Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Karami a hannunsa Yana goge jikinsa Alama daga wanka ya fito,Husna surarsa ta tafi da ita ta manta me ya kawota,Harara ya watsa Mata tare da cewa Mene kike kallo na? Ahm...ah...Uhm...na Gama wankewa Amma na kasa kamo igiyar tsayina Bai Kai ba.

Basu fita ba ki koma kiyi ta wanke su har sanda zanzo nace Sunyi,Allah sarki Husna sabo da ance ta Zama me biyayya duk abinda miji yace to tayi, Yi nayi Bari na Bari,Komawa tayi wajen wankin cikin katon botiki ta kalli kayan tare da cewa ba komai ai Yafendo tace Yi nayi Bari na Bari, dawowa tayi Kamar yanda yace Haka take tayi ba ji ba gani har yatsunta Suka Fara fashewa Amma Bata daina ba Kamar Yana wajen Haka take ta tayi.

Shi kuwa tunda ta fita ya kalleta ba karya yasan tayi kyau kayan sun amsheta, sai da ya gama kallon News har yayi bacci ya farka tare da duba agogo yaga karfe dayan dare,mugunta ya shiryawa Husna ya tabbatar yanzu ta gaji tayi bacci zai tuhumeta a Kan wankin Daya sata,Bedroom dinta ya shiga ya iske ba kowa ciki,Motsi yaji kamar a toilet ya bude kofar da mamakinsa sai yaga Husna Tana gyangyandi a zaune tana wankin Kuma,mamaki ya kamashi yace ke uban me kikeyi bakiyi bacci ba? Idonta cike da bacci ta Dago da kanta cike da Shagwaba tace ba Kaine kace nayi ta wankewa ba sai kace yayi da kanka,Haushi ma ta bashi yace Ke nifa ba Umma bane da zakiyi min Shagwaba, Nima ita nake yiwa tawa kije can kiyi Mata ita zata kulaki.
Kayan ta Karasa daurayewa Yana Shan kallonta tace ya Isa Haka? Mamaki ta bashi dama tana da hankali Haka? a fili yace Yeah,Mikewa tayi tsaye ya kalleta sama da kasa ta bar toilet din tana cewa sai kace wani sadakin kirki ka biyani,kamarka me kudi Haka Amma Dubu dari kacal ka biya sadaki na Kamar za a siyi ragon Hakikar suna Amma shine harda sani wanki duk hannayensa sun fashe.

Farhan Bai San sanda yace Iyyee na fasa Jin tausayinki sai kin kwana a zaune yau tunda baki San arziki ba,a ransa yace har Ina yabonta Ashe ba Hankali,Toilet ya Kara sata ta koma taci gaba da wankewa daga inda ta tsaya,yace in Banda Ni wa zai biya sadakinki dubu dari,kinyi tsada da yawa dubu goma, me Zaki tsinana min? Kwaila kawai sai na fadawa Umma abinda Kika ce,yanda yace sai na fadawa Umma shi ya bawa Husna dariya Kamar wani yaro, Kallonta yayi tana ta dariya tana wankin Kuma, tunda na sanki kike sani magana Ina Ciwon kai,ki daina kulani mayya ya fice Daga room din Fuuuu,Yana tafiya ta wanke hannunta tare da fadawa saman Bed sai bacci yayi awon gaba da ita.
Shi kuwa da haushin Husna yayi bacci.

Salma tunda ta samu labarin an Kai Amarya Abuja hankalinta ya Kara tashi,zuciyarta ta shiga kunci,waya kawai Sukeyi ita da Asiya yanda zasu sa Farhan Kar ya so Husna,Yaya zasuyi su nakasa ta shine burinsu,kamar Kullum yau ma Haka Salma ta Kira Asiya,bugu Daya ta daga.. Hello ya akayi kawata? Hmm ke nifa na gaji da wannan biyayyar naga Alama Tsohon Nan bazai barni naje Abujan ba,Zan sato jiki Next week Saturday so kawai mu tafi Abuja Driver din gidanku sai kawai ya kaimu ba tare da Baba ya gane ba,iyakaci na kirkiro karya na fada Masa,Dariya Asiya tayi tace Allah ya kaimu sai muje ai,gyaran Muryar Baffa tajiyo da sauri ta katse wayar tare da furta Zan kiraki a dare kit ta kashe wayarta.

Washe Gari da Asuba Husna ta Saba da tashin Asuba,Maganar Umma ce ta Fado Mata ita ce zata dinga tashinsa a bacci da Asuba,Da Sauri ta Shiga Toilet tare da yin Brush da Alwala ta fito ,Hijab ta saka sannan ta fita zuwa dakin Farhan, lullube cikin bargo ta hangoshi Yana baccinsa cike da nutsuwa Husna ta tsaya a kansa ta rasa ta ya zata tasheshi ma, wayarta ta kunna tare da kunna wani Ringtone me Kara taje dai dai saitin kunnensa ta Kara Masa wayar, a firgice ya tashi zaune Yana Salati,Ganin Husna ce ransa ya baci ba Haka Ummansa ke tashinsa a bacci ba,da lallashi take tashinsa,Husna tana ganin fuskarsa ta canja ta gudu dakinta,Tsaki yaja tare da Mikewa ya Shiga Toilet shima Alwala yayi ya wuce masallaci,Umma ta ganshi ta window ya tafi masallaci taji Dadi a ranta Husna tayi abinda ta sata.

Husna sai da gari yayi haske sannan ta koma bacci bayan ta Gama addu'o'inta, 8:30am ta tashi daga baccinta, kitchen ta Shiga Babu abinda Babu na Kayan sarrafa Abinci, tunani ta Lula wanne girki zatayi a cikin Wanda ta iya,Jullof din Taliya tayi Tasha Kifi dama ta iya Jullof, a plate ta juyeta iya cikinta,a kujerar dake kitchen din ta zauna tana ci da hannunta,ga zafi da kyar take ebowa da hannunta,tana ci tana Jan yaji shiiiii, Farhan ne ya shigo kitchen Sanye yake cikin kayan Exercise dinsa farare tas, Wandon iya cinya da Alama daga dakin Jim dinsa yake, Bai San da Mutum ba sai da ya shigo ya Iske Husna tana ta kokawa da Taliya me zafi,gefe Kuma ga Madara peak Nan ta ruwa,maimakon ta hada tea ai Husna tsabar Jin Dadi da ganin Wadata madarar ta fasa da wuka tana kwankwada tana cin taliyarta, ganin Farhan yasa taji kunya ko dankwali Babu a kanta,gashi ya rudata da surarsa a waje ya wani sa guntun kaya,kanta ta sadda kasa tare da Furta Ina kwana? Kansa ya dauke bai ko amsa ba ya bude Fridge ya dauki Drink ya fita abinsa.
Sai lokacin Husna ta shaki dogon numfashi.

Tana kitchen din Yan aiki suka shugo Suka Fara gyara part din lungu da sako Banda Dakin Husna Dana Farhan,sabo da Haka Husna ta Fara Shiga dakinta ta gyarashi sosai tare da toilet din ya dauki Kamshi.
Lokacin data shiga dakin Farhan Yana wanka har ta Gama gyara Masa room din,Yana Fitowa ita kuma a firgice ta shige Toilet dinsa ta wanke Neat Yana kyalli,Farhan ya yaba gyaran nata,Bai zaci tana da Tsafta haka ba sai gashi gyaran nata har yafi na Yan aiki kyau,tana gamawa ta fice fitt Yana kallonta duk tsoronsa take ji.

Wanka ta sheka tazo ta shafa Mai Kamar yanda Umma ta koya mata,sannan tasa bra da sauran Inner, akwatin lace ta bude tare da dakko wani dankareren Lace Maroon and Green color doguwar Riga me dogon hannu,sama ya matse kasa ya bude,Powder ta shafa sama sama tare da Sa lipgloss,ta fesa turarukanta Kamar yanda Umma ta koya Mata sai gashi ta fito fess da ita Yar birni,kallon kanta tayi a mudubi tace na Dade Ina cutar kaina,Wai Yar wannan kwalliyar na kasa koya tun tuni, ba komai Yanzu na Fara ganewa, Fitowa tayi tana bin steps zata sauka kasa shi Kuma Farhan ya hauro zai je Bedroom suka ci Karo da juna,sanye yake cikin fitted Jallabiya Coffee color tayi Masa kyau sosai Yana bulbula kamshin dake ruda Husna,Ido ta zuba Masa tana kallonsa sabo da Masifar kyansa,Bata sani ba tayi missing Step daya,da karfi ta Fado rigif sai kirjin Farhan,wani Abu yaji ya zaga jininsa Yana Masa yawo Wanda Bai taba ji ba a game da jikin mace,Husna ma hakan taji a jikinta,jikinta ya mutu murus yayi sanyi,ga wani Niima da take ji Yana ratsa jikinta, Jikin Farhan wani laushi ga kamshinsa me kashe jikin ya mace,wata duniyar ta Lula ta lumshe Ido Nan take bacci ya kwasheta sabo da Niimar data ji a jikin Farhan, Shuru yajita Bata tasar Masa a jikinsa ba, tunaninsa ya dawo jikinsa,ke tasar min a jikina ya furta,Shuru yaji ba amsa da sauri ya tureta a jikinsa ta farka daga baccin Daya sace ta,tsaki yaja ya tureta da karfi ta bige kanta da jikin Karfen steps din.

Kara ta saki kadan tana Sosa wajen,tuni ya shige bedroom Yana huci tare da mako kofar kamar zai ballata,Allah ya saka min Husna ta furta sannan ta yafa gyalenta ta wuce part din Umma,Umma ta wuce Office tuni sai masu aiki kawai,a waya Husna ta Kira Umma Suka gaisa tace Umma Ina part dinki bakya Nan sai yaushe Zaki dawo? 5pm Zan dawo Husna,ki duba kitchen nasa a shirya muku Breakfast ki dauka ki bawa Farhan yaci,idan Baki bashi ba zai iya yini Bai ci komai ba,pls ki lallaba shi yaci Husna kinji? To Umma Husna ta furta,Bayan ta kashe wayar tace ya zanyi Umma tana son Dan Nan nata sai sani takeyi Ina kula shi gashi Nan sai wulakantani yakeyi.

Tana fadar Haka ta wuce kitchen tare da Dauko Abincin a basket me kyau ta wuce part dinsu.
A main Palo ta iskeshi ya zauna saman 3seater tare da daura kafarsa saman center table ya harde Yana kallon Ball a tv.
Da sallama Husna ta shigo Palon a hankali ya amsa idan baka kula bama baza kace ya amsa ba,a gabansa ta ajiye Masa abincin tare da Durkusawa a gabansa tace ga abincinka, kallonta yayi sai ta bashi mamaki data yi Hankalin kawo Masa abinci,shi a tunaninsa yanda ya ganta ba nutsuwa gata yarinya baiyi zaton zata iya komai ba Daya shafi kula da Miji.

Ba tare daya kalleta yace Serve me,Husna Bata gane ba tace Na'am me kake nufi? Tsaki yaja da karfi irin tana takura Masa yace ki zuba min nace,tsoronsa Husna takeji yanda taga Yana da Saurin Jin haushi,bude Flasks din tayi Daya bayan daya,kamshi ya daki hancinta,farfesun Kayan ciki,Chips and egg,Fried bread and cheese,sai ruwan zafi a flask yasha hadin Kayan kamshi, Husna Bata San me zata zuba Masa ba tace me zaka ci na zuba maka? Tsaki yaja Wanda Husna ta Kara Jin tsoronsa,da kyar ya nuna Mata chips and egg da tea, Duk kamshinsa ya hanata sakewa yana sa mata kasala a jikinta,Hannunta na rawa ta zuba Masa komai yanda ya Dace, Ketchup ya zuba a gefe da kansa sannan ya shiga ci a hankali.

Kadan yaci yasha tea,da matukar gadara yace kwashe tarkacen Nan daga gabana,Husna dake can kujerarta a Zaune ta mike da sauri ta kalli plate din tace har ka koshi? Dan kadanfa kaci Dan Allah kaci da yawa,Cikinki ko nawa? Bana son fa shishigi ki shiga hankalinki Tam cewar Farhan, Allah ya baka Hakuri gyara kayanka baya Zama sauke mu raba Husna ta furta tana kunkuni dama Ni ai ba niyyar kaina bace da Zan damu kaci da yawa Umma ce ta sani.yaji abinda tace Sarai Amma sai yace Me kike cewa? cewa fa nayi tunda ka koshi Bari Ni na cinye sauran,Harararta yayi ita Kuma ta kwashe komai ta koma kujerarta taci duk abinda taga dama sannan ta bawa masu aiki sauran ko akwai masu ci,wata a cikin masu aiki Gambo ta karba da murna,Husna tace idan kun cinye ki Kai part din Umma gaba Daya kwanikan, Gambo ta amsa da to ta fice.

Bayan kwana Uku da kawo Husna zamansu da Farhan Babu Dadi,Umma ta dakkowa Husna me Mata lesson Chinaza akan English Saturday Sunday,Chinaza Igbo ce Amma tana Jin Hausa ba laifi, ta sata a secondary schl private me tsadar gaske,makarantar hade take da Boko da Arabic, da Yamma Kuma ta sata a makarantar koyon girki da kwalliya tare da koyon yanda ake kula da me gida,itama makarantar kudi ce me tsada Husna ta Fara zuwa Babu Hutu ko kadan,Haka tana dawowa gida Umma tana koya Mata Assignment da sauran Abubuwa,gashi tana Masifar jin kunyar Umma,Bata son Umma taga laifinta ko kadan wannan dalilin yasa ta dage sosai taba da himma tana koyon duk abinda aka koya Mata,gashi tana Jin kunyar Farhan ace Bata iya komai ba,mutane duk sun rainata Ana wulakantata shi yasa ta dage itama tana so ta Faso Gari.
Gashi yanzu tana kula kawaye Yan Mata ba irin da ba.

A gurguje Husna ta fito cikin shirinta na Arabian Gown Dark blue tayi Rolling ba karamin kyau tayi ba,makarantar koyon Girki zata tafi, ta garden ta fito da sauri,Farhan Yana zaune a kujera Yana Hutawa, Dan bakin ciki irin na Farhan yaga Wai Bata aikin gida yanzu sai dai makaranta tsawa ya daka Mata Keeee da sauri ta tsaya cak tare da juyowa ta karaso gabansa inda yake zaune a nutse tace gani, kallonsa ya dauke a kanta yace koma gida baza kije ba,ban gane ba,ae baza kije ba,tunda kike zuwa schl din Nan uban me kika taba yi a gidan nan Wanda zai nuna cewar kina koyo abinda ake koya Miki? Amma idan Kai baka sani ba ai Umma ta sani ka tambayeta Kuma ai ba Kaine ka sani a schl din ba,Ok Haka kikace? Kwarai kuwa Husna ta furta tana fari da Ido,Mikewa yayi zai damkota ta arce da gudu tare da komawa cikin palonsu tana haki.

Ganin bazai Bari taje ba kawai ta koma Bedroom dinsa ta kara gyara Masa shi fes ta fito tare da shiga kitchen ta dakko littafinta da aka koya musu wasu kalar Abinci na zamani,ta Fara gwadawa,kitchen din ya shigo daukan cup ya isketa tana girki tana karantawa a Littafinta data rubuta komai tana cewa

Daddawaaa....idan aka zuba ta cokali Biyu sai me..me na rubuta anan ne? Kai Ni dai na cuci kaina da ban iya rubutu da wuri ba sai yanzu nake koya,Littafin ta daga tare da Kura Masa Ido sosai tace Atta...at...attarunhu...yawwa Attaruhu...Yess....Farhan Hannayensa ya harde a kirji Yana kallonta Yana Jin me takeyi, Bata San ya shigo kitchen din ba taci gaba da karantawa,
Yawwa idan aka jajja...ga...Attaruhu a ajiye shi gefe,sai a dakko.....ta saka kurawa Littafin Ido ta Dade a Haka kamar zata shige cikin littafin sannan tace uhum na gane sai a yanka albasa kadan,da sauri ta dakko Albasa ta ajiye a gefe.

Farhan Yana tsaye Yana jinta ta Fara gyara Albasa tace Yawwa Bari na yanka me shape din Kan Farhan din Nan,ita Zan Fara yankawa irin kansa ne wannan Albasar dama ya takura min sai nayi Miki kaca kaca Albasa tunda Kika yi shape irin Kan Farhan wlh kin shiga uku sai na dagargaza ki yau, Farhan Yana gefe a ransa yace Lallai sai naci uban Yarinyar Nan.
Yana ganinta tana yankawa tana dariya,tace Dama Kan nasa ko keya bashi da ita Kamar Lemon Zaki a lailye,da wani Hancinsa Kamar Attaruhun nan ta Sa wuka tare da raba Attaruhun biyu, sai da ta Gama surutunta ta juyo zata dakko abu a fridge kawai taga Farhan a tsaye ya Harde Hannaye.



Na kusa Gama posting Free page.


Masu son Siyen Rashin Sa'a Naira dari biyu ne(200).

Me son siye ta banki ga accnt Number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad, zenith bank

Masu son siye ta hanyar tura Number katin waya Mtn ga Number ko ta Whatsapp ko ta Sms 0803 393 3642.


Masu son yin Vtu Transfer ga Number 09032409668






AsmaBaffa
[2/29, 10:46 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…











31-35







Official





By
AsmaBaffa







Page naku be

Maryam k Abdallah
Maman Abdallah
Fauziya Abdullahi
Zainab
Mrs Hass@n
Fatima Saleh &
Ummyn Zahra.





Gabanta ne ya yanke ya Fadi ganin Farhan a tsaye ya hade Rai kamar Hadari, a hankali ta koma inda take yanka Albasarta da sauri ta dauki wukar taci gaba da yankawa tana cewa Irin Kan Yaya Kb ce wannan Albasar,tun farko dama nace in dai na tantance wanne Kai kikayi Kama dashi to na gane gaskiya yanzu shape dinki Albasa ba irin na Ya Farhan bane Sam Babu Kama ko kadan da Kan Yaya Kb kikayi Kama dama shine mugu Amma Farhan ai mutumin kirki ne ga hakuri ba ruwansa da duniya ko me akayi Masa hakuri yake ya Mai da komai ba komai ba,wannan Attaruhun ma irin hancin Kb ne shine duk gidanmu bashi da Hanci me kyau.

Farhan Yana tsaye Yana Jin wayon Husna,Kai ya girgiza har dariya ma taso bashi Wai duk kyansa yarinyar Nan Dan ta rainashi shine me Kai Kamar lemo ko Albasa Lallai,a hankali ya taka inda take cike da Izza, tana Jin takunsa jikinta ya dauki rawa karrrr...hannunta dake rike da wukar ya Kama tare da murdeshi Nan take ta saki wukar ta Fadi sai ta Fara kuka tana rokonsa Dan Allah kayi hakuri na daina na tuba bazan sake ba.
Sai kin fada min waye me Kan lemon Zaki? Farhan ya Furta Rai a bace,tana kuka tace Dan Allah kayi hakuri Allah bazan Kara ba,Kuma bada Kai nake ba Ni da Ya Kb nake fa,wukar ya dauka,Hannun Husna da ya rike shi ya daura saman abinda take yanka albarsa,Husna zatonta Yatsa zai yanke Mata sai ta saki kuka da karfi,Ba Imani yasa tsinin Kan wukar ya caka Mata a yatsanta jini ya Fara fitowa sannan ya nunata da wukar Duk ranar da Kika Kara gangancin rainani sai na yanke Miki yatsu gaba daya Yana fadar Haka ya saketa tare da barin kitchen din.

A wajen Husna ta zauna tana kuka ta gaji ta daina taga Farhan ba Imani Babu tausayi,Shi kuwa Bedroom ya wuce,wani kamshi na Musamman ya daki hancinsa,dakin yabi da kallo duk anja Masa fasali komai ya canja kuma hakan yayi kyau matuka,yasan Husna ce tayi Masa,a fili yace watarana tana da Dan hankali.

Bayan kwanaki kadan Husna tana ta kokari sosai a ko wanne fanni Musamman bangaren girki da Kwalliya tare da koyo rayuwar zaman aure,duk ta canja ta goge kullum wayewa takeyi Babu Wanda zai ce itace,tayi wani irin kyau haske da kiba kadan, Umma tana kula da ita sosai,Farhan ne kadai kullum zaman doya da manja sukeyi dashi,duk abinda ya sata tanayi da Kuma Wanda Bai sata ba duk tanayi,Husna tayi kawaye a makaranta Sakina da Rasheeda sune kawayenta na sosai Yan Mata ne Yan gayu yaran masu kudi.

Kamar Kullum Husna Bata da ranar Hutu sai Saturday Sunday idan me lesson ta zo ta tafi sannan take da time,Yau Saturday da safe Chinaza tazo Suka Gama lesson a part din Umma sannan Husna tayiwa Umma sallama ta dawo part dinta,tana shigowa da Sallama Farhan yana zaune Yana aikin danna laptop, Har zata wuce sai kuma ta dawo wajensa can nesa dashi ta tambaya me za a dafa maka yau? Bata taba yin Abinci dashi ba,ita kadai takeyin abinta ta cinye sabo da lokacin Bata wani iya ba Kar ta bashi ya gwasale ta,Amma yanzu tasan ta iya girke girke Bata da matsala, Farhan bashi da matsala da waye zai Masa girki matukar zaka dafa abinda yake so to zaici ba ruwansa.
Duk abinda Kika ga dama ki dafa idan yayi min Zan ci ya furta Yana tabe Baki.

Bedroom ta koma tana tunanin me yafi so ta dafa Masa,Ummansa ta Kira a waya,Umma me Farhan yake so na abinci nayi Masa?, Umma taji Dadi a ranta tace Yana son Abincin gargajiya irinsu waina,Founded Yam,Funkaso,gurasa,tuwon shinkafa,Cabbage soup, Fried rice, suna da yawa Husna har na zamani du Yana ci kadan ne baya ci,ki dinga gane me yafi son ci da kanki ga wasu Nan na fada Miki, ok Umma tace Sannan ta kashe wayar tare da wucewa kitchen.

Tunani ta shiga Yi a cikin Wanda Umma ta lissafa Mata ta Zabi Founded Yam da Cabbage Soup Tasha Kifi ta shirya tare da Hada Fruits salad me Dan Karen Dadi ta shirya Dining tsaf ka rantse ba Husna ce tayi ba.
Ko data dawo Palo Farhan Baya Nan ya fita Garden Yana Hutawa.
Yan aiki tasa Suka Kara gyara ko Ina,ita Kuma ta shirya Bedroom dinta Dana Farhan Babu wani Dirty Amma sai data Kara gyarawa ko Ina Yana kamshi.

Tana wanka ya dawo Palon ya Iske ta shirya Dining sosai,a ransa yace Ashe da gaske takeyi zata Yi girkin,Kujera yaja ya zauna yace Bari naji karyar iya girkin nata a Ina ya tsaya,Me Aiki ya Kira yace tayi Serving nasa,tana cikin Zuba Masa sai ga Husna ta fito Sanye cikin Riga da Skert na material Pink and Blue color ,kwalliyar data yi ba karamin kyau tayi Mata ba kamar a saceta a gudu,ta cika kayan Nan taf, Ga wani Dauri data yi Yayi kyau matuka,kamshin dayaji me Dadi yasa shi dago da kansa tare da kallon inda yaji motsi, zuciyarsa ta buga da karfi yau ce Rana ta farko Daya karewa mace kallo,Ido Suka hada da Husna ta kashe Masa Ido tana zuba Murmushin dake narkar da zuciyar maza,Harararta yayi sannan ya Fara cin abincinsa, sai da tazo saitin kunnensa tace laifin Malama ce ita ta koya Mana tace mu dinga kashewa mazajenmu Ido,gabansa ta dawo tana dariya tace na Iya? Kallonta yayi taso bashi dariya na tonawa kanta asiri, kafafu ta Fara dokawa a kasa tana Shagwaba tare da girza jikinta ko Ina ya motsa,Farhan Yana kallo zuciyarsa ta harba tana Masa lugude dam dam,Nan ma Husna tace ya ka gani na iya? Itace tace muyiwa mazajenmu,banza ya mata.

Me aikin dake niyyar fita ta kwalawa Kira, tana Karasowa tayiwa me aikinsu Magana Gambo karki Kara zubawa Mijina Abinci yau shine na karshe ba ruwanki da shi matukar bani na saki ba,
A rude Gambo ta shiga bawa Husna Hakuri,Allah ya huci zuciyarki baza a sake ba tana Gama fadin Haka ta fice da sauri,Kujera Husna taja tare da Zama itama, Muryarsa ta tsinta ba tare daya kalleta ba yace sau nawa Zan fada Miki bana son Shishigi a rayuwata, Ina ruwanki da wace zata zuba min abinci? Cikinki ko nawa ko Uwata ce ke? Bazai yuwu ba wata Gardiya ta zuba maka Abinci,yanda na tsara Haka abin zai kasance cewar Husna ta furta tana turo lips,Harararta yayi again yaci gaba da cin abincin ya Masa Dadi ya yaba girkin kwarai.

Salma ce zaune a kusa da tap tana wanke wanke gefe Kuma ga kayan wanki ba masu Dirty bane,Wayarta ce tayi Kara,Asiya ta gani a screen nata,da sauri ta daga tare da cewa Hello ya kk,? Ba wani gaisuwa Mene labari kawai kin San ba lafiya ce Dani ba Ina gabzar Garau Garau kullum Ina lafiya a wajena,Dariya Asiya tayi tace Kai Salma Baki da kirki to Albishirinki! Da Sauri Salma tace Goro fari kwal, Na samo Mafita Babba Amma ba yanzu zamu sa ayi aikin ba,Yara ne masu zafi zasu kaddamar da aikin,Yanzu ba sai Munje Abuja din ba? No zamuje gobe zamu tafi Inshaallah sabo da yarinyar ta tabbatar kina tare da Umma sannan Lallai ki shigewa Farhan yanda yarinyar zata sanfa ko yaushe Zaki iya aure Farhan,Amma idan taji Shuru zata samu dama ta baje kolinta tare da cusawa Farhan kaunarta,Salma tace hakane kawata gata dama da shegen kyau kamar Aljana.
Washe Gari sai da Salma ta Bari Babanta ya fita kasuwa ta hada akwatinta tayi waje Lubabatu tana kwala Mata Kira Salma karki sake ki tafi, karki manta Babanki yace idan Kika je Abuja Bai yafe ba,Salma ki guji bakin iyaye,ki kiyayi duniya,Tsaki Salma taja tayi ficewarta, Asiya tana cikin mota tare da Driver, Salma ta Karasa itama ta shiga baya kusa da Asiya suka wuce Abuja,Asiya karya tayi a gidansu tace University dinsu ce ta shirya musu zuwa escotion Abuja zasu Yi sati biyu.

Husna tana zaune a Main Palo ta baje littatafai na ko wacce schl tana karatunta,Kamshin data ji na daban ya cika Palon ta gane Farhan ne ya fito,ta dauki wani littafi ta bude tare da karashi a Fuskarta Wai

Please Login or Register in order to submit comment