Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


COPY BY ZAINAB BUTALAWA

Official


By
AsmaBaffa




TA GYARU COMPLT NAIRA DARI UKU NE 300. GA MASU JIRANSA.

RASHIN SA'A COMPLT SHIMA DARI UKU 300 GA ME BUKATAR WANNAN NOVELS:

MASU SON TURA NUMBER KATIN WAYA MTN GA NUMBER DA ZAKU YI MIN MAGANA
08033933642.

MASU BUKATAR YIN TRANSFER KATIN WAYA KO VTU GA NUMBER DA ZAKU YI
09032409668.

MASU BUKATAR BIYA TA BANK GA ACCNT NUMBER DA ZAKU TURA KUDIN
2177560408, YAHAYA GARBA MUHAMMAD, ZENITH BANK.
YAN NIGER GA NUMBER DA ZAKU NEMA IDAN KUNA BUKATAR SIYE.
+227 90795939

INA MIKO GAISUWA GAREKU FANS DINA BAKI DAYA INA KUMA JINJINA.😂🥰🥰
[4/16, 9:20 PM] Sis Asma: 📙TA GYARU📙











1






FREE PAGE






Official










By
AsmaBaffa






NA KUDI NE

Kamar yanda kuka sani Allah yasa an Gama RASHIN SA'A lfy, ga masu bukatar Complete Rashin Sa'a Naira Dari Uku ne 300 ku min Magana ta pc ta wannan Number
0803 393 3642. Tnx.


NA KUDINE

TA GYARU na kudi ne Naira Dari biyu 200 ne ga masu bukata.

Ga masu son tura Number na katin MTN ta WhatsApp to ga Number
0803 393 3642.

Masu son siye ta Hanyar Transfer ko Vtu ga Number din da zaku iya turawa 09032409668

Masu son siye ta Hanyar Turawa ta bank ga Accnt Number 2177560408, Yahaya Garba Muhammad, Zenith bank.








BISMILLAH





Alhmdllh Muna godiya ga Allah da ya bamu Rai da Lafiya har ya sake bani ikon Rubuta sabon Novel Ta Gyaru.
Kamar yanda na Fara lafiya Dani daku Baki daya Fans Allah bamu ikon gamawa Lafiya.

Ina matukar Godiya da jinjina ga Fans Dina Wanda Allah ya Basu ikon siyen Novel Dina da Kuma Wanda ma Basu samu damar siye ba Ina godiya Ina kaunarku Baki daya.

Jinjina ga masu Sharhi har kullum kune a gaba mutanena,da Sa hannunku typing ke tafiya dai dai tnx alot.






Page kacokan na DIYAR KATIBI ne da FULATAH LUV.










Hamshakiyar Barauniya ce ni Raudat, Asalina Sunana
Raudat M. Usman
Babana Muhammad Usman Yan Asalin Adamawa ne,Fulanine usul, gaba daya danginmu Suna Yola cikin kauyen Fulani,Babana Malam Muhammadu shi kadai Iyayensa Suka Haifa,tun Yana Karami Allah ya karbi rayuwar Babansa Wanda yake da gida a Kaduna wannan gidan shi kadai ya Mallaka sai gonaki da sauran dababbobi na kauye, Malam Muhammadu ganin bashi da Wasu Yan Uwa na jini sosai ya tattara gadonsa kaf ya siyar sai gida daya ya Bari na Kaduna Wanda shine muke zaune a ciki har yanzu.
Da kudin gadonsa yayi aure ya Auri Salamatu Mahaifiyarmu kenan,Salamatu Yar larabawan Yemen ce Amma iyayenta Suka zauna a Niger Wanda Allah yayota Kamar Balarabiya har ma tafi wasu Larabawan kyau gashi da diriin sura,Danginta kaf suna Niger wasu Kuma suna Yemen.
Bayan ya Auri Salamatu Marainiya Bata da uwa Bata da Uba,sai dangi Marasa zuciya,Salamatu Mahaifiyarmu wacce muke cewa Mami ya daukota zuwa gidansa Daya rage na gado dake Rigasa Kaduna,gidane Karami tun irin na da Wanda ko a da gidaje namu gidane na talaka futuk, Mahaifiyarsa wacce take Kakarmu ta wajen Uba tal data rage Binta Muna ce Mata Inno, Abbanmu Malam Muhammadu ya dauko Uwarsa ta dawo Kaduna gidansa da Zama ya Bata daki Daya,Suna zaune Lafiya da Mami.
Malam Muhammadu karatun Muhammadiya yayi kawai,itama Mami Salamatu Na Muhammadiya tayi Amma tayi Primary ta boko.
Muhammadu Messenger ne a Office din Wani ma'aikaci a Ministry of Justice dake Garin Kaduna, yana daukan Albashi duk wata fiye da dubu ashirin.

Abinda yasa Muhammadu ya dakko Inno Babarsa Gidansa shine Zuciyar Muhammadu Matacciyace matuka,Yana samu dai dai gwargwado Amma baya godewa Allah, burinsa Roko da Maula gaba Daya ya zubarwa da yaransa Mutunci a Unguwa kaf,har samarin yayansa rokonsu yakeyi,Haka duk Wanda ke mutuntashi to sai ya je Maula gidansa,Salamatu Shuru Shuru ce Bata da zafi ko kadan shi yasa kowa abinda yaga dama yakeyi har yaranta,sai dai tace Bari ko ba kyau shike Nan.

Inno Kakarmu kuwa Itama sabo da son danta da jikokinta Bata iya musu fada ko kadan,sannan ita take Kara Goyawa danta Muhammadu Baya yake ci gaba da maula da roko gida gida.
Ita kanta Inno ta tsufa Amma Danta bashi da Imani ko kadan,baya tausaya Mata,maimakon ya dau nauyinta ya hutar da ita sai itace ke daukan Nauyinsa.

Gidajen Masu kudi Inno take zuwa duk tsufanta take musu aikin wahala iri iri Ana biyanta,Ana Bata ragowar Abinci da sauran jagwalgwalo, Yan kwancen sutura ta kawowa Muhammadu da yaransa,komai ta samu shi Danta ko jikokinta,Itace ta kaita da yawon Maula itama tana daukan Raudat da tafi kowa kyau a gidan sai ta daukeni muyi ta zaga unguwa unguwa gidajen manyan Yan Siyasa,.
Tun ban Saba ba Har na Saba na koma kasurgumar Barauniya,yayin da idan nayi wata satar sai mutum yace Aljanune sabo da tsabar kwarewa ta,Babanmu ba ruwansa da Ina na samo zai karbe,Mami kuwa sai dai ta kalleni ta girgiza Kai tace Ki Bari ba kyau shike Nan fadan.

Yayyena Mata da kanwata Mace gaba dayanmu Allah ya zuba Mana Iyayin tsiya ka rantse yaran shugaban kasa ne,nice Raudat kadai sabo da salon sata da Maula na nemi yanga ta da iyayi na rasa, Halin Mahaifinmu yasa gaba Daya samari Suka gujemu,aka tsanemu, bamu Dame son mu bare ya aura.

Malam Muhammadu Da Salamatu yaransu Biyar gaba Daya mata Kuma duk manya ne mu ba Yara,Sabo da matacciyar zuciyar Abba yace Dole sai Mami tayi tsarin iyali ta daina Haihuwa Dole sabo da ya gaji da Haihuwa nauyi zaiyi Masa yawa musamman gamu mata.
Aymana 25yrs itace ta farko, ta gama secondary da kyar Inno ce ta biya mata kudin schl har ta Gama Abba cewa yayi bazai iya ba,Aymana tayi sana'a kala kala Amma Abba ya cinye kudin hakan yasa ta daina gaba Daya Babu jari ta zauna a gida ba makaranta ba aure sai kayan iyayi da yanga sabo da gaskiya Allah ya zuba Mana kyau gaba dayanmu musamman Ni Raudat uwar kuri.

Daga Ayamana Sai Fadeela 23yrs itama Inno ce ta tsaya Mata tayi iya Secondary da Islamiyya tana Nan itama a gida a zube sai dai mukan Dan leka Islamiyya jefi jefi, itama tayi sana'a daban daban Abba ya Lashe kudin.
Sai Khairat 20yrs itama an Gama schl iri Daya dai da yayyenta Sai dai ita akwai cin kudin samari tana yaudararsu idan ta samu, sai Ni Raudat 18yrs Nima kwana Nan na Gama secondary schl da kyar Inno ta biya sai da aka tsallake min Shekara Guda ma sannan tayi min komai har na zana exam na Gama,sai dai Ni Halina Ya banbanta, Sata tasa bana yanga bana komai sai gantalin tsiya, Amma Abba duk yafi Sona sabo da Samo kudi da abinci harda sutura,duk gidanmu kowa yasan sata nakeyi don a gidanma in dai Zan ga Dan sabulu wuf Zan dauke Amma bana satar kudi a gida,Amma Abinci,sabulu,man shafawa etc Zan daukesu kuwa.

Daga Ni sai Autar mu ta biyar Rufaida 15yrs tana Ss1 itace kanwarmu last itama ta girma sai Jarabar cin tsiya sabo da Haka Abba yafi tsanarta Sabo da Wai tana cinye Masa abincin gida.
Dukkanmu Allah ya zuba Mana basira da kokari a aji Kamar Ana Bude Kwakwalwarmu Ana zuba Mana.
Mun Dade Muna tunanin me Abbanmu yakeyi da kudi baya iya tsinana Mana komai sai daga baya Muka gano Ashe gidan rawa da kallon Hawan Bori a kauyuka,sai Gidan kallon Dambe acan yake Karar da kudinsa acan yake zuwa ya dinga Lika musu kudi,idan ya Tara kudin sai ya tafi can ya kadarsu a banza.

A Haka Muna mutuntashi Muna bashi mutuncinsa na Uba,nice kadai ma nake Fitowa na fada Masa gaskiya ba ruwana sabo da ba wata kunya gareni ba.
Kadan kenan Daga cikin Tarihinmu gaba zaku ci gaba da ji.
Ni Raudat Fara ce Kamar yanda duk Yan gidanmu suke har Abbanmu da Inno zuwa Mami kaf dinmu.

Amma Ni ta daban ce Allah ne yayi Ni Haka,duk yanda kuka san me kyau wacce ta Dace a buga a labarai to na kai, kyan diri da sura abin sai Wanda ya gani, gani da gashi ya Kai tsakiyar bayana Baki wuluk me santsi ko kitso ba a iya Yi min,gaban goshina Kananan gashi ya kwanto masu santsi,da Dan sajena zuwa kunne na,Hancina bai fiye tsayi ba sannan ba gajere ba,ga Dan bakina Karami da lips Dina jajir dasu,idona Dara Dara Normal farare tas,gani da Round face, Boobs Dina Manya Kuma ba can ba normal tsaye sosai,Haka ga Hips da tarin tuwon Mazaunai.
Skin Dina ka rantse bana wahala,ka rantse cikin daula nake ku hango Ni masu karatu.


Aabid Hamshakin Matashi ne me ji da baiwar kyau,ga aji,zafin zuciya,Baya dariya ko kadan,baya mu'amula da kowa sai wani abokinsa Daya tal Faruk, Aabid akwai Jarabar gadara takama da Isa ga mulki Kamar basarake,kaf Unguwarmu Babu kalarsa, me kyansa kuwa sai dai ko a kasar waje Maybe a samu,Yana da addini,ga ilmin Boko yayi nisa a karatunsa na Degree dinsa a A.b.u Zaria.
Skin dinsa kamar ta Halfcast ruwa biyu,sumarsa ma Haka take,gashi Dan gayu ya Tara uwar Suma me matukar Baki da santsi ga Dan saje kadan da gemu dai dai,Dan gayu ne na gaske, ga uwar Tsafta kullum cikin wanka yake da kayansa tas Yana uban kamshi me dadi.
wani irin hancine dashi me azabar kyau, lips dinsa da Bakinsa karami Kamar na kyawawan Mata, fuskarsa shafe dinta round kadan sannan tsayi kadan,kana ganinsa kaga Namijin Daya amsa sunansa, tsayinsa baiyi yawa ba Kuma ba gajere ba,gashi ba me kiba ba ba siriri ba,duk wanda ya ganshi zai ce Dan kasar waje ne ko ruwa biyu ne.
Duk Wanda ya ganshi sai ya jinjina kyansa da kyan surarsa ga Uwa uba Mulkinsa da nuna Isa.

Kaf schl dinsu an San da zamansa,Yan Mata suyi ta rubibinsa har so suke ko magana yayi sabo da yanda yake da murya me Zaki da Dadi
Baya son raini akwai son girma Bai son raini ko kadan.
Duk wannan abin Aabid Talakawa ne ko ace a gidan talauci ake rikonsa Bai San iyayensa ba Bai San danginsa ba bare garinsu Bai San komai akansa ba yasan dai labarin tsintarsa.

Marikiyar Aabid Rahinatu Dattijuwa ce ta kirki me Hankali da ilmi ga nutsuwa tayi aure da yawa Amma Bata Dace da Mazaje ba, Allah Bai Bata Haihuwa ba sai mijinta na farko data aura a can Gombe inda Ta Haifi Danta Hamisu,Bayan sun rabu da mijinta ta tafi da danta,har kotu ya kaita akan ta bashi dansa Amma kotu tace a barwa Uwa danta.
Haka ta Raini Hamisu inda itama macece me nema Bata Zama, sana'a iri iri manya sabo da cikin danginta dake Kano suna Bata jari me yawa, Haka ta Raini danta har ya samu yayi Diploma a Polytechnic Zaria ya Samu aiki a wata Primary ta Gomnati yayi aure a Kaduna da Matarsa Hauwau da dansa Daya,a Haka Kuma Yana da zuciya yanzu da abinda yake samu da Kuma wasu buga buga yake ciyar da iyalinsa da Mahaifiyarsa, Yana kokarin sosai,itama Kuma Rahinatu tana nemanta taimakekiya sukeyiwa juna da danta dake can Unguwar shanu a can ya Kama haya da iyalansa.itama Rahinatu Umma tana gidanta a Rigasa Unguwarmu Daya ni Raudat.

Watarana Hamisu Yana Shekara goma Rahinatu taje Kano Wajen Yan Uwanta tana hanyarta ta dawowa Kaduna sun bar Kano kadan,Tana Zaria road cikin Motar Haya Wata Mota karama ta Haya Gulf ta shigo da uban gudu ta daki tasu Wanda Allah ya kiyayesu su basuyi Hatsari ba,ita kuwa Gulf din gefe ta tuntsira tare da fadawa cikin gonaki da mutanen cikin Motar baki daya,motarsu da sauri tayi gefe ta Tsaya nesa da Gulf,ita kuwa hayaki ya turnuke zata Kama da wuta,mutane da gudu Suka je wajen ko za a iya taimakon wasu Amma abin yaci tura, Cikin Yan ceton Rahinatu ita kadai ce mace,Da Sauri wata zukekiyar Mace wacce baza ta wuce 26yrs ba ta Miko Mata wani jariri da kyar aka fasa window aka karba da sauri Hayaki ya turnuke,Dattijuyar tace Sunana Raudat wannan Dana ne watansa hudu da haihuwa sunansa Aabid,Sunan Babansa Mahmoud.....duk Wuta ta Kama motar Baki daya ba a samu an ceci ko mutum Daya ba Ana ji Ana gani Suka kone kurmus ba yanda aka iya,ba Wanda baiyi kuka ba a wajen nan.
Haka Rahinatu ta karbi Kyakyawan danta Aabid ta sanarwa danginta da Danta Hamisu tare da Yan Uwa da abokan arziki.

Da Madara ta shayar da Aabid har ya girma a hannunta,tana matukar kaunarsa fiye da danta ma data Haifa,komai ta samu nasa ne tun Yana yaro har ya girma lokacin Hamisu ya girma shi sosai,ganin irin Son da Rahinatu take nunawa Aabid kuma yasan ba ita ta haifeshi ba ya jawo ya tsani Aabid matuka,ji yake kamar ya kasheshi har ya girma,ya Gama schl har yanzu da yayi aure baya kaunar Aabid,Haka Matarsa ma Hauwau ta tsani Aabid sabo da mijinta Bai sonsa, Aabid yasan komai tun Yana yaro irin yanda Hamisu ke dukansa Yana kwace Masa abubuwansa,Yana zaginsa Yana fada Masa Dan shege ne Dan tsontuwa tun Bai gane ba har ya girma ya gane ya tambayi Umma Bata boye Masa ba ta fada Masa komai yanda ta sameshi,kasancewar Bai taso da iyayensa ba Yana so ya ga ubansa Amma yasan da kyar ne kawai ya fawwalawa Allah kawai ya hakura,Dangin Umma sun isheshi tunda suna sonsa,Hamisu kuwa har yanzu kiyayya yake nuna Masa ta gasken gaske.
Aabid Mahmoud yake ko a schl tunda yasan sunan Babansa.

Abokin Aabid shine Faruk Dan gidan me kudi ne na gaske Faruk Babansa ya rike mukamai da dama na siyasa sannan yanzu Ambassador ne England.
Faruk tun suna Yara suke haduwa a filin ball suna buga Ball irin na Yara, Faruk da Aabid Haka kawai Allah ya hada Jininsu,Faruk Yana Masifar kaunar Aabid, Duk da Halayen Aabid Amma Faruk ba ruwansa dama shi Baya nuna Dan me kudi ne,ba ruwansa me hankali da nutsuwa sai dai Faruk yana da Surutu kadan da fara'a ga kula Matan tsiya iri iri Wanda Aabid ba Haka yake ba shi Sam.
Ko kallon Mata bayayi ba abinda ya shafeshi dasu, Faruk a turai yayi University ya Gama da wuri dake Bai samu wata matsala ba,yanzu Yana aiki Babba na masu kudi a Abuja,idan yazo Gari to Yana wajen Aabid,Aabid ma Yana zuwa wajensa a Abuja jefi jefi sannan Yana zuwa Wajen Iyayensa a Kaduna Yana gaida su, Faruk shike taimakawa Faruk da kudin karatunsa kaf shi yake daukan Nauyinsa ma komai, kasancewar tunda ya Gama secondary sai da ya zauna Shekara Uku Bai Shiga wata schl ba sabo da Umma Bata da kudi shi Kuma Hamisu dama ya tsani Aabid ko Abinci Dan dole yake kaiwa sabo da uwarsa Amma Bai so ko kayansa Farhan ya taba bare yaci abincin da ya siya da kudinsa ya kaiwa uwarsa,Umma tayi fadan tayi fadan da Nasiha har ta gaji Hamisu yaki canjawa,gashi gaba da yakeyi da Aabid.

Aabid Yana gudun Kayan wani ba ruwansa da kayan mutum Shi yasa ko Faruk Dole ce tasa ya hakura yake biya Masa kudin schl inda yake karanta Electrical Engineering, shi yasa ya nemi sana'a sabo da Allah ya bashi baiwar basira musamman akan gyaran wuta da gyaran su Tv,radio,computer, etc.hakan yasa yake Sana'arsa a wani shagon christain Alex suna aikinsu lafiya Yana biyansa da tsoka kuma sabo da Aabid akwai kwarjini karyarka ka rainashi sai ya takaka baruwansa kadan yake jira yaci mutuncin mutum,Kirar me kudi ce dashi,Yana zuwa schl yaje Kuma aikinsa kusa da gidansu.
Gidansu ma fitilar da suke Haska gidansu idan ba Nepa wani Wiring ya hada ta ko Ina kitchen,toilet,tsakar gida,dakin Umma,dakinsa etc ko Ina ya zaga sai ka rantse Nepa ce a gidansu, Haka speakers ya hada a gidan yayi wiring Toilet kitchen da dakinsa Umma tace Bata son Jarabar kidan da watarana yake kunnawa na turawa suna damunta Bata so a dakinta shi yaji abinsa shi kadai,indai Yana nishadi zaka ji ya kunna Amma duk gidansu ya dauki kida har toilet Yana ji kawai,gashi latest yake Downloading a wayarsa Me kyau da Faruk ya kawo Masa sabuwa daga Turai,sutura ma da yawa Faruk ke dinka musu har kana Nan Kaya sai ka ganshi Kamar Dan me kudi Yana sa Kaya Maya Mayan gaske na Alfarma,shi yasa ake zaton ko Danginsa masu kudi ne,ga kyau ga iya gayu komai yasa kyau yake Masa.
Yan Mata suyi ta turuwar zuwa inda yake aiki suna kallonsa kawai suna Jin Dadi Amma shi ko kallo Basu ishe shi ba.
Matan banza sunsha nemansa harda masu kudi Amma ba ruwansa.
Yasan gidan su Raudat farin sani yasan Kuma halin Iyayensu kaf da komai nasu Yana Jin labari wajen masu gulma Amma Raudat ce ba Wanda yasan tana sata,sabo da ita Bata yanga shi yasa ake mugun yabonta a ko Ina Ana ai duk tafi su kyau Amma itace ta kirki,ba iyayi ba yanga ga tarbiya,gata da Mutunta mutane tayi ta gaida mutane,Aabid kullum ya fita sai yaji yanda ake yabon halayen Raudat har ya gaji da ji, shi bai ma Santa ba yasan dai Yan gidansu musamman Khairat sabo da son Aabid da takeyi sai tayi ta kawo Masa gyaran wata tsohuwar radio karama wacce kusan kullum sai ta kawo gyaranta Dan kawai ta kalli Aabid gashi ta kasa fada Masa tana sonsa,baza ta iya ba yanda yake da kwarjini.
Aabid Yana tuna Uwarsa ta rasu wajen Hatsari hankalinsa Yana tashi musamman idan ya tuna Ina zai ga ubansa wannan shike damunsa idan ya tuna Yana hanashi walwala.
Wannan kenan kadan daga Aabid.


Yanzu Za a Fara Typing din ku biyo Ni.

Yayata ta Uku Khairat itace ta kwala min Kira Raudat zo,da sauri na fita tsakar gida wajenta sabo da Allah ya zuba min Fitsara wata Rana, Hannu biyu na cusa a cikin aljihun dogon wandona Na gwanjo Jean pencil black nace Khairat gani ya akayi ne? Yawwa Raudat naga duk gidan Nan kece tsagera Dan Allah muje ki rakani wajen Aabid me gyaran Radio ki fada Masa Ina sonsa kin gane,Dariya nayi kawai nace Wai Aabid suna ko Dadi Babu Kamar Abida mace Allah kiyaye yanzu Haka wani garan ne kike so muje Ni na fada Masa shi din banza.

Hijab na dauko wankakke sabo da muna da Tsafta matuka a gidanmu na talakawa futuk Amma sai Tsafta, itama Khairat Hijab tasa ta fito tana yanga Da iyayi Wanda ni dariya suke bani, Fada na Fara Mata Kamar nice yayarta nace Khairat wlh ku daina Iyayin Nan Abba ya Gama zubar Mana da mutunci Kuna wani Bata lokacinku duk unguwar Nan kin sani kowa ya San komai namu Amma Kuna wani yanga,Zagina Khairat tayi na kyaleta kuwa naci gaba da gaisawa da mutanen Dana sani harda Wanda ban sani ba gaida su nake sabo da Ina so Lallai sai an Soni an yarda Dani Ana yabona.
Nima badan Allah nake mutuncin ba,Shagon Alex Muka shiga da Sallama, zuciyata ce ta buga ta sake bada bugu dam dam har sau uku ganin Aabid da nayi, Ni dai iya sanina ban taba ganin me kyau kamarsa ba ko a film din turawa,ga kwarjini,ga iya wanka Kaya masu tsada latest, wani kamshinsa na Shaka Wanda sai da na lumshe Ido ni Raudat.
Firgit na dawo Hayyacina na Kara komawa baya na buya a bakin kofar Ina leka Ido daya Ina kallonsa tuni zuciyata ta Gaya min wannan me kudi ne Dole Zan lallaba na dankara Masa sata,Yanzu na manta da wata Khairat ma tunani na Lula yanda Zan saci rabona a jikinsa na kashe gararin gaba na, lekawa nakeyi da Ido daya sai na dawo baya da sauri na tuntsire da dariyar mugunta a hankali Dan Kar a jini,Nan take Basira ta Fado min lokacin Khairat sai Hararata takeyi tana min Inkiya nayiwa Aabid magana,Ni kuwa ta sata ta nakeyi, a hankali na yiwa Alex magana Da turanci Ina son Azo a hada min Wasu speakers a gidanmu basa kida sosai,Alex kuwa yace Aabid ka san gidansu? Dan sarkin mulki da kyar ya daga Kai ko kallonmu baiyi ba,Baki na tabe a hankali na Furta zaka ci Ubanka ba Aabid kake ba ko Abida kake zaka San wace Raudat.

Oga ne yasa Aabid akan yabi mu gida ya mana aikin,ransa ya baci Amma Haka ya hadiye tare da Mikewa locakinsa

Please Login or Register in order to submit comment