa,Aiko su Inno Suka taho su Uku tsofaffi suna masifa.

Faruk Kuwa tuni kishi ya cikashi Aabid ya aureni,Nan take yaji ya tsani Aabid yace Inshaallah sai Aabid ya sakeni ya aureni, Fauzan yazo shima Daurin aure Yana Jin Haka yayi fushi da Aabid Wai ya munafunce shi,yasan Yana Sona zai Kara ta biyu Dani Amma yayi Masa Bakin ciki yaci Amanarsa,Kuma wlh sai iya inda karfinsa ya Kare Dole sai ya aureni ata biyu.
Hamisu Kam kwana biyu asirin da Hauwa tayi Masa ya sakeshi kaf, ya dinga bakin ciki ya rasa Dalilin da yasa a baya dare Daya yaji ya tsaneni,Bai San dalili ba,wani azabar Sona yake ji sabo dal, Yana so zai fadawa Umma kawai Kuma yace Bari sai ta Gama bikin Aabid kawai Kuma sai yaji an daura da Aabid, shima yace Aabid yaci Amanarsa munafiki shine ya rabashi da Ni,Dan Haka Wlh sai ya dauki fansa bazai Bari auren yaje ko Ina ba.

Inno tana shigowa gidan Aymana ta rufeni da duka ta ko ina, Ina ta ihu da kyar tsofaffin mutum biyu suka bawa Inno hakuri, a gidan Aymana tasa nayi wanka ta dakko min sabon wani lace me Masifar kyau Wai Umma ce ta dinka min, Ina ta Bata lokaci Ina shiri ga kuka Ina ta faman Yi Haka na fito ko gyale naki yafawa, Inno ta yafa min da kanta Muka tafi Ina ta cin uban kuka,Khairat aka Fara kaiwa,Ni Kuma Ina gaban Mami da Abba sun Gama Yi min Nasiha sannan motocin bangaren Aabid Suka zo da yawan gaske aka dauki Amarya da kawaye tare da Yan uwa,tsinke ba ayi min ba Aabid yace ya zuba komai baya bukata ya yafe, gidan kowa ya yaba musamman part Dina da aka kaini ansha kallon kyau, duk yan Kai Amarya an maida su,Rufaida aka bar min tana jiran mijinta zai zo ya dauketa,Yana zuwa tace to Raudat Ni zan tafi kiwa kanki gata kiyi biyayya Kinga dai halaccin Umma, duk abinda ya shige Miki duhu ki kiramu a waya mu tsofaffin hannu, banza nayi Mata, tayi dariya ta tsokaneni Idan Aabid ya shugo dan Allah a bude Masa cinyoyi ta cikin lumana Raudat, Dariya na kyalkyale da ita Dama tamu tazo Daya da Rufaida Muna shiri sosai bama boyewa juna komai,nace Kamar yanda Kika budewa naki kenan? Dariya Muka sake yi,tace Ashe kin Gane.

Ashe dai Aabid shine rabonki Abu kamar Wasa daga nace kije ki fada Masa Ina sonsa,nace hmm ai munyi kuruciya wlh,To Allah ya kyauta Ade kula da Tsafta Raudat ko Ina,jiki da cikin gida kin dai Gane a rikewa kamshi wuta,Allah ya kawo kazantar daki,nace tab zaku ga shuru ba ciki ba da,Dan ba son juna muke Yi ba,Kinga batun ciki Babu, dariya Rufaida tayi tace sanda zakuyi wa Zaki fadawa,uwar kurin banza, da Allah a kula da bawa kiss hakkinsa gashi an samu Jan lips,dariya Muka sake Yi,Aabid yazo shi kadai kamar Maye zai shigo room Dina ya Kira Rufaida yaji tace Raudat wannan Bed na Room din Aabid Hadadde Haka ai ko Bai niyya ba Dole ya fatattaka ki a Kai, dan Allah biyayya Raudat Banda kuruciya,ki Zama Babbar yarinya, ban gane me take nufi ba nace Babbar yarinya? Yo Allah Bai bani shekaru da yawa ba sai na jawo su na Zama Babba,Rufaida tace Kai Naga ta kaina,ki dai Zama mage kina makalewa a jikinsa kullum Yana kara kauna,ko yaushe idan Yana gida Kina jikinsa,Aabid Yana ji a ransa yace jikin ubawa zata hau sai dai wacce nake so, Ni Kuma nace mage? Ni Allah bazan taba Masa ko yatsa ba ai sai dai na Zama Kunama na cijeshi amma na wani kwanta Masa a jiki Haka kawai katuwa Dani Ina zai iya Dani ai na Masa girma ma.
Dariya Rufaida tayi tace Allah ya shiryeki Raudat na tafi,tana Fitowa Aabid ya turo kofa taja da baya yayi Murmushi yace yace dama kije Yana ta kiranki, Murmushi nayi nace to ga dai Amanar mu Nan Dan Allah a riketa, Inshaallah yace kawai ita Kuma ta tafi,shi Kuma ya shige room dinsa.



Karshen Free page kenan. Wanda Suka biya kudi za a Fara Baku ci gabansa.

Fans na gode na gode kwarai musamman masu Sharhi.







AsmaBaffa
[4/16, 9:53 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙








36-40






Official






By
AsmaBaffa





NA KUDI NE







page dinku ne

Jameela Abdullahi
Ummi Zaria
Phaaateeemah
Ummu Islam and
Queen Bella.








Aabid Yana zuwa Room dinsa wanka yayi kawai tare da Shirin bacci ya Sha tea yayi Kwanciyarsa Yana tunanin wannan aure har bacci ya kwashe shi.
Ni kuwa Jin Shuru nasan bazai kalleni ba bare yazo gareni,ga Yunwa Ina ji, Gefen bed Dina na duba Naga Kazar Maganin Mata da Aymana ta kawo min guda tasha Hadi da saiwoyi, Haka na zauna na ci iya yanda zan Iya na rufe Sauran.
Wanka nayi tare da Shirin bacci cikin Rigar bacci na Riga da wando 3qtr ban taba na lefe na ba,Fadeela ce ta siya min su kala biyar.
Kwanciya nayi Ina Tunanin ya rayuwa zata kasance tsakanina da Aabid Wanda baya so na Haka Nima ban damu dashi ba Yaya zamu Yi Haka bacci ya sace Ni.

Washe Gari da Asuba naji Ana kwankwasa min kofa, Mikewa nayi idona cike da bacci jikina duk gajiyar biki,Da kyar na bude Ina layi Kamar wata Yar Maye, Aabid na gani sanye da Jallabiyya zai tafi Masallaci, Kallo na yayi sama da kasa sannan Yace Sallah Hajiya, Idona na bude tar nace Ok, yayi wucewarsa fuska ba Rahma, Baki na tabe tare da shigewa Toilet.
Brush nayi tare da Daura Alwala sannan nayi Nafeela nayi Sallar Asuba tare da Azkhar sannan na mike na koma saman bed naci gaba da Bacci na, shima Aabid Bai dawo ba sai da Gari yayi haske sannan ya dawo tare da komawa bacci.

Misalin 10am na tashi ko wanka banyi ba na Fara shiga kitchen naga komai akwai na abinci Babu abinda Babu na rufin Asiri, doya da kwai na soya sannan Naga har gasashiyar kaza a fridge da gani Aabid ne ya siyo min girman Kai ya Hana ya bani, warming nata nayi na tafasa Tea yasha kayan hadin kamshi na ajiye a Dining sannan na hau gyara part din, Babu Dirty ko kadan Amma sanin halin Aabid yasa na Kara gyara ko Ina Yana kamshi,dakinsa ne kawai ban gyara ba,a hankali na lallaba tare da tura kofar naji Karar Ruwa a bayi,Da Sauri na gyara Masa room ya dawo neat dama dakinsa na gayu ne,Ina gamawa saura toilet tunda Yana ciki Dole na tafi dakina Nima nayi wanka tare da daura Alwala na Riga da na saba ko yaushe da Alwala a jikina.

Body lotion Dina na shafa me dadin kamshi,cikin kayan lefe na! na zabo wata atamfa peach and green dinkin riga da skert ne ya hadu sosai musamman Dana sa a jikina kayan sun amshi jikina sosai, gashi sun kamani, Zama nayi na tsara Yar kwalliyata sama sama,Ni bana wata kwalliya me yawa,jikina nabi da turare Kala uku yunwa tana cina na fito palo.
Ina taka steps har na karaso palonmu, na Iske Ango ansha sabon Kaya wani yadi light blue, ba karamin kyau yayi min ba,Sai da na Kare Masa kallo sannan na karaso inda yake na duka har kasa nace Barka da Asuba ka tashi lafiya? Kallo na yayi sosai yau yasan Lallai Ina da mahaukacin kyau,lfy na tsinci Muryarsa ya amsa,Your Food is Ready ...kafin na Karasa yace na sani ai,girki ba Dadi ba an damu mutum.

Ki kawo min na ji idan da dadi, Harararsa nayi kadan ta gefen Ido nace Dan Allah ga Dining kaci Mana a can? Na kafeshi da ido Ina bukatar amsarsa, Dan tsaki yaja kadan tare da Mikewa yace Muje, Ina gaba Yana bina a baya zuwa Dining side,Serving dinsa nayi na zuba Masa Har tea sannan na ajiye Masa komai a gabansa,Ni Kuma na Shiga kitchen na Hadawa Umma nata kayan kari,na leka ta window na Kira Almajirin dake Share compound, ya shigo tare da gaisheni nace ga Abincin Umma ka Mika Mata,ka dawo ka karbi naka, Dauka yayi a katon tire ya kaiwa Umma dake akwai Danginta mutum biyu Basu tafi ba ta Mika musu,tana cewa oh Raudat da kokari haka, Allah yayi Albarka dai.

Ina bawa Almajirin ya tafi Ni Kuma na bugawa Mami waya a Aiko min da gasarar Koko nasan akwai ma, Cikin lokaci kadan sai ga Wani Yaron layinmu an aikoshi da gasara a juck harda Kosai me zafi, ai kuwa na damawa kaina Koko, na Saba da shansa kullum a gidanmu idan ban Sha ba bana Jin Dadi.
Dining na zauna Nima muna Facing Juna Yana jina duk abinda nakeyi,yaga kuwa Na zauna na tsugawa Koko na sugar tare da juyawa da Spoon sannan ga Kosai na da yawa manya,Naci Kosaina na kora da Koko me zafi, Aabid Yana kallo na na cinye

Please Login or Register in order to submit comment