Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Husna wacce ke harkar gabanta ba ruwanta,Amina tace ita wannan ma Bata damu ba ko a jikinta uwarta guda,da Yafendo ce sai ta damu Amma dake Mama ce ba ruwanta gaskiya Mama canja Miki yarinya akayi da asiri na manta Uwa,Nima Haka nake tunani cewar Kb, Husna ko inda suke Bata kalla ba sai data ji Amina tace me bakar kafa tunda tazo Alheri ya daina zuwa gidan Nan sai sharri yanzu gashi Mama an koreta daga aiki.

Husna tace yo Ni nace a dauko Ni daga kauye? Ko nace a dakko Ni? A maida Ni Mana idan anyi zuciya,Kuma da kuke cewa nice me farar kafa kune Baku yarda da kaddara ba,dama Haka Mama ta rubuta da hannunta littafi Kuma ya bushe bare ayi gyare gyare,ai Allah yace kowa da hannunsa ya rubuta komai nasa na rayuwarsa arzikinsa,ajalinsa,wuta ko Aljanna da sauransu,Mama data dauki Alkalami tace Ni Nurse ce ya Allah Amma Za'a kore Ni sanadin bawa Mara lafiya magani ba bisa ka'ida ba, sannan Kuma kuce Ni na jawo Dama Haka ta rubuta,ke Anty Amina wa yasan me kika rubuta mummuna da kanki, Ni ba Gashi ba da Hannuna na rubuta zaman kauye,idan mutum Aljanna ya rubuta Allah zai bashi ikon yin aikin da zai shiga Aljanna,Haka wuta ma,Dan dako zaka Zama,Dan garuwa,Gomna duk ka rubuta abinka da Kuma sanadin faruwar abin.
Mama mamakin Husna ne ya cikata data iya musu wa'azi Haka me shiga jiki,duk Basu tuna Wannan ba sai ga Husna da suke ganinta Jakar kauye tayi musu Nasiha sosai Amma Kuma yanda ta fada ka rantse masifa Takeyi, batayi da suffar Wa'azi ba sai ma rashin kunya da Haka ta furta sannan tayi tafiyarta dakinta, duk Sunyi Shuru tabbas Husna gaskiya ta fada Amma Basu dauka maganarta ba.

Umman Farhan ce ta shiga Bedroom dinsa a fusace,Yana cikin bargo a hadadden bed dinsa Yana bacci Umma ta Dana Masa duka da karfi,da sauri ya farka a firgice sai yaga Ummansa ce,gefen kafarsa data duka ya shiga shafawa Yana Haba Ummana yanzu idan kaina ya Fara ciwo fa? Yayi uban ciwo ma,sau nawa Ina turo Salma ta tasheka kaki tashi har Sha biyu ta wuce baka Yi Breakfast ba,Farhan Wai yaushe zaka Yi hankaline? Gata da Jin Dadi ne yayi maka yawa,na gaji da maka aiki Ina juya maka dukiyarka ya kamata ka taimaka min karfi na karewa yake Yi,ubanka ma sai aiki yake maka Dana hannunsa kasan yanda ake komai Farhan Amma baza ka iya aikin ba,ya dace ka Zama Namiji cikakke?

Ta sigar sangarta da Shagwaba yace Ummana na kusa shiryuwa fa,kiyi ta min Addua karki Yi fushi kinji,yanzu Farhan Haka zamu ci gaba da Zama daga bacci sai kaci ka sheka wanka aikinka kenan,frnds ma sai dai suzo wajenka idan sun matsu,ba laifinka bane ubanka ne ke sangar taka,Umma Hutawa nakeyi fa kin San Nasha wahalar bikin Imran sai Dana dawo Abuja Kika ce sai na koma Kano washe Gari kin San it's not easy, Baki Bude Umma ta saki Salati Farhan bikin da anfi sati biyu da yinsa shine har yanzu gajiya kake hucewa? Gajiya fa Farhan 2weeks da biki fa, Kai ko dai Aljanu gareka Dan ubanka mu tafi wajen malamai? Dariya Farhan Yayi ba shiri yace Kai Ummana wlh da gaske a gajiye nake tun lokacin jikina ciwo,a jirgi fa kaje Securities ne Suka Kai motocin ba komai Zan dauki mataki a kanka Farhan ,aure zakayi Dole sannan na sallami Securities din Baki daya kana driving da kanka,Dariya ya Shiga Yi yace Umma kin San ban iya ko Keke ba bare mota,Sai lokacin ta tuna Farhan ko mota Bai iya ba sai dai a tuka shi tunda ya taso a duniya da guards kusa dashi ko Ina domin Babansa ne ya Bata shi sabo da Kudi ya ratsa su.

Alright ai ga Salma Nan Kanwar Haneefarka tunda Haneefa ta rasu dama Salma na sonka sai ka aureta ko zaka Yi hankali, fuska ya Bata Allah bana sonta Ummana,To sai ka Fara Shirin tafiya Qatar Abbinka yace shima yayi maka Mata acan balarabiya Yar uwarsa yake so ka aura,don ya sanar Dani a waya,wlh Farhan ka sake ka amshi tayin Abbinka to karka dawo wajena Babu Ni ba kai kaji na fada maka,ka Fara Shiri ma.

Nifa Umma ban shirya aure ba,wa Zan aura bayan wacce nake so ta rasu Kuma Ni ai bazan iya soyayya ba,oho maka to kaji dai Ni zabina Salma shi Kuma ubanka yace Yar uwarsa sai ka zabi Daya,Murmushi Kawai yayi a ransa yasan Babu ko Daya ciki da zai aura Dan Bai son ko wacce cikinsu Kuma yasan Iyayensa suna sonsa baza suyi Masa Dole ba.
Salma kuwa tana labe tana Jin Haka ta cika da murna dama ta Dade tana kaunar Farhan,ta nuna Masa hakan Amma ko saurararta baiyi ba.

Husna ta Fara zuwa Schl kullum dariya ake Mata a makarantar sabo da Bata San komai ba,Bata iya komai ba,sabo da kyanta Ana kaunarta Amma tunda aka ga jaka ce sai kowa ya daina saurararta a schl din tasu, Bata Jin dadin makarantar sabo da kiyayyar da student ke nuna Mata, ita kadai take Zama a bench,malaman ma Sam ba ruwansu da ita sabo da Bata da kokari,ganin Haka yasa Husna ta tsani kowa itama,ta kulle a niyar Fara tafka rashin mutunci akan kowa daga malamai har dalibai.
Yau Monday suna aji Wata malama me shegen iyayi ta shigo tana musu Agriculture, burin Malama Latifa ta fito da Husna gaban aji tayi ta Mata tambayoyi na rainin hankali a gaban Yan aji tana kunyatata,sabo da Bata Jin turanci,tunda Husna taga Latifa ta shigo hankalinta ya tashi yanzu zata wulakantata a gaban kowa,ita Latifa haushin kyan Husna takeyi yarinya sai shegen kyau shi yasa ta tsani Husna.

Ido Suka Hada da Husna,Malama Latifa tayi Murmushi tace can i Helf u? Husna ta gane Ma'anar Helf kadai, sai ta mike tsaye tace Malama Latifa ki cire Helf din nan sabo da ke Baki Isa ki taimaka min ba,sai ma nice nake taimakonki sabo da kudin makarantar da nake biya dashi ake biyanki Albashi har kike wannan Iyayin,Ni Husna Nice nake taimaka miki.

Yan aji sukayi Shuru wasu suna dariya kasa kasa,Latifa tace da turanci Zaki fada min,Yaren turancin ai bana ubanki bane cewar Husna, Ni Kika zaga? Kwarai kuwa Latifa Hausa itace yaren ubanki,ko Ubanki a America aka haifeshi? Ai baza ki birgeni ba sai kin fito kince Zaki ja da malaman addini.
Latifa ranta ya baci da irin zagin da Husna tayi Mata a gaban dalibai,tace wlh yau sai na sauya Miki kamanni,Tazo ta Fara dukan Husna da katuwar Bulala Husna ta kwalla firgitacciyar Karar da duk makarantar sai da aka firgita kowa ya fito waje,Husna Kuwa ta damki wuyan Latifa ta Shiga yin Aljanun karya tare da kwace bulalar ta dinga Zane Latifa tana yayyaga Mata kayan jikinta,dama Latifa Bata fi 25yrs ba gata Yar gajeriya ba kiba,Husna sai da tayiwa Latifa kaca kaca da jiki,Malamai Suka shugo agaji,da kyar aka kwaci Latifa.

ita Kuma Husna ta Fadi a kasa tana ta Shure Shure da ihu da birgima tana fadin Ku tafi Dani Bahar maliya na huta a cikin teku,ku kaini Nasha kumfar Bahar maliya ko zanji saukin zuciyata yiiiiiiiiiii ta Kara fasa ihu harda hawayen karya taci gaba da Nuna pc tace Aljana Farisha Ina son pc ki dauko shi a fiffkenki mu tafi dashi Can Kan dutsen Libiya, Pc Yana Jin Haka ya Fara karanta Ayatul kursiyyu a zuciyarsa ya fice da sauri ya bar ajin, malaman masu karfin Hali sune sukayi ta tofawa Husna adduoi Basu San karya takeyi ba,sai da Suka Dade sunayi sannan ta Fara tarin karya da atishawa sai tayi lagaf sannan ta mike tana dube dube irin Wai Bata San tayi komai ba,tana me ya faru wayyo me na aikata, malamai da Yan aji yanzu kowa ya Shiga tsoron Husna,tace wayyo Allah yasa banyi kisan Kai ba? Ku fada min ban kashe Latifa ba? Haka rannan ma ban sani ba na kashe wani Malamin a kauye,sai kowa ya Kara firgita duk abinda Husna tace shi akeyi.

Malama Latifa tafi kowa tsorata da Husna tace haba nasan wannan dukan sai Aljanu hannunta kamar Katako Haka,Yar yarinya da karfi Haka ai wannan sai Aljanu,PC kuwa meeting yayi da malamai ya tsawatar Kan Kar Wanda ya sake taba Husna ko ya Bata Mata Rai,Dalibai ma Haka aka bada Sanarwa,tun daga wannan Rana Husna Babu wanda ke nunata da yatsa sai abinda taga dama,duk abinda malami ya koya Sam zata ce Bai iya ba, ba Haka abin yake ba.
A gida kuwa Taki yarda Nusaiba ko Kb su koya Mata karatun turanci tace ba uwar da Suka iya zasu Raina Mata hankali a banza a wofi.

Yau Shu'aib Baffa ya kaiwa babban Amininsa ziyara Alhaji Salisu,Bayan sun Gama Hirarsu ta abokai,Alhaji Salisu yace Shu'aib nifa aure zan Kara kwana Nan,na Samu matar Aure, haba Salisu da tsufanka Haka ga Yara Manya sun girma, Allah ya rufa min asiri Ina da abinda Zan ciyar dasu aurena Zan Kara,Kuma Albishirinka? Shu'aib yace goro,Salisu ya washe baki ya furta budurwa ce sabuwa Kar a Leda,gata kyakyawar gaske inda kasan ita tayi kanta,ko Kaine ka ga yarinyar sai kace kana sonta abokina, Baffa ya kece da dariya suka tafa yace mutumina kace ta daban ce, gaskiya ka aureta,Ni kaina kasan na kusa retire a aiki duk sanda na karbi kudin Retire ta aure Zan Kara wlh,na gaji Nima da mace daya Kamar fitilar machine, ai ka Bari Kai dai dama yau zanje da dare zance tace nazo bayan Magrib sai mu tafi ka rakani zance,Suka sake kecewa da dariya Hhhhh shege mutumina hhhhhhh.

Baffa Bai tafi ba suna ta Hirar aure har sukayi sallar Isha tare da Salisu bayan uwar gida ta kawo musu girki sun kwashi gara sai suka tafi zance wajen Budurwar Salisu.
Can wani Dan bayan Gari ne Babu gidaje ko Daya a Nan tace su hadu,Tunda suka karaso wanjen a motar Baffa Baffa ya rude da kyawun matar shi dai tsawon rayuwarsa Bai San da me kyau a duniya Haka ba,yarinya matashiya Wai Kuma take son Dattijo Haka kamar Salisu shi ba wani me kudi ba Kuma,Baffa ya tambayi Salisu kafin su Karasa inda Budurwar take yace Salisu Wai ya sunanta ne? Salisu ya washe Baki yace Ma'kisha, tab to muje cewar Baffa.
Bayan sun Isa Suka gaisa da Ma'kisha sai lokacin Alhaji Shu'aib ya kalli jikin Ma'kisha sai yaga Rabin jikinta irin na Mermaid (Mari babban Kifi) ,Jikin Baffa ya dauki rawa karrrrrr ya Fara ja da baya a hankali Yana sadadawa baya da baya, Salisu Yana Kai Shu'aib meye Haka Wai,me ya sameka? Wai me kakeyi Haka,Baffa sai Daya Bari yayi nisa sosai ya kwallawa Salisu Kira yace Salisu Mari Babban kif.....sai ya Fadi kasa Shirim ya sume,Bat sai Salisu ya nemi Ma'kisha ya rasa ko sama ko kasa ta bace Ashe Aljana ya Hadu da ita Garin son Yan matansa.

Wajen Baffa ya nufa da gudu tare da yayyafa Masa ruwa ya farfado Amma Baffa baya iya ko motsi Yana ji Yana gani Amma baya motsi,Salisu ya fashe da kuka hankali tashe ya Sa Baffa a mota sai asibiti,Sunyi gwaje gwaje ba hawan jini ba Ciwon komai,a asibitin kudi private ya barshi sannan ya Kira su Mama da Kb.

Da kuka Suka shugo asibitin har Anty Amina da mijinta,Husna da Nusaiba suna ta kuka, Sai da Salisu ya fita tare da Mijin Amina Husna tace Mama a Kira Yafendota a sanar mata,Harara Mama ta watsawa Husna tace mu dai zuwanki Babu Alheri a cikinsa,tunda Kika zo masifa take samun mu sai yanzu na yarda da Zancen Amina,Husna ta fashe da kuka tana haba Mama haba Mama Kamar bake Kika Haifeni ba?
Husna ta Karasa kusa da Baffa tana Sannu Baffa Amma Baffa sai ya dauke kansa ya kalli can gefe daya shima ya yarda tunda Husna tazo bala'i yake samunsu shi Daya sani Bai dakko ta ba, Husna ta jinjina Kai Hawaye na tsiyayo Mata tace ya kamata ku dai Yarda da kaddara Kamar Baku da ilmin addini,wlh da Yafendota ce baza tace Haka ba,Ina wayewar taku take?,Zan karyaki wlh Kika ce Zaki Mana rashin kunya anan cewar Kb,Ki bar mu muji da abinda ya Dame mu,ko ya Zaki damu Baki kaimu ba Tunda ke Baki San kowa ba Baki shaku da kowa ba,sabo da Haka matsalarmu ce ki kyale mu ehe cewar Nusaiba.

Ran Husna ya baci matuka tace Amma ai iyayenka iyayenka ne ko mutum dabba ne Dan ban rayu dasu ba ai na Saba dasu Kuma iyaye daban ne, Ni yanzu da zaku ce na jawo muku ai kune ma Kuka jawo min,da Ina can kauye cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali,sai abinda nake so kunzo Kun dauko Ni kullum cikin bacin Rai nake....Mari Mama ta kashe Husna dashi,Husna ta Kara fashewa da Kuka sannan a hankali tace yo Ni nace ki bawa Maralafiya guba yaci ya mutu Kuma ai bani na koreki daga aiki ba,Baba Kuma ai shi ya Kai kansa da Budurwar zuciya me ya kaisu zance wajen budurwa daga ganin kyakyawa, ba Wanda ya kula Husna suna ta shige da ficensu sun kyaleta zaune kusa da Baffa,Sai da suka fita gaba Daya saura Husna kadai.

wajen Baffa Husna ta lallaba kusa da kunnen Baffa ta rada Masa Baffa Kai me ya kaika zance wajen budurwa sabo da Allah? Fada min a hankali bazan fadawa Mama ba,duk halin Daya ke ciki Saida yayi Murmushi Husna Bata Jin magana,shike Nan kyale sirrinka Baffa basai ka fada min ba,Amma Baffa ka yarda da kaddara,kaddara ce ta kaika,Allah yayi hakan sai ta faru,zaka warke Insha'Allah Baffa zamuyi ta Addua kaji,Haka Husna tayi ta kwantar Masa da hankali Kuma yaji Dadi ya samu nutsuwa,Har adduoi ta tofa masa fatiha kafa Bakwai,falaq da nass,sai Iklass,Ayatulkursiyyu da Amanarrasulu tayi matukar birge Baffa duk tafi Yan uwanta don su ko BISMILLAH Basu tofa masa ba, Da warsh ta karanta sannan a wani wajen tana mistake kadan kadan a karatun nata,Mama suna shigowa Suka ji karshen karatun Husna tace warar rarin(waladdawwlin) Akan Baffa tana tofa Masa.






Fans masu bukatar siyen wannan Novel din Naira dari biyu ne (200)
Yanzu Free pages nake bayar wa kafin na Gama bayarwa.

Ga masu son Siya ta hanyar bank Transfer ga number Kamar Haka
0033441422 Yahaya Garba Muhammad, zenith bank.

Idan Kuma numbobin katin Waya zaki turo ta WhatsApp sai ki min magana ta pc ko ki kirani a waya ta wannan number 0803 393 3642 ga masu bukata.

Masu son yin Vtu ga number 09032409668.



Allah ya Baku ikon Siya kafin na Gama Free pages fans.

Ga Wanda Basu samu damar siya ba Allah ya bar kauna Ana tare iya wuya duk fans ne Ina kaunarku.


Masu Sharhi pls ayi min Sharhin novel din ko naji Dadin typing da wuri na daina sheka bacci.🀣πŸ₯°πŸ₯°


Daga yau kullum Za ayi posting Insha'Allah Babu Bata lokaci.








AsmaBaffa
[2/29, 10:44 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…










6-10








Official








By
AsmaBaffa





Fancy Honey,Hadiza Mukhtar, Maman Abba,Zainab Atiku salama,Mrs Mukhtar and Maman Fahad
Ina Miko gaisuwa page naku ne.








Baki Amina ta tabe tare da cewa dan Allah Nusaiba ku tafi gida kuyi Abinci kafin a sallamemu sunce cutar Bata asibiti bace gida zamu koma ayi na Islamic.
Husna da Nusaiba a Daren Suka Shiga Napep zuwa gida, Husna Bata iya girkin komai ba Nusaiba ce tayi gaba Daya, a Daren su Mama Suka dawo da Baffa Wanda ko motsi baya yi abin tausayi.
Tun daga wannan Rana suke kashe kudi akan nemawa Baffa lafiya Amma abin yaci tura.

Aikin da Kb yakeyi ba wani kudi ne masu yawa ba,Mama an koreta sai dai Albashin Baffa Dana kb duk komai nasu ya Fara karewa a Neman magani,Kadarori Wanda Suka dan Mallaka duk sun Kare an siyar an kaiwa malamai daban daban gari Gari, Kullum gidan cikin kunci suke ba walwala,Nusaiba Da Husna suna ta zuwa makarantarsu,makarantar Nusaiba da Autansu Aliyu schl dinsu Daya,Husna schl dinta daban,tana Nan ka rantse ba a birni Husna take ba Taki wayewa yanda tazo Haka take sabo da ba a koya Mata sannan Kuma baza ma ta Bari a koya Mata ba,kwalliyarta da komai tana yin abinta na kauye.

Bayan wata biyu,Baffa yaki samun lafiya komai nasu ya Gama karewa sai Albashin Kb Dana Daddy Amma cutar Bata barin salary ga Schl na Yara da ci da Sha dukka,bukatun sun yiwa kudin yawa, tun suna maganin ma har sun gaji an hakura sai Addua da sukeyi kawai.
Tun Yafendo Bata sani ba har tasan halin da Dan uwanta ke ciki, Babu irin taimakon da Bata kawo ba itama da kudinta.

Husna gaba Daya suna Palo Suka ji Sallama,sai data shigo Suka gane Inna ce Ashe wacce Husna taje gidan Suka Sha biki,da Fara'a Mama ta tarbeta,Husna Kuwa Kamar sun Shekara dari Haka ta buga ihu tare da makalkale Inna har sai da Mama ta harareta sannan ta nutsu, Suka gaisa Inna tace Husna sai naji ki Shuru kuma ai gani nazo da kaina,Dariya Husna tayi tare da cewa Bari na fada Miki gaskiya Inna nace zanzo Mama ce ta hanani Wai Bata son shige shige,Nusaiba Kanwata ta zugata,tsuru tsuru su Mama sukayi Husna ta kunyatasu, Inna tace ba komai ai hakan ma tarbiya ce gashi Ni nazo sai naji yaushe Zaki zo? Ni dai bazanzo ba da ace me Sa'a zaizo ne sai nazo,waye Kuma me Sa'a? Inna ta tambaya tare da Mama,Nusaiba tace wannan Dan masu kudinfa take nufi Wanda ake yawan nuna shi a TV ya Kai ziyara makarantu ya bada Tallafin marayu etc, Inna tayi magana Farhan abokin Imran take nufi,ai mu Dan gidanmu ne,Business ne ya Hada Mahaifiyarsa da Baban Imran shine sanadin alakar har ta girmama haka Farhan ya Zama abokin Imran sukayi karatu tare Kuma.
Allah sarki Cewar Mama data kawowa Inna ruwa da lemon gongoni.

Husna ce ta Shiga bawa Inna labarin cutar Baffansu,Inna ta tausaya kwarai tace akwai wani Malami a kauyenmu can Maiduguri Zan Masa waya a gwada nasa ko Allah zaisa a Dace,Mama a fakaice ta tabe Baki irin ba Yi zaiyi ba,a fili Kuma tace mun gode Allah saka,idan kunyi magana dashi sai ki sanar Mana, Inshallah Har gidan Nan Zan kawo malamin ai an Zama Daya ba komai.

Bayan Inna ta tafi gida da kwana Uku sai gata ta dawo da Malamin yazo ganin jikin Baffa,su Kb ma duk Basu damu da Malamin Inna ba gani sukeyi ai irin wajen maganin da sukaje Sunyi yawa ba a Dace ba sai wannan malamin wani tsoho dashi kazami.
Malamin Inna ya duba Jikin Baffa da ko motsi bayayi yace ai wannan me sauki ne ma Inna shafar Aljanu ce, a kawo min ruwa a cup,Husna ta kwashe da Gudu ta kawo ruwan, Malamin ya tofa Addua a cikin ruwan sannan ya bawa Baffa a kwancen yasha kadan ya shafe Masa jikinsa,minti biyar tsakani sai ga Baffa Yana motsi a hankali,sai gashi ya mike Garau ka rantse baiyi jinya ba,Gida ya rude da murna da farin ciki,Mama ta Kira Anty Amina,Yafendo,Alhaji Salisu da sauran Yan Uwa da abokan arziki ta sanar musu samun lafiyar Baffa,Baffa sabo da Murna harda kuka,sun rasa da wanne Baki zasu godewa Inna,da farko sun Raina abin,Baffa ya dinga Godiya Mama sai fada takeyi tana wacce Husna ta kwana a wajenta ce,Sai lokacin Baffa ya tuna dukan Husna da sukayi Ashe gashi sanin Inna shi yayiwa Rana ta taimakeshi,Godiya yake zubawa Inna ba ji ba gani,Inna tace Haba ba komai,Kudin aiki nawa za a biya? Kb ya tambaya,Inna tayi Murmushi tare da jawo Husna jikinta tace komai danayi nayi shi sabo da Allah sannan sabo da Jikata Husna,kudin aikin malamin dubu dari biyu ne Amma na rigada nasa Dana Ya biya kudin maganin sabo da Husna Jikata,Allah ya Samin kaunarta Haka kawai,Nusaiba taji wani Dukul takaici ya cikata ba ita ake so ba.

Baffa kuwa Murna ta hanashi magana yaci arzikin Husna Alhmdllh,Suna Haka sai ga Yafendo ta dira itama Husna ta fada jikinta tana Ihun murna,Yafendo tace ja'ira ai Ina Hanya Mama ta buga min waya na karaso da karfina,Alhaji Salisu ma yazo da iyalansa da farin ciki.

Bayan kwana Uku komai ya lafa Yafendo kwananta biyu ta koma kauye,Husna Bata ji Dadi ba,ji takeyi kamar tabi Yafendo su koma,Baffa ya koma bakin aikinsa tuni yanzu Alhmdllh komai sai kawai Husna da suke Dan takurawa a gidan.
Husna Exam zasu Fara ranar Monday ta first term, Anyi anyi tayi karatu Taki Yi,Baffa bakin ciki Kamar ya hadiyi zuciya yace Husna kin manta maganata second term Kika dauki ta karshen aji wlh sadaka Zan aurar dake Babu fashi bana magana biyu, Baki ta turo tunaninta Baffa bazai iya ba.
Ranar Monday ta fito cikin shirinta na Uniform zasu Fara Exam Mama tace shashasha a Haka Zaki ci Exam din? Ko kinyi karatun? Husna ta kalli Mama tayi dariya tace Ai da Ka Zan daketa Mama anfi ci,Ai idan kana lallaba Abu to baka Samunsa Amma idan ka dake shi da ka irin ko ka samu ko ka rasa baka damu ba to kafi Samunsa,Cinyewa zanyi zaku Sha mamaki wannan Award din da ake bayarwa duk Term to Ni Zan cinyeta,Nusaiba ce ta fito tana karatu tayi shiri itama,Auta Aliyu shima Yana ta Buda littafi suna karatu Kb ya tafi kaisu a mota Amma Husna kudin Napep ake Bata ba Wanda ke kaita schl.

Exam sukeyi kullum har suka Gama sati daya,Ranar Friday aka Yi musu Hutu,Ranar Saturday aka sa musu ranar suje su karbi result sannan za a raba kyaututtuka ga masu kokari etc.
Husna tafi kowa Murna Harda Bawa Baffa labari tace Baffa,yayi zaton wata Maganar kirki ce yace Naam Ina jinki,Tace naji a jiki na Ni Zan Lashe kyautar Nan, don Haka kuyi shiri da karfin gwiwa,Baki Baffa ya tabe yace sai dai Kb,Amina da Nusaiba suje zasu bamu labari Amma Ni da Mama baza muje ba, Allah ya kaimu goben cewar Husna.
Da kyar ta iya bacci tana ta faman tunanin kyautar gobe da zata Lashe,washe Gari Saturday da wuri ta shirya,Kb,Nusaiba da Aliyu sun shirya zuwa susha kallon Husna da gaske itace ta lashe kyautar ko karya ne,Anty Amina ma tace zata je schl din su hadu a can.

9am makaranta ta cika makil da dalibai tare da iyayensu, Husna wacce ba Wanda ke kawo Mata raini tana ta shige da fice a schl din,su Kb Ana gefe,Yan Ss3 aka Fara rabawa result,har aka zo Kan su Husna jss3,Husna ta gyara tsaiwa Ana damkawa kowa nasa itama Husna ta karbi nata tare da komawa gefe ta bude, kaca kaca yake da rubutun Jan biro,itace tazo ta karshen ta 120 dari da ashirin.
A karshe Kuma aka rubuta Mata *wake Up*, jikinta yayi sanyi sai Kuma ta Fara kuka,su Nusaiba suna kallonta abin dariya ma ya Basu ai dama sun San baza ta taba ci ba Gwara kawai ayi Mata aure.
Bayan Husna ta Gama share hawayenta sai tazo gaban su Kb tace to sai me banci ba sai akayi Yaya? Sai na Mutu? Auren sadaka ayi min Mana sai na fasa rayuwa,Dalla daina Mana boring kunya Bari muga kyautar Taki sai mun ga me za a baki cewar Kb.



Please Login or Register in order to submit comment