Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka sa a shara,dauko abinta tayi ta koma daki,
Nusaiba tana kallonta taje ta fadawa Mama abinda Husna tayi.

Sai ga Mama a fusace tana shiga dakin tace Dan ubanki me Zaki ajiye Mana Tsumma a gida,Ni sa'arki ce? Ga sababbin Kaya Nan komai akwai me zamuyi da Tsumma, Baki Husna ta turo gaba tace Ni dai Ina son kayana Yafendota ce ta kashe kudi ta dinka min tare da Affana.
Mama a ranta tace an cuceni kawai an rabani da yata Bata kaunata sai Yafendo, Haka kawai sai shedan ya shiga zuciyar Mama ta Fara tunani na daban akan Yafendo sai dai idan asiri tayiwa yarta na manta Uwa gashi Husna ko kadan Bata kaunarta, kallon Husna tayi tare da fisge kayan na kauye Wanda na Yafendo ne data dinka Mata,waje ta fitar dasu ta Cinna musu wuta suka kone kurmus, Husna tana gani ta barke da kuka sannan ta fito Tsakar gidan da daura kirjinta na Towel tana ta kuka.

Babu Wanda yacewa da Husna ci kanki har sai da da Baffa ya dawo da sauri ya fito daga motarsa Yana tambayar Husna lfy? Da hannu ta nuna Masa ba Mama bace ta kwashe kayana ta kona min Kuma Yafendo ce ta kashe kudi ta dinka min,an San haka birni take za a kawoni Ni na fasa Zama a maidani kauye, Baffa ya gane Maganar Gaskiya Husna tafi Mama gaskiya Amma sai yace to kiyi hakuri watarana zansa Yafendo ta dinka Miki wasu,cikin kuka Husna ta Furta Amma Baffa kasan hakan Bai Dace ba,Kuma a dinga Wulakantani me nayi musu sabo da Ni Ina kauye,? Tunda nazo gidan Nan ba Wanda ya saurareni Bayan gaisuwa shike Nan ba Hira ba komai kawai Ni ba mutum bace duk gidan Nan wa ya Kama kafata a kyau? Nafi kowa kyau za a rainani,gwara ma su Gyara halinsu in ba Haka wlh Ni ba mutunci na sani ba.

Zasu gyara tashi mu shiga ciki ki shirya kinji Zan yiwa Mama fada cewar Baffa,yo wani Jin fadanka zatayi Baffa Bayan ka zauna ta rainaka,da kansa ya mikar da ita tsaye sannan Suka shiga ciki.

Doguwar rigar Atamfa tasa red an green tayi kyau Amma sai ta Bata Fuskarta da wata shegiyar kwalliya tare da dambara jambaki,Daurin Dan kwalinta ka rantse Bata taba zuwa birni ba ko da wasa,Kamar Bata ganin film a waya ta dan rage duhun Kai,ganin Husna ta Gama birgewa ta fito Palo tana yanga,Ya Kb Yana zaune Yana kallon Ball,Nusaiba da Aliyu suna gefensa sai ko sukayi Arba da Husna ta fito tana yanga ko kallo Basu isheta ba ta ficewarta tsakar gida,Dariya ta kamasu Suka kwashe Mata da dariya tana jinsu sai ta dawo zuciyarta ta baci,idan wani Abu tayi marar kyau ai sai su Gyara Mata Amma ba Wanda ya gyara Mata sai dariya.

Nusaiba ta Fara shararawa Mari,ta saki ihu tare da dafe kumatu,Kan Aliyu tayi ta rufeshi da duka iya karfinta da kyar ya kwaci kansa ya gudu yana kuka sabo da Husna akwai karfi komai da jikinta takeyi bil hakki,tana Huci ta dawo ta kalli Kb tace kaja girmanka Ya Kabeer wlh zan iya zaginka watarana dan kawai ka girmeni ne na baka girmanka, Daga anyi dariya wa yace kiyi kwalliyar Haka wallahi yar kauye ce ke Anty Husna cewar Nusaiba,Husna ta Kara harzuka ta shaki kwalar rigar Nusaiba ta tsargeta gida biyu,Nusaiba sai Vest a jikinta, Kb ne ya mike tare da damkar Husna ya fesa Mata mari ya kai biyar sannan ya jefar da ita a kasa,Kuka ta kwalla da karfi iya karfinta Wanda yasa Mama da Baffa suka fito ba shiri.

Me ya faru? Baffa ya tambaya Kb ya kwashe duk yanda akayi ya fada musu,Mama ta kalli Husna tace to Mene Dan an Miki Dariya kalli yanda Kika Bata fuskarki Husna kin kalli kanki a mudubi kuwa? Mutum ce kuwa Husna? Cewar Mama, A'a ku kyale min Yar Yafendo tayi kyau sosai cewar Baffa ya furta Yana Jan Hannun Husna.
Shuru Husna tayi ta daina kuka sai Masifa takeyi ita kadai tana daga zuwa na birni,Ni sai an maidani Kauye yafi Dadi acan sai abinda nake so nakeyi Nan gaba Daya takura ne.

Washe gari Husna ta Saba tashi da Asuba Haka ta tashi tayi Sallah gari Yana yin shaaaaa ta fito palo,lokacin kowa Yana bacci ba Wanda ya tashi,sun Saba da tashin safiya da gaishe da mutane,dakin Mama ta nufa ta shiga buga Mata kofa,bacci me Dadi takeyi ta tashi da kyar ta bude Kofa sai taga Husna ce ta duka tare da cewa Ina kwana An tashi lafiya? Ina Baffan? Yunwa nakeji Ni,Harara Mama ta watsa Mata a fili tace an cuceni wlh sai da aka lalata min yarinya sannan aka dawo min da jangwam, sai kije dakin Baffan Yana can,Abinci Kuma mu bama Karin sassafe anan,Bata ce komai ba ta wuce dakin Baffa Yana ta lazimi ta shiga ta zauna a gefensa tare da gaishe da shi ya amsa da sakin fuska,Husna ya bakunta? Baffa yunwa ce zata cinye min hanji na birni Babu Dadi Baku iya rayuwa ba,Murmushi Baffa yayi tare da cewa ai kin iya girki jeki kitchen ki dafa abinda kike so kici.
Husna ta mike da sauri tace Baffa ban iya kunna abin girkin ba,Kuma Ni dumamen tuwo nake so naci, Baffa yace to kiyi hakuri Mama ta tashi sai tazo ta baki, to kawai Husna tace ta fito ba a son ranta ba ta koma Dakinta ta kwanta tana ta Jin yunwa,sai karfe goma taji kamshin girki,Bata ko leka ba sai da taji hayaniyar su Nusaiba sannan ta fita taga kowa yaci kwalliya sunsha wanka,ita kuwa tun kayan jiya ne a jikinta dasu tayi bacci,Mama ta kalleta tace maybe ma da kayan Nan kikayi bacci ko? Akwai kayan bacci a cikin kayanki shashasha,Baki Bude Husna tace yanzu baccin ma sai an Masa kayan sawa? Don fitina ace bacci sai kasa wani kayan cab.

Ba Wanda baiyi dariya ba,Sai taga Kb Yana Fitowa harda rungume juna shi da Nusaiba,Husna ta tabe Baki tace mu idonmu da raba,Kb ya Bata amsa da namu a bushe yake mu.

Saida ta zauna taga abinci na Yan gayu,su kwai dankalin turawa etc kala kala gasu Nan,shi yasa kuke kyau kuna ja,jikinku lukwi lukwi gaskiya an Dade Ana cutata ,kwai ta dauka tare da sawa a bakinta Bata hadiye ba ta fito dashi,kowa ya zuba Mata Ido tace wannan wacce irin suya ce Haka Bai soyu ba duk karni,Ni bazan Ci wannan girkin ba kyankyaminsa nakeyi a bani dumamen tuwo naci abina.

Mu a nan bama cin Dumame idan baza kici wannan ba sai dai ki yini da yunwa,Baffa baice komai ba kowa cin abincinsa yakeyi Saida taga Allah ba Wasa ba ta Fara ci itama tana mita wannan Abinci ba Dadi sai asarar kudi ba Gwara girkin Yafendo ba, Abinci kamar na Yan fursuna,wani dankalin turawa mu ba turawa ba, bakaken mutane Dan kwaikwayon abincin nasara ace abincin Nasara shima sai an kwaikwaya shi za aci,duk shigarsa da aka kwaikwaya ba a gode ba abincin ma sai na bature Allah kyauta.

Sai da Mama tayi Murmushi sabo da Husna abin tsofaffi takeyi sak tare da cewar Uhm goyon tsohuwa dama abinda na guda kenan sai da rayuwar yarinya ta lalace aka dawo min da ita sabo da Anga baza a moreta ba an Gama kashe Mata kuruciya,Baffa yaji zafin Maganar Mama yasan da Yafendo Yar uwarsa take Amma Bai ko ce kala ba.

Husna ta mike Bayan ta cika cikinta tace ke Nusaiba Bari nayi wanka na cakare ki rakani na zaga unguwar Nan zuwana Birni Biyu Hutu ban taba leka ko kofar gida ba yanzu kuwa na dawo gari da Zama Dole nasan lungu da sako sabo da na dinga Shan kallon Duniya.
Tasan Masifar Anty Husna da sauri Nusaiba tace to Anty Amma a zuciyarta kunya take ji yawo da Husna a kalli Husna ace yayarta ce tab sai dai ta daure ga kawayenta Yan Unguwa da gidan masu Hannu da shuni suna zirga zirga Uhm zata ji kunya.

Baffa ne ya katse Sake saken Nusaiba da ki tabbata duk abinda take so kin Mata wlh naji kin rainata saina Saba Miki,kamar ba jininku ba Dan kawai ta girma a kauye,ay kamata yayi ku dinga nuna Mata yanda zata Yi kwalliyar ba ku dinga Mata dariya ba bayan kun kasa koya Mata,kaima kasan Husna wa ya Isa yace Bata iya abin duniya ba ko girki fa Bata iya komai ba cewar Mama, Baffa ya nisa yace sai hakuri Ana nusar da ita,ke Nusaiba jeki ki koya Mata kwalliya indai ba so kike ta kunyata ki ba cewar Mama.

Jiki ba kwari Nusaiba ta shiga dakin Husna ta Iske Husna tana wake wakenta na kauye a hayye nanaye soriyal, Zani ta daura tare da shigewa ban daki mamakin Nusaiba da taji kafin Husna ta shiga bayi sai da tayi adduar shiga bayi sannan ta shiga Wanda ita kanta Husna ta manta rabonta da tayi adduar shiga bayi, ta Dade a bayin sannan ta fito har Brush ta karayi domin Husna sai tayi Brush sau hudu sau biyar a rana Yafendo tayi ta Mata fada akan ta dawo Yi sau biyu safe da dare Amma taki yarda.

Tana Fitowa tayi adduar Fitowa a bayin,Nusaiba sai kallon Husna takeyi ba ko kyafta Ido sabo da tsananin kyan Husna skin dinta ta dabance, mayuka masu kamshi da sauran Kayan kwalliya duk Mama ta zuba Mata saman mirror Amma dake ba a Mata gwaninta sai tace ke Nusaiba dakko min Aron manki na shafa, Baga naki ba duk fa Sai da aka siyo Miki komai, bakin ciki kike min kenan munafuka Dan Kar nayi kyau ai ba kaunata kukeyi ba nasan baza ku siya min masu kyau ba,Amma Bari na shafa wlh idan nayi sati daya ban canja na Kara kyau ba sai na kwashe naki gaba Daya, ae na yarda cewar Nusaiba,tana zaune Husna ta dangwalo Mai sau Daya a hannunta Dan kadan ta murje jikinta gaba Daya Wai ya isheta ta Gama shafawa kenan,Nusaiba ta hangame Baki tace yanzu wannan ko bayan Hannu bazai isheshi ba Amma dukka jikinki Anty bafa Haka akeyi ba,rufe min Baki Dan Uwarki har kin Isa ki koya min abin duniya ke nifa nafiku sanin harkar gayu kawai banayi ne so nakeyi Naga iya karshen gayunku sannan ku Fara ganin nawa,ki Bari na shiga makaranta Zaki Sha mamaki.

Bayan ta Gama shafa mai ta Buda kayanta harda su bra kanana size nata,dariya tayi ta daga Daya tace breziyya kawai na kwaso abuna na zuba a cikin Nan wlh ba ruwana bazan sata ba,vest ta saka sannan ta zabo doguwar rigar bacci tace ita take so tafi kyau, da Kya Nusaiba ta lallabata ta Bata Arabian Gown me kyau Dark blue da mayafinta,Husna gefe ta koma tana yiwa Nusaiba Habaici Wayis (wise) Wai ku wayayyu a Haka tasa rigar,kyan da Husna tayi ba a magana, Nusaiba gefe ta koma tana kallonta sabo da kyan Husna me gigita Dan Adam ne,Zatayi kwalliya Nusaiba tace Anty Dan Allah ki rufana asiri mu tafi Haka, Harara Husna ta watsa Mata tare da furta Yar bakin ciki Dan Kar na Samu saurayi baki Isa ba yarinya ke nifa ba sa'arki ba bace,jikin Mudubi ta zauna ta lalata Fuskarta da wata mahaukaciyar gira da Jan baki ,tace kwalliyar yau ta dabance Bari ki gani ta zana katon Fashin goshi ta juyo tace ya kikace? Nusaiba tace normal,Ke Kika San wani Namal(normal) muje Ni yau birni Sunyi Baki.

Nusaiba Kamar zatayi kuka suka fito Mama tana gani tace ke Husna wacce hauka CE wannan? Koma ki goge da gudu tayi waje abinta Dan baza ta iya goge wannan gayun data yi ba,Ba yanda Nusaiba ta iya Haka ta bi bayanta sanye cikin Atamfa Riga da skert tayi kyau da mayafinta.

Tafiya sukayi me nisa Husna tana ta kalle kalle tana washe Baki tana Wai Wai Kai... kalli Nan wayyo Nusaiba Dan ubanki kalli wani gida,kalli wani Dankareren gida harda fulawawoyi, Nusaiba kunya ta Gama cika ta,Sun shiga dai dai wani layi na masu kudi dai dai lokacin Farhan ya shigo Kano a jirgi ya dawo wedding dinner jiya Kuma Yazo Daurin aure ya koma Abuja yau ya dawo.

Ana ta biki a wani Dankareren gida na Alfarma Yan Mata da samari suna ta sintiri Farhan ma motocinsa Suka wuce fuuuuuuu ta gaban su Nusaiba, Husna tabisu da kallo tace wlh na ganeshi mutumin jiya ne me Sa'a ne, ga motarsa can Nusaiba dama Ina so na Karasa Masa labarin jiya Yaya kb ya hanani muje na Karasa Masa,Nusaiba tunaninta shirmen Husna ne Ina tasan wannan Hamshakin me kudin har zai saurari labarinta na haukar kauye,a fili Nusaiba Dan ta kure Husna sai tace gaskiya Anty gashi can ma gidan da ake Dj din can zai shiga da Alama biki sukeyi muje na rakaki,a ran Nusaiba tana Allah yasa ya Zane Husna kowa ya huta.

Falauuu falauuu Husna ta wuce gaba tana kiyi sauri Nusaiba Kinga motocinsa zasu shiga gidan na kasa Samunsa,Aiko dake mugunta Nusaiba ta tsarawa Husna sai ta Fara sauri sauri gudu gudu,.
Yan biki sunga Husna da Nusaiba Tunaninsu Yan uwan masu gidan ne suka zo daga kauye, Nusaiba kowa ya ganta yasan Yar birni ce Amma suna Dan Kama da Husna sai dai Husna da kauye a jikinta ta Gama Bata kanta da kwalliyarta da Kuma yanda take Abu, Kamar gidan Ubansu Suka shige cikin gidan,Husna tana gaba dai dai lokacin Securities sun budewa Farhan mota ya fito ya zuro kafa daya Amma Yana ta Izza a ciki yaki Fitowa Yana latsa wayarsa me tsadar gaske, kamshinsa ya cika wurin me dadin tsiya.

Wani takalmi ne me shegen tsada da kyau kafar wandonsa kawai zaka gani kasan kudi ya zauna Masa, sanye yake cikin Seablue shadda Tasha dinki na masu kudi na manyan Yara masu tashe,hannun links komai cif cif shi,Dan Gaye ne na bugawa a Jarida,kyau kuwa Kamar shi yayi kansa Fari kar, hanci da fuska me kyau, komai me kyau ga Naira.
Gajiya Husna tayi yaki Fitowa ta Nufi motar.









AsmaBaffa.
[2/29, 10:44 PM] Sis Asma: πŸŒ…πŸŒ…RASHIN SA'AπŸŒ…πŸŒ…









4








Official







By
AsmaBaffa







Mmn Mubeen
Maryam
Sa'adatu kebbi &
Fatima Musa
Page nakune Allah ya bar kauna.












Koda Securities din Farhan Suka lura da Husna zata Isa ga Ogansu tayi musu asarar hanyar Samun abincinsu sai suka yi sauri Suka tareta suna muzairai Kamar zasu masgeta tare da daka Mata tsawar data razanata Wanda yayi sanadiyyar sarawar Kan Farhan da sauri ya dafe Kai Amma baiyi magana ba,Husna tsoro ya kamata Kamar zatayi fitsari,jikinta ya Fara rawa karrrr, Nusaiba kuwa da gudu ta juya bakin gate ta tsaya tana kallo.

Yan Mata masu aji sun San waye Farhan da sauri kallo ya dawo Kan Husna ana ta dariya har da samari matasa masu ji da Kai suka Shiga dariya suna yarinya ta kyasa ta kasa jurewa, Mata Kuma suna taga kudi da kyau anzo ohhh Ashe Yan kauye ma Haka suke da karfin hali da Rashin kunya,idan ba rashin kunya ba kamar wannan kucaka tace zata je wajen Farhan yaro me tsada Haka Wanda ko Yan birnin ma masu class basa kusantar Farhan Dan ko kallo Baki isheshi ba,Nan fa aka shiga dariya Ana sauti Yana fita.

Kunya ta Kama Husna tayi matukar muzanta taji ba Dadi,anci Mata fuska Kuma an wulakantata Wanda tayi Dana sanin zuwa gidan Dan Bata son wulakanci,Nusaiba kuwa Kamar ba Yar uwarta ba tana gefe tana ta dariya,Farhan Yana Jin duk abinda akeyi Bai san wace ma tazo wajen nasa ba shi, hakan yasa ya fito daga motar, guard nasa ya rufe Motar,sauran Securities Suka taho suna take Masa baya Yana gaba,ko kallon Husna baiyi ba Bai ma San Allah ya halicci mutum ba,Sai wani ne cikin securities Wanda yana da Dan tausayi yace Sir ko kasan Waccen? Sai lokacin Farhan ya kalli Husna kadan ya tabe Baki,sai Kuma yaga Kamar ya taba ganinta Amma ya rasa a Ina ya santa,mutane suka Kara kecewa da dariya Ana ta kallon Husna irin karuwar kauye tazo birni zata gwada sa'arta amma anfi karfinta.
Da Kai Farhan ya musu Alama da a tambayeta me ya kawota wajensa ko taimako take nema? Security ya tambayeta baiwar Allah Sir Yana jinki me kike so ko taimako kike so? Mutane sai dariya hhhh again, Husna takaici ya cikata sai ta danne zuciyarta tace da Security ka fada masa wacce Suka hadu a titi ne wacce ta leko ta motar yayanta Husnan Yafendo wacce ta dawo Birni itama,Ina ta bashi labarin irin dakikantata a aji Yayana Dan bakin Halinsa ya dukeni ban karasa Masa ba,shine na ganshi yanzu a motocinsa ya wuce nace Bari nazo na Karasa Masa,Kace Masa me Sa'ar rayuwa ne shi, Farhan Yana tsaye Yana Danna waya Amma Yana saurarar Husna tana cewa me Sa'a ya tuno data mota me tabin kwakwalwa sai yanzu ya gane tabbas itace Kuma Muryarta ce.

Amma kamar Aljana ta iya ganeshi Kuma har ta biyoshi Dan jaraba,yayi niyar shareta sai yaga mutane Mata da maza suna ta Mata dariya Ana sa Mata Ido da kuskuskus, Bayan Haka ga irin maganganun da suke Yi akanta Yar kauye etc Dan Allah ya ajiyeta acan idan da sune a inda take fa, Husna Kuma a ranta tana Adduar Allah ka rufa min asiri,Allah karka Bari naji kunya duniya da lahira,Allah Kar ka Bari ya wulakantani,ta rufe Ido tana ta fada a boye, ga mamakin kowa sai suka ji Farhan a nutse cikin muryarsa me dadin saurare wacce ba kowa ke jinta ba yace Let's go, Wai sai kallo da mamaki wata Yar gayu tace Farhan din da ko kai waye sai dai kuyi magana da Securities nasa su fada Masa.

Su kansu Securities Sunyi mamakin Ogan nasu Jin yayiwa Husna magana da kansa,Bata Jin turanci Husna tace Me Sa'a ko A ban sani ba da turanci, bana jin turanci gwara ma ka min Hausata ance maka kowa irinka ne me Sa'a a duniya.
Bai kalleta ba da kyar Kamar Wanda aka yiwa Dole ya furta Muje nace,Da Sauri Daya security dinsa yace Muje Hajiya kinyi goshi,Husna ta washe Baki tare da cewa laaaa Kai banfa je Makkah ba,karka Kara cewa Dani Hajiya Allah,ban iya karya ba,yaushe naje makkan zaka ce wani Hajiya,ganin Farhan ya Fara tafiya tayi sauri ta iskeshi tare da jerawa dashi tace da securities albarkancin kaza kadangare Kan Sha ruwan kasko ku take min baya Nima na dangwali arziki.
Farhan ko inda take Bai kalla ba waya ma yakeyi da Abbinsa suna ta zuba turanci,Husna tana ji tana ta washe Baki tana kallonsa da sha'awa Kamar da ita yake wayar, Dan Murmushi ya saki Sai ji akayi Husna tace Uhmm Kyakyawan duniya Iyyeee.

Farhan Yana jinta suna ta tafiya tana binsa Kamar kanwarsa ta juya baya ta kalli masu take Masa baya tace bakwa aikinku yanda ya Dace ku jeru sosai sai wani ya harbo Mana bindiga ko kibiya ta coke Mana ciki kuce tsautsayi ne Kuma ku Fara bada hakuri.
Dariya ta bawa Guards din gaba Daya da kyar suke iya dannewa.
Farhan ma ta sashi Murmushi kadan,Wani matsiyacin Palo Suka isa Wanda ya gaji da haduwa,wasu manyan Mata ne a ciki masu ji da Naira, Da Sauri Matan suka Fara magana Farhan sai yanzu ka Iso Kai da Ummanka tace tun safe zata Koro Mana Kai ka dawo,Murmushi yayi kadan sannan da kyar ya iya furta na tsaya wurin Frnds ne,Ina Ango Imran? Suna sama da abokai jeka huta a kawo ma Abinci.

Ok ya Furta kawai,Cikin Matan wata tsohuwa ta kalli Husna tace Yar Nan lafiya? Ko kema a bikin Nan Kika zo ban sanki ba,Husna ta danyi Murmushi sannan tace Makwafta muke daku shine Muka zo Muku biki,Allah sarki sannu Yan mata wannan kwalliyar duk ta bikin ce? Husna tace A'a ba taku bace akan bikin ku zanyi kwalliya Haka?,nifa da bazan shugo bama sabo da duk Yan bikin Nan Basu da mutunci,abokina na biyo me Sa'a shi yasa ma Kuka ganni, Matan Nan Suka ce ikon Allah,To zauna ga wuri cewar wannan tsohuwar, Zama Husna tayi a Daya daga cikin kujerun Suka nutse da ita wani laushi Bata San sanda ta lumshe Ido ba ga sanyin AC sai kawai bacci ya kwashe ta ba tare data sani ba.Matan Nan Suka cika da mamaki da dariya.

Nusaiba matsoraciya tana can Compound tana ta faman jiran Husna,Farhan Bai San Ina ta Yi ba,,ya ma manta tare suke da Me tabin kwakwalwa,wurin Angwaye ya Isa suna Hira daga Nan ya shiga Bedroom masaukinsa yayi wanka lokacin an kawo Masa Abinci na Alfarma iri iri yaci sannan yayi Sallah ya fito wurin Imran Ango da abokai,Husna ta dan Dade tana kwasar bacci abinta kafin masu Shirin Dinner su farkar da ita ta shiga Neman Nusaiba lokacin Nusaiba ta gaji tayi tafiyarta gida ga Husna Bata San hanyar gidansu ba,da gudu mutane suka ga Husna ta fice,sai da ta Gama zaga layin Bata gano hanyar gidansu ba,Dole ta koma Gidan bikin tana rasgar kuka wiwi.



Nusaiba tana gida tana mamakin Husna Babu tsoro ba komai,Kuma gashi tayi nasara Ana ta kallonsu anan ta sarawa Husna tayi kokari ta Nan fagen don su tsoronsa suke ji ma.
Karya Nusaiba tayiwa Mamansu da Baffa tace Husna tana Nan shigowa ta tsaya siyen Agwalima a jikin gidansu,a zuciyarta Kuma murna takeyi Allah yasa Husna ta bace Tasha wahalar gano gidan ai daga yau baza ta sake cewa ta Rakata yawo ba.

Shuru Shuru Husna Bata dawo ba,Mama hankalinta ya tashi Haka Baffa ma suka shiga Neman Husna gida gida lungu da sako Babu labarinta,Nusaiba Kuma Taki fadan gaskiya tace ai ita a bakin gate ta barta zata siyi Agwalima maybe daga Nan tayi wani wajen. Mama ta kalli Nusaiba hankali tashe tace ki fada Mana gaskiya Nusaiba Dan Allah,Nusaiba tace Allah da gaske nakeyi Mama,Zama sukayi gaba Daya gidan sukayi jungum jungum har anyi sallar Magrib Husna Shuru ko Abinci ba Wanda yaci.
Daga Nan Kara ficewa sukayi nemanta Har Nusaiba munafuka tana kukan karya.

Husna kuwa tana gidan bikin taci ta koshi Ana ta Shirin Dinner Ana daukan wanka,tsohuwar Nan wacce suke Kira da Inna tace Yan Mata baza a nemeki a gida bane? Husna ta fashe da kuka tace Da Kanwata Muka zo Nusaiba ta tafi gida ta barni bazan iya gane gidanmu ba,Kuma Ni jiya aka dauko Ni daga kauye na dawo Birni da Zama sabo da bani da kokari a makaranta.
Murmushi Inna tayi tace to ai ba abin damuwa bane tunda tasan kina Nan Dole zata zo ta tafi dake,gaki Kyakyawa Kinga party za aje na biki kema da Zaki shirya sai aje dake, Husna Tasha Jin kalmar party Amma Bata San me akeyi a party din ba tunaninta ma wani gari ne party, tace zanje na kalleshi Nima ban sanshi ba.
Inna tace to zo muje toilet na kiyi wanka kema kiyi shiri Kamar kowa sai mu tafi dake,da sauri Husna tabi bayan Inna tana gaskiya Inna kirki ne dake duk birni Babu kamarki kece shugaban masu kirki ta birni Baki daya,dariya Inna

Please Login or Register in order to submit comment