Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sadaf Husna ta zare jiki ba Wanda ya sani ta fice Daga schl din tare da shigewa Napep sai gida,sun San dama Haka zata yi, Suna komawa gida Suka dinga dariya suna fadawa Baffa,Baffa Dan boko shi Dole sai anyi Boko Islamiyya Bai damu da yaro yaje ko Bai je ba Amma Boko Dole kaje Kuma kayi kokari Dole,shi yasa yaran Basu wani damu da Islamiyya ba, Haka shima tunda Husna tazo Bai sata a Islamiyya ba,sai dai kullum yace bashi da time,sai ya samu time zai kaita,su Nusaiba kuwa sai suyi wata guda Basu je Islamiyya ba.

Shu'aib da Mama Suka Kara tsanar Husna sabo da Rashin kokari,tana sasu asarar kudi,Baffa ya kalli Husna yace bazan Miki fadan komai ba Husna kina da last chance shine second term, kina dai gani yanzu zamani abinda ya koma rayuwa sai da Ilmi,sai da aikin Gomnati,matukar kikayi aure Baki da Madafa to shike Nan mazaje ba mutunci garesu ba,ciyarwa ma gagara takeyi musu,Kuma ba kowa zai dauki nauyin Karatun Mace ba idan ya aure ta,kin samu dama kinki amfani da ita, Dama sau Daya take zuwa, haba Baffa kasan gaibu ne? Ya kuke so nayi? Haka na rubuta tun a littafina,Haka Allah ya tsara min,Kika tsarawa kanki dai marar kwakwalwa tashi ki ban waje kafin na karyaki cewar Baffa.

Farhan Koda yaje Qatar Babu yanda Abbinsa baiyi dashi ba Kan ya auri zabinsa yaki yarda,Abbi Yana kaunar dansa tilo Dole ya hakura tare da Masa fatan Alheri .
Koda ya dawo Nigeria itama Ummansa Ta takura Dole zabinta zai aura Salma,ba yanda ya iya ya Amince, Mama Da kanta taje Kano ta sanarwa Mahaifin Salma,Mahaifin Salma kuwa shi Haushin Umma yakeji akan ta rike Masa yarsa wato yar- Yar Uwar Umma data rasu sai abinda Umma tace,Sannan Salma sun maida shi Kamar ba ubansu ba tun Kafin Haneefa ta rasu suke Raina Masa hankali,sun maida shi banza sabo shi bashi da kudi,ganinsa Umma ke zuga Masa Yara,Bai San Umma kullum Nasiha takewa Salma ba,Amma Salma Taki ganewa Bata so ma a ga Babanta ace shine ya haifeta.
Mama ta rike Masa Yara bazai iya Mata musu ba Haka ya Amince ya hakura,tare da dangi aka tsai da Rana Nan da 3mnths.

Farhan Dan gata komai sai dai ayi Masa,Amma fa ko magana baya yiwa Salma,ita Kuma Salma Sai Iyayi takeyi tana shige Masa, gashi Masifar tsoronsa take ji.

Farhan Yana kwance a palon Umma saman 3seater yayi pillow da cinyar Umma suna Hira sama sama Yana Shagwaba shi Allah Bai son Auren Nan,suna Haka Salma ta shigo anci wanka,Ko inda take Bai kalla ba,Umma tace Salma babanki fa ya Aiko cewar ki koma gidansa ki zauna a wajen Matarsa har ayi biki sabo da Danginsa ya rokeni Alfarma.

Baki Salma ta turo tace wannan gidan Umma gara kauye da shi Umma,Kuma ki duba yanda Baba yake fa frnds Dina su ganshi suce Ubana haba haba ai ba girma,mutunci na ya zube,mamaki ya Kama Umma da Farhan,Umma tace Salma abin naki har ya Kai Haka? Baki da mutunci? Yanzu wani yaji ai sai yace ban Baki tarbiyya ba,ai ko ya iyayenka suke sune komai naka,sune silar zuwanki duniya a hakan da kike gani,ban taba sanin Baki da tarbiyya ba sai yau wlh.
To ki shirya Dole ki koma can wuce ki bani waje, ficewa tayi tana kunkuni, Farhan Yana jinsu farin ciki ya kamashi dama Umma Bata ganin laifin Salma,sai yace Umma da surukarta Allah ya bar kauna,Kallonsa tayi kawai Amma Umma tasan Wai magana ya fada mata.

Bikin Farhan Yana ta karatowa yayin da Salma Amarya ta koma Gidan Babanta dake Gwale Kano state,gidane na talaka talak Haka take ta musu rashin kunya a gidan yayin da Babanta yake ganin Laifin Umma ne, Ko kawayenta Bata yarda suzo wajenta dan kar aga Babanta talaka,Haka matarsa Har zaginta Salma keyi, Yau da yamma Salma ta aika an siyo Mata Abinci a resturanta sabo da baza ta iya cin abincin gidan Babanta ba Wai Garau Garau ne,Kawarta ce ta gidan su Imran Aliya tace zata kawo Mata ziyara,ba yanda ta iya Haka ta kyale Aliya tazo,Lokacin Baba Yana Alwala a tsakar gida Aliya ta tsuguna har kasa ta gaida shi a mutunce ya amsa Yana Jin Dadi,a hankali Aliya ta tambayi Salma wannan shine Babanki Salma? Baki Salma ta tabe a hankali itama tace ke ba Babana bane Can Dangin Su Umma ne,Karaf a kunnen Baba, tunda yake a duniya Bai taba bacin Rai irin wannan ba,Amma sai ya danne Kamar Bai ji ba,a ransa yace Zan dauki mataki wannan laifin Umma ne Amma ba komai duniya ce.

Tunda Salma tazo Kano tafi Zama gidan su Imran, Yau Saturday ba makaranta yau Husna tayi wanka tare da zuba kwalliyarta ta kauye,ba yanda ba ayi da ita ba ta canja Taki yarda tayiwa Mama Sallama akan zata je wajen Inna Gidan su Imran.
Palon gidan ta Shiga da sallama dauke a bakinta,Salma da Aliya suna ganinta Suka saki ihu tare da kankame juna tunaninsu Aljanna ce sai da Inna taji ihun yayi yawa ta fito sai taga Husna ce,Babar su Imran ma ta fito tasan Husna sai dariya tayi kawai ta koma ciki,Inna tace Yar albarka wannan kwalliyar fa Haka? Dariya Husna tayi tace taki ce Innata,Aliya da Salma lalacewa sukayi wajen kallon baiwar kyau wajen Husna musamman data yi Murmushi Kamar a sace ta.
Sai lokacin Suka gano daga kauye take,Salma tace No wonder,Karaf Husna tace da wando na wallahi a jikina, Alqur'an sai Dana sa Dan diras dina kafin na fito Zaki ce No Wando,to da wandona idan turanci ne ai baza a Gaya Mana ba.

Ido Salma ta zaro waje a fili tace kaga fitsarriyar kauye ke harni Zaki kalla ki iya min magana yanda kike so? Fari Husna tayi da tafi tace sannu kece Azara'ilu? Yo ke har wata mutum ce? Inna tace oh Husna badai tsiwa ba ban son fitana,kin San Farhan? Wanda kike ce Masa Me Sa'a to wannan Itace Zai aura sunanta Salma saura sati biyu bikinsu.

Salma harda gyara Zama tace yawwa Inna Gaya Mata wannan Matar Farhan ce idan kin sanshi a tv ko ya taba Baku tallafi,Da Sauri Husna taja baya tare da karewa Salma kallo tace cab anan dai me Sa'a baiyi Sa'a ba, yanzu ya rasa wacce zai aura sai ke wata karmashashiya dake kunne Kamar balangu, wlh matukar ya aureki na daina kula me Sa'a har abada,ko a Hanya na ganshi ko kallonsa bazanyi ba bare na Masa magana ehe, Salma Baki bude tace Aliya wannan kuwa kalau take? Ke har kin Isa Farhan ya kalleki bare magana har kike ikirarin daina kulashi, dariyar takaici Husna tayi tace Inna ki fada Masa idan yazo bana Nan Kar ya sake ya auri wannan ba mace bace,tana Gama fadin Haka ta shige dakin Inna,Inna tabi bayanta tana fada bana son Tsokana Husna wannan yarinyar kin San Halinta kuwa? Fada da ita baya mutuwa masifaffiya ce,Husna ta daga hannu sama tace yo aini Alhmdllh Haka nake so,aini da Kika ganni bana son a zauna lafiya nafi so kullum a dinga masifa,Inna nifa Wanda take da mutunci ma bana abokantaka da ita,nafi son Marar mutunci, Auzubillahi Inna ta shiga ja,tana salati,Husna Kuwa dariya ta dinga yi.

Salma an barta da bakin ciki ya kamata ace ta yiwa Husna dukan da zata kasa tashi,Haka ta zauna tana jiran fitowar Husna,sai wajen Magrib sannan Husna ta fito daga dakin Inna zata tafi gida,Salma tace yawwa ke Mai maita abinda Kika ce dazu Dan ubanki,Husna ta galla Mata Harara sai da taje bakin kofar fita tace In Allah ya yarda me Sa'a bazai aureki ba, Inshaallah sai an fasa auren Nan naku,Salma ta mike a fusace kafin Husna ta arce ta damko ta,Inna tana ke Salma ki Bari wlh karki taba min jika,Salma sai da ta Mari Husna,Husna taji zafi tace in Allah yarda kwarankwatsa sai ta Fado miki, InshaAllah Me Sa'a bazai aureki ba,Inna ce ta rike Salma tana Mata fada,haba Salma da girmanki,yaushe Zaki biyewa Husna yarinya ce ai,kiyi hakuri koma Palo,Husna tuni ta Gudu gida,Salma Haka ta Gama bacin ranta ta hakura.

Sosai Umma ta shiryi bikin danta na cikinta da Daya tilo,abokai daga kasashe ma an gayyace su,Haka gida Nigeria su Imran Ana ta zuruftu ba Zama,bangaren Amarya ma Haka,Ana ta shirye shirye ba matsalar kudi,Naira tayi Kuka,Lefe na gani na fada akwati goma Sha shidda na lefen Salma.
Ana daura aure za a dauki Amarya a koma Abuja acan za a ci gaba da shagalin biki.

Husna yanzu kullum sai taje wajen Inna ko zata ga me Sa'a yazo ta fada Masa Kar ya auri Salma Basu Dace ba Amma Bai zo ba, Gashi Suma Husna sun Fara Exam ta second term wacce Kuma a lokacin Baffa ya yanke indai Bata yi kokari ba tazo ta karshe aure zaiyi mata Kuma ya Gama yankewa a ransa Wanda zai Bata Dan gidan Alhaji Salisu zai aurawa Tijjani kowa ya huta.

Bayan sun Gama exam again ta karshe ta sake zuwa Baffa ya Gama fushinsa ya hakura Amma aure ba fashi domin Nan da sati Uku yake so a daurawa Husna aure.
Inna har gida ta kawowa Baffa Iv din bikin Farhan tana gayyatarsa,Bai San su ba Amma Dole zaije yanda Inna ta taimakeshi ai Dole ma yaje.
Husna Bata fasa zuwa gidan Inna ba Neman Farhan ta fada Masa Kar ya sake ya auri Salma Amma Bai zo ba.
Har ta gaji ta hakura tace ke Husna Ina ruwanki yayi ta aurenta can da yawarsa.

Amarya ansha gyara anyi kyau,kawayen Amarya gidan su Inna tayi musu Masauki kafin a daura aure su tattara zuwa Abuja tare da angwaye aje can Kuma a Sha shagali.
Ana gobe Daurin aure gaba Daya Abokan ango kusan duk sunzo a Kano zasu kwana Hotel aka Yi musu masauki,Ango ne sai gobe zaizo ranar Daurin aure,Umma tana can da mutanenta Yan Uwa da abokan arziki,Baban Farhan ma da tawagarsa suna Nigeria za a daura dasu,Washe Gari Ango baiyi wani nuku nuku ba Dan yasan auren Nan ba fashi sai anyi shi,kawai yayi shirinsa Imran da Ayman suna gefensa manyan abokai,Ango cikin fararen shadda Yar gaske kyau Kam ba a magana abinka da fari ga kyau kamar shi yayi kansa,Ita kanta Umma kallon Dan nata takeyi kamar Bata sanshi ba,tana tsokanarsa Angon Salma, jajayan lips dinsa ya turo gaba tana fesa Masa turaruka,itama ta Gama shirinta cikin Danyen lace na Alfarma da kawayenta su biyu suka bi jirgin Ango aka tafi Kano dasu Umma cewar ita farin ciki baza ta iya jira ba Gwara tana Kano kusa da inda za a daura auren tana ji da kunnenta a speaker a daurawa danta aure data Fi so a duniya,Abbi ma tuni da Yan Uwa suna wajen Daurin aure a babban masallaci dake kusa da gidan Baban Salma.

Salma shaddarta iri Daya data Ango, tana cikin gida dasu Aliya Ana murna Ana jira aji sanarwa.
Lokacin mutane sun cika iya cika daga kasa daban daban abin ba a cewa komai,Farhan kamar zaiyi kuka duk sabo da shi aka taru gaskiya ya godewa Allah,Umma suna ciki tare da matar Baba Suma suna jira a daura.
Lokacin Husna tana tsakar gidansu ta hau keken Aliyu tana ta tukawa tana koya,daga ita sai dogon wando da Yar Vest kanta ba dankwali gashinta Yana yawo a bayanta dogon gaske.
Ihu takeyi kawai tana zaga gidan,Baffa da Ya Kb Sun tafi wajen Daurin auren sabo da Inna.

Suna zuwa Wajen Suka shiga Kusa da Ango Suka zauna Basu San juna ba,Aka bada kudubar Daurin aure,Baban Salma ne yace Kai a dakata na fasa daurawa yata aure a matsayina na Ubanta,wannan yaro Farhan na fasa bashi 'yata sabo da wani dalilina Wanda daga Ni sai Allah, Mamaki ya Kama mutane aka Fara kuskus,Farhan yaji kunya matuka,ya muzanta,baiji Dadi ba,mutane zasu ce wani Hali ne dashi na banza,an Bata musu lokaci,anyi asarar dukiya,an yaudaresu, Farhan bashi da abin cewa kawai ya zauna Kamar gunki,Abbinsa Allah ya Kara yayiwa Umma a zuciyarsa gashi tace sai ya auri Yar uwarsa jininta to ga Abinda ya faru,Baffa yaji ba Dadi Kam,Farhan ya bawa kowa tausayi domin zaton mutane auren soyayya ne,Baffa yace yaro Kaine Angon? Imran yace ae wlh Shine yanzu ya zamuyi kenan? Sai dai a sallami dubban mutane? Baffa yace Ga 'yata idan har kana so a daura da ita, Yarinyata Bata da makusa sai dai a kauye ta girma akwai Shirme a kanta bazan boye muku ba,Mutane dai sunga Baffa suna ta kus kus da Imran abokin Ango.

Inna Babar Alhaji Dan Gwal ta sanni tasan asalinmu,Karaf Imran Yace Inna ai Kaka tace,Baffa yace Alhmdllh to tasan mu tasan danginmu,idan ka Amince gata Nan sadaki kawai zaku bani a daura sabo da ku fita kunyar jama'a Amma sai kayi hakuri sabo da yarinya ce 16yrs take,Imran ya Kama murna yace ba komai idan ka Amince,Kb yace Baffa ka fasa bawa Tijjani auren Husnan? Baffa yace ae Allah yasa ma ban furta musu ba,Farhan ya kalli Baffa sosai sai yaga ya Masa kwar jini sannan ya Kara ganin mutuncinsa Wanda ya sanshi ma yasan waye ya hanashi auren yarsa,Wanda Ummansa ta rainar Masa Yara tun suna Kanana har suka girma ya hanashi auren yarsa,yau sai ga bare Wanda Bai taba sani ba ya bashi yarsa guda ko asalinsa Bai bincika ba ya bashi yarsa shi Kam ko Akuya ce yarinyar ai ya aureta ya huce takaici.

Baffa ne ya katsewa Farhan tunani yace Yaro Farhan idan baka so ba damuwa, Farhan sai lokacin ya iya magana da cewa Ina sonta na gode Allah ya saka,Nan take Baffa ya nada waliyyan Amarya, Sadaki Dubu dari ba tare da Bata lokaci ba aka sanar An Daura auren Farhan Elmustapha da Husna Shu'aib Yafendo.
Tuni Imran ya shige cikin gida Neman Umman Farhan, duk Matan dake gidan sunji sanarwar daban duk gida ya rude sun hargitse,Imran ne ya tsaya tare da yiwa Umman Farhan cikakken bayani,Ran Umma ya baci,ita tausayin ma danta ne ya kamata da Salma dake mutuwar sonsa,Amma Baban Salma Bai Mata adalci ba,ta wani fannin Kuma farin ciki ya mamayeta da taji wani can ya rufa musu asiri sun fita kunyar mutane Basu ji kunya ba,Imran Yace Umma Amma fa yarinya ce ance 16yrs,Umma tana murna tace ko yau aka haifeta An gode.

Bayan mutane sun watse komai ya lafa Farhan suna ta kashe pics aka Gama,Umma ta Nemo Baba tace naji komai,Amma Dan Allah ko zaka iya Gaya min dalilinka na Hana auren yarka? Baba da masifa yace ba ruwanki ki dauki danki ku bar min gida,Yata Kuma Salma a bar min abata anan baza ta biku ba aini na haifeta ba Ke ba,kuje can ku karata Kuma tsakanina dake ban yafe ba Allah ya Isa,Umma ta rasa kan zance tace hm ba komai watarana zaka Yi Nadama ta fice Masa a gida.

Tunda Salma taji me ya faru tayi Suma ya Kai biyar sai asibiti aka kaita Bata San Husna Farhan ya aura ba, idan ta sani ya zata Kare musu?
Umma Da Angwaye tare da kawayenta gaba Daya gidan su Imran suka wuce sabo da yanzu Inna ce Yar jagora zuwa gidan Amarya da sauran bayani.
Sauran Kuma dasu Abbi duk sun tafi Abuja bayan Gama Daurin Aure.
Farhan ya Zama Rakumi da akala Baya cewa komai sai abinda akace,Baban Salma ya Gama daure Masa Kai.

Inna tunda taji Labari daga bakin Umma tafi kowa Murna Zama ta gyara ta Basu labarin su Husna kaf data sani,har haduwar Inna da Husna,da fadan Husna da Salma etc,Umma tace surukar tawa Yar rigima ce,Inna tace tasan Farhan ma fa yarinyar don Me Sa'a take ce Masa,a Dalilin zuwa Wajen Farhan na santa,lokacin bikin Imran,Nan take Farhan dake zaune gabansa ya yanke ya Fadi,Aljanar yarinyar nan ga kauyanci da shashanci ace ita ya aura ai kuwa Nan gaba sai dai ya saketa Dan bazai iya Zama da mace irin Husna me tabin kwakwalwa ba,a fili kuwa Shuru yayi Bai ce komai ba sai da Suka huta zuwa yamma bayan Sallar la'asar, Inna tace ku taho mu tafi gidan Amarya taga Angonta.

Dariya akayi gaba Daya Banda Farhan,dai dai lokacin Husna tayi Sallar Azahar ta Kara Fitowa tsakar gida ta hau kekenta tana ta tukawa tana ihu ta cika gidan da karadi, tun safe take tuka keken,Baffa ya sanar da Yan gidan kaf Banda Yafendo Bata San Zancen ba, Husna ce kadai Bata San anyi Mata aure ba,tana ta wasanta akan Keke tana Mama zo ki gani na Iya yeeeeeeeeee,Har motoci Suka tsaya a kofar gidan Bata sani ba,Inna ce a gaba Farhan na bayanta sai Umma dasu Imran,Muryar Inna taji tace gata Nan ma kin ganta tana wasanta,Da gudu Husna ta jefar da keken tace Inna Kin Gama birgeni Inna yau da Kika kawo Me Sa'a gidan Nan,Yau sai ya Samin Albarka Nima na Samu nasibin rayuwa ko na dinga cin jarabawa.

Sharhi Fans nake bukata ba tnx ba etc.




Mai bukata dari biyu ne( 200)
Accnt number 0033441422 Yahaya Garba Muhammad, zenith bank.

WhatsApp number 0803 393 3642 ga masu son tura Number katin waya.

Ga masu Vtu ga Number 09032409668.







AsmaBaffa.
[2/29, 10:44 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…









11-15









Official







By
AsmaBaffa











Page nakine ke kadai ta wajena Yar Aljanna
KHADIJA A HAMZA






Inna ta kalli Husna wacce daga ita sai Vest sai Yan kana Nan nonuwanta gasu nan,Inna ce tayi magana to sauko daga keken muje ciki da Baki nake tafe,Da Sauri Husna ta gyara kekenta tare da parking dinsa gefe,tana zuwa har kasa ta zube tana gaida su Umman Farhan Ina Yini, ya gida,Kunzo lafiya? Ya sanyi? Umma tun tana amsawa har ta gaji race jeki fadawa Mamanki kunyi Baki mu shigo? Husna tace gaku ma tare da Inna ai ku shigo kawai gidan Yan Boko ne ba ruwanmu da wani Neman Iznin shiga gida,ai kawai kowa yazo ruftowa yakeyi,Umma tayi dariya tace to Lallai Amma dai ki fada kice da maza muke,Husna tace Me Sa'a ne fa ba wani bako bane ya sanni tun tuni abokina ne ku shigo kawai mu Yan Boko ne musamman Baffa Kamar Bature Haka yake, Umma tace to mu shiga haka,Inna tayi dariya tace indai Husna ce ai zaku gaji da ji ma,Imran Yana ta dariya a ransa yace ga me surutu ga Farhan Bai son magana,a fili Imran Yace to Yar Boko muje ciki,Husna tayi Murmushi tace ai jiya nayi turanci nayi turanci har bakina sai da ya Fara kumbura gaskiya Bature Yana aiki wata kalma da Zan fadeta sai da Harshena ya Fara radadin zafi,ya Dade yayi jajir, Su Umma Basu San sanda Suka kwashe da dariya ba gaba Daya,Shi kanshi Ogan Farhan Bai San yayi Murmushi bama da kyar ya danne dariyar data taso Masa ta tsaya a Murmushi Wai akan turanci Baki zai kumbura.

Da Sallama Suka shiga Palon gidan Wanda yasha gyara Yana kamshi,Dukkan Yan gidan suna Palo Ana ta labarin auren Farhan da Husna zai Sha hauka.
Tunda suka ga Farhan Suka gane shine Angon, Nusaiba ji takeyi Ina ma ita aka aurawa Farhan,Haka Mama ma sabo da cewa takeyi Husna in Banda kauyanci me zata yi, yaro ga kudi ga kyau komai yaji a dauki yarinya irin Husna a bashi baza ta dangwalo musu arziki ba,Husna Bata iya komai ba ko girki,gata a Yan kauyen ma ita dakikiya ce Bata ganewa,Mama ta zauna ta karantawa Baffa me yasa yayi Haka? Baffa ya nisa yace Ni kaina ban gano hakan ba sai bayan an daura auren,gwara Nusaiba itace baza ta bamu kunya ba zata kula damu ta Nemo Mana arziki a wajensu,Amma an rigada anyi da Husna sai dai mu nuna Mata yanda zata Tara Mana dukiya.

Husna da Bata San anyi aure ba da kanta ta shiga kitchen ta dinga jera abin ciye ciye da shaye shaye har Wanda Bai kamata ba sai data kawo gaban su Umma,da gudu Kuma take kawowa ta ajiye ta koma ta kawo wani har sai da ta gama sannan ta zauna kusa da Inna ta nutsu, Baffa ne yace Bismillah fa kuci Abinci Inna,Kadan Suka tsakura suka ce Alhmdllh shi Kam Farhan da yake ta faman danne dannen waya lemo kawai yasha,Inna tace Alhmdllh Ashe Haka abin Alheri ya faru Amma munji Dadi Allah ya saka,Umman Farhan wannan shine Shu'aib din,Umma tayi Murmushi tare da furta kalaman Godiya har ma Bata San ya zata godewa Baffa ba,Mama tace ba komai Haka Allah ya tsara ai wannan rubutacce ne,A Nan Umma ta Basu tarihinsu kaf da danta,Su Mama sunji Dadi ko ba komai sun San Dole Suma su Zama masu kudi,karshe Addua sukayi sai Mama tace Amma Muna Neman Alfarmar a bar Mana Amarya ta Kara ko 3mntths ne sabo muyi shirinmu muma tunda abin yazo Mana bakatatan, tunanin Su Umma tsakani da Allah Baffa ya Basu auren yarsa.

Murmushi Umma tayi tace ah haba ai Nima ta Zama yata duk abinda iyaye zasu yiwa yarsu na dauki nauyin komai,sannan lefe ma zamuyi Inshallah,da Sauri Baffa yace a'a bana bukatar lefe tunda an biya sadaki shike Nan duk wani abin Bama bukata, Umma taji Dadi gaskiya sun auri Yar manya har Bata San Dame zata sawa Baffa ba,Number waya Suka yi exchange da Umma sannan Umma tace an Zama Daya yanzu tsakaninmu zumunci ba yankewa,Allah ya bamu ikon saka muku muma Kamar yanda kuka Mana, ba komai ai yiwa Kaine cewar Mama.

Husna tana ta kallonsu suna ta Hirar biki yayin da aka yanke Nan da sati biyu za a zo a dauki Amarya,Husna tana ji tace Wai Mama wa aka yiwa aure? Sai lokacin Baffa ya tuna Basu fadawa Husna ba.

Kallon Husna Baffa yayi yace Husna kin San dai Alkawarin dake tsakaninmu ko? Na fada Miki dama kina Gama Second term Zan aurar dake? Husna tayi Murmushi tare da cewa ai nasan Wasa kakeyi ko? No ba Wasa nakeyi ba yanzu Haka Husna kina da aure,yau Allah yayi an daura Miki aure da Farhan gashi Nan kina ganinsa sabo da Haka kiyi shiri Saura sati biyu a kaiki Abuja dakin mijinki.

Zumbur Husna ta Mika Mama da Baffa duk sun tsorata sunyi sun san tabbas Husna sai ta Basu kunya,sai da ta samu jikin banko sannan ta tsaya Kamar gunki,Farhan lokacin ya Dago kansa sukayi Ido Hudu da Husna,sai gani akayi Husna ta Kama bango ta rungume tana satar kallon Farhan tana murmushi Wai kunya takeji ita,sai ta kalleshi sai ta juya da sauri ta boye Fuskarta a jikin bangon,sai yanzu taji kunyar kayan dake jikinta, yatsa tasa a Baki tana tsotsa tare da Kara rungume bango, da gudu tayi dakinta.
Duk ta Basu dariya Banda Farhan Wanda ke galla Mata Harara, said wurin 5pm sannan su Umma Suka ce zasu tafi a Kira musu Husna suyi Sallama,Husna harda sa Katon Hijab ta fito tana sadda Kai kasa,sai Wasa takeyi da yatsunta.

Umma tace zamu tafi Zaki ga Inna da sako,Kai kawai Husna ta daga irin Amaryar Nan,Umma kudi masu yawan gaske ta ajiyewa su Baffa sannan suka fita Baki daya, ya rage daga Umma sai Farhan da Husna,Umma ta kalli Farhan tace ka tsaya

Please Login or Register in order to submit comment