Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bangaren mijinta,Umma sai Godiya takewa su Yafendo,Kayan Husna Kuwa dama Umma tace karsu dakko ko tsinke tayi Mata kayan lefe.
Su Yafendo sunji dadin yanda Umma take kulawa dasu Kamar zata goyasu,Abinci na Alfarma ba yankewa. Har part din Farhan ta nuna musu ko Ina har dakinsa tace shine part din Amarya, Amina da Nusaiba Baki Suka saki galala.
Sai da Suka huta Bayan sallar Isha Husna daga ita sai Nusaiba da Amina a daki Daya suke,duk Sunyi Wanka suna Hutawa,Husna ma itama tayi wanka Umma ta Bata doguwar Riga marar nauyi pink sabuwa dal ta bacci ta saka Suka kwanta.
Amina da Nusaiba ne kadai suke hira,Husna Bata cewa komai ta kwanta kawai tayi Shuru tana tunanin yanda zasu zauna da Farhan.

Umma ce tayi sallama ku fito Amina ga Ango yazo ku gaisa,Amina da Nusaiba da sauri Suka daura hijab saman Kayan baccinsu Suka fito,Umma ta kalli Husna tace ke baza ki gaisa dashi ba?, Husna kunya tasa da sauri ta danne Fuskarta da pillow tace Ni dai a'a, dariya Umma tayi tana jin Dadi da halin Husna,ficewa tayi ta barta, Amina kuwa Palon Umma Suka shiga Suka Iske Farhan zaune Yana karanta magazine ya harde kafa daya Kan Daya ga lemo Yana korawa, sanye yake da wani yadi me tsadar gaske Coffee color,dinkin zamani fitted cib a jikinsa,Yana zuba uban kamshi,Sumar Nan taci kudi sai sheki da walwali yakeyi kawai, suna shigowa ya ajiye jaridar a gefe da fara'a sosai yace Aunty Ina yini,Amina a dole ita Anty tace lfy Alhmdllh Kanina ya gajiyar taro? Farhan yace Alhmdllh,Nusaiba ma ta gaidashi ya kalleta kwarai Amaryarsa tafisu kyau nesa ba kusa ba,ko kafarta ma Basu Kama ba cewar Farhan a ransa,A fili yace sis ya gajiya Amma ke Zama Zaki yi a Nan sai next Year? Dariya sukayi gaba Daya har Farhan yayi kadan,Sunyi mamaki matuka dama Yana magana Haka harda fara'a da dariya,Ashe dai Yana da Dan kirki suke fadi a ransu, Nusaiba tace baka ce Ina Amarya ba, Farhan ya basar kawai yace ai nasan Inda abata take, Amina sai Murna takeyi da Alama Yana son Husna Lallai da wuri zasu samu kudi.

Sun Dan Dade kadan suna Hira sama sama sannan Suka Masa sallama tare da komawa dakinsu sai Murna sukeyi Suma sun kusa Zama masu kudi,Husna tana jinsu suna hirarsu Bata kulasu ba,Farhan kuwa Umma ya Kira a waya ta rakashi masaukin Yafendo dasu Inna yaje har can ya durkusa ya gaida su da mutuntawa,Yafendo tafi kowa Murna Husnanta tayi Dace,Yafendo tana ta shekawa Farhan da Husna Addua, Allah ya muku albarka,Allah ya albarkaci zamanku,Allah ya Kara budawa,Allah ya rabaku da sharrin masharanta,shedan,mutum,Aljan,dare,Rana,karfe,Allah ya rufa asiri duniya da lahira,Allah yasa ku zamewa juna Alkhairi,Allah ya Baku ikon farantawa juna,uban giji ya Kade fitinu,Farhan Kamar gaske Yana ta amsawa da Ameen Ameen,Inna ma tana Ameen, har ta Gama sannan yayi musu sallama ya tafi part dinsa Ummansa tana ta murna Bai watsa Mata kasa a Ido ba.
Koda ya koma Part dinsa tsaki yaja yace duk an takura min akan wannan yarinyar.

Washe Gari da wuri Yafendo ta damesu Azo a tafi,Nusaiba da Amina su ba Haka Suka so ba sunfi so sai Yamma sabo da su Kara kallon duniyar gidan Amma Yafendo da Inna sunce a tafi gida,ga bakin Umma ma duk sun tafi ba kowa Wanda ya rage a gidansu bako ko bakuwa.ko ba komai sun shiga jirgi albarkacin Husna.
Tunda Husna taji zasu tafi ta Fara kuka,Yafendo Sunyi lallashin Amma Taki hakura,wayo Inna ta hada Mata tace ke banza ce kalli fa gidan harda su lilo ga wajen wanka,harda tsuntsaye Kuma Ni ba tafiya zanyi ba Ina Nan a Abuja gidan Dana kullum zanzo na duba ki, sai lokacin Husna ta daina kuka ta hakura tace to na yarda ku tafi Amma kullum idan Baki zo ba Inna sai nazo wajenki, dariya sukayi kawai sabo da sun San Wayo aka yiwa Husna.

Sha Tara ta arziki Umma ta hada musu ga kudade masu yawa Farhan ya bawa kowacce n su sannan yazo sukayi sallama yasa aka kaisu airport,cikin kankanin lokaci Suka Isa gida lafiya Umma tayi Godiya ga Allah.
Husna kuwa tunda Suka tafi take kuka,dama da kyar aka lallasheta, Yan aiki ne suke ta gyara gidan kafin kace me gidan ya Kara canjawa da kamshi tare da daukan Ido.

Umma bayan tayi wanka ta shirya cikin Arabian Gown Black and Golden dakin da Husna ke ciki ta shiga ta iske ta ta kudundune cikin Hijab tana ta kuka Kamar ranta zai fita, da sauri Umma ta Karasa tare da Zama a gefenta, Kamo kafadun Husna tayi ta zaunarta sosai,Jin Hannun Umma a jikinta yasa Husna ta Shiga Jin kunya tana nuku nuku, Murmushi Umma ta saki tana son kunyar Husna,a nutse ta goge Mata hawayen da hannunta ta shiga Lallashinta da kalamai masu Dadi haba Husna Kamar ba gida ba,Nan ma gida ne Husna,Nima Mamanki ce,ki daina kuka Nan gidanki ne,gidan mijinki Ki saki jikinki duk abinda kike so Zan Miki sannan Farhan ma zai Miki,abinda nake so dake Husna ki kwantar da hankalinki nasan yarince Farhan zai saki a schl,Zai dauko me Miki lesson Ana koya Miki komai na ilmin Addini Dana zamani, Kwalliya da Girki tare da sauran Abubuwa da ya Dace mace ace ta iya Insha'Allah Husna Zan koya miki sabo da Haka ki daina kunyata,tsakaninmu Babu kunya, sannan Nasan bakya son Farhan Shima Kuma Bai sanki ba bare ace kun shaku,Ki daure ki dasa Masa sonki ki Zama wise Husna nasan halin Dana bashi da sauki, sai kin jajirce Ni Kuma Inshaallah Zan daura ki a Hanya.

Husna tuni ta daina kukan ta nutsu tana sauraron Umma har ta Gama sannan Husna tace na gode Allah ya saka da Alkhairi,Ameen Umma ta amsa tana murmushi daga bisani tace to tashi muje yanzu na Fara koya Miki yanda ake amfani da komai na gidan na harkar electronic etc,sannan muje har part dinki keda mijinki kiga komai na koya Miki komai na amfani,Husna Murnarta kasa boyuwa tayi tace Umma Wai ko engine buga kudi ne daku? Dariya Umma tayi tace a'a babu ko Daya Kinga Business mukeyi sosai na gaji kudi a wajen iyayena,Haka na dage na Tarawa Farhan su har yanzu juya Masa nakeyi suna bunkasa,komai da kike gani na Farhan ne,dukiya,Kadarori tare da sauran duk abinda na Mallaka na Farhan ne halak malak. Haka bangaren Ubansa masu Arziki ne na gaske shima Kuma Juyawa Farhan yakeyi Amma tunda aka Haifi Farhan ya Mallaka Masa komai.

Abinda yake damunmu daga Ni har uban Farhan shine rashin son aikin Farhan,Baya son wahala ko kadan na Gama kera Masa Building da ma'aikata Amma nayi nayi yaki zuwa tunda ya Gama Degree nake fama dashi yaki,Haka ubansa ma ya gaji kin ganni kullum bana Hutawa Ina Office da aikace aikace idan na dawo ma aikina daga wayoyi Danna computer bana Hutawa shi Kuma kullum sai dai yace ayi Masa Addua ya kusa shiryuwa.

Murmushi Husna tayi tare da cewa ai wlh kece Kika kyaleshi Umma kiyi Masa dukan tsiya Mana,Ai ba kallonsa zakiyi ba ai danki ne komai girman sa Allah ki samu Bulala ki zaneshi Tass, Dariya Umma tayi tace gaskiya na Samu Suruka me sani nishadi,Suna Hira Husna tana ta Bata dariya ita Kuma Umma tana ta koyawa Husna Yanda ake amfani da komai na gidansu,sabo da gidan Na daban ne ba irin na mutane bane komai na musamman ne, kofofi ma da remote da Kuma wani abin dannawa a jikin kofar sannan ake Bude na Palo,Bedroom kuwa sai ka Danna wani madanni sannan zata Bude,Haka Kitchen duk sai da Umma ta koyawa Husna komai sannan ta kaita part din Farhan,anan Husna ta rude da ganin haduwa,Nan ma ba abinda Bata koyawa Husna ba har na kitchen,Dakin Farhan kuwa da Suka shiga Husna sai da tayi suman tsaye sabo da gadon nasa da komai abin alajabi ne,Kamar dakin mace yasha gyara komai a jere ga kayan turaruka da lotion etc cikin Kan Mirror, Haka Toilet dinsa Kayan Wanka da liquid soap a jere gasu Nan na manyan Yara masu jii da Naira.Kayan sawarsa da Umma ta nuna Mata a cikin sip dinsa abin ya wuce hankali,bangaren shadda kala kala duk sababbi ga Kuma Wanda ya taba sawa gasu Nan jibge,Haka Bangaren yadi ma Haka,kana Nan Kaya Kamar suyi magana,Inner wears Ba a cewa komai.

Ko Ina kamshi yakeyi a dakinsa da Toilet,Har Tv Umma ta nuna Mata,Karshe dakin Takalma da agogunan Farhan ta kaita, Takalma na Alfarma wani ban garen farare ne gaba Daya sunfi kala ashirin,wani bangaren Baki sunfi Talatin,wani bangaren brown,wani bangaren Milk,arsh,blue etc gasu Nan iri iri iya kallonka,Haka bangaren agoguna gasu Nan.
Husna tace kamar kanti Umma Dole yaki Fita aiki wlh kece kike kashe Masa kudi, Dakin Jim dinsa Umma ta Kai Husna kayan exercise ne ba kalar da babu gasu Nan,Sai wuraren Hutawa iri iri duk a part din.
Dakin Husna Kuwa lefenta ne kawai da Umma ta hada Mata akwati goma cif Kaya na gaske ba abinda Babu na daukan wanka daga na bature har na hausawa.
Husna da yake tsoron Umma takeji tana Jin kunyarta gata surukarta,sai gashi ta nutsu duk abinda ta koya Mata ta iya daram a kwakwalwarta Bata manta komai ba.

Sai Yamma Umma ta Gama nunawa Husna gidan gaba Daya har bangaren ma'aikata sannan ta gabatar da Yan aikin Daya Bayan Daya a wajen Husna,Tunda Yanzu Farhan yayi aure Zan canja maza da suke Masa aiki Mata Zan maida part dinsa,Babu wani Namiji da zai shiga
part dinku Husna sabo da tsaro kiyi shigar da kike so daga ke sai mijinki, Uhmm kawai Husna tace,Girki kawai da gyaran bedroom dinki Dana Farhan zakiyi,karki Bari Yar aiki ta shigar Miki room din miji da naki kinji? Husna tace to Umma duk wacce na gani sai nayi Ball da ita Allah, a'a Husna Cewa zakiyi karta sake shiga Umma ta Furta tana dariya.

Yanzu baza kiyi girki ba,Ni Zan dinga Aiko Miki dashi part dinku watarana Kuma idan kinzo wajena sai muyi tare kina koya ko? Husna tace ae ai Ni ban iya girki ba sai kin koya min tunda naga Nan gidan akwai Sa'a komai Ana koya min sai naji na iya Ashe Ina da Sa'a ta nima,sai da Suka Yi sallar la'asar sannan Umma tace maza je kiyi wanka Farhan yanzu ya kusa dawowa,na rasa me ya fita Yi yau,baya fita Amma yau ko Breakfast baiyi ba ya fice.

Abinda Mama Bata sani ba Farhan Yana tashi da safe yace yanzu Umma zata kawo min yarinyar Nan me shegen surutu ta Sa min Ciwon Kai gwara na dinga barin gidan da wuri,Shine Dalilin da yasa Farhan ya bar gidan ya koma guess House dinsa yasha baccinsa.
Sai yamma yayiwa Umma text gashi Nan zai dawo yunwa yake ji.

Yanda Umma tace Haka Husna tayi wankanta tare da lambace jikinta da body lotion me kamshi,Tana sanye da Hijab Umma ta shigo dauke da Atamfa Super me shegen kyau black da zanen sea blue,Riga da skert ne sunsha dinki na gaske,Ko Umma ta mika Mata harda pant da bra tare da skin tight 3quarter dukkansu sea blue ne kalar kayan,Husna taji kunya ganin Bra ga Umma,Ajiye Mata Umma tayi tace ki saka yanzu Zan dawo, Husna Jin Umma tace zata dawo da sauri ta saka Bra din tare da pant da tight din sannan tasa Riga da skert din,komai Kamar an gwada ta,cif cif ita,Husna ga hips Kamar babbar mace,Masifar kyan data yi ya baci,Bata Yi kwalliya ba ta zauna,Sai ga Umma ta shigo tana jinjina kyau irin na Husna da kyan sura gaskiya Danta yayi Dace,Allah ya saka Masa da wacce tafi Salma Allah kenan.
Husna Kuma kunya duk ta lullubeta sai Wasa takeyi da yatsunta Bata Saba ba,Umma tace 'yata Allah yayi Miki kyau masha'allahu gasu powder Nan saman mirror ya Baki shafa ba? Husna tace ai na daina kwalliya dariya ake min wai Yar kauye, Umma da kanta ta zauna tare da shafawa Husna powder ta Sa Mata eyeliner saman Ido kadan tare da zizara Mata a kasan Ido kadan,sannan ta Sa Mata maroon Jambaki tace to ai Kinga yanda nayi ki koya ko iya wannan watarana sai ki dinga Yi kafin Nan gaba ki iya,Husna Bata San ma dame zata sakawa da Umma ba,abinda Yan uwanta Basu taba yi Mata ba sai tayi ba dai dai ba su dinga Mata dariya baza su koya Mata ba.
Gashinta ta taje sosai tare da shafeshi da mayuka masu kamshi,Umma ta fesa Mata Hair spray sannan tayi Mata Daurin ture kaga tsiya na manyan Mata masu ji da kansu.
Gashin ta Kara gyara Mata tare da dakinsa har tsakiyar bayanta,fadin irin kyan da Husna tayi Bata Baki ne,ita kanta Husna yau tasan ita din ta dabance,sai Murna takeyi tana kallon mudubi,Turaruka masu tsada da kamshin Dadi Umma ta Bata ta shafa su.
Husna tace Ashe Nima mutum ce me daraja Haka Umma? Da banyi aure ba yau nasan sai nayi samari sun Kai guda dari.
Umma tana murmushi ta furta Kash amma Kuma kinyi aure ta Dana ce shi Daya,Dariya da kunya Husna ta Fara Yi.
Gaban Husna ya yanke ya Fadi Jin Muryar Farhan me shegen Dadi Yana ta Kiran Ummana hankali Kamar Yana magana da wani Wai a Haka kwalla Kira yakeyi, Husna duk ta rude ta Fara diri diri,Umma ce ta kalleta tare da cewa ki saki jikinki kinji? Muna Palo ki fito ki gaida shi kinji, Kai kawai Husna ta iya dagawa tana Jin kunya.

Umma tana fita ta Harari Farhan yasan laifinsa dariya yayi tare da Rungume Umma Yana I'm sorry Ummana gajiyar biki ce naje Guess House na nayi bacci yunwa nakeji ki kawo min abinci.
Amma kasan kana da aure yanzu bana son Shirme ya kamata ka kula da yarinyar Nan fa Farhan,mutanen kirki ne daga gidan girma,a daure a saka musu da alheri Suma,Haushi yaji a ransa a fili Kuma yace to Ummana Inshaallah.
Dadi taji tace a kawo maka Nan ko Dining? Na gaji a kawo min Nan,ya harde kafa Yana latsa waya a palon Umma,Sanye yake cikin kana Kan Kaya masu shegen kyau da tsada crazy Jean ne a jikinsa an fatattakashi ta ko ina kamar wani mawakin turawa.

Yar aiki tana Shirya Masa Abinci Umma ta bar Palon ta haura sama tana waya,Husna Kuwa gajiya tayi da nuku nukun da takeyi ta Sa flat shoe din da Umma ta Bata ta saka, a bakin kofa tace ke Husna Zaki iya fita Me Sa'a ne fa ba wani ba,kawai ta fito a hankali tana tafiya a hankali sai data hangoshi yaci uwar gayu Yana cin Abinci cikin salon iyayinsa, a hankali tace kaga Dan gayu wannan wanka Kamar baza a mutu ba, kai Kuma Dan duniya sai yayi kyau wlh,ohh Kai wannan ya Gama morewa a duniya Ni kuwa badan yanzu na aure shi ba ai sai nace rako nayo duniya.

Nunawa tayi Kamar ba wajensa tazo gaidashi ba ita a dole Fitowa tayi kawai,taku ta canja Kamar yanda taga Farhan Yana tafiya da Izza da dagadara Yana basarwa itama Haka Husna tayi sak irin tafiyarsa tana uban Shan Shan kamshi tazo ta wuce ta gabansa, Kamshinta ya daki hancinsa yayi zaton ma bakuwa ce,ya Dan kalleta kadan Bai gane Husna bace, Irin muryarsa ta kwaikwaya magana kasa kasa Kamar ba magana akeyi ba tace barka da yamma,ka yini lafiya? Tunani ya Shiga Yi a ransa yace wannan wace Haka me irin tafiyata da Maganar ma,dagowa yayi a hankali ya tabbatarwa idonsa me tabin kwakwalwace wacce aka ce Amaryarsa, Dauke kansa yayi ko amsawa baiyi ba yaci gaba da cin abincinsa, Ganin Haka Husna ta Nemi kujera itama ta zauna irin yanda taga ya zauna da wani salo na gayu,itama tayi Haka kadan ya kalleta Karo na biyu yaga da Alama Husna Yar rainin hankalice gaba Daya wato kwaikwayonsa takeyi ta rainashi, canja style din Zama yayi don ya tabbatar da zarginsa,tana ganin Haka ta canja itama tayi irin nasan, Kai ya girgiza ya kwanta a kujerar, sai data Bari Yana kallonta ta zaro Masa harshe tare da yin Haushin Kare wan..wan..wan...wullu..ai kuwa ganin hakan a fusace ya Danna waya yace Ina son ganinku, Husna tana ji Bata San dawa yake magana ba minti Daya sai ga wasu manyan Mata narka narka ga tsayi ga kiba, Yan aikin gidan ne suma, sai ji tayi yace ku kawo min yarinyar can Nan wajen, da gudu Husna ta arce tayi kitchen sai ga Umma ta fito tana Ina Husna? Da Sauri Farhan yayiwa Matan nuni da su fita Kar Umma ta ganeshi, suna fita Husna ta fito Jin Muryar Umma,Yana daga kwance a ransa yace Zan koya Mata hankali Yar iskar yarinya.

Fitowa ta sake Yi a hankali tace Ni ba ruwana da Kai ba da Kai nake ba Wasana fa nakeyi,Bai ko kalleta ba Yana Danna wayarsa sai ga Umma tace Kai tashi ka zauna baka da aiki sai kwanciya duk ka tare min Palo,uban me tayi maka?Lips dinsa ya turo da sigar Shagwaba ya zauna Yana Me zanyi Miki Umma? Umma kuwa Husna tayiwa Inkiya Wai ta zauna kusa dashi,Husna tasan tayi Tsokana sai tayi Miki Miki,Umma tace zauna Mana Husna,Farhan ya Bata Rai Kamar zaiyi kuka Yana gani ta zauna a kujerar da yake,Kamshinsa duk ya ruda Husna,ya Gama tafiya da Imaninta,ga kwarjininsa.

Umma tafiya tayi ta barsu,tana ganin Haka ta mike da sauri tare da dauke lemon da yake Sha ta koma wata kujerar daban suna facing juna,A ransa yace sai na balla yarinyar nan lemon Dana ke Sha ta dauke,Husna Kuwa ta kurbi lemon me sanyi ga Dadi Bata taba Shan irinsa ba,Ido ta lumshe tare da lulawa duniyar tunani a ranta tace na birni ya cuci na kauye da tuni Salma karmashashiya ce a gidan Nan take Shan wannan lemo me Dadi, Farhan sai ji yayi Husna ta fashe da kuka,tunaninsa iyayenta ta tuna, ita kuwa Husna Kukan Dadi takeyi da tuni Salma ce take Shan Lemo ba ita ba,a hankali ta kalli Farhan dake kallonta Suka hada ido tana kuka Muryarta tana rawa tace Me Sa'a.. ka...ka tayani.. Murna..na ..na ...tsallake Rijiya da Baya,Bai gane me take nufi ba kawai yace ai wannan tabin kwakwalwa ne da ita shi yasa Baffanta ya aura Masa ita,ya cuceshi dama can yasan yarsa ba lafiyayya bace,gata kwaila yarinya karama me ta sani.





Na kusa Gama Baku Free page fans.πŸ˜‚ Page na kyauta ya kusa karewa ga Wanda Basu siya ba.



Rashin Sa'a Naira dari biyu ne (200)

Masu son Siyen Rashin Sa'a ta bank ga accnt number 2177560408 Yahaya Garba Muhammad, Zenith bank.

Wacce zata tura number Kati ga number WhatsApp na AsmaBaffa
0803 393 3642.

Idan Vtu zakiyi transfer ga number 09032409668





AsmaBaffa.
[2/29, 10:45 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…







21-30








Official







By
AsmaBaffa







Page naku ne
MOMCEE
A.H.H.N
MRS MUKHTAR
MAMAN AFFAN
MAMAN MUHIBBA
MRS HASSAN AND
MARYAM BAKATSINAH.











Farhan ya dauke kansa tare da gyara Kwanciyarsa ya juya Mata baya,Koda Umma ta fito tasan halin Farhan idan zasu kwana a wajen ba Lallai yayi wa Husna magana ba,Husna Kuwa bedroom ta koma tayi kwanciyarta kenan sai ga Umma da waya sabuwa me tsadar gaske, ta dade tana ganin manyan waya a hannun su Husna,Anty Amina da Mama Amma basa Bari ta taba musu yau gashi Allah ya Bata wace tafi tasu,Godiya Husna tayi ta karba tana murna,a gabanta Umma ta hada Mata wayar ta koya Mata wasu abubuwan da Suka Zama dole,Umma tana fita Husna ta Kira Yafendo da Abba,ta Kira Mama da Baffanta Suka gaisa Baffa yace Husna Karki Zama me mantuwa da bukatata idan Kika ki bin Umarni na wlh sai kin bar gidan Mijin naki kema,Husna tace Gaskiya Baffa bazan iya ba wlh Kuma Dama ai Kai kace zaka Yi min Aure tunda bani da kokari tunda kayi min ba sai ka kyaleni ba Allah Baffa Babu Kyau ka Zama me wadatar zuci, Wa'azi zakiyi min Dan Uwarki ko Ni sa'anki ne? Na Baki Nan da wata biyar matukar bakiyi abinda nace ba Zaki ga Abinda zanyi.
Ni bazan iya ba ban Yi alkawari ba Babu ruwana, Ummansa tana ta yabon halinku baka ga yanda take kula Dani ba ai a tunanina wannan yafi komai a wajenku tunda Ni yarku ce Kuna kaunata ya kamata idan wani ya kyautata min kuji Dadi Amma Baffa son kanku yayi yawa gaskiya,Ni bazan iya ba akan na cucesu gwara na bar gidan baki daya,Takaici yasa Baffa ya tsinke wayarsa.
Tunani Husna ta Lula irin halin na iyayensu abin ba kyau.

Ganin Farhan Yana share Husna Bayan Sallar Isha, Tasa Husna tayi wani wankan ta Bata Arabian Gown Yar kasar Egyft pupple,powder kawai ya shafa sai lipgloss.

Umma tace Husna zo na Rakaki part din mijinki,Dan Allah Umma ki barni a Nan muyi zamanmu,Murmushi Umma tayi tace Ke yarinya ce Husna baza ki gane ba muje kullum sai ki dinga zuwa muna gaisawa, tashin Asuba Farhan indai bani na tashe shi ba to baya samun Sallah yanzu Yana da Mata Husna Dan Allah karki dinga bacci kema ki kula da addini sannan da Asuba tayi ki tashi Farhan yayi Sallah,karki barshi ko yaki tashi Dole ki tasheshi kiyi alkawari, Insha'Allah Umma Husna ta furta,Har Bedroom Umma ta Kai Husna tace to Ni na tafi duk abinda ya shige Miki duhu ki kira Ni kinji? Inshaallah Umma zanyi yanda Kika ce.

Tunda Husna taga ba Umma ta nutsu sabo da tasan Farhan Baya kulata shima ya rainata kallonta yake a Yar kauye.
Sai data ta shirya bedroom dinta sannan fito Palo tana danne dannen waya sabo data Kara koya,tana zaune ya shigo da Jallabiya Fara tas Yana kamshi, uban Yan Isa da takamar ko kallonta baiyi ba,itama kallo daya tayi Masa ta dauke kanta tare da ci gaba da Danna wayarta,a ransa yace wato an siya Mata waya baza ta gaishe Ni ba,sabo da ya kuntatawa Husna a ransa yace yau baza tayi bacci ba, Fitowa yayi baya son yin magana sai dole da kyar yace ke zo,Husna ta mike zumbur a tsorace zatonta laifi tayi masa da sauri tace Dan Allah kayi hakuri, tsaki yaja kadan kayansa Daya Ware zai bayar dasu masu uban yawa yace kwashe ki wankesu tas gobe idan sun bushe ki gogesu ki kawo min,Husna a ranta tace wanki da dare, a fili tace a Engine wanki Zan wanke? a'a baza kiyi amfani da washing machine ba da hannunki Zaki wankesu yanzu.

Bata ce komai ba ta eba ta tafi toilet din dakinta ta zuba ruwa a bokiti da omo sannan ta cire kayan jikinta ta zabo 3quater da Yar t-shirt cikin kayanta na lefe ta saka ba karamin kyau tayi ba,ita kanta sai ta ganta daban sabo da bata sa kananan kaya.
Gashinta ta maida zakiyar kanta ta Kama ta kalli kanta tace Nima na Fara fitowa Gari.

Toilet ta koma ta Fara wankinta har wakokinta take rerawa,gashi da sauri takeyi kamar zata tashi sama,Kayan Babu Dirty ko Daya kafin kace me ta Gama,Tabi ta baya wurin shanya Amma ta kasa tabo igiyar sabo da tayi Mata tsayi har tsalle takeyi Amma ta kasa,Komawa tayi Bedroom dinsa tare da kwankwasa Masa Shuru har ta gaji da tsaiwa kawai ta Danna inda ake dannawa kofa ta bude,tana budewa ta kutsa Kai ciki da sallama lokacin ya fito daure da towel a kugunsa da

Please Login or Register in order to submit comment