Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku danyi magana da Amaryar taka Mana, tun dazu sai Danna waya kakeyi Wai uban me kake dannawa ne? Umma ta juya zata fita tace Muna jiranka a mota, da Sauri Farhan ya rike gyalen Umma tare da shagwabe fuska yace pls Mana Ummana ke kuyi Maganar da ita Mana, kaji shashasha me zanyi Kuma wannan ai aikinka ne Farhan ba nawa ba,Kai komai sai dai ayi maka,a kunne ya radawa Umma pls Ummana kice taje gida mun tafi,Baki Umma ta bude taja tsaki tare da fisge jikinta ta bar Farhan da Husna a tsaye bakin gate.

Husna ta kalleshi ya wani hade fuska Yana muzurai sai Harararta yakeyi, Husna tace me Sa'a karka damu tunda baka iya zance ba Ni Zan dinga zance ka tunda na fika baki,to Wai auren Nan Kai me zaka Yi da aure ma? Gaka da kudi to indai Dan Abinci ne Ni ban iya girki ba.
Tsaki yaja yayi ficewarsa ya bar Husna tsaye,Husna tace to fa Nan ta Fara tunani da sauri ta zabura a fili tace bashi yace Yana so na ba Baffa ne ya basa Ni sadaka,shike Nan auren Sadaka aka Yi dani bani da wata daraja, Bari na dai daita sahuna idan an kaini Abuja ba ruwana da su nayi rayuwata shima yayi tasa idan ya takani wlh nima sai na taka shi a Kan me Zan Bari ya wulakantani,idan kyaune yo ai Nima ba baya bace mutum kullum ba Uhm bare Uhm Uhm.

Umma tana ganinsa tasan ba abin arziki yayi ba Gashi ya fito Kamar an Aiko Masa da sakon mutuwa,Inna tace Munafuncin Farhan ne yarinya zukekiya ai kayi Dace wlh,da Wuri su Umma Suka koma Abuja a jirgi,Basu boyewa kowa ba yan Uwa da abokan arziki duk sunji me ya faru,tunaninsu Baban Husna Dan Allah ya bada yarsa Ana ta yabon Halinsa Ana sa Masa albarka,Umma tana ai Ni nayi surukai Yan mutunci wlh Babu son abin duniya,Kai madallah Baku gani ba,Shi kuwa Abbin Farhan ba son lamarin yakeyi ba yafi son dansa ya auri balarabiya jininsa sabo da wannan dalili ko kwana Basu sake Yi ba sukayi tafiyarsu Qatar yace idan Amarya ta tare watarana za a kawo Masa ita har gida ya ganta.

Salma yini tayi tana kuka,Bata San me ya faru ba Baba Sule yace bazai aura Mata Abin kaunarta ba Farhan,Tunda ta farfado tace su Aliya su kaita gidan Babanta,Haka suka kaita a mota,Aliya kuwa Suna Ajiyeta a mota suka bar unguwar Salma ta shige sakarkarin gidansu.
Baba ta iske ya mike kafa Yana Jin radio suna Shan kankana shi da Matarsa lubabatu tana gefensa.

Kusa dashi Salma ta tsuguna Wanda tunda yake da Salma Bata taba tsuguna Masa ba,ya kalle ta kawai yayi banza da ita,Hawaye ya balle mata tace Baba pls me ya faru? Haba Baba? Me nayi maka ka azabtar Dani Haka? Nifa yarka ce Baba kasan wallahi Ina son Farhan idan ba shi bazan rayu ba,Why Baba? Why me? Baba Yana jinta har ta Gama Yana dagowa ya dauke Salma da lafiyayyen Mari ji jake kauuuuu,.kunci ta dafe Nan take fuska ta kumbura sai lokacin Babba ya furta Ni zakiya turanci Dan ubanki? Ni Zaki kalla kiwa turanci? Sa'anki ne Ni? Au rainin naki ya Kai Haka kamar Ni Salm......yiiiiiiii Baffa ya fashe da kuka,Mamaki ya Kama Salma Mene Abun haushi akan anyi turanci ai yare ne Amma sai tace Baba Dan Allah ka bawa Umma hakuri a dawo a daura min Aure da Farhan kaji tausayina Baba.

Murmushi Baba yayi na takaici,yace aini ba ubanki bane Salma kin manta? A gaba na Kike fadawa kawayenki Ni ba ubanki ne,can a Dangin su Umma nake, irin rashin tarbiyya da wulakantani da kike Salma duk Baki San kina Yi ba? Kina ganina banza sabo da Ni talaka ne, ke gaki kin taso a gidan masu Arziki ko? Waye silar zuwanki duniya? Kuma sai Dana ga dama na bada ke riko wajen Umma har Kika girma ke wato kin Zama mutum ko?

Yau na nuna Miki tawa isar ta uba Wanda kike ganin ba kowa bane,Ina Umman taku yau me yasa Bata daura ba? Sai yau kika San Ni ubanki ne? Bari na fada Miki abinda Baki sani ba Salma,Bazan Miki Baki ba wannan kadai ya isheki,Kuma na haramta Miki Zama gidan Umman Farhan har gaban Abada ko hanyar Abuja Kar ki sake naji kinyi in ba Haka ba wlh Kinga abinda nayi Miki to na gaba sai yafi wannan, Kuma matukar Baki ji maganata ba Kika je Abuja wannan har uwar Taki zai taba Umma duk zan hada nayi maganinku.
Ki daina sa ran auran Farhan har abada baza ki aureshi ba matukar Ina Raye, tashi ki bani waje,Lubabatu matar Baba Sule tace sai ki zauna muci talaucin mu,ga dakinki can sai ki koyi tarbiyya,lefe Kuma da komai da Suka kawo sunce sun yafe sai nima ki bani rabona Kayan sawar, ai dole ma ta Baki rabawa zakiyi dai dai cewar Baffa Yana fadawa Matarsa.
Idan Zaki Suma sau dari bazai sa na canja ra'ayi ba Salma,kince Ni ba ubanki bane yau na nuna Miki Power ta,kuma wlh a gidan Nan Kika sake Yi Mana turanci ko kalma Daya ce sai kin kwashi kashinki a hannu.

Salma ta fada Dan wani akurkin dakin da aka ce nata ne ta fashe da uban kuka harda kururuwa da birgima,ba Wanda ya kulata,Tana cikin kukanta Aliya ta bugo Mata waya,tana dagawa Aliya tace Dan ubanki Bude kunnenki kiji labari me zafi,ki daina kuka Salma kiji,da kyar Salma tace Ina jinki,Aliya tace Zaki tuna Yar iskar yarinyar Nan? Yar kauye data zo gidanmu rannan? Salma tace Husna take ko wa me kwalliyar Nan ta kauye,wacce tayi min mugun fata gashi Allah ya karbi Adduar yarinyar Nan wlh an fasa aurena da Farhan wannan yarinyar ko mayya ce ko Kuma kusanci ne da ita da Allah gashi Adduarta taci,Zanzo ki rakani gidansu Zan nemi yafiyarta ta tayani Addua Allah yasa ayi aurena da Farhan ko Allah zai karba .

Aliya ta Kara Jin tausayin kawar Tata Amma ta daure tace Salma wannan Husna da kike labari to wlh itace Farhan dinki ya aura,ita aka daura Masa aure da ita,Inna ce take bani labari,yanzu ma Ango da Ummansa Saida Suka Dade a gidansu sannan suka wuce Abuja,Babanki Yana cewa bazai aura Miki Farhan ba Baban Husna yace a daura da yarsa.

Salma tana Jin Haka ta duro Ashar tace Amma Baba ya cuceni Allah ya saka min bazan yafe Masa ba,Aliya da sauri tace Auzubillahi kina da hankali kuwa Salma? Karfa so yasa ki kauce hanya,ke yanzu Farhan dinma tunda ba sonki yake ba kin sani Amma kike fadawa babanki Mahaifi haka,Wlh ki tuba ki gyara halayenki tun kafin duniya ta juya Miki baya,duk abinda zakiyi karki taba iyaye ba Wasa ki kiyaye harshenki Baki San sanda Zaki mutu ba,Salma tayi Shuru Amma ji take kamar ta kashe Babanta ta huta,a fili tace Aliya ki rakani gidan su Husna pls sai na kasheta kowa ya huta,Aliya tayi dariya tace banda kisa ke Baki da hankali Ina laifin ma muje mu watsa Mata Acid a fuska Kinga ko banza ta nakasa bazai taba rayuwa da ita ba,Nan take zuciyar Salma tayi sanyi tace Alhmdllh kin kawo Shawara,wlh Haka za ayi Yar Gari dadina dake kina ja,suna ta dariya sun shirya mugunta,duk abinda sukeyi Baffa Yana jinsu, sai da Suka Gama wayar ya shigo dakin da katuwar bulala,ya shiga jibgar Salma Kamar zai kasheta,yace Bari ke na Fara nakasa ki kafin ki nakasa Yar wani,tana ihu tana bashi hakuri Amma sai da yayi Mata jina jina ko tashi ta kasa Yi,yace Kuma matukar Kika taba lafiyar Yar wani ban yafe Miki ba.

Salma tana ta kuka ta Fara tsorata da Baba Kuma zai iya kasheta, Suna yin waya da Aliya tace gwara ki kwantar da Kai sannan ki samu abinda kike so, ai bullowa Baba zamuyi ta bayan gida,ki koma ladabi da biyayya ki nuna komai ya wuce kin shiryu sai mu samu ya Bari mu fita kamar zamuje yawo ayiwa yarinyar Illa.
Salma tace nafi so ayi komai da sauri mu bayar da kudi ayi aikin ba sai munyi da kanmu ba kawai,Aliya tace ki Bari zanyi tunani ya zamuyiwa yarinyar kafin a kaita gidan Farhan sabo da ya kamata a kaita a nakashe Kuma Fuskarta zamu lalata kin San matsiyaciya kyau ne da ita, Salma tace haka za ayi kawata fuskar kawai zamu kashe.

Tun daga wannan Rana Salma da Aliya suke sake sakensu,Amma Basu samu Mafita ba,yayin da Baba Sule yasa Salma duk aikin gidan Nan ita take yin komai ba hutu,ita Kuma sai biyayya take tana kwantar da Kai Dan ya kyaleta ta Shana,shi Kuma Baba ya Gama ganeta yaki yarda.

Husna Bayan tafiyar su Umma Ranar kawai wani Murmushi takeyi ita kadai sai dai aga tana murmushi tana fari da Ido ko ta shanye hannu Daya tana taku dai dai a palon, Nusaiba da Mama ne Suka fito daga kitchen suka Iske abinda Husna takeyi tana ta yanga tana taku dai dai tana fari da Ido,ko Kuma tana wani kallon Up and down, Ikon Allah Mama ta furta,Nusaiba ta tabe Baki tace ko kunya Babu daga daura aure yau duk ta damu mutane Dan kawai ta auri me kudi me kyau to ai Farin fata ne kawai har wani kyau yake dashi ki Bari kiga namu kalar,Idan ba kauyanci ba me zakiyi Masa ya gaji ya koreki,Wa zai so ki a Haka,ba iya girki,ba kwalliya,ga rashin cin jarabawa komai Baki iya ba.
Husna tsayawa tayi cak tana Jin radadin kalaman Nusaiba sabo da Hassada Wai Farhan ne bame wani kyau ba,Murmushi Husna tayi kawai tare da cewa ba komai a hakan dai nazo Kuma na taka matsayin da baza ki taba takawa ba,Kuma wlh ki kiyayeni Ni ba sa'arki bace, ki jira ki gani yanda zuciyarsa ma sai ya cirota ya damka min a hannuna tsabar so duk sai nayi maganunku,nasan fa me nakeyi karki Yi tunanin banza ce Ni,ya Isa Haka Mama ta tsawatar.

Suna Haka Anty Amina ta shigo da yaranta Kanana,sai ga Kb,Aliyu da Baffa sun dawo daga masallaci,a Palo aka zauna Baki daya,Baffa yace meke faruwa ne ke Husna? Ba komai Baffa kawai Hira akeyi ta boye Bata fadawa Baffa ba,Kinga ki fada munafuka cewar Kb,Mene amfanin fadar tunda ba iya daukan mataki za ayi ba? Husna ta furta,Amina race uwar bakin Hali kenan wlh Ina mamaki Baffa hhhh ta kwashe da dariya tace Wai Husna Amarya miji Kamar Farhan,wannan za a Kai gidan daula Haka ai wlh Yafendo da Baffa ne kawai zasu ji dadin kudin Amma mu baza ma ta sauraremu ba bare ta kawo tallafi,Mama ta nisa tace nima Haka nake gani wannan baza ta iya taimakonmu ba,dama Nusaiba ce da munji Dadi.

Baffa ne ya gyara Zama yace ke Husna karki ga kin shiga daula ki manta da Iyayenki da Yan Uwa,nayi ne Dan mu huta,Kinga na kusa retire ga Uwarku Babu aiki Haka Kb ba wani Babban aiki ne dashi ba,dama na gani mun samu shi yasa nayi amfani da ita,ba Haka kawai na taimaka nace ya aureki ba sai Dan Nima Ina da wani buri akansu,damar daza mu huta,sabo da Haka kiyi amfani da damarki mu Zama wasu muma a duniya,ko wasu milliyoyi ki samo min na Kama kasuwanci Babba,ki samowa Kb babban aikinyi,sai Amina dasu Nusaiba,Mama tayi caraf tace Ni fa? Nasha wahalar Haihuwa Amma a kyaleni ai wlh Nima jari nake so ko na milliyan goma ne zanyi manage haka.
Baffa ya kalli Husna yace kalleni da kyau Husna wannan dalilin yasa nayi Miki wannan auren,da tunanina na Baki talaka dai dai dake tunda Baki da basira Amma sai tsuntsu daga sama gasasshe ya Fado nayi amfani da damata,kina gani ko mitocinmu da muke Hawa duk Babu na kirki.

Kb yace Kuma wlh saura muji ki Shuru ubanki Zaki ci Dole ki taimakemu muma a San damu a kasar Nan,Dole ma sai kinyi abinda muke so ko Kuma ki gane kurenki,Ya kamata Kuma ki koyi kwalliya,Tsafta,iya girki sabo da kiyi Saurin sace zuciyarsa mu samu rabonmu da wuri,ko yaushe bukatun kudi Zaki dinga Kai musu Dole su Baki sabo da zasu tuna halaccin da aka musu.

Mikewa Husna tayi tsaye tace nufinku wai naci Amanar Mijina? Na dinga karya Ina karbo kudade Ina Baku? Wacce cin Amana? Ki dai samo Mana kudi kawai cewar Amina,Husna ta tabe Baki tare da Mikewa tsaye tace tab Ashe kuwa talauci zai kasheku wlh bazan cuci Mijina ba,ba Haka naga Yafendo tanayi ba,sannan nasan dai dai da Kuma rashin dai dai bazan taba aikata hakan ba,idan kudin sauki ne me yasa ku bakuyi shi ba? Sannan ma Baffa idan Mama tayi ma Haka zaka ji Dadi? Ke Kuma Anty Amina ai kina da Miji lecturer Yana samu dai dai gwargwado me yasa ko Yar dubu ashirin Banga kina kawowa ba sai nice da bakwa kauna? Motoci da kuke cewa duk bana kirki bane wlh ku godewa Allah wani ko Keke baida shi.
Basu ce Mata komai ba tayi tafiyarta ta barsu.Baffa yace ku kyaleta nasan me zanyi ta Amince.

Husna tunani ta Shiga Yi Yafendo Bata San anyi Mata aure ba sabo da Haka kawai taje Wajen me aikin Mama ta karbi Aron wayarta ta buya ta Kira Yafendo,Yafendo ta gane Murya tace Husnata ya gida,yau kece Haka,Ina Nan nayi kewarki yata,Husna tace Nima Haka Yafendota,Amma Yafendo kin San anyi min Aure? Yafendo tace hmm wannan Baban naku ya fada min a waya ya bani labarin komai Amma ban yarda Dan Allah ya bada aurenki Haka kawai ba,Husna tace badan Allah bane ba Yafendo nan ta kwashe komai ta fadawa Yafendo,Yafendo tace Maganar Bata waya bace,ki kyalesu kice musu kawai zakiyi,jibi yace za a kawoki wajena har sai ya rage saura kwana Uku a kaiki dakin Miji za a daukeki,Husna sabo da Murna harda Ihu,tace Yafendo basa koya min komai fa,kyalesu sai kinzo kawai.haka Suka Gama wayarsu.

Bangaren Ango kuwa ji yake kamar ya bar garin yasan Ana kawo Husna Ummansa zata sa a kawo Masa ita part dinsa su zauna tare,gaskiya shi za a takura Masa rayuwa,gata da surutu kullum ma sai yayi Ciwon Kai,Kuma frnds su ganta ace itace Matarsa,gata Yar kauye,yarinya karama shi Kam ya Shiga uku,
Farko zai kyaleta Amma Nan gaba shi korarta zaiyi sai dai Umma tayi duk abinda zata Yi Masa Amma bazai iya ko hada yatsa da wannan yarinyar ba da ake cewa Wai Amaryarsa.
Ita kuwa Umma shirye shirye takeyi kawai na tarbar Amarya da yanda zata kula da yarsu Baffa itama sai ta saka musu da Alheri Kamar yanda Suka fitar dasu kunya, lefe take hadawa Husna na gani na fada za a ajiye idan tazo a Bata abinta tunda Baffa yace Bai son komai.
Kullum Umma sai ta Kira Maman Husna da Baffa suna gaisawa Ana karfafa zumunci,sai nuna mata sukeyi su na Gari ne.

Husna tana so taje gidan Inna Amma ba a Bari ta fita ko waje, da kyar Mama ta Bari taje sau biyu Allah yasa Basu hadu dasu Aliya ba har ta tafi kauye wajen Yafendo Kb ne ya kaita,Yafendo da Abba suka sa Husna a gaba da fada da Nasiha me ratsa jiki,Suka sanar Mata Mene auren ma gaba Daya,daga Nan Yafendo take tsumata tana koya Mata Abubuwa a hankali Kuma dake tasa a ranta tana so ta iya Sai ta koya da wuri,Haka girki ta iya jullof din Taliya,Indomie,shinkafa Fara,dafa ruwan zafi,soya kwai da dankali shike Nan ta iya,daga Haka tace ita Allah ta gaji ta iya girki da yawa.

Saura kwana Uku a kaita Suka taho Kano tare dasu Yafendo,Husna ta Kara kyau da Yar kiba,tsumin Yafendo Yana aiki sannan tafi Jin dadin Kauyen ma ita,duk Husna ta Dan nutsu kadan,Inna ma kullum sai tazo gidan Mama wajen Husna da nata nasihar da kayan gyaran jiki,Inna tana ta Mata fada akan kwalliya ta daina ta kauye Husna tana so miji ya sota sai kuwa tace ni dai Inna indai akan kwalliya ne nama daina Yi gaba daya ba ruwana,shike Nan tun daga wannan Rana Husna ta daina ko shafa powder,anyi anyi ta dinga shafa ko powder ce tace ba ruwana bazanyi ba naje na lalace, Mai ma tana shafawa kadan akace ta dinga shafawa da Dan yawa ai shike Nan sai ta koma laftawa tana lambace jikinta kullum maiko takeyi kamar me shafa man gyada.

Mama tace ku kyaleta gwara Haka ta dinga maiko akan wannan shegiyar kwalliyar Tata,Ana gobe za a zo daukan Amarya Baffa ya Kira Husna Wai zaiyi Mata Nasiha yace to mu dai Babu fadan da zamuyi domin mun Gama Yi Miki tuntuni,idan kinyi da kyau kin sani idan ma kin Bata kin sani, Mama ma tace kinji dai saura ki zauna lusaranci na Dade Ina adduar Allah ya bani surikin da zai kaini Hajji da Umrah ya siya min mota ya bani jari.

Sai da Suka Gama kaf Yafendo ta sake saka Husna a daki tayi Mata fada na masu Ilmi da sanin ya kamata tare da Dora Husna a hanya me kyau,Haka ma Inna sannan ta dauki nauyin kwalliya gobe idan za a Kai Amarya.

Washe Gari aka Tara Yan Uwa da abokan arziki harda Dangin Umma Mata guda biyu akayi yinin bikin Husna,Amarya Tasha kwalliya da kyau na musamman anyi pics,Umma ce ta Aiko da Kaya kala uku masu tsadar gasken gaske Wanda Amarya tasa,Shadda,lace da Atamfa,sai shoes and bags da mayafai, har Inner wears,Haka ta Aiko da makudan kudade,Baffa sai washe Baki yakeyi,Inna,Yafendo,Anty Amina,Nusaiba,da Yar Uwar Mama sune Suka tafi raka Amarya tare da Dangin Umma su biyu.

Airport aka kaisu Suka shiga jirgi Husna Amarya sai jikin Yafendo da Inna ta kankame Wai tsoron jirgi,a kasa kasa Kuma sai kuka takeyi bilhakki da gaskiya har suka Isa Abuja.
Umma tasa motoci na Alfarma aka ebo su daga Airport zuwa gidan miji,Husna tana lullube cikin mayafi Amma sai ta dinga leko da kanta kadan tana kallonta ta window,ganin haduwar garin Abuja yasa ta yaye mayafin ta ajiyeshi gefe tana hawayenta Kuma,ganin irin azababben gidan da za a shiga ta tabbatar shine gidan su Me Sa'a Bata San sanda ta nemi kukan ta rasa ba,cik kakeji Driver ya Danna mota zai shiga Husna tace Kai Haka ake Kai Amarya bazanyi Addua ba,ai anayi ko? Yafendo tace wannan Haka yake indai shine gidan da zata zauna da mijinta to ya kamata ayi Addua,sai tayi a motar ma ba wani Abu bane cewar Driver.

Husna tace Kai ina magana kanayi? Tsaya da mota mu a kafa zamu shiga idan nayi addua ta,Inna tace Iyye Jikata har an Fara mulkin gaskiya ta fada a fito kawai,ita kuwa Husna ba adduar ta damu da ita ba Dan kawai tayi kallo ne tace a saukesu a gate,dukkan su har na dayan motar Suka firfito.

Gaba Daya su Amina sun rude da gidan Husna da zata zauna,sun koma Yan kauye Suma, Husna tana kalle kalle ta cikin mayafinta shara shara tana Addua,hankalinta baya jikinta sam tunda ta hango wani hadadden lilo a cikin gidan,ko Ina a gidan matakan tsaro ne suna tsaro,Bayan an Gama Addua Husna ta shiga da kafar dama tana Bismillah tare da wasu adduoin,tana tsakiyar Inna da Yafendo tana Inna kalli Lilo can kullum Zan dinga Hawa,Kai ..Kai kalli bishiyar Gwanda can Zan dinga shanyeta Ina tsinko kayata,laaaa harda Goba aka shuka min Ashe nice Zan shanye su ba Salma karmashashiya ba yiiiii Husna ta fashe da kukan Dadi tace wlh Inna na godewa Allah harda kogin ruwa(swimming pool) Zan dinga fanjamawa ciki.




Ga masu siyen Rashin Sa'a Naira dari biyu ne (200)

Masu son Siya ta banki ga accnt number 0033441422 Yahaya Garba Muhammad,zenith bank.

Ga masu son Siya ta hanyar tura Nambobin katin waya Mtn ta WhatsApp number ta gashi 0803 393 3642.

Masu son Siyen Rashin Sa'a ta hanyar Vtu ga number da za a yiwa transfer 09032409668.

😍😍😍πŸ₯°πŸ’‹
Ina godiya fans Dina Ana tare iya wuya.a ajiye min sharhi na zanyi replying.





AsmaBaffa
[2/29, 10:45 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…









16-20






Official







By
AsmaBaffa








HAJJA HAUWA AHMAD page naki ne kiji dadinki.

KHADIJA DANDUME REAL MAMAN WALEEDA
AUNTY SUMEE
JANNAT AND
MAMAN FAHAD.
Ina muku fatan Alheri.

Fans Dina masu Sharhi Inshaallah zan Baku page a Kara hakuri Ina gani Kuma ina sane da kowacce.








Ikon Allah Yafendo ta furta tare da radawa Husna a kunnenta tace kiyi Shuru Husna Dan Allah karki kunyata mu,ki nutsu Kinga tare zaku zauna da surarki,ki taimakemu mu asan Nutsatsiya aka aura kinjin Yata, Kai Husna ta daga tare da Sa hannunta a saman lips dinta ta matse bakinta tace nayi Shuru,na daina Amma ai kince na dinga jin kunya ko Yafendo ta? Da Sauri Yafendo tace ae Haka shine Kika cika macen kwarai,da sauri Husna ta Kara gyara mayafinta ta rufe ruf tace naji kunyar Yafendo kin gani ki kalla kin ganni,Yafendo tace ae hakan yayi to kiyi Shuru,Husna tace to nayi Shuru,Amma idan suna tafiya sai ta dinga rike hannun Yafendo tana Uhmmmm...uhmm..Wai baza tayi magana ba,Ana Haka Inna ta dinga rangada guda,Suma Yan Uwan Umma Suka dauki guda da Ayyiri yiri Amarya ta iso,ragowar da Suka rage Yan biki Dangin Umma sune Suka tarbi su Yafendo.

Amina da Nusaiba da kyar suke iya daga kafa ganin irin rantsatsen gidan da Husna zata Yi rayuwa,gidane ko a kasar waje samun kamar sa zai wahala,part hudu ne a gidan,ko wanne part sama da kasa,part din Farhan yafi na kowa tsaruwa komai white and dark Brown ne, Yana sheki da daukan Ido, tunda bikin ya kusa aka canja tsarin gidan,part din Umma Milk and Golden color ne,sai na Baki da Kuma na ma'aikata bangaren Mata Yan aiki daban na mazan ma daban.
Side din Garden daban katon gaske ba abinda Babu a ciki har bangaren tsuntsaye kala kala,
Swimming pool guda biyu ne Daya part din Farhan Daya Kuma a garden.
Sai parking space ga motoci Nan maka maka masu tsadar gaske sai ka gaji da kallon motoci ka rasa wacce tafi wata.
Gidan dauke yake da flowers ko Ina,ga wani uban Round about a tsakiyar gidan anyi Masa wani irin kwalliya ga wasu fitulu da Suka zagayeshi abin gwanin birgewa,gate a gidan ya Kai hudu, duk inda kuke zaton gida to wannan gidan ya wuce tunani,ko gidan shugaban kasa sai Haka, furniture din dake gidan da irin tsarin da akayi musu abin alajabine sabo da kyau kamar aljannar duniya Haka zaka ji idan kana wannan gidan, duk Wanda ya shiga bazai so ya fito ba.

Amina sai rada takewa Nusaiba a kunne shike Nan Husna ita Allah ya Bata,Kinga yarinya Muna rainata maza mu dauki hotuna sabo da mu nunawa Mama da Baffa susha kallon Duniya,Nusaiba tace Allah yasa dai Baffa su takurawa Husna ta samo Mana dukiya muma muyi kudinmu,ya Kika gani Ina ma mune da wannan arzikin Amma nasan Husna Yafendo zata Fara ginawa jarababba, hmm ai wlh sai na zuga Baffa ya bullo Mata ta bayan fage cewar Amina.

Amarya Husna Zaune a gaban Umma a kasa kanta lullube,Umma Baki har kunne,akayi adduoi sannan itama Umma da kanta tayiwa Amarya Nasiha,Umma tace ai ga part din Amarya can daban Amma baza ta koma can ba sai komai ya lafa an gama Sallamar bakin nesa sai na kaita da kaina

Please Login or Register in order to submit comment